TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 17

 Bayan sati uku...*

*No.181, Guzape, Abuja...*

*09:30pm*

MISHAL POV.

Kwance take a falo, ta duƙunƙuna cikin blanket, idanuwanta sun yi ja saboda kukan da ta ci, ta kunna tv ta tsura mata ido amma ba kallon take ba.

Damuwa da ruɗani ne suka saka rayuwarta a gaba, yau kusan sati uku kenan, amma Antinta Adawiyya ba ta zuwa makaranta, tun ta na ganin abun kamar fashi ne, har fashin nata ya zo ya soma bata tsoro, dan zuwa yanzu ma an kawo wata sabuwar me yim shara a makarantar, kullum sai ta yi kukan rashin sanin halin da Adawiyyan ke ciki, ga kuma kaɗaici da yake damunta a yanzu, ga shi dai ba wani jimawa suka yi da Adawiyyan ba, amma haka kawai take jinta cikin kaɗaici, yanzu haka ta hana idonta bacci ne dan jiran dawowar Kuliya, tun da shi ɗan sanda ne wata ƙila zai iya yin wani abu akan case ɗin yayar tata.

Ta na kwance a wurin har goma ta wuce, kuma sai a lokacin Kuliya ya shigo gidan rai a ɓace, wanda ya samo asali daga wurin aikinsa, Mishal na jin shigowarsa ta miƙe da sauri ta sha gabansa, kallonta ya yi na 'yan wasu sakkani, sannan ya shiga ƙoƙarin raɓata ya wuce, amma sai ta ƙara tare masa hanya.

“Abu Aswad.Yayata ce ba ta zuwa makaranta. Kuma ban san meke faruwa da ita ba, dan Allah ke nemo min ita” ta faɗi hawaye na mata zuba.

“Ke me ya sa baki san abinda ya kamata ba?, Yanzu na dawo gida da ɓacin rai, me makon ki bari na huce shi ne za ki tarbeni da wannan maganar?!”

Kamar de wancan karon haka ya mata magana cikin hargagi, Mishal ta fashe da kuka sannan ta naushi ƙirjinsa.

“I hate you Abu Aswad!”

Ta na kaiwa nan ta juya da gudu ta faɗa ɗakinta.

“Zan iya shigowa?”

Kuliya ya tamabaya ya na turo ƙofar ɗakin Mishal, wadda ke zaune a kan gado ta na kuka, sai bayan da ya je ya yi wanka sannan ya samu sauƙowa, shi ne ya taso ƙafa da ƙafa don ya nemi yafiya. Saboda ya san ba laifinta ba ne, shi kansa yabna bincike a kan yarinyar me suna Rabi'a, amma har yanzu babu abun da ya samu.

Ya je makarantar Brickhall yafi sau biyar a cikin sati ukun, amma sam sun ƙi su ba shi adireshin Rabin, ga kuma wani renin hankali da suke masa na cewar ai jiya ma ya zo, bayan shi kuma ya san bai zo a ranar ba.

Zama ya yi a bakin gadon ta setinta, ya na kallon gefen fuskarta da ta kawar, fuskarta ta yi jajir, alamun dai ba ƙaramin kuka ta sha ba, shi ya rasa wannan wata iriyar ƙauna ce tsakaninta da wannan yarinyar.

“Hafsat”

Ya kira sunata a tausashe, sai ta ƙara haɗe rai ta na kumbura baki.

“Ki yi haƙuri ba zan sake ba!”

Juyowa ta yi suka haɗa ido, ta wurgar masa harara, ta ƙara kawar da kan nata, sai ta bashi dariya, hakan ya sa ya murmusa a ransa.

“Yanzu ba za ki yafemin ba?”

Ta kuma juyowa ta kalleshi. Jin yanda ya yi maganar kamar maraya.

