TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 46

 *BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS (46)*

*Abuja..*

HANAM POV.

“Kinga gaskiya wannan yayi duhu, dan wallahi mu baƙaƙe ba zai mana kyau ba”

Hafsi ƙanwar Kamal, wadda take yaya a wajen Hanam ta faɗa, suna zaune ne ita da Hanam, Na'ima, Zainab, Ummu kulsum, Mariya, Rahina, Firdaus, Hafsin kanta, Rafi'a, Nabila, Kamila, fatima da Aisha a babban falon gidansu, yayin da suke zab'ar kalar lace d'in da zasu saka ranar bikin Kamal dan shirye-shiryen bikin suke.

“Anti Hanam wallahi gaskiya yaya ta faɗa, duk gidan nan babu wanda blue color kewa kyau sai ke, tunda kinga mu gaba ɗayan mu baƙaƙe ne”

Cewar Nabila, Hanam ta tura hoton gaba, wani ya shigo a cikin ipad ɗin.

“Wannan fa ?”

Ta tambaya tana nuna musu.

“Yauwwa, ai gwara farin, shine zai hau da kalar jikin mu”

“Kema de Nabila da wani abu kike, yanda kike ta magana a kan baƙin fatar nan taku sai kace wani shuni”

Gaba ɗayansu suka saka dariya.

“Ai maganar gaskiya ce, kaf gidan nan waye me hasken fata ban da ke ?, sai wannan yarinyar da ta shiga shago ta siyo”

Rafi'a ta faɗi tana ɗakawa Mariya duka.

“Rafi'a bana san iskanci, ni na hana wata cikinku shiga shago ?, kuma idan kuna san farin ku shiga mana”

“Allah stirbiƙui inji kishiyar me doro, Allah tsare mu da shafa mai, ke baki san baƙin fatar mutum yafi kyau ba ?, me ake da wani mai”

Rafi'a ta bata amsa.

“Anti Hanam wai ina Aryaan ne ?”

Aisha ta tambaya, Hanam ta yi murmushi.

“Arya yana Cairo, jibi ma zanje na ɗauko shi, dan bana so a yi bikin nan baya nan”

“Ai kuwa gwara ya zo mu ganshi ”

Wayar Hanam ɗin ce ta yi ringing dan haka ta kai hannu ta ɗauka 'Benidita'.

Har da saurinta ta miƙe ta bar falon sbd hayaniyar da suke, a ƙofar shiga falon ta tsaya, sannan ta ɗaga wayar.

“Ya ya mijin ki?”

Benedita ta tambaya a sanda suke gaisawa, Hanam ta yi murmushi tunowa da shi da ta yi, shine da kansa ya kawota gida, sannan yace mata zai je ya karb'o musu visa ɗinsu.

“Yana lafiya”

“Kira na yi na sanar miki dama, kinsan Gebriel ya mutu....”

Duk da akwai hasken rana a wajen, Amma sai da Hanam taga kamar wata walkiya ce ta haskota daga sama, bakinta a sake kuma yana rawa ta furta.

“A garin ya ya ?”

“Guba suka sha shi da matarsa, wai dan sbd sun haihuwa, yanzu fa shine labarin dake tayawo a new york baki ɗaya”

Hanam ta damƙe ƙarfen balcony, dan ƙoƙarin faɗuwa da take, ba wai tausayinsa take ba, ba kuma haushi ta ji dan ya mutu ba, kawai de zafin rasa rai ne ya dake ta, haka kuma koda ta ruɗi kanta cewa shi ba baban Arya bane ta sani cewa shi ɗin ne baban nasa, amma, ba musulmi banr, bata san wata kalar addu'a zata masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, dan wata ƙila hakan ne mafita.


*RNo.202,Taj Skyline Hotel, Ahmedabad, India*

*09:30am*

ESHAAN POV.

