TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 48

 *BABI NA ABA'IN DA TAKWAS (48)*


*Kano Road, Hadejia Emirates*

*05:20pm*

Wata kyakyawar mota ce fara sol take tafiya a nutse. Daga cikin motar kuma Tafida ne da Maryam zaune.

Jiya suka sauƙa a gidan baban Neha dake abuja, kuma a can suka kwana, a jiyan Maryam ta gano dalilin da yasa Neha da Eshaan suke kama, dan baban Neha ɗin kamarsa ɗaya da Tafidan.

Bayan gari ya waye suka yi shirin tafiya, kuma Baban Neha ɗin wanda Maryam ta ji Tafida na kira da Appa shi ya basu motarsa, har gidan Neha ɗin ma sunje, wani gida Me kama da fada inji Maryam.

Dan gidan ba ƙarami ba ne, sbd ba su kaɗai ke rayuwa a ciki ba, akwai ƴan uwan mijinta a gidan.

Duk da ta gaji amma waƙoƙin motar sunfi gajiyar mata da kunne, dan haka ta shiga daddana botton ɗin sauyawa.

_🎶Kuzo gidan Ahmen ku gani_

_Na Garba me nasara a Ruwa🎶......_

Maryam ta tintsire da dariya a  sanda waƙar ta shiga playing, ita irin wannanƙoƙin a wurin Maanmu ko kakarsu Jaruwa ta saba jinsu, ashe shima yana jin irin su. Ta jiyo ta kalleshi a sanda ta ji yana rera waƙar shima, harda wani turo hula gaban goshi.

_🎶Mutum da ganin motar A ruwa..._

_Tilas yaka ba giwa hanya, yasan akwai manya a ciki_

 _Na Garba me nasara A Ruwa, Kuzo gidan Ahamen mugani🎶...._

Maryam kam me za ta yi in ba dariya ba, Tafida ya juyo ya kalleta.

“Cikkaken ɗan gargajiya ake faɗa miki”

Tana girgiza kai ta kai hannu ta sauya waƙar.

_🎶Gadar gayan Mamman ɗan sha'aibu_

_Gadar Gayan Mamman ɗan sha'aibu_

_Mota ki dakata ki aje ni a birnin gadar Gayan...._

_Direba dan dakata kaɗan zan sauƙa a birnin gadar gayan...🎶_

Yanzun ma dariya ta yi tana kallonsa, yanda ya dage bilhaƙƙi da gaskiya ya na bin waƙar.Ta sauwa waƙar wata ta shigo.

_🎶Khadal yen khabiye, ni yen arugul ban dale_

_Fasi faga bai maride, ani bani yallem madu fogum🎶...._

“Wato har waƙoƙin Telugu kake saurare?, dan na san wannan ba hindi ba ne,yafi kama da Telugu”

Se ya tura hular kansa baya kaɗan, yana gyaɗa mata kai.

“Ai ina jin Talugu ɗin ma, sanda muna makaranta akwai wani abokin mu Srinivas, ɗan talugu ne, kuma Mahesh ma yana jin Telugu, dan Babarsa 'yar telugu ce”

Ta gyaɗa kanta tana sauya waƙar dan ita har yanzu bata samo wadda take nema ba.

“Yare nawa ka ke ji a India”

Ya ɗan ɗaga kansa sama kaɗan yana tunowa, can kuma sai ya sauƙe.

“Mts, ina jin kamar biyar ne, Kinga inajin Hindi, Talugu, tamil, urdu sai bengali”

Maryam ta gyaɗa kai tana sauya wata waƙar.

_🎶Wataran wata rana, za'a kaiki gidana_

_Matsayin matata, kece madarata..._

_Na matsu, na matsu, na matsu naga wannan rana,na matsu..._

_Allah kaimu, Allah kaimu, Allah kaimu ranar nan.....🎶_

Maryam ta kuma sauyawa.

_🎶You hit my heart, oh, hit it like a heart attack...._

_We talking all the time like insomniac....🎶_

“Mts!”

Eshaan ya juyo ya kalleta.

“Me ya faru ?”

“Ni ban samu waƙar da nake so ba”

Se ya yi murmushi.

“Mun shigo gari ai”

Maryam ta kalli inda suke, bakinta ya buɗe cikin dariya, ta yi missing gida, ta yi bala'in kewar komai na haɗejia.

Farin cikinta be ƙara ninkuwa ba sai sanda taga sun wuce ƙofar fada sun nufi Garko. A ƙofar lungunsu ya yi parkinga.

Se da Maryam ta riga shi fita daga motar, bakinta fal murna, ta tsaya a wajen tana ta bin unguwar tasu da kallo.

A sannan Tafida ya zagayo inda take tsaye bayan ya fito mata da jakarta dake booth. Matasan dake zaune a kan bencina suna ganinsa suka ta so suka rufe shi suna ta miƙo gaisuwa.

Tafida be iya shariya ga matasa ba, seda ya tsaya suka gaisa har ya musu ihsani, sannan suka barshi ya tafi, Maryam kam har ta yi gaba, saida ya haɗa da sauri sannan ya cin mata.

A ƙofar gida taga auta da abokasa suna wasa, tamanta da wani Tafida dake binta a baya ta ruga da gudu inda suke tana faɗin.

“Auta!”

Shima jin Muryar yayar tasa yasa ya miƙe da sauri, yana ganinta ya ruga inda take shima yana dariya, suna haɗewa suka rungume juna, Maryam ta ɗaga shi masa tana juyi da shi, tuni batun zuwan Maryam ya karaɗe unguwa.

Maƙota da ƴan mata duka aka loƙo ana ganin Maryam da Tafida.

Sai da Maryam da auta suka gama yarintar tasu sannan ta ja hannunsa suka shiga cikin gidan.

“Maanmu wata sabuwar Ps5 ce ta fito...”

Hussain be ko ƙarashe ba, Maanmu da wata mata dake zaune a kan tabarma suka saka dariya, harda Hassan da ya fito daga banɗaki.

Ya kalli kwanon dambun da ke gabansa sannan ya kallesu.

“Ni fa ba santi nake ba, labarine kawai nake san baku”

Matar da ke zaune kusa da Maanmu tace.

“Babu wanda yace kana santi ai, kawai de labarin naka ne abun dariya ”

Sai kawai shima ya yi dariya yana kai loma.

“Wato anti Hanne ai a gidan nan babu girkin da za kuyi ya saka ni santi, Yaya ce kawai take yin girkin da ke sakani santi”

Kamar daga sama suka ji sallamar Maryan da Muhsin.

Gaba ɗayansu suka sakawa bakin ƙofar ido, ko amsa sallamar an rasa wanda ze yi.

Ita ɗince kuwa ta shigo, sede wannan Maryam ɗin tana da banbanci da waccan, wannan Maryam ɗin tana da jiki, kuma tafi waccan fari, amma maganar da ta yi yasa suka fahimci cewa ita ɗin ce.

“Wai baku ji muna sallama ba ne ?”

Ta ƙarashe tana zama kusa da Maanmu tare da rungumeta, Anti Hanne ta miƙe tsaye tana faɗin.

“Ko wannan itace Yayan?”

Ihun da su Hussain suka saka shi ya tabbatar mata da maganarta. Gaba d'aya suka zauna a gaban Maanmu suna ta yi Maryam sannu da zuwa.

“Kuma ina Yaya ?”

Maryam ta kalli Hussain, tana so ta tuno waye Yaya, nan take ƙwaƙwalwarta ta hasko mata Tafida dake tsaye a bakin ƙofa riƙe da jakarta. Ita ɗaukin ganin ƴan uwanta ma ya mantar da ita shi. Ta dafe goshinta.

“Oh!, yana waje, kaje ka shigo da shi ”

“Auta bani hijabina gashi can”

Muhsin ya miƙe sannan ya ɗauko mata hijabin, Maanmu ta karb'a ta saka, sai bin Maryam take da kallo yanda ta ga tasauyamata, duk da dama Anti fati tana fad'a mata yanda Maryam d'in tace suna zaman lafiya da mijinta, amma ganin 'yarta ta ya k'ara tabbatat mata da waccan magana.

“Sirikin mu ne zai shigo ?”

Maryam ta juya ta kalli matar da kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa bafulatana ce.

“Eh Hanne, mijin Maryam ne“

“Ah to nima bari na je na saka hijabi“

Cike da kokwanto Maryam ta bita da kallo har ta shige ɗakinta na da. Ta juyo ta kalli Maanmu.

“Maanmu waye ce wanna ?”

“Husain ka ɗauko wannan dardumar ta ɗakina ka shimfiɗawa Tafida”

Maanmu ta faɗi memakon ta amsa mata, ita fa kanta ya kulle, ta kasa ganewa.

Sallamarsa ta ji daga waje shida Hassan, Hassan ɗin ne ya fara shigowa sannan shi, kansa a ƙasa har ya zauna a kan dardumar da Hussain ya shimfiɗa masa, suna gaisawa da Maanmu Hassan yace da Maryam.

“Yaya a ina zan aje miki jakar ?”

Ta kalli jakar da ke hannunsa se taga jaka ɗaya, bayan ita tasan da jaka biyu ta taho.

“Ka kaimin ɗakin na”

“Ai yanzu baki da ɗaki a gidan nan, sai dai na Maanmu ”

Maganar Hussain ta ƙara kulle mata kai, amma ba komai zata tambayesu tunda Maanmu taƙi amsa mata, sai kawai tace.

“Kai min ɗakin Maanmun to”

A lokacin Hanne ta fito daga ɗakin Maryam na da, ta ja kujera ta zauna itama suna gaisawa da Tafida.

Duk yanda ya kai da gujewa kada Maanmu ta masa godiya sai da ta masa, shi kuma sbd baya san yawan godiyar yasa koda su Hussain suka turo masa lambarsu be bawa Maryam d'in ba, dan bayama so ta san da abinda yama 'yan uwanta.

Har ruwa aka kawo masa amma yace tafiya ze yi, sai da ya tashi ya fita sannan Maanmu ta kalli Maryam.

“Kije ki taka masa mana”

Ita gaba ɗaya rudanin dake kanta ya hanata cewa komai, a kunyace ta miƙe ta fita.

Can ta hangoshi har ya kusa fita daga lungun, ta bi bayansa, sanda ta isa wurin har ya shiga mota.

Ita ma seat ɗin gaba ta buɗe ta shiga.

“Akwai jakata ɗaya”

Ya juyo ya kalleta.

“Na sani ai, amma ai wannan kayan sakawar ki ne”

“Eh kayan sakawar, dama su nake faɗa”

“Keda ba'a nan zaki kwana ba, anjima zan zo na ɗauke ki”

Bata san sada ta furta “Huh?”

“Eh mana, baki da wurin kwana a gidan Maanmu, baki san an bawa wata ɗakin ki a gidan ba?”

Zuwa yanzu kam abun ya gama kulle mata kai, kenan har Tafida ma ya san da zaman waccan matar amma ita bata sani ba ?, to me yake faruwa haka?.

“Kije ku gana da ƴan uwanki, nima zanje na ga nawa“

Ita de ba haka ta so ba, tana san ta kwana a gida yau, a cikin 'yan uwanta. Dan ta yi kewar kowa a cikin su.”

Ta juya jiki a sanyaye zata fita, caraf ta ji ya riƙe hannunta, ta juyo ta kalleshi, a kan lips ɗinsa ya furta.

“I love you”

Bata ce Komai ba, dan kanta cike yake da ruɗani.

Ya saki hannunta ta buɗe motar ta fita, sai yanzu take kallon yanda jama'a suke binta kallo, gaba ɗaya maƙota an leƙo ana san a ga ƙwaƙwaf.

Ko da ta shiga cikin gidansu se ta ga su Hussain na irga kuɗi.

Ta zauna a inda ta tashi ɗazu tana faɗin.

“Wannan ribar shagon wayar ce?”

“A'a mijinki ne ya bayar yace a bawa Maanmu da Anti Hanne”

Ta ɗanyi murmushi, ita de kam ta ƙagu ta san wacece wannan Anti Hannen, gashi kuma tana zaune a wajen, babu damar ta tambayi su Hussain.

