TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 26

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*26*

~~~

*You ware using your ear to hear, and i am using my heart...*

***

*No.181, Guzape, Abuja...*

*10:11pm*

KULIYA POV.

_🎶I lost my way, somewhere in another galaxy_

_Too much to take, these memories end in tragedy_

_And all of these pleces , all of these faces, I didn't wanna let you down_

_And all these mistakes of mine I can't replace it, i gotta move on somehow 🎶..._

Waƙar dake tashi kenan a falon gidan. Daga can ɓangaren da kujerun gidan kuma suke, Kuliya ne durƙushe a gaban Mishal, wadda ke zaune a kan kujera, ya kama ƙafarta ta dama yabna saka mata safa, saboda sanyin da ake a gari.

Safar ya gama saka mata, sannan ya kai hannunsa ya janyo hular sanyita dake gefen kujera, ya miƙe tsaye yana saka mata a kanta. Binsa kawai take da kallo, tana shawara da zuciyarta, kan ta yadda za ta ɓullo masa da maganar da suka yi da Adawiyya a yau. Zama ya yi a gafenta ya na cewa.

“Shikenan?”

Kanta ta gyaɗa masa tana gyara zamanta. Kallon da suke suka ci gaba da yi, kafin Kuliyan ya miƙe ya shiga kitchen ya aje plates ɗin da suka ci abinci. Har ya kamo hanya zai fito, sai kuma ya fasa ya koma dan ɗaukar ruwa. 

Babban kuskuren da ya tafka kenan a ranar. Dan a sa'ilin da ya rufe murfin fridge ɗin, asa'ilin wani ɗan ƙarami, kuma mulmullallen ƙarfe, ya fito daga cikin bindigar da aka harba da ƙarfin tsiya, kuma bai tashi sauƙa a ko ina ba, sai a damtsen Kuliya na dama.

Wani irin shiga harbin ya masa, hakan ya sa shi sakin gorar ruwan dake hannunsa da sauri, sannan ya yi luuu zuwa baya ya na shirin faɗu, cikin dauriya da zafin nama ya kai hannunsa ya dafa island. Da ƙyar ya tsaya a kan ƙafafunsa ya na layi. Wani irin zugin azaba hannun nasa yake masa, hakan ya sa ya kalli hannun, bai tabbatar da abun da yake gani ba, sai da ya kai hannunsa ya kawar da ɗan guntun hannun T-shirt ɗin jikinsa, ya ga ramin da harbin da aka masa ya yi.

Ji ya yi jini na ɗibansa, tunawa da ya yi da Mishal dake falo ya sa shi cije leɓensa na ƙasa. Ya kai hannunsa na hagu ya riƙe damtsen nasa dake ta zubar jini, da ƙyar ya ja ƙafarsa zuwa falon, dan ya san ko ma su waye suka zo gidan dan shi suka zo, kuma idan aka jima kaɗan za su iya shigowa cikin gidan, wata ƙila su cutar masa da ita.

“Ab... Abu... Abu Aswad... La... lafiya...”

Mishal ta faɗi tana miƙewa tsayi, ganinsa cikin wani hali ba ƙaramin ruɗata ya yi ba, kamar an kunna famfo, haka hawaye ya shiga mata zuba, da sauri ta nufi inda yake tana kiran sunansa, duk ta birkice, ta rasa abin yi.

“Zo... Zo mu je ka zauna!”

Ta faɗi tana  jan hannunsa na hagu dake kan damtsensa na dama. Da sauri ya riƙe nata hannun ya na girgiza mata kai cike da dauri, leɓensa ya ƙara datsewa. A sanda ya fara jan hannunta zuwa ɗakinsa. Kamar raƙumi da akala haka ta riƙa binsa har zuwa ɗakin nasa, duk kuwa da shi ɗin ba ya tafiya da kyau, ta lura ma da layi yake.

Wani abu da ya bata mamaki shi ne, ganin ya nufi closet ɗinsa da ita. Mamaki bai gama cinyeta ba har sai sanda ta ga ya danna wani switch da duk shigowarta wurin ba ta taɓa lura da shi ba. Ba tare da ɓata lokaci ba, lokar kayan dake wurin ta zuge zuwa gefe sannan ƙofa ta bayyana a gabansu. Hannunsa na hagu wanda ya yi kaca-kaca da jini ya kai ya tura ƙofar ta yi baya, sannan ya tura Mishal ɗin ciki, shi ma ya shiga. Ya na shiga ya rufo ƙofar, ya danna wani switch dake kusa da ƙofar, nan take lokar nan da ta yi gefe ta koma mazauninta na ainahi, kamar ma ba'a taɓa motsa ta ba.

Mishal ta ci gaba da bin wurin da kallo, ganin cewar ɗaki ne, har da gado a ciki, ga kuma wani work table dake ɗauke da computers da kuma tardu. Duk da tana cikin halin ruɗu, bai hanata jin mamaki na jan ƙafarta zuwa ƙasa ba, to shi wannan ɗakin ta wani ɓangare yake a gidan?, dan ita ko da wasa ba ta taɓa sanin cewa akwai wasu ɗakuna bayan waɗanan ukun da ta sani a gidan ba.

Jin abu ya faɗi yaraf a bayanta ya sa da sauri ta waigo. Idonta ya sauƙa a kan Kuliya dake yashe a ƙasa, hannunsa na hagu dafe da damtsensa na dama, wanda yake ta ɓuɓullar da jini.

