TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 23

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*23*

~~~

*The one thing that holds more power than ‘I love you’, is ‘I got you’...*

***

*No.86, Garki 2, Abuja...*

*09:00 PM.*

RABI POV.

A hankali ta zura ƙafarta ta dama cikin kitchen ɗin gidan, sai kuma ta tsaya ta na kallon irin yawan kayan dake cikin falon, sai da ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, kafin ta sako ƙafarta ta hagu ciki. Kamar sauran sassan gidan, shi ma kitchen ɗin ya haɗu. 

A jiya danginta, wato 'yan uwan mahaifiyarta suka rakota har ɗakin mijinta, kuma a nan suka kwana, ba su tafi ba sai ɗazu da yamma, sun tafi sun barta cikin wannan gidan, bayan da suka mata nasihu kala-kala, sai de kuma ita ba ta jin ko nasiha ɗaya cikin nasihunsu zai yi aiki, don kuwa ba ta jin za su yi wani dogon zama ita da Zaid. Kowa a familynsu burinsa kawai ayi auren, to gashi an yi, ita kuma za ta san yanda za ta yi dan ya saketa, da ta ci gaba da zama da makashi, gwara ta koma can Haɗejian ta ci gaba da zama, . Duk da tasan cewa zuciyarta ba za ta so hakan ba, amma za ta haƙurƙurtar da ita, ta faɗa mata cewar zamanta da Zaid ba zai haifar da ɗa me ido ba.

Motsi ta ji a bayanta a lokacin da ta kai tsakiyar kitchen ɗin, da sauri ta juya ta na kallon bakin ƙofar kitchen ɗin, ganin Zaid tsaye a wurin kuma jingine da jikin ƙofa ya sa ta shiga dube-dube a kitchen ɗin, can ta hango set din wuƙa, ba tare da sake wata shawara da zuciyarta ba, ta rarumo wuƙa ɗaya daga cikin set ɗin, ta nuna shi da ita ido waje.

“Kada ka shigo nan!”

Raja na kallonta ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, hannyensa harɗe a ƙirjinsa, sai murmushi yake zabgawa, don shi a yanzu babu wani abu dake damun ransa, komai nasa ya hau seti, rayuwar ma sai ya ga kamar tana sauri ne. Wai yau Ammatansa ce a cikin gidansa, matsayin matarsa ta aure, halalinsa!. Duk barazanar da za ta masa ba za ta dame shi ba, don shi bai fara santa don ya bari ba, bai aureta don ya saketa ba, ya aureta ne don ya zauna da ita har zuwa ɗan lokacin da Allah ya ɗiba masa cikin duniya. Hannayensa ya ware, tare da zuba su cikin aljihun wandonsa, ya soma takawa zuwa gabanta.

Ganin hakan ya ƙarawa Rabi ƙaimi wurin ci gaba da cuna masa wuƙar a setinsa, sai de kuma ko gezau ba ta ga ya na yi ba, nufota yake gadan-gadan, har ya iso gabanta ba ta bar nuna shi da wuƙar ba, sai zare masa ido take kamar za su faɗo, kuma bai dena tahowa gareta ba har saida ya riski wuƙar, har tana taɓa jikinsa.

Da sauri Rabi ta janye wuƙar zuwa gefe, ba shiri ta cillar da ita can gefe ta na ƙara matsawa baya, shi ma kuma be fasa ba, binta yake ta na ja da baya, har sai da Rabi ta kai jikin wata cabinet.

“Ai ni na san ba za ki iya cutar da ni ba”

Ya faɗa yana kafeta da idanuwansa. Rabi'a ta haɗiye wani abu ta na kawar da kanta gefe, kuma ita kanta ta san gaskiya ya faɗa, ba za ta iya cutar da shi ba sam, ko me zai mata ita ba za ta iya masa koman ba. Amma saboda ƙarfin hali irin nata sai cewa ta yi:

“Me zai hana ba zan cutar da kai ba. Idan ta kama har kasheka ma sai na yi...”

