TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 21

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*21*

~~~

*Look out for those who look out for you. Loyalty means everything...*

***

*Unguwar Jama'are, Haɗejia...*

RABI POV.

“Wai har kun dawo?”

Cewar kakarsu Hajiya ta na binsu da kallo, dawowarsu kenan daga kasuwa, sun je siyyayar kayan biki, don a yanzu haka bikin saura wata ɗaya, sai shirye-shirye ake a gidan, duk sun zuzzube a falon Hajiyan suna maida numfashi.

“Wallahi Hajiya, kin san yau Lahadi... To kasuwarce a cike, ko siyyayar ma ba mu gama ba, kawai mun dawo ne, kin ga ko zuwa gobe ne sai mu ƙarasa siyyayar”

Cewar Kairiyya ta na cire hijabin jikinta, Hajiya ta gyaɗa kai ta na kaɗe ƙuda daga kan furarta. A dai-dai lokacin Nafisa ta shigo, wadda take daga ɓangaren mahaifiyarta, dan ita bata bisu kasuwar ba. Zama ta yi suka shiga firfitar da kayan da suka siyo.

“Ku wai ni yanzu wa za mu nema ya mana lalle?”

Momi ta tambaya ta na ɗaga wata doguwar riga cikin kayan da suka siyo.

“Akwai wannan Balkisan, ƙawar anti Shafa (Yayar Kulsum), ita ma ta iya lalle”

Cewar Nafisa.

“Ku na iya lalle fa, ku bari sai na muku”

Rabi ta faɗi tana dudduba nata kayan da ta siyo.

“Ke kuma a ina kika koyi lalle?” 

Jidda ta tambaya.

“A can mana”

“Ai kiwa ke za ki mana”

“To ke wa zai miki ?”

Fati ta tambaya.

“Sai ku kira min wadda kuka ce za ta muku da farko, sai ta min”

Kamar yanda suka saba a kwanakin haka suka shiga hirar bikin, dan daga zarar sun zauna kamar haka ba su da hira da ta wuce ta bikin.

Rabi'a ta saki jikinta a cikinsu tana sha'aninta, sai a yanzu take jin kamar rayuwarta ta setu, sai a yanzu da ta dawo cikin 'yan uwanta farin cikinta na da ya dawo, har wata ƙiba ta yi a cikin satin.

Kuma babu wani abu dake damunta face shi, wannan sunan; Raja!, har zuwa yau ba ta manta shi ba, ta yi iyaka i yinta amma ta kasa, ko bacci za ta kwanta da ta rintse idonta za ta hango waɗanan lumsassun idanuwan nasa. Ba za ta yi wa kanta ƙarya ba,ta san a cewa tana kewarsa!.

KULIYA POV.

Ya na daga zaune a falo ya na dudduba wani aiki a cikin ipad ɗinsa, hannunsa na dama riƙe da mug ya na shan coffee. Kamar daga sama ya ji muryarta a kansa.

“Abu Aswad... Barrow me your phone please”

Kansa ya ɗaga ya kalleta, mug ɗin kare da bakinsa, kamar kullum sanye take cikin ƙananu kuma ɗangallallun kayan da ta saba sakawa, shi har mamaki ma ya yi, a sanda ta faɗa masa cewar kaf cikin kayanta babu atamfa da lace ko makamantansu, ban da ƙananun kaya ba ta da wata sutura, hannunta na dama riƙe yake da littafi, yayin da na hagu kuma yake riƙe da pen. Gashin kanta nannaɗe cikin bun.

“Me za ki yi?”

Ya tambaya ya na ɗaga kafaɗarsa, tare da aje mug ɗin hannunsa a kan coffee table.

“Assignment zan yi please”

Sai ya ɗan kalleta na wasu sakkani, kafin ya aje ipad ɗin hannunsa, ya kamo nata hannun na hagu ya zaunar da ita kan cinyarsa. Ya na shirin sakin hannunta ya lura da hannun nata ya yi jajir sosai, kamar wadda ta ƙone. Hannun nata ya saki ya na kama waist ɗinta da hannunsa ɗaya.

“Me ya samu hannunki?”

