TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini 17 -- 18

 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️



                           


Narrnarhh Bukar✍️



🌹Perfect Essential Writer's

Association🌹

  ✨ P. E. W. A✨



Wattpad:@AISHAABUBAKAR812

Arewabook:@Narrnarhh002





1⃣7⃣---1⃣8⃣


A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu.


"Mai zan gani ni Hafsy,Musa haka ka koma !!!" cewar Maman Jummalo wacca fitowarta kenan daga ɗaki.


Wa'inda ma basu san da dawowarsa ba kowa ya bisa da kallon ƙurilla,gaskiya dole Maman Jummalo ta ce mai zata gani ita Hafsy,haƙiƙa duk wanda yasan Musa dole yayi mamakin ganinsa haka.


Mutumin da a da baƙi ne sosai yanzu ya koma fari sai kace bature,bancin haka ga wani askin ƴan iska da yayi,an saisaye ƙeyar kan  ambar tsakiyar kai da mirɗe-mirɗen gashi sai kace kan zakara,ga kayan da ya saka  wanda zakayi tunanin cikakken inyamuri ne ba Bahaushe ba kuma ɗan musulmi,wannan duk bashi ne matsalar ba kuma bashi ne abin mamakin ba yanayin maganarsa duk ta canja takoma kamar na ɗan daudu.


Cike da barikanci Musa ya fara magana kamar mace"Hi Maman Jummalo ƴar uwa, ya jin nice,kwana da yawa,ashe zamu aurar da yara"


Sai wani lanƙwasa da karairaya yake kamar wata mace,macan ma karuwa.Haba gida ba sai ya kaure da salati da sallalami ba,ma gulman layi an samu sabon rahoto.Matan gida na cikin wannan yanayi sai ga Umma Kande ta shigo gidan,dama bata nan ya dawo ba,taje siyayyar wasu kayan biki a kasuwa,saukanta kenan daga keke napep aka ce mata Musa ya zama ɗan daudu sai zance yakeyi a gidan da matan aure,bata ɓata lokaci ba ta shiga gidan cike da tashin hankali.


"Musa!,Musa!!,Musa!!!,kai ne haka!!!" 


Waro idanu tayi  waje tare da dafa ƙirjinta hannu bibbiyu  sai kuma ta fashe da kuka har da shassheƙa don tayi mamakin a ce wai yau ɗan da ta haifa da cikinta ya zama ɗan daudu,to ya hakan ta faru ne,mai ya maida shi haka,tana kukan ne ya zo kusa da ita tare da cewa


" Oh My God,haba mommy na,why cry naaaa,keda zaki ji daɗin ganin ƴan matanki amma sai kuka,no no no,stop mommy na"


"Ƴan matana fa kace Musa,da hankalinka kuwa,kai macace da kake kiran kanka da ƴan mata,mai ya shiga ƙwaƙwalwarka Musa,wayyo ni  Saratu jikar sarkin ruwa,naga ta kaina!!! "


"To miye a ciki don na zama mace,ai normal ne wallahi chass Mommy na,kinga nazo miki da tsaraba harda kayan mata ma wallahi sai kiba su Zaliha su gyara jikinsu kinsa ina harka da kayan mata kuma ina saidasu,naga ƙannena zasuyi aure shiyasa nace bara na kawo musu suma"


Ai ba shiri da tsagaita kukanta,jin ɗanta na wa'inan kalamai,yau mai ke faruwa da ita ne.


"Musa anya ƙwaƙwalwarka a  daidai take aiki kuwa,kodai maƙiyana suka ma asiri  ne,na shiga uku ni Saratu,wayyo ni wayyo ni shikenan sun mai damin ɗa ɗan daudu!!!


Kowa a gidan na mujiya ya zuba musu,jin wannan sabon salo  sharri wai asiri a aka ma Musa,habawa tuni Umma Kande ta katse ma kowa tunani da kururuwanta wanda ya karaɗe gidan gaba ɗaya,har wasu ƴan waje sun fara shigowa cikin gidan don kashe kwarkwan idanunsu saboda har an fara kai rahoton Musa ya zama ɗan daudu.


" Wallahi bazata saɓuba,wannan aikin asiri ne! Wallahi bazan yarda ba,asiri akama yarona don anga arziƙi ya fara samun mu,to wallahi ƴan baƙin ciki sai dai su mutu,wallahi bazan yarda ba,sai na ɗau mataki wallahi kawai a maida min ɗa mace, wayyo ni Saratu,wayyo ni sarere jikan sarkin ruwa,yau naga ta kaina,yiiiiiiiiii,yiiiiii,wayyo  niiiiiiii!!!"


Da sauri Maman Jummalo tayi cikin ɗaki da ita saboda ta fara sakin layi,kar ƴan layi suji sirrinsu,da ƙyar ta shigar da ita ɗaki,ta ce kowa ya wuce gidansa.


