TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 39

 *BABI NA TALATIN DA TARA (39)*



*Hanam fashion house, Gwarinfa, abuja*

HARIS POV.

“Me ya faru ?”

Ya tambaya yana kallon Hanam data kirashi tace yazo. Sai kawai ta girgiza masa kai, sannan ta ɗauko wani ƙaramin envelope ta miƙa masa.

“Kasan SSGF ai ?”

Ya karb'i envelope ɗin yana kallonta sannan ya kalli envelope ɗin.

“Mall ɗin Falaq ?”

Ta jingina da jikin kujera tana gyaɗa masa kai.

“Eh ita, kaje ka kai mata wannan pls”

Har zai ce wani abu, amma sai kawai ya yi shiru, ya miƙe zai fita, ƙofar da aka turo yasa shi dakatawa.

A razane Hanam ta miƙe tsaye, ganin wanda ya shigo, bakinta a buɗe take kallon suɗayen idanunsa, wanda ya kafa mata su yana kallonta, a take wurin ya fara sauyawa a idonta.

Office ɗin ya rikiɗe ya koma mata ƙofar gidanta na USA, yanda yake kallonta a yanzu haka ya kalleta a time ɗin.

Waɗanan shuɗayen idanuwan irin wanda Arya ya gada daga wurinsa. Da ƙyar fatar vakinta ta furta sunan da ta riƙe ta yi haddarsa a cikin kanta.

“Gabriel!!”

*Flash back......*

A shekarun baya Hanam fashion sun samu takardar kwantiragi da ga kamfanin The House of Sofia couture dake New York USA, suna buƙatar da C.E.On Hanam Fashion house da ta zo ta yi aiki dasu na shekaru biyu.

Sun yi yarjejeniya a kan hakan, sannan suka tsara komai. Har zuwa lokacin da Hanam ɗin ta shirya ta tafi can USA ɗin.

Sun fara aiki cikin nasara, domin komai na tafiya dai-dai, kuma sunajin daɗin aiki da Hanam ɗin.

Wata ranar monday, wadda Hanam ta kira da baƙar rana. Ranar da ta mata mugun tabo a dayuwarta, ranar da ta zama sanadiyyar shigowar wani haske rayuwarta, ranar da ta zana silar rushewar rayuwarta.

*

Zaune suke ita da abokan aikinta a office ɗinsu, a lokacin kusan 10:00pm, sun gama haɗa kayansa za su fita.

“Guys, me zai hana muje bar yau”

Cewar Camilla

“A'a ni bana shan giya”

Hanam ta faɗi tana buɗe musu ƙofa.

“Ai ba sai kin sha ba, kawai muje mu ɗanyi rawa”

Cewar Tomas, ba haka Hanam taso ba amma taga suna san hakan, dan haka ta furta abinda ya rikito da duniyarta daga sama zuwa ƙasa, kalaman biyu ne, amma fasirinsu ne yasa komai na rayuwarta hargitsewa.

“Ok muje!”.

*3679 st, Queens, New York Doha Bar lounge*

Wurin cike yake da 'yan mata da samari, banda kiɗa me ƙarfi babu abinda ya ke tashi a wajen, wasu na zaune suna shan barasa, wasu kuma na rawa.

Haka su Hanam suka shigo wajen, gaba ɗaya sai wajen ya bata ƙyanƙyami, ita bata tab'a zuwa irin wajen nan ba. Daga can inda babu mutane suka zauna, Camilla ta yi musu oder na giya, tasa a kawowa Hanam ruwa kawai dan shi tace tana buƙata.

“Gabriel kalli can!”

Kyakyawan baturen me blue eyes da farar fata irin tasu ta turawa ya juyo ya kalli inda abokin nasa ya ke nuna masa.

“Wacce da ga ciki ?”

Ya tambaya yana rarraba idanunsa a kan matan biyu dake wurin.

“Balarabiyar mana”

Ya saki wani kasaitaccen murmushi a sanda ya haɗa ido da ita.

“Tana da kyau, bari naje na gwada sa'ata”

Yana miƙewa abokan nasa suka saka ihu suna masa tafi.

Hannunsa riƙe da wine glass wanda ke ɗauke da giya ya ƙarasa wajen da suke zaune.

