TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 28

 *BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS (28)*


*Da misalin 01:00am*

Maryam ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da jug me ɗauke da ruwa, so take yau ta yi sallahr dare, bayan ta farka kuma sai ta ji ƙishin ruwa, dan haka ta sauƙo domin ta ɗauki ruwan.

Ji kake taratsa-tsa!, jug ɗin glass ɗin dake riƙe a hannunta ya faɗo a dandaryar tiles ya fashe. Sakamakon abinda ta gani.

Idanuwa waje take kallon Tafida daya shigo cikin gidan, rigar dake jikinsa duka a yage, ga jini na zuba a jikinsa, daga yanayin yanda yake tafiya ta san cewa a galab'aice yake,to ina yaje da wannan daren ?.

Gani ta yi ya faɗi ƙasa yaraf!, duk wani tsoro da take dashi ta ji ya gushe, babu abinda take hangowa sai mutumin daya alkinta rayuwarta tafannuka da dama kwance ba a cikin hayyacinsa ba, kuma yana zubar da jini.

Da gudu ta nufi inda yake, har tana taka kwalbar data fashe a ƙasa amma bata kula ba, kansa taje ta tsugunna, tana kiran sunansa, gaba ɗaya hankalinta ya tashi kuka kawai take tana faman kiran.

“Eshaan!, Eshaan!.....Eshaan!!!”

Hannu ta kai ta riƙe fuskarsa tana jijjiga shi, idonsa taga ya buɗe, duk da hasken fitulun dake falon bashinda yawa saida taga ƙwayar idonsa data koma ja, kallonta yake shima yayinda taga ya buɗe bakinsa yana so ya mata magana, anan tayi arba da dogayen haƙwaran dake bakinsa, hawaye gaba ɗaya ya gama jiƙe mata fuska har yana ɗiga akan tasa fuskar.

“Miriam....s..stay away..f..from..me”

Ya furta maganar a rarrabe, Maryam ta shiga girgiza masa kai tana ci gaba da yin kukanta me sauti.

“Eshaan me ya sameka haka ?”

Bai amsa ta ba sai ƙoƙarin tureta daga jikinsa da ya shiga yi, da ƙyar ya samu ya rabata da jikinsa, ya miƙe zaune tare da jingina da jikin bango, Maryam ta ƙara matsowa kusa da shi, ya shiga ɗaga mata hannu alamun ta dakata, kuma bata dakata ɗin ba saida ta matso kusa da shi.

“Eshaam dan Allah....”

Maryam taga yanayin fuskarsa ya sauya zuwa fishi, bakinsa ya buɗe haɗi da cije haƙwaransa wannan fikar ta sauko masa har kan haƙwaransa na ƙasa, ya kalleta da jajayen idanuwansa.

“Nace ki ƙyale ni ko!”

Ba ƙaramar razana ta yi ba, ƴaƴan hanjinta suka yamutse, ganinsa cikin wannan fusatar, shifa dan ita yake yin haka, baya so ya cutar da ita, ya kamata ace ta fahimce shi.

Amma bata fahimta ɗin ba, ta ƙara riƙe shi tana sakin wani sabon kukan.

“Miriam stay away from, i am a monster Maryam, i am a beast!”

Maryam ta ɗora hannayenta akan fuskarsa tana gursheƙan kuka, goshin ta jingina akan nasa sannan ta girgiza masa kai, wanda yasa nasa kan shima motsawa.

“A'a Eshaan, i can't, i can't stay away from you”

Idamuwansa ya rintse yana jan numfashi da ƙyar, kanta ta ɗaga daga goshinsa sannan ta miƙe ta riƙe hannunsa tana san ta mikar da shi

“Ka tashi dan Allah”

Da ƙyar ya iya miƙewa, dan babu wani ƙarfi a jikinsa na arziƙi, ita ta kama shi har zuwa ɗakinsa, in da taga komai a hargitse, rabonta da ɗakin nasa tun ranar da ta fara zuwa gidan, dan ba shiga ɗakin nasa take ba, hatta da shara ba masa take ba, shi yake kayarsa da kansa.

A kan gadon ta samu ta aje shi, sannan ta shiga bin jikinsanda kallo, idonta ya ƙara zarewa ganin yanda duka jikin nasa ke da rauni.