Tana iya jin sautin murmushinsa. Raja ya fitar da duka hannayensa daga cikin aljihu, sannan ya mata rumfa a tsakiyarsu, ya ƙara matsar da fuskarsa kusa da tata dake kallon gefe.

“Ba za ki iya ko da cire silin gashi ɗaya daga jikina ba. Saboda... Kina... Sona, ki yarda kawai. Ko ki yarda ko karki yarda Ammatan Raja... You love Raja... Oh i mean Zaid... Yaya Zaid!”

Ba shiri Rabi'a ta ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, ta rintse idonta gam-gam, ta shiga kokawa da numfashinta dake shirin fita gaba ɗaya, hannunta dake kan rigar jikinta ta damƙeshi tare da rigar.

“You see... Magana ma kawai na miki ta sa kika shiga cikin wannan halin. Ina ga idan na...”

Ba tare da ya ƙarashe ba ya sauƙe hannunsa na dama, sannan ha sako shi ta bayanta, yana turota zuwa jikinsa, hakan ya sa Rabi ƙara ƙanƙame idonta, dan haɗuwar jikunansu sai ya sa ta ji kamar wani irin electric shock ne ya faru tsakaninsu. Kuma hakan be isheshi ya gama wargaza tunaninta ba, sai da ya sauƙe ɗayan hannun nasa ya kama gefen fuskarta da shi. Ya na ƙara kusanta fuskarsa da tata. Allah ne ya ara mata ƙarfin da ta yi amfani da shi wurin turashi zuwa baya.

“Dan Allah ka rabu da ni. Ni ba na buƙatarka a rayuwata, tun ba yau ba na faɗa maka haɗuwata da kai kuskure ne, ka ƙyaleni Zaid, dan Allah ka ƙyaleni!”

Ta ƙarashe hawaye na sauƙo mata.

“Ni kuma ina buƙatarki a rayuwata, ina sonki. Ina.... Matuƙar sonki, dan Allah ki fahimta”

Rabi'a ta share hawayen idonta, sannan a dake tace.

“A haka kake so na? Ni fa ba kamar sauran mata ba ce!. Ina da banbanci da su. Maza biyar... Biyar ne suka haikemin... A haka kake sona?... To ka sani ni ba ni da wannan martabar ta 'ya mace... Ban mallaki komai ba sai raina, idan ka ce za ka ci gaba da kusanta tata irin haka ina me tabbatar maka da cewar ran nawa ma zan rasa shi nan ba da jimawa ba!” Ta faɗi hakan ne don ta tunzurashi ya rabu da ita, kuma ta na ganin kamar ya manta abun da ya faru da ita ne, don da ace ya na tunawa da ba zai aureta a yadda take ba, shi ya sa ta yi ƙoƙarin tunatar da shi.

Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na shafa sumar kansa, me take so yace ne? Wata hanya zai bi don ya ganar da ita kalar san da yake mata?, da wani yare take so ya yi magana dan ta fahimci kalar son da yake mata?, tun kafin tsautsayin nan ya auku yake santa, yanzu kuma kawai dan ƙaddara ta sameta sai ya rabu da ita?, wannan ba me iyuwa ba ne, santa a cikin jikinsa yake, ba ya jin zai iya rabuwa da santa ko me za ta zama a duniya, kuma ya na fatan bugu na ƙarshe da zuciyarsa za ta yi ya kasance da sunanta ne. Lips ɗinsa ya lasa ya na sakin sumar kansa da ya riƙe.

“Ammata, ni...”

Ya nuna kansa, sannan ya ci gaba.

“Ba dan komai nake sanki ba.  Ba na sanki dan kina da wani abu. Bana sanki dan kin mallaki wani abu. Haka kuma ba na sanki dan ina buƙatar ki wadata ni da wani abu. Zuciyarki kawai nake buƙata Adawiyya!. Da zarar kin mallakamin ita zan nuna miki so. Zan nuna miki yanda ake so. Zan koyar dake so. Zan nuna miki yanda ƙaryyayar zuciya, kan haɗe ta dawo me kyau fiye da sabuwa. Zan tabbatar da na ƙawata duniyarki Ammata. Ko da sau ɗaya ne. Dan Allah, ki gwada ni... Ki gwada mallakamin zuciyarki ki ga kamun ludayina. Na roƙeki, Please!”