“Sannun ku de 'yan mata”

Camilla ce tace.

“Gabriel sannu”

Baki washe ta furta hakan, dan duk wanda ke zuwa doha bar yasan Gabriel, musamman 'yan mata da ke matowa a kansa.

“Menene sunanki kyakyawa ?”

Hanam bata ko kalleshi ba, tun ɗazu da suka hada ido ta ji tsanarsa ta daki ƙirjinta, ta tsani mashayi.

“Maganafa nake....”

Ya yi maganar yana shafar damtsenta, Hanam ta miƙe a fusace sannan ta ɗauke shi da mari. Ji kake tsit!, wajen ya yi shiru, sai kiɗan dake tashi kawai, idon kowa ya dawo kansu, wannan wata me sa'arce haka ta mari Gabriel.

Hannunsa kan kunci Gabriel ya miƙe tsaye, wata wutar masifa da bala'ice ke ci a idonsa.

Hanam ta nuna shi da ɗan yatsa cike da kashedi tace.

“Kada ka kuskura ka sake, ni ba irin akuyoyin da kasaba bi bace ka kula da abinda ka ke!”

Kuma tana kaiwa nan ta ɗauki jakarta ta bar wurin.

“Sannu Gabriel”

Abokinsa ya faɗi, yayin da yake miƙo masa handkacief, ya karb'a a fisge yana goge jinin daya fito daga bakinsa, abinka da fatar turawa ba wani ƙwarin arziki gareta ba, ɗan marin da ta masa shine ya fasa masa baki haka.

Hanyar da Hanam ɗin ta bi ya bi da kallo

“Me ya kamata a mata ?”

“Dolene na sameta a yau, sai na ɗanɗana mata kuɗarta, zata san ta yi wasa da Gabriel Vicente”.

*House 1011,188 power street, Brooklyn New York*

*Da misalin 1:30am*

Hanam ce zaune a falon gidan, domin bayan zuwanta garin nan ta kama haya, kuma wajen yana kusa da wurin aikinta, shi yasa ta kama gidan.

Coffee take sha, yayin da take waya da Jabeer (wanda zata aura).

Ƙarar door bell ce ta karaɗe falon, dan haka tace dana cikin wayar.

“Ana ƙwanƙwasa ƙofa babe, ma yi magana daga baya”.

“Ok i love you”

“Me too, bye”.

Daga haka ta sauƙe wayar, mayafinta ta ɗauka ta rufe kanta, sannan ta nufi ƙofar, ta wani ɗan ƙaramin rami ta leƙa dan ganin me danna door bell ɗin, sai taga mutum tsaye, kansa sanye da p-cap ta shagon Joe's pizza, haka ma rigar jikinsa, kansa a sunkuye yake, hakan yasa bata iya ganin fuskarsa ba.

Mamaki ya kamata, itafa ba ta yi order ɗin komai ba, dan haka ta buɗe zata faɗa masa cewar ba ita bace ta yi order ba, may be gidan gaba ne.

Tana buɗewa ƙofar tace

“Ba nan ban....”

Maganar ta maƙale a maƙoshinta sbd kansa da ya ɗago, yana mata wani irin kallo da blue eyes ɗinsa, da ƙyar bakinta ya iya furta sunan da ta ji Camilla ta kirashi da shi ɗazu.

“Gabriel?.........”.


*Present day....*

“Fita min da ga office”

Cikin ƙaraji da fishi ta yi maganar, tana kallon mutumin da ke gabanta. Idonta a bushe, babu ko alamar hawaye.

Bai fasa shigowa ba, shida wata mace biye a bayansa, wadda suke da tabbacin matarsa ce.

“Hanam me ye faruwa ne wai ?”

Haris ya biɗa a ruɗe, sam ya kasa gane abinda ke faruwa.

“Hanam listing to.....”

“I said get the hell out of here!”

Ta faɗi tana nuna masa hanyar da ya shigo.

“Dan Allah ki tsaya ki ji abinda yazo damu...”

Hanam ta kawar da kanta daga barin kallon fuskokinsu, hakan ya bawa matar damar cewa.