Numfashi ma da ƙhar Tafida yake, dan Allah ne kaɗai yasan abinda yake ji yanzu haka, Maryam ta ƙara ruɗewa tana dudduba jikin nasa.

“Me...miye haka a j...jikin ka ?”

Hannun ta dake dudduba jikin nasa ya riƙe sannan a hankali ya furta

”Ki tafi.... kada na cutar... dake, dan Allah Miriam”

Yanzun ma kai ta girgiza masa kukanta na ƙara ƙaruwa, ko a ranar da aka aura mata shi bata shiga tashin hankali irin wanda take ciki ba a yau.

Jikinsa ne taga ya fara girgiza harda wani fisge-fisge yake.

“Eshaah?!.....Eshaan?!...Esh..”

A kiɗime ta faɗi, jin yanda ya matse mata hannunta dake cikin riƙon nasa, idanuwansa taga sunyi sama, kamar wanda ya suma, kuma kamar....., ta kasa ƙarasawa sbd hannunta daya saki, kansa yayi gefe sannan ƙwayar idonsa ta yi sama gaba ɗaya.


HANAM POV.

“Kin tabbatar kin ji sauƙi ?”

Muryar Uchenna ta fito a sanda yake kallonta, Hanam ta gyaɗa masa kai, tsaye suke a parlo yayin da ta fito cikin shirinta na tafiya office, dan yau taji sauƙin jikinta, kwananta uku kenan tana jinya, kuma kulawa babu kalar wadda Uchenna bai bata ba.

Ko office baya fita sbd ita, ga ɗawai niyar kula da Arya kullum shi yake. Dan haka ta saka a zuciyarta cewa zata je ta samu Abba yau, tana so ya faɗa mata waye ainahin Uche, tana san sanin asalinsa.

Shima kan ya gyaɗa mata sannan ya miƙa mata Arya daya gama yiwa wanka ya shirya shi cikin wata hoodie da wandonta black color.

Karb'ar Arya ɗin ta yi tana ci gaba da kallonsa.

“Yau bazaka je aiki ba ?”

Kansa ya gyaɗa mata yana faɗin.

“Nayi magaa da Abba kan bazan samu damar zuwa ba yau, wata ƙila sai gobe”

Ta gyaɗa masa kai a hankali sannan ta juya tana faɗin.

“Sai na dawo”

“A dawo lafiya”.

Office ta fara zuwa, ta tarar da tarin aikin dake jiranta tsawon kwanaki, dan haka bata samu damar tashi ba sai wajejen karfe 05:00pm.

Kuma daga fashion house ɗinta Hakuɗau Group of Industries ta nufa.

*

“Kayi shiru Abba”

Hanam ta faɗi tana duban Abban, sbd ta faɗa masa abinda ya kawota wurinsa amma sai ya yi shiru yana kallonta.

Abba ya gyara zamansa yana bawa Arya pen dan yayi wasa da shi, yana kallon Hanam.

“Maman babanta Abban ki ya tab'a zab'a miki abinda zai cutar da ke ?”

Ta girgiza masa kai.

“Good, to ki tabbatar da auren Haris ma haka ne”

“Harees ?, waye Harees”

Taja 'ree' ɗin, sbd arabic ascent ɗin dake bakinta, bama iyaka wannan ne take kiransa a haka ba, sunaye da dama ita bata furta su kamar yanda bahaushe ke yi, tana furta su yanda larabawa ke yi.

“Uchenna”

Abba ya b'ata amsa hankalinsa kwance, idanuwa waje kuma cikin tsantsar mamaki take kallon Abba, Harees ?, wai uchenna ne Haress.

“Nasan yanzu duk abinda zan faɗa miki ba lalle ki yarda ba, ga wannan adireshin da lambar wayar, kije ki samu matar zata baki ko wani bayani akan Uchenna Haris Franklin”

Hanam ta kai hannu ta karb'i takardar da Abba ke miƙo mata, ita ta ma rasa takamemen tunani ɗaya da zata yi a kanta.

Takardar ta shiga dubawa tana karanta adresa ɗin 'SULE JA, RAFIN CINNAKA'.


TAFIDA POV.