Da gudu ta isa kansa tana kiran sunansa, a hankali ta kama kansa tana shirin zaunar da shi. Da ɗan sauran kuzarin da ya rage masa ya miƙe zaunen ya na jingina da bango. Mishal sai duba jikinsa take, kamar wadda aka cewa akwai wani switch da za ta danna a jikin nasa, wanda zai hana zubar jinin da yake. Gaba ɗaya ya haɗa gumi sharkaf, kasancewar babu wata isashiyyar iska a ɗakin, dan ita ba ta ga windo ko wata ƙofa bayan wadda suka shigo ba. Hular kanta ta cire ta na faɗin.

“Tsaya na saka maka wannan a wurin, may be zai hana jinin zuba”

Da ƙyar Kuliya ya iya sauƙe hannunsa na hagu daga kan raunin, sannan cikin sauri Mishal ta cikukuye hukarta pink color tana danawwa a wurin. Jin ya yi wani irin nishi ne ya sa ta fashe da kuka me sauti tana kallon fuskarsa, idanuwansa har sama suke, alamun dai ya na gaf da rufesu gaba ɗaya.

“Na shiga uku ni Hafsat, Abu Aswad kar ka mutu, dan Allah kar ka mutu ka barni, Abu Aswad ka min alƙawarin kasancewa tare da ni fa, kuma na san Anna ta faɗa maka cewar karya alƙawari ba kyau, kar ka karya alƙawari, Abu Aswad ka kasance tare da ni, Abu Aswad ɗina dan Allah!...”

Sambatu take tana ƙarawa, ita kanta ba ta jin ma tana cikin hayyacinta, hular kanta da ta cire ce tasa gashin kanta barbajewa a bayanta, ta koma kamarwata wadda sanyi ya taɓawa ƙwaƙwalwa.

“Kana ji ko?!”

Ta tambaya tana mammarin gefen fuskarsa, idonsa da ya lumshe ya buɗe a kanta.

“Kar ka mutu baka haɗu da Zaid ba!...”

Kuliya ya ja wani kalar numfashi yana buɗe idonsa da ƙyar, cikin wani irin sauti yace.

“A... Ina... Ki... Ki ka san... Za... Zaid?”

Ba dan babu sautin komai a ɗakin ba,  da balalle ta ji abun da yake faɗi ba.

“Yau Anti Adawiyya ta zo makaranta ta same ni, shi ne take faɗamin cewar Zaid ne mijinta, kuma... Kuma da ma ina ganinsa a layin makaranta”

Kansa ya kawar gefe yana ƙoƙarin ƙwato numfashinsa da ya nufi wata duniyar.

“Zaid ya gudu... Gu... Guduwa aka ce ya y... yi”

Da sauri Mishal ta share hawayenta, hakan ya sa gefen fuskarta ɓaci da jinsa. Ta gyara zama ta shiga ba shi labarin da ta sani a kan Zaid ɗin. Duk kuwa da ba ta da tabbacin yana fahimta. Sai de kuma yana fahimtar, dan babu abu ɗaya da ta faɗa wanda bai samu mukkulin kansa ya buɗe ƙofa ya shiga ba, ya ji komai, kuma ya haddace komai. Kallonta yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa gaba ɗaya.

“Hafsat! Ballale... Na... Na kai gobe ba... Amma idan... Idan kin haɗu... Haɗu da Zaid, ki ce... Ki ce masa ina kewarsa... Sa... Sannan... Sannan kuma ba duk tswon wannan lokacin, ban manta da shi ba... Ki kuma faɗa masa cewar... Cewar ke matata ce, ya kula min dake!”

Mishal ta ƙarawa kukanta sauti tana kamo hannunsa.

“Aliyu Dan Allah ka dena faɗin haka... Na rantse za ka rayu, Allah na tare da mu... Yanzu Aliyu idan ka mutu ina zan sa kain?... Aliyu ba ni fa da kowa sai kai. Kai ne kawai ka rage min, dan Allah kai ma ka zauna, kar ka mutu ka barni kamar Babana da Mamana da kuma yayana, a ƙalla de ya kamata ace na samu ko da mutum ɗaya ne a cikinku!”

Tausayinta ya ƙara kama raunanniyar zuciyar Kuliya, hakan ya sa shi ɗagowa da hannunsa na hagu dake ɓace da jini, ya kama gefen fuskarta, hannun nasa gaba ɗaya  karkarwa yake, hawaye na fita daga idonsa, wanda ya haɗe da zufar da yake.

Matsowa ya yi da fuskarta dab da tasa, har tana iya jiyo yanda numfashisa ke fita a gurɓace, saboda hancinta da ya kara da nasa, hakan ya sa Mishal lumshe ido tana buɗe wani sabon babin na kuka.

“Idan na mutu kar ki yi kuka, na san ma Zaid ba zai bari ki yi kukan ba, amma zan yi kewarki, Allah ya haɗani da ke a aljanna!...”

Da sauri Mishal ta kai hannayenta kan fuskarsa tana girgiza masa kai.

“Dan Allah kar ka tafi... Allah ina sonka... Wallahi ina sonka”

Cikin wani irin ƙarfin hali ya mata murmushi. Da gaske yake faɗa mata cewar ba ya jin zai iya kaiwa safiyar gobe, ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa da ita, haka kuma ba ya jin zai ƙara buɗar idonsa ya ganta kusa da shi. Wasiyya ce yake bata, dan wata ƙila bai sani ba, ko wanna ne kaɗai lokacin da Allah ya ara masa dan ya yi magana da ita ta ƙarshe.

“Silly girl... Ki me... Me da hankali kan karatunki, ki zama yarinyar kirki, idan kuma Allah ya sa akwai rabo tsakanina da ke, Allah ya raya mana shi, dan ina zaton kamar na baki baby shekaran jiya, ki kula da shi pleace”

Duk da halin da yake ciki sai da ya bawa Mishal haushi, ana ga yaƙi shi ya na ga ƙura, ɗan ƙaramin mari ta masa a kuncinsa, hakan ya sa ya buɗe idonsa da ya lumshe.