“Hassan ɗauko min jakar nan”

Hassan ya miƙe ya shiga ɗakin Maanmu ya fito mata da jakar, se yanzu Maryam take ƙarewa gidan kallo, har sabon fenti suka sake, an gyara gidan sosai.

Bayan Hassan ya kawo mata jakar ta buɗe ta shiga raba musu kayan tsarabar da ta kawo musu, kowa se murna yake har da Abti Hannen da bata tsara kawo gujirin da ita ba itama ta samu, harda maƙotansu.

TAFIDA POV.

Kai tsaye fada ya wuce, sai da ya yi parking motarsa a babban parking lot ɗin katafariyar fadar, sannan ya buɗe motarsa ya fito.

Kamar yanda aka saba, dogarai da hadima dama bayi sai kirari ake masa da miƙo gaisuwa.

“Tafida ɗan Tafida, ruwan kogi tafi sannu sannu wanda ya yi wargi zai halaka, giwa ta gama da masu ƙarfi ta wuce......”

Haka wani dogari me kaifin murya ya ci gaba da rangaɗowa Tafida kirari har ya shige soron farko.

Ya ci gaba da taka sorayen fadar har ya isa inda yake san isa, wato b'angaren Fulani Khadija.Sai da aka masa iso da ita sannan ya samu ya ganta.

Yana zaune a falo na uku ta fito cikin wannan tafiyar tata ta ƙasaita. Tun da ta fito take binsa da kallo, ya sauya mata sauyi ba ɗan kaɗan ba. Ita a yanda me martaba me bata labarin ya sauya ma sai ta ga ya fi, ya yi ƙiba ya ƙara haske, kai da ganinsa kasan cewa hankalinsa ya kwanta.

Zama ta yi a kan kujera tana amsa gaisuwar da yake mata.

“Ina Nadra?”

Sai da wasu sakkani suka wuce kafin ta amsa da.

“Taje wani bikin ƙawayenta”

Ya gyaɗa kansa.

“Ina Maryam ?”

“Na kaita gidansu, inshaallah zata zo ku gaisa”

Itama kan nata ta gyaɗa.

“Bari na saka a kawo maka abinci”

Muryarta ta faɗi cikin shirun da falon ya ɗauka.

“A'a ranki ya daɗe, sauri nake, dan a can gidana zamu sauƙa, zan shiga na duba jikin Galadima sannan na wuce, kuma dama mun yi magana da me martaba kan sai gobe zamu gaisa“

“Babu matsala, Allah kai mu goben, zaka iya tafiya”

Ya miƙe yana mata sallama sannan ya fice.

Fulani Khadija ta ɗaga kanta tana godewa Allah, zuciyarta cike take fal da farin ciki da kuma murna, murnar ta sauƙe nauyin marayan Allahn da aka ɗora mata, murnar ganin tilon ɗan da zata iya kira da nata na cikin farin ciki bayan wani abu da ta yi a rayuwarsa.

Tafida ya yi sallama a falon Fulani Sadiya, jakadiyar da ta masa iso ce a kan gaba, yayinda shi kuma ke biye da ita.

A gaba ɗaya zamansa a fadar wannan shine karonsa na biyu da ya shiga b'angarenta, na farkoma da Fulani Khadija suka fara zuwa sanda ta haifi Amina, bayan nan bai sake shiga ba.

Bin mutanen dake falon ya yi da kallo kafin ya samu waje ya zauna. Fulani Sadiya, Maimun, Amina da Nabil.

Ɗaua bayan ɗayan suka gaida shi, kafin shi ya gaida Fulani.

“Ya Galadima da jiki ?”

Ya tambaya yayinda suke gaisawa, Fulani Sadiya ta jinjina kai.

“Jiki da dama, sai godiyar Allah”

“To Allah bashi lafiya, ni zan wuce”

Ya ƙrashe yana miƙewa.

Ya kuma musu sallama sannan wuce.

Gidansa ya koma, yaje ya yi wanka sannan ya ƙara fita ya tafi asibitinsa.

