TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 25-26

 *PAGE* *25*~*26*


 




    *Ina taya ki murnan gama litafinki sister na NI BA 'YAR KOWA BACE Allah ya k'ara basira Allah yasa muyi amfani da darrusan dake ciki,Muna maraba da zuwan sabon novel d'in ki na BAWAN ALLAH, Allah yasa ki gama lafiya, Ameen*









 



*Har ta* koma office tunanin shi takeyi ji takeyi kamar kar su rabu, zuciyar ta tace why?meyasa take jin haka game da FAWAS?bata da mai Bata wannan amsar dole ta hak'ura taci gaba da aikin ta. 



Ranar haka ta yini cikin wani irin hali da k'yar ta iya aikin. 








The following day



NUWAIRA ce zaune a office d'in ta abin duniya yayi mata yawa ta rasa ya zatayi da rayuwar ta zuciyar ta na mutuwar son KAMAL amma ta k'arfi an raba su she really don't know what to do. Kifa kanta tayi akan table har bataji shigowan MEENAL ba. Har sai da ta d'an buga table d'in.


Firgigit ta dawo hayyacin ta wani irin mugun kallo ta watsa ma MEENAL tace"uban me ya kawo ki office na?"


D'an zaro ido tayi tace"Kai NUWAIRA abin har da zagi ne haka, I'm sorry dama na shigo ne in sanar da ke cewan Mom na neman mu a office d'in ta"


Mik'ewa tsaye tayi tace" to dole sai kinzo da kanki wallahi ni na tsani ganin face d'in ki gaba d'aya" taja tsaki ta bar office d'in.



Jikin MEENAL a sanyaye ta fito office d'in, HUSNA na kallon ta tasan akwai abin da ya same ta Dan ba haka ta shiga office d'in ba.





 

Da sauri ta fito gurin parking lot tana murmushi, NUWAIRA dake lab'e bayan ta tana son ganin ina zata take sauri. Haba zaro ido tayi lokacin da taga KAMAL suna gaisawa da MEENAL cikin farin ciki. Wani irin bak'in ciki taji,da sauri ta nufa gurin tana zuwa ta wanke MEENAL da wani irin azababben mari, cikin huci ta kalla KAMAL tare da rik'o hannun shi cikin kuka ta fara cewa"what have I done wrong to deserve this? shin ka yarda a raba mu? Ka yarda ka cire soyayyar da kake min a zuciyar ka,uhm tell me what's happening?"


Lokaci d'aya yaji wani irin sabon son ta a zuciyar shi da k'yar ya iya cewa" No kawai ina son kiyi ma iyyayen ki biyayya ne that's why"


Kallon shi tayi tace"look into my eyes and tell me you love me"


Idanun su ne ya had'u guri d'aya cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa suka shiga gaba d'aya sun bar duniyar mu sun shiga na soyayya.



MEENAL dake gefe rik'e da gurin da NUWAIRA ta mare ta hawaye ne kawai ke zuban mata, she's totally speechless, Dan taga ainihin k'aunar dake tsakanin KAMAL da NUWAIRA, lokaci d'aya taji sun bata tausayi Kuma sub burge ta. Gaskiya ita ta hak'ura da cewar tana son KAMAL domin basu dace ba.he only meant for NUWAIRA, ita yanzu ta d'auki KAMAL a matsayin yayan ta ne, murmushi tayi ta bar gurin.



KAMAL ne ya fara dawowa hayyacin shi cikin sauri ya k'wace hannun shi gudun kar Mom ta hango su da sauri yace"look NUWAIRA I really love you but bazan iya cigaba da soyayya dake ba kuma kinsan meke faruwa I'm begging you please let's end it now"


Wani irin kuka ne ya k'wace mata da gudu ta bar gurin. Tana Jin wani irin zafi a zuciyar ta.






******************************







After two weeks



Gobe ne ranar da su NUWAIRA da MEENAL zasu cika shekaru ashirin da d'aya da haihuwar su.tsakanin NUWAIRA da MEENAL wata d'aya ne. Kawai Mom ta shirya musu BIRTHDAY party domin tayasu farin ciki,duk da Daddy yace kar ta had'a domin a ganin shi wannan ai bidi'a ne amma tace ina ai Sam ba zai yuwu ba dole ta shirya musu BIRTHDAY party. Kawai ya k'yale ta tunda tana da kafiya.






Gown masu shegen kyau na mussaman tasa aka shirya musu. Dan kowa ne d'aya zai Kai duba saba'in ga Kuma takalman su hill masu shegen kyau, mussaman ta d'auko Wanda zasuyi musu make-up.



Dilka aka Fara musu sanan akayi musu lalle amma ja sai suka fito kamar larabawa. Sannan akayi musu gyaran Kai  dayake Allah ya basu gashi Nan aka gyara shi amma ba'a sa relaxer ba, gaba d'aya gashin aka had'a guri d'aya akayi musu donut da shi, gashi anyi inviting d'in mutane dayawa, har 'yan company d'in su they're invited, invitations card da aka kawo ma Mommy ne FAWAS ya gani gaba d'aya ya cika da farin ciki dan haka yaje SAHAD STORE ya siyo wani necklace silver me shegen kyau tare da earring d'in shi, 





*RANAR BIRTHDAY PARTY*


                    🎂




Wata mai yin make up ce ta shigo tayi ma MEENAL wani irin make-up amma light make-up course yafi fito da natural beauty, sannan tasa mata nata gown d'in light pink colour da torch d'in red Yana want irin shining like stars, hill shoe da wallet d'in duk light pink ne, earring kawai na gold aka sa mata. Sannan aka d'auko wani abu kamar butterfly aka sa mata ta bayan gown d'in, akayi mata rolling d'in veil akai Wanda yake kamar net Kuma transparent. Masha Allah nace she's looking like doll baby. Tayi masifar kyau ba k'adan ba.






 Ta b'angaren NUWAIRA ma haka ne duk abin da akayi ma  MEENAL ita ma haka akayi mata banbancin colours be kawai dan na NUWAIRA komai golden colour ne Kuma ita ansa mata necklace. Wayyo fan's kar kusu ku ganta tayi massifar kyau,kuyi imagining d'in mace chocolate colour cikin Kaya golen, sannan Kuma mace fara cikin Kaya pink and red, ni dai nasan sun had'u over,




A ko'ina ansa balloons an Kuma rubuta sunayen su. *NUWAIRA &AMINA*







  NUWAIRA ce  da MEENAL suka fito a tare  shigowa sukayi  cikin hall d'in inda yake cike da mutane dayawa.tafiya take cikin k'asaita kamar baza ta taka ba, yayin da MEENAL ke tafiya mai cike da natsuwa, gurin ansa wani irin wuta me colours sai juyawa yakeyi,  dai-dai zasu hau high table aka hasko su da wuta tare da zubo musu da red flowers Yana zuba a kansu,


Masha Allah kawai mutane ke cewa dan sun had'u over sai suka fito kamar stars, NUWAIRA gaba d'aya ta cika da haushin MEENAL gani take kamar ta fita kyau, zuciyar ta ya cika da kishi mai zafi.


Tun lokacin da su MEENAL suka fito FAWAS ke kallon ta domin gaba d'aya tayi wani irin bala'in kyau sosai, haka shima KAMAL yaga Masoyiyyar tashi NUWAIRA tayi Mai kyau dan tare yazo da FAWAS.






MEENAL ko murmushi kawai takeyi zuciyar ta fari fes, wani irin kid'a aka sa Yana tashi a hankali wak'ar mai dad'i mai sanyaya zuciya mai sauraro.