Zaune yake a kan wata sofa, hannunsa riƙe da littafin Aakhoki Gustakhi, wanda Saree ya rubuta, littafin yake karantawa, yayin da yake jiran fitowar Maryam da ga banɗaki, so yake ta yi sauro ta fito su tafi, dan yau za'ayi final, kuma wasa ne tsakanin India da Australia.

Sannan yana sa ran a gobe zasu wuce Delhi, dan jibi ne ɗaurin auren Mahesh abokinsu.

Tunaninsa ya katse tare da karatun da yake, a sanda Maryam ta fito daga banɗakin sanye cikin chickankari, rigar orange color ce, kuma ta sauƙo mata har kan guwa, yayinda wandon ya kasance fari, kuma wandon yana da faɗi, ta yafa farin mayafin kayan a kanta, ta rataya shi zuwa bayan kafaɗarta.

Ƙafarta sanye cikin fararen boots, kamar kullum fuskarta babu kwalliya, amma shi a hakan da take tafi masa kyau, dan yafi san ya ganta a yanda take, haka ɗin nan nata, dan hausawa sunce wai dai-dai ɗin wani, karkattaccen wani. Litafin ya rufe tare da aje shi a kan coffe table, ya miƙe yana shafa sumarsa.

“Kin shirya?”

A hankali ta gyaɗa masa kai.


*Narendra Modi stadium, Ahmedabad, India*

*12:00pm*

Hayaniyar masoya da kuma magoya bayace ke tashi, sai kuma masu bayyana yanda wasan ke kasancewa, gaba ɗaya stadium din cike take maƙil da mutane, daga tsakiyar fili kuma ƴan wasan india da na australia ne ke fafatawa, dan yanzu haka ana zagayen ƙarashe ne.

Daga cikin kujerun ƴan kallo, akwai ta Eshaan da Maryam, wanɗan da suka zuba ido suna so suga yanda wasan zai kaya, a farkon fara zuwansu wajen babu abunda Maryam take ganewa a wasan.

Amma a hankali a hankali ta fahimci kan wasan, kuma kamar Eshaan itama tana fatan ace india ce ta lashe wasan, dan yanda ta ga indiyawa nasan wasan cricket idan suka fad'i wata ƙila Ahmadabad ta kama da wuta.

Wajen ya yi wani irin shiruu, kamar mutuwa ta ratsa, kamar da ba wajen ne ake ta hayaniya ba, sun yi shirun ne saka makon Rohit Sharma babban ɗan wasa india, da ya riƙe bat a hannunsa ya ɗau matsayarsa yana jiran Jones ɗan wasan austrelia ya cillo ƙwallo.

Jones ya ɗan ja da baya kaɗan, kafin ya tako a guje, kuma yana zuwa tsakiyar filin ya cilla ƙwallon, wani irin duka da Roshi Sharma yayiwa ƙwallon saida ta fita daga ginin stadium ɗin.

Kamar magoya bayan india jura suke, sai suka saka ihu, ana tafi ana fito, india taci wasa, bakin Eshaan kamar ya rabe biyu dan tsabar murna, Maryam ma ta taya su murna sosai. Da a wajen su abun farin ciki ne sosai, dan indiawa na martaba wasan cricket.


*Cairo Internacional airport*

*05:40pm*

HARNAM(Harees and Hanma) POV.

A tare suka fito daga cikin terminal, yayin da Haris ke riƙe da jakukunansu, gaba ɗaya hanam ta ƙagu taje taga Arya, so take taga yanda ya sauya, dan tana da tabbacin ya sauya sosai.

Haris ne ya tsare muasu taxi, sannan suka shiga, kai tsaye Acasa Mia suka nufa.

Ta ta haddace address ɗin gidan, dan haka taxi na sauke su ita ta fara shiga gidan.

“Aryaan?!”

Shine abinda ta fara faɗi, a sanda idanuwanta suka gane mata shi suna wasa shi da Al-amin,Salwa da Khalil a garden ɗin gaban gidan.

Da gudu ta yi inda suke ta sure shi tana rungume shi, kafin ta dago shi daga jikinta tana kissing face ɗinsa, ta yi kewarsa sosai, fiye da yanda baki zai iya furtawa.