Ƴan uwan Umma Kande ne da dangin Maman Jummalo d'a ɗakinta tare da ita kanta Maman Jummalo suna bama Umma Kande baki akan tayi haƙuri,ta kwantar da hankalinta bayan biki sai a bi lamarin na Musa a hankali.


Haka dai suka lallaɓata har da rage kukan sai dai shassheƙa wanda lokaci bayan lokaci take ajiyar zuciya.


Shiko Musa ko a jikinsa hasalima fita daga gidan yayi,daman baida niyyar kwana gidan,hotel na garin yaje ya kama na kwana huɗu har a gama biki ya koma Calabar abinsa.


Ƙarin Haske


*****Abinda bata sani ba game da Musa shi ne,tun farkon tafiyarsa Calabar halayansa suka fara canjawa,duk da lokacin akai-akai suna waya da Umma Kande, zuwanshi gida wanda daga shi bai ƙara zuwa ba sai wannan zuwa duk halayansa sun canja,kasancewarsa mai sanyin murya,gashi ba mai hayaniya ba yasa a lokacin da yaje Calabar abubuwa suka mishi wuya,tunda baida zafin nama da karsashi a komai nasa kamar wata mace haka yake ji da kansa.Farko ya fara dako sai daga baya yaga babu ci ya daina,sai wani abokinsa da suke kwana a ɗaki ɗaya yaji tausayinsa yayi mishi hanyar aiki gidan abinci wanda yawancin ƴan aikin  hausawa ne amma fa cikakkun ƴan bariki mai gidan abincin ma bahaushiya ce,haka ya fara aiki gidan abinci wanda daga ƙarshe ƴan daudun gidan abinci suka fara bashi sha'awa ganin suna samun kuɗi sosai,manya-manyan matan garin suna zuwa ɗaukarsu fita cikin manyan motoci,shima kawai  ya tsunɗuma cikin wannan harkar,abinda yafi ƙarfafa mishi son shiga harkar shi ne Mamansa Umma Kande,a duk sanda sukayi waya da ita sai ta mishi ƙorafin rashin turo kuɗi akai-akai da ba yayi,wai ya cika son jiki kamar mace,shi yasa bai samun komai a acan, ga abokanansa wasu har da gidaje da mata amma shi ko sisi bai turowa balle tunanin yin aure,shi kuma a gaskiya maganganunta  suna ƙona mai rai sosai,shi yasa ya bama kanshi shawaran zai naima kuɗi kota y'halin ƙaƙa ne in har Mamansa zata daina ce mishi  rago ne.Wannan ne asalin dalilin da yasa Musa shiga cikin harkar ƴan daudu a Calabar har shi ma yanzu yayi suna a can ana kiransa da Pretty Mussy,don ba laifi tana kai mai yanda ya kamata.Daman wannan zuwan da yayi bayan biki yake son ya siya gida sannan ya siya shagugguna a kasuwa wanda kuɗi zai dinga shigo masa akai-akai har Mamansa tayi alfahari da shi kamar yadda take alfahari da Nusaiba wai tafishi samun kuɗi kuma tana tallafa musu a gidan****.


        @@@@@@@@@@@@@@


Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta Allah yasa basama gidan a lokacin da Musa ya dawo,balle suga abin mamaki da al'ajab,kuma koda suka dawo ɗaki suka shige abinsu,daman ba shiga harkar bikin suke ba tunda ba'a sakasu ciki ba,Sa'eeda da take budurwa ma babu wacca a cikin ƴan uwan nata ya gayyace ta balle taje ƴan matanci a bikin.


Dangin Abbansu Sa'eeda tun fil-azal ba son Umma Kande suke ba shi yasa koda wannan lamari ya afku suna ɗaki basu fito ba sai dai Allah ya kyauta suka iya cewa, dayake mata uku ne sai namiji ɗaya sukazo bikin.Ƙannan Abbansu Sa'eeda  mata da yayarsa ɗaya sai kuma ƙaninsa namiji  sukazo bikin.


Dayake suna shiri sosai da Umman Sa'eeda haka sukai ta janta da Sa'eeda a jiki.Hakan yama Sa'eeda daɗi a rai,ganin yanda suke janta a jikinsu da hira har da Ummanta.


Daman auran Umman Sa'eeda su ne suka ƙarfafa gwiwar sai ya ƙara aure saboda halin Umma Kande,bata girmama iyayansu  tun suna raye,gashi da tsani wani daga daginsu ya raɓa Abbansu Sa'eeda saidai ita da yaranta kaɗai,wannan dalilin ne yasa aka aura masa Umman Sa'eeda saboda tanada hankali da girmama na gaba da ita ba kamar Umma Kande ba.