Mom ce ta fito gurin tare da d'aukar speaker ta gabatar dasu NUWAIRA. Duk gurin aka d'au tafi sannan ta Kiram Daddy ya fito yaje gurin, karb'an speaker'n yayi ya Kira Ummie wacce duk jikin ta yayi sanyi, da k'yar ta k'arasa gurin.


Mom ko haushi ne ya cika ta ganin yanda Daddy yake nuna kulawar shi akan Ummie.


Duk gurin aka d'au tafi sannan NUWAIRA ta yanka,taba Mom a baki, Koda ta gutsura sai ta had'a hannun ta Dana NUWAIRA taba Daddy shima a baki. Kallon Ummie ba suyi ba. MEENAL na kallon su Kuma bataji dad'i ba.


MEENAL ta yanka cake, Ummie'n ta tafara ba sannan Daddy sai Mom habawa duk gurin aka d'au tafi.



Daga Nan aka cigaba da yin birthday d'in inda suka samu kyauta sosai, FAWAS yaba MEENAL nashi gift d'in taji dad'i sosai, babban abin da yayi mata dad'i Kuma ya ba kowa mamaki shine kyautar mota Mom taba MEENAL,dank'a Mata key tayi hannun ta, MEENAL ita kanta tayi mamaki, sai farin ciki ake yayin da zuciyar NUWAIRA tayi zafi sosai dan me yasa za'a ba MEENAL mota banda ita abin ya Mata zafi,



MEENAL na tsaye ita da KAMAL yana fad'a mata irin son da yake ma NUWAIRA,ita Kuma tace zatayi k'okari taga sun koma sun cigaba da soyayya, kawai sai ganin NUWAIRA sukayi a gaban su tana huci a tunanin ta ko soyayya sukeyi, 


Cikin d'aga murya tace" sai yaushe Zaki fita harkar na? Wai menayi miki ne a rayuwa MEENAL" sai ga hawaye.


Da sauri MEENAL tace" menayi miki ne? ni har yanzu baki gayamin abubuwan dana ke miki ba"


Cikin zafi ta fara magana tace" kina son sanin abin da kikayi min ne? To bari in fad'a Miki, kin k'wace min soyayyar da iyaye na ke min,kin k'wace min gatan da ake nuna min har a gurin aiki kin fini matsayi, kin k'wace min KAMAL Kuma kinsan massoyina ne, kin k'wace min komai yanzu har mota aka baki amma ni ba'a bani ba, Wai meya kawo ki cikin rayuwa ta ne? Me kike so game da ni?" Ta fashe da kuka,da sauri KAMAL yayi k'okarin rik'e ta, ta dakatar da shi.


Cikin hawaye MEENAL tace" ban k'wace miki komai ba kece kike ganin hakan, ban shigo rayuwar ki ba, sai dai Allah ya k'adara cewa Daddy shine mahaifina, maganar dukiya bai dame ni ba komai kike so zan baki indai nawa ne dan nafi sonki a matsayin 'yar uwa ta akan dukiya, ki gafarce ni dan Allah ki janye wannan tsanar da kike min ki so ni kamar 'yar uwa'n ki, NUWAIRA mu *ZURI'A D'AYA* ne"



NUWAIRA ba abin da ta tsana irin MEENAL tace su *ZURI'A D'AYA* ne dan ta tsane ta cikin zafi ta k'wace key d'in motar a hannun MEENAL tayi waje da gudu, da sauri ita ma MEENAL tabi bayan ta tana Kiran ta,


Dai-dai lokacin da FAWAS ya fito Yana neman ta ganin shima KAMAL ya bi su waje yasa ya fita, 


Mota ne mai shegen kyau pink colour 'yar k'arama na mata, cire flowers d'in dake jikin motan NUWAIRA tayi sannan ta bud'e ta shiga ciki, ganin hakan yasa MEENAL ita ma ta shiga tana ba NUWAIRA hak'uri, da gudun gaske NUWAIRA taja motan suka hau kan titi.


