TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 47

 *BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI (47)*

{ESHAM}

~~~

*R 78, TC Maurya Hotel, New Delhi, India*

*11:15pm*

“Dama Mahesh ba musulmi ba ne?”

Muryar Maryam ta tambaya, yayin da take shirya kayan sakarwarsu a cikin jaka.

Eshaan da ke zaune a kan gado yana danna system ya juyo ya kalleta.

“Eh, ɗan addinin hindu ne, ai ina jin kaf abokamu daga ni sai Arjit ne musulmai”

Ta gyaɗa kanta tana zipping ɗin jakar, sannan ta ajeta a ƙasa kusa da wardrobe.

Ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, ta fito ta saka hijabinta, sannan ta kwanta a,kan gadon, tana kallon Eshaan dake gefen gadon har yanzu yana danna system.

“Yanzu gobe gida zamu koma ?”

Sai ta ga ya dakata da danna systen ɗin, kafin ya juyo yana kallonta ta cikin ɗan guntun hasken da ya rage a ɗakin.

“Indian ta isheki ne ?”

Sai ta gyara kwanciyarta tana girgiza masa kai.

“Naga mun gama komai ne, to me zamu jira ?, ko akwai inda zamu sake tafiya ?”

Sai ya girgiza kansa yana rufe laptop ɗin, sannan ya ajeta a kan bedside drawer.

Ya kwanta yana jan bargon, kansa na kallon sama yace.

“Mun gama zuwa ko ina, kawai de ina ga ya kamata a ce mun ɗan yi yawo a delhi”

Ya ƙarashe ya na juyowa ya kalleta, itama shi take kallo.

“Ina zamu je to?....”

Ta tambaya a sanda yake kashe sauran fitulun da suka rage a ɗakin, Maryam ta rintse idonta tana ƙanƙanme pillown da take kwance a kai, har yanzu bata dena tsoron duhu ba, kullum zai kashe wuta sai ta tsorata.

Hannunsa ta ji yana lalubar nata, kafin ya haɗe tazarar dake tsakaninsu ya janyota jikisa, kanta ya sauƙa a kan kafaɗarsa, hannayensa biyu duka suka kewaye waist ɗinta.

Maryam ta ƙara duƙunƙunewa a cikin jikinsa, a hankali ya lalubo kunnenta sannan yace.

“Akwai wurare da yawa da zamu iya zuwa a Delhi, Qutub Minar, India gate, safdarjung tomb, Humayun's tomb, lodhi art district suna da yawa sosai, ina so ki yi yawo sosai a india”

Maryam ta ƙara matse jikinta dake cikin nasa, har wa yau ta kasa sabawa da wannan yanayin.

“Yanzu de ki kwanta ki huta, dan a gobe zamuje mu zaga gari, kuma a goben jirgin mu zai koma nigeria, kinsan idan mun koma lagos kwana biyu za mu yi mu tafi haɗejia”.


*Chida Event Center, Jabi, Abuja, Nigeria*

*07:40pm*


HANAM POV.

Babban ɗakin taron a cike yake maƙil da jama maza da mata, daga can wajen zaman amaryam da ango kuwa Kamal Muhammd Hakuɗau ne da amaryarsa Kalisa Usman.

Daga b'angaren zaman dangin ango kuma gaba ɗaya ƴan uwansa ne maza da mata sai hira ake ana cin abinci, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci cewa suna cikin tsantsar farin ciki.

A cikin su kuma akwai Hanma. Wanda itama ke sanye cikin irin nasu kayan, kuma harda ita ake hirar.

“Ya Hanam wai ki zo inji Ya Harees!”

Nabila ta faɗa mata da ɗan ƙarfi, kasan cewar hayaniya da kiɗan dake tashi a wajen. Ta juya ta kalleta sannan ta miƙe tsaye.

“Hanam wai Ina Aryaan ne ?”

Ta juyo ta kalli Hafsi, sannan kuma ta shiga hange-hange ko zata hango shi, ita rabonta da shi tun da safe. Allah ya temaketa ta hango shi zaune a kan wani table.

Ƙanenta maza ne gaba ɗaya a kan table ɗin, hatta kayan da ke jikinsa ma irin na su ne. Ta nuna wajen da hannunta.

“Gashi can a wajen su Hafiz”

“Bari naje na karb'o shi, ai basu kaɗai suke san sa ba”

Hanam ta yi dariya tana tafiya, sai kuma ta tsaya ta juyo ta dawo wajen tana faɗin.

“Nabila yana ina ?”

“Ni dai a waje na ganshi, ki duba cikin motarsa”

Sai ta gyaɗa kanta, sannan ta fita daga wajen da ƙyar sbd tarin mutanen dake wurin.

A parking lot taga motarsa dan haka ta je ta buɗe zata shiga gaba, amma sai taga baya gaban, yana baya, ta rufe ƙofar gaban ta buɗe ta bayan sannan ta shiga. Kuma tana shiga ya janyota jikinsa ya rungume.

“Wai bakwa tausayi na ne?, kun barni daga ke har Arya ”

Hanam ta saƙala hannayenta ta wuyasa a sanda ya saketa.

“Kamar baka ci abinci ba ma”

Sai ya gyaɗamata kai.

“Tun safe banci komai ba, kinsan mu ne abokan ango, duk gwagwarmayar da akayi da mu akayi ta”

“Awwww, Alah sarki rex (king), sannu”

Ya kai hannunsa yana janyo wata leda dake gidan gaba na motar, ya aje mata ledar a kan cinyarta bayan ya ɗauko.

“Ga abincin nan, a bani na ci”

Ta ɗanyi dariya tana buɗe kayan dake cikin ledar. Sannan a lokaci guda ta ɗago ta kalleshi cikin hasken futulun waje dake shigowa cikin motar, farar shaddace sanye a jikinsa, kansa harda hula, kuma ta ga kayan da ke jikinsa irinsa ne a jikin ango, dan yanzu sun ɗiki, aminta suke shi da Kamal kamar waɗan da suka ta so tun yarinta.

“Ni fa na yi tunanin Mama zata zo”

Uchenna ya jingina da jikin kijerar motar yana cire hular kansa, sannan ya shafa kansa.

“Wai Zakiyya ce za ta yi graduate, shi yasa bazata zo ba”

Hanam ta buɗe wata roba tana saka spoon a ciki.

“Ai mu ma kuwa ya kamata a ce munje, ka je wurin Baba yau ?”

Ta kai masa lomar farko tana masa tambayar, ya haɗiye abicin da ya gama taunawa sannan yace.

“Da safe kawai naje, amma ban koma ba, wata ƙila kafin mu koma gida sai muje”

“Kaida wa ?”

“Ni da ke”

Ya amsa mata yana karb'ar abincin da take ba shi.

“A'a ni yau bazan kwana a gida ba”

“Da izinin wa ?”

Sai kuma ta yi shiru, dan ya kamata a ce shi sai da ta tambaye shi tukunna.

“A ina za ki kwana ?”

“A gida, su Ya Kamila ma duka a can zasu kwana”

“Shikenan tun da kina so bazance a'a ba, sai yaushe kenan?”

Spoon ɗin hannunta ta aje a cikin robar abincin sannan ta riƙe fuskarsa da duka hannunta biyu, ta yi pecking fuskarsa.

“Thank you mi rex (my king)”

Hannunsa ya kai ya kamo waist ɗinta ta baya, sannan ya shiga kissing ɗinta, da ƙyar ta samu ta ja baya da shi.

“Ka ci abincin”

Ta faɗi kanta a ƙasa, sai ya yi murmushi yana karb'ar abincin.

“Ina Arya ?”

“Yana wurin su Hafiz”

“Kwaliyarki ta yi kyau, me yasa kika dena kwalliya yanzu?, ba ki ga yanda ta miki kyau ba”

“Sanda na kusa zama uwa na dena, kuma har bayan da na zama uwar ma ban ci gaba ba”

Hannunta ya kama, sannan ya ƙara matsota cikin jikinsa sosai.

“Yanzu kuma kin zama mata, mijinki yana so, dan Allah dan shi ki riƙa yi”

A hankali kamar me raɗa ya furta hakan, yana yi yana shafa gefen fuskarta da ta ɗau heavy make-up.

Kafin ya kuma kissing ɗinta kaɗan, ya ɗan ja baya yana haɗe fuskarsa da tata, suka shiga musayar numfashi.

“I love you Rex”

Ya ɗan ja baya da fuskarsa kaɗan,sannan ya yi pecking gefen fuskarta.

“I love you too”.


*House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos*

*09:56pm*

MARYAM POV.

A hankali ta fitar da gaba ɗaya kayan da ta siyo na gujirin da zata kaiwa ƴan gidansu, jiya suka dawo daga India, kuma basu bar delhi ba sai da ya kaita duk inda ya lisaafa mata harma da inda be faɗi ba, kuma har kasuwa suka shiga, a nan taga takalma da ɗankunnaye ta tsaya ta si yi wanda zata kawowa ƴan uwanta, tun da yace gobe zasu wuce Haɗejia.

Jiya ta tambaye shi me yasa zasu je haɗejia.

_ “Kinga hutun dana ɗauka da saura be ƙare ba, kuma idan hutun nan ya ƙare bana jin za'a ƙara barina na ɗauki wani hutun kwana kusa, kuma kema kinga hutun ki da saura, kafin ya ƙare se muje mu dawo”_.

Idan aka bincika zuciyarta cike take fal da farin ciki a sanda ya bata wannan amsar. Bayan wasu watanni zata je ta haɗu da Maanmu, Hussain, Hassan da auta.

A cikin jakar da za ta yi tafiyar ta saka kayan, sannan ta ɗauki hijabinta ta saka ta fito ƙasa.

Tafida baya gidan, dan ya faɗa mata cewar zai je asibiti ya dawo, kitchen ta shiga dan ta sama masa abinda zai ci, dan ita bata jin yunwa, taci abincin da Maman Ilham ta aiko mata, duk da babu wasu kayan girki a gidan, dole ne bayan sun dawo da ga haɗejia su yi siyyaya.

TAFIDA POV.

Da sallama a bakinsa ya shigo parlon, amma be samu kowa ba kuma dama yasan cewa ba zata wuci kitchen ba, dan haka kai tsaye ya wuce kitchen ɗin.

Har ya buɗe ƙofar bata san ya shigo ba, sai ji ta yi anyi hugging ɗinta ta baya.

wata iriyar iska ta shaƙa, wadda ta taho mata da ƙamshinsa, a hankali ta ɗora hannunta a kan nasa, a sanda shi kuma yake saka kansa a cikin wuyanta.

Ba shiri ta yi saurin juyowa a cikin hannayensa ta riƙo gaban rigarsa, hannayenta da ke b'ace da fulawa suka b'ata gaban rigar, sai kuma ta janye hannun nata ganin ta b'ata masa jiki.

Sai ta ga yana dariya, hannayen nata biyu ya kamo ya ƙara meda su kan kirjinsa, sannan ya kara fuskarsa a tata.

“Borrow me a kiss Miriam”

Maryam ta zaro ido tana jan fuskarta baya, amma sai ya saka hannayensa yana dawowa da ita.

“To ba bashi, kiss me then”

Zaburar da ta yi yanzu tafi ta ɗazu. Kansa ya gyaɗa mata.

“Kiss me pls, i like your soft lips”

Roƙon da yake mata yasa bazata iya musawa ba, dan haka sai ta ɗago da hannayen ta ta kama fuskarsa har tana bata masa ita da garin fulawar dake hannun nata, ta ɗan yi kissing saman lips ɗin nasa kaɗan, sannan ta sake shi tana ja baya.

”Me ki ka yi wannan ?, wannnan ai ba kiss ba ne Miriam, bari na koy.....”

A guje ta zare ta fice da ga kitchen ɗin, Tafida na dariya ya juyo ya kalli fulawar da take kwabawa, be san me zata ta yi da ita ba, amma sai ransa ya ba shi kamar ɗan ƙwantalaka za ta yi, dan ga manja da yaji nan ta aje.

Da ƙarfinsa ya yi amfani ya yi girkin da kansa, bayan ya gama ya zuba mata a warmer, sannan ya zauna yaci nasa.

Har kusan sha ɗaya bai ganta ba, hakan ke nuna masa cewar wata ƙila ta yi bacci, shi kuma ta barshi gadin gida.

miƙewa ya yi da ga kan kujerar da yake, ya kashe duka wutar gidan, sannan ya koma ɗakinsa ya yi wanka ya saka kayan baccin sa ya kwanta.

Sai yaji baccin ya gagare shi, dan a kwanakin nan ya saba sai da ita yake bacci, ko jiyama da ya iya yin bacci shi ɗaya gajiya ce a jikinsa.

A zaune ya miƙe, sannan ya sab'a slide sandals ɗinsa, ya fita ta balcony ɗin ɗakinsa ya yi wani irin talle da ba duka ɗan adam ze iya ba, ya dira a balconyn ɗakinta.

Kamar yanda ta saba yau ma bata kashe wutar ɗakin ba, a kan gado ya ganta ta duƙunƙuna cikin bargo.

Kamar yanda shima ya kasa baccin haka itama ta kasa, ita ko jiyan ma ba ta iya yin baccin ba. Jin gadon yana motsi yasa ta yi saurin juyawa, aiko ta yi kyakyawan gani, dan tana juyawa Tafida ya janyota jikinsa ya ƙanƙame kamar me shirin medata ciki.

“Me yasa za ki tafi ki barni”

Ya faɗi yana ƙara ƙanƙameta, Maryam ma ta saka hannayenta biyu tana rike shi.

hannunsa ya ɗaga setin switch ɗin ɗakin ya motsa, wutar ta mutu, yau ɗinma sai da ta razana, amma kuma Tafida ya riƙeta da kyau, yana shafa kanta har sai da ta yi bacci.

Shi kuma se ya kasa baccin, kawai ya saka ta a gaba yana kallo, duk da babu wani wadataccen haske a ɗakin.

jinta a jikinsa da kuma kallonta da yake irin haka yafiye masa baccin.




Post a Comment

0 Comments