“I love you Teddy Bear... Mishallyn Aliyu...!”

Da sauri ta haɗe bakinta da nasa ta shiga kissing. Kafin a hankali ta saki bakinsa tan kallon idonsa.

“I love youuuuu too Abu Aswad!”

Murmushi ya mata, yana ɗaga hannunsa ya shafa kanta. Nan take kuma jikinsa ya saki, hannun nasa ya dawo ƙasa yaraf, fuskarsa dake hannunta ta ƙara nauyi, idonsa ya rufe ruf.

Daga can wajen gidan kuma, bayan da 'yan ta'addan da suka zo ɗaukar fansa suka gama dube-dubensu a cikin gidan ba su ga kowa ba, sai suka yanke shawarar kiran ogansu dan su sanar masa da su fa basu ga kowa ba. Ogan yace su bar gidan kawai tun da har sun ce sun harbe shi, ko haka ma suka barshi ai shikenan, sun ɗau fansar abin da ya musu, na kama babban ogansu da ya yi.

ZAID POV.

Da misalin ƙarfe 12:40am, ya fice daga gidansa, yayin da ya bar Rabi kwance tana bacci, shi ba zai iya jira har zuwa gobe da safe ba, dan tun bayan da ta kawo masa maganar Aliyu na raye ya shiga mata tambayoyi a kan Aliyun. Amma sai ta ce masa ita ba ta san komai a kansa ba bayan inkiyarsa, wato Kuliya, sannan kuma ta san cewa ma'aikacin DSS ne. Yanzu haka tafiyar da yake a motar, tunani, ruɗani, jimami da mamaki su ne suka cika kansa taf. Ya rasa ma wani kalar yanayi yake ciki, amma idan ya duba wani ɓangaren sai ya ga cewar kamar mamakin da yake ciki ya fi yawa. Dan ya na mamaki mutuƙa, na yanda Aliyun ya iya tserewa wutar da ta kama a gidan marayu, sai kuma mamakin sanin cewa shi ma SS ne, su na aiki a hukuma ɗaya, amma ba su san juna ba. Sai kuma wani murmushi ya suɓuce masa, tunawa da ya yi da alƙawarin da suke yawan ɗaukawa juna, na idan sun girma aikin SS shi ne za su yi. Wato bai manta ba kenan, tun da ga shi ya cika alƙawari.

Hannunsa ya kai ya ɗauki wayarsa, a sanda yake faka motar a gefen hanya. Cikin jerin gwanon lambobin dake wayarsa, ya nemo ta RAM, tare da  aika masa kira. Kusan ringing uku ta yi ba tare da  an ɗaga ba, har ransa ya soma ɓaci, dan ya san halin RAM ɗin, shi a rayuwarsa sam bai iya zama da waya ba, wayat ma sam ba ta gabansa, mutumin da sai ya yi sati ba tare da ya san inda wayar tasa take ba.

Sai a kira na biyar sannan ya ɗaga. Cikin magagin bacci ya soma gaida Zaid ɗin, ya amsashi a dake.

“Ina san ka buɗe bayanan ma'aikatan hukumarmu, ka duba min wani wai shi ALIYU ZAID, inkiyarsa KULIYA!”

Umarnin ya biyo baya. Daga ɗayan ɓangaren Ram ya miƙe tsaye daga kan gadonsa yana fita daga ɗakinsa, gudun kada ya tashi matarsa a bacci, ya koma falo ya zauna, har zuwa lokacin wayar na kare a kunnensa. Sai da ya murza idonsa kusan sau biyu, kafin ya sosa wuyansa, dai-dai kan wani tatto dake rubuce a wuyan nasa.

“Sir a yanzu ba zai iyu na duba bayanan ba, sai de na datsi na'urar, amma ni zan iya baka amsa!”

Daga ɗayan ɓangaren Zaid ya gyara zamansa ya na ɗaga kafaɗa.

“Umhumm, Ina jinka”

 Ram ya ɗauko numfashi, sannan ya dire, dan kuwa ya san abun da zai aikata a yanzun, saɓawa ƙa'idar aikinsa ne, ba'a yarda su bawa juna sirrin wasu jami'an ba, amma kuma dole ne ya yi hakan, dan yana da tabbacin temako ne zai yi.

“Tun shekaru biyar baya na fara aiki da kai Sir, haka ne?”

Zaid ya gyaɗa kansa, a idonsa yake hango haɗuwarsu ta farko da Ram ɗin.

“Haka ne”

Ya faɗi cikin tabbatarwa.

“Bayan shekara uku da fara aiki da kai, sai aka haɗani aiki da wani me kamarka, dan kuwa ba zan kirashi da kai kai tsaye ba, saboda akwai wasu banbaci biyu tare da ku. Wannan banbanci shi ne yasa na gane cewa, ku mutane biyu ne mabanbanta. Shi wannan wanda aka haɗani aikin da shi, sunansa ALIYU ZAID BICHI, inkiyarsa KULIYA. Confusing ɗin da kuka saka ni a ciki ya sa na fara bincike a kan rayuwar ko wannenku ba tare da sanin kowa ba. Kuma cikin ikon Allah sai na gano komai a kanku, sai de kuma na gano cewar ba ku san da zaman juna ba, kai kana zargin cewa Aliyu ya mutu, shi kuma an sanar da shi cewar ka gudu. A lokacin sai na samu Sir Andi, na masa bayanin abun da na gano, shi ne ya gargaɗeni da kada na kuskura na ɗaga zancen, na barku a haka, domin kuwa sanin junanku zai iya haifarwa da ɗaya daga cikinki matsala a aikinku. Sai na yarda da abun da ya faɗi, hakan tasa na yi shiru da bakina. Amma tun da har ka tambayeni a yau, na ji cewar ba zan iya ɓoye maka ba!”