Rabi ta buɗe idanunwata dake a lumshe ƙwalla wata na bin wata. Idon nata ta sauƙe a kan Raja dake durƙushe kan gwiwoyinsa a gabanta, ya na roƙonta abun da za ta iya mallaka masa cikin sauƙi. Ya Allah! Me ya sa wai ita nata ƙaddarorin basu da sauƙi ne?. Ta san da cewa soyyayar Zaid na ɗaya daga cikin ƙaddarorinta na duniya, wannan haka yake, kuma a rubuce yake.

Durƙusawar ita ma ta yi a gabansa ta na kallon idanuwansa.

“Raj ni ba ni da wani abu da zan baka. Fanko!.... Fanko ce ni, na zama wata kala, saboda kwai ƙaddara ta faɗa min. Ƙaddarar da ba ni na tsrawa kaina ba, ƙaddara ce fa Raj, ƙaddara ce, amma haka Yaya ya guje ni saboda wannan ƙaddarar da ban jarabci kaina da ita ba. kuma na san ko ba Yaya ba babu wanda zai iya aurena a yadda nake, kai ma kawai de ka dage ne. Amma ni da kai ba mu dace ba...”

Kafin ta kai ƙarshen kalaminta, Zaid ya saka hannyensa duka biyu ya janyota cikin jikinsa, tare da haɗe bakinsa da nata, ƙwalla me ɗumi na sauƙa daga idon ko wannensu, Rabi'a ta kama bayan rigarsa gam, dan ji take kamar za ta zame daga hannayensa, kamar ƙasa ce za ta tsage biyu, ita kuma ta rufta ciki.

A hankali  Zaid ya saki bakinta ya na rungumeta, tare da shafa sumar kanta dake cikin ɗankwali.

“I adore you Adawiyya, i na sanki ko da ba kya gani. Ina sanki ko da ba ki da ƙafafu. Ina sanki ko da ba ki da hannaye. Adawiyya ko da mutuwa kika yi ba zan dena sanki ba... I love all of you!”

Kalamansa ba ƙaramin tasiri suka yi a zuciyar Rabi ba, don tsabar tasirin da suka yi, Rabi'a ba ta san sanda ta ɗago da hannyenta ta ɗora su a kan bayan Zaid ba, ta na ƙara ƙanƙameshi a cikin jikinta, tare da ƙarawa kukanta sauti.

Sai de kuma cikin sakan ɗaya... Biyu... Uku...

A cikin na ukun ta yi sauri ta tureshi, saboda wannan fuskar tasa da ta hango, fuskarsa a lokacin da ya harbi wani bawan Allah. Da sauri ta miƙe da gudu ta bar kitchen ɗin. Ɗakin da yake a matsayin nata ta faɗa tana bankowa ƙofar. Tare da jingina a jikin ƙofa, ta silale ƙasa tana fashewa da kukan da ba ta san daga ina yake fitowa ba, ƙafafunta ta takure a jikinta tana sunkuyar da kanta cikin kuka. Ita da Allah zai ɗau ranta ma da sai abun ya fi mata sauƙi, ƙaddarorinta suna da tsauri, ga su kuma a laye, wata kan wata.

Har ta bar kitchen ɗin kan Raja a sunkuye yake, da ƙyar ya samu ya ja da baya zuwa jikin cabinet, ya jingina da ita, sai sauƙe numfashi yake da sauri-sauri. Zai iya cewa a karo na farko kenan a rayuwarsa da ya yi nadamar shiga aikin DSS, wai me ya sa?, me ya sa komai nasa akan soyyayar Adawiyya yake da wahala haka?, ya tabbatar ba dan wannan aikin ba, da ba za ta ganshi ya harbi wani ba, da ba za ta ƙishi tana masa kallon makashi kamar haka ba. Duk sai ma ya ji ya tsani rayuwar, ji yake kamar kansa na tiriri. Cike da fusata ya ɗaga hannunsa na dama ya na dukan cabinet din dake bayansa. Ya gaji, dole ne ya ƙarƙare aikin nan cikin wannan satin, dole ya kawo ƙarshen komai.

