TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 23-24

 *PAGE* *23*~*24*




       *DEDICATED TO SEEMBY LUFF*😘



  *Aunty SEEMBY kina fad'akarwa tare da ilimantarwa a cikin litafin ki na SAHR-KHULAYD a gaskiya naji dad'in litafin sosai Allah ya k'ara basira da hazak'a,k'warin ido da laushin hannu Allah yasa kifi haka Allah ya kare ki daga sharin mahassada*













 



*MEENAL* ce ta iddar da sallan asubah, direct kitchen ta nufa course tana son tayi duk abin da zatayi da wuri dan bata son tayi late gurin aiki, fere dankali tayi da plantains ta fara frying, bayan ta gama ne sai ga NUWAIRA ta shigo, MEENAL tayi mamakin tashin ta da wuri har ta shigo kitchen.



Yamutsa fuska tayi sannan ta d'auka wani cup ta had'a tea. Samun kujera tayi ta zauna sai murmushi take yi. tana gamawa ta fita. Har MEENAL zata fita sai ta tarar da Sauran tea d'in da NUWAIRA ta rage Wanda ta had'a amma ba Wanda tasha ba. Da yake MEENAL idan ta tashi barci sai tasha tea sannan take wanka ta Shir sai a sake breakfast da ita. Zubawa tayi a cup tare da Sha sai da ta shanye sannan ta hau upstairs. Tana shiga bedroom ta fad'a toilet tayi wanka tana cikin shafa mai taji wani irin barci komawa kan bed tayi tana tunanin ko barci lafiya ne haka dan ita idan ta tashi barci to ta tashi kenan Bata komawa, tana zaune taji wani irin mugun barci kawai sai ta fara gyangyad'i can ta kwanta sai barci.





NUWAIRA ce ta fito cikin riga brown da wandon jeans duk ya matse ta sai tayi rolling d'in veil ga wani sunglass daya rufe rabin fuskar ta. Straight bedroom d'in MEENAL ta nufa tana dariyan mugunta. Ganin da tayi MEENAL sai barci take ne yasa ta saurin rufe bakin ta kar dariyan da take rik'ewa ya fito cikin zuciyar ta cewa take hmm yarinya k'adan ma Kika gani indai kina shiga harka na. wai har Mom na wani baki matsayin da yafi nawa ko to wallahi bazan yarda ba. Taja tsaki ta bar bedroom d'in.




 Da missalin k'arfe 10:30 am 



MEENAL ce ta farka daga barci mai nauyin da ya d'auke. da k'yar ta iya mik'ewa tsaye tana dafa bango. D'agowan da zatayi me zata gani k'arfe 10:30 am. Dafe kanta tayi cikin rud'ewa tace"oh my God what's happening? daga kawai in shirya sai barci" ai da sauri ta fad'a toilet ta wanke fuskar ta cikin sauri ta fito Arabian gown black tasa da sauri veil d'in ma  d'aura shi tayi a kanta. Handbag da takalmi flat shoe duk a hannu ta rik'e su da sauri take saukowa daga upstairs.


Ummie ta gani ta fito kitchen da sauri ta fara tambayar ta tace" Ya akayi sai yanzu ai nayi tunanin kin tafi me yasa meki ne wai?"



Fita tayi da sauri tana cewa" Ummie na ba time d'in magana I'm late" 


Dafe kanta tayi tace"oh yarinyan nan ko lafiya a haka ma zata fita"



 Da sauri driver ya k'araso. Ta shiga yayin da ya tashi motar suka nufa gurin aikin. Ko parking bai gama yi ba ta fito da sauri tana cewa" sorry"



Da sauri ta shiga ciki kowa sai ya kalle ta ganin gaba d'aya bata cikin hayyacin ta. 


Zata shiga office d'in ta kenan sai ga Mom. Tsayawa tayi duk ta rud'e da k'yar ta gaishe da Mom. Bayan ta amsa ne tace" are ok? Ya akayi kinsan yau kuka fara aiki shine zakiyi late. Kar ki manta kece shugaba, ki san lokacin da Zaki dinga zuwa" 


Tace"sorry wallahi ban San ya akayi nayi late ba I'm very sorry"


Juyawa kawai Mom tayi ta bar gurin, da k'yar ta shiga office d'in ta tana tunanin ko ya akayi tayi barci har tayi late, Nan ta fara aikin gaban ta bayan HUSNA ta shigo Dan sectary d'in ta ce. 


NUWAIRA dake lab'e ta k'ofar ta tana kallon meke faruwa sai farin ciki take tunda tasa MEENAL yin late.




Sanye yake cikin suit da alama aiki zai je cikin tafiyar shi mai d'aukan hankalin 'yan mata ya shigo gurin. Gaba d'aya kowa sai kallon shi suke daga matan har mazan. Wucewa yayi straight office d'in Mom.


Tana ganin shi tace" welcome FAWAS sorry mun takura maka ko? gashi Kuma kayi late"


Bai ce komai ba ya mik'a mata wani leda babba wanda Mommy'n shi ce tace ya kawo ma Mom, duk da bai so ba sai da tasa shi dole.


Yace"Morning"


Tace"morning FAWAS kace mata za muyi waya"


Yace"okay sai anjima" ya fita.


Sauri-sauri ta fito office d'in ta tana tunani ji tayi ta fad'a kan wani abu. Cikin fushi ya ture ta da k'arfi yana Shirin fara mata massifa sai dai Kuma me MEENAL ya gani, rabon da ya ganta tun lokacin da suka had'u d'in nan.


Mik'ewa tsaye tayi tana cije lips course taji zafin ture tan da yayi cikin massifa tace" are blind or what da baka ganin han......." Maganar tane ya katse lokacin da taga FAWAS.



 Lokaci d'aya taji wani irin farin ciki gaba d'aya ta ma rasa mai za tace she's very happy. Tace"I'm sorry please"


Murmushi yayi kawai ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Mamaki tayi yanda baiyi mata magana ba. Sai ta tuna had'uwar su na farko inda har takalmin ta ya tsinke murmushi tayi cikin farin ciki marar missaltuwa.



FAWAS gaba d'aya ya cika da farin ciki yau yaga masoyiyyar shi wow he really missed her, dama ya bata time ne ta huta bai son ya cika damun ta, that's why ya fita harkar ta, but now he's back again to win her heart inshallah.





Post a Comment

0 Comments