TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 15-16

 *PAGE* *15*~*16*





 


*DEDICATED TO MUSAN JUNA O.H.W. & TIMES ⏱ WRITER'S*



*Ina rok'on Allah ya k'ara muku basira da k'warin ido tare da zak'in hannu, Allah ya k'ara zumunci da k'aunar junan mu baki d'aya, Ameen*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*RUBUTACEN AL' AMARI*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Aunty AISHA ALI GARKUWA Ina taya ki murnan Kamala litafin ki Allah ya k'ara basira da k'warin ido tare da zak'in hannu*🍇


    *Up*


            *Up*


                     *Up*


*Ke d'in ta daban ce naki ba irin nasu ba ne a gaskiya kin fad'akar Kuma kin ilmantar da mu a cikin litafin ki,Allah ya Kare ki daga sharin makiyya da mahassada Ameen sai mun ciki a sabon litafin ki*🍇



*Allah ya jikan HAMMA UMAR FARUQ Allah ya raya abin da ya bari, UMMUL Allah ya raya ZURI'AR ki baki d'aya, Allah ya bar ki keda HAMMA USMAN dinki*🍇



*Nagaishe ku y'an group d'in AISHA ALI GARKUWA Fans tare da RUBUTACEN AL' AMARI Fans, UMMU BASHEER na k'aunar ku*🍇

 






*Kallon*  kaka sukayi gaba d'ayan su cikin rud'ewa, Abba ne yayi k'arfin cewa"Baba da gaske ne kana nufin MEENAL y'a tace amma ai Zainab tace yaron ya rasu?"


Kaka yace" babu d'an da ya rasu MEENAL ita ce 'yar ka, wacce Zainab ta haifa"


Cikin rud'ewa da rashin fahimta MEENAL tace" Kaka nifa ban gane maganar ku ba ya za'ayi kace wai Daddy'n NUWAIRA shine mahaifina?" Gurin Ummie ta nufa wace take zaune a k'asa, rik'e hannun ta MEENAL tayi tace"Ummie na ki fad'a min meke faruwa, ba kince mahaifi na ya rasu ba to ya za'ayi Kuma yanzu Kaka yake fad'in haka?"


Rushewa da kuka Ummie tayi cikin bak'in ciki, yayin da Kaka yace duk su shigo su zauna ayi magana Dan su fahimci meke faruwa,


Kaka ya ganar da su komai,inda Daddy yaji wani irin farin ciki tare da k'aunar y'ar shi MEENAL, cikin kuka MEENAL ta rungume Daddy tana kuka, shafa kanta yayi Yana cewa" Y'a ta ki gafarce ni duk Ni naja komai ban zama namiji tsayayye ba a gida na da har na Bari mace na juya Ni ki yafemin keda mahaifiyar ki"


Cikin hawayen farin ciki tace"ba komai naji dad'in had'uwa da Kai  mahaifin na"


 K'ara rik'e 'yar shi yayi cikin k'auna, yayin da Ummie ke share hawaye,


Daddy ne ya d'auki waya ya kira mahaifin shi ya gaya Mai,yayi farin ciki ba kad'an ba, Nan ya kira Hajja ita ma tayi farin ciki tace Kuma ya d'auko su Ummie su zo Abuja, haka ko akayi duk suka shirya Ummie gaba d'aya kunyar had'uw take da Hajja Dan Bata san me zata gaya Mata ba, MEENAL ko tunani take ko yaya Mom zata karb'e ta, amma sai dai Daddy ya fad'a musu suna rik'on NUWAIRA ce ba y'ar shi ba ce, sosai ta tausaya ma NUWAIRA ta so ace yar'uwan ta ce,


Ummie ce ta shigo d'akin da MEENAL ke shiryawa tace" MEENAL nasan da k'yar zamu dawo tare Dan nasan mahaifin ki zai rik'e ki ba zai bar min ke ba, ki gafarce ni k'in gaya miki gaskiyan da nayi"


Cikin kuka" Ummie na meyasa zaki raba Ni da mahaifina tsawon shekaru goma Sha takwas, meyasa Kika samin a raina cewa Mahaifina ya rasu,meyasa Baki  barni na rayu da mahaifi na ba naji dad'in soyyayan shi gare Ni da kulawar shi, duk meyasa....why ..... Ummie..... meyasa?" Kuka ne yaci k'arfin ta.


Rungume ta tayi tana cewa"ki yafemin wallahi bana son a raba mu ne banyi hakan dan wani abu ba nayi ne saboda k'aunar da nake Miki kuma nake ma mahaifin ki"


K'wace Kan ta tayi tace"please kawai ki k'yale ni" ta fita d'akin da sauri tana share hawaye,


Ummie ko kuka ta fashe da shi ganin yanda y'ar ta tak'i yarda da ita lokaci d'aya,




Sun Isa Abuja direct gidan Hajja suka tafi, already dama Hajja ta kira mom(Aisha) ta sanar mata, NUWAIRA ko lokacin da Mom ta gaya Mata sai da gaban ta ya fad'i ashe Daddy na da wata Y'a, tun bata gan ta ba taji ta tsane ta tare da wani irin kishi da taji, haka suka nufa gidan Hajja, Abba ko da yaji bai so aka gan su ba tunda su basu da mutunci a cewar shi dan shi fa har yanzu yana Jin tsanar Malam Zakariyya (Kaka),



Lokacin da suka shigo parlour'n gidan kowa a razane suka mik'e tsaye,


Mom ce ta nufa gurin Zainab cikin zafin nama ta Kai mata wani irin mari ji kuke taaaasssss, a firgice kowa ke kallon su, mom tace"kin cuce mu kin yaudare ni dana San abin da zakiyi kenan da bazan tab'a yarda ki auri Nasir ba wato......"


Hajja ce ta katse ta da tsawa tana cewa"kina da hankali, kin san me kikeyi, kuwa duk ba kece Kika jawo komai ba saboda rashin hak'urin ki, duk kowa ta samu guri ta zauna"


Ji kuke tsit dan suna shakar Hajja, zama kowa sukayi,inda Kaka da kanshi ya bud'e taro da addu'oi sannan ya fad'a duk abin da ya faru bayan barin Zainab gidan Nasir har zuwa yau,ya nuna musu MEENAL a matsayin yarinyan da Zainab ta haifa wato 'yar Nasir,



Cikin razana NUWAIRA ta mik'e tsaye tana girgiza kai tare da cewa"No it can't be MEENAL, ban yarda ba hakan ba zai tab'a kasancewa ba, she's my friend, Aa ba *ZURI'A D'AYA* muke ba" cikin kuka ta bar parlour'n.


Yayin da MEENAL ta mik'e tsaye domin ta bi bayanta saurin rik'o hannun ta Mom tayi ta rungume ta tace" welcome back my sweet daughter dama tun ba'a haife ki ba Daddy'n ki ya bani ke halak"


MEENAL hawaye kawai takeyi,ta rasa farin ciki zatayi ko bak'in ciki,


Ummie ko abin da take gudu ne ya faru wato rayuwar MEENAL a hannun mom,


Abba ne ya mik'e tsaye cikin tsanar MEENAL yace"yanzu wannan ita ce Yarinyan wannan marar kunyar, gaskiya ba ku bata tarbiyya ba"tsaki yaja ya fita waje,


Duk basu ji dad'in abin da yace ba amma suka share, Nan Hajja taja hannun MEENAL tana farin cikin yanda Zainab tasa sunan k'anwar ta AMINA, 



Hmm masu karatu ranar MEENAL taga gata da k'auna, Hajja Kuma tayi ma Ummie fad'a akan tafiyan da tayi tace hakan Bai dace ba, Nan dai tayi musu nasiha sai dai Mom bata d'auka ba domin tana Jin zafin Ummie da kishin ta,



Daddy ya d'auki MEENAL ya Kai ta gurin iyyayen shi,haka suka dinga murna da yake babban gida ne sosai haka aka dinga gabatar da ita gurin Yan'uwa, sannan Daddy ya Mai da Kaka k'auye Dan Hajja tace a bar mata Ummie ta kwana biyu wurin ta,


NUWAIRA ko bayan ta fita parlour'n direct mota ta shiga ta bar gidan, gida ta nufa ta dinga kuka sannan ta kira KAMAL ta fad'a Mai abin da ke faruwa,yayi mamaki sosai sai dai Bai ji dad'in yanda NUWAIRA ta nuna Jin zafin dawowan MEENAL ba ko da ya tambaye ta sai ta fad'a Mai gaskiya cewan ita ba y'ar gidan bace Kuma dole taji haushin dawowan MEENAL gidan Dan tasan sai sun nuna son y'ar su a kan ta, KAMAL ya tausaya mata sosai haka ya dinga lallashin ta da bata hak'uri har ta daina kukan sannan suka yi sallama,




Post a Comment

0 Comments