Shuuuuuu! Wata iska ta shiga wucewa ta gefen kunnen Zaid da ba wayar, hannunsa na hagu dunƙuke a kan bakinsa. Wai shi kam meke damunsa ne yau?. Ji yake kamar duk abun da yake faruwa  a mafarki ne, kamar idan wani ya zungureshi zai farka ya ga cewar ba gaskiya ba ne. Ashe kenan duk tsawon wannan shekarun Aliyunsa na raye?. Miyau ya haɗiye da ƙyar, yana laluben muryasa a  maƙogwaransa.

“Ina ne address ɗin gidansa?”

Da gudu motar Zaid ta shigo layin gidan Aliyu, Allah-Allah yake ya isa gidan, dan zuciyarsa na faɗa masa kamar biyuninsa baya cikin ƙoshin lafiya. A dai-dai ƙofar gidan da Ram ya faɗa masa ya yi parking, bai ko kashe motar ba, ya fito da gudu ya shiga cikin gidan, da megadin y fara cinkaro, yashe a ƙasa,, hakan ya sa hankalinsa ninkuwa wurin tashi. Zuciyarsa ko kamar za ta fashe dan tsabar bugun da take da ƙarfi.

Cikin gidan ya kutsa, ya shuga dube-dube, amma be ga kowa a falo ba, ya shiga kitchen, babu kowa, ya fito ya nufi corridor ɗin dake ƙunshe da ɗakunan gidan, haka ya yi ta shiga ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, kafin ya samu nasarar gano ɗakin Kuliyan a cikin ɗakunan uku. 

Ya bincika ko ina be ga kowa ba, kuma tun da ya ga me gadin gidan a sume, ya fuskanci cewar hari aka kawo musu, imma de sun tafi da su, shi da matarsa, ko kuma suna ɓoye a wani ɓangare na gidan. Tun da de har aka faɗa masa cewar Aliyun SS ne, to tabbas akwai maɓoya a cikin gidan, dan su ba sa zama haka kawai, hatta shi kansa akwai maɓoya a gidansa. To amma a ina ta gidan Aliyun take?.

Ya tambayi kansa, sa'ilin da yake dudduba ɗakin, wai ko Allah zaisa ya samu wata makama, amma haka ya hargutsa ɗakin, ba tare da ya samo komai ba. Har ya fara karaya, sai kuma idonsa ya sauƙa a kan ƙofar toilet, dan haka ya shiga ya dudduba nan ɗin ma. Amma bai samu komai ba, ya fito yana jin ƙirjinsa ya masa nauyi, kamar da aka ɗora masa wani gingimemen dutse a kan zuciyarsa, kamar da aka sa igiya aka ɗaure masa magudanar nunfashinsa haka yake ji, kansa ya masa nauyi, dan tarin abubuwan dak ciki za su iya sakawa ya tarwatse ma.

Haka ya kai ƙasa yana haki, kamar wanda aka koro, idonsa har lumshewa yake, kuma a cikin lumshewar idonsa ya hangi ƙofar closet. Kamar an cillo shi daga wata uwa duniya haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar closet ɗin. Ya shiga cika ya na ta dube-dube. Har ya fara fawallawa Allah, yana tunanin cewa wata ƙila sun tafi da su ɗin. Kuma a dai-dai lokacin idonsa ya sauƙa a kan wani ɗigon jini, kamar ƙofar da aka buga da ƙarfi haka zuciyarsa ta buga. Ya dawo da dubansa kan lokar da yake tsaye a gabanta. Ya shiga bin jikinta da kallo a hankali, kafin ya samo wata makkuna a jiki. Hannunsa na rawa haka ya danna switch ɗin. Lokar ta zuge zuwa gefe, wata ƙofa ta bayyana a gabansa. Sai da ya haɗiyi yawu, na tsoron abun da zai iya tararwa a bayan ƙofar. Kafin ya kai hannunsa ya turata ciki.

Abu na farko da ya fara cin karo da shi shi ne; wannan yarinyar da tace yana kama da yayanta ce durƙushe a ƙasa tana kuka, gefen fuskarta ɓace da jini. Daga ɗayan ɓangaren kuma, Aliyunsa ne jingine da bango.

Shin kun san yanda mutum kan ji a sanda ya ga wani abunsa da ya cire rai da samunsa?. Ko kun san yanda ake ji a sanda ka samu abun da baka taɓa tsamaninsa ba?. To idan de har kun sani, wannan shi ne halin da Zaid Aliyu ya shiga.

*There is no WiFi in  forest, but you will find a better connection.*

***

*No.86, Garki 2, Abuja...*

RABI'A POV.

A hankali ta shiga ƙi-ƙifta idonta, kafin ta buɗesu gaba ɗaya. Hannunta ta kai kan side drawer tana kunna wutar ɗakin, kafin dubanta ya dawo gefen inda take kwance, inda take kyautata zaton Zaid na kwance a wurin. Sai de me?, wayam haka ta ga wurin, sai wata takarda da aka yi rubutu a jiki, ajet a kan pillownsa. Ganin hakan ya sa hankalinta da ya fara tashi kwanciya. 

Hannunta na dama ta miƙa tana ɗaukar takardar, a lokaci guda kuma tana hamma, dan baccin be isheta ba.

