TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 17-18

*PAGE* *17*~*18*



*Driver* ne yayi parking cikin gidan Hajja inda MEENAL ta fito ta shiga parlour'n gidan, da sauri Hajja ta fara mata barka da zuwa, cikin ladabi ta gaishe da Hajja, Ummie ce ta fito daga kitchen da sauri MEENAL ta rungume ta tana cewa"Ummie na ki yafemin nayi nadamar abin da nace miki"


Shafa kanta tayi tace"ba komai b'acin rai ne"


Nan suka had'u sukayi ta hira,    ya rage daga ita sai Ummie, rik'o hannun ta tayi tace"Ummie na Dan Allah zan rok'e ki alfarma guda d'aya ki taimake ni kiyi min shi"


Tace"ina Jin ki mene ne shi?"


Tace" Ummie na Dan Allah ki aure Daddy na"😰


Mik'ewa tsaye tayi tace"are out of your sense?, look maganar nan ta tsaya a nan bana son ki sai ke maimaita shi kinji ni ko?"


Cikin marairaicewa tace"haba Ummie na ko dan ni ya kamata kuyi aure, ina son ganin ku tare please Ummie na kar kice A'a"


Mik'ewa tsaye tayi ta bar gurin, yayin da MEENAL ke rok'on Allah yasa Ummie'n ta ta amince, Sai dare ta koma gida, 


Bayan Daddy ya gama dinner ne taje ta same shi a parlour'n shi, inda shi ma ta rok'e shi da ya aure Ummie'n ta, ai kamar ta sosa Mai inda yak'e k'aik'aiyi, yaji kuma dad'in yanda tazo mai da wannan maganar dan har ga Allah Yana son Zainab sosai,bare kuma ga 'yar su MEENAL, cikin farin ciki yace"don't worry inshallah zanje in same ta da maganar"


Tayi farin ciki sosai tace" yauwa Daddy na I'm proud of you thanks so much"



Yaji dad'in ganin yanda tayi farin ciki yace" Allah yayi miki albarka, oya yanzu kije kiyi barci dare nayi"


Nan tayi mai sallama ta tafi,




The following day



MEENAL na Kitchen tana had'a breakfast sai ga NUWAIRA ta shigo cikin gadara da tak'ama, indomie ta dafa tanayi tana wak'a duk Wai Dan ta ba MEENAL haushi, MEENAL ko ajikinta bai Dame ta ba, haka NUWAIRA duk ta b'ata gurin, ta tafi ta barshi haka, 





Da missalin k'arfe 8:00pm 


FAWAS yayi parking a cikin gidan su MEENAL, Kiran ta yayi a waya sai ta fito, tana sanye da Riga da skirt na wani orange less mai kyau, tasa gyale orange a kanta,


Tun daga nesa ya hangota ba k'aramin kyau tayi ba, fuskar ta sai shining yakeyi, ga hasken wuta dake k'ara hasko ta, cikin natsuwa ta k'arasa gurin motan shi,


Sauko yayi daga saman motan shi yace" tsarki ya tabatta ga Allah Wanda yayi wannan hallitar" 


Murmushi tayi cikin kunya ta sunkuyar da kan ta,


  Murmushi shima yayi yace"you look beautiful"


Gaishe shi tayi ya amsa cikin farin ciki sannan ta shigar da shi cikin parlour'n bak'i sannan ta kawo mai drinks,


Gurin ya d'auki shiru kamar na 5 minutes sannan ya katse shirun da cewa" na jima ina son gaya miki wani abu Wanda yake cikin zuciya na, zan so ki bani time dan in gaya miki"


Murmushi tayi tana wasa da zoben hannun ta, saukowa yayi daga kujera ya durk'usa a gaban ta tare da cewa" ko zaki iya fad'a min meyasa har yanzu kike tare da zoben nan?" ya nuna zoben,


Tace" please ka zauna tukun sai in gaya maka"


Yace"no until you tell what I asked you"


Murmushi tayi tana murza zoben hannun ta, tace" Yana min kyau Kuma haka kawai nake son shi"


Murmushi yayi cikin farin ciki yace" AMINA"


D'ago da kanta tayi cikin mamakin yanda ya Kira sunnan ta dan bai tab'a Kiran ta haka ba Kuma cikin wani irin murya,


Cikin sanyin murya mai dad'in sauraro yace" zuciya na ya jima da k'aunar ki tun ranar da na had'u dake nake son ki, amma na kasa fad'a miki *I REALLY LOVE YOU MEENAL*"


Mik'ewa tsaye tayi cikin tsananin mamaki dan ko a mafarki bata tab'a tunanin FAWAS zai so ta ba, ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, 



Cikin tsoro shima ya Mike' ganin halin da ta shiga yace" Please accept my love for you, MEENAL ina miki son da bazan iya rayuwa Babu ke ba, amma zan Baki lokaci kiyi tunani da kyau"


Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tace" ban tab'a tunanin cewa zaka so ni ba, I.... really... don't.. know what to do...." ta k'arasa cikin kuka,


Ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba yace" no please don't cry, zuciya na namin wani irin zafi idan kina kuka, ki gafarce ni idan magana na ya b'ata miki rai"



Juyawa tayi da sauri ta bar parlour'n, direct bedroom d'in ta ta shiga ta fad'a kan bed tare da fashewa da kuka, yayin da take Jin duniyar gaba d'aya na juya mata, har ga Allah zuciyar ta na son KAMAL gashi Kuma aminin shi FAWAS na son ta, bata San ya zatayi da son KAMAL ba da take fama dashi Wanda shi bai ma San tanayi ba, 





Da k'yar ya iya driving yaje gida, cikin wani irin yanayi ya shigo parlour'n, Mommy na zaune tana duba wasu takardu, ganin yanda ya shigo cikin wani irin yanayi ya sa ta a cikin damuwa, kwamtar da kanshi yayi a cinyar ta yayin da take tambayar shi lafiya meke damun shi, gaba d'aya ya kasa magana idon shi yayi jajazur, zuciyar mommy ya cika da tausayin d'an nata, tayi-tayi yayi mata magana amma yak'i cewa komai,haka dai tayi ta lalashin shi da bashi hak'uri, har bedroom d'in shi ta rakashi ya kwanta sannan ta fito tana mamakin ko meke damun shi Allah kad'ai ya sani,



FAWAS gaba d'aya ya rasa meke damun shi,haka Kuma ya dage da addu'a Allah yasa MEENAL ta amince da shi,





 ***********************



Daddy yaje ya samu Ummie da maganar son a d'aura musu aure ya Kuma nuna mata cewan Yana son ta Kuma he's serious akan auren su, da farko bata amince ba Dan gaskiya bata San abin da zai had'a ta da Mom ba, amma kusan Koda yaushe sai yazo Kuma ya fad'a ma Hajja ita ma taji dad'i sosai, haka Hajja tasa Ummie a gaba da fad'a Dan Daddy yace tak'i yarda, shine ta amince, Daddy ya samu mahaifin shi ya sanar da shi yayi farin ciki sosai Nan ya aka k'ara neman ma Daddy auren Ummie a karo na biyu,


Abba cewa yayi shi Sam bai yarda ba, Hajja bata ji dad'in yanda yace ba Kuma ta nuna Mai tunda mahaifin Ummie na Nan to aure na hannun shi shine zai yanke komai, an samu Kaka inda ya amince,Nan take aka sa ranar aure bayan sati uku,



 

Post a Comment

0 Comments