TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 31-32

 *PAGE* *31*~*32*



  

   *Sister MUNEERA ina taya ki murnan Kamala  litafinki mai sunna ITA CE A TAINA Allah ya k'ara basira, gashi yanzu har kin fara wani mai suna NAGA TA KAINA, Allah yasa yanda Kika Fara lafiya ki gama shi lafiya, Ameen*



 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



   *Maman Waleed REAL MAI DAMBU CE🥗, kina matuk'ar k'okari a litafin ki na NAMIJI MA YA YARO NE Allah ya kare ki daga sharin mahassada,ina mutakar yin ki irin sosai d'in nan,muje zuwa,kina k'amshi ina bin ki da humra tawan*😊


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



  *Hip Hip Hip Hurray*


   


    *HAPPY BIRTHDAY ACTION BABY*🎂



  *Sister ina taya ki murnan zagayon ranar haihuwar ki Allah ya k'ara tsawon kwana, Allah ya kare ki, UMMU BASHEER wishing you Happy birthday*🎂



    *Ga nawa birthday cake d'in manage it please*🎂



  *Allah ya k'ara basira da hazak'a a litafin ki na DEEJE DA SANGHAMI*


🌹


       🌹


                🌹










  *Washegari da safe*



 *Lokacin* da gari ya waye ba k'aramin kunyar FAWAS bane ya kamata,dan gaba d'aya kunyar had'a ido take da shi, bayan sunyi breakfast ne taje har gurin Mommy ta gaishe ta cikin kunya. 



   Bayan sati biyu


Cikin satin nan ansha amarci ta b'angaren duka amaren da angwayen, sannan duk sun koma gurin aikin su, lokacin da MEENAL ta had'u da NUWAIRA ta gaishe ta amma ko amsa mata batayi ba, duk da MEENAL bataji dad'i ba kawai sai ta hak'ura ta share.



  Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, sosai FAWAS yake nuna ma MEENAL tsantsar k'auna da tarairaya, haka ita ma tana mai ladabi da biyayya kuma tana nuna mai k'auna, yayin da NUWAIRA da KAMAL ko kamar zasu cinye junan su tsabar soyayya.


 Bayan wata biyu



 Jan blanket d'in yake tare da jan yatsun k'afan ta a hankali yana cewa"come on my love wake up now, barcin ya isa haka"


K'ara shigewa cikin blanket tayi tace"let me sleep please Honey"


  Da k'yar ya d'auke ta cak ya Kai ta toilet, sai Jin ta tayi cikin ruwa tsundum, da sauri ta bud'e ido tace"please please, ni ka maida ni I'm feeling sleepy kaji honey?"


 K'okarin cire mata kaya ya fara yana cewa"no you have to wake up, za muyi late a office, oya take your bath?"


Fita toilet d'in yayi ita Kuma tayi wanka,ko da ta fito baya bedroom d'in kawai sai ta shirya cikin Arabian gown peach colour, sannan ta fito a parlour ta same shi yana breakfast, cikin shagwab'a ta iso gurin tana cewa"ni nifa nace ka dinga tashi na ina had'a breakfast amma sai ka barni inyi ta barci ina Jin ma sleeping sickness nakeyi"


Habawa ai bai san lokacin da ya tuntsire da dariya ba yace" gaskiya wannan barci nake my love ba na lafiya bane, kizo muje Mommy na ta duba min ke, may be na Baki ajiya ne"


Turo baki tayi gaba tace"No nak'i d'in, kawai so kake ayi min injection, wait ajiyan me ka bani?"


 Yace"oya come, zo in fad'a Miki"


  Tana zuwa kusa da shi ta shak'i k'amshin perfume d'in shi da k'amshin indomie with eggs da yayi taji wani irin amai yazo mata da sauri ta juya ta nufa toilet, da sauri yabi bayan ta cikin rud'ewa, yana zuwa ya tarar sai amai takeyi, rik'e ta yayi yana mata sannu, bayan ta gama ya wanke mata fuskar ta, ya wanke gurin suka fito.


Cikin tausayawa yake tambayar ta mene ne ya sata amai? Ita dai bata sani ba dama two days tana jin tashin zuciya sai yau ta samu tayi amai. Fita yayi yaje ya Kira Mommy'n shi, gani yayi har ta fito zata tafi aiki da sauri yace mata MEENAL ba lafiya, sannan suka nufa side d'in shi,


 Kwance take kan bed wani irin jiri ne ke damun ta da k'yar ta bude idon ta, ganin halin da take ciki yasa Mommy tace su tafi hospital ta da tayi mata test, haka ko akayi suna zuwa aka d'ebi jinin ta da k'yar ta tsaya sai da FAWAS ya ririk'e ta sannan  akayi test har Urine sai da akayi test inda suka gano cewa tana d'auke da ciki, habawa ai ba k'aramin farin ciki FAWAS yayi ba, ita ma taji dad'i, sannan suka nufa gida, ai ranar ba aikin da FAWAS yaje Zama yayi a gida ya dinga kula da ita.




