TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 49

 *BABI NA ARBA'IN DA TARA (49)*


MARYAM POV.

Tafe suke ita da su Hussain a lungun unguwar tasu, Bayan Tafida ya kirata yace gashi nan a wajr ta fito su tafe, shine su Husaain ɗin suka ce zasu taka mata.

“Hussain wai yaushe aka samu sauyi a gidan nan har haka ?”

Ta tambayi abinda ya maƙale a ranta tun bayan sauƙarta a garin.

“Hummm, ai Yaya tun bayan auren ki komai ya sauya, kin ga da sadakin ki Abba yaje ya auro Anti Hanne a ƙauye, ya kawota gida, ita kuma Anti Hanne tun bayan zuwanta gida sai Allah ya haɗa tata da Maanmu, biyyaya babu kalar wadda batawa Maanmu, duk abinda Maanmu zata ce mata shi take, amma fa a wajen Abba bata masa da sauƙi, dan ita ta saka Abba ya buɗe wani shagon provition, ya dawo shi ne yake kawowa abinci a gida, duka ɗawainiyar gidan ta dawo kansa. Ya setu ya dawo dai-dai, abun de sai alhmd”.

“Wallahi yaya auren ki alkairi ya zama ga gidanmu”

Maryam ta yi murmushi, tabbas aurenta da Tafida alkairi ne ga rayuwarta.

“Amma Hussain me yasa to ni ba'a sanad da duka wannan ba ?, kuma fa muna waya da Anti fati, ko da wasa bata tab'a sabar da ni ba”

“Maanmu ce tace kada wanda ya faɗa miki, wai dan kada a tayar miki da hankali”

Allah sarki Maanmu, Maanmu uwa ta gari.

“To mu zamu juya daga nan, sai gobe, ai zaki zo ko ?”

Cewar Hassan a sanda suka fito bakin titi har suna hange motar Tafida dake tsallake.

“Inshaallah zan zo, sai goben auta”

Ta ƙarashe tana dafa kan Muhsin. Daga haka suka mata sallama gaba ɗayan su suka juya, ita kuma ta nufi motar Tafida.

Yana gidan gaba, ya jingina kansa da kujera, kayan jikinsa ma ya sauya.

Ita kuwa wanka kawai ta yi, amma bata sauya kaya ba, dan kayan nata ya tafi da su.

“Hello!, bacci kake ne ?”

Ta furta a sanda ta shiga cikin motar , A hankali Tafid ya buɗe idonsa ya kalleta, asa'ilin da take rufe ƙofar motar, ƙwayar idonsa ta koma ja, zuwa yanzu Maryam ta saba da wannan abun, dan sam baya bata tsoro. Sun glasses ɗinsa ya janyo sannan ya saka.

“Mts!, ba bacci nake ba”

Muryar sa ta fito kamar me jin baccin, kuma kamar wanda yake a wahale.

“Baka da lafiya ne ?”

Ya girgiza mata kai yanawa motar key.

“Lafiyata ƙalau, kawai yunwa nake ji”

Ta zaro ido cikin faɗin.

“Baka ci abinci ba wai ?”

Ya gyaɗa mata kai, ai dole yaji yunwa, sanda zasu taho daga abuja ma beci abinci ba, cewa ya yi idan ze yi dogon tuƙi baya cin abinci.

Tafiya suka fara, babu wanda yace da wani ƙala, koda suka zo round about ɗin fada se taga ya yanke hanya, tunaninta fada zasu je.

Mamaki be kamata ba sai da taga sun ɗau hanyar Kano road, bata de ce komai ba, a kusa da sabuwar tasha taga yatsaya wajen wani me seda gasashiyar kaza da doya.

Ya fita, ta yaje wajen mutumin, ita batasan cewa mutane irinsa na cin irin waɗanan kayan ba.

Bayan ya siya ya dawo motar, ya miƙe titin express ɗin nan, sannan ya yi kwana ya dawo hanyar shiga gari, sai kuma taga sun ɗau hanyar Maje road, kuma a Maje road ɗin ma ya tsaya ya shiga Wani store ɗin dake kan hanya.

A nan kuma bata san me ya siyo ba se ganinsa ta yi da ledoji niƙi-niƙi, yabuɗe gidan baya ya saka a ciki, sannan ya shiga ya tayar da motar suka ci gaba da ta fiya.

Hanyar Shagari G.R.A taga ya nufa, hakan ke nuna mata cewa gidansa zasu je, gidan da a da sai de ta wuce ta ƙofar sa, wani lokacin har gaisawa suke da masu gadin gidan.

Yau se gata zata shige shi a matsayin matar me gidan. Kafin su kai gidan har bacci ya fara ɗauketa, dan bata ma san sanda suka isa gidan ba.

Ƙarar buɗe ƙofar motarsa ne ya farkar da ita daga gyangyaɗin da ya soma ɗaukarta, ya zagaya ya buɗe mata motar ta fito, sannan ya kuma zagayawa ya ɗebo ledojin dake baya.