_Ba zan iya jira zuwa gobe ba, dan haka na tafi, zan turo Rhoda ta kaiki AS roma Academy, ki je, ki buga wasa me kyau, ba na son ki bani kunya, na san matata jarumace, dan haka ki nuna ƙwarewarki... Daga mijinki abun somki... Zaid (Raja)_.

Dariya ta ɗan yi tana aje takardar. Abun be bata mamaki ba, dan ta ga ƙoƙarinsa a jiyan da tace masa ya bari sai gobe kuma ya bari ɗin, ashe shi bai haƙura ba.

Sauƙa ta yi daga kan gadon tana hamma. Kamar jiya, yau ma bata jin daɗin jikinta. Ita ta rasa abun da yake damunta a kwanakin nan, sai ta yi ta amai, ga kasala, ga kuma rashin san cin abinci da ba ta yi.

Sallah ita ce abu na farko da ta fara yi, kafin ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama gyara gidan, ta ɗora girki, tana gama girkin ta faɗa wanka. Bayan ta fito daga wanka ta saka wani baƙin leggings, da wata baƙar long sleeve high neck shirt, ta ɗora kimonohnta a kan kayan, sannan ta kawo wani baƙin baby hijjab ta saka. Ba ta yi kwalliya ba, dan da ma ita ba gwanar kwalliyar ba ce. Mai kawai ta shafa a jikinta, sannan ta ɗauki backpack ɗint ta saka kayan sport ɗinta a ciki.

Ta fito ta zauna a danning ta fara cin abinci, sai da ta kusan gamawa sannan Rhoda ta ƙaraso, ba ta yarda sun tafi ba, sai da ta zubawa Rhodan abinci ita ma, Rhodan na ci Rabin na bata labarin ɗan uwan Aliyun da suka gano. Ita kuma Rhodan na ba ta bayani a kan shari'ar da za su shiga gobe.

Da haka har suka gama, sannan Rhoda ta ɗaukesu zuwa can acadamy ɗin. Bayan da Rhodan ta kaita sai ta tafi, tare da faɗa mata cewar; idan sun gama, ta mata waya, ita kuma za ta zo ta ɗauketa.

Rabi ce zaune a kan kujerar jira, sanye take da wannan jerseyn da kum wandonta, wanda ta saka leggings da kuma long sleeve high neck shirt a ƙasansu, ƙafarta sanye da football shoes. Kanta kuma rufe da baby hijjab, yanayin shigar tata akwai gwanin ban sha'awa, dan kaf matan dake wurin babu me irin shigarta, ba za ta ce babu musulmai a cikinsu ba, amma babu bahaushiya ko bafulatana ɗaya a cikinsu, duka 'ya'yan iyamurai ne. Shi ya sa ita ta fita da ban a cikinsu.

“Rabi'a Muhammad!”

Me tantancewar ya kira sunanta da ƙarfi, hakan ya sa ta amsa tana miƙewa. Inda ya nuna mata ta ƙarasa ta tsaya. Har zuwa yanzu ba ta da wani isasshen kuzari a jikinta, ga cikinta da take jin yana yamutsawa, kamar za ta yi amai. Amma kuma ba za ta bari hakan ya zama ƙalubale gareta wurin cimma burinta ba, ita ta sa kanta cewar za ta iya, kuma da yarda Allah za ta iya ɗin. Za ta yi abun da za ta bawa kowa mamaki, ciki kuwa harda 'yan uwanta na haɗejia.

Ball aka sa musu a tsakiya ita da wata yarinya da ta karanta sunanta a bayan rigarta, wai ita ‘Chioma’. A yanayin girman jiki ta fi Rabi ƙiba, amma kuma Rabi ta ɗan fita tsayi, gata a ƙasa duf, ta ci doya da tuwon mama Iyabo ta ƙoshi.

A sa'ilin da aka hura usur, a lokacin suka fara gudanar da wasan. Tashin farko sai da Chioma ta ci Rabi'a har sau biyu. Kasancewar ita Rabin babu kuzari a jikinta. Bayan sun ci gaba da wasan, Rabi ta kaiwa Chioma wani yanka, wanda ya sa Chioman ta yi amfani da ƙarfinta ta hankaɗa Rabi gefe. Faɗuwa ta yi, hakan ya sa gwiwar hannunta kurjewa da grass carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin. 

Tashi ta yi zaune tana kallon Chioma ɗin. Me ya sa ta yarda kan cewa Chiomar za ta iya kada ta?, ita ma fa macace kamarta, babu wani abu da ta fita da shi, dan kawai ba ta jin daɗin jikinta sai ta saki jiki Chioma ta na nasara a kanta?, ya isa haka! Menene ba ta gani ba a duniya, ta shiga halin da ya ɗara wannan ma, ta ga ƙalubale a rayuwa wanda ba ta taɓa sanin zasu afko mata ba ko da a mafarki kuwa. Dan Chioma tana 'yar kudu ba shi ke nuna cewar ta fita ƙarfi ba, su ma matan arewa suna da tasu jajircewar, ya kamata ace ta nuna musu hakan.

Cike da ƙarfin hali da na gwiwa ta miƙe tsaya, sannan ta koma aka ci gaba da wasa, wannan karon a zafafe take wasan, hakan yasa ta riƙa cin Chioma har sai da lokacinsu ya ƙare. Couches ɗin dake wajen ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin har yanzu Rabi'an ba ta manta da wasu abubuwa da ta koya daga garesu ba.

“Ina taya ki murna mrs. Zaid!”

Cewar ɗaya daga cikin Coach ɗin nasu yana miƙa mata hannu alamun su gaisa, hannun nasa ta kalla, yayin da take dafe da guwar hannunta na dama wanda ke mata ciwo. Kanta ta girgiza masa tana faɗin.