“Na san cewa mijina ya miki kuskure, amma dan Allah ki yafe masa, yanzu haka abinda ya miki shine yake bibiyar mu, wattani shida da aurenmu ya yi haɗarin mota, kuma an tabbatar mana da cewa bazai sake haihuwa ba, mu kuma muna matuƙar san haihuwa, haka muka shiga neman duj hanyar da zata sada mu da samun ɗa na kan mu, amma bamu samu ba, daga baya yace dani ya tab'a yin wani kuskure a baya, wata ƙila shine yake bibiyarsa, dan haka muka shiga bincike a kan ki, maƙociyarki ce ta sanar mana cewa ke yar nigeria ce, kuma ta faɗa mana inda kike aiki har take sanar mana da cewa kin haihu ma, munje can inda ki kayi aikin, kuma sune suka bamu address ɗin wannan wajen naki, dan haka muka taso ƙafa da ƙafa dan muzo mu baki haƙuri.....”

“Kun gama ?,......To ku fita!”

“Hanam ya kamata a ca.....”

“Ku fita nace!”

Matar ta kalli mijinta da idanuwanta da suka cika da ƙwalla, kafin idonta ya kai kan wani hoto dake manne a jikin bango, hoton wani ƙaramin yaro ne, yana kama da matar da suke tsaye a gabanta tana musu cin mutincin.

Amma kuma farin fatarsa da kuma ƙwayar idonsa irin ta Gabriel ɗinta ce, sak irin nasa ne. Hakan ke nuna mata cewar wannan shine ɗan da ta haifa, ɗan da ta haifawa Gebriel. 

Hannunta na rawa ta ɗaga tana nunawa Gabriel hoton, a lokacin har ƙwallar da ke tare a idonta ta zubo.

Shima kansa ya juya ya kalli wurin, idonsa ya sauƙa a kan hoton, ya juyo ya kalli Hanam sannan ya kalli hoton, shima sai a lokacin ya zubar da hawaye.

“Wannan shine ɗan da ki ka haifa?....”

“Kar ka kuskura ka sake magana a kan ɗana!”

Ta yi maganar tana nuna masa ɗan yatsa, ya girgiza kansa.

“Wannan ba ɗanki ba ne ke kaɗai, ɗan mu....”

“Kada ka ƙara dan ganta ɗana da kai, kai ba ubansa ba ne, Arya ɗana ne ni kaɗai !”

“Arya ?, haka sunansa ?”

Gaba ɗaya kan uchenna ya kulle, ya kasa gane komai, kawai binsu yake da kallo baki buɗe.

Gabriel ya durƙusa guwowinsa ƙasa hannayensa a haɗe yana kuka kamar ƙaramin yaro.

“Na roƙeki Hanam, Sbd uban gijin da ki ke bautawa kada ki min haka, na roƙeki”

“A wacan ranar, nayi maka roƙo irin wannan fiye da yanda za'a iya ƙirgawa, amma baka kula ba, baka amsa ba, saida ka aikata abinda zuciyar ka ke raya maka, yanzu haka nima bazan saurare ka ba, ka fitar min daga office, daga kamfani na, daga garina, daga jasata, daga nahiyata, idan zai iyu ma ka bar min duniyar, inaga kamar zai fi”

Matar Gabriel ta dafa shi itama tana kuka, ta riƙe kafaɗarsa har ya miƙe. Sun juya zasu fita sai Gabriel ya tsaya, ya juyo ya kalleta.

“Idan zai iyu, ki sanarwa da ɗana cewa ni ne mahaifinsa”

Daga haka ya juya suka fice daga wurin.

Uchenna ya juyo ya kalli Hanam wadda idonta yake a bushe babu ko alamar hawaye.

“Ka je kawai, i am okay”

Sai kawai ya gyaɗa kansa, duk rintsi de ai zata komo gida, sai ya tambayeta ya ji meke faruwa. Dan zuwa yanzu ya fara fahimtar inda zancen ya dosa.

*

“Uche manyan gari, ashe ana ganin ku ?”

Muryar Falaƙ ta tambaya, yayin da Uchenna ke zaune a tsallaken teburinta, ya yi murmushi.

“Ana ganin mu mana, kune de ku ka b'uya”

Falaƙ ta yi dariya.