“Kawo na taya ka”

Ya girgiza mata kai.

“Ke da kike bacci“

Au ashe ya ganta, se bata sake cewa komai ba har suka shiga cikin gidan, duk da dare ne hakan be hanata ganin kyan gidan ba.

Shine a kan gaba ita kuma na biye da shi, har ɗakin da taga ya shiga, a cikin ɗakin ne kuma taga jakar kayanta. Kai tsaye wurin jakar ta wuce, ta buɗe ta ta ɗauko wasu pyjams riga da wando masu kyau, ta shiga bayi ta saka kayan sannan ta fito.

Sanda ta fito ta iske shi zaune a kan sofa yana cin abinci. Bata ce masa komai ba ta wuce ta ɗauko hijabinta,sannan ta dawo kan gadon ta kwanta, kamar daga sama ta ji muryar sa.

“Ba za ki ci abincin ba ?”

Ta juyo ta kalleshi amma shi ba ita yake kallo ba kamar yanda ya saba. Kuma har yanzu idonsa sanye cikin baƙin glashin nan.

“Naci abinci a gida”

Shi ma be ƙara cewa komai ba, har ya gama cin abincin nasa, ya aje sauran kayan da ya siyo, ya miƙe ya shiga ɗakinsa na gidan, kayansa yaje ya sauya sannan ya dawo ɗakin da ya bar Maryam.

A kan gadon ya kwanta yana kallon fuskarta ta cikin hasken dake ɗakin, hannunsa ya motsa a setin swithch, take wutar ɗakin ta mutu.

Tsoron da ya saba kama Maryam shi ya kamata, dan haka ta matsa kusa da Tafida ta shige jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa ya riƙeta, ya mata peck a ka.

“Ka yi addu'ar bacci ?”

Addu'a ?, ita bata san cewa shi ba kamar kowa yake ba ?.

Tana jin kansa da ya girgiza mata.

Kamar yanda ta saba idan suka kwana tare se ta yi addu'ar sannan ta tofa masa.


*Cosgrove Estate wuse,st 3, house NO 334*

*08:40pm*

HARIS POV.

Seda ya tabbatar da ya gama aje komai a yanda yake, sannan ya yi sama zuwa ɗakin Hanam.

Zaune ya samesu ita da Arya, tana waya  wadda yake da tabbacin da Masarrat suke yi, dan ya ji tana larabci, pyjams ne a jikinta iri ɗaya da na jikin Arya.

Kanta ta ɗago ta kalle shi a sanda ta aje wayar.

“Ammi tace tana tayaka murna, da waƙarka da ta yi trending a africa baki d

ɗaya”

Ya yi murmushi yana ɗaukar Arya.

“Godiya nake, muje”

Ta miƙe tare da faɗin.

“Zuwa ina ?”

"Ƙasa mana“

Bata kuma cewa komai ba ta bi bayansa.

Baki sake take kallon falon nasu, wutar falon a kashe take, sai wani haske me kyau da ɗaukar ido kalar purple dake haskawa a farlon, ga katifa an shimfiɗe a ƙasa an rufeta da bed sheet, ga pillows manya manya an kewayeta da su, katangun falon na glass ya sauƙe curtains, sannan ga wani farin bord da aka aje a wajen.

Ga wani table da aka ɗora projector a kai, wanda ke facin farin bord ɗin, a kan coffee table kuma kayan kwaɗayi ne kala-kala aka jera.

“Wow!, amma fa wurin nan ya yi kyau”

Haris ya aje Arya a kan katifar yana faɗin.

“Disney ne suka saki wani sabon film, wai shi 'WISH' shi ne nace bari mu kalla“

Hanam ta zauna akan katifar itama, yayinda shima Haria ɗin ya zauna, suka saka Arya a tsaya, ya kunna ya danna wani switch a jikin projectorn, nan take film ɗin ya shiga playing.


MARYAM POV.

Yau da safe da suka ta shi bayan sun shirya gidan Wani abokinsa Muktar ya kaita ta gaisa da matarsa har da ɗansu da suka ce mata me sunan Tafidan ne.

Sun ɗan jima a gidan, kafin suka tafi, kuma daga nan unguwarsu taga ya nufa, a ƙofar lungunsu ya yi parking.

“Se yau she kenan ?”

Ya tambaya idonsa a kanta.

“An jima mana”

Se ya gyaɗa mata kai yana cije lips ɗinsa.

“To a dawo lpy”

“Ameen Allah ya sa”

“Ki gaida Maanmu da Abba da Anti Hanne”

Maryam ta fita daga motar a ranta tana faɗin wato shima ya san Anti Hanne, itace ba ta da labarinta, koma me ya faru lefin Anti Fati ne, ai suna waya ya kamata a ce ta faɗa mata.