Cikin razana da rud'ewa FAWAS ya shiga nashi motan tare da KAMAL, suka bi bayan su,


Daddy ne dasu Mom suka fito bayan sunga wucewar motocin gaba d'aya hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba duk sun rud'e, Daddy ne ya fara kwantar musu da hankali.





Gudu sosai NUWAIRA takeyi,yayin da FAWAS yake binsu a baya Yana yin horn alamar su tsaya, sai dai ina NUWAIRA bata saurare shi ba, cikin kuka MEENAL tace" NUWAIRA me kikeyi haka ne so kike mu mutu ne?"



Juyowa tayi cikin zafi da d'aga murya tace"eh mu mutu gaba d'aya nafi son mu mutu....." Bata rufe baki ba kallon gaban ta da zatayi wani irin babban mota ne DAF ta gani a gaban su cikin tsoro da firgici duk sun rud'e sun fita hayyacin su, MEENAL sunan Allah take Kira, cikin ikon Allah NUWAIRA ta kauce ma motan yayin da motan yayi gefen titi ya bugi wani bishiya da k'arfi, duk kansu yayi gaba NUWAIRA ta buga Kai haka ita ma MEENAL,




 Parking FAWAS yayi cikin tashin hankali shida KAMAL suka nufi motan, da sauri FAWAS ya bud'e murfin motan tare da ciro MEENAL, kwantar da ita yayi a jikin shi gaba d'aya ya fita hayyacin shi especially da yaga jini na zuba ta goshin ta, 


KAMAL ko gurin NUWAIRA yaje ya rik'e hannun ta da k'yar ta iya bud'e idon ta, ya fito da ita daga ciki, yayin da take Jin wani irin jiri na d'aukar ta,


FAWAS d'aukan MEENAL yayi yasa ta a mota sannan su KAMAL suka shiga, inda ya wuce direct hospital,


Da sauri aka shiga da MEENAL emergency room, hankalin FAWAS duk ya tashi, Kiran Daddy ne ya shigo wayar shi Yana d'auka ya fad'a mai hospital d'in da suke,



Doctor ne ya fito Yana sanar da su cewan Babu abin da ya same ta doguwar  Suma tayi sai ciwon da taji a goshin ta shima k'adan ne, sannan aka duba NUWAIRA ba abin da ya same ta, a lokacin ne su Daddy suka shigo gurin,


D'akin da aka kwantar da MEENAL suka shiga, ganin ta sukayi tana zaune idon ta biyu, duk sun gode ma Allah da abin ya tsaya iyakar nan,


Mom ce ta fito ta samu NUWAIRA a zaune ita da KAMAL,Yana ganin ta ya mik'e ya bar gurin, k'arasowa tayi gaban ta tare da d'aga hannun ta, ta Kai Mata wani irin Mari Mai shegen azaba, da sauri NUWAIRA ta rik'e gurin tana hawaye,


Cikin zafi Mom tace"Ashe Zaki iya kashe MEENAL? wannan wani irin tsana kikayi mata ne? Kin samu na Raine ki kamar 'yar da na haifa Amma yanzu da abin da Zaki saka mana dashi kenan?"


Girgiza kai tayi tace"kiyi hak'uri mom bansan ya akayi hakan ya faru ba"


Tsawa ta daka mata tace"Yi min shiru idiot kawai Baki da hankali ne? Idan da ace ta mutu wallahi sai nayi shari'a dake stupid, wannan ya Zama last warning da zan Miki domin duk abin da ke faruwa tsakanin ki da MEENAL ina sane" taja tsaki ta bar gurin,



Kuka NUWAIRA ta fashe da shi, yau ita Mom ke fad'a ma haka har tana yin mata gori, lalai ya Zama dole ta nema *ZURI'AR TA* tunda har an Fara mata gori sai ta Nemo asalin ta.



Post a Comment

0 Comments