“I hate you, ka fita min daga ɗaki”

“In dai yayarki ce zan nemo miki ita, yanzu ma na zo dan ki bani wasu bayanai a kanta ne, ta yanda zan yi saurin samo miki ita!...”

Kallonsa take tana son tabbatar da kalamansa, can kuma sai ta matso kusa da shi.

“Ka yi alƙawarin za ka nemomin ita?”

Sai ya gyaɗa mata kai ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, shi kansa bai san haka yake da laushi ba sai a kan Mishal, ita ce zai ɗagawa murya daga baya kuma ya zo ya na bata haƙuri.

“Ni dai ki yafemin!”

Ya faɗi murya ƙasa-ƙasa, kuma amon muryar tasa ya sa Mishal ɗin lumshe ido sannan ta buɗe.

“To ba na ce maka ba na san tsawaba.Amma kullum idan ka fusata sai ka min...”

“Daga yau ba zan sake ba, na miki alƙawari”

Ya katseta tun kafin ta rufe bakinta, sai ta yi murmushi tana share hawayenta.

“Ina san ki ba ni duk wasu bayanai da kika sani a kanta, saboda ina san na fara bincike a kanta, kuma na miki alƙawarin samo miki ita”

Farin cikin kalamansa suka sa Mishal miƙewa a kan guwowinta, sannan ba tare da ya shirya ba, ta faɗo jikinsa, tare da saƙala hannayenta ta wuyansa. Be san ya akayi ba, amma ya ji duniyar ta wani iri shiruu, kuma kamar shi ɗaya ne yake jin shirun, sai wata siririyar iska dake wucewa ta gefen kunnensa, ɗumin jikinta dake kama da na me zazzaɓi ya ratsa fatarsa ta cikin sayin acn dake ɗakin, wadda ya haddasa bugawar zuciyarsa fiye da kima, idonsa ya lumshe ya na sauraron nata bugun zuciyar da ya haɗe da tasa.

“Thank you Abu Aswad, kai miji na gari ne”

Mishal ta faɗi cikin tsantsar murna, hannun Kuliya na rawa ya ɗago shi, tare da ɗorawa a kan bayanta, ya na ƙara matseta a jikinsa, hakan ya sa Mishal ankara da abun da ta aikata, cak wannan dariyar da take ta tsaya, duk wani tunani na cikin kanta ya ɗauke, numfashinta ya ɗan yi nisa, kunnuwanta suka toshe, babu abinda take ji sai yanda ya matseta sosai, ta yanda har tana iya jin bugun zuciyarsa da ya haɗu da nata, nan take sanyi ya shiga bi ta jijuyoyin jikinta, ba shiri ta saki hannayenta dake kewa da wuyansa, amma kuma shi be saketa ba, face ƙara matseta da ya yi.

“A... Abu As...as... Aswad!”

Ta kira sunan a rarrabe, don ta tuna masa da halin da suke ciki, saboda ta lura da be ma san ya na yi ba, kuma maganar tata ce ta sa shi dawowa hayyacinsa. Ba shiri ya saketa da sauri ya na kawar da kansa gefe, ita ma sai ta ja baya daga zaunen da take, ta jingina da jikin gado, sai meda nunfashi take kamar wadda ta yi gudu a kan keke.

“Ki... Kin yi abinci yau?”

Ya tambaya ya na miƙewa, kuma ba tare da ya kalli fuskarta ba, da sauri ta gyaɗa masa kai, kuma ya ga hakan ta gefen idonsa.

Ba tare da ta ƙara cewa komai ba, ta sauƙa daga kan gadon ta fita daga ɗakin, bayanta ya bi da kallo, kafin shi ma ya fice daga ɗakin.

Kitchen ta nufa, hakan ya sa shi kuma ya zauna a falo ya na jiranta ta kawo masa abincin, don yanzu kullum girkinta yake ci, baya cin abincin waje kamar yanda ya saba sai da rana, da ranan ma dan ba ta gida ne, amma duk weekend sai ya dawo gida ya ci abinci.