*

Rabi'a na zaune a falo tana kallo. Jin wani sauti me kama da ƙaran kiran waya ya sa ta juyo ta kalli ƙofar ɗakin Zaid. Mamaki ne ya kamata a sanda ta fahimci cewa tabbas, sautin kiran waya ne ke tashi daga ɗakin, to be fita ba ne ko kuwa?, ita de ta san sassafe ya fice daga gidan, amma kuma yanzu ga ƙaran  kiran waya ta na ji, duk yadda aka yi manta wayar ya yi.

Bakinta ta taɓe tare da juyowa ta ci gaba da kallonta, jin sautin kiran wayar na ƙara tashi ya sa ta ƙara waigowa ta kalli ƙofar ɗakin nasa. Ko de wani abu ne yake faru? Ta tambayi kanta a sanda take miƙewa. Ɗakin ta nufa. Sai de bisa ga mamakinta ba ta ga wani abu mekama da waya a ɗakin ba.

Har ta juya za ta fita, ƙaran kiran wayar ya ƙara dakatar da ita, hakan ya sa ta juyo ta shiga bin inda sautin ke fita. Can cikin loka ta ji sautin, don haka ta buɗe lokar, sai ta yi arba da wata kalar waya da za ta ce bata taɓa ganin irin ta ba.

Har zuwa lokacin wayar na ringing, hannun ta kai ta ɗauki wayar, amma kuma babu lamba bare suna. Gaba ɗaya ta riga ta gama shiga duniyar mamakious, wani irin abu ne haka?. 

Ɗaga kiran ta yi, tare da kara wayar a kunnenta, shiru ta yi ba tare da tace komai ba, kuma daga ɗayan ɓangaren ma sai ta ji shirun, hakan ya sa ta yi ƙoƙarin sauƙe wayar, sai kuma ta tsinto wani ɓangare na Zaid, wani ɓangare na gaskiyar sa da take tutiyar ta sani, wani ɓangarensa da ɗai-ɗaiku ne cikin mutane kawai suka sani.

“...Lion, umarni ya zo daga sama, duk yanda za ka yi ka yi don ka kawo ƙarshen wannan aikin, oga yace ba zai iya jira sama da haka ba, saboda haka sai ka san yadda za ka yi dan ka miƙo duka hujjojjin da ka haɗa!...”

*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*

ZAID POV.

Zaune yake a kan kujera ya na facing Rhoda, wadda ke daddana system ɗin dake kan cinyarta, hankalinsa rabi na kanta rabi kuma na ga wayar da yake ta jira, dan kuwa a jiya ya aikawa da office ɗinsu saƙon yana san magana da ogansu, ya san da cewa a yau ɗinnan za su kira, amma kuma ba zai iya jure zaman gidan suna cikin wannan halin shi da Adawiyya ba, ba zai iya zama a gidan ta na gudunsa ba, gwara ya ba ta space, ko ta samu damar sararawa a gidan, ina yado bayan ya koma sai ya amsa kiran.

“Dude!... Zo ka gani!”

Cewar Rhoda, mamaki mamaye da fuskarta, idonta kyar a kan system ɗin gabanta. Da sauri Raja ya miƙe ya dawo gefenta ya na kallon system ɗin.

A jiya suka samo putage na CCTV camera ɗin dake layin da aka cillar da Adawiyya bayan da aka haike mata, ba ƙaramar wahala suka sha ba kafin suka samu putage ɗin, sannan kuma suna da tabbacin putage din shi ne zai kaisu ga karshen binciken da suka fara.

A tare suka juyo suna kallon juna shi da Rhoda, bayan da vedion ya kai ƙarshe.

“Usman?!”

Rhoda ta tambaya tana dubansa. Nan take idon Raja ya kaɗa ya yi ja, babu abun da Rhoda ke iya hangowa sai wutar masifa da tashin hankalin dake ci a cikinsu.

“Ba zan barsu ba!...”