“Ga wannan wai tace na kawo miki”

Falaq ta karb'i 'yar envelope ɗin, ba sai ta buɗe ta ba, dan tun farko sun yi magana, dan haka kawai sai ta miƙe tana faɗin.

“Biyo ni”

Bayanta ya bi suka fita har waje, b'angaren studio ya ga sun nufa a cikin mall ɗin.

Kuma suna shiga Falaq ɗin ta yi magana da me kula da studio ɗin sannan ta kalle shi ta furta abinda ya sauya rayuwarsa tun farko har ƙarshe.

“Ka shirya yin waƙa ?”.


MARYAM POV.

“Zuwa jibi yace zamu tashi, dan Allah ki faɗawa Maanmu”

Maryam ta faɗi, yayin da wayarta ke kare a kunnenta, tana waya da Anti Fati, Muryar Anti Fati ta fito daga cikin wayar.

“To ba damuwa, zan faɗa mata, Allah ya tsare, ya kiyaye hanya, and Maryam dan Allah a kula, kinga mijinki wayyaye ne, gashi ya taso cikin jinsin kyawawa, wallahi Maryam idan bakya kula da shi kina zaune zaki ji anyi wuff da shi”

Maryam ta yi murmushi, a duk sanda za suyi waya da Anti Fati sai ta mata magana irin wannan, dan haka tace.

“Insha Allah, a gaida Ƙauna, da babansa, kuma kicewa Maanmu ina gaida ta”

“Zasu ji, sai anjima”

Ta sauƙe wayar da ga kunnenta, hijabin dake jikinta ta cire, ya rage daga ita sai wata farar high neck top, da wata bluen high waist skirt.

Yau ta tashi da niyyar gyara ko ina na gidan, dan ya faɗa mata cewar idan sunje india zasu jima, dan ko kayan abincima yace wanda tasan zai lalace ta bayar shi.

Cat ears headphones ɗinta ta ɗauko, ta yi connecting da wayarta, sannan ta kunna waƙa.

Da ga ɗakinta ta fara gyaran, inda ta cire curtains ɗinsa duka, ta zubasu a cikin wani basket da ta ɗauko daga store, ta yi moping ko ina da ina, da gogge shi tas, sannan ta ɗauki basket ɗin ta yi waje.

Balcony ta shiga nan ma ta gyaggyara komai, ta fito ta shiga ɗakin Eshaan, nan ma gyaran ta masa fiye ma dana ɗakinta, dan ɗakinsa ya fi nata yawan tarkace. 

Shi ma nasa curtains ɗin ta ciro, ta sauƙo ƙasa, suma gaba ɗaya curtains ɗin ta ciccire su, ko wani lungu da sako ta share ta gyara, har da gym ɗin da za ta iya cewa ita bata wani ga amfaninsa ba, dan tun bayan zuwanta gidan baifi sau uku ta ga ya shiga ba, ita kuwa bama ta shiga, dan bata ga abinda zata yi a ciki ba.

Duka curtains ɗin da ta ciro ta zube su a cikin wishing machine. Ta kunna sannan ta fito, kitchen ta shiga ta dudduba kayan ciki, yau tana so ta yiwa Eshaan girki, kuma ta kai masa har wajen aiki, dan haka ta zage ta masa girki mai kyau, inda ta girka masa, dambun shinkafa da chicken kebabs haɗi da kunun ayar da ta haɗa shi tun safe.

Sai da ta kammala komai sannan ta zuba su a cikin wani kyakyawan basket, ta gyara kitchen ɗin tsaf.

Ta fita taje ta kwaso curtains ɗin da suka gama wankuwa, ta fita can saman gidan, inda take shanya, ta shanya su a wurin. Ta dawo ɗakinta ta ɗauki wayarta ta kira Devid.

“Dan Allah Devid so nake ka zo, za ka kaini wani waje, amma kada ka bari Eshaan ya sani”

Muryar ta ta faɗi bayan devid ɗin ya ɗaga wayar sun gaisa, Devid ya ɗanyi jim, kafin yace.

