TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 21

 *BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA (21)*


UCHENNA POV.

Tsaye yake daga can nesa da masallacin da ake taron ɗaurin auren Hanam, waya yake da mamarsa tana faɗa masa cewar bazata samu damar zuwa ba, sbd ciwon mijinta ya tashi jiya da daddare.

“To mom ba damuwa, kice ina gaida shi, Allah ya bashi lafiya”

“Ameen, ka bashi hakuri please kace masa inshallah zan zo ko bayan bikin ne”

“To”

“Zan kiraka letter” 

Daga haka ya sauƙe wayar yana kallon Abba daya taho wajensa da sauri.

“Abba lafiya?”

“Ina fa lafiya Haris, call this number for me”

“Ok” 

Ya faɗi yana karb'ar wayar da Abban ke miƙa masa sam, hankalinsa ba akwance yake ba, ya kira Jabeer amma yaƙi ɗagawa, Uchenna ya saka lambar a wayarsa sannan ya aika mata kira.

“Ta shiga ?”

“Eh ta shiga...” 

Baima gama rufe bakinsa ba Abba ya warce wayar, saida ta kusa katsewa sannan aka ɗaga.

“Hello jabeer nine....”

Daga can b'an garen Jabeer ya sauke wayar daga kunnesa ya duba screen ɗin, shide lamba ya gani.

“Dan Allah kar ka kashe”

Ya rintse idonsa, dan da shirin kashewar yake.

“Ina kake Jaber ?” 

Murya ciki-ciki jabeer ya amsa da 

“Ina gida”

“Me yasa zaka min haka Jabeer ?, kasa na tara mutane amma kaƙi zuwa, haba jabeer”

Cike da rashin kunya Jabeer yace.

“Dallah daka tamin malam, ni bance me yasa kamin haka ba sai kai zaka zo ka wani titsiyeni da maganar banza, Da kake so na aure guntuwar yar ka to Allah ya toni asirin ku kaida ita, ashe karuwanci taje tayi a USA shine har ta dawo maka da jika, To Allah yasa matarka mutuniyar arzikice, ta kirani ta faɗa min komai, Dan haka ni bazan auri guntuwar yarka ba, wadda maza suka gama da ita, kada ka ƙara kirana sai anjima”

Dib!!, kiran ya yanke, duka abinda Jabeer ya faɗi a kunnen Uche, saurin kamo hannun Abba ya yi gani yana shirin faɗuwa.

“Abba ka nutsu, ciwonka kada ka bari ya tashi”

A lokacin Baba da kanin Abba suka ƙaraso wajen suma.

“Kai harisu me yake faruwa wai ?”

“Baba yaron nan yaci amanar mu, yace wai bazai iya auren Hanam ba”

Abba ya faɗi cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki, tunanika da yawa suna ta yawo a cikin kansa, to yanzu me zaije yace da Hanam, kuma wai tsaya yace matata?, wacece ta kirashi ta kitsa masa ƙarya da gaskiya ?.

Mero, wata murya ta faɗi a cikin kansa. Idanuwansa suka kaɗa sukayi ja, wato Mero duk abinda zai zo ya samu Hanam na farin ciki ita bata so.

Yayi ƙwafa a fili, sannan ya juya ya kalli Uche wanda ke riƙe da shi, sannan ya furta abinda ya zama sanadiyar sauyawar Ƙaddarar mutum uku a lokaci guda. Hanam, Arya, da shi kansa Uchennan.

“Haris, dan Allah inaso ka auri ƙanwarka Hanam”.

second ɗaya.... biyu....uku.


HANAM POV.

Zaune take a ɗakinta ita da ƙawayenta biyu na amana tun na primary, Falaq da Iqra, she can't believe wai yau aurenta ake, abun na bata mamaki.

Sanye take da farin lace ɗinkin doguwar riga kuma kamar kullum fuskarta babu kwalliya, yau sai take jinta a kaɗai ci, dan tun safe Rafi'a ta rabata da Arya.

Hayaniyar mutane a waje da taji ne yasa ta fahimci cewa ƴan ɗaurin aure ne suka dawo, sai taji gabanta ya takarkara ya faɗi, yanzu wai an daura mata aure ?, shikenan yanzu ta zama matar jabeer ?.