Ya faɗi ya na miƙewa, da sauri Rhoda ta kamo hannunsa tana maida shi inda ya miƙe. Kai ta shiga girgiza masa alamin a'a.

“Zuwa yanzu case ɗin ya zama biyu Zaid... Ka fara miƙa hujjojji game da Alhaji Bala tukunna, idan an bamu izinin kamu, sai mu haɗa mu kamasu su duka!”

Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga ya na cije leɓensa na ƙasa.

“Kin tabbatar da haka ya kamata a yi?”

Rhoda ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa.

*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.*

Habiba ce zaune a tsakar gida ta na dunduma jikinta da ruwan ɗumi, kwana uku kenan da aka sakota daga hannun 'yan sanda, kuma dukan da ta ci a hannunsa ne har yanzu be bar jikinta ba, dan ta doku ba ƙarya. Ita ta yi ma mamaki da suka sakota da wuri haka, duk da shi Ɗan Lami ma ko kwana be yi a wurinsu ba.

Sallamar Saratu ta ji daga bakin ƙofa, hakan ya sa ta juya ta na kallonta. 

“Sannu Umma... jikin ne?”

Habiba ta gyaɗa kai tana matsa ƙafarta.

“Amarsu kenan, daga ina kike ne?”

Habiban ta tambaya kamar ba ita ba, a sanda Saratun ta karɓi ƙyallen hannunta ta shiga dunduma mata jikin nata. Saratu ta yi murmushi.

“Gidan su Farida na je, zuwa gobe za mu fara rabon cingam”

Habiba ta gyaɗa kanta, zuwa yanzu ta fara shiga hankalinta, ta fara gane gaskiya da akasinta, a jiya Saratu ke faɗa mata cewar wai Rabi ta yi aure, kuma wannan me kamar tata ne ya aureta, sai kuma ganin nutsuwar da Ɗan Lami ya fara yi, ita ma ta sa ta shiga taitayinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne, dan kuwa ga shi dai duk wannan abubuwan da ta yi ta yi, ba su hana Rabi auruwa ba, kuma duk wannan makirce-makircen da ta yi ta yi, ba su hana ikon Allah faruwa ba.

Wata sallamar suka ji cikin wata murya me kama da ta Mama, cikin sauri kuma a tare suka kalli ƙofar gidan. Sannan cikin daƙiƙa ɗaya suka miƙe a zabure. Kallonta suke suna san su gane wacece.

“Ni ce Umma, ni ce Mamanki!...”

Cikin kuka Mama take faɗin hakan, tare da sakin jakar hannunta, hannu na karkarwa Habiba ta nuna Maman dake tsaye a gabanta.

“Ma... mama... Mama!”

Tsaye take a gabansu, jikinta ɗauke da cikin da ya fara fitowa, ga wasu ƙuraje da suka bai-baye mata jiki, ta wani kalar rame ta ƙwanjare, ta yi baƙi ƙirin da ita.

Allah kenan, za ka yi ta saɓa masa ya na ara maka dama, rana ɗaya kuma idon  ya tashi kamaka, sai ka gwammaci ba a hallici me kamarka a duniyar nan ba. Domin kuwa shi ya fi kowa iya kamu.

*Don't be afraid to lose people. Be afraid of losing yourself by trying to please anyone around you*

***

*No.86, Garki 2, Abuja...*

RAJA POV.

A hankali ya turo ƙofar shiga falo, bakinsa ɗauke da sallama. Cak ya tsaya, sakamakon ganin Rabi tsaye a tsakiyar falon, hannayenta harɗe a ƙirjinta, ta kafe shi da wani irin kallon tuhuma, duk wata ƙwarin gwiwa da ya zo da ita dan ya mata wasu tambayoyi game da abun da ya faru da ita sai ya ji ya gushe, kallon da take masa yana ƙarasawa ya ji ya muzanta, don ita ba ta kallonsa a matsayinsa miji gareta ko yaya, kallo take masa a matsayin ɗan daba, kuma makashi.

