TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 35-36

*PAGE* *35*~*36*





       *Shafin k'arshe*



           *The last page*


                    *The End*




   *B'angaren* Mom kuwa, bayan ta Kira Aliyu ne yazo suka had'u a wani park, inda duk ta rud'e ta fara tambayar shi cewa ya fad'a mata ko mahaifin NUWAIRA asalin 'yan Ina ne ? Gaba d'aya sai ya rikice ya kasa amsa mata har ta gaji da tambayar shi ta gano bashi da gaskiya, tace lalai sai ya fad'a mata gaskiya akan NUWAIRA,


Cikin rud'ewa da rasa yanda zaiyi yace" maganar gaskiya NUWAIRA da na kawo miki 'Yar da Ummie ta haifa ne tare da MEENAL"


 Cikin tashin hankali tace" me kake nufi? Mai kake son cewa?"


Cikin dauriya yace" Ina nufin Ummie 'YAN BIYU ta haifa, NUWAIRA da MEENAL, nine na raba su na d'auki NUWAIRA na kawo miki Dan kawai in samu kud'i Kuma ita ma tayi rayuwa gidan mahaifin ta, kiyi hak'uri na Miki k'arya tun farko"


 Ba tasan lokacin da ta d'auke shi da wani irin gigitacen Mari ba tace" why do you betrayed us? Me yasa tun farko baka gaya min ba? All this years ka kasa fad'a min gaskiya, gashi can yanzu NUWAIRA ta tafi neman Asalin ta, idan ta gano me kake son inyi da wani idon Zan kalla mutane? Allah ya Isa tsakani na da Kai" tana gama fad'in haka ta bar gurin.




 Cikin sanyin jiki da nadamar abin da ya aikata ya koma k'auyen su, bai b'oye ma Kaka komai ba ya fad'a mai gaskiya, ai ko dama a gaban mahaifin Aliyu'n ne Nan yayi Mai fad'a sosai yace bai yafe Mai ba tunda ya cuce 'yar uwa'n shi, haka Aliyu yayi ta basu hak'uri sannan da kanshi yaje  har Abuja gidan su Ummie, da farko Mom taji tsoron ganin shi, amma sai duk yace Yana son magana dasu har dasu Hajja.



MEENAL ma yayi mata waya yace tazo gidan, gaban ta sai da ya fad'i tana tunanin ko lafiya, FAWAS ne Mai bata hak'uri akan ba komai, Nan suka je.



 Bayan duk sun taru ne a parlour gaba d'ayan su ya fad'a musu gaskiyan abin da ya faru har d'auke d'ayan jaririyan da yayi na Ummie Wanda ita ce NUWAIRA duk ya fad'a musu!.



 Cikin tsanin b'acin rai Daddy ya mik'e tsaye ya nuna Mom da yatsa yace"Ashe duk zaman da nake dake na yaudara ne, Ashe kina cin Amana na ne ban sani ba, Dan me yasa zakiyi min k'arya akan NUWAIRA, sai ki fad'a min gaskiya gashi na rayu da 'YA ta a matsayin marainiya ban tab'a sananin cewa yarinyan da na haifa bane, meyasa rashin samun haihuwa ya rufe miki ido ne? Kin cuce ni ban yafe Miki ba"



 Gaba d'aya Mom ta rud'e ta rasa mai ke mata dad'i a duniyar.


 Ummie cikin rashin fahimta tace" ALIYU kayi min bayani da kyau Sam ban gane mai kake nufi ba?"


Cikin nadama yace" abin da Kika ji na fad'a gaskiya ne, kiyi hak'uri ki gafarce ni"


Mik'ewa tsaye tayi ta Isa inda yake tare da wanka mishi Mari Mai shegen azaba tace" kana hauka ne shin kasan me kake cewa? Kana nufin 'YAN BIYU na haifa? NUWAIRA da MEENAL sune 'YAN BIYUN da na haifa? Amma tsawon shekarun Nan ban tab'a sani ba Kuma Muna tare da kai, Ashe Kai macucu ne mayaudari ne Allah ya Isa tsakani na da Kai wallahi bazan tab'a yafe maka ba, akan kud'i ka raba ni da abin da na haifa, ban yafe maka ba, Kuma Allah sai ya saka min abin da kayi min" ta fashe da kuka, Hajja ce ta rungume ta tana mai bata hak'uri.