Ƙofar ɗakin aka turo Rafi'a ta shigo hannunta riƙe da Arya dake sanye cikin farar shadda wadda su kayi anko shida Abba, Hanam ta kallesu su duka.

“A'a masoyi ina ka shiga ne bamu ganka ba?”

Cewar Iqra tana miƙewa ta ƙarasa inda Rafi'an ke tsaye riƙe da Arya.

“E ba, nima ban ganshi ba” 

Cewar falaq, a lokacin kuma Rafi'a tace.

“Anti Hanam kije inji Abba, yana babban parlonsa” 

Hanam taji gabanta ya tsananta bugu, kamar wani abu ne da ban ya faru da wanda take tsammani.

*

Ganinsu su uku a parlon yasa gabanta ƙara tsananta bugu, Abbane da Baba da kuma ƙanin Abba wato kawu Audu.

“Zo ki zauna a nan” 

Taje ta zauna a kusa da Baba dake wannan batu, tun da ta shigo Abba ke binta da kallo tausayinta na ƙara kama masa zuciya, ta wahala sosai a rayuwarta, kuma yana fatan wannan auren da ya mata ya zama silar samun farin cikinta a rayuwa, yasan abinda yayi daidaine.

Dan yanaganin shine ma abinda da yadace ace ya yi tun-tuni, amma da Allah ya ƙaddara cewar hakance zata kasance gashi ta kasance, kuma yana da tabbacin za ta yi farin ciki a nan gaba.

“Hanam”

Ya kira sunanta, a hankali ta ɗago da kanta ta kalleshi tana amsawa, sai kuma ta ƙara sun kuyar da kan nata ƙasa.

“A yau na ɗauri miki aure da wani ba Jabeer ba, sai a yau na tabbatar da Jabeer sam bai dace da ke ba, ya sakani na tara jama'a shi da wakilansa kawai ake ake jira amma yaƙi zuwa, na kirashi a waya sai yake cemin wai shi ba zai auri sauran ƴata ba, ya faɗi maganganu da yawa, daga karshe yace kada na ƙara kiransa....”

Sai kuma ya yi shiru, Hanam dake jin duniyar ta mata shiru tun a maganarsa ta farko ta ɗago ta kalleshi, idan ba Jabeer aka aura mata ba to waye ?!!.

“Hanam, na aura miki wanda na aura miki ne dan na isa da ke, nasan da cewa ke me biyyayace ga duk abinda nake so, nasan baki tab'a bijire min ba, kuma nasan cewa wannan karon ma bazaki bijire ba....”

Ya kuma yin shiru yana ci gaba da kallon reaction ɗinta, har yanzu bata ce komai ba kallonsa kawai take, ita buƙatarta taji waye ya aura mata.

“Hanam, ba kowa na aura miki ba face UCHENNA!”.


MARYAM POV.

Tafe suke akan titi, ita da sabbin ƙawayenta ne, Aisha da Zara, hira suke ta yi amma Maryam bata saka musu baki ba, dan hira suke akan wani kyakyawa dake a block3.

Tun da Maryam ta fara zuwa makarantar ta lura da ƴan matan ajinsu basu da aiki se hira akan wani kyakyawa, kuma ita jikinta na bata cewa Tafida ne, kuma tunanin nata baije ko ina ba ta tabbatar da hakan lokacin da Zara tace.

“Wai ke Maryam baki sanshi ba ?, a block3 ɗinku yake fa, sunansa Tafida”

Damm!, gaban Maryam ya faɗi, wani abu me kama da kishi nasan taso mata, ji take kamar ta koma Makarantar ta tara duka ƴan matan ajinsu, musulmai da Cristian, turawan da baƙar fatar duka tabisu da mari ɗaya bayan ɗaya, ciki kuwa harda su Zara dake tareda ita....

“Ya za'ayi tace bata san shi ba, ke babu budurwar da bata san shi ba a Alaro city gaba ɗaya” 

Maryam ta juya ta kalli Aisha, sai kuma ta kawar da kai taci gaba da kallon hanya.

“Ke nifa wannan gashin kan nasa kawai nake san tab'awa, daga nesama fa har sheƙi yake, gashi jiya dana ganshi naga gashin nasa ya ƙara tsayi” 

Cewar Zara, idonta har wani kyallin murna yake.

