TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 29

 *BABI NA ASHIRIN DA TARA (29)*

*1986*

Auwal Abubakar Masu haifaffen nigeria ne, a jigawa state cikin wata local government me suna Haɗejia, Ya kasance ɗa a wajen sarkin haɗejia na wancan zamani, wato Alhaji Abubakar masu, ba shine ɗansa na farko ba, hasalima shine ɗansa na biyu, sai maza biyu dake bi masa sannan ƙaramar kanwarsu mace, wadda a haihuwarta ne mahaifiyar su ta rasu.

Kuma duk cikin ƴaƴan nasa shine kaɗai harkar karatu ta ɗauke shi zuwa ƙasar waje, ya tafi arewacin india garin mumbai, inda yake karantar fannin likitanci.

Bayan ya kammala karatunsa ne ya samu aiki, sannan kuma a lokacin ne Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa.

Ya dawo gida sbd rasuwar, bayan an gama zaman makoki ne aka naɗa babban ɗan sarki Abubakar Masu, wato Abdullahi, wanda ya kasance yaya a wajen Auwal, shi kuma Auwal ɗin a ka naɗa shi a sarautar Tafidan haɗejia.

Bai koma india ba saida ƴan uwansa suka shawarce shi akan batun aure, tun a lokacin ya sanar musu cewa shi bashi da wadda yake so, kuma kamar abun haɗin baki yana komawa india ya haɗu da wata ba'indiya wadda ya fara santa.

Roshni, shine sunanta, ƴa a wajen Iƙbal Khan, mahaifinsu ya rasu tun suna yara, ƴan uwanta biyu kuma duk maza, Imran shine babba, sai Irfan me bi masa, sannan ita, yayanta Imran yana da aure, kuma ɗan kasuwa ne, yana harkar kasuwancinsa a Nigeria, yayinda shi Irfan ke zaune tare da su a india.

Bayan sun fara soyyaya da Auwal, kuma basu ɗau wani lokaci ba ya bayyana mata cewar aurenta yake san yi, babu jayyaya ta sada shi da iyayenta, yayanta Imran dake nigeria mahaifiyar su ta wakilta ya yi bincike akan dangin Auwal ɗin.

Kuma ya basu result me kyau, dan haka suka amince masa da ya turo iyayensa, tun daga nigeria yayansa Me Martaba da kawunansa suka taho India nema masa aurenta, kuma an bashi, babu b'ata lokaci a kayi aure.

Ango da amarya suka ci gaba da zama a india cikin garin mumbai. Aure yayi albarka, bayan auren da shekara uku Roshni ta haifo ɗanta na miji, wanda aka saka masa suna Eshaan.

Eshaan ya samu soyyayar dangi, tun daga dangin mahaifiyar sa har na mahaifin sa, domin yaro ne wanda ya nininnka iyayensa kyau, hatta da mahaifiyar sa sede ta fishi farin fata, shima ɗin dan ya haɗa jini da Africans ne, amma shima ɗin akan Africans ɗin fari ne, fari sosai.

Yaro ne me wayo duk da bashi da san hayaniya sosai, amma kuma akwai kazar-kazar, kuma yafi shaƙuwa da mahaifiyar sa fiye da kowa.

A lokacin da Eshaan ɗin ya cika shekara biyar, Auwal yace da Roshni ta shirya zasu tafi Nigeria, tun bayan aurensu da shi Roshni bata tab'a zuwa nigeria ba, amma shi yana zuwa, kuma ya sha tafiya da Eshaan ma, amma ita koda wasa bai tab'a tafiya da ita ba, duk da ita ɗin tana san zuwa.

Dan haka da ɗaukinta ta shirya ta bishi nigeria, koda suka isa nigeria sai da suka tsaya a gidan yayanta dake abuja, suka kwana daya sannan suka wuce haɗeji.

Roshni ta samu kyakyawar tarba a wajen dangin Auwal, se ƴan wasu tsirari dake ta yada magana akan cewar wata ƙilama ita ba musulma bace, tun da musulman india ba wani riƙon addini ne da su ba.

Abinda Auwal ɗin ke gudu kenan, shi yasa bai tab'a barinta ta zo nigeria ba, dan yasan halin mutanen mu. Shi kam Eshaan dama ɗan gari ne, dan ya saba zuwa, tun a zuwansa na farko nigeria aka masa tsagu uku a gefen fuskarsa kusa da sajansa, wanda yake nuna cewar shi cikakken bahaɗeje ne.

