TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 21-22

*PAGE* *21*~*22*





   *DEDICATED To ALL MY FAN'S*




 *Oh my fan's I'm speechless I don't even know what to say u make me feel happy, Alhamdulillah naji sauk'i, nagode sosai da addu'oin ku gare ni, masu Bina ta private charts suna gaishe ni nagode sosai wallahi, wayyoo gaskiya Kuna k'auna na, ina rok'on Allah ya bar mu tare, I really appreciate,  and ni UMMU BASHEER I love you so much my fan's,  Kuna shagwab'a ni dayawa fa ji nake kamar inyi Mai course I'm happy, sai da ku nake samun k'arfin gwiwa, NUWAIRA and KAMAL tare da MEENAL and FAWAS suna mik'o sak'on gaisuwar su gare ku gaba ki d'ayan ku massoya, thanks again for your love and support, I love you wujiga-wujiga duk wuya duk runtsi ana mugun tare ina nufin irin taren nan*


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


  *My Aunty Rahmat Nalele ina rok'on Allah ya baki lafiya, kiyi ta suburbud'o Mana SAMAREEN BANA course fan's gaba d'aya ke suke jira*




*Sister Maimounath ke d'in ta daban ce wallahi kinfi k'arfin su na fad'i Kuma na k'ara fad'a bana tsoro ehe idan ba bomb ne zai tashi to sai dai ya tashi, Allah ya k'ara miki basira tawan da k'warin ido*












  *FAWAS* ya lura gaba d'aya friend d'in shi na cikin damuwa, a hankali cikin sanyin murya yace" my friend i know something is bothering you please tell me?"


Jikin KAMAL a sanyaye yace" friend you know I won't hide anything from you"


Yace" no ban yarda ba common feel free and talk to me please"



 Bai b'oye mai komai ba game da raba shin da akayi da NUWAIRA sai dai ya b'oye mai Koran shi aiki da akayi course baya son ya tayar Mai da hankali, ya tausaya Mai course shima yana jinyar rashin masoyiyyar shi before yana cewa soyayya ai shirme ni yinshi wasting of time ne ya d'auki Wanda ke soyayya just like a mad person, but now he realized what  actually true love is, 


Magana ya fara cikin tausayin friend d'in shi yace" na tausaya maka sosai, before I was saying love is useless thing but now I realize what love is, friend Allah yasa ka samu NUWAIRA course I know she's your happiness"


  Ya fahimci cewan akwai abin da ke damun FAWAS, Nan ya tambaye shi meke damun shi, amma yak'i fad'a mai sai da k'yar yace" I know idan na fad'a ma you will laugh at me bare kuma I'm rejected by the woman I truly loved" kasa magana yayi dan tuno da abin da ya faru between him and MEENAL.


Cikin mamakin abin da ya fad'a yace" don't tell me wacce kake so bata son ka?"


  Kamar ya fashe da kuka yace" yeah friend I really love her and I don't want to lose her yazan yi please?" Lokaci d'aya idon shi ya canza colour zuwa red.


Hak'uri tare da lalashin shi ya fara har zuciyar shi yayi sanyi sannan yace" inshallah zan ta yaka da addu'a Allah ya zab'a maka mafi alkhairi a rayuwar ka, but tell me who's this beautiful woman that you are dying for her?"


Dukan wasa ya Kai mai yace" I don't know, kar ka sani a gaba da tsokana"



Ai ko dai bai fad'a mai ba, suka d'an yi hira daga k'arshe FAWAS ya kai KAMAL har gida,





 ***************   **************



Cikin dressing d'in ta na Arabian gown black tayi rolling d'in veil akan ta, light make up tayi, amma tayi mugun kyau, cikin sauri-sauri ta sauko downstairs ta nufi dining area inda duk aka had'u ana break fast, gaishe su tayi, sannan ta fara breakfast d'in ta, tunda ta sauko downstairs NUWAIRA take Jin wani irin bala'in haushin ta, mik'ewa tsaye tayi zata bar gurin da sauri Ummie ta rik'o hannun ta tace" Ayya please ki gama breakfast sai ku wuce tunda MEENAL ta shirya"


Wani dogon tsaki taja tare da k'wace hannun ta da k'arfi ta bar gurin, dan gaba d'aya haushin Ummie takeji,


Girgiza kai Daddy yayi a zuciyar shi cewa yake wannan wani irin tarbiyya ne Aisha ta ba yarinya nan?, tsaki yayi ya bar gurin, 


Ummie bata ji dad'in abin da NUWAIRA tayi mata ba ita dai Allah ya d'aura mata son yarinyan a zuciyar ta,


Mik'ewa tsaye MEENAL tayi tana musu sallama, lokacin da ta fito waje ta tarar da NUWAIRA tsaye a jikin mota ran ta a b'ace yake k'arasawa tayi tace"I'm sorry sister na miki wasting of time"


Tsaki taja tace" you are very stupid,  don't pretend to love me as your sister course I will never forget how you betrayed me"


 Girgiza kai tayi tace" wallahi banyi betraying d'in ki ba believe me, buri na d'aya shine inga mun dawo yanda muke a da please try to understand me"


D'aga hannu tayi alamar bata son wani magana, ta shige mota. da sauri driver ya k'araso. MEENAL ta shiga ya wuce da su school.