“Kede bari Zara, wallahi sumar nan tasa tana burgeni, shi tsiyarsa ɗaya, ba ya yiwa ƴan mata magana sai de maza, kuma mazan ma ba sosai yake musu magana ba, ke nifa ina ganinma jinin sarauta ne”

Maryam tayi shiru, sumarsa ?, itama de taga a kwanakin nan ya fara tara suma, wata ƙila so yake ya tara kamar ta wannan hoton, sai tunanin yaso ya bata dariya, taji itama tana san ta tab'a sumar tasa ta ji, ita zata iya hakan, amma su fa?, kawai de suna karanta wasiƙar jaki ne.

“Hmm aisha sai kingan shi yana magana, damn!, i can't wait to sit on that mouth....”

“Sai goben ku”

Maryan ta faɗi tana jara saurin tafiyarta haɗi da shan kwana ta shige block finsu, dan idan ta tsaya ta ci gaba da jin zantukan da suke zuciyarta kan iya bugawa, ko wata ƙilama ta yanke jiki ta faɗi, ko kuma ta make ɗaya daga cikinsu, tafiyar tata itace mafi a'ala.

“Me yake damunta ?” 

Aisha ta tambaya girarta a haɗe waje guda tana duban Zara, Zara ta dage kafaɗa alamun bata sani ba tareda faɗin.

“Ni ya za'ayi na sani, wata ƙila bata da lafiya ne”

“wani irin rashin lafiya kuma ?, bayan ƙalau muke tare da ita yanzu”

Zara ta tab'e baki cikin faɗin 

“Allah yasa lafiya, kinsan ita Maryam ba san surutu take ba, wata ƙila damunta mukayi”

Daga haka sukaci gaba da tafiyar su suna ci gaba da hirar da suka fara.

Maryam ta tsaya a ƙofar gate ɗin gidansu, sannan ta saka hannunta a cikin jaka ta zaro remote control ɗin da Tafida ya bata domin ta riƙa amfani da shi wajen buɗe gate din gidan.

 Ilham ce ta fito daga gidansu hannunta riƙe da leda, tana ƙwala mata kira, Maryam ta tsaya daga buɗe ƙaramar ƙofar da take shirin yi, ta juyo ta kalli ilham ɗin.

“Ina yini Anti Maryam” 

Ilham ta gaisheta yayinda ta ƙaraso kusa da ita, Maryam ta ƙaƙalo murmushi tana amsawa, ilham ta miƙa mata ledar hannunta tareda faɗin.

“Wai gashi inji Mamanmu, tace na kawo miki wai mamarta ce ta aiko mata daga kano” 

Maryam tasa hannu ta karb'a, a lokacin da itama tata mamar ta faɗo mata a rai.

“To ki ce nagode”

“To” 

Ilham ta faɗi bayan ta juya. Maryam ta ƙarasa buɗe ƙofar ta shiga.

A parlo ta aje jakarta ta makaranta, ta shiga kitchen ta aje ledar da Ilham ta bata, sannan ta shiga fito da kayan dake ciki.

Kub'ewa ce da kuka, kanwa, sob'o harda jan lalle, Maryam ta yi murmushi, tana hango yanda za ta yi amfani da kayan, dan dama tana buƙatar irinsu, kuma bata san inda zata samu ba.

Maman Ilham kamar da ta buɗe zuciyarta ta gani, aiko idan an jima za taje tai mata godiya kafa da ƙafa.

Ma'aji tai wa kowanne, sannan ta ɗauki lallen ta fita a ranta take faɗin, yau kuwa tuwo za ta yi, dan dama tayi missing ɗinsa, lalle kuma sai jibi za ta yi, jakarta ta ɗauka a inda ta aje sannan tayi sama.

Ta shiga ɗakinta ta aje jakar a inda ta saba, sannan ta aje lallen a cikin bed side drawer, ta cire hijabin jikinta ta shiga ban ɗaki, bayan fan wani lokaci ta fito, yau azumi take, dan haka ba abinci zata ci ba, koda safema iyaka na Tafida kawai ta girka, yanzun ma bazata tsiri yin tuwan ba sai anjima.

Balcony ɗin corridor ɗin nan ta tafi ta zauna akan lilon dake wajen, tana jin daɗin iskar garin, dan ba'a jima da ɗsukewar yayyafi ba.