“Yauwwa shigo, ai kinganni nan sammako na yi yau, tun da an ce mana ganinki se an cike file”

Muryar Iya Ummi ta faɗi bayan Maryam ta yi sallama, da gudu Maryam ta yi kanta tana dariya.

“Allah sarki ta gidana, na yi missing ɗinki wallahi”

“Ba wani nan, ɗagani ni, ai da ace kin yi kewata ba zaki koma lagos ki yi zaman ki ba”

“To ai keɗince baki da waya..”

“Inji ub*n wa ?, to wallahi na yi waya”

Ta ƙarashe tana miƙo mata wayartata, Maryam ta karb'a.

“Iyeee?, ki ce Iya Um...”

“Ke ke dakata dallah!, na soke wannan sunan, sunana Hafsa, idan kuma bazaki ce Hafsa ba ki barshi”

Maryam ta ɗaka mata duka tana juyawa wajen Maanmu.

“Maanmu ina kwanan ku”

“Lafiya”

“Anti Hanne ina kwana”

“Lpy Maryam ”

Anti Hanne ta amsa mata da fara'a, bata tambayi ina su Hussain ba, dan tasan akwai school.

“Ina gujirin nawa”

Maryam ta miƙe tana faɗin.

“Muje ɗaki na baki”

“Ke ta gidana kinga yanda kika yi kyau?, kin yi fresh a binki, ko dan wa ya sani ma ko akwai ƙaramin Tafida a cikin ki....”

Maryam ta ɗaka mata duka a sanda suke zama a kan gadon Maanmu.

“Wallhi Hafsa bana san iskanci, ke tsiyata da ke kenan, baki iya bakin ki ba”

“Yau ai gaskiya na faɗa, kinsan ni ba'a ƴar b'oye-b'oye da ni ehee“

“Ah!, me hali ba ze fasa ba”

“Se na dawo na iske ƴar iskar nan ta bar gari”

Maryam ta yi dariya.

“Ko ba Badar ba ?, ta koma kano wallahi”

“Umm!, Maryam yanzu duk yanda ƴan matan Haɗeji ke zilamar Tafida kece kika yi wuf da shi, ke nifa ko hira ake se na ce ƙawata ce ta auri Tafida”

Maryam ta tintsire da dariya, dan tasan wannan ba ƙaramin aikin Hafsa ba ne, idan aka ce ta yi fin haka ma ba za'a musa ba.

“Wannan tabon na fuskarki fa”

Maryam ta kai hannu ta tab'a gefen fuskarta, dede inda ta ji rauni sanda Heleen ta daketa.

“Faɗuwa na yi”

“Oooh!,Muga wayar taki to”

Maryam ta miƙa mata, hoton wallpaper farko ta gani, wanda na Maryam ne ita da Tafida, da a ka musu a Mumbai, a Marine drive.

“Oh ni duniya, wai dama Maryam har indian kuka je ?”

Maryam ta janyo wata jaka a cikin kaya da ta zo da shi tana faɗin.

“Mun kusa wata ma a can, bamu fi kwana huɗu da dawo ba”

“Kai ƙawata Allah saka mu a danshin ku”

“Ga wannan shine gujirin ki”

Hafsa ta aje wayar Maryam ɗin dake hannunta, ta miƙe tsaye ta ware rigar da Maryam ta bata, ta kara a jikinta baki buɗe. Ta aje rigar sannan ta ɗauko ɗan kunnen da ta haɗa mata da shi ta gwada.

“Kai na gode amaryar Tafida, irin wannan kyauta haka....”

Sallamar Anti Fati suka ji a gidan,Maryam ta fito da saurinta har da ɗan gudu, tana ganin Anti fati ta faɗa jikinta.

“Oyoyo ƙaunar Imran”

Anti Fati ta faɗi cike da jin daɗin ganin ƙanwar tata, Maryam ta saketa tana karb'ar Imran dake hannunta, Anti Fati ta shiga ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta sauya, ta ƙara ƙiba ta ƙara fari.

“Anti fati sannu da zuwa”

Muryar Hafsa ta faɗi daga bakin ƙofar dakin Maanmu, Anti Fati ta amsa mata su na shigowa cikin gidan.

Imran na wasa da ɗankwalin kan Maryam ya ja shi baya, ɗankwalin ya faɗi, gashin kanta da bata nannaɗe shi ba ya baje a bayanta.

“Kni ni kuwa yau naga ikon Allah, wai da ya kai ki indian gashi suka sake miki ?”

Hafsa ta faɗi tana kallon gashin Maryam ɗin.

“A'a wallahi babu wani gashin da na sake, in faɗa miki gyara makawai ya ji”

Maryam ta faɗi a sanda ta miƙawa Anti Fati Imran, ta ɗauki dankwalinta tana ɗaurawa.

“Ai ko baki ga yanda gashin kan naki ya yi kyau ba”.




Post a Comment

0 Comments