            @@@@@@@@@@@@


Umma Kande dai ta dangana,tayi haƙuri  sai bayan biki kamar yanda Maman Jummalo ta ce da ita saboda bikin,ta haƙura ta cigaba da shirya shiryan biki sosai,tun ana saura kwana uku amare suka fara shagalin biki har yau da ya kasance gobe ɗaurin aure suna shagali kala-kala.


Day 1 sunyi ƙauye day, sai day 2 sunyi fulani day sai yau kuma ana kamun amare,anyi kashe kashen kuɗi,ba laifi angwaye sunyi ɓarnar kuda don Naira tayi kuka😁.Nusaiba tayi ɓarin Naira sosai dan yanxu ta zama wata himmm da ita sai kace wata babbar mace ,tayi ƙiba sosai ga bleaching ɗin da take yanxu na allura ne, tayi haske sosai sosai.


Duk wannan bidirin da ake yi a gidan bai hana Sa'eeda zuwa makaranta ba,sannan Ummanta ma haka kullun sai ta fita shara abinta,a tare suke fita da safe abinsu.


         @ @@@@@@@@@@@@


Ranar ɗaurin aure


Yau take asabar kuma ranar ɗaurin auran yara uku a gidan Malam Sulaiman Sani,a Masallaci aka ɗaura auran na ƴaƴan  uku akan sadaki Naira dubu #100,000 lakadan ba ajalan ba ga kowaccansu,sannan aka shafa fatiha aure ya ɗauru(Su Umma Kande sai a zuba ruwa a ƙasa a sha😁😁😁😁).


Angwaye babu wanda yazo gaisuwan iyayen amare kamar yanda ake a al'adan ce,nan ma akaita surutai musamman ƴan layi( Ƴan layi akwai gulma,kunsama su Umma kande da Maman Jummalo ido,kun hanasu rawar gaban hantsi haba😁😁😁🙃🤔) ,wurin ƙarfe 8:00pm aka zo ɗaukan Jummalo, sai kuma Zaliha,ita kuma Iklima sai 11:00pm aka ɗauke ta,wannan abu ya janyo surutun mutane da dama, su Umma Kande hakan bai dame su ba tunda an ɗaura mai ya rage can tamatse musu da gulmar,duk lokacin da suka zo ɗaukar amare  suna mara ba dasu tunda dai an ɗaura auran ƙarshen tika-tiki-tik.


Haka aka kai kowacce ɗakinta,babu laifi angwaye sunyi bajinta sosai,sai dai bamusan ya yanayin zaman auran nasu zai kasance ba.


      @ @@@@@@@@@@@


Bayan kwana biyu da biki,dangi na kusa da na nesa kowa ya koma gidansa da abin arziƙi daga wurin su Umma Kande da Maman Jummalo banda dangin Abbansu Sa'eeda taƙi basu abin biki wai tunda dama ba sonta suke ba kuma wannan zuwa biki wurin su Umman Sa'eeda suka tare to wallahi babu abin biki da zata basu,har Abbansu Sa'eeda saida ya roƙa amma taƙi,haka suka wuce garinsu daman su can basu sa rai a abin bikin ba balle hakan ya damesu.


A ranar bayan tafiyar ƴan uwan Abbansu Sa'eeda daman su kaɗai suka rage, Musa ya shigo gidan,tun sanda yazo gidan ta fara kuka bai sake zuwa ba kuma koda yaje ɗaurin auran bai zo nan gida ba.


Lokacin ƙarfe 12:00pm na rana,shiga ɗakin Umma Kande ya yi da sallama kamar mutumin arziƙi amma muryar nan a lanƙwashe take kamar mace,ya samu wuri akan kujera ya zauna.


Maman Jummalo ce ta amsa masa sallamar amma Umma Kande ko kallan inda yake batayi ba.


Ɗakin shiru ya ɗauka na ɗan wani lokaci kowa na zancen zuci kafin Musa ya ƙatse shirun da gaishe dasu.


"Mommy na barka da rana,na same ku lafiya,ya gajiyan biki"


Yana maganar yana yanga sai kace mace,su Umma Kande dai ido suka zuba mai babu ɗaya a cikin wanda ya iya amsa mai,tsabaragyen mamaki da ya cika su musamman Umma Kande wanda har yanzu ta kasa yarda ɗanta ne Musa,shi Musa ɗanta ya zama ɗan daudu.


"Yanxu Musa wannan wani irin ɗabi'a ne ka ɗauko,kaga kuwa yanda ka koma yanzu sai kace mace wallahi abinda kakeyi ko wata macan baza tayi ba,haba Musa ya kamata ka dawo cikin hayyacinka don Allah" cewar Maman Jummalo


"Nahiiiiii Maman Jummalo inji ƴan india kinsa nayi yaransu , wannan ra'ayina ne,babu ruwanki koma mai zanyi,haka nake da ra'ayin zama,kuma ina alfahari da zama na haka,chass wallahi"


Miƙewa yayi duk suna binsa da kallo yayi wani juyi a ɗakin tare da girgiza ɗan ƙaramin kafaɗunsa sannan ya ce 


"Yanzu ki kallo dubeni kyakkyawa dani san kowa ƙin wanda ya rasa,ke a Calabar ma har bukin ɗina akai manya manya Mata suna ji dani,zaki wani ce in dawo hayyacina,to da ba a hayyacina nake ba"


"Shikenan ni Saratu, ta faru ta ƙare Musa,yanzu a gabana ni mahaifiyarka kake girgiza kafaɗunsa haɗe da rangwaɗa,wayyo ni Sarere jikar sarkin ruwa!!!,na shiga uku!!! "


Kuka take yi mararan,da sauri Musa yazo wurinta haɗe da dafa kafaɗunta tare da cewa" Sorry mommy mi,kibar kukan nan don Allah babyn ki da kika sani a da bana yanzu bane,don nayi kuɗi sosai sosai "


Tsagaita kukan Umma Kande tayi tana dubansa tare da cewa"Da gaske kake Musa na ɗan albarka"


Ɗaga mata kai ya yi alamun eh,haba sai  Umma Kande ta haɗe ido da Maman Jummalo nan  suka kwace da dariya.


"Haba sai yanzu naji sanyi a raina,mai yasa tunda  kazo baka faɗamin ba,kabarni ina kuka akan yanayin da ka koma,ai babu laifi tunda akwai samu"


"Wallahi mommy  naso faɗa miki amma sai naga duk kin rikice kawai sai na bar gidan na tafi hotel abuna,daman na bari sai bayan biki  nazo muyi maganar dake"


"Toh yanzu dai fadamin maganar ina jinka kace kayi kuɗi,ni kuma banga komai ba"


Dariya Musa yayi yana wani lanƙwasa ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya ce"Suna account Mommy,daman nazo ne da niyyar siyan gida,tare da shaguna koda biyar ne a kasuwa,sai nasa haya,kinga zaki  dinga samun kuɗi akai-akai ko Mommy na? "


"Da kyau ɗan albarka,naji daɗin wannan batu wallahi, Allah yama albarka,amma gaskiya idan zakazo garin nan,inaso ka koma yanda kake a da,bayan ka tafi sai ka juya saboda ƴan gulmar layi kaji ɗana"


"Bakida case Mommy mi, yanzu sai ku fara cigitamin gidan haɗe da shagunan ko"


Da "Eh"  dukkaninsu suka ce suna murmushi ,sai ya ciro bandri ɗin dubu kuda uku ya miƙa ma Umma Kande da Maman Jummalo, haba wannan karon harda kuɗa tare da rungumeshi su duka(Allah ya kabamu wadatar zuci da ƙarin imani).Wannan kenan.


         @@@@@@@@@@@@@


A bangaren karatun Sa'eeda sai dai muce maa shaa Allah,tana maida hankali sosai da sosai dan yanzu har sun kammala  first semester suna a second semester a lokacin first semester result ɗinsu har ya fito.Sa'eeda ce ta samu highest score a class ɗin nasu wanda baima da yawa daga cikin ƴan ajin  daɗi ba.


Yanzu ma haka su Sa'eeda sun tashi a school kasancewar yau Friday da wuri suke tashi.Bayan sun fito daga department ɗinsu ita da Maryam zasu nufo wajen gate ɗin makarantarsu don su samu mai keke napep ya kaisu gida,sukaji horn ɗin mota a bayansu,dukkansu babu wacca ta zuyo suka cigaba da taifiyarsu,mai mota da yaga alamun ba tsayawa zasuyi ba,yayi saurin parking a gefen titi sannan ya fito daga motar.............




****waye wannan mai yima su Sa'eeda horn kuma mai yazo dashi wurinsu?.......



****Gashi dai burinsu Umma kande ya cika an aurar da ƴaƴa,koya zaman nasu zai kasance da mazajensu?.........



🌹🌹🌹Shin ya kuke ganin mugun son kuɗin Umma Kande wanda ko kallon yanda ɗanta ya koma batayi ba,mai zakuce akai........



Sai mun haɗu da pages na gaba in

shaa Allah🙃🙃🙃



Ina matuƙar alfahari daku My Esteem Fans💝💝💝🌹🌹🌹🌹



I love y'll lodi lodi domin da bazarku nake taka rawata💝💝💝💝🙃🙃🙃🙃🤗🤗🤗🤗




Daga alƙalamin 

🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.

[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 

Post a Comment

0 Comments