TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sarauniyar kyau page 25-26

 *๐‘ท๐’‚๐’ˆ๐’† 25 & 26*


Sannan ta fito daga bedroom ษ—in, cikin sanษ—a kamar yadda ta saba take wuce palon duk girman shi, a hankali ta tura door ษ—in kitchen ta shiga, haka kawai taji gabanta na faษ—auwa, da sauri ta buษ—e ฦ™ofar kitchen ษ—in ta fita, da sauri sauri take tafiya har ta dan gana da ฦ™aramar ฦ™ofar garden ta fice da sauri.


Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke daga inda take a bakