TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 25

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*25*

~~~

*Heart broken over a love that didn't even exist...*

***

*No.181, Guzape, Abuja...*

MISHAL POV.

Zaune take kan gadonta, babban yatsan hannunta na dama sanye a bakinta tana sha. Hannunta na hagu kuma riƙe da wani littafi me ɗauke da rubutun "The Happiest Baby on the Block" .

Kuliya ne ya shigo ɗakim yana dube-dube, tare da faɗin.

“Hafsat ina kika aje min cable ɗin system ɗina?...”

Ba tare da Mishal ta kalleshi ba ta amsa masa da:

“Ka duba drawerta. Yana ciki”

Drawer ya nufa, ya shiga duddubawa, kafin ya samo abun da yake nema, har ya juya ya nufi ƙofar ɗakin, sai ya tsaya ya kalli inda take. Abun na farko da ya fara kalla shi ne, sunan littafin dake hannunta. Wata dariya ta shiga ƙoƙarin ƙwace masa, amma sai ya shanye yana kallonta.

“Mishally!”

Hannunta cikin baki, kuma ba tare da ta kalleshi ba ta amsa da.

“Umm!”

“Me kike ne?”

Ya tambaya yana isowa jikin gadon, littafin ta sauƙe ta kalleshi.

“Littafi nake karantawa a kan yara!”

Ta amsa masa tana maida littafin saitin fuskarta. Dariya ya yi mara sauti, ya zauna a bakin gadon, hannunsa ya miƙa saitin side drawer ya aje cable ɗin da ya ɗauka. Sannan ya dawo da dubansa kanta, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana cewa.

“Yara kike so?”

Da fara'arta ta sauƙe littafin kan cinyarta, har wani farr ta yi da idonta kafin tace.

“Ehen nah!”

Ya yi dariya yana sosa kansa.

“Da gaske kina san yara?”

Sai kuma ta cire hannunta daga bakinta tana ɓata fuska.

“To wai miye na tambayar?”

“Wai da baki nake san yi”

Cikin sakan ɗaya wannan fara'ar da ta ɗauke a ɗazu ta dawo, da rarrafe ta ƙarasa kusa da shi tana ɗora hannayenta a kan cinyarsa.

“Da gaske wai?... Yaushe?”

Kansa ya girgiza.

“Sai bayan kin yi candy”

Fuska ta kuma ɓatawa tana ɗaukewa hannunta daga kan cinyarsa, bakinta ta turo gaba tana juya masa kai.

“To wai kai sai ka sawa mutum rai a kan abu kuma ka zo ka hana shi”

Shi de bai ce mata komai ba, ya ci gaba da kallonta yana murmushi.

“Ni dan Alah ka bani yanzu”

Ta kuma faɗi tana masa fuskar tausayi. Kansa ya kuma girgizawa yana ɗaga kafaɗarsa.

“Dan Allah Love Muffin!”

Ta faɗi tana kamo fuskarsa, idonta ya cika da ƙwallar kukan shagwaɓa.

“A'a fa?!”

“Ni dan Allah ka bani ina so....”

Kuliya na dariya yace.

“Ba matsala ke kika nema ai!”

*

“Hafsat!”

Kuliya ya ƙara kiran sunanta a karo na barkatai. Mishal dake duƙunƙune cikin bargo tana hawaye ta masa banza tana share hawayen.

“Magana fa nake...”

Ya faɗi yana taɓota. Hannunsa da ya taɓata da shi ta doke.

“Ni ka rabu da ni... Kuma Allah sai ya sakamin... Ashe dama ba kayanka ne baƙaƙe ba ka ɗai, zuciyarka ma baƙa ce”

Ta faɗi cikin kuka tana ƙara duƙunƙunewa. Kuliya ya ƙunshe dariya yana faɗin.

“To me na yi?... Ke ce fa kika ce kina buƙata”

Kuka ta fashe da shi tana rintse idonta gam.

“Allah ban yarda ba... Kuma idan muka haɗu da Anti Adawiyya sai na faɗa mata abun da ka min”

Dariya ya yi mara sauti yana kwanciya a gefenta.

“Ki yi haƙuri to”

“Anƙi a haƙura ɗin... Wayyo Allah na Anna... Wayyo Aki... Wayyo Anti Adawiyya!”

Ta ci gaba da faɗin abun da take faɗi a ɗazu.

“Kuma Allah sai ya mana hisabi, wannan sunansa zalunci, kuma Allah ya hana zalunci...”

Juyowa ya yi yana kallonta, duk da tana lulluɓe da bargo.

