TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 13-14

 *PAGE* *13*~*14*






 


*Tun daga* wannan ranar sai ya zama ba ko da yaushe NUWAIRA da KAMAL ke had'uwa ba yayin da FAWAS ke yawan Kai ma MEENAL ziyara, sai dai ya kasa fitowa fili ya gaya mata son da yake mata,





Bayan wasu kwanaki ne Ummie ta kawo ma MEENAL ziyara a makaranta, sosai MEENAL taji dad'i sai farin ciki takeyi,sai ga FAWAS yazo Nan suka gaisa da Ummie, har yace shi zai mai data idan zata koma,haka akayi kuwa, lokacin da zata tafi yazo ya d'auke ta, MEENAL kamar zatayi kuka tace ita ma sai ta raka Ummie tunda yau basu da lecture,Nan ta shiga mota FAWAS na tsokanar ta, sai da ya biya da su wani Store mai kyau Dan yayi musu shopping,




Shiga sukayi inda suke d'aukan abun da yayi musu duk da Ummie ba son haka Dan tace ya barshi yak'i, MEENAL ce ke d'aukan mata komai, b'angaren performs suka shiga, FAWAS yace ma MEENAL tazo su duba wani abu ta d'aya b'angaren, Nan suka bar Ummie a gurin tana duba wasu performs da tasan NASIR na so, ganin wani turaren shi da yake massifar so na TOUCH ME, Kai hannu tayi zata d'auka yayin da shima ya Kai hannu zai d'auka, hannayen su ne ya tab'a juna wani irin shock sukaji yayin da a lokaci d'aya suka d'ago Kai,Ido cikin Ido sukayi, fuskar da ya Jima Yana son gani, fuskar da ya tafi ya barshi tsawon shekaru goma Sha takwas, ji yakeyi kamar ba ita d'in bace,



Yayin da Ummie ta shiga tashin hankali da rud'ani har abada baza ta manta da wannan fuskar ba, tabbas wannan NASIR ne mijinta Kuma mahaifin y'ar ta AMINA, cikin tashin hankali ta juya domin barin gurin, saurin Kiran sannan ta yayi domin tabbatar da cewan ko ita ce, "ZAINAB kece?" abin da ya fad'a kenan,


Juyowan da tayi ne ya tabbatar mai da cewan tabbas wannan ZAINAB ce, k'afar tane ya d'auki rawa domin ta rud'e sosai,


K'arasawa yayi har gaban ta yace"Ashe akwai ranar da zaki gudu daga gare ni, ZAINAB why yanzu ma tafiya zakiyi ki bar Ni?"


Gaba d'aya ta rasa abin da za tace, magana ya k'ara yi yace"Zainab kiyi min magana"


Da k'yar tace"Naam"


Cikin zak'uwa yace"Zainab Ina abin da Kika tafi min da shi,Ina nufin abin da Kika haifa?"


Rasss taji gaban ta ya fad'i sai yanzu ta dawo hayacin ta, d'aurewa tayi tace" abin da na haifa ya rasu"


Gaban shine ya fad'i,yayin da ta cigaba da cewa"bayan Bari na gidan ka Ina cikin mota Dan tafiya wani k'auye shine mukayi accident lokacin da aka kaini hospital akayi min aiki aka ciro namiji amma ya rasu" ta shararo k'arya,


Jikin shine ya d'auki rawa sai da ya dafe bango cikin tashin hankali yace"Amma meyasa baki dawo kin sanar da mu ba,meyasa zaki tafi ki bar mu cikin tashin hankali da damuwa, yanzu kina wani guri ne Kuma Mai kikeyi anan?" Ya jero Mata tambayoyi lokaci d'aya,


Ta rasa mai zata ce mai addu'a takeyi a zuciyar ta Allah yasa Kar MEENAL tazo ta ganta da Nasir da sauri tace"Ni yanzu ba anan nake ba sai anjima"tayi hanyar fita, da sauri yabi ta yana cewa ta bashi number'n ta, duk ta rud'e Nan ta bashi number'n tare da fita da sauri, dafe Kai yayi cikin damuwa ya bar gurin,



FAWAS da MEENAL ko wani b'angaren flowers ne kala-kala ya kai ta, gurin ba k'aramin kyau yayi Mata ba, haka ya dinga d'auka Yana bata sai hira sukeyi shi ko yana Jin wani irin k'aunar ta a zuciyar shi, lokacin da suka fito basu tarar da Ummie ba, sai suka nufa gurin mota, ganin ta sukayi ta jingina da mota hankalin ta a tashe,da sauri MEENAL ta k'arasa tana tambayar meya same ta,ganin Kar su zargi wani abu sai ta daure ta cire komai a ranta, tace musu ba komai, nan suka d'auki hanyar k'auye,



Har cikin gida suka shiga, inda suka d'an huta suka d'auki hanyar Abuja Dan basu so dare yayi musu,





K'arfe 6:00pm suka shiga Abuja direct School ya Kai ta,bayan ya ciro wani zoben gold Mai shegen kyau a jiki an rubuta ANA UHUBIKI,da kalmar larabci yasa mata a yatsan ta yayi bala'in yin mata kyau dama dan ita akayi, duk da Bata san ma'anar bata zoben ba amma taji dad'i sosai har tayi mai godiya nan suka yi sallama ta nufa hostel, murmushi yayi cikin farin ciki ya nufa gida,







Ummie ta kira baban ta suka zauna har da Aliyu ta fad'a musu had'uwan ta da NASIR har da k'aryan da tayi mai, da farko fad'a Kaka yayi yace Hakan bai dace ba,da ta fad'a gaskiya Kuma tunda ta bashi number'n ta to tabbas zai neme ta, Kuma lokaci yayi da zata bashi y'ar shi domin gaskiya ta raba mahaifi da y'ar shi, kuka tayi-tayi ita a gaskiya bata son rabuwa da MEENAL gaskiya bata shirya bada MEENAL ba, 


Kaka yace ai ya rage nata dan a gaskiya ya gaji da goya mata baya akan abin da bai dace ba a matsayin shi na mahaifin ta Kuma Malami,



Aliyu ko cewa yayi ya Kamata ta had'a MEENAL da mahaifin ta domin tayi rayuwan talakawa bayan Kuma mahaifin ta Mai kud'i ne ya Kamata yanzu taji dad'in Rayuwa da mahaifin ta, Ummie tace bata yarda ba,






Tun bayan da ya koma gida tunanin Zainab da d'an shi da tace ya mutu yakeyi amma Yana ji a jikin shi cewa d'an shi na raye, mom ta lura Yana cikin damuwa ko data tambaye shi bai fad'a Mata komai ba Dan baya son hankalin ta ya tashi,




Bayan kwana biyu


Kullum sai ya kira number'n Zainab amma bata d'aukan wayan shi, haka Kuma Yana had'uwa da MEENAL Yana Jin k'aunar ta a jinin shi,Kuma ita ma yanda yake sonta kamar y'ar shi yasa take son shi kamar mahaifin ta tare da bashi respect na mussaman, 




B'angaren NUWAIRA suna soyyaya a b'oye ita da KAMAL yayin da shima ta wani b'angaren yake kyautata ma MEENAL Dan tana burge shi halayyen ta kyawawa ne,


FAWAS na jin k'aunar MEENAL sosai a cikin zuciyar shi sai dai har yanzu ya kasa fad'a Mata amma Yana kyautata mata da nuna Mata alamun so Wanda ita Kuma bata gane ba, yayin da zuciyar ta ke son KAMAL Wanda tak'i Bari a gane don tana fatan ta daina son shi,






Bayan wani lokaci



A yau ne su MEENAL suka gama jarabawa inda tayi shirin komawa k'auye, FAWAS da kanshi yazo ya Kai ta,Dan wani irin shak'uwa ne a tsakanin su na mussaman,




Lokacin da suka Isa k'auyen haka Ummie tace bazai tafi ba sai ya ci abinci gashi yamma yayi,



MEENAL ce ta shirya musu abinci shi da Kaka,Nan suka fara ci Dan Kaka akwai barkwanci ga Wasa da dariya, gaba d'aya Kaka ya gama gano FAWAS Dan yaga sai binta yake da kallon k'auna ga hiran da yake mata kina ji kinsan na soyyaya ne amma duk bata gano ba, Murmushi Kaka yayi yace"yaro in tambaye ka?"


Yace"Eh kakan mu inaji"


Gyara zama yayi yace"akwai wace kake so ne?"


Cikin rud'ewa da mamakin yanda akayi Kaka ya gano shi ya fara in Ina"Eh..... Aa.... uhm... hmm ba wace na.....ke.."katse shi yayi da cewa"Kar ka damu nagane,amma da alama baka sanar ba ko?"


Sunkuyar da Kai yayi cikin kunya yace"Aa"


Yace"To ya Kamata ka sanar da ita domin ku fahimci juna"


Yace"Inshallah"




Daga Nan yayi musu sallama ya tafi cike da kewar massoyiyar shi,ta gefe d'aya Kuma mamakin Kaka yakeyi,




Bayan kwana biyu



Daddy ne ke faman Kiran number'n Ummie Amma Sam Bata d'aga ba, can kawai yaji an d'auka muryan namiji yaji Nan suka gaisa Aliyu yace wake magana Nan Daddy ya fad'a Mai shine, da murna Aliyu yace dama ya shigo d'akin ne yaji ringing d'in waya ita Kuma Ummie ta fita Nan yace ai shine Aliyu,


Cikin murna Daddy yace" Dan Allah ka taimake ni ka fad'a min inda kuke, wallahi Ina son had'uwa da Zainab Ina son ta sake bani dama a karo na biyu,duk da jikin na bani abin da ta haifa Yana raye"



Ba tare da b'ata lokaci ba Aliyu yayi Mai kwatancen k'auyen Dan shima Yana son yaga MEENAL ta rayu da Mahaifin ta, Daddy yaji dad'i sosai Nan ya shirya ya d'auki hanyar k'auye,




Parking yayi a k'ofar gidan,sai ga Aliyu ya fito Nan suka gaisa sannan yaje ya fad'a ma Kaka, fitowa yayi suka gaisa inda Aliyu ya fito da tabarma ya shimfid'a sannan Kaka yaji duk abin da ya faru bayan rabuwar Nasir da Zainab inda baiji dad'i abin da sukace akan sakin Zainab ba Kuma baiji dad'in yanda Zainab ta bar gidan Nasir ba,


Hak'uri sosai Daddy ya bama Kaka sannan yace ya shigo cikin gidan su had'u ayi magana har da Ummie,


Ba k'aramin mamaki Ummie tayi ba da ganin NASIR, 


MEENAL ce ta shigo gidan dan dama Ummie ce ta aike ta, ba k'aramin mamaki tayi ba da taga Daddy, shima d'in yayi mamaki sosai,


MEENAL tace"Daddy Kai ne a gidan mu?"


Cikin mamaki yace"Eh MEENAL Nan gidan ku ne?"


Kaka ne ya katse su day cewa"kin san shi ne?"


Tace"eh Kaka ai shine Daddy'n NUWAIRA da nake zuwa gidansu"


Gaba d'aya sun shiga tashin hankali ba kamar Ummie da tafi su shiga tashin hankali ashe haukan takeyi sun san juna, da sauri taja hannun MEENAL tana cewa"wuce ki shiga cikin d'aki Kar ki kuskura ki fito"


Kaka ne ya daka ma Ummie tsawa yace"meyasa zakiyi haka duk wani b'oye-b'oye ya tashi lokaci yayi da za'a San gaskiya Dan bazan sa miki ido kina abin da kika  ga dama ba"


Cikin tsoro da rud'ewa tace"Aa baba Dan Allah Kar ka fad'a komai"


Kaka ne ya jawo hannun MEENAL da na Daddy ya had'a tare da cewa" MEENAL ga mahaifin ki, NASIR ga y'ar ka wace Zainab ta haifa bayan ta bar gidan ka"



Gaba d'ayan su d'agowa sukayi tare da kallon Kaka!


Ummie ko zama tayi a k'asa dirshan tana girgiza kai!




Post a Comment

0 Comments