Jikinsa tabi da kallo tana ganin yanda ya sauya, bakinsa taf cike da haƙwara, girma ya ƙara bayyana a tare da shi.

“Arya Ammi ta yi kewarka”

“Ammi ?”

Cikin gwarancinsa ya furta hakan, Hanam ta yi dariya tana sake rungume shi.

“Eh Ammi, Amminka ta yi kewarka”

“Papi ma ya yi kewarka”

Ta juya ta kalli Uchenna dake bayansu, hannu ya kai ya karb'i Arya daga hannunta yana rungume shi shima, sai a sannan ta dawo kan ƴan ƙanenta data ga a wajen, ɗaya bayan ɗaya tabi ta rungume su suna gaisawa da ita.


*09:30pm*

“Bani ɗayan”

Muryar Masarrat ta faɗi, a sanda suke tsaye a kitchen ita da Hanam. Hanam ta ɗauko plate cike da cabbege ta miƙa mata.

Saida Masarrata ta juye cabbege ɗin, sannan ta rufe pot ɗin, ta jiyo ta kalli Hanma.

“Ana biddi ahki ma'ak bi maudu'u daruri”

(Ina so nayi magana da ke akan wani abu me muhimanci).

Hanam bata ce komai ba sai ci gaha da kallonta da ta yi alamu ina ji.

“Waye mahifin Arya ?, dan inada tabbacin cewa Harees ba shine mahaifinsa ba”

Bisa ga manakinta sai taga Hanam ɗin na murmushi. Dama sai da ta ayyana hakan a ranta, tasan cewa dole zata tambaya.

Sai kawai ta ɗago da hannayenta ta sunkiyar da kanta tana kallonsu, yayin da ta haɗesu waje guda tana wasa da su.

“A sanda naje New york wani aiki, na haɗu da wani, kuma shine yayimin fyaɗe, har na samu cikin Arya”

Kalaman basu da yawa, amma kuma sun yiwa Masarrat nauyi a ka, gani take kamar ko wani ƙunci da ya faru a rayuwar Hanam itace sila, kamar duk wata damuwa da Hanam ɗin ta shiga duk ita ta ja. Nan da nan ta fara hawaye, Hanam ta ƙarasa kusa da ita sannan ta rungumeta tana shafa bayanta.

“A'a Ammi, ba kuka za ki yi ba, komai ya wuce yanzu, dan Allah ki dena saka damuwa a ranki”

Kafin ta saketa, Masarrat ta kai hannu ta share hawayenta, sannan ta dafa kafaɗar ta.

“Allah ya miki albarka, muje muci abinci, zuwa gobe zaki zaga dangi”

Hanam na murmushi ta ɗauki wani bowl ta fita, a falo ta same su duka suna hira.

“Yauwwa abinci yakammala, wallahi yunwa muke ji, ya yi kyau yarinyata, Allah ya miki Albarka ”

Dr. Taiyyab Abu Al-aminya faɗi, Hanam ta yi dariya, dan mutumin yana da kirki, kamar Abbanta, Abbanta ?, a ranta ta yi masa addu'a kamar yanda ta saba a duk sanda zai shigo cikin tunaninta.

A hankali ta juya ta kallesu su duka, Abuya kamar yanda ta ji su Al-amin na faɗa masa, Harees, Arya, Al-amin, Salwa da Khalil dukan ninsu suna cikin farin ciki.

A da ita kaɗai take rayuwa, daga ita sai Abba, bayan Abba sai Arya ya zo, daga shi kuma sai ga Harees, wanda zuwansa ya zama sanadiyyar shiryawarta da mahaifiyarta, bayan kuma ta shirya da mahaifiyar tata sai ta samu ƙanne harda mahaifi.

A cikin ranta ta godewa  Allah, a sanda ta tuna abinda Abba yake faɗa mata a kullum.