“Wai ba a muku biology ne?... Ya kamata a ce an muku a biology”

“An mana ai... Ai an mana, amma ai basu ce da wahala irin haka ba... Wayyo Allahna!”

Ta faɗi tana ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, saboda ƙasusuwanta da suke mata ciwo, ga wani zazzaɓi dake shirin rufeta, wani irin sanyi take ji yana shiga ko wace kusurwa ta jikinta. Kuliya ya yi dariya me sauti a wanna karon.

“Ai da ma ba za su faɗa muku cewar akwai wahala ba”

“Dariya kake min ko?...Ko... Ko?... Ko?”

Ta ƙarashe tana fashewa da wani kukan. A hankali ya buɗe blanket ɗin, har ya samu damar ganin fuskarta, ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye, ga kuma jan da fuskar ta yi, gashin kanta a yamutse, idon nan ma a koɗe.

“Ki yi haƙuri please!... My bad, and I'm truly sorry”

Ya faɗi yana rungumeta daga kwancen da take, dukan ƙirjinsa ta shiga yi, dan ita yau gani take nan duniya bata da maƙiyi kamar shi.

“I hope we can move past this, ko kina so ni ma na yi kukan?”

Sai kuma ta tsaya da dukansa da take, jin yanda muryarsa ta fito a sanyaye. Ta dakata da kukan tana kallon fuskarsa, wadda ya mata yanayin abun tausayi.

“To ni ka min alƙawarin ba za ka sake min ba!”

Cabɗi jam!, ai wannan ai shi ne wasa farin girki, ya faɗi a zuciyarsa, a fili kuma sai ya kyaɓe fuska yana girgiza mata kai.

“Ba zan sake ba”

Hanci ta ja tana kallonsa. Yayin da shi kuma a hankali yake motsa babban yatsansa a gefen fuskarta.

“I hate you Abu Aswad!”

Peck ya mata a goshi.

“Mishallyn Aliyu you are the sun, moon, and stars, i love you more than my morning coffee, my heart is pitter-pattering for you”

Naushi ta kai masa a ƙirji.

“I hate da gaske”

“Ni kuka na ce i love you da gasken-gaske... Jikinki akwai zafi sosai, yanzu ki kwanta, gobe sai mu je mu ga likita”

Kai ta gyaɗa masa tana lumshe idonta.

*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*

ZAID POV.

“Zuwa gobe za a tura takardar ƙara kotu, daga nan za a fara zaman shari'a”

Cewar wata garjejeyar murya da ke futowa daga cikin wata ipad dake aje gaban Zaid da Rhoda. A tare Rhoda da Zaid suka dubi juna. Kafin wannan muryar ta kuma faɗin.

“A yau aka kamo wasu daga cikin waɗanda Alhaji Bala yake hulɗa da su, dan haka kuna cikin haɗari, fatan za ku kula!”

“Ok sir”

Suka amsa masa a tare, kuma daga haka wayar ta katse.

“Yanzu yaushe za ki karɓi musulunci?”

Zaid ya tambaya yana duban Rhoda, a sanda yake rufe ipad ɗin. Rhoda ta yi murmushi.

“Zuwa ranar da kotu ta yanke hukunci, kuma daga nan zan je na duba dangin Mom. Sai kuma...”

Dariya Zaid ya bushe da ita ganin yau ɗaya Rhoda na kunyar furta masa wani abu. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa cikin faɗin:

“Iko sai Allah, abun mamaki Rhoda yau ke kike jin kunyata?”

Duka ta kai masa tana turo baki. Shi kuma ya yi dariya, dan ya san maganar aurenta take san yi.

“Allah Rhoda ke da Ammata kun raina ni, daga na yi abu sai ku kawo min duka... amma ba damuwa, na dena muki wasa”

Ya ƙarashe yana haɗe rai kamar gaske. Rhoda ta yi murmushi tana faɗin.

“Ba ka ji ne ai”

“Ji tsaurin ido, ni fa yayanki ne ba ƙaninki ba?”

“Yi haƙuri to” ya yi murmushi uana ci gaba da kallon ƙanwar tasa.

“Rhoda ki na san Zakar?”

Ya mata tambaya irin wadda ya saba mata a duk sanda magana irin wannan ta haɗosu.

Kanta ta gyaɗa masa tana murmushi.

“Allah ya tabbatar mana da alkairi Cuzzie”

*

“Me gida Raja wai ina muka shilla ne?”

Cewar Zuzu, wanda ke zaune a back seat na motar Zaid, daga gefensa kuma Jagwado da Alandi ne. A front seat kuma Zaid ne da Rhoda. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa.

“Ba na faɗa muku cewar aikin mu ya ƙare ba?... To wani wuri nake san kaiku”

Daga haka babu wanda ya sake cewa komai cikinsu, har suka ida Rehab, wato gidan da ake kawai mutanen da suke shaye-shaye, ko waɗanda shaye-shayen ya fara taɓawa ƙwaƙwalwa. Su Zuzu ba su fuskanci hakan ba sai da suka ga an shiga da su ciki.

*No.86, Garki 2, Abuja...*

RABI'A POV.

“Ammatan Raja!”

Zaid ya kira sunan Rabi, wadda ke kwance a kansa tana daddana wayarta. Yayin da shi kuma yake kwance a kan kujera. Rabi ta ɗauke idonta daga kan wayar da take daddanawa ta kalli fuskarsa.

“Au... Ina nufin 'Yan matan Yaya!”

Nan da nan Rabi'a ta sha mur, dan ya tuna mata da abun da take san mantawa da shi. Harara ta wurga masa tana juyar da kallonta kan wayarta. Zaid ya yi 'yar dariya.

“Wasa nake. Yanzu faɗamin, menene burinki a da, bayan kun yi aure da Yaya?”

Sai ta ƙara kallonsa cikin rashin fahimta, kuma tun kafin ta furta cewa bata gane me yake nufi ba yace.

“I mean, menene burinki, ko wani fatanki, ko mafarkin da kike, na irin rayuwar da za ki gudanar da shi bayan kun yi aure?”

Ba ta yi mamakin sanin Yayan da ya yi ba, dan a yanda ta fahimci mutum me aiki irin nasa, idan da hali har yanda hanjin jikin mutum ke aiki zai iya bincikawa. Wayarta ta aje a kan cikinsa tana ɗora hannunta kan ƙirjinsa. Idonta na kallon sama ta shiga faɗin.

“Farko dai auren mu, sai kuma mu zauna a wani ɗan ƙaramin gida, ba fa dole sai babba ba, kullum da daddare idan ya dawo, ya riƙa kunna mana wasan ball muna kalla a tv, ko da ba mu da tv a gidan, sai mu kalla a waya, ko ma de ya kasance laptop ɗinsa da shago. Idan wata rana kasuwa ta yi kyau, ya ɗauke ni a bayan mashin, mu shiga zaga gari ni da shi. Ɗan ƙaramin burina kenan. Amma cikin wattanni komai ya wargaje, na tsani Yaya Raj!” 

Zaid na wasa da geshin kanta ya furta.

“Wai kekam tsana ba ta miki wahala ne?”

Kallonsa ta yi na wasu 'yan sakonni, kafin ta miƙe daga jikinsa tana zuro da ƙafafunta ƙasan kujerar. Zaid ya kai hannunsa yana ɗaukan wayarta da ta aje masa a kan cikinsa ya miƙe zaune shi ma. Kallon gefen fuskarta kawai yake, yana san sanin abun da take tunani. Kamar Rabi ba za ta ƙara cewa komai ba, can sai tace.

“A sanda na taso ban san soyyayyar kowa ba sai ta Umma data Yaya Baby. Bayan rasuwar Baby sai ya rage daga ni sai Umma, bayan rasuwar Umma kuma sai na haɗu da soyyayar dangi. Bayan na bar wurin dangina na koma gidan mahaifina a nan ne aka fara koyarwa rayuwata wani sabon darasin da ko da wasa ban taɓa kawo shi a kaina ba. Tsana!, Kar ka yi mamaki idan na ce maka a tasowata ban san tsana ba, dan babu wanda ke nuna min ƙi... Kowa haba-haba yake da ni. Amma daga sanda na dawo gidanmu komai ya sauya, mafarkaina suka durƙushe, komai nawa ya hargitse, babu wanda nake raɓa na ji sanyi sai Anti Saratu. Kowa tsana yake nuna min. Daga baya kuma sai na haɗu da Zara, ita ma ba laifi, tana nuna min tata soyyayar. Bayan wani lokaci kuma sai ga Yaya. Shi ne na miji na farko da ya fara koyar da ni yanda ake so... Shi ne mutum na farko da ya fara buɗemin hanyar soyyaya. A lokacin da muka fara soyyaya da Yaya, a lokacin na fara zuwa Makarantar Brickhall. Daga malaman har ɗaliban makarantar babu wanda bai taka rawa wurin nuna min ƙi ba. Sai mutum ɗaya, wata yarinya ɗaya kacal, ita ce ta nuna min soyyaya. Daga lokacin kuma sai na haɗu da kai...”

Ta ƙarashe tana maida dubanta gareshi. Shi ma kuma ita ɗin yake kallo da lumsassun idanuwansa. Yana nazarin kalaman nata bi da bi.

“Rabin rayuwata ta a kan tsana take Raj, me ya sa ni ma ba zan koyi tsanar ba?, an nuna min cewa ba'a so na, me ya sa ni ma ba zan nuna cewar ba na san wanda ba ya so na ba?...”

“Shhhhhh!”

Zaid ya faɗi yana ɗora yatsansa a kan lips ɗinta. Kusa da ita ya matsa. Ya ɗora hannayensa a kan kafaɗarta.

“Ke abar so ce Adawiyya, kuma ko duniya za ta ƙiki, Adawiyya ni me sonki ne, ina ganin fuskar ɗan uwana a kan taki, haka kuma ina ganin fuskar Momma gwamitse da taki, above all Adawiyya ke ce 'yar favourite sistern Momma, so please ki dena faɗin haka, da ma rayuwa ba zata iyu ba tare da maƙiyi ba, hatta ɗan adam ɗin kansa ba zai cika ɗan adam ba tare da yana da maƙiyi ba”

Murmushi ta yi ta na kallon fuskarsa, ita kanta a wasu lokutan ba ta san wani kalar so takewa Zaid ba, ita dai kawai ta san tana sansa, tana sansa fiye da yadda za'a iya ƙirgawa.

Hannunta ta ɗago ta kai kan wannan chain ɗin na wuyansa, tare da maida shi cikin rigarsa, a duk sanda za ta ga chain ɗin a waje sai ta sa hannu ta mayar masa da shi cikin riga. 

Jikinsa ya ƙara janta, hakan ya bata damar kwantar da kanta a kafaɗarsa.

“Zuwa gobe ki shirya zan kaiki islamiyyar nan”

Kai ta gyaɗa masa domin ta gane wace islamiyya ce, jiya yake faɗa mata cewar yana nema mata wurin karatu a wata isalamiyya nan kusa da su, tun da tace ita ba za ta ci gaba da karatun boko ba.

“Allah ya kaimu goben”

“Ameen”

Zaid ya amsa.

*Say i love you to your problems and maybe they will leave you one day too.*

***

*No.181, Guzape, Abuja...*

MISHAL POV.

“Zauna a hankali!”

Cewar Kuliya yana zaunar da ita a kan kujera.

“Did you feel better now?”

Kai ta gyaɗa masa. Don tun jiya bakin tsiwa da na surutu ya mutu murus, saboda yanzu haka daga asibiti suka dawo, fuskar nan a koɗe, kuma ajeme, ta yi jajawur.

“Na kawo miki abinci?”

Kanta ta girgiza tana faɗin.

“Ni school zan je”

Kuliya ya girgiza mata kai.

“No way Teddy Bear. Ki tambayi wani abun da ban, amma ban da zuwa school”

Daddafawa ta yi ta miƙe tsaye tana kallonsa.

“Ni school zan je to”

Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa yana ci gaba da kallonta.

“Ba ki ga halin da kike ciki ba ne Hafsat?... Ba ki da lafiya fa!”

Kanta ta girgiza idonta na cika da ƙwalla. Yau za su na da exams, kuma ita za ta iya wasa da komai a duniyar Allahn nan amma ban da exam, ko faɗuwa ta yi a exam har jinya take wani lokacin. Bare a ce result ɗinta ya yi ƙasa da ta biyu, ai ranar kuwa za ta yini tana kuka.

“Ni na warke, kuma zan iya zuwa school ɗin”

Ta faɗi ƙwalla na mata zuba.

“Hafsat! Ba ki ji me na ce ba ne?,babu zuwa school, faƙat!”

Cewar Kuliyan kusan a tsawace. Nan take Mishal ta fashe masa da kuka tana zama a kan kujera.

“Da ma ai na son ba so na kake ba... Da ma na san ka tsaneni, in ka san za ka hana ni zuwa school me ya sa ka min... Ka min...”

Sai ta kasa ƙarasawa tana fashewa da wani sabon kukan. Kuliya ya ɗaga kansa sama. Shi kam Allah ya haɗashi da mata.

“Je ki shirya na kaiki!”

Ya faɗi ya na  sauƙe kansa. Ɗif, kukan da take ya tsaya, ta miƙe tsaye a daddafe tana share hawaye. Bayanta ya bi da kallo har ta shige corridor. Ban da rigima irin ta Mishal, me zai sa ta je school a irin wannan yanayin da take ciki?, hatta da tafiyarta ta sauya.

Bayan ta shirya cikin uniform ta fito, ba dan ya so ba haka ya kaita makarantar ya sauƙeta.

*No.86, Garki 2, Abuja...*

RABI POV.