“Sorry sir, but ni matar aureci”

Hakan ya sa Coach ɗin janye hannunsa a sanyaye.

Daga nan kuma sai aka turasu sashen fara ɗaukar darasi, tun a ranar aka fara musu training kuma ba su suka gama ba sai ƙarfe biyar na yamma.

*

Rhoda ce ke tuƙa motarta a kan titi, tana tafe tana biya waƙar Dalling Jesus dake tashi a motar.

“I love you so much darling Jesus... My darling Jesus... Darling Jesus...”

Wayarta ce ta yi ringing, hakan ya sa ta faka motar a gefen hanya, tana kashe waƙar. Ganin Zaid ne ke koranta ya sa ta kai hannu ta ɗau wayar tana ɗaga kiran.

“Kina ina ?”

Abun da muryarsa ta fara tambaya kenan bayan da ta ɗaga wayar, amon muryar tasa ya bata tsoro, dan sautin nasa na ɗauke da wani abu me kama da damuwa ko tsoro. Kamar me san tantance wani abu, ta shiga wulƙita idonta a kewayen wurin da take.

“Ƙarfe shida yanzu, na kai Ammatanka gida ne... Kai wai ina ma ka shiga ne?”

Ta ƙarashe tana jefa masa tambayar. Sai ta ji ya yi shiru, kafin yace.

“Ki koma gidan ki ɗaukota, sannan ki kawota Hymill hospital!”

Damm, gaban Rhoda ya buga.

“Zaid! Zaid!. Me yake faruwa?. Ka ga ɗan uwan naka?”

Ta tambaya a kiɗime.

“Ki je ki zo da Adawiyya... Ɗaki me lamba ashirin da shida”

Daga haka ya katse kiran ba tare da ya jira abun da za ta faɗi ba. A hankali Rhoda ta sauƙe wayar daga kunnenta, duk yadda aka yi ba lafiya ba. Dan haka ta tayar da motar da sauri ta juya kan motar zuwa gidan Zaid.

RABI'A POV.

Rhoda na aje ta a gidan ta shiga wanka. Kuma kafin ta bar banɗakin ma sai da ta yi amai, ta rasa abun da yake mata daɗi, ko mai ta ci ba ya zama a cikinta sai ya dawo. Haka ta ɗaura towel ta fito jiki ba ƙwari. Duk da yau tana cikin farin ciki sosai, domin a yanzu ta na ganin labarinta ya gama cika, tun da har Allah ya mallaka mata Zaid a matsayin miji, ya sa mahaifinta shiryuwa, ya ganar da Habiba da 'yarta Mama tafarki madai-daici, sannan ya nuna mata auren Anti Saratu, ya kuma cika mata burinta na ci gaba da buga ƙwallo. Ita kuwa me za ta ce? Da ya rage ta dage kan ibadunta, don ta nunawa Allah jin daɗinta kan ni'imomin da ya mata.

Ta ƙarashe tunanin tana saka wata doguwar rigar atamfa. Wayarta ta dawo ta ɗauka, ta aikawa Zaid kira, dan ta na so ta ji daga gareshi, tana san ta ji wani hali yake ciki, shin ya haɗu da Aliyun?, ko ba su haɗu ba?. Sau huɗu tana shiga amma ba ya ɗagawa, hakan ya sata shiga mamaki, a gefe guda kuma sai tsoro ya fara shigarta.

Ta kama hanya da niyyar barin ɗakin aka turo ƙofar ɗakin da ƙarfu, Rhodan da ta tafi a ɗazu ce ta dawo, cikin wani irin birkitaccen yanayi da Rabin ta kasa gane masa.

*Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja*

*07:00pm*

MISHAL POV.

Zaune take kan wata kujera dake bakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Aliyu bayan zuwansu asibiti a daren jiya. Abun da likitocin suka rara sanar musu shi ne, ya rasa jini da yawa, haka aka gwada na Zaid, sannan aka ɗiba ganin ya dace da nasa. Kuma tun safe ake ƙara masa jinin. Bai ƙare ba sai da azahar, amma har zuwa yanzu bai farfaɗo ba. 

Ita kanta ba ta san in da kanta yake ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kawai tana nan ne, amma hankalinta ba ya tare da ita. Tun a ɗazu da safe da suka gama zirga-zirga. Zaid yace mata ta zauna,shi zai tsaya a kan komai. Kuma tun lokacin take zaune a nan ɗin. Babu yanda Zaid ɗin be yi da ita ba kan ta ci abinci, amma fur haka taƙi. Ko sallah ma ba ta jin ta yi. Gani take kamar Aliyu tafiya zai yi ya barta, kamar shi ma zai bi Abbanta, Mamanta da yayanta. Wata ƙila ita ba ta da sa'ar zama da kowa a rayuwa, haka Allah ya tsara tata rayuwar, ba tare da yin zama me ɗorewa da makusantanta ba, wata ƙila haka za ta ƙarar da rayuwarta cikin kaɗaici.

A hankali Zaid da ya dawo daga masallaici ya zauna ɗan nesa da ita. Kallonta kawai yake yana san sanin me ya kamata ya yi?. Ga ɗan uwansa a cikin wani hali na mutuwa ko rayuwa, ga kuma matarsa da ke cikin tashin hankalin rasa mijinta, shi kansa idan za'a rarrasheshi so yake, dan ba ya so Aliyu ya sake tafiya ya barshi, ji yake kamar ya saka igiya ya ɗauresu da juna, gudun kada wani abun ya kuma zuwa ya gifta a tskaninsu.

Sai de kuma a matsayinsa na namiji, kuma babba, dole ne ya haɗiye nasa tashin hankalin, ya san hanyar da zai bi dan ganin ya kwantar da hankalin matar ƙaninsa.

