TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 51

 


*BABI NA HAMSIN DA ƊAYA (51)*


MARYAN POV.

*01:00am*

Bige-bigen da Maryam ke jiyowa yasa ta buɗe idonta, da ƙararma jinta take kamar a mafarki, a hankali ta shiga baza idonta a cikin duhin ɗakin, dan babu haske se na farin wata da ke shigowa da ga balcony.

Hannunta ta kai ta laluba inda tasan Tagifa na kwace, dan tare suka kwanta.

Kafin ƙwaƙwalwata ta faɗa mata cewar baya gadon wani gurnani ya shiga cikin kunnuwanta.

A zabure ta miƙe zaune, ta kai hannu ta kunna wutar ɗakin, baya cikin ɗakin, to amma yaushe ya fita ?.

Wani irin gurnani da ta ji yana yi ne ya ƙara tsoratata, a cikin ranta take karanta duk addu'ar da tazo bakinta.

Kafin wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo mata. Ta kai tsawon minti biyar a haka, kafin ta ji ya saki wata ƙara.

Bata san sanda ta miƙe tsaye ba, idonta ya ƙafe, babu ko ƙwayar tsoro. Ba tare da tunanin komai ba ta kama hanyar barin ɗakinta.

Fita ta yi da ga ɗakin nata, sannan bata bari komai ya dakatar da ita ba ta buɗe ƙofar ɗakinsa.

Hasken fitilun da ke ci a ɗakin suka haska mata shi, duk da babu wani wadattacen haske, durƙushe yake a ƙasa, yana karta faratan hannunsa a kan carpet, duk da baya ya bata amma tana iya jiyo gurnanin da yake.

A hankali ƙafafunta suka shiga taka tiles ɗin ɗakin har zuwa kan carpet, duk wani tsoro da tasan an haifota da shi ta ji ya gushe, babu wani abu kuma da take ji ko ganin ze iya tsoratata.

“Eshaan!”

Tafida dake durƙushe a wajen ya motsa kunnensa yana sakin wani irin gurnani kamar zaki, kafin ya ɗago jajayen idanuwansa.

Yana miƙewa tsaye ba tare da ya juya ba yasa hannunsa ya buge Maryam, ta faɗi can a gefe, yayin da ta saki ƙarar a zaba, sbd hannunta da kanta da suka bugu.

Se a sannan ya juyo, Maryam zata iya rantsewa da Allah kayan cikinta sunyi juyin waina, kafin ta ji wani abu na shirin sub'ucewa a mararta. Sakamakon kallon da yake mata, ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja, fiƙoƙi guda biyu sun sauƙo daga haƙwaransa na sama.

Se huci yake yana gurnani kamar bear, da ƙyat Maryam ta miƙe tsaye. Bata fasa abinda ta yi niyya ba ta shiga takawa zuwa gabansa, shi kuma be fasa kallonta ba, yana huci da gurnani.

“Kaga Eshaan, ka saurare ne”

Muryarta ta faɗi cikin wani irin sauti wanda yake nuna daf take da fashewa da kuka.

Tafida ya ɗaga hannunsa ya damƙi wuyanta, tareda ɗaga ta sama, Maryam ta shiga kakarin azaba, hannayenta a kan nasa da suka shaƙeta.

“Esh...Eshaan.....Esh...Esho!”

Cikin wani wahallalen sauti ta furta hakan, tana faɗi tana kallon idonsa, kalmar sunan 'Esho' da ta shiga kunnensa ta haske masa da wani zamani daya shuɗe.

_ “Kada ka damu Esho, zan dawo, kaide ka kula da kanka”_

“Maa!”

Ya furta hakan a iya kan leb'ensa, Maryam dake wutsil-wutsil da ƙafafunta tana kallonsa.

A hankali wani abu kamar haske ya gifta ta idon nasa, jan ya shiga washewa nan take, sannan ya saki Maryam ta faɗo ƙasa tana dafe wuyanta haɗi da tarin azaba.

Gani ta yi ya faɗi ƙasa shima, yana dafe kansa.

“Maa!, Meri Maa!, Maa kyu?!kyu Maa?!”

(Maa, Maana, Maa me yasa ?, me yasa Maa?).

Kan nasa ya ƙara dafewa yana rintse ido, hayyacinsa na dawowa cikin jikinsa.

A tarihin rayuwarsa baƙin ruhinsa be tab'a tashi ya tafi cikin sauƙi haka ba.

Ya kai minti goma durƙushe dafe da kansa, Duka Maryam dake dafe da wuyanta tana kallonsa.

Kafin kuma tashi ɗaya kamar wanda aka zabura ya miƙe zaune yana dube-dube, Maryam ta yi saurin ƙarasawa kusa da shi tana dafa shi.

“Eshaan lafiya?”

Tsayawa ya yi yana kallonta, sai kuma abinda ya mata daki-daki ya shiga dawo masa, a hankali wata ƙwalla ta silalo masa.

Kafin ya saka hannunsa ya ture na Maryam dake jikinsa.

“Maryam ki yi haƙuri”

Cikin kuka ya furta hakan yana sunkuyar da kansa, Maryam ta shiga girgiza masa kai tana ƙara kamo hannunsa amma se ya fisge yana ja baya da ita daga zaunen da yake.

“Dan Allah Maryam ki yi haƙuri, ni ban dace da ke ba, kina buƙatar mijin da ya cancanceni amma ba irina ba, ni ban kamace ki ba”

Maryam ta ƙara matsayawa kusa da shi tana share hawayenta.

“A'a Eshaan, ni kai ne naga ka kamace ni, kai na ke so Eshaan....”

“Ni kuma Maryam cutar da ke zan yi, ba za ki iya zama da ni ba, i am monster Maryam, i am beast, lalata miki rayuwa kawai zan yi, ni ban kamaci zama da kowa ba....kaɗaici ne ya dace da ni, na yi kuskure  da na saka kika fara so na, na yi kuskure da na fara sanki, ban kamaceki ba Maryam, sam ban kamace ki ba”

Muryarsa har wani sarƙewa take sbd kukan da yake, jikinsa na jijjiga sosai, dan kuka yake bil haƙƙi da gaskiya, kuka yake wanda rabonsa da ya yi irinsa ya manta, kuka yake na rabuwa da Maryam, zuwa yanzu yasan cewa idan har yaci gaba da zama da ita to cutar da ita kawai zeci gaba da yi, sam Maryam bata kamace shiba.

“Ni mara amfani ne...”

Ya shiga marin fudkarsa yana faɗin.

“Ni annoba ne, lalata rayuwar kowa nake....”

Yanda Maryam ta haɗe bakinta da nasa ne yasa shi yin shiru, kusan a tare suke fitar da ƙwalla masu zafi, Maryam ta ja da kanta baya kaɗan, sannan ta tallafe fuskarsa da hannayenta biyu.

“Kana da amfani Eshaan, kana da matuƙar amfani a gare ni, kai ba anno ba ba ne, kai mijina ne, abun alfaharina, madubin kallo na, gobe na dama komai nawa kai.......ne”

Wata sabuwar ƙwalla na cika masa ido ya kama fuskarta sannan ya ƙara haɗe bakinsa da nata.

Yana kissing ɗinta kamar ba ze dena ba, kafin ya saketa yana meda numfashi.

“Ina sanki Maryam, ina mutuƙar sanki, dan Allah kada ki rabu da ni, idan kika rabu da ni wallahi zan iya mutuwa......”

Da sauri Maryam ta miƙe a akan guwowinta, sannan ta rungume kansa a ƙirjinta, shi kuma ya kewaye hannayensa a ƙugunta yana ƙara matseta a jikinsa, hawaye na ƙara tsananta a fuskarsa.

“Bazan rabu da kai ba, trust me, ina nan tare da kai”

Kafin ta saki kan nasa tana dawo tana kallon fuskarsa, a hankali ta shiga share masa hawayen da yake.

Sannan ta kara goshinta a kan nasa, ta lumshe idonta, shi kuma ya yi amfani da hakan wajen riƙe fuskarta, ya haɗe bakinsa da nata ya shiga kissinga sosai.

Kafin ya motsa hannunsa a setin switch. Duhu ya mamaye ɗakin, babu haske se wanda yake shigowa ta balcony.

A wannan daren abubuwa da dama suka warware, a wannan daren abubuwa da dama suka gyaru. Babin ƙaddarar ya zo ƙarshe, littafin ya rufe, aka buɗe wani sabo, wannan daren ya zama mabuɗin wara sabuwar ƙaddara da zara tu karosu wadda basu da masaniya a kanta. Kuma Allah ya riga ya hukunta faruwarta.

A wannan daren.

*Haɗejia Emirates*

Galadima na kwance a kan gadonsa, yana baccin a zaba kamar yanda ya saba kullum, dan har yanzu jikinsa ba sauƙi, kullum jiya i yau.

Kawai ji ya yi ƙashin bayanasa na ƙara, hakan yasa ya buɗe idonsa, a hankali a hankali yake jin kasusuwan jikinsa na komawa inda suke, kamar da sab'a su a ka yi, yanzu kuma suke warewa cikin ƴancinsu.

Yana jin yanda ƙafarsa ta miƙe ƙalau, ya ji sanda hannunsa ke komawa yanda yake da, ya ji bakinsa na dawowa yanda yake, komai nasa ya dawo normal.

Kamar bacci ya kwanta kuma ya farka, kamar idonsa ya ƙifta sannan ya dawo dai-dai, babu shiri ya miƙe tsaye, ya yi tsalle a kan ƙafarsa dan ya tabbatar.

Aiko yana gani haka ya fita da gudu, be yi birki a ko ina ba se tsakiyar ɗakin Fulani Sadiya, wadda take sallar tsakar dare.

Bata ko idar ba ta miƙe tsaye tana kallonsa, mamakinta ya kaa b'oyiwa a fuskarta, tsabar farin ciki haka ta rungume ɗan nata tana sakin kuka.

Kafin kuma ta sake shi ta yi sujjada tana godewa Allah, shima ganin hakan yasa ya yi tasa godiyar.

Allah kenan ƙadurin ala man yasha'u, daga ranar Fulani ta ƙudirce a ranta cewar ba zata sake jifan wani da sharri ba, ba zata ƙara shiga sabgar kowa ba a masarutar ma.

Dan taga ishara da ayara Allah, ta ƙara jaddada girman Allah a ranta, ta ji tsoron lahirarta ya ƙara kamata.

A wannan daren de.


*Kurabi forest, Balu Thanda Village, Telangana state, South india*

“Oum nabishkar, oum nawaskamaha, oum jejebahawah, oum takdarsukaddam, naleyancifale......”

Wani mutumi dake zaune a gaban wanu kaskon wuta da ke ci ke karanto waɗanan ɗalasiman tsafin, gashin kansa ya taru da yawa an ɗaure shi da wasu zarririka, fatar jikinsa ta yi baƙiƙirin, ga wasu fararen layuka huɗu da aka ja daga gaban goshinsa, an ɗisa ja a tsakiyarsu.

Idonsa a rufe yake, amma bakinsa na furta waɗanan ɗalasiman, yayin da hannunsa na dama ke ɗebowa wani farin gari dake cikin wata kwalla yana zubawa a cikin wutar, a duk sanda ze zuba se wutar ta ƙara ta shi sama, jikinsa babu riga, hakan ya bayyana wasu tarin sarƙoƙi dake rataye a wuyansa, yanayin siffar jikisa de kamar mahaukaci.

“.....Na miskar waskam, taren minde bani maham....”

Da wani irin sauri ya buɗe jajayen idanuwansa wanda suke kama da garwarwashin wuta. Firgici, razani, tashin hankali da bala'i sune kwance a kan fuskarsa.

Abinda ya haɗa da hannayensa tsawon shekaru talatin da ɗaya shi ne ya karye, wannan abun da ya haɗa shi da kansa dan cimma burinsa shi ne yau aka karya.

Cikin wata iriyar fusata ya miƙe tsaye ya nufi wani rami dake cikin kogon nasu, wata mata dake cikin siffar haske ta shiga binsa a baya, ƙafafunta basa tab'a ƙasa amna tafiya take, duk da ba cira ƙafafunta take ba.

“Ina kuma zaka je ?”

Muryar matar ta faɗi cikin harshen telugu, be ko kulata ba ya ci gaba da tafiya yana taka ciyayin dake ƙasan wajen, har ya kai gaban wata ƙasa da aka tarata gu ɗaya.

An barbaɗa wani jan gari a samanta, ga ƙwarangwal ɗin kan saa an aje a kai, sai wasu lemun tsami da aka kewaye tarin ƙasar da su.

Da sandar hannunsa ya yi nuni ga ramin, nan take kayan kai suke baje zuwa gefe, ramin ya shiga haƙa kansa da kansa, har ya kai ƙarshe.

Wata kwalba ce ta bayyana, wadda take a fashe, jinin dake ciki ya zube, ga wani baƙin hayaƙima da ya fito daga ciki.

Cike da takaici ya ɗaga kansa sama ya ƙwalla wata ƙarar hasalla, wadda ta haddasawa tsintsayen dake a kan bishiyoyin wajen kogon ta shi sama.

“Me ya faru Subhurmanyam?”

Wata murya ta tambaya da ga bayansu cikin harshen telugu, matar da mutumin suka juyo a tare suka kalli tsohon mutumin dake tsaye.

“Kace min idan har na binne wannan abun asirin ba ze tab'a karyewa ba, kace babu wanda ze iya temakonsa a hannu na, amma gashi yanzu asirin ya karye ”

Tsohon ya ɗan karkata kansa kaɗan ya leƙa cikin ramin.

Se kuma ya juya musu baya, sannan ya rufe idonsa, ya shiga karanto ɗalasiman tsafinsa.

“Nimratr, nakamji, biktahne, abhikiratre, ghumbans.....”

Yana yi yana motsa hannunsa a ƙasa.

Wani wawakeken rami ya buɗe, hoton Tafida da ke kwance a kan gadon ɗakinsa da Maryam kwance a jikinsa ya bayyana.

Tsohon ya zaro idonsa yana ja baya, ya kusa faɗuwa dan sai da Subhurmanyam ya kamo shi. Kansa ya leƙa shima yaga a binda mahaifin nasa ya kalla.

“Wacece ita?”

“Ka yi sake Subhu, ka yi babban sake...”

Baban ya faɗi yana girgiza kansa, Subhurmanyan ya juyo da shi suna fuskantar juna.

“Meke faruwa ?”.

“Ka binne asiri tsawon shekaru talatin da ɗoriya, baka waiwayarsa, sai ƙarfin da ka ke ƙara masa da ga gefe, amma baka sani ba har suka aura masa makarin baƙin ruhin da ke jikinsa, yanzu haka ya kusanci yarinyar, kuma daga lokacin asirin ya karye, kowani laifi akwai lokacin karb'ar hikuncinsa, haka kuma ko wani abu da aka binne a ƙarƙashin ƙasa wata rana dole se ya fito, akwai ranar ƙin dillanci Subhu, lokacin ya yi”

A fusace Suhbu ya juya.

“Kullum abinda nake faɗa muku kenan, na sha faɗa muku cewar wanna ba rayuwa ba ce me kyau, na ce daku ku ajeta a gefe amma bakwajina yanzu ga irinta nan...”

Wannan matar ta cikin siffar haske ta faɗa.

“Ya isa haka Mama, ki bari!”

Matar ta yi shiru tana ƙara ta shi sama kafin ta b'ace a iska.

“Ba ze iyu ba, sam ba zai iyu ba, ni bazan karb'i wani hukunci ba, bazan yarda ba.....”

“A'a Suhbu, lokaci ya ƙure”

Cikin fusata ya juyo ya shaƙi wuyan baban nasa da babu riga a jikinsa, jajayen idanuwa sa waje.

“Kai baka isa ka faɗa min abinda zan yi ba, ba zan tab'a faɗuwa ba, dole se na yi nasara”

Ya saki wuyan Manikandan ya na juyawa ya fuskanci wata ƙatuwar gunkiya dake kafe a kogon, hannayenta huɗu, ɗaya ta riƙe wuƙa, ɗayan kuma kan mutum ne, na ɗayan b'angaren kuma wata mashun tsini uku ne riƙe a ɗayan hannun, ɗayan hannun nata riƙe da wani kwano, ta ɗora ƙafarta ta hagu a kan wata gawa dake yashe a ƙasa babu kai, ga damisa tsaye a bayanta, ta zaro harshenta waje tare da zare ido.

“Na rantse da abar bauta Shakti, se na shayar da jininsa ga abin butata, dole ne ya mutu ”

“Subhu Eshaan ba shi ne matsala ba, wannan yarinyar da ke tare da shi ita ce matsala, dole se mun kawar da ita tukunna, domin idan har tana raye ba zamu iya kashe shi ba ” Cewar Manikandam mahaifin Subhu.

A karo na farko Subhu ya ɗago da kansa yana dariya, baƙaƙen haƙwaransa da basa samun arziƙin wanki suka bayyana.

“Zan kuwa kasheta, kuma shi da kansa zan saka ya kasheta”

“Tayaya kenan ?”

“Zuwa gobe ina so ka buɗe ƙofar kogon nan a nigeria, a cikin garin lagos, cikin Alaro city”......

Daga wannan maganar tunaninsa ya ɗauke shi ya yi cilli da shi shekaru arba'in baya.............




Post a Comment

0 Comments