Kansa ya ɗaga ya kalleta a sanda ta aje masa plate ɗin tuwo da miya, alamun dai shi ne ta girka ɗin, ta juya da nufin barin falon, amma sai dakatar da ita ta hanyar faɗin.

“Ina zuwa?”

Sai ta tsaya ta na kallonsa, kafin tace.

“Ɗaki”

Sai ya ja plate ɗin da ta aje zuwa gabansa ya na girgiza mata kai.

“Ki zauna, magana za mu yi”

Sai ta kai hannunta ta ɗauke blanket ɗin da ta rufu da shi ɗazu, ta zauna a kusa da shi. Tambayoyi ya shiga mata a kan Rabi, ita kuma ta na ba shi amsa dai-dau da abun da ta sani, babbar matsalar a nan shi ne, adireshin gidansu, ita kanta Mishal ɗin ba ta san gidansu ba, kawai cewa take a Suleja take.

“Na gode Abu Aswad, dan Allah idan ka samo ta ka haɗata da 'yan uwan Ummanta, Wallahi ta na shan wahala a gidansu”

Kuliya ya juyo ya kalleta ya na haɗiye abincin bakinsa.

“Ke da kika ce kin tsaneni”

Mishal ta zumɓuro baki gaba.

“To ba kai ne ka min tsawa ba”

Ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.

“Ai na baki haƙuri”

“To ai ni da ma ban tsaneka ba”

Sai juyo gaba ɗaya ya na kallonta.

“Me ki ke min to?”

Tambayar tasa ta rikita Mishal, to ta ya za ta faɗa masa cewar ta na sansa, bayan shi bai furta mata abun da yake ji a kanta ba, to kuma ma kawai sai ta kalli idonsa tace ta na sansa?, ai abun ma be yi tsari ba.

“Hummm?”

Ya kuma tambaya ya ka kafeta da manyan idanuwansa, kanta ta sunkuyar ta kasa cewa komai. Kuliya ya juya ya ci gaba da cin tuwonsa, kafin muryarsa ta fito.

“Kin tsaneni kenan?”

Ta girgiza kanta da sauri, memakon ta ba shi amsar tambayar da ya mata, sai ta mako masa tambayar da ta sa ya dakata da kai lomar tuwon bakinsa.

“Kai me kake ji a kaina?!”

Juyowa ya yi ya kalleta, sai ya ga ta ƙara girma a idonsa, kamar ba wannan ƙaramar yafinyar da aka aura masa ba, ya kamata a ce ya faɗa mata abun da ke zuciyarasa, zuwa yanzu shi kansa ya san ya na buƙatar matarsa, da ɗin ma ba komai ne ya sa ya rabu da ita haka ba face ganin yarintarta, zuwa yanzu ya san cewa ta nutsu, ta kama kanta, duk da har yanzu ba za'a rasa guntun ɓirɓishin yarintar a cikin kanta ba. Sai de kuma akwai banbanci tsakanin Mishal ɗin da aka aura masa, da kuma wannan wanda yake zaune da ita.

“Ni ma ban sani ba. Kawai de na san tun ranar da na fara ganin ki na shiga wani hali, ko me zan yi sai tunaninki ya shigo cikin kaina, ina san na riƙa kallon fuskarki, ina san a kullum ki riƙa zamma kusa da ni kamar da haka... Hafsat akwai wani abu a ƙirjina dake motsawa a duk sanda zan ganki, abubuwa da dama idan kika yi suna burgeni, walau shirme ko shirirta. Wata ƙila za'a iya kiran abun da nake ji a kan ki da SO! Amma ni ban sani ba, ban san menene ba”

Ya ƙarashe ya na kallon fuskarta, hannunsa ya wanke a cikin ruwan da ta aje masa, sannan ya goge hannun, kuma har zuwa lokacin Mishal na kallonsa, kenan shi ma ya na santa? Amma me ya sa bai taɓa faɗa mata ba?, ya kamata ace  ita ma da kanta ta gano hakan, to yanzu sai me ?, ita ta na san sa, ta san da wannan tun a waccan ranar da kishi ya rufe mata ido har ta aikata aika-aika.