_ “Bayan wuya sai daɗi Bannute”_

Haƙiƙa baka ne, bayan wuya sai daɗi, dan a yanzu tajita a matsayin cikakkiyar ƴar adam, ta samu komai, babu abinda take nema, kewar Abba kaɗai ta dameta.


*No.803, Tolstoy Rd, New Delhi, India*

*05:00pm*

MARYAM POV.

Zaune take daga kan wata sofa, ta yi tagumi tana bin ƴan matan wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, yaren hindi suke wanda ita sam bata fahimta, ko magana za ta yi da su saide ta musu da turanci, su kuma su amsa mata da turancin nan nasu dake bata dariya.

Tun safe take tare da ƴan matan, waɗanda suka kasance ƙawayen amarya Komal, kamar yanda Eshaan ya faɗa mata sunanta. 

Dan jiya suka sauƙa a delhi, kuma ya faɗa mata cewa yau za'a ɗaura auren abokin nasa, shi yasa suka taho tun safe, ya danƙata a hannun amaryar shi kuma tun bayan nan bata ƙara ganinsa ba.

Sai biryanin da ya aiko mata dan yasan ita ba komai take iya ci ba, sai laddu ɗin da sukai ta bata. Hayaniyar ƙawayen amaryar ta cika mata kunne, dan yanzu haka amarya suke shiryawa.

Sai kawai ta ɗauki wayarta ta buɗe ta shiga message, kusan jarin mesages uku tana turawa Eshaan amma ba ya replying.

Dan haka kawai sai ta fito daga wajen ta aika masa kira, amma de kamar ɗazu bai ɗaga ba.

“Mts, ina ya shiga ne?”

Babu me amsa mata dan haka kawai sai ta meda wayar cikin jakarta ta ci gaba da kallon ƴan matan, kyawawa wanda babu ɗaya da zaka iya cillarwa a cikinsu, domin babu baya a cikin.

“Wow...., a ina kika si yi wannan saree ɗin”

Maryam ta juyo ta kalli budurwar, sannan kuma ta kalli jikinta, nan take tunanin ta ya dawo mata da abinda ya faru a ɗazu.

Tana zaune a bakin gado tana cin abinci, Eshaan ya shigo ɗakin hotel ɗin da suka sauƙa, hannunsa riƙe da wani kwali, yacemata saree ne a ciki, kuma nata ne, so yake ta saka.

Ta faɗa masa cewar ita fa bata iya ɗaura saree ba, shi kuma yace taje ta saka blouse da skirt ɗin tazo sai ya ɗaura mata.Yanda aka ɗaura saree ɗin nema bata san tunawa, dan yau d'an guntun hankalin da take ji Tafida ya bar mata shi seda ya zube, notukan kanta suka karasa kuncewa.

“Kin gane saree ɗin Krishan?, shine fa wannan wanda na taya a Metropolitan Mall, amma na fasa sbd tsadar da ya min”

Maryam ta kuma kallon ƴan matan, sannan ta ƙara kallon saree ɗin, jar kala ne, an masa ado da wasu golden stones, kuma yadin sa silk ne, hakan ke ƙara nuna mata tsadarsa, duk da ba wani sanin kan saree d'in tayi ba.

“Ba ni na siya ba, mijina ne ya siyo min”

“Aiko mijiniki yana sanki, saree ɗin ki kud'insa ɗaya da na amarya”

Maryam ta kalli sareen da ke jikin amaryar sannan ra kalli nata, kusan kallarau ɗaya ma, dan hatta da kalar blouse d'in iri ɗaya ce, kawai de yanda aka jera stones d'in jiki ne ya banbanta.

“...Kai ga tawagar ango sun iso...”

wata matashiyar budurwa da Maryam ta ji suna kira da Rakshi ta faɗi baki washe.

Ƙawayen amarya suka shiga gyarta, dan dama jama'a sun jima da fara taruwa, ita Maryam ba wannan ne ha dameta ba, duk da tasan cewa ba al-adarsu ɗaya ba, dole de ango idan zai zo wajen ya taho da abokansa, kenanan Eshaan na tare da su?.