Wani yawu ya haɗiya, sannan ba tare da yace mata komai ba ya ɗauke idonsa a kanta ya shiga ƙoƙarin nufar ɗakinsa. Sai de me?, tsulum ya ganta tsaye a gabansa, ta na ci gaba da kallonsa cike da tuhuma.

“Waye kai?”

Tambayar ta doka wata ƙatuwar ganga me amon gaske a cikin kan Zaid, ya kafeta da idonsa, amma ya kasa ce mata komai.

“Zaid! Waye kai?”

Yawu ya haɗiya ya na faɗin.

“I'm a goon!”

Kanta ta girgiza tana sauƙe hannayenta daga ƙirjinta.

“I mean real you... Waye kai!”

Ta kuma maimaita masa tambayar, hakan ya saka zuciyar Zaid cikin kokwanto, to me take nufi da waye shi?, ko de ta gano wani abu a kansa ne?, ina ba zata gano komai ba. Dan haka ya haɗiye yawu yana faɗin.

“I am a killer and drug trafficker. I'm goon”

Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa, sosai rungumar ta ba shi mamaki, idonsa ya lumshe sannan ya buɗe, kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta sake shi tana kallon fuskarsa.

“Akwai wani rubutu da na taɓa karantawa. A rubutun an ce, idan har ka rungumi mutum na tsawon muntun biyar, to za ka fara yarda da duk abun da zai ce, amma har yanzu ni ban yarda da kai ba. I will ask you for the very last time... Who are you Zaid”

Raja ga haɗiye wani kakkauran miyau me ɗaci, sannan ya lumshe idonsa ya buɗesu a kanta, kana ya amsa mata da:

“Zaid Aliyu... Department of state service (DSS) officer!”

*No.181, Guzape, Abuja...*

MISHAL POV.

“Yaushe za mu je gidan Anna?”

Ta tambaya ta na saka kayan Kuliya da ta wanke yau da safe a cikin loka. Kuliya dake zaune a bakin gado yan danna waya ya kalleta.

“Me ya faru?”

Ya tambaya. Mishal ta girgiza kai ta na saka wata rigar cikin lokar.

“Kawai de ina kewarta ne?”

Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai.

“Nanbda sati ɗaya ne fa Teddy Bear,saurin me kike?”

Ta juya ta na ci gaba da aikinta tare da faɗin.

“Na gaji da zuwa school ne... Kuma mun kusa mu fara exams”

Lokar ta rufe, sannan ta juyo ta iso gareshi.

“Next term za ku fara Neco da Waec right”

“Ummm!”

Ta amsa masa tana karɓar wayar hannunsa.

“Lokacin danna waya ya ƙare, let's fall asleep”

Murmushi ya yi ya ja kamo hannunta, tare da zaunar da ita akan gadon. Wayarsa dake haannunta ya karɓa ya na ajeta kan side drawer. Kwantar da ita ya yi a kan gadon, ya juya ya kashe wutar ɗakin, sannan shi ma ya kwanta ya na karata da jikinsa.

“Abu Aswad?”

Mishal ta kira sunan bayan wani lokaci.

“Ummm!”

Muryar Kuliya ta amsa ƙasa-ƙasa, alamun kamar ma ya fara bacci.

“Yaya batun Anti Adawiyya?”

Tar Kuliya ya buɗe idonsa cikin duhun ɗakin. Jin ta ambato masa sunanta, bayan da ya gama bincike ya gano komai a kanta, ciki kuwa har da fyaɗen da aka mata, sai de kuma baya so ya faɗa mata komai, dan baya so hankalinta ya tashi, shi ya sa bar wa cikinsa maganar, ba tare da ya faɗa mata komai ba.

“Sharon tace zuwa gobe za a iya samo address ɗin gidansu, ki kwantar da hankalinki!”

Ya faɗa mata dan ta kwantar da hankalinta, wata ƙwalla ce ta taru a idon Mishal, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta silalo. Sai jin damshi Kuliya ya yi a gaban rigarsa, kasancewar kanta na kan ƙirjinsa ne. Iska ya furzar daga bakinsa ya na ƙara ƙanƙameta.

“Hafsat?”

“Na'am!”

