TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 27-28

 *PAGE* *27*~*28*






   

 

 *Bayan* doctor ya duba ta yaga babu wani matsala ne akayi discharging d'in su, bayan sun dawo gida Mom ta samu NUWAIRA tace lalai ta tabattar taje ta nema yafiyar MEENAL duk da bata so amma haka dole taje bedroom d'in ta,



 MEENAL ce kwance kan bed Ummie na fama da ita akan ta tashi tak'i, cike da shagwab'a tace "Nifa Ummie na ba maganin da zan Sha kawai ki barni Kuma ni bana son faten shuwa kan nan ya cika d'aci"


  Ummie tace" to ai shikenan kinga sai ayi miki allura kawai" 


Da sauri ta tashi tsoro d'auke a fuskar ta zatayi magana kenan NUWAIRA ta shigo,


NUWAIRA a ranta cewa take ina ma zata samu mahaifiyar ta tana bata irin wannan kulawar na mussaman gaskiya da taji dad'i sosai,dan Mom bata mata irin haka. Komai dai take so za'ayi mata amma ba a nuna mata irin wannan kulawar. Jikinta a sanyaye ta zauna a gefen bed d'in cikin fuskar tausayi kamar da gaske tace" I'm sorry about the accident that just happened please kiyi hak'uri duk nice naja hakan ya faru forgive me"


Ummie ce tace"haba NUWAIRA dan me Zaki ce haka? Karki manta musulmi Yana yarda da k'adara Mai kyau ko mare kyau, Allah ya k'adara cewa sai hakan ya faru kuma mun gode ma Allah da ba abin da ya same ku,dan haka karki ce komai"


Taji dad'in abin da Ummie tace amma duk da haka tana jin haushi dai.


MEENAL ko mutuwar zaune tayi ganin ba'a jima ba da NUWAIRA ke cewa sai ta kashe su gaba d'aya, Kai amma da NUWAIRA ta hak'ura da komai ne tayi nadama da tafi kowa Jin dad'i, course bata son yanda take nuna mata.

 

  Cikin farin ciki tace"No stop apologizing for what happened, kamar yanda Ummie na tace to haka ne, fata na da buri na mu zama *ZURI'A D'AYA* hope you'll forgive me too?"


Cikin murmushin yak'e tace"why not sweet sister? komai ya wuce inshallah"


Ummie ko dariya tayi ta fita tana jin dad'in yanda take ganin su cikin farin ciki.


 Ummie na fita NUWAIRA ta mik'e taja tsaki tace"do you think that is over? No I said no this is just the beginning of the war" ta bar bedroom d'in.



Mamaki da rud'ani ta shiga wannan Kuma wani irin sabon salo ne NUWAIRA ta fito da shi? Lailai da abin da take shiryawa amma ko ma mene ne zata sa mata ido kawai.






In the morning



Cikin kwanciyar hankali take barcin ta kamar a dream taji phone d'in ta na ringing,da k'yar ta iya danna answer tasa a kunnen ta cikin barci tace"hello"



Lumshe ido yayi tare da tsotsan lips d'in shi, wani irin yanayi ya shiga na soyayya, yace" ina fatan kina lafiya, ya jikin ki?"


Da sauri ta zauna cikin farin cikin jin muryan FAWAS tace" Alhamdulillah ya Mommy?"


Murmushi yayi yace"she's fine, hope ba abin da ke damun ki ko?"


Tace"No ba komai headache ne Kuma da sauk'i"


Yace"okay dama ina son jin ko ba abin da ke damun ki ne, bye"


Murmushi jin dad'i tayi tace"thanks for the care bye"


Bai ce komai ba ya kashe wayan, samun kanshi yayi cikin nishad'i gaskiya he really miss her sweet voice.





  

Sati d'aya tayi bata koma aiki ba dan Mom tace tafi so ta samu sauk'i sosai, NUWAIRA ko ba k'aramin haushin MEENAL take ji ba, amma fa a jikin mutane nuna mata so da kulawa takeyi, tun abin naba MEENAL mamaki har ya daina bata mamaki. A cikin satin nan taga kulawa da gata gurin FAWAS, ga wani irin son shi da ya shiga zuciyar ta ji takeyi kamar kar su rabu idan sun had'u. 