Zaune take daga bakin gadonta tana latsa wayarta. Ta shirya tsaf dan zuwa islamiyyar da Zaid ya ambata mata, yanzu haka shi take jira. Ji ta yi zuciyarta na tashi, hakan ya sa ta aje wayar hannunta. Jin cikinta murɗawa ya sa ta miƙe tsaye, sai kuma ta ji amai, ba shiri ta nufi banɗaki da gudu.

Amai ta shiga yi kamar me shirin amayo hanjinta, duk abun da ta ci na safiyar tas ta zazzage shi. Kuma bayan ta gama aman sai ta ji kasala ta kamata, ta ji jikinta duk ba daɗi. Kafin ta fito daga banɗakin ma sai take jin juwa na ɗinbata. Da ƙyar ta iya ƙarasawa ta zauna a bakin gadonta, hannunta na dama dafe da cikinta.

A dai-dai lokacin Zaid ya shigo ɗakin yana kiranta, ba ta samu damar amsawa ba, face binsa da kallo kawai da take, ganin yanayinta ya ɗarsa masa wani zargi a ransa.

“Baki da lafiya ne?”

Kanta ta girgiza masa tana miƙewa.

“Lafiyata ƙalau”

Be yarda ba, amma ba ya so ya takura mata, sai kawai ya gyaɗa kansa ya na kama hannunta.

“Na fahimta... Kin shirya?”

Kanta ta gyaɗa tana ɗan cije baki, saboda cikinta da take jinsa babu daɗi.

“Raj!... Me muke a nan?”

Muryar Rabi ta tambaya, a sanda ta ga Zaid ya kawosu wata football academy, makarantar da ta yi ta lokacin tana yarinya, dan a sanda Ummanta ke da rai nan take kawota training ɗin ball.‘As Roma Football Academy’ haka sunan makarantar.

Zaid be amsa mata ba, sai fita da ya yi daga motar, sannan ya zagayo ta ɓangarenta, ya buɗe mata motar, mamaki ya ƙi barin kan Rabi, haka ta fito baki buɗe, sai bin wurin take da kallo, wurin da rabonta da shi kusan shekaru shida kenan.

“Zuwa yanzu ta girma... Dan haka ba daga rukunin da ta tsaya za ta ci gaba ba, za mu turata cikin rukunin sa'o'inta”

Cewar shugaban makarantar, yayinda Zaid da Rabi ke zaune a tsallaken teburin office ɗinsa. Zaid ya gyaɗa kansa, duk da ba yau ya fara faɗa masa hakan ba, tun ranar da ya fara zuwa makarantar shugaban ya sanar masa da wannan batun. Kuma ya yarda da hakan, shi ya sa ma ya kaita aka mata gwaji a asibiti, kafin ta fara buga ƙwallon da ta kasance burin rayuwarta. Juyowa ya yi ya kalleta. A dai-dai lokacin da ita ma ta kalleshi, idonta ya ciko da ƙwalla, bakinta har rawa yake, ta ma rasa abun da za ta ce da shi, sai kawai ta kafe shi da ido tana kallo.

Da haka suka bar office ɗin, aka bata kayan da zata riƙa sakawa idan ta zo makarantar, wata jar jersy ce, da wandonta, shugaban ya sanar musu da cewar zuwa gobe za su dawo, domin za su mata gwaji, idan ta ci gwajin da za su mata, za ta iya fara karɓar horo tun daga ranar.

Suna tafe a mota ledar kayan na kan cinyar Rabi, hannunta ta kai ta fito da jersyn ta ɗagata sama tana kallo. ‘ADAWIYYA’ shi ne abun da aka rubuta a bayan rigar. Ƙwallar da take ta shanyewa tun ɗazu ce ta gangaro kan kuncinta. Sai ta ga kamar tana rayuwa ne cikin mafarki, domin da ƙwallo a mafarki take ganinta, bayan hargitsin da ya ahigo rayuwarta sai ta manta da ƙwallon. Ta haƙa wani wawaken rami a zuciyarta, ta cilla burikanta na rayuwa, ta binnesu, don a lokacin gani take rayuwar tata ta zo ƙarshe, labarinta ma ya ƙare, komai ma ya ƙare. 

Shigowar Zaid rayuwata ya sauya komai, ya sauya yanda take kallon kanta, ya sauya yanda take ganin rayuwa, ya cika mata burikanta na rayuwa, duk abubuwan da take ganin ba masu iyuwa ba ne sun iyu, ta rasa me zata ce da shi, tace ta gode?, a'a, godiya ta yi kaɗan ta isar da shi, addu'a ita ce kawai abun da ya kamata ta masa, sannan ta ba shi ko wace kulawa, ƙauna da soyyaya. Ganin ya nufi hanyar Kaura ya sa ta share hawayenta, don bayan wani lokaci me tsayi, yau Allah ya yi za ta haɗu da ƙanwarta.