Ta amsa a raunane.

“Ni fa da kaina na ce miki zan gano miki inda take, babu abun da zai sameta”

Hawayen ta goge da kanta tana gyaɗa kai.

“Umhumm!”

“I love you, maza ki yi baccin ki.....”

“I hate you”

Ta faɗi tana lumshe idonta.

*No.86, Garki 2, Abuja...*

*10:20 PM.*

RABI'A POV.

Tsaye take daga jikin dressing mirrorn ɗakinta, a hankali ta aje wayarta dake riƙe a hannunta, bayan da suka gama waya da Jidda. Juyowar da za ta yi ta ji an buɗe ƙofar ɗakin. Ba shiri zuciyarta ta doka tsallen albarka a ƙirjinta har sau biyu. Dan kuwa ko ba'a faɗa ba, ko ba ta kalla ba, ta san waye, hakan ya sa ba tare da ta ko kalli side ɗin ƙofar ba, ta juya ta ƙara fuskantar mirronrn. 

Allah ya sani, sam bata son su haɗu, ba ta son wani abu ya haɗasu, ta na jin kunyarsa da kuma kunyar kanta da ta yi masa mummunar fahimta, tana ta zarginsa game da abun da sam bai aikata ba, me ya sa zuciyarta ta yarda da abun da idanuwanta suka gani?, me ya sa har take zaton shi zai iya aikata wannan mummunar ta'asar?, kaiconta da ta kasance mace me matuƙar san kai. Satinsu ɗaya da aure, amma fur ba ta yarda su haɗu ko da wasa, kullum za ta yi girki ta aje masa nasa amma ko da kaɗan ba ta bari ya ganta.

Ba za ta iya haɗa ido da shi ba, ta kalli tsabar idonsa tace shi makashi ne, tace za ma ta iya kaksheshi, duk da ba da gaske take ba, amma ai ta faɗa. Tunaninta ya katse a sanda ta ji tsayuwarsa a bayanta. Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa ta cikin mudubin dake gabanta.

Zaid ya ci gaba da kallonta da lumsassun idanuwansa, tun bayan ranar da ya bayyana mata gaskiyar kasancewarsa ma'aikacin DSS suka shiga wasan 'yar ɓuya shi da ita, wata ƙila kunyarsa take ji, wata ƙila kuma ba ta yarda da abun da ya faɗa ba ne. Ko ma de me take tunani a kai, shi de be damu ba, damuwarsa ita ce rashin ganinta, nisantarsa da take ya fi sosa masa rai, shi be ƙi a kullum ya kasance da ita ba, ko da kuwa za su ci gaba da zaman doya damanja ne, dole ne ta sama musu mafita, dan shi kam gaskiya ya gaji da wannan tazarar da suke bawa juna.

“Ammatan Raja!”

Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, ko a da ma ya ake ƙarewa idan ta ji sunan?, bare yanzu da sunan ya samu ƙari a gaba, ‘Ammatan Raja!’ haka yake kiranta. Sai ta kasa amsawa, ta ci gaba da kallonsa ta cikin mirrorn.

Raja ya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya yi taku ɗaya... Biyu.. Wanda ya ƙara kusanta shi da ita, sannan ya ɗaga hannayensa tare da zurasu ta ƙugunta, suka kewayo zuwa cikinta, kafin ya jata baya zuwa jikinsa, ya sunkuyo da kansa zuwa wuyanta.

Ba shiri Rabi ta rintse idonta gam, wai me ya sa?, me ya sa duk yadda zai taɓa jikinta irin haka sai ta ji wani sauyi tare da ita,me ya sa?.

“Na yi lefi ne?... Ko har yanzu ni makashi ne a idonki?”

Ya tambaya muryar ta sa na fita a hankali, Rabi'a za ta iya cewa sai da kalaman suka gama shawagi a kan fatar wuyanta kafin suka isa zuwa ga kunnuwanta, a lokaci guda kuma sai ta ji jikinta ya ɗauki wani irin ɗumi, kamar wata wadda aka kara a jikin kyandir, ko wata ƙofa ta gashi a jikinta ta buɗe. Amma sai ta ture komai ta girgiza masa kai.