Kaf gidan sarautar babu me san Eshaan da mahaifiyar sa sama da matar sarki Abdullahi ta farko, wato Fulani Khadija, tun sanda aka haifi yaron da suka je india ta ɗora idanta a kansa san yaron ya dasu a zuciyarta.

Dan haka lokacin da su Auwal suka tashi tafiya, Fulani tace a bar mata shi ko na ƴan wasu watanni ne, ta yi alƙawarin dawo musu da shi, daga Auwal har Roshni basu damu ba, dan haka suka tafi suka bar Eshaan ɗin a haɗejia.

Sai de kuma a ranar da suka tafi, mummunan labarin haɗarin motarsu ya riski kunnuwan ƴan uwansu, na india da na nigeria, ba ƙaramin kuka kowani b'an gare ya yi ba, dan sunyi babban rashi.

Kuma kowa babu wanda yake tausayawa sama da ɗan ƙaramin marayan da aka bari. Bayan an shafe makoki, Fulani Khadija ta nemi da a bar mata riƙon Eshaan, da saida ƴan uwan Roshni suka ja, musamman ma mahaifiyar ta, amma daga baya bayan sarki da kansa ya musu alƙawarin Eshaan ɗin zai riƙa kawo musu ziyara, sai suka yarda.

Haka suka koma india ba tare da Eshaan ɗin ba, duk da su ba haka suka so ba. Fulani Khadija bata tab'a haihuwa ba, duk da kasancewar ta matar sarki ta farko, dan haka ta riƙi Eshaan da hannu biyu, duk da babu wata shaƙuwa a tsakaninsu, amma tana nuna masa soyyaya sosai, dan ji take kamar ita ta haifeshi. 

Haka Eshaan wanda sunansa ya rikiɗe ya koma Tafida, ya ci gaba da tasowa a garin haɗeji, kowa na nuna masa ƙauna banda mutum ɗaya, Fulani Sadiya, wadda a lokacin take shayar da ɗanta na fari, wato Habibu, ita kullum a ganinta kamar idan Eshaan ya girma zai zama sarki ne, ba za'a bawa ɗanta da yake jinin sarkin ba.

Eshaan na da shekaru 6 a duniya, wasu alamomi suka fara bayyani a tare da shi, yawan muggan mafarkai, yawan zabura, ya dawo yana ware kansa daga cikin mutane, ya rage kazar-kazar irin na yara, da ƙyar ake samu ya ci abinci, baya san zuwa islamiya daga an masa magana akan islamiya sai fushi.

Duka Fulani na lura da shi, wata ranar asabar ɗin da Fulani bazata tab'a mantawa da ita ba, ta sameshi zaune a ɗaki yana dunƙule a wuri ɗaya.

“Ba zaka je makaranta ba ?”

Wannan muryar tata me cike da izza da ƙasaita ta tambaya a wancan lokacin, ya ɗago da shuɗayen idonsa ya kalleta, kallon daya hassadawa gabanta faɗuwa, amma sai ta b'oye fargabar ta.

“Tashi ka tafi islamiya”

Cike da iko da umarni take maganar, kuma tana ƙoƙarin kamo shi, tana riƙe hannunsa yana saka wani irin ƙarfi ya fisge, ya miƙe akan gadon yana wani irin huci.

Abinda Fulanin ta gani shine ya saka mararta ƙullewa, har take jin kamar zata saki fitsari a wajen.

Ƙwayar idon Eshaan ɗin taga ta rikiɗa zuwa ja, wasu dogayen haƙwara suka ƙara sauƙo masa daga haƙwaransa na sama ƙasan fiƙarsa.

“Chor mujeh!, me islamiya nahi chal (Ki rabu da ni!, ni bazan islamiyar ba)”

Cikin yaran hindi ya yi maganar, amma Fulani ta gane me yake faɗa, tsoro ya hanata ganewa komai.

“Bazanje ba nace, bahhar jayiye! (ki fita)”

Da ƙarfi yake mata maganar, kuma idonsa tsaye a kanta, sai kuma ya yanke jiki ya faɗi, Fulani ta rushe da kuka tana tattab'ashi.

Ranar babu wanda ya yi kwanan lafiya, addu'o'i babu kalar wanda ba'a masa ba, haka aka kawo masa rubutu dana shaƙa harda na turare.