Bayan sati uku



 Sosai take samun kulawa ta b'angaren FAWAS da Mommy'n shi, komai take so ake Mata, 



  Zaune take a office d'in ta tana tunanin ko sai yaushe NUWAIRA zata dinga kula ta? HUSNA ce ta shigo ciki suka gaisa inda MEENAL tace" ni Wai HUSNA ina Zan samu tsamiyar biri ne da garin kuka?"


Dariya tayi tace"toh fa, ya za'ayi kenan Dan nima ban san inda zan samu ba"


Kamar MEENAL zatayi kuka tace" wallahi ina son Sha yanzu ya zanyi? Let me call FAWAS" ta d'auki waya tare da Kiran shi,


 Yana office Yana aiki yaga call d'in ta da kamar bazai d'auka ba course aiki yayi mai yawa sai ya d'auka, 


Cikin shagwab'a tace" Honey garin kuka nake son Sha yanzu please"



 Dafe kan shi yayi yace" oh my God, my love what is garin kuka?"


 Cikin shagwab'a tace" wani abu ne, ni dai kawai ina son Sha"


 Cikin lalashi yace"ok don't worry inshallah Zan sa a Nemo min"


Sannan suka yi sallama.



 Lokacin da ta tashi aiki dai-dai ta fito office taga NUWAIRA ita ma ta fito k'arasawa tayi cikin farin cikin ganin ta dan two days basu had'u ba, sai dai ta lura akwai abin da ke damun ta, da sauri tace"sister what's wrong with you, naga kin canza min?"



 Wani irin wawan tsaki taja tace" ban sani ba, kin San dai bana son shishigi koh? Toh ki kiyaye ni" ta wuce abin ta,


Gaba d'aya a tare suka fito inda kowa ce taga mijin ta yazo d'aukar ta dan ita ma NUWAIRA ciki take dashi sosai KAMAL ke tarairayar ta da nuna mata k'auna, 


FAWAS da KAMAL suna jingine da mota suna hira suna jiran fitowan matayen nasu,


NUWAIRA ce ta wuce cikin zuciya ta shige mota, ganin halin da take ciki yasa MEENAL ta k'arasa dan ta bata hak'uri, da sauri su KAMAL suka k'arasa dan Jin meke faruwa duk da sun San da cewar basa shiri,


Ganin yanda MEENAL ta biyo ta yasa ta fito tare da wanka mata Mari mai shegen azaba,


Cikin tashin hankali da rud'ewa FAWAS ya rungume Matar shi yayin da yake Jin haushin NUWAIRA, 


KAMAL ne ya rik'e hannun NUWAIRA Yana cewa meyasa zatayi haka?



Cikin zafi tace" ai na fad'a mata tun farko ta fita harkar na what's her own business with me? Nace ta k'yale ni ko dole ne sai ta kula ni?"


Cikin hawaye MEENAL tace"ba laifin ta bane ko mene ne nina jawo ma kaina dan kawai na d'auke ki a matsayin *ZURI'A D'AYA* muke dake hakan ne zai sa kiyi min haka? Ok Inshallah daga yau na fita harkar ki, that's final"


Cikin zafi tace" kar ma kice *ZURI'AR mu D'AYA* Dan wallahi ni dake ba jinin mu d'aya ba Kuma zanje in binciko ainihin iyaye na"


 Shiga mota tayi, da sauri KAMAL ya fara basu hak'uri, NUWAIRA ce ta Kira shi ya shiga mota kamar wani golo.


Tsananin takaici ya hana FAWAS motsawa daga inda yake, da k'yar yaja hannun MEENAL suka shiga mota Yana Mai lalashin ta.






Cikin satin nan NUWAIRA hankalin ta ya kasa kwanciya burin ta kawai tasan su wane ne asalin iyayen ta, haka take sa KAMAL a gaba da kuka shine shima yace zai Taya ta bincike har sai ta gano iyayen ta,



Gurin Mom ta nufa tana tambayar ta ko wace ce mahaifiyar ta tana son zatayi bincike ta bata dama Dan tasan su wane ne iyayen ta, ba k'aramin tashin hankali Mom ta shiga ba, da farko bata yarda ba sai da NUWAIRA ta dinga kuka tana rok'on ta sannan ta amince amma fa zufa ne kawai Mom keyi dan ta shiga rud'ani, 


 Cikin hawaye NUWAIRA tace"Mom so nake kawai insan wane ne mahaifina tunda mahaifiyana ta rasu, amma ko Zaki iya fad'a da Zan gano har in Fara bincike?"




Cikin rud'ewa tace" k'auyen kura zaki je, Dan naji kamar kafin ta rasu ta fad'i sunan k'auyen Nan"


Cikin zafi da tuno da mahaifiyar ta ta rungume Mom,


Ita ko Mom ajiyar zuciya ta sauke tana sama NUWAIRA albarka amma da sharad'in kar ta fad'a ma kowa inda zata je.



 Haka ko akayi NUWAIRA da KAMAL sun shirya tafiya k'auyen kura dake cikin Kano,



Post a Comment

0 Comments