Bakinsa ya buɗe zai yi magana, idonsa ya sauƙa a kan Rabi'a da Rhoda da suka shigo corridor ɗin ɗakunan. 

A hankali Rabi ta yi a jiyar zuciya bayan ganin mijinta cikin ƙoshin lafiya, sai de hankalin nata be gama kwanciya ba sai da ta tafi da gudu ta yi wurin da yake, miƙewa tsaye ya yi yana kallonsu. Rabi ta manta da Rhoda dake bayanta, da kuma Mishal ɗin da hamkalinta bai ma kai kanta ba. Ta yi saurin rungume mijinta tana shafa bayansa. Shi ma riƙeta ya yi da kyau a jikinsa, yana jin kamar ya fashe mata da kuka. A hankali ta sake shi tana ci gaba da duba jikinsa.

“Me ya faru?...”

Ta tambaya tana yawatawa da idonta a kewayen wurin da suke, bata rufe bakinta ba idonta ya sauƙa a kan Mishal dake zaune a kan kujera, ta sunkuyar da kanta ƙasa, gashin kan nata a yamutse, ga jinin da ya fara bushewa a gefen fuskarta. A kiɗime ta zauna kusa da ita tana rungumota jikinta. Mishal na jin kanta ya sauƙa a kafaɗar Rabi ta saki kukan da yake cin ruhinta tun safe. Kukan da Mishal ɗin ke yi ne ya ƙara karya zuciyar Rabi. Mishal na rungume a jikinta ta juyo da kanta ta kalli Zaid dake tsaye yana ƙoƙarin hana hawayensa zuba.

“Raj! Me yake faruwa wai?”

Zaid ya ɗan kawar da fuska yana ɗaga kafaɗarsa.

“Aliyu ne ba shi da lafiya”

Sunansa kawai da ta kira ne ya ƙara karya zuciyar Mishal, ta ƙarawa kukanta ƙarfi tana ƙanƙame Rabi a jikinta. Da Zaid ya ga ba zai iya ɗauka ba, sai ya yi wa Rhoda alama da ta biyoshi, ya kama hanyar barin corridorn.

Duk yadda Rabi ta so Mishal ta kwantar da hankalinta ya gagara. Kukan ma da ƙyar ta sakata ta dena shi. Sai hawayen da take gogewa. Sai wajajen ƙarfe takwas Zaid da Rhoda suka dawo.

Zaid ɗin ya umarci Rhoda da ta ɗauki Rabi da Mishal ta kaisu gidansa, kuma ita ma kar ta tafi, ta zauna ta kwana tare da su. Kamar wata gawa haka Rabi ta miƙar da Mishal ta shiga janta zuwa waje, dan bata ma san inda take saka ƙafarta ba, duk inda aka jata bi take kawai.

Rhoda da Mishal suka shiga mota, yayin da Rabi da Zaid suka tsaya daga can nesa da su. Rabi ta goge ƙwallar idonta ta tausayin mijinta da kuma ƙanwarta, ta kai hannunta ta dafa kafaɗar Zaid ɗin ta dama.

“Ka ci abinci?”

Kansa ya juyo ya kalli fuskarta ta cikin hasken fitilun dake wadace a harabar asibitin. Nan take idon nasa ya cika da ƙwalla. Sai ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya na barin hawayen fita daga inda ya tsaresu tsawon ranar.

“Ban ci ba”

Ya amsa mata a raunane. Rabi ta ci gaba da kallonsa, tana jin ina ma tana da damar da za ta buɗe zuciyarsa, ta cire wannan damuwar da yake ciki. Ƙwalla ta kuma gogewa tana faɗin.

“Na ga ko wanka ma ba ka yi ba. Amma ya kamata ace ka ci abincin”

Sai ya ɗago da lumsassun idanuwansa ya ɗorasu a kanta yana ɗage kafaɗarsa ta dama.

“Adawiyya ta ya kike tunan zan iya cin abinci a irin wanna yanayin da nake ciki, ni yunwar ma kanta ba na ji. Kaina ne kawai ke min ciwo, ji nake kamar zai tarwatse!”

Sai ta ɗan yi tattage tana riƙe kan nasa.

“Ka ga ba?. Yunwar ce ta saka mata ciwon kan, ka daure ka taɓa wani abun, sai ka sha magani, Aliyu ba zai ji daɗi ba idan har ya ji cewar baka ci abinci ba!”

Kiran sunan Aliyin ya sa wata ƙwalla ta ƙara sauƙowa daga idonsa. Rabi ta saka hannyenta ta share masa duka ƙwallar.

“Na san kana da dauriya da kuma juriya, ka ƙara kan wadda kake da ita, Allah zai tashi kafaɗun Aliyu!...”

Da sauri ya saka hannyensa biyu ya kewaye waist ɗinta yana janta jikinsa tare da fashewa da kuka mara sauti. Ita ma Rabin kukan take. Tana shafa ƙeyarsa. Sun jima a haka kafin Zaid ɗin ya saketa ya na share ƙwalla.

“Ki san yanda za ki kwantarwa da...”

Sai kuma ya yi shiru, dan sunan nata ya kwanta masa. Rabi ta kai hannunta na hagu ta kama chain ɗin wuyansa, sannan ta yi amfani da hannunta na hagu ta kama wuyan rigarsa tana janyo shi gaba, kafin ta saka sarƙar a cikin rigar tasa tana faɗin.

“Mishal?”

“Eh Mishal... Ko sallah ba na jin ta yi, dan Allah ki kula”

Kanta ta gyaɗa tana sharar tata ƙwallar.