MEENAL ko ta kasa ko motsawa ashe dama NUWAIRA jinin ta ce, shiyasa take matuk'ar k'aunar ta, Ashe mahaifa d'aya suka fito,Ashe su d'in *ZURI'A D'AYA* suke.


Cikin hawaye tace" Kawu Aliyu me yasa zaka aikata mana haka Shin dama Dani da NUWAIRA' YAN BIYU ne? Amma ka kasa sanar da mu? Meyasa zaka aikata wannan d'anyar aikin?Ashe nida NUWAIRA *ZURI'A D'AYA* muke" ta fashe da kuka, FAWAS ne ya rungume ta Yana lalashin ta ko kunyar mutane bayayi, shi dai kawai burin shi ya lalashi matar shi,



Jin an bud'e k'ofa ne an shigo yasa duk suka kalla k'ofar, wa zasu gani!? NUWAIRA ce da KAMAL suka shigo.


Straight NUWAIRA gurin Mom ta nufa ta rik'e hannun ta tana girgiza ta cikin d'aga murya tace"Yau Ina son ki fad'a min gaskiya, shin a Ina Kika same ni? Aliyu shine Wanda ya baki ni ko har Kika bashi kud'i ko?"


 Mom duk ta rud'e ta rasa mai zata ce, k'ara girgiza ta NUWAIRA tayi cikin d'aga murya tace"ki amsa min tambaya na, shin Daddy da Ummie sune iyaye na? Shin nida MEENAL 'YAN BIYU ne? Answer me please"


Durk'ushewa tayi a k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsananin gaske, da sauri Ummie ta k'arasa gurin ta zata rik'e ta ne, ta tashi cikin b'acin rai tace"No karki kuskura ki tab'a ni duk kece Kika jawo komai ya faru idan da baki bar gidan Daddy na ba da duk hakan bai faru ba, yanzu da ace bandage Nan gidan Aliyu ya kawo ni ba da a Ina Zan rayu? Da ke da shi tare da Mom duk Kun cuce ni kunsa na rayu a gidan mahaifina a matsayin marainiya Kuma 'Yar rik'o, duk na tsane ku" ta fashe da kuka tare da barin parlour'n da sauri, Gaba d'ayan su basu ji dad'in yanda NUWAIRA tayi ba amma kuma bata da laifi domin tana cikin tsananin b'acin rai tana buk'atar hutu yanzu dan zuciyar ta tayi sanyi, 


MEENAL ce ta fito waje dai-dai NUWAIRA zata shiga mota ta rungume ta tace"nasan yanzu Zaki San ainihin k'aunar da nake miki na 'Yar uwa ta mu 'YAN BIYU ne, kin yarda mu *ZURI'A D'AYA* ne?"


NUWAIRA lokaci d'aya taji wani irin k'aunar 'yar uwa'n ta lokaci d'aya da nadamar abin da take mata a baya cikin hawaye dukan su suka kalla juna tare da sakin murmushi, suka rungume juna.


KAMAL da FAWAS da suke tsaye suna kallon su duk sai suka burge su, sunji dad'in yanda suka shirya dan dama tun farko tare suka gansu a matsayin Aminan juna.


NUWAIRA murmushi tayi tace"Tun farkon had'uwa na dake nake k'aunar ki, ko abubuwan da nayi ta aikata miki duk kishin ki ne yasa nayi hakan Amma Ina rok'on ki da ki yafemin, na yarda mu *ZURI'A D'AYA* ne mu d'in 'YAN BIYU ne" duk sukayi murmushi.


FAWAS ne ya k'araso yace" TWINS SISTERS idan Kun gama soyayyar sai ku kula mu mazajen ku" 


Dariya sukayi gaba d'aya cikin k'aunar junan su, suka shiga mota gaba d'aya zuwa gida cikin farin ciki marar missaltuwa.