Kuliya ya juyo ya kalli fuskarta, tare da kamo hannayenta ya matsesu cikin nasa, hakan ya sa Mishal lumshe idonta, wannan sanyin da ya saba ratsa fatarta a duk sanda zai taɓata irin haka ya shiga aikinsa, ji ta yi jijiyoyin jikinta sun ɗau sanyi, bakinta ya shiga rawa, a sanda ta ji Kuliya ya matso daf da ita, babu wata tazara tsakaninta da shi, hatta da ɗumin numfashinsa a setin fuskarta yake sauƙa.

A hankali ta buɗe idonta, sannan ta ɗan ɗaga kanta sama, ta inda za ta samu damar kallon fuskarsa, ba ta san haka ya yi kusa da ita sosai ba sai da hancinta ya gogi nasa, idanuwansu suka sarƙafe a cikin na juna, babu abun da take gani a cikin idanunsa face tsantsar soyyayarta da yake san ya bayyana mata, amma kuma ya rasa hanyar da zai bi ya faɗa matan.

Zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, burinsa ɗaya, ya bayyana mata gaba ɗayan abun da ke cikin wannan raunnaniyar zuciyar tasa, a hankali ya lumshe idonsa, hakan ya sa ita ma Mishal ɗin lumshe nata idon.

“Hafsat!”

Ya kira sunan nata a hankali.

“Umm... um... umm”

Ta amsa idon nata a lumshe, hannunta na dama dake cikin nasa ya ɗora a saitin zuciyarsa, kusan a tare suka buɗe idanuwansu.

“Kin ji yanda take bugawa ba?... Da ko wani bugu da take ta na bugawa ne da sunanki, da kowani bugu da take tana bugawa ne da sanki, Hafsat... I... Love... Youuuu!”

Ba shiri Mishal ta matse gaban rigarsa da hannunta dake kan setin zuciyarsa, saboda yanda kalaman suka saka jikinta rawa. Ba ta za ta ba ta ji hannun Kuliya ya kewaye waist ɗinta ta baya, sannan ya matso da ita jikinsa sosai, hakan ya sa ta buɗe idonta ba shiri.

“Answer me Hafsat, did you love me?!”

Ya tambaya ya na goga lips ɗinsa a kan nata, hakan ya sa Mishal ɗago ɗayan hannun nata, tare da ƙara matse gaban rigarsa.

Sakan ɗay... Biyu... Uku...

*Washe gari...*

*07:10 AM.*

Mishal ta rufe lunchbox  ɗinta, bayan da ta gama jera abincinta a ciki, sanye take da complete uniform ɗinta, ta juya za ta fita daga kitchen ɗin idonta ya sauƙa a kan flask ɗin abincin Kuliya.

Kuliya?!, Sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, nan take abun da ya faru a jiya ya dawo mata. A jiyan bayan shuɗewar sakan uku, muryarsa ta katse shirun dake wanzuwa a falon.

“Na ba ki daga yanzu zuwa gobe da safe, ki yi tunani a kai”

Abun da yace kenan, kafin ya saketa a hankali, ya ɗauki plate ɗin da ya ci abinci ya nufi kitchen, hakan ya bata damar faɗawa ɗakinta da gudu, ta sakawa ƙofar  sakata. har gari ya waye ta na saƙawa da kuncewa.

Ko da safe da ta tashi ayyukanta ta shiga yi cikin gaggawa, don so take ta yi sauri ta kammala abun da za ta yi don ta bar gidan kafin ya fito, hakan da ta tuna ne ya sa ta zabura za ta bar kitchen ɗin, sai dai kuma fatan ta bai cika ba, don a dai-dai lokacin ƙofar kitchen ɗin ta iyo ciki, Kuliya ya shigo, kamar kullum sanye cikin baƙaƙen kaya.