Ba ta yi tunanin komai ba ta miƙe, ta ɗauki wayarta da wani golden mayafi ta yafa a kanta, dan bazata iya yawo kanta a buɗe ba haka.

Ta cikin tarin firmitsin jama'ar da suka taru a gidan tabi har zuwa bakin ƙofa inda take jiyowa kiɗe-kiɗe.

Waje ta ja ta tsaya tana kallon ikon Allah, ango da abokansa dama 'yan uwansa sun iso gidan, sai tiƙar rawa ake ana watsa kuɗi. Ga masu kiɗa suna aikinsu.

Cikin abokan ango ta hango Eshaan,sai daj shi ba rawar yake ba, tafi kawai yake yana fito.

Cikin tarin jama'ar wajen ya hangota a gefe, ba zai ce yasan daliliba, amma se yaga babu kowa a wajen, duk wannan hayaniyar da ke tashi a wajen babu ita.

Babu kowa sai itan da yake gani, sanye cikin red silk saree, me ratsin golden, wuyanta hannayenta da kanta dauke da jawellies, babu wata kwalliya da yawa a fuskarta. Amma kuma ta yi kyau, domin ta yafa wani golden ɗin viel a kanta.

A hankali ƙafafuwansa suka shiga takawa setin inda take, kallonsa take yayin da shima yake kallonta.

“Ina ka shiga Sundar ?” Muryar Maryan ta tambaya da ɗan ƙarfi ta cikin kiɗa da hayaniyar da ke tashi a wurin.

Eshaan ya lumshe ido sannan ya buɗe yana ci gaba da kallonta.

“Kinyi kyau Wifey”

Sai ya faɗi hakan me makon ya amsa mata tambayar da ta masa. 

Me ?, ɗazuma fa sai da ya faɗamata hakan, me yasa yanzu ze sake ?.

“Mu shiga ciki, za'a fara gudanar da ɗaurun auren ”

Muryar sa ta faɗi, ta cikin hayaniya da kiɗan dake tashi a wajen, hannunta ya kama ya shiga janta har zuwa cikin farajiyar gidan inda za'a gudanar da ɗaurin auren.

A kijerun gaba suka zauna, har yanzu idonsa a kanta ya kasa janyesu, hannunsa ya kai ya gyara nata zaman veil ɗin.

A lokacin kuma ango da ƴan uwansa suka ƙaraso wajen, har yaje ya zauna a wajen da aka tana da domin shi, Suwami ya shiga jero addu'o'i.

Kafin aka kawo amarya, itama ta zauna a kusa da ango, aka ci gaba da yin addu'o'i, sannan aka bawa ango red Tikka (wannan jan garin da matan auren ƴan addinin hindu ke sakawa a tsakiyar gashinsu, alamun suna da aure).

Ango Mahesh ya sakawa Amarya Komal tikka a tsakiyar gashinta daga gaba, sannna aka maƙo mangalsutra, (sarƙar aure). Ango ya sakawa amarya, sannan suka miƙe, mahaifin amarya ya zo ya ɗaure mayafin amarya dana kafaɗar ango, sannan suka shiga zagaya wuta.

A lokacin kuma aka shiga rabawa jama'a fure suna watsawa amarya da ango, yayina da shima Swami ya miƙe yana karanto addu'ar aure.

“Mangalan fagbani bishnu mangalan madradda shar, mangalin gundari fakshar mangala yatarobari......” Har zuwa ƙarshe.

Eshaan da Maryam suka miƙe a sanda suma aka miƙa musu fure suka shiga watsawa amarya da ango.

Maryam na watsa kamar kowa sai ji ta yi ita kuma ana watso mata, ta juya ta kalli Eshaan, yayin da kowa ke watsawa amarya da ango shi kuma ita yake watsawa.

Ta saba ganin irin wannan auren a Tv, yau gashi a gaban idonta tana ganin yanda ake ɗaura shi.




Post a Comment

0 Comments