Zaid ya saka hannayensa ya na juyowa da ita, ta fuskanceshi, ya sunkuyar da kansa dan samun damar haɗa ido da ita amma fur ta ƙi barin hakan ta faru, don nata idanuwan kulle su ta yi gam.

“Idan de kika ci gaba da yin abun da kike ɗin nan zan ɗauka cewar har yanzu baki yarda da ni ba!”

Da sauri Rabi'a ta buɗe idonta, dan kuwa gwara ta sha kunya da ace ya ɗauka cewar bata yarda da shi ba ne, a yanzu tana jin wani irin girma da kamarsa na ƙara hauhawa a cikin ranta, wani irin kwarjini yake mata, wanda ba za ta iya kwantanta kalarsa ba.

“Trust me Diary... Wallahi gaskiya na faɗa...”

Da sauri Rabi ta ɗago da hannunta ta rufe masa baki tana girgiza masa kai.

“I trust you Raj. And I'm sorry”

Cikin hanzari Zaid ya kai hannunsa ya kamo nata dake kan bakinsa, ya riƙe hannun nata ya na kallon fuskarta da ta fara jiƙewa da hawaye.

“Babu buƙata Ammata, kuskuren fahimta ne”

Rabi ta ja hanci.

“Amma me ya sa to ni na kasa fahimtarka?. Ya kamata ace na fahimceka Raj... I'm sorry... I'm really really sorry...”

Saurin rungumeta Zaid ya yi, hakan ya bata damar sakin kukan dake cin ranta, ta masa kuskure, abun da ta masa sam be kamataba, ta aikata babban kuskure.

“Ka yi haƙuri please!”

Kansa ya ci gaba da girgiza mata yana ƙara ƙanƙameta a cikin jikinsa.

“Wallahi sam ba ki min kuskure ba. A ko da yaushe ni me miki uzuri ne ko da kin yi laifi, bare kuma ba ki aikata komai ba. Ba dan komai ya sa na ɓoye miki ba sai dan yanayin aiki, ina kan wani assignment ne yanzu haka”

Rabi ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tana sakin wani kukan, ba ƙaramin ɗaɗi wannan shauƙin yake da ba, me yafi wannan daɗi a duniya?. Ka kasance a tsakiyar hannun wanda ƙaunarsa ke daddatsa ruhinka a ko da yaushe, wanda shi ma taka ƙaunar ke kai kawo a cikin nasa ruhin. Me ya fishi daɗi?.

Ta jima a jikinsa tana kuka, kafin ya ɗago da ita yana share mata hawaye, a lokacin ta samu damar kallon fuskarsa, dan haka ta ɗaga nata hannayen ita ma, tare da kamo fuskarsa.

“Ban taɓa faɗa maka wannan ba, amma yau zan faɗa. I love you... I love you Raj...”

Da sauri Zaid ya kara fuskarsa kan tata yana sauƙe tagwayan numfashi. Rabi ta lumshe idonta hawaye wani na bin wani.

“You love me Adawiyya?”

Ya tambaya, dan ya kasa gaskata kunnuwansa, he can't believe, wai yau shi Ammata take cewa tana so?, abun is unbelievable. Bakin Rabi tale cikin kuka, idonta a rufe ta gyaɗa masa kai, wanda hakan ya sa nasa kan ma motsawa tare da nata.

“I adore you, i love you...”

“Kwatankwacin yaya?”

“Like damn... Damn much Raj!”

“Alhamdullilah!”

Ya furta yana ɗora lips ɗinsa a kan nata.

“Adawiyya!”

Idonta ta buɗe jikinta na tsuma, saboda yanda ya yi maganar lips ɗinsa na goguwa a kan nata.

“Can i kiss yah?...”

Bai ko ƙarashe ba, ita ta saka hannyenta ta kama fuskarsa, tare da haɗe bakinta da nasa.

Zaid ya saka hannayensa ta bayanta yana ƙara matseta a jikinsa. 




Post a Comment

0 Comments