Sai da suka fara zuwa suka ga Rhoda, kafin ta fice ita ɗaya, bayan ta da faɗa musu cewar za ta je ta ga ƙanwarta, Zaid be hanata ba, don shi ma ya na so su tattauna da Rhoda kan case ɗinsu, saboda suna kyatata zaton zuwa gobe za'a shiga kotu.

Kanta tsaye Rabi ta shiga makarantar, masu gadi sai tambayarta suke, kan dalilin dena zuwanta makarantar, ita kuma tana amsa musu da rashin lafiya ta yi, kuma su ma sai suka yarda, saboda ganin tabon dake kwance a gefen fuskarta. Duk da  sun ga sauyi sosai a tare da ita.

Kafin ta kai ss3 har ta fara hawaye, saboda ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, ta ƙagu ta haɗu da Mishal, don ta bata labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu.

Cikin wata irin sa'a, tana isa ƙofar ajin ana kaɗa ƙararrawar break, hakan ya sa ta tsaya cike da zumuɗi tana san ganin fitowar Mishal. Sai da ko wani ɗalibi ya fice daga ajin, kafin Mishal ta miƙe tana muzurai, sai ciza baki take don tafiyar ma da ƙyar take, haka ta shiga taku cikin ƙarfin hali, har ta kai waje.

Ba tare da ta lura da wanda ke tsaye a bakin ƙofar ajinsu ba ta fara tafiya ta na nufar playground. Rabi'a ta lura da yanayin tafiyarta, amma kuma ɗaukin ganinta ya sa ta ture komai tace.

“Mishal!”

Cak Mishal ta tsaya da tafiyar da take, sakamakon sauƙar sautin muryar yayarta da ta ji, yayarta mafi soyiwa a ranta, yayarta da take ji da ita, yayarta da take cikin halin damuwa na rashin ganinta. 

“... Kin ji abun da ya faru da ni!”

Cewar Rabi, a sa'ilin da ta ɗiga aya a ƙarashen labarin da take bawa Mishal, suna zaune ne kan kujerun da suka saba zama a da, Mishal wadda idonta ya cika da ƙwalla ta kalli yayarta. Duk da Yazid bai samu damar ci mata zarafi ba, amma ta san yaya zafin abun yake, ta san irin baƙin ciki da ƙuncin da ake shiga, ta san zafi da tabon da abun kan barwa 'ya macen da ta fuskance shi. Ita ba ta da wani wayo sosai, amma ta san irin ƙasƙancin da mata 'yan uwanta kan fuskanta, idan har basu kai budurcinsu ɗakin mazajensu ba.  Duk da ita Adawiyyan ta tsallake wannan ramin.

“Yaya ina so na faɗa miki wani abu”

Rabi ta share hawayenta tana kallon Mishal.

“Kina kama da Aliyu, kuma na san ke ma kin san hakan, kina da danganta da shi?”

Rabi ta yi murmushi tana ɗauke kai.

“Wata ƙila idan na faɗa miki ba za ki yarda ba. Amma mijinki cousin brother ɗina ne, sannan kuma shi ne ƙanin mijina. Ɗan biyunsa ne, amma abun da ya shiga tsakaninsu ya rabasu ne... ban sani ba”

Wani irin shiru ya gifta a wurin, ba ka jin komai sai sautin wucewar iska. A cikin wannan shirun, Mishal ta kunce ta kuma saƙa ya fi sau a ƙirga. Kenan wannan wanda take gani a tsallaken makarantarsu shi ne Zaid ɗin da Adawiyya ta aura?. 

“Da... Da ma Raja shi ne Zaid ɗin?”

Mamaki ya kama Rabi.

”Kin san shi ne?”

Mishal ta gyaɗa kanta da sauri ta na share ƙwalla.

“Na sanshi...”

Rabi ta yi ajiyar zuciya tana ɗaga kanta sama.

“Ya kamata mu san abun da ke faruwa a tsakaninsu”

Rabi ta faɗi tana sauƙe kanta ƙasa. Mishal ma kai ta gyaɗa mata cike da gamsuwa.

“Yau idan muka koma gida zan tambayi Aliyu”

Rabi ta yi murmushi.

“Ni kuma zan tambayi Zaid”

Sai kuma suka yi dariya a tare, ashe soyyayar da sukewa juna ba za ta faɗi ƙasa ba, ashe Allah ya hukunta zamowarsu facalolin juna. Dariyar da Mishal ta yi ce ta sa jikinta jijjiga, hakan ya sa ta yi famu, sai ta ɗan cije lips ɗinta cikin jin zafi. Sai a lokacin Rabi ta lura da abun da yake faruwa da ƙanwar tata.