*Unguwar Garko*

*Da 08:15pm*

Suna zaune a kan babbar tabarma, abinci suke ci suna hira, Hassan, Hussain da Muhsin suna ci a kwano ɗaya, yayin da Maanmu da Anti Hanne da kuma Maryam suke ci a kwano ɗaya.

Zuwa yanzu Maryam ta saki jiki da matar dan tana da kirki, kuma wani abu ɗaya ne ya gifta a tunaninta kan matar, da alama Abbansu ne ya yi aure, dan ko girkin daren ma ita ta yi.

“Yanzu da bana nan waye yake shara da wanke-wanke ?”

“Da da bakyanan Ko ni ko Hussain, amma bayan zuwan Anti Hanne kullum ita take yi” Cewar Hassan.

Maryam ta kalli fuskar matar ta cikin hasken wutar dake tsakar gidan.

“Hassan cover nake so me kyau“

Hassan ya kai loma yana miƙa mata hannu.

“Muga wayar taki”

Da hannunta ɗaya ta zaro wayar a cikin jakarta sannan ta miƙa masa.

“Inalillahi wa inna ilaihi daji'un Hussain kalli wayarta ka gani!”

Ya ƙarashe yana miƙawa Hussain ɗin.

“Kai miye ya samu wayar tawa ?”

“Babu abinda ya sameta, kawai de kuɗinta muke lissafawa”

“Ai nake gaya maka matar nan ta faso gari, kai baka ga hasken da ta yi ba?”

“Harda ƙiba ma ta ƙara”

Maryam ta girgiza kanta tana tauna abincin bakinta.

“Maryam Iya Ummi ta dawo fa“

Maryam ta tsame hannunta daga cikin trayn da suke cin abinci tana kallon Maanmu.

“Tana gari yanzu haka ?”

Maanmu ta gyaɗa mata kai.

“Tana nan, karkiga abinda ta riƙa yi akan wai anyi auren ki bata gari”.

Iya ummi itace babbar ƙawar Maryam tun tasowa, dan hatta da makaranta basu tab'a rabawa ba, da sukayi candy ne ita Maryam ta ta shiga Binyamuini, ita kuma Iya Ummin ta tafi Gashuwa. Ko sanda akayi bikin Maryam ɗin bata gari.

“Yaya akwai irin cover wayar taki”

“Me kwaliya fa nake so”

“Kar ki damu gobe zan kawo miki”

“Ah-ah su Yaya a india”

Cewar Hussain bayan yaga hoton da ke kan wallpaper wayar tata.

“India ?, mu gani”

Muhsin ya faɗi yana dawowa kusa da Hussain, daga haka kuma se hirar ta koma a kan India, Maryam na ta basu labarai akan wuraren da suka je, ta na yi tana nuna musu hotuna.

“Salamu Alaikum!”

Muryar Tijjani ta rangaɗa sallama daga bakin ƙofa, da gudu Muhsin ya miƙe ya yi kansa, Tijjani ya riƙeshi yana dariya.

“Kasan minene a nan ?” Tijjani ya tambayi Muhsin yana nuna masa ledar da ke hannunsa.

“Yalo ?”

“A'a agwalima ce”

Muhsin ya karb'a yana masa godiya, Tijjani ya ƙarasa shigowa cikin gidan, Hassan, Hussain, Maanmu da Anti Hanne duka suka masa sannu da zuwa, ya amsa yana zama a kan tabarmar shima, Anti Hanne ta miƙe ta kawo masa abinci.

Gaba ɗaya mamakinsu ya hana Maryam cewa komai, Abbansu ya sauya, amma yaushe hakan duk ta faru ita bata sani ba?, abun akwai ɗaure kai.

“Ah-ah ashe mutanen lagos ne a gidan”

Sai yanzu Maryam ta ankara da bata gaida shi ba.

“Abba ina wuni”

Tijjani ya amsa da fara'a kamar ba shi ba, daga haka kuma se ya shiga neman yafiyarta, har da saka mata albarka sannan ya rufe da nasiha.

Abun ya bala'in ɗaurewa Maryam kai, ashe akwai rana irin wannan da zata zo ?, koda a mafarki bata tab'a zaton ta.




Post a Comment

0 Comments