Ya tambaya ya na gyara mata gashin kanta na gaba, Mishal ta shaƙi wata iska, kafin tace.

“Wani malami ne ya dake ni”

Kuliya ya miƙa hannunsa ya ɗauko wayarsa ya miƙa mata.

“Me kika yi?”

Ya tambaya a hankali. Sai ta turo bakinta gaba.

“Note ne ban yi ba... Ai Wallahi da da ne shi ma bai isa ya dake ni ba... Yanzun ma de kawai...”

Sai ta yi shiru tana daddana wayar tasa. Kuliya na kallon fuskarta yace.

“Yanzun ma dai me?... Yanzu kin girma ko?... Kin zama matar aure”

Ta ɗan yi dariya, ta na kallon wayarsa ta amsa masa da.

“Ba haka ba ne... Kawai de dan Anti Adawiyya ta min faɗa ne, ita tace duk malamin da ya min wani abu na ƙyaleshi kawai, malamai ba sa cuta sai dai gyara, idan kuma mutum ya cuceni na barshi da Allah, Allah zai saka min, shi ne fa ya sa na yi sanyi, amma ni da akwai malamin da ya isa ya dake ni!...”

Kuliya ya ci gaba da kallon bakinta dake furta kalaman, tsakaninta da Allah take bayananta, duk abun da Mishal za ta faɗa daga zuciyarta yake fitowa, ba ta san wani abu ba wai shi ƙarya, kanta tsaye take furta zantikanta, maganar ta ci gaba da masa idonta kan wayar, yanda ta sauƙe su ƙasa sai ka ce rufe su ta yi, dogayen gashin idonta sun kwanta a kan fuskarta, hasken wayar ya ƙara haska masa fuskarta, sai ya ji kamar ya saka makulli ya buɗe zuciyarsa ya sakata a ciki ya kulle, ya nesanta ta daga duk wani abu na cutarwa da ɓacin rai.

“Me nene wannan a haƙorinki?”

Sai ta tsaya da maganar da take masa ta kalli fuskarsa, gira ya ɗaga mata cikin sigar tambaya. Sai ta maida idonta kan wayar ta na faɗin.

“Datti ne... Dama haka haƙorina yake, duk wata Aki yake kaini a wanke min, da braces aka saka min ma, kwanaki aka zire min su”

“Ok gobe zan je na ɗauko ki a school... Daga nan sai mu wuce asbitin a wanke miki”

Ta kuma kallonsa.

“Angelica ta ce min ma wai an kawo wasu sabin teddies a Jabi Lake Mall, za ka kai ni?”

Kuliya ya yi murmushi ya na ƙara matse hannunsa a ƙugunta. Shi ne ya kamata a kira da mijin yarinya.

“Har Magic land ma za mu je”

Bakin Mishal ya tale cikin dariya. Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta na ci gaba da danna wayarsa.

“Abu Aswad?”

Muryarta ta kira sunansa bayan wani lokaci, ipad ɗin ya kawar daga fuskarsa ya kalli ƙasan kanta, don har zuwa lokacin ta na kwance a jikinsa.

“Hmm”

“I hate you”

Sai ya yi murmushi ya na ci gaba da kallon ipad ɗin.

“And i love you”

*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*

RAJA POV.

“Ku kamata!”

Wannan shi ne umarni da ya bawa jami'an da ya zo da su, a yayin da ya shigo cikin gidan su Rabi ba tare da ko neman izini ba, ya jure abubuwa da dama, amma ba zai iya jure rashin Rabi'a ba, zai fiye masa sauƙi ma a ce ya rabu da rayuwarsa, da ace ya rasata, Habiba ta azabtar da ita bakin gwargwado, dan haka lokaci ne da ita ma za ta ɗanɗani kuɗarta, ba ma ita kaɗai ba, har da Ɗan Lami ya sa an kamo shi, dan sai sun faɗa masa inda Rabi'a ta shiga.

Habiba ta fashe da kuka a sanda 'yan matan jami'an suka yi kanta, ciki kuwa har da Rhoda, Fatima da Mahmud har da Saratu suna tsaye suna kuka, haka aka kama Habiban aka fita da ita ta na ta roƙonsu.