  After four hours


 Cikin gajiya ta k'arasa gurin parking lot d'in course a gajiye take dan lectures d'in yau me zafi ne, cikin riga da wando na shadda white colour yayi kyau sosai ta hango shi. Ko a mafarki bata tab'a tunanin cewa zata gan shi ba.


Murmushi ya sakar Mata, k'arasawa tayi tana cewa" are you really the one KAMAL?"


Dariya yayi yace"yeah I'm the one, two days bana ganin ki so I decided to come here mu gaisa" ya k'are maganar yana waige-waige alamar yana neman wani abu.


Murmushi tayi cikin farin ciki tace" ayya ka kyauta sosai ya aiki ya mama da my little brother"


Amsawa yayi cikin jin dad'in yanda ta nuna kulawar ta ga abin da duk duniya bashi da kamar su wato Maman shi da k'annin shi yana son su sosai,



 Nan suka fara hira suna dariya cikin nishad'i, abin da basu sani ba ashe NUWAIRA na kallon su tun fitowan MEENAL ta fito Kuma ta gansu, zuciyar ta ne ke tafasa tana jin wani irin kishi, abin da yafi bata haushi yanda KAMAL ya nuna kamar bai ma san tana makarantar ba. duk da cewan an raba su.


 Sallama KAMAL yayi ma MEENAL ya tafi, a lokacin ne NUWAIRA ta iso cikin b'acin rai ko kallon ta batayi ba ta shige mota tana had'a rai,


Murmushi kawai MEENAL tayi dan ita gaba d'aya tana cikin farin cikin ganin KAMAL ne.





 


Hmm masu karatu guess what? in taik'aita muku dai kusan Koda yaushe sai KAMAL yazo sun gaisa da MEENAL inda shak'uwa ya shiga tsakanin su. Yayin da a Koda yaushe zuciyar NUWAIRA ke cika da bak'in ciki da kishi mai zafi. gashi tana ganin gaba d'aya kamar KAMAL ya manta da ita ne yana rayuwar shi,


Abin da bata sani ba shine. Kullum da sonta yake kwana Kuma yake tashi, plan ya had'a na ganin ta wato kullum zai had'u da MEENAL to yasan tabbas zai gan ta. Shiyasa da ya fara zuwa yake ta waige-waige yana neman ta. tunda an raba shi da ita shi Kuma zaiyi k'okari ya dinga had'uwa da ita ta hanyar MEENAL. Abin da ya lura shine MEENAL ta na da kirki tana son Maman shi k'annin shi. tana kyautata mishi sai ta fara burge shi. Ba wai Yana  son ta bane No kawai he likes her behaviors ne. 



 MEENAL ko ji takeyi kamar something is missing in her life. But she don't know ko mene ne. Haka Kuma tana jin KAMAL a ranta Kuma tafi tausayin shi course yanzu tasan komai a kanshi har abin da ke faruwa tsakanin shi da NUWAIRA dan ya d'auke ta like his sister shine ya fad'a mata damuwar shi. Sai dai yace Mata ya samu wani aiki. Ashe aikin kanikanci yakeyi gareji yake zuwa yayi gyara a biya shi. Wayyo ni ummu basheer na tausaya mai.




Tsakanin Mom da Ummie kuwa Babu abin da yake had'a su na shiri, ita dai Ummie zata gaishe amma sai taga dama take amsawa. Dan ma bata da time bata cika Zama a gida ba kullum tana office.





**************************** 




    A yau ne suka Kamala karatun su inda suka fito da results mai kyau. Daddy yaji dad'i sosai haka yayi ta sa musu albarka. KAMAL yazo gurin sai dai a b'oye ya ba MEENAL gifts. NUWAIRA ko kamar zatayi hauka ranar tasha kuka.



 

MEENAL ko sai duba wristwatch d'in ta takeyi kamar tana jiran wani abu ji takeyi kamar something else is still missing in her entire life. Har taro ya watse lafiya suka koma gida.





Bayan ta shigo bedroom ta cire Kaya sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito sai tunani take Wanda ta rasa na mene ne. Ta gama sa kayya kenan taji anyi banko k'ofa da k'arfi an shigo. D'ago da kan da zatayi wa zata gani. NUWAIRA ce fuskar ta yayi ja alamar tana cikin b'acin rai.


Da mamaki MEENAL tace" lafiya NUWAIRA? naga kin shigo ba sallama?"


Wani wawan tsaki taja tace" ank'i yin sallaman. nazo ne inyi miki warning domin na riga na gano cewan kina son KAMAL! Kuma KAMAL nawa ne ni kad'ai kinyi k'arya ki raba mu wallahi course we meant for each other" 


Zaro ido tayi cikin mamakin abin da ta fad'a tace" you are wrong, kinyi mistake ni ba son KAMAL nake ba"


Tsawa ta daka mata tace"shut up your dirty mouth, kina tunanin ban Gane ba, let me warn you for the last time, ki fita harkar na ki daina shiga rayuwa ta na tsane ki, na tsane ki a rayuwa ta ina rok'on ki for God sake ki rabu da ni" ta fashe da kuka.