“Madam ai baze iyu na ɗauko motar bai sani ba, tun da sai na karb'i key a wajen sa”

“Eh kaje ka karb'a, amma kada kace masa wajena zaka zo, kawai ka nemi wani abun ka faɗa masa”

“Ok”

Ya amsa bayan ɗan wani lokaci, tana katse kiran nasa sai ta kira lambar 'SUNDAR'.

“Yaya ne matar mijinta ?, ya kike ya gidan ki ?”

Sai da Maryam ta ɗanyi dariya sannan tace.

“Lafiya lau nake, kai fa?”

“Main theek hoon”

“Sundar nifa bana jin hindi”

“Au haba ?, ai ko ya kamata ki koya, dan idan naje india bana hausa”

Maryam ta kama baki.

“To yanzu de fassaramin me kace”

“Cewa nay lafiya ta ƙalau”

Maryam ta gyaɗa kai cikin cije leb'enta na ƙasa.

“Fita nake san na yi, shi ne nace bari na tambaye ka...”

“Minti ɗaya, Devid ne ya shigo”

Sai kawai ta gyaɗa masa kai, tana jin maganar da suke da devid ɗin, har ya ɗau keyn motar ya bashi sannan ya fita.

“Ina jinki Miriam”

“Nace ina so na fita ne, shi ne nace bari na tambayeka”

Bai ko tambayeta ina zata je ba, yace.

“An baki dama, kije Allah ya dawo dake lafiya”

“Ameen, sai ka dawo”

“Umhum!”.

Tana aje wayar ta faɗa banɗaki, dan tana so ta yi wanka kafin Devid ya ƙaraso.

Ta gama wankan ta fita ta saka wani swiss lace purple, sannan ta saka hijabinta har ƙasa pink color, kasancewar akwai ratsin pink a jikin lace ɗin, ba ta yi wata kwalliya ba, mai kawai ta shafa, sannan ta ɗauki jakarta da kuɗin da ta ciro a account ɗinta jiya.

Tana kitchen wayarta ta yi ringing, hakan ke nuna mata cewar Devid ya ƙaraso, dan lambarsa ce.

Dan haka ta ɗauki basket ɗin, tana kashe fitilun kitchen din, ta fito ta kashe ta falon ma, sannan ta fita. 

Shiɗin ne kuwa, yana zaune cikin mota yana jiranta, ganinta riƙe da kaya yasa ya fito zai karb'a amma sai tace.

“No Devid, ka barshi kawai”

Ta zagaya gidan baya ta buɗe, ta saka basket ɗin, sannan itama ta shiga. Devid ya tayar da mota yana fita daga gidan.

“Ina zamuje Madam”

“St Nicholas Hospital”

Mamaki ya ɗan kama shi kaɗan, amma de bai ce komai ba har suka isa.

Shi ta tambaya ya faɗa mata a inda office ɗin Eshaan yake.

Tana fitowa daga elevator suka haɗu da wannan Dr. Abubakar ɗin, suka gaisa a mutunci kafin yace.

“Wajen Dr. ki ka zo ko ?”

Maryam ta gyaɗa masa kai, yo idan ba wurinsa ta zo ba, wurin zata zo ?.

“Ai suna meeting ne, nima can zanje yanzu haka, amma ga office ɗinsa can, ki je ki jira shi a ciki...... Joke zo ki karb'a mata kayan nata, ki kai mata office ɗin Dr. Eshaan”

Ya ƙarashe yana magana da wata nurse, Kamar Maryam zata cewa nurse ɗin ta bari kawai zata iya ɗaukan kayanta, amma kuma karamcin da Dr. Abubakar ya mata yasa bata ce komai ba, ta miƙa mata kayan sannan ta bita a baya har zuwa office ɗin, a kan wani coffee table Joke ta aje basket ɗin, sannan ta fita.

Tana fita ta haɗu da wata ƙawarta suka tafa tana faɗin.

“Yau kuma mutumin naki, wata macace ta zo nemansa”

Ƙawar tata ta kama baki.

“Ke matarsa ce fa, ai sanda kika ta fi gida ya kawota nan bata da lafiya”

“Ke dan Allah?, yanzu kaf matan ƙasartasu, ya rasa wacca zai aura sai wannan ?”

Ƙawar ta tab'e baki.

“Su suka jiyo de”.




Post a Comment

0 Comments