 Mom gaba d'aya ta rasa mai ke mata dad'i Daddy ya juya mata ba haka ma Hajja, sai binsu take tana basu hak'uri da k'yar suka hak'ura.



Daddy da kanshi yaje har gidan NUWAIRA suka gaisa ya bata hak'urin abin da ya faru ita ma ta bashi hak'uri, sannan sukayi ta hira irin na 'Ya da mahaifi cikin k'aunar junan su.



 Ummie ko tana yawan kyautata ma NUWAIRA Dan ta gyara laifin da ta aikata Mata, duk da haka NUWAIRA na fushi da ita kwata-kwata tak'i yarda suyi rayuwa irin na 'Ya da Mahaifiyar ta, Ummie bata Jin dad'in hakan MEENAL ce ke yawan bata hak'uri tace taba NUWAIRA lokaci zata huce.


  *****************************


 Rayuwa ce mai cike da Jin dad'i sukeyi, yanzu cikin NUWAIRA da MEENAL ya shiga wata na tara. Haihuwa yau ko gobe kuma suna samun kulawa ta b'angaren mazajen su.


 Yau tun safe MEENAL ke Jin wani irin azababben ciwon mara daurewa kawai takeyi. Har sun kwanta zasuyi barci dan lokacin k'arfe 9:00 pm ne,  jawo ta jikin shi yayi tare da rungume ta very tight yana shafa cikin ta cikin k'auna, can taji wani irin azababben ciwo, tayi d'an k'ara dan taji azaba.


Da sauri FAWAS ya zauna yana kallon ta yace"me ya same ki, ko haihuwar yazo ne muje hospital?"


Daurewa kawai tayi tace"No kawai juyi ne, let's sleep"


 Rungume ta yayi tare da had'a lips d'in su guri d'aya ya fara kissing, can taji wani irin ciwo Kuma da sauri ta ture shi ta tashi tsaye, cikin rud'ewa yace"baby Ina Jin fa labour kikeyi please let's go to hospital"


Tana zagaye bedroom d'in tace"nifa ba labour nake ba kayi barci kawai,juyi ne Kuma zai daina"


 K'in yarda yayi kawai sai ya nufa side d'in Mommy ya Kira ta, ko kafin su zo nak'udan yayi tsanani dan wani irin Nishi takeyi, sai addu'a takeyi.



Mommy na shigo taga halin da take ciki tace ai labour ne, FAWAS duk ya rud'e tausayin matar nashi ya kama shi, k'in tafiya yayi duk da Mommy na korar shi yak'i tafiya,



 Cikin ikon Allah MEENAL Allah ya sauke ta lafiya inda ta haifa 'YAN BIYU duk maza, Kuma identical twins ne masu kama da baban su Dan komai sak na FAWAS ne, habawa zo kuga murna gurin su ba'a cewa komai.



Ranar suna yara suka ci sunan Daddy'n FAWAS da Daddy'n MEENAL, ana Kiran su da AMAN da IMAD, yaran sun ga gata sosai.


Washegarin suna NUWAIRA ma ta haihu inda ta haifa 'YA mace Mai kama da KAMAL, ranar suna yarinya taci sunan NANA AISHA sunan Mom aka sa, ai ko taji dad'i sosai, NUWAIRA tun bayan ta haihu take Jin kunyar had'a ido da Ummie dan tayi nadamar abin da tayi mata, haka Kuma tana jin wani irin k'aunar Ummie a ranta sosai. Bayan tayi arba'in ta rok'e Ummie gafara ta yafe Mata abin da tayi Mata, Nan suka shiga da shiri sosai, Ummie ta had'a kan yaran ta NUWAIRA da MEENAL tana nuna musu k'auna sosai Kuma ita da Mom suna zaman lafiya.