Sai kusan shida ta tashi daga wajen, ta nufi kitchen bayan ta dauko wayarta da ring light din naan, ta jona Ring light ɗin, sannan ta saka wayarta a ciki, ta shiga daukan vedio tana recording girkin da take, ita bata iya editin ba, sai idan Tafida ya dawo yake mata sannan tayi posting.


TAFIDA POV.

_🎶You...._

_you got the keys to my heart, my baby never let me down_

_My baby never lets me down, my baby never_

_You...._

_You deserve a crown, my baby never lets me down_

_My baby never lets me down, my baby never_

_Baby you're my dealer, you my energy _

_I will give you my love, i will give you all of me.....🎶_

Sassanyar waƙar my baby, wanda Ayra Star da Bien suka rera ce ke tashi a cikin motar tasa, a kwanakin nan yana cikin nishaɗi sosai, kuma ba sai an tamabayi daliliba, Maryam ce sila.

A da shi kaɗai yake rayuwarsa, yanzu kuma ya samu abokiyar rayuwa, jinsa yake enough, baya buƙatar ƙari, ji yake ya gama samun komai na duniya, bashi da wani wayo lokacin da iyayensa suka rasu suka barshi, ya taso a wajen Fulani, saide sam babu wata shaƙuwa a tsakaninsa da ita, me martaba kuwa yakan kwana uku ma bai saka shi a idonsa ba a lokacin.

Bayan ya gama secondary kuma ya koma india, a can ne ya samu kulawa, soyyaya da ƙaunar ƴan uwa, duk a da ɗinma yakanje indian ziyara, amma zai iya cewa gidansa a india yake, domin farin cikinsa gaba ɗaya yana can.

Tinaninsa ya katse, a sanda ya ƙaraso ƙofar gidansa, gidan da a yanzu ya fi masa haske fiye da da, a duk sanda zai tako ƙafarsa cikin gidan sam baya san fita, yana so yaci gaba da zama da Maryam, koda babu wani kusanci tsakaninsu, sautin bugun zuciyarta ma kaɗai ya isheshi kasancewa cikin farin ciki.

Yasan i yanzu tana kitchen, dan haka yana shiga sama ya yi, ya yi wanka ya sauya kaya zuwa ash hoodie da baƙin chinos trouser, ya sauƙo ƙasa cikin farin ciki da ɗaukin ganinta.

Hannu ya kai ya murɗa handle ɗin ƙofar, tsaye ya ganta a jikin cabinet tana ɗaukan plate.

Tafida ya kasa kunne yana sauraron bugun zuciyar ta, yana jin abinda ya saba ji a kullum idan yana hakan.

A lokacin kuma ta jiyo ta kalli ƙofar dan taji lokacin daya turo ƙofar, tana ganinsa zantukan su Zara suka dawo mata, sai ta yi saurin kawar da kanta taci gaba da abinda take.

“Sannu da zuwa”

Muryarta ta faɗi sanda ya ƙaraso cikin kitchen ɗin.

“Yauwwa”

“Na gama recording” 

Ya gyaɗa kansa sannan ya ƙarasa zuwa jikin socket din data jona ring light ɗin ya cire, ya ɗauke ring light ɗin da wayar ya fita.

A kan danning ta jera masa abincin nasa kamar kullum, bayan ta gama, tana kallonsa a parlon yana daddana wayarta, da alama editing ɗin yake.

“Na gama abinci” 

Tafida ya jiyo ya kalleta, sai kuma aje wayar akan sofa ya taso ya ƙaraso zuwa danning ɗin, zama yayi akan kujera yana kallonta, ita kuma ta shiga buɗe warmers ɗin tana ƙoƙarin zuba masa abincin, ƙamshin miyar ya daki hancinsa.

“Tuwo kika yi ?” 

Muryar sa ta fito a lokacin da yake kallonta, itama ba tare da ta kalleshi ba tana saka tuwan semolina ɗin da tayi a plate tace.

“Eh, da miyar kuka”

“A ina kika samu kuka ?”

“Maman ilham ta aiko min ɗazu”

ya gyada kansa a hankali, rabonsa da tuwo ya manta ko a hadejia baya samu yaci shi.




Post a Comment

0 Comments