Da sauri MEENAL ta Isa gurin ta, rik'o hannun ta tayi tace" ki fahimce ni Dan Allah wallahi ni ina k'aunar ki a matsayin ki na 'Yar uwa ta, mu *ZURI'A D'AYA* ne"


K'wace hannun ta tayi cikin zafi ta Mari MEENAL, da sauri ta fad'i k'asa tare da dafe inda ta mare ta,


Cikin hawaye tace" me kike nufi da mu *ZURI'A D'AYA* ne? How comes muka zama *ZURI'A D'AYA* bayan ba jinin mu d'aya ba, na tsane ki MEENAL, I hate you" da gudu ta bar bedroom d'in, 


Yayin da MEENAL ta rushe da kuka. tana jin wani irin zafi a zuciyar ta course tana jin NUWAIRA kamar sister'n ta.





  After two weeks




 Mom ce take sanar da dukan su cewa zasuyi aiki a company d'in ta na manufacturing Kaya, sunyi farin ciki sosai su Daddy ma sun taya su murna. Kuma tunda company na Mom ne tace zasu fara aiki next week.





         Next week Monday



 NUWAIRA ce ta shirya cikin riga red and black skirt tayi rolling kanta da black veil sai sunglass da tasa taci heavy make-up, fitowa tayi cikin tafiyar k'asaita,



MEENAL ce sanye cikin Arabian gown dark pink colour tayi rolling veil d'in akan ta, heavy make-up tayi ga wani hill shoe pink da handbag da ta sa. cike da natsuwa take saukowa daga upstairs. 


Kallon ta NUWAIRA tayi taja tsaki. 


Ummie cikin farin ciki tace"Allah yayi muku albarka Allah yasa ku fara aiki cikin sa'a"


Ameen MEENAL tace ita ko NUWAIRA fita tayi a zuciyar ta tace matar nan ta cika shishigi mtwwwssss taja tsaki ta shiga mota. Mom ce da MEENAL suka k'araso tare da shiga motan jefi-jefi suna hira. NUWAIRA ko wani irin zafi takeji. Dan kafin zuwan MEENAL ita da Mom ke hira tana nuna mata so amma yanzu tana ga kamar bata son ta ne,




  


Cikin wani babban gini na bene mai girman gaske driver yayi parking. Fitowa sukayi, tare da shiga ciki. Wani elevator suka shiga inda suka fito a 4th floor. Mai aikata ne duk suka mik'e suna musu barka da zuwa. D'aga musu hannu kawai Mom keyi, cikin farin ciki MEENAL ke amsa gaisuwar su tana murmushi lokaci d'aya sukaji ta burge su.



  Gurin meeting suka shiga dan kowa sun hallara su Mom kawai ake jira. Tana shigowa duk suka mik'e tare da yin gaisuwa. d'aga musu hannu kawai Mom tayi sannan suka zauna inda su MEENAL suka zauna a kujerun dake kusa da ita.



Bayan kamar 5 minutes Mom ta mik'e tsaye ta gabatar musu da yaran ta wato NUWAIRA da MEENAL. tashi suka tsaye tare da gaishe da shugabanin gurin. Sannan suka zauna. 


Mom ce ta kalle su Nan take ta fad'a musu matsayin su a gurin aiki. Inda MEENAL aka bata PRESIDENT na gurin making Kaya sannan ita Kuma NUWAIRA matsayin VICE PRESIDENT.



Duk gurin aka d'au tafi. Ana musu congratulations. Yayin da zuciyar NUWAIRA ke bugawa cikin matsanan cin damuwa da k'yar ta iya daurewa, cikin farin ciki marar missaltuwa MEENAL ke amsawa. Sai flowers ake basu.




 

Mom ce ta nuna musu office d'in su. Na MEENAL na kusa da na NUWAIRA, office d'in yayi bala'in kyau da tsaruwa. Especially na MEENAL course she's the President. Komai na office d'in ta orange and white ne. Yayin da na NUWAIRA komai Navy blue ne, wow ama sunyi kyau,




 Wasu ce aka kawo mata su biyar Wanda zasuyi dinga mata wani aikin. Baban cikin su sunan ta *HUSNA* lokaci d'aya MEENAL taji ta kwanta mata a rai. Suma gurin duk sun yaba da kirkin MEENAL.




 NUWAIRA wata aka kawo mata a matsayin wace zata taimake ta da wani abin sunan ta *Bilkisu* ama ana Kiran ta da BILLY, 


NUWAIRA k'are ma office d'in kallo tayi ta zauna a kujera tana juyawa can ta mik'e tsaye ta buga table d'in da k'arfi tace" kinyi k'arya ki fini komai hakan ba zai tab'a yuwuwa ba bazan tab'a yarda ba ni NUWAIRA nafi k'arfin ki MEENAL" ta bushe da dariyan mugunta.


 


Post a Comment

0 Comments