Fuskar wannan matar ce, take kallonsa, fuskarta ɗauke da murmushi, gudu yake yayinda yake bin ball ɗin nan a baya, ita ma tana biyoshi tana kiran sunansa, daga can wata ƙofa kuma a bayan gidan, wani mutum ya fito, hannunsa riƙe da mug yana faɗin.

“Roshni!, Eshaan!”

A tare suka tsaya da gudun su duka, suka kalli kyakyawan baƙin mutumin, wanda kana ganinsa kasan ɗan africa ne, murmushi ya sakar musu, yayinda su kuma suke kallonsa da blue eyes ɗinsu su duka.

“Guje-guje ko ?, ki dena sai kunje kun faɗi?”

Yaron ya juyo ya kalli babarsa wadda take kallon babansa da murmushi.

“Ball ce zamu ɗauko”

Cikin gurb'attaciyar hausa ta faɗi zancen.

Daga nan kuma sai wata ƙara ta cika wajen, ƙarar Roshni tana kiran sunan Eshaan, yayinda shi kuma baya ganin komai sai duhu, daga can kuma sai muryar mahaifin sa yana kiran sunansa.

“Eshaan!, Eshaan!...Eshaan!!”

Yadda ƙarar kiran sunan ta cika masa kunne yasa ya toshe kunnesa ya durƙushe a wurin.

Sai kuma ya shiga fisge-fisge kamar zai karya gadon da yake kwance a kai.

Maryam dake share ɗakin ta yi saurin sakin broom ɗin ta ƙaraso wurin gadon, ta zauna a kusa da shi tana riƙe hannunsa na hagu.

Bai fasa fisge-fishen ba, kum idanuwansa a rufe suke, ya rintse su gam-gam, gashin kansa ya musu rumfa.

Maryam tana hawaye tana tofa masa duk addu'ar da tazo bakinta.

“Maa!, Baba!, Appa!, Maa!...Maaaa!”

Sai kuma ya buɗe idonsa gaba ɗaya, a sa'ilin daya buɗe idon, wuta ta kama a hannunsa na dama, ya ci gaba da ware ido yana kallon inda yake, hannunsa na dama yake san ya kai kansa sbd ya riƙe kan nasa dan ciwon da yake masa.

Yana ɗagowa hannun yaga wuta na ci, hannun ya dunƙele tare da rufe idonsa, wutar ta b'ace, hakan ya bashi damar ɗqora hannun a kansa.

Hannunsa na hagu yaji kamar an riƙe, ya yi sauri ya miƙe zaune. Idonsa ya ɗora a kanta yaga yanda idonta ya yi ja sosai, alamu dai taci kuka, daki-daki abinda ya faru jiya ya shiga dawo masa a ka.

Yana zaune a work table ɗinsa yana aiki, ya fara jin jikinsan ya ɗau zafi, kansa na sarawa, hakan ya sanar da shi zuwan aljaninsa, kuma tun daga farkon zuwan nasa ya san cewa yau ba da sauƙi ya zo ba, duk da yana cikin wani hali bai manta da Miriam ba, dan haka ya fita ta balcony ɗin ɗakinsa, ya shiga tsalle ta kan rufin gidagen mutane har ya fice daga Alaro city.

Ya shiga cikin wani daji, anan baƙin aljanin ya tashi, kuma kamar yanda ya zata babu sauƙi a lamarin, haka ya yi ta duka da ya kushin jikinsa har na wani zuwa wani lokaci.

Kafin ya dawo hayyacinsa shine ya kamo hanyar gida. Kuma yana dawowar ya isketa a falo.

Kansa ya dafe yana ture sumar da ta sauƙo masa kan ido, ta yanda zai samu damar kallon fuskarta da kyau.

Har yanzu kukan take ba ta dena ba, kuka take sosai, wanda yake fita tun daga ƙasan ruhunta.

“Ka bani tsoro sosai, nayi tunain ka....”

Sai kuma ta kasa ƙarasa maganar, ta shiga share fuska.

“Kullum haka nake Wifey, idan baƙin ruhina zai tashi irin wannan yanayin nake shiga”

Hannu ya ƙara kaiwa ya tura sumar kansa baya tare da furzar da iska, sai a sannan ya kalli jikinsa, gaba ɗaya ta bi duk inda yaji rauni ta saka masa plaster, wanda yake da tabbacin a first aid kit ɗinsa ta samo. Hannu ya kai ya shiga cire plasterr.