KAMAL kullum yana tare da NUWAIRA a waya Dan sun shirya kansu basa Jin zasu sake rabuwa, wani irin k'auna suke nuna ma junan su.




MEENAL ce a office d'in ta tayi shiru da alama tayi nisa cikin tunani,har HUSNA ta shigo bata sani ba har sai da ta d'an buga table d'in sannan ta dawo hayyacin ta.


Murmushi HUSNA tayi tana tambayar ta ko lafiya, da farko kamar baza ta fad'a mata ba sai Kuma taga cewan sun shak'u da HUSNA tana da kirki kuma HUSNA matar aure ce har da yaran ta biyu Ilham da Imad, bata b'oye mata komai ba ta fad'a mata.


Murmushi HUSNA tayi dan tun Ranar birthday party d'in su ta lura akwai abin da ke tsakanin su, tace"  gaskiya naga alamar yanda yake k'aunar ki, ni ina ganin me zai hana ki amince da shi, dan Naga kema kina son shi"



Taji dad'in maganar HUSNA dan haka tace" gaskiya nayi kuskure tun farko gashi yanzu ina regretting, HUSNA Allah ya jarabce ni da son FAWAS so mai tsananin gaske wallahi har kunyar shi nake ji"



HUSNA tace"yanzu dai abin da zakiyi shine kawai ki amince da soyayyar shi, dan kowa ce mace zatayi burin malakar FAWAS a matsayin miji dan haka ina muku fatan alkhairi"


  Murmushi tayi tace"nagode sosai da shawarar ki gare ni gaskiya ke d'in k'awa ce ta gari"


 Nan sukayi d'an hira jefi-jefi sannan kowa ta koma kan aikin ta.





 


A yau ne FAWAS yayi Shirin zuwa gurin MEENAL a karo na biyu domin samun soyayyar ta wannan karon a shirye yake ba gudu ba ja da baya inshallah sai yayi winning heart d'in ta course Yana Mata wani irin so mai wuyar fassaruwa.





Cikin riga da wando na shadda navy blue kan shi ba hula sai dai kan nan yaji gyara balarabe sak ya fito. 


Mommy dake kitchen taji an rungumeta ta baya, juyawa tayi tana cewa" wai kai FAWAS sai yaushe Zaka girma?"


Murmushi yayi yace"Mommy kece fa kika ce baki son ace kin tsufa kuma yanzu kince ban girma, I need your prayers"


Juyowa tayi tace" ina zaka je ne haka?" 


Sunkuyar da kai yayi tare da rufe idon shi wai shi a dole yaji kunya yace" wace nake fad'a miki ce, zanje gurin ta, kiyi min addu'a Allah yasa ta amince da ni course I love her Mommy"


Murmushi tayi cikin farin ciki dan tana son farin cikin shi dan haka tayi mai addu'a sannan ta d'auko wani perfume mai k'amshin gaske ta fesa mai, sai farin ciki yake, mota ya shiga ya nufa gidan su MEENAL,



  NUWAIRA na zaune taga FAWAS ya shigo gidan, gaisawa sukayi tana mamakin meya kawo shi gidan Dan babu alamun sak'o ya kawo ma Mom, dama already ya Kira MEENAL ya fad'a mata yana gidan sai kawai ta bud'e mai guests room ya shiga, NUWAIRA ko mamaki take duk yanda akayi akwai wani abu tsakanin Su.



  Sanye take cikin riga da wrapper skirt na wani Swiss less tayi kyau sosai dan colour d'in ya karb'e ta milk and chocolate colour ne, shigowa parlour'n tayi tana d'auke da tray da juices sai cupcakes, 


FAWAS na ganin ta yayi sauri ya k'arasa ya karb'a yana mata welcome, ajiyewa yayi kan center table, sannan ya zauna kan kujera dake fuskantar na MEENAL.


 Gaishe shi tayi cike da natsuwa da kunya, amsawa yayi cikin farin ciki, gurin ya d'auki shiru kusan 5 minutes kafin yayi magana cike da natsuwa yace" MEENAL do you love me?"