Cikin ƴan kwanaki ya warke, saida me ?, sati biyu bayan hakan ta koma ruwa, sai ta zamana idan Aka bashi ruwan addu'a yasha wanda ya kawo masa maganin shine zeyi ciwon ciki, idan kuma na shaƙa ne, to mutum zeyi ciwon kai, idan kuma na shafawa ne to duk inda ya tab'a a jikinsa kai kuma nan ne zai maka ciwo.

Ciwo ba na wasa ba, ciwo na gasken gaske, haka kowa ya haƙura ya zubawa sarautar Allah ido, suda bashi wani temako sai na addu'ar baka.

A haka har yaci gaba da tasowa, rayuwarsa taci gaba da gangarawa, yana ɗan samun sauƙi, sai ya zamana abun baya tashi sai idan ransa ya b'aci, ƴan uwan mahaifinsa sun gano cewa shine wanda ɗaya daga cikin kakkaninsu ya yi rubutu a kai, amma kuma a lokacin bai kai aure ba. Dan haka su kayi haƙuri suka barwa Allah zab'i. 

Eshaan ya taso cikin nutsuwa da hankali, gaba ɗaya ƴan uwan mahaifin sa dama na mahaifiyar sa suna yabawa da shi, shi bai cika surutu ba, amma yana da sanin ya kamata.

Abokinsa ɗaya a haɗejia, Muktar shima sun haɗu ne lokacin suna primary. A lokacin yanada shekaru goma sha uku ya gano cewa baƙin aljanin dake Jikinsa yana bashi super natural, kuma se yake amfani da hakan wajen yin wasu abubuwan.

Amma hatta shi da kansa baya san rayuwar da yake, shibda kansa tsoron kansa yake. Tun daga ranar da Fulani Sadiya ta faɗa masa cewar shi dodo ne, ya riƙe hakan a ƙwaƙwalwarsa, kuma dai-dai da second ɗaya bai tab'a mantawa ba.

Domin a nasa b'angaren yanaga kamar gaskiya take faɗa, domin duk irin halin da yake shiga marabarsa da dodon kaɗance.

Duk da dama yasan cewa Fulani Saidiya ce kawai bata sansa a gaba ɗaya ƴan uwansa na haɗejia.

Eshaan ya taso a matsayin mutum me girmama al'ada, yana san al'adunsa duka biyu, domin in har yana nigeria, abune mawuyaci ka ganshi da ƙananun kaya, saide idan zaman gida yake, kazalika kuma idan yana india baya saka kayan hausawa, saide nasu na can ko ƙananun kaya. Wannan ɗabi'ar tasa ce take burge kowa da shi.

Bayan Eshaan ya kammala secondary sai ta bayyanawa sarki cewa karatun likita yake so ya yi, sarki yaji daɗin hakan, ko ba komai zai maye wurin mahaifinsa ne.

Kuma yace musu india yake so yaje, inda dangin mahaifiyarsa suke, Dan ya san su, ya san komai a kansu, Dan yana zuwa hutu wajen su, hakama abuja wajen kawunsa. Babu b'ata lokaci aka shirya masa komai yaje ya fara karatunsa a can.

Ya shafe shekaru a can ɗin, kafin ta dawo nigeria, kuma yana dawowar ne aka naɗashi kan sarautar Tafida.

Ba jimawa da dawowar sa ya saka aka gyara masa gidan mahaifinsa da yaci hado a garin haɗejia, ya tare a gidan sannan ya buɗe babban asibiti na CROWN HOSPITAL.

Bai jima ba aka ɗauke shi aiki a ST NICHOLAS HOSPITAL, Dan haka ya bar komai ya koma lagos, amma har zuwa lokacin wannan abun na jikinsa.

***       ***        ***

“Na saba da mahaifiyata sosai a sanda ina ƙarami, ko mahaifina banyi sabo Da shi kamar yanda na yi da ita ba, a duk sanda wannan abunzai tashi min, kafin na farka sai na yi mafarkin ta.Har yanzu ban mance yanayin fuskarta ba, bana mance komai nata, komai Wifey”

Sai ya yi ajiyar zuciya, yana ƙara riƙe hannun Maryam dake cikin nasa. Zaune sume a bakin gadonsa, yayinda suke facing juna.