“Me ya faru ?”

kansa ya girgiza mata sannan ya ci gaba da cire plasterr har sai da ya cire su duka, sannan ya hade raunin yana faɗa mata cewar.

“Wannan ba rauni na bane, na baƙin ruhi ne”

Ita de bata ce masa komai ba, sai yanzu ma ta lura da ashe fa bashi da riga, kuma itace ma ta cire masa rigar jiya da ta kiɗime ta yi tunain ya mutu.

Saurin miƙewa ta yi daga kan gadon ta koma ta ɗauki broom ɗinan ta ci gaba da shara tana share hawaye, gabanta sai bugun tara-tara yake. Da ƙyar ta iya daurewa tace.

“Kaje ka yi wanka da alwala, gari ya waye”

Tunda ta tashi daga wajen yake kallonta, bai ce mata komai ba sai dubansa daya kai ga balcony, yaga kamar ma rana na shirin fitowa, Dan haka ya miƙe a hankali ya shiga banɗaki.

Maryam ta saki numfashin da ta riƙe sanda yazo giftawa ta kusan ta, kafin ya fito ta gama sharar, ta fita domin ta kawo masa abinci sannan ta ɗauko duster dan ta goge kurar da taga kayan ɗakin sun yi.

Ko da ya fito bai ganta ba sai ya ɗauko jallbiya a wardrobe ɗinsa ya saka ya tada salla.

Sanda ta dawo har ya idar ya koma banɗaki yana wanke bakinsa, abincin ta aje masa akan table sannan ta shiga goge kayan ɗakin, har tazo kan hotunan dake maƙale a bango.

Sai da ta zo kan nasa shida iyayensa sanda yana ƙarami ta tsaya, so take ta tantace dawa yafi kama a cikin iyayen nasa, last time da ta ga hoton bata gama ƙarewa Tafidan kallo bane, amma yanzu data gama karance kammaninsa sai ta rasa gane da wa yafi kama a cikin iyayen nasa.

Farinsa de irin na mahaifiyar sa ne, duk da ta fishi haske, kalar idonsa ma tata ce, hatta da gashin kansa irin nata ya ɗauko, amma tsayinsa da zatinsa irin na mahaifinsa ne, hancinsa ma irin na mahaifina sa ne, amma bak.....

Tunanin ya maƙale a cikin kanta, sbd jin an riƙo waist ɗinta ta baya, Maryam taji wanna abun dake shiga jikinta idan har Tafida ya riƙeta irin haka, yau har kamar wani zazzab'i-zazzab'i ma take ji haka, ta riƙe numfashinta kamar me tsoron idan ta sake shi wani abu zai faru.

Sauƙar hab'arsa ta ji a tsakiyar kanta, hakan ke nuna mata cewa Tafida ya fita tsayi nesa ba kusa ba.

Bayan ya gama brush ɗun ya fito sai ya ganata tsaye a wajen tana kallon hotunan, dan haka ya tako har inda take ya riƙeta haka.

Maryam ta rintse ido, a sanda taji hannunsa ya ci haba da kewaye kugunta.

“Mahaifiyata kenan, Roshni Iƙbal Khan, shi kuma mahaifina ne Auwal Abubakar Masu Tafidan haɗejia a zamaninsa, nasan baki san shi ba, dan sanda ya rasu bana tunanin an haifeki”

Ɗaya bayan ɗaya jawabin nasa ke shiga ƙwaƙwalwar Maryam, kamar daya bare kanta yake zuba mata su haka take ta ɗauka. Amma kuma bata buɗe idonta ba.

Hannunsa yasa ya juyo da ita ta fuskance shi, da ƙyar ta iya buɗe idonta ta kalli fuskarsa, har yanzu wannan gashin daya tara na nan a kan fuskarsa.

“Kina san kisan waye ni?....”

______________________

_Ai ba Maryam kawai ba, harda muma muna san musan waye kai, ko ba haka ba?_

_Tofa labarin Uchenna na tafe zuwa gobe, ni de na ƙagu naji meke faruwa a rayuwar wanga bawan Allah_

_A har kullum ina muku godiya mara adadi🙏_




Post a Comment

0 Comments