Kallonta yake cikin wata iriyar siga da Mishal ba ta san ta inda za ta mata fasarra ba, hancinta ta ja, sakamakon murar da ta kamata a jiya, ta haɗiyi yawu da ƙyar. Numfashinta ya kusa ɗaukewa a sanda ya tsaya a gabanta.

“Har kin shirya?”

Ya tambaya ya na kallon hancinta da ya yi jajir, da alama dai mura take.

“Eh”

Ta amsa masa cikin muryar me mura.

“Ba ki da lafiya?”

Ya tambaya ya na duban yanayinta, da sauri ta girgiza masa kai, sai kuma ta gyaɗa kan nata tana shaƙar ƙamshin turarensa da duk murar da take ba ta hanata jinsa ba.

Wani sauti ta ji me kama da na murmushi, hakan ya sa ta kalli fuskarsa da sauri, kuma sai ta ga da gaske ne, Kuliya ne yake mata murmushi, wani abu sabo, wani abu da za ta cewa ba ta taɓa ganinsa a zahiri ba. Kuma murmushin da ya yi sai ya ƙara bayyana mata kamarsa da Adawiyya, haka zalika murmushin nasa ya ƙara bayyana kamar da suke da ɗan uwansa...

Tunaninta ya katse a sanda ta ji sauƙar tafin hannunsa a kan fatar wuyanta, wannan sanyin ya shiga bi ta jijiyon jikinta, hakan ya sa ta ɗan ɗauke numfashinta na wasu sakkani, kafin ta dawo da shi ta na jansa da sauri-sauri.

“Har da zazzaɓi kenan?”

Ya tambaya ya na dawo da hannun nasa goshinta.

“Zan bawa Ibrahim (Drivernta) maganin mura ya kawo miki”

Da sauri ta gyaɗa masa kai tana jan hanci.

“Ban manta ba... Mecece amsata?”

Ta kalli fuskarsa, amma sai ta kasa cewa komai, bakinta ya mata nauyi, kamar wanda ta haɗiyi dutse.

A hankali Kuliya ya ƙara matsawa kusa da ita, sannan ya saka hannunsa na dama ya kewaye ƙuginta, ya haɗeta da jikinsa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, hakan ya sa Mishal rintse ido tana kawar da kanta, hannunsa na hagu ya sa ya kamo haɓatar ya juyo da fuskarta.

“Look at me!”

Sai ta buɗe idon nata tana kallon fuskarsa.

“Did you love me?”

Saboda abun da Mishal take ji ba ta san sanda ta shiga gyaɗa masa kanta da sauri ba kuma ta gyaɗa ya fi sau biyar.

“Kin tabbatar?”

“E... Eh!”

Kalaman sun yi wa Kuliya daɗi, hakan ya sa ya yi wani irin murmushi da sai da ya bayyana haƙoransa, kafin ta ɗauke hannunsa daga kan haɓarta, ya dawo da shi gefen fuskarta, yana shafawa a hankali.

“I love you Teddy Bear!”

Ya na kaiwa ƙarshen maganar, ya raba leɓensa biyu, sannan ya sa nata na ƙasa a tsakiya, kafin ya haɗe bakinsa da nata gaba ɗaya.

Abun da ya yi ya sa Mishal ɗaga ƙafarta sama, sannan ta dunƙule hannayenta a kan ƙirjinsa. Ba ta san ma me yake faruwa ba, ba ta san me ake yi a duniyar ba, ba ta san me yake wakana a kitchen ɗin ba, abu ɗaya ta sani, shi ne ita ce riƙe a hannun Kuliya, yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da gefen fuskartsa na dama, bakinsa kuma cikin nata, ya na aika mata da wani laffiyayyen kiss.




Post a Comment

0 Comments