“Me yake damunki Ƙanwata?”

Nan da nan ƙwalla ta cika idon Mishal, ta turo bakinta gaba tana shirin fashewa da kuka.

“Wallahi Anti Adawiyya Abu Aswad mugu ne, kuma zuciyarsa ma baƙa ce kamar kayansa, da ma ai na faɗa masa cewar sai na faɗa miki idan muka haɗu...”

Nan take Rabi ta gane inda zancen ya dosa, amma kuma sai sunan da ta kira mijin nata da shi ya bata dariya.

“Abu Aswad kuma Mishal?”

Mishal ta share ƙwallar da ta zubo mata.

“Abu Aswad mana, ba shi ne ba kullum cikin saka baƙaƙen kaya, shi ya sa na saka masa sunan...”

“Na ji kin ce kin gaya masa cewar za ki gayamin abun da ya miki, da ma ya sanni ne?”

Mishal ta kuma goge ƙwalla.

“Ya sanki mana. Sanda kika ɓata shi na sa ya yi ta nemanki, kuma na san cewa shi ma ya gano cewar an saceki , amma shi ne ya ƙi faɗa min”

Haƙuri Rabi ta shiga bata, kafin ta ƙarashe da bata shawarwari kan yadda za ta kula da kanta, da kuma gyara jikinta. Basu rabu ba sai da suka yiwa juna alƙawarin sanin dalilin rabuwar waɗanan 'yan uwan biyu.

*No.86, Garki 2, Abuja...*

*07:30pm*

ZAID POV.

Gama wayarsa da shugabansu ke da wuya, ya ji wayar ta sa na ringing. Hakan ya sa ya duba screen ɗin wayar, don ganin me kiran. Ganin Kawu Abdullahi ne ya sa shi yin murmushi, ya na ɗaga kiran.

Gaisawa suka yi cike da girmamawa, kafin dalilin kiran ya taso.

“Ɗazu muke jin wani zance a gida. Wai ka kai Rabi'a makarantar ƙwallon ƙafa!”

Zaid dake tsaye a ƙofar ɗakinsa ya sosa kansa cikin jin nauyi, kafin yace.

“Eh haka ne”

“To tun wuri, ka yi gaggawar janye wannan ƙudirin naka... Ka bar ganin ita matarka ce, mu iyayenku ne, tun farko ya kamata ace ka shawarce mu kafin ka yanke hukunci a kanta. Ko a sanda take yarinya da mahaifiyarta ta kaita makarantar ba so muke ba, dan de muna ga yarinya ce, shi ya sa muka yi shiru. Amma a yanzu ta girma, tun da har mun mata aure, dan haka ba zamu ɗauki wannan shashancin ba. Tana mace me ya haɗata da wata ƙwallo?, zaman gida da kula da tarbiyyar yara shi ne ya dace da ita, ba gudu da gajeren wando a kan idon tarin mutane ba!...”

Haka Zaid ya ja bakinsa ya yi shiru, har Kawun ya kai ƙarshe a faɗan nasa bai ce masa ƙala ba, sai da ya tabbatar da Kawun ya kai ƙarshe a wajen amayar da abun da ke bakinsa kafin ya seta kamillalliyar muryarsa, ya shiga koro bayani a natse, kuma cikin da girmamawa.

“Na fahimce ka Kawu, kuma duk abun da ka faɗi gaskiya ne. Amma kuma ita ma Adawiyya tana da gaskiya. Ka san a ina ta yi gaskiya?”

Kawu Abdullahi dake zaune a kusa da su Baba ya juya ya kallesu, dan kuwa suma suna jin duk maganar da Zaid ɗin yake, sai kuma ya girgiza kansa cikin faɗin.

“A'a, sai ka faɗa”

“Lokacin da ta farfaɗo a asbiti, ta kalli idona tace min maza ba su da adalci, kansu kawai suka sani; kuma kasan dalili?”

Ya tambaya ba dan ya na buƙatar amsa ba, dan kafin ya amsa masa ya ci gaba da cewa.