“Na je na an min gwaji, kuma na ci, dan har training mun fara!”

Bai iya ce mata komai ba, sai kansa da ya gyaɗa, daga haka suka yi sallama, shi ya koma zuwa cikin asibitin. Ita kuma ta nufi motar Rhoda.

Ko da suka isa gidan, wanka tasa Mishal ta yi, kafin ta bata wasu kayan cikin kayanta tace mata tasa. Sawar ta yi, sannan Rabi tace mata ta yi sallah tana zuwa. Sallar ta fara kafin Rabin ta dawo.

A falo ta iske Rjoda kwance a kan kujera tana waya da Zakar, yayin da take sanar masa halin da suke ciki a yau. Ba ta ce mata komai ba ta wuce kitchen. Ta shiga kiciniyar girka musu abinci. Kasancewar babu wani isasshen lokaci, ya sa ta yi gaggauwar girka musu jallof ɗin taliya.

Duka ta jiye musu it a tray, sannan ta fito da ita ta aje a falo, zuwa lokacin Rhodan ta gama wayar tana zaune tana danna wayar tata.

“Bari na kira Mishal...”

Ta faɗi tana nufar ɗakinta. Ko da ta shiga sai ta iske Mishal ɗin zaune kan darduma. Ba ta san me take ba,amma bisa ga dukkan alamu ba sallah take ba. Sai ta shiga cikin ɗakin tare da nufar inda take.

“Ƙanwata!”

Ta kira sunanta tana dafa kafaɗarta, firgiyar da da Mishal ɗin ta yi ya ankarar da Rabi cewar tunani take. 

“Kin idar da sallahr?”

Mishal ta gyaɗa mata kai.

“Mishal! A yanzu Aliyu ba ya buƙatar kukanki ko damuwa, addu'a kawai za ki masa, da yardar Allah zai tashi!”

Wata siriryar ƙwalla ce ta biyo kuncin Mishal.

“Anti Adawiyya idan na tuna maraicina sai na ji kamar zan fasa ƙara. Ba ni da kowa fa, Aliyu shi kaɗai ne ya rage min, bayan shi ban da kowa. Idan ya mutu kuma ya zan yi?!”

Da sauri Rabi ta girgiza mata kai.

“Insha-Allah zai warke, zai tashi kin ji?”

Ta faɗi tana jan Mishal zuwa jikinta. Kafin ta saketa a hankali tana share nata ƙwalla. 

“Mu je mu ci abinci...”

Mishal ta girgiza kanta. Rabi ta zare mata ido tana faɗin.

“A gidana ba'a min musu, dan haka salin-alin ki tashi mu je mu ci abinci”

Duk da halin da Mishal ke ciki be hanata yin murmushi ba. Tashin ta yi suka fita, a falon suka zauna a kan carpet suka fara cin abincin. Ko rabi ba su yi ba, Rabi ta ji amai na taso mata. Dan haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta da gudu.

“Lafiya?”

Mishal da Rhoda suka faɗi a tare suna miƙewa tare da bin bayanta da kallo.

“Zauna ki ci gaba da cin abincin, ni zan je na dubata”

Cewar Rhoda. Ba dan Mishal ta so ba, haka ta zauna tana ta kallon ƙofar ɗakin Rabin.

“Sannu! Sannu kin ji... Sannu!”

Rhoda ke ta jerawa Rabi sannu, wadda ke ta amayar da taliyar da ta samu shiga cikin. Bakinta ta wanke tana jingina da bango, bayan da ta gama aman.

“Baki da lafiya ne?”

Rabi ta girgiza kai tana dafe cikinta.

“To sannu”

Falon suka dawo, inda Rabi tace ita fa ta ƙoshi, dan haka su su ƙarasa cin abincisu. Babu yadda Rhoda ba ta yi da ita ba kan ta daure ta ƙara abincin, amma tace ita ta ƙoshi. Haka suka ƙyaleta su ma suka ci gaba, da ƙyar Mishal ta iya cin abincin da yawa. Kafin Rabi ta ɗauke trayn ta kai shi kitchen, ta fito tana faɗin.

“Sai mu kwanta ko?”

Rhoda ta miƙe tana faɗin.

“No, ku de ku je ku kwanta a ɗaki, ni a nan zan kwana!”

 Rabi ta girgiza kanta.

“A'a... Ke ma zuwa za ki yi mu kwanta, gadon fa babba ne, zai ɗaukemu mu uku”

“Ok, mu je”

Da haka suka koma ɗakin, gadon kuwa tas ya ɗaukesu su ukun, har da sauran space. Rabi da Rhoda ne kawai suka yi bacci, ban da Mishal ɗin da ta kwana ido buɗe. Dan ba ta jin za ta iya baccin, hakan ya sa daren ya mata tsawo, fiye da sauran dararen da suka shuɗe a rayuwarta.

*Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja*

ZAID POV.

Zaune yake a kan kujera ɗaya dake cikin ɗakin da Aliyu ke kwance. Ya kafe Aliyun da ido, kamar idan ya kira sunansa zau amsa. Hannunsa ya kai ya shafa sumarsa tun daga gaba zuwa baya. Sannan ya dawo da hannun nasa kan bakinsa. 

Aliyun dake kwance kan gadon marasa lafiya, ba ya iya numfashi sai da temakon na'urar numfashi.  Ba ya jin zai iya ko da rintsawa. Dan gani yake kamar idan ya kumshe idonsa na minti ɗaya, Aliyu zai iya ɓacewa. Haka ya ci gaba da zama a wurin, har zuwa asuba.




Post a Comment

0 Comments