Da ƙyar Raja ya iya dai-daita kansa, sannan ya lalubo ainahin muryarsa ya na kallon Saratu yace.

“Ka da ku damu, tambayoyi za a mata kawai, insha-Allah idan ta amsasu da wuri ina me tabbatar muku da za ta iya dawowa a yau ɗin nan, idan kuma ta yi taurin kai, ba zan iya muku alƙawarin dawowarta gareku da wuri ba!...”

Ko kafin ya kai ƙarshen maganarsa, Fatima ta ƙarawa kukanta volume ta shige ɗaki, Mahmud ma bayanta ya bi ya na nasa kukan, duk da shi ba wani wayi gareshi ba, shi dai ya ga an tafi da Uammansu. Saratu ta share hawayenta tana faɗin.

“Babu komai Zaid, Allah ya bayyanar da gaskiya!”

“Na gode”

Ya faɗi ya na gyaɗa mata kai, tare da juyawa.

“Ammm, baka ji ba”

Tsayawa ya yi tare da juyowa ya na kallonta.

“Maganace akan Rabi, ina zaton duk inda take a yanzu ba za ta wuce Haɗejia ba!”

*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*

RAJA POV.

“Wai ina za ka je?”

Rhoda ta tambaya, a sanda ta shigo ɗakinsa ta tarar da shi ya na haɗa kaya a cikin jakarsa.

Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya furta.

“Haɗejia!”

Trayn hannunta ta aje ta na faɗin.

“Haɗejia?... Me za ka yi a haɗejia?”

Ya zuge duffle bag ɗin da ya saka kayansa kala biyar a ciki, sannan ya juyo ya kalleta.

“Yayar Ammata ta ce min ta na can... Dan haka dole na je nemanta, wata ƙila ma na haɗu da dangin Momma”

Ya faɗi cikin karyayyar murya, Rhoda ta iso gabansa ta dafa kafaɗarsa.

“Kada ka damu Zaid.... Za mu samota, and ina so mu je tare”

Kansa ya girgiza mata.

“No Rhoda, ban sani ba ma ko za ta amince da ni, sanin kanki ne fishi take da ni, ba na san abubuwa su ƙara cakuɗewa”

Rhoda ta girgiza masa kai.

“Tun bayan da muka san juna komai tare muke, dan haka wannan ma tare za mu yi, ko wani ƙalu bale tare muka fuskance shi, shi ya sa ba zan barka kai kaɗai ba”

Kallonta kawai ya ci gaba da yi, kafin ya ɗaga kafaɗarsa ya na sunkuyar da kansa ƙasa.

“But dole ki sauya yanayin shigarki...”

Jikinta ta kalla ta na dariya.

“Wannan ba damuwa ba ne Dude, hatta da sunana sai na manta da shi indai a kanka ne, ballantana ma da na kusa dena saka irin waɗanan kayan, na kusa musulunta fa!”

Maganar tata ta tuna masa da zagayen halin da suke ciki gaba ɗaya, ta tuna masa da bincinken da suke kan waɗanda suka yi wa Rabi'a fyaɗe, ta sa ya tuna case ɗinsu da Alhaji Bala.

“So yanzu ka san address ɗin gidan da za mu je?”

Kansa ya gyaɗa ya na ɗaukewa jakar.

“Saratu have told me everything a kan gidan... But a mota za mu tafi, babu jirgin da zai je kano a gobe da safe, shi ya sa zamu tafi da motar”

*Magic Land, Abuja.*

YUSHAL POV.

Ticket suka fara siya, kafin suka shiga ciki, ko wani kalar game Mishal ta ga ni sai ta ce sai sun buga, kuma idan sun buga ɗin ita take cinyewa, don shi bai iya ba, ita kuwa babu wanda bata sani ba. Lilo ma babu kalar wanda bata hau ba, Kuliya kam guda ɗaya ya gwada hawa, bai sauƙo ba sai da hajijiya, hakan ta sa yace ba zai sake hawa ba.

Sai da ta buga wasanni sosai, kafin suka siyi ice-cream suka samu wasu kujeru can daga baya, suka zauna suna sha.