A lokaci guda kuma yana ƙif-ƙifta ido, Maryam ta kula kamar idon nasa na san sauya kala ne, shi kuma baya so, abinda take zato ya tabbata, a sanda ya ɗago da idonsa ya kalleta, tana kallon yanda ƙwayar idon nasa take rikiɗewa a hankali zuwa ja, taji tsoro, dan har jikinta sai da ya ɗan yi rawa, amma sai ta dake, ta shanye tsoronta, tunda harde jiya ma bata ji tsoronsa ba me zaisa taji tsoronsa yau ?.

“Ranar da Maa da Appa zasu tafi, Maa ta riƙe hannuna tana cewa 'Kada ka damu Esho, zan dawo, kaide ka kula da kanka' ashe bazata dawo ɗin ba, ta yi tafiya me nisa, me nisan da bazan sake ganin ta a nan duniya ba, kullum ina cikin yawan mafarkai akanta, tana mun murmushi, ko muna wasa tare, ko....”

Sai ya yi shiru yana ci gaba da kallon Maryam, wadda itama ta kafe shi da ido tana jiran ta ji abinda zai karasa faɗi, hannunsa dama ya ɗago, bayan ya saki hannun Maryam, ya kama gefen fuskarta, hannunsa akan hijabin dake jikinta, yana motsa hannun nasa a hankali a gefen fuskarta, da ƙyar Maryam ta iya riƙe kanta tana ci gaba da kallonsa.

“Ba ƙaramin dace kika yi ba, kina da Maanmu, da Abbanki, ga ƴan uwanki, ni kuma ni ɗaya na rage a ahalina, babu kowa tare da ni sai dangina, ban rasa komai ba, ciki kuwa harda soyyayar dangi, amma na rasa abu da dama ta wani fannin, na rasa soyyayar uwa, na rasa kulawar uwa, na rasa soyyayar uba, na rasa kulawar uba, bani da ƙanwa ko ƙani, yaya mace ko na miji, ni kaɗai na ragewa kaina, sai kuma ke da Allah ya bani, samunki babban rabo ne a wajena Miriam, babban rabo sosai, kuma a koda yaushe ina gode masa idan ina sallah, dan shi kaɗai ne lokacin da nake da shi na addu'a, a da bani da addu'a sai ta Allah ya yaye min abinda ke damuna, amma yanzu kuma saide na godewa Allah da kyautar ki daya bani cikin rayuwata, kin zama wani tsagi na farin cikina Miriam, da idan ina murmushi ba har zuciyata nake ba, iyaka kan leb'ena ne kawai, amma bayan kin shigo rayuwata, abubuwa da dama sun sauya, ina murmushi harda dariya, kuma duka daga ƙasan zuciyata suke fitowa, idan baƙin ruhina ya tashi kowa guduna yake, dan kada na illata mutum, amma ke sai kika kusance ni, kika nuna min cewa ko me zan miki bazaki gujeni ba, Miriam irin ki suna da ƙaranci a duniya....”

Ya kai ƙarshen maganar yana sunkuyowa ya ɗora gashinsa akan nata, Maryam ta matse bed sheet ɗin da hannunta ke kai, tare da lumshe ido, tana jin sauƙar numfashinsa me ɗumi akan fatar fuskar ta, wai shi be san me take ji bane ?, ya kamata ya sama mata lpy, ba zata iya ba wallahi, abun ya mata yawa.

“Wifey...”

Cikin wata murya me kama da raɗa ya kira sunanta, Maryam ta ƙara rintse idanunta tana karanto duk addu'ar da ta zo ranta, bata amsa shi ba, kuma shima sai yaci gaba da kallon saman gashin idonta.

“Miriam you make home inside of my  heart, i wish that one day you will know what it feels like to make a home inside of someone's heart, eventually i find that one person that understand the melody of my soul, and now you are sing it back with ease, and see, it's beautiful....i find a women that can vulnerable with, while feeling completely safe, you mean everything to me Maryam, you complete me, tum mera aakhoka tara hai tu, (you are the star of my eyes)”

Ba komai Miriam take fahimta ba, jinta take kamar tana yawo a space, babu gravity ɗin da zai iya jawota ƙasa sam, ta kasa jurewa yanayin, ba zata iya ba, gaba ɗaya ilahirin jikinta rawa yake, kamar me jin sanyi ko kamun zazzab'i, wata ƙilama zazzab'in ne zai kamata, dan tana jin yanda jikinta ya ɗauki dumi kamar wadda ake gasawa.




Post a Comment

0 Comments