“Dalilin shi ne; mu maza a kullum gani muke mune a gaba, dan haka dole duk abun da muke so shi za'a ayi, hakan ba wai kuskure ba ne, saboda mu Allah ya bawa girma, amma kuma su ma suna da nasu 'yancin. Domin ko addini ya basu 'yanci, daraja da kima, sai de ni kuma a yau ba ma duba hakan, sai namiji ya auri mace, ya zaunar da ita a gida, ya hanata rawar gaban hantsi, ya sa ƙafa ya take mata burinta da kuma 'yancinta, ga shi de ba ta son abun da yake mata, amma saboda ganin ita macace sai ta haƙura ta ja bakinta ta yi shiru. Kawu a mafiya yawan lokuta muna dannewa mata hakkinsu, suna da baiwa kamar mu, suna da shauƙi kamar mu, suna da zuciya kamar mu, duk abun da zai fusata mu suma zai iya fusata su, banbanci mu da su shi ne, su sukan iya jurewa abun su shanye a cikinsu, wata dan 'ya'yanta, wata dan iyayenta, wata ma dan mijin shi kansa, haka za ta jure rintsi da wuya. Kawu, Adawiyya ta shiga taskun rayuwa kala-kala, taga iftila'i da ban da ban, yanzu ne ya kamata ace ta samu jin daɗi da hutu, a yanzu ya kamata ace burukanta sun cika. Ni kuma ina son ta yi farin ciki, kuma na yi alƙawarin sama mata duk wani abu da zai dawwamar da murmushi a fuskarta. Ƙwallo mafarkinta ne, lefi ne dan na temaka wurin ganin ya zama gaskiya?!”

Shiruuu, har bayan shuɗewar wani lokaci, a cikin wannan shirun Baba dake kishingiɗe ya miƙe zaune da kyau, cikin alfaharin kasancewar Zaid jika a gareshi, Kawu Abdullahi kuma nadamar kiransa da masa wannan kashedin yake. Kasa cewa komai ya yi, ya kashe wayar. Jin wayar ta katse ya sa shi sauƙe wayar. 

Sannan ya fita daga ɗakin, dan da ma niyyar fita yake, kiran shugaban nasa ya same shi. Shi ya sa ya tsaya ya amsa saboda muhimmanci kiran. Kitchen ya nufa, dan ya san ba za ta wuce can ba.

Damm, zuciyarsa ta harba bindiga, lokacin da ya saka ƙafarsa a cikin kitchen ɗin, abu na farko da ya fara arba da shi shi ne, Wutar gas a kunne tana ci. Irin waɗanan dalilan ya sa baya san shiga kitchen, ko da magana yake san yi da Rhoda idan har tana kitchen sai de ya haƙura. Ba shiri ya ji kansa na juyawa, duniyar ta fara masa duhu, numfashinsa ya shiga kokawar ɗaukewa.

Rabi dake wanke nama a sink ta juyo da sauri jin fitar wani kalar numfashi.

“Ga ruwa”

Cewar Rabi tana miƙa masa ruwa a cikin wani glass cup, Zaid da ke zaune kan kujera a falo ya ɗago da kansa ya kalleta. Kafaɗarsa ya daga ya na miƙa hannunsa tare da karɓar glass ɗin. Rabi ta zauna a gefensa tana shafa kafaɗarsa a sanda yake shan ruwan. Ita ta karɓi cup ɗin ta aje, bayan da ya kammala shan ruwan.

Gefen fuskarsa take kallo cike da damuwa. Har zuwa lokacin tana shafa kafaɗarsa a hankali. 

“Na zubo maka abinci?”

Zaid da ya cilla duniyar tunani ya girgiza mata kai, ya na jingina da bayan kujera, hakan ya sa Rabi ta ɗauke hannunta daga bayansa, ta dawo da shi ƙirjinsa tana masa tausa. Ganin har zuwa lokacin be dawo dai-dai ba ya sa tace.

“Me yake damunka wai?”

Kallon fuskarta ya yi na wasu 'yan sakkani, sai kuma ya kama hannunta dake kan ƙirjinsa, ya kwantar da ita akan ƙirjin nasa, ta yanda har tana iya jiyo sautin bugun zuciyarsa dake shirin ɓalla allon ƙirjinsa ta fito.

“Na san komai a kanki, ya kamata a ce kema kin san komai akaina!...”

Tun kafin ya kai ƙarshen labarin nasa Rabi ta fara hawaye, tunawa da ta yi cewar ɗan uwansa da yake so, kuma yake tunani ya mace yana raye.

“Zaid!”

Ta kira sunansa tana sharar ƙwalla. Kanta Zaid ya shafa yana amsawa.

“Aliyu ya na raye!”

Wani irin bugu da ta ji zuciyarsa ta yi ya sa ta yi saurin tashi daga jikinsa, dan a tunaninta ko zuciyar tasa ta buga ne gaba ɗaya. Amma kuma sai taga har lokacin yana da rai, sai de kuma kamar ya mace, dan kallonta kawai yake, amma jikinsa a ƙame. Wai me take faɗi ne?, Aliyu yana raye?, Aliyunsa bai mutu ba?. A'a, wata ƙila dai kunnensa ne ke haihuwa, ko kuma Rabi'a tana faɗin hakkan ne dan ta kwantar masa da hankali. Aliyu na raye?.




Post a Comment

0 Comments