“Ki bi ice-cream ɗin nan a hankali fa Teddy Bear, saboda mura”

Kuliya ya faɗi ya na kallonta, ganin yanda take shan ice-cream ɗin kamar wani abinci.

“Babu fa abun da zai yi”

Ta faɗi da ice-cream ɗi a bakinta,  Kuliya ya girgiza kansa ya na ɗaga wayarsa, saboda kiran da Sharon dake shigowa wayar.

Ya ɗan jima ya na wayar, kafin wayar tasa ta ƙare, juyowa ya yi ya kalli Mishal. Wadda ta gama shan ice-cream ɗin tana ta kalle-kalle a wurin.

“Kin gama?”

Ya tambaya ya na miƙewa tsaye, tare da ɗaga kafaɗarsa ta dama. Ita ma sai ta miƙe tana turo baki.

“ummm”

Hannunsa ya kai ya gyara mata zaman gyalen kanta, sannan ya saka hannunsa a aljihu ya zaro wani hanki, ya na faɗin.

“Ji bi yanda kika ɓata bakinki”

Ya faɗi ya na goge mata bakin.

Kafin ya jata suka bar wurin, asbitin da aka saba mata wankin haƙori suka je, aka mata wankin haƙorin, kafin suka wuce Jabi mall.

Siyyaya suka yi sosai, kuma duk kayan wasa sun fi yawa a ciki, don da ma tace ta bar nata a gida. Kuma daga nan Gidan Anna suka wuce, nan ma sun jima,dan sai dare suka bar gidan.

*Anyone can tell you that they love you, but it takes an authentic soul to show you that they so*

***

RAJA POV.

Da misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa cikin garin haɗejia, bayan doguwar tafiyar da suka kwashe a mota, kasancewar unguwar Jama'aren da aka musu kwatance, ta na a farkon gari ne, kuma su ta kano road suka shigo garin, ya sa ba tare da sun shiga cikin gari ba kai tsaye suka shiga cikin unguwar.

Bayan ɗan neman gidan da suka yi, Allah ya sa suka samu, a bakin ƙofar babban gate ɗin gidan suka yi parking, a tare suka fito shi da Rhoda, wadda ke sanye da wata purple abaya, ta tsefe wannan kalbar attachment ɗin kanta nata da ta saba yi, ta dawo musulma sak. Sai de abub da ba'a rasa ba. Don har zuwa yanzu akwai ɗan wannan guntun baƙin kafircin tare da ita.

Raja ya tsaya ya na kallon gate ɗin gidan, gidan da mahaifiyarsa ta barshi da cikinsu, gidan da aka kori mahaifiyarsu daga cikinsa, kuma gidan da muradin ransa ke ciki a yanzu.

Taku biyu kawai suka yi da niyyar nufar cikin gidan, cak suka tsaya, sakamakon ƙaton gate ɗin gidan da aka wangale, hakan yabsa suka tsaya suna kallon wanda zai fito, wasu magidanta ne guda biyu suke tafe a tare, ɗaya ne yake wa ɗaya magana, yayin da ɗayan kuma ya tsaya sauraronsa.

Raja ya daskare a wurin ya na kallon ɗaya daga cikinsu, wanda fuskarsa take sak, ta Momma, Mommansu dai. Kuma suma magidantan sai a lokacin suka kula da su.

Sakan ɗaya... Biyu... Uku...

*

Durƙushe suke shi da Rhoda a gaban tarin manyan mazajen gidan, a ɗazun iyaka mutum biyu kawai ya gani, yanzu kuwa kusan su goma sha ne yake durƙushe gabansu, 'yan uwansa, 'yan uwan Momma, kuma ba ma su kaɗai ba, harda wani farin tsoho, wanda yake da tabbacin shi ne mahaifin Momma, shi ne mutumin da ya kori Momma saboda ƙaddarar samun cikinsu da ta faɗa mata.

Ɗaya daga cikin mutum viyun da suka ga a ɗqzu ne ya yi gyaran murya yana dubansu.

“Ɗan samari meke tafe da ku?”

Dammm, gaban Raja ya buga, amma sai ya kame kansa yan na ɗagowa da lumsassun idanuwansa tare da zuba su a kan mutanen falon baki ɗaya.

“Sunana Zaid, kuma ni ne manemin auren Rabi'a, a can garin Suleja!...”

Ya zaɓi da ya zaftara musu wannan kantamemiyar ƙaryar, ko ya samu abun da ke masa nauyi a ƙirji ya sauƙa, dan a tashin farko bai isa ya kallesu yace musu shi ne ɗan Rabi'ar da suka kora shekaru talatin da bakwai baya ba, gwara su je a hakan, idan su sun gano da kansu shi kuma sai ya musu bayani.

Alhaji Ali ya gyara zamansa ya na ci gaba da ƙarewa yaron kallo, tun a kallon farko da ya masa ya tabbatar da cewa shi jininsa ne, jinin nasa ma wanda ya fito daga tsatson Rabi'a 'yarsa, zarginsa ya ƙara tabbata ne a sanda ya furta sunansa 'Zaid!' haka aka ce musu shi ne sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan da Rabi'ar ta haifa.

Ya yi zaton yaron ya zo ne dan neman ahalinsa, sai kuma ya ji wani zance da ban, kenan ita Rabi'an har saurayi gareta a garin Sulejan?, amma kuma ya kamata ko ita Rabi'an da ta ganshi ta gane cewa shi jinin gidansu ne,domin kuwa ko ita kanta Rabi'an ta na kama da shi, amma to me yake faruwa haka?. Kuma ba shi kaɗai ne wannan tunanin ke  yawo a cikin kansa ba, kusan kowa na wurin irin tunani da mamakin da yake kenan.

“Yaro!”

Tsoho Alhaji Ali ya furta, hakan ya sa hankalin kowa ya dawo kansa. Ciki kuwa har da Raja.

“Shin ita Rabi'an tana sanka?”

Kafin Alhaji yace komai Kawu Abdullahi ya riga shi furta hakan. Raja ya haɗiye wani abu me ɗaci, duk da ya san abun da zai furta ɗin ba ƙarya ba ne, saboda ya san cewa Rabi'a tana sonsa, amma bai sani ba ko har yanzu akwai wannan son.

“Eh... Muna son juna, kuma mun dai-daita junanmu, wannan tsautsayin da ya gifta ne ya sa ba ma tare, kuma ni sam ban sani yaushe ta dawo nan ba”

Wani irin shiru ya ƙara ratsa falon, kafin Tsoho Alhaji Ali ya samu damar furta abun da ke bakinsa.

“Yaro kai jini na ne?!”

Ba Rajan da aka wurgowa tambayar kaɗai ba, tambayar ta doka wata uw*r ƙara a ƙirjin kowannensu, duk da kowa a cikinsu ya na zargin hakan. Raja ya lumshe idonsa sannan ya buɗe.

“Ka ga... Ka... Ka yi haƙuri... Ka san Halin tsufa”

Cewar Kawu Muktar cikin sigar bada haƙuri, ba don shi ma ba ya zargin hakan ba, sai dan ganin kamar yaron bai so tambayar ba. A hankali Raja ya girgiza kansa.

“Ba kuskure ya yi ba.... Ni jininsa ne!”

Ido waje kowa yake kallonsa, ba don sun yi mamakin kasancerwasa jininsu ba, sai mamakin yanda ya amsa kansa tsaye.

Ƙwalla ta zubo daga idon tsoho Alhaji Ali.

“Yanzu kai jinin Rabi'a ne?”

Raja ya ɗago da kansa ya kalleshi.

“Eh... Ni ɗanta ne”

“Amma an ce ku biyu ne... Ina ɗan uwan naka?”

Wannan karon Kawu munzali ƙanin Alhaji Ali ne ya wurgo masa tambayar.

“Eh... Mu biyu ne, kafin ƙaddara ta zo ta raba mu...”

Tun daga yanda suka yi rayuwa a gidansu su uku, zuwa lokacin rasuwar Rabi'a, zuwa lokacin da suka sha wahalar rayuwa su biyu, da yanda suka rabu da Aliyu, da kuma yanda ya koma wurin Maman Rhoda, har zuwa sanda ta rasu, da kuma yanda ya riƙe Rhodan har wa yau, da aikinsa bai ɓoye musu komai ba, ya sanar da su komai a kansa.

“Innallilahi wa inna ilaihi raji'un... Yanzu jinina ne ya rayu irin haka?... Jinin gidan nan ne ya yi bara a kan titi?... Ka yi haƙuri yaro, ka yafemin... Ni ma ina da hannu cikin lalacewar rayuwarku... Da ban kori Rabi'a ba da duk hakan ba ta faru ba, na yi nadama. Na yi nadama Wallahi. Rasuwar Rabi'a da shekara ɗaya Allah ya ganar da ni gaskiya, sakamakon irin nasihar da yayansu ke min, hakan ta sa na tambayi ita kakar taku, ta sanar min da inda zan samu Rabi'a, na je, amma ban samu kowa ba, sai ce min aka yi wai ta rasu a gobara, sannan kuma an wayi gari babu wanda ya san inda kuke”

Raja ya girgiza kansa ya na kallo tsohon.

“Babu komai Baba, ƙaddarar mu ce a haka, Allah ne ya hukunta faruwar duka lamuran nan, ko da ka kori Momma ko ba ka koreta ba, idan har Allah ya hukunta za mu sha wahala dole mu sha”

Tsoho Alhaji Ali ya miƙawa Raja hannu ya na hawaye.

“Zo nan jikana, zo... Ta ho gareni”

Raja ya miƙe daga inda yake, ya ƙarasa gabansa, Alhaji Ali ya rungume shi ya na kuka, duk taurin zuciya irin ta Raja sai da ta karye, shi ma ya yi hawaye, ɗaya bayan ɗaya ya Alhaji Ali ya shiga gabatar da shi ga mutanen dake falon, kafin Alhaji Alin yace.

“Yanzu kai da gaske kuna soyyaya da ita me sunan mamar taku?”

Raja ya ɗan yi murmushi ya na goge hawayensa, tare da gyaɗa kai.

“Eh, muna son junan mu”

“Allah me iko, Allah buwayi gagara misali, kun ga ƙaddara ko?. Saboda soyyayar da iyayenku ke wa juna ya sa ita mahaifiyar Rabin ta wa Mamarku me suna, ashe da rabon za ku haɗa kanku har alaƙarku ta kai ga aure”

“Yanzu ita wannan ita ce yarinyar da mamarta ta riƙeka?”

Kawu Munzali ya tambaya ya na kallon Rhoda dake gefe tana nata hawayen, dan ita ma ta tuna nata dangin. Raja ya gyaɗa kansa.

“Eh ita ce, sunanta Rhoda”

“Iko sai Allah, har yanzu ba ta musulunta ba kenan?”

Ɗaya daga cikin iyayen me sunan Mamman ya tambaya.

“Eh... Amma za ta musulunta nan ba da jimawa ba”

“Zo nan 'yata, kema ai kin zama 'yar gida”

RABI'A POV.

Kamar kullum suna zaune a falon Hajiya suna hira, yayin da ita take gefe tana daddana sabuwar wayar da kawu Abdullahi ya mata kyautar ta yau ɗin nan da safe, duka 'yan matan na nan, sai hayaniyarsu suke, kuma bayan su ɗin ma har da yayunsu, waɗanda suka girme musu.

“Kai jama'a, kun ji labarin abun da yake faruwa a waje kuwa?”

Gaba ɗayansu suka zubawa Hafiza ido, wadda ta shigo tana ta wannan batu, ita Hafizan ba sa'ar su Rabi ba ce, don ta ma girmewa Baby, ƙawar su Shafa yayar Nafisa ce, kuma ita ce BBCn gidan, ko wani sabon labari a bakinta za ka tsince shi.

“Faɗa mana mu ji ta gidana”

Shafa wadda ke kishingiɗe a kan kujera ta faɗi tana miƙewa zaune.

“Wai ɗan gidan Gwaggon mu ne ya zo!”

Cike da rashin fahimta kowa yake kallonta.

“Wata gwaggon namu?”

Momi ta tambaya.

“Ke Rabi 'yan biyun Mamanku, me sunanki nake nufi”

Ba shiri Rabi ta miƙe zaune tana kallonta, ɗan gidan me sunanta?, Zaid ne ya zo?, ko de ɗayan ne ya zo?, amma ta ina suka san nan ɗin?, kuma wata ƙila ma Raja ne ya biyo ta?...

Kuma tunanin nata bai yi wani nisa ba, zarginta ya tabbata, a sanda Hafizan tace.

“Kuma ma ni a yanda na ji, haka aka ce wai saurayinta ne, tsabar abu irin na yarinyar nan wai ba ta san ɗan uwanta ba ne, kuma fa an ce kamarsu ɗaya da ita”

Dammm!, gaban Rabi ya buga, saurayinta kuma?, haka yace kenan?, duk yadda aka yi ma Raja ne?, Wai shi me ya sa ba zai barta ta hutawa rayuwarta ba ne?.

“A'a fa yaya Hafiza, yaran da aka bamu labarin sun mutu”

Hafiza ta wurgawa Jidda harara.

“Ƙarya zan muku?, kuma ai da aka bamu labarin cewa aka yi sun ɓata, ba sun mutu ba...”

A dai-dai lokacin Hajiya ta fito daga ɗakinta, duk abun da suka faɗi babu wanda ba ta ji ba.

“Me... Me kuka ce... Ɗan Rabi ne ya zo?”

Ko kafin Hafizan da ta buɗe baki ta bata amsa, suka ji sallamar Kawu Abdullahi a ƙofar falon. Miƙewa suka yi a tsaye cikin girmamawa. Bin su ya yi da kallo kafin yace.

“Duka ku bamu wuri, Hajiya tana da baƙo”

Ɗaya bayan ɗaya suka shiga ɓacewa suna silalewa zuwa ɗakin Hajiyan, har zuwa lokacin Hajiya na tsaye tana kallon Kawu Abdullahi. Isowa ya yi gabanta ya na zaunar da ita.

“Ina zuwa Hajiya”

Ya faɗi yana fita waje. Jim kaɗan sai ga shi ya dawo, bayansa biye da Alhaji Ali da kuma ƙannen Kawu Abdullahin guda biyu, sai kuma wani saurayi guda ɗaya biye da su, wani saurayi me kama da 'ya'yanta 'yan biyu, wani saurayi me kaka da jikarta ɗaya. Har matashin ya shigo ya zauna kusa da ita idonta a kansa.

“Kin ga ikon Allah ko Hajiya?”

Ta juyo ta kalli Kawu Abdullahi kafin ta ƙara juyowa ta kalli matashin, kuma a lokacin ne Rhoda ta shigo ta zauna daga can nesa da su.

Hawaye ya zubo daga idon Hajiya, hannunta na karkarwa ta kai ta kama fuskarsa.

“Ji... Jikana!”

Ta ƙarashe tana rungume shi, tare da sakin kuka me sauti. Kafin ta sake shi tana ta dudduba jikinsa.

A hankali Rabi ta saki labulen ɗakin Hajiya, bayan da ta ɗaga shi ta ga jikan Hajiyan da ya zo, a gaskiya ta yi babban kuskure, ta yi kuskure da ta zama sanadiyyar shigowar makashi ahalinsu, amma kuma ba za ta ce ba ta farin cikin ganinsa ba, kuma ba za ta ce ta na  ɓaƙin cikin zuwansa ba, kawai dai halinsa ne yake ba ta tsoro.

“Kun ga tabbaci, Wallahi haka yace shi saurayinta ne”

Hafiza ta ƙara faɗi tana kallon bayan Rabi, Rabi ta juyo ta kallesu, su ma kuma su duka ita suke kallo.

“Wai da gaske ne Rabi?” Cewar Kairiyya.

Ta kasa cewa a'a, ta kuma kasa cewa eh, kawai ta ci gaba da tsayuwa a wurin, hannunta riƙe da wayarta.

“Ni bari ma na leƙa na ganshi”

Cewar Hafizan ta na miƙewa, leƙawar ta yi, Allah ya sa ta ga fuskarsa kuwa.

“Ikon Allah, wai kin ga kamar da yake da ita kuwa?”

Haka suka riƙa tasowa ɗaya bayan ɗaya suna leƙawa, sai mamaki suke ta yi, yayin da Rabi ta koma gefe tana karanta wasiƙar jaki.

Kawu Abdullahi ne ya lura da su, hakan ta sa ya yi gyaran murya, bayan da ya gama bawa Hajiya labarin da Zaid ɗin ya basu.

“Leƙen kuma na miye, ai za ku iya fitowa ku ganshi”

Da gudu Fati da Kairiyya suka koma ɗakin cike da jin kunya.

“Ko ba ku ji ba ne?!. Ku fito ku gaisa da yayan ku!”

Ɗaya bayan ɗaya suka shiga fito suna gaisawa da Zaid, amma fur Rabi ta ƙi fitowa. Ba za ta iya fitowa ta haɗa ido da shi ba, gwara ta zauna a ɗakin zai fi mata sauƙi.

Ta na cikin saƙe-saƙen nata ne Rhoda ta buɗo ƙofar ɗakin ta shigo, kanta ta ɗaga suka haɗa ido, da sauri ta miƙe ta isa gaban Rhoda suka rungume juna, duk yanda za ta kai da fushi da Raja ba za ta yi da Rhoda ba, don kuwa ita ba ta taɓa ganin aibunta ba.

“Ya kike Rabi'a?”

Cewar Rhidan ta na sakin Rabi, Rabi ta gyaɗa kanta cikin faɗin.

“Ina cikin ƙoshin Lafiya”

“Ashe ma kun san juna?”

Jidda da ta biyo bayan Rhoda ta faɗa ta na dubansu. Rabi ta gyaɗa kai.

“To kawu yace tare za mu kwana da ita, su sun fice, sai ki zo mu koma ɓangarenmu, dan su fati sun wuce”

Ba tace komai ba ta kama hannun Rhodan suka raɓa Jidda suka fice.

*

“Ga su nan, suma 'yan uwanka ne, sai ku kwana tare zuwa gobe...”

Cewar Kawu Abdullahi, a lokacin da yake sada Zaid da samarin gidan waɗanda ba su yi aure ba, su huɗu ne cas, Muhammad, Sani, Auwal da Zakar. Raja ya kallesu ya na gyaɗa kansa. A sanda ko wannensu yake gabatar masa da kansa, ɗaya bayan ya ya basu hannu suka gaisa, kafin suka nuna masa shimfiɗa in da zai kwanta, bai kwanta ɗin ba sai kawai ya zauna ya na saƙe-saƙe kala-kala a ransa.

*

“Rabi!”

Rabi ta juya ta kalli Jidda da ta kira sunanta, ta na zaune ne a bakin gadonta, lokacin kusan ƙarfe sha ɗaya, amma Rabin bata samu rintsawa ba, tunani ya hanata ta yi bacci.

Jidda ta taso daga kan nata gadon ta dawo ta zauna a bakin gadon Rabi ta na dubanta.

“Me yake damunki?”

Rabi ta kawar da kanta tana furzar da iska.

“Babu komai”

“A'a Rabi, duk yadda aka yi da komai. babu komai ba za ki zauna kina tunani ba. Kuma na lura da tun zuwan wannan Zaid ɗin yanayin ki ya sauya”

Rabi ta sunkuyar da kanta tana kallon yatsun hannunta, amma ba ta ce komai ba.

“Menene yake faruwa?. Ko bakya sonsa kamar yanda Hafiza tace?”

Rabi ta yi saurin girgiza kanta tana faɗin.

“A'a, ba haka ba ne. Ina sonsa, kawai de wata matsalar ce da ban”

Jidda ta gyaɗa kanta tana dafa kafaɗarta.

“Na gane, to Allah ya kawo miki mafita, ke de kawai ki yi addu'a... Kin ji?”

Sai ta gyaɗa kanta kawai. Jidda ta ƙara dafa kafaɗarta, sannan ta miƙe ta koma gadonta.

Rhoda dake kwance a gefen gadon Rabi ta yi murmushi ta na gyara kwanciyarta.



Post a Comment

0 Comments