  ***************************


      *Ten years later*



   *Bayan shekaru goma*




  Wasu kyawawan yara na gani su biyu suna yin basketball, AMAN da IMAD kenan, can sai ga wata yarinya sa'ar su ce ta zo gurin tana wani yamutsa fuska tace" ku dai baku da aikin yi sai basketball, mtttsss Allah ya shirya ku"


AMAN ko kallon ta baiyi ba sai IMAD yace" Ke NANA na lura kin raina mu ko mu sa'an ki ne?" Ya fad'a Yana zaro ido.


Wata yarinya ce ta k'araso gurin da gudu tana cewa"eh d'in ai ko sa'an mu ne" har da murgud'a Baki.



 Da gudu IMAD ya fara bin ta suna zagaye gurin Wai sai ya buge ta Yana cewa"  ke marar kunya ZEE ko? Ai sai nayi maganin ki yau"


Cikin parlour ta shiga  tana zuwa ta taga wasu yara su biyu suna wasa ta buge su ta ruga d'aki ta kulle tana dariyan mugunta,


IMAD ko tsayawa yayi Yana lalashin yaran ITRAN da JAWAHIR kenan,



Can sai ga NUWAIRA da MEENAL sun fito daga bedroom suna tambayar me ya faru, dukan su suna d'auke da tsohon ciki, IMAD ya fad'a musu ai ZEE CE ta duke su ta gudu, Nan MEENAL tace ta bud'e amma tak'i, can sai ga FAWAS da KAMAL sun shigo, Zee na Jin muryan baban ta ta bud'e k'ofar, ta rungume FAWAS tana ma IMAD gwalo. Shi ko hararan ta yayi.



MEENAL tace" idan na rik'e ki Zaki sani"


KAMAL yace"meye ta Yi ne da za'a rik'e ta? na lura Kuna takura ma Zee d'ina"


FAWAS yace"ka bar ni da Mommy'n su nice maganin ta" ya kashe ma MEENAL ido d'aya alamar zamu had'u.


Hararan wasa tayi mai, can sai gasu AMAN da NANA sun shigo, 



Nan sukayi ta hira cikin nishad'i da farin ciki.




Bayan MEENAL ta haifa 'YAN BIYU ne sai ta haifa ZAINAB Wanda taci sunan Ummie, daga Nan ta haifa ITRAN Mai sunan Mommy'n FAWAS,


NUWAIRA Kuma bayan NANA ta haifa JAWAHIR, sai cikin da suke d'auke da shi yanzu, 


FAWAS da kanshi ya gina musu gida shi da KAMAL yanzu gida d'aya suke kowa da side d'in shi,



Zaman lafiya sukeyi sosai, da k'aunar junan su, haka Mom da Ummie, suna cikin kwanciyar hankali bare kuma idan aka kawo musu jikokin su ai basu da wani matsala. Ummie ta Gina ma mahaifin ta Kaka gida yayi aure Kuma ta yafe ma ALIYU abin da yayi mata. Abba Kuma yanzu shiri suke sosai shi da Kaka.



Sanye take cikin wani night sunyi mata bala'in kyau, ta nufa kan bed inda FAWAS yayi mutuwar zaune Dan ba k'aramin kyau tayi Mai ba, tana zuwa ya rungume ta ya fara kissing d'in ta duk ya rud'e, ita ma ta dage sai maida martani takeyi, ganin sun cire kayan su ne yasa na fito Dan ba Dani ba. Lolx.




*Alhamdulillah*




*Anan na kawo k'arshen litafina Mai suna ZURI'A D'AYA, Ina ma Allah godiya da yasa na Kamala lafiya*




 *Allah ya yafe min kuskuren da nayi a cikin litafin Nan Allah yasa mutane su gane darasin da yake cikin litafin nan, Allah ya bamu ikon amfani da abin da ke ciki, Ameen*


  *Massoya na nagode sosai da yanda Kuke k'aunar novels na, Allah ya k'ara zumunci da k'aunar juna,Ina godiya sosai massoyan ZURI'A D'AYA*



*Muje zuwa sabon novel na Wanda zaizo muku Nan ba da jimawa ba, sai mun sake had'uwa,kar ku Bari a baku labari*


*TAKU CE UMMU BASHEER MAI K'AUNAR KU*✍🏻🌹 





Post a Comment

0 Comments