 Lokaci d'aya taji duk ta rud'e dan batayi tunanin wannan question d'in zaiyi mata ba, shiru tayi ta kasa cewa komai har sai da ya k'ara mai-maitawa sannan ta tuna hiran ta da HUSNA da abin da ta fad'a mata.da k'yar tace" Me yasa kace haka?" 


  Murmushi yayi yace" I want to know whether you loved me or you still love that person you've said?"


  Gaba d'aya ta rud'e da k'yar tace" oh that time, nifa ba wanda nake so" ta fad'a cikin shagwab'a.


  Yaji dad'in yanda tayi magana ji yake kamar ya rungume ta da alama yanzu zai samu guri a cikin zuciyar ta, yace" are you serious? MEENAL na k'ara zuwa a karo na biyu ki taimake ni ki amince da soyayya na gare ki, please I'm begging you I truly love you" 


  Kai bata san irin farin cikin da ta shiga ba, yau rana ce na farin ciki a gare ta, cikin kunya tace" I'm....." She's confused she actually don't know what to say.


Kneeling yayi a gaban ta yace" Please accept my love, I love you MEENAL"


Rufe fuskar tayi cikin Jin kunya tace" na amince" da sauri ta bar parlour'n cikin jin kunya.


Sujudud shukra yayi tsabar farin ciki Alhamdulillah kawai yake cewa, cikin farin ciki ya bar gidan.





MEENAL ko saura k'adan ta buge NUWAIRA dake kan stairs, ta shiga bedroom d'in ta da gudu, NUWAIRA ko tsaki taja cikin takaici.





  A wannan kwanakin wani irin soyayya su MEENAL da FAWAS sukeyi suna k'aunar junan su sosai, kussan ko da yaushe suna tare ko a phone ma suna mak'ale da juna,


Tun ba Wanda suka sani har su Ummie suka gane, NUWAIRA tayi mamaki sai dai ta nuna su suka sani, Mommy'n FAWAS ko tafi kowa farin ciki ganin cewa 'yar aminiyar ta ce, Kuma ta yaba da natsuwar da tarbiyyan MEENAL.




  



  Bayan wata biyu

     

        After two months



  


  NUWAIRA ce kwance a bedroom d'in ta tana wani irin kuka mai tsananin gaske domin Daddy yace duk su fito da Wanda suke so za'ayi musu aure, gashi Mom tak'i bata damar gabatar da KAMAL,  MEENAL ko har Daddy'n FAWAS yazo anyi maganar auren,


 Ummie ce ta shigo bedroom d'in tana tambayar ta meya same ta da farko tak'i fad'a mata sai da tace zata taimake ta idan har tana da buk'ata, Nan NUWAIRA ta fad'a ma Ummie komai game da soyayyar ta da KAMAL da Kuma irin tsanar da su Mom suke nuna mai.


 Sosai Ummie taji tausayin ta Kuma tace zatayi ma Daddy maganar domin Wanda NUWAIRA ke so zata aura babu takura. NUWAIRA taji dad'in maganar Ummie lokaci d'aya taji tana k'aunar ta sai godiya take mata.





  


Ummie ta samu Daddy da maganar NUWAIRA da KAMAL Kuma shima ya amince yace ba zai mata auren dole ba dan haka yasa ta Kira KAMAL d'in dan yayi magana da shi.


Cikin farin ciki NUWAIRA ta fad'a ma KAMAL sai farin ciki suke, ba tare da b'ata lokaci ba KAMAL yaje gurin Daddy inda ya yaba da halin KAMAL Kuma yace ya yarda ya turo magabatan shi domin asa musu Ranar aure da NUWAIRA,


Kawun KAMAL Wanda yake matsayin yayan Maman shi shine yaje gurin Daddy shi da wasu aminan shi inda aka tsayar da maganar aure.dan Daddy ya lura mutane ne masu mutunci.

 

    A yau ne aka sa ranar d'aurin auren NUWAIRA da KAMAL, sai MEENAL da FAWAS, Nan da wata biyu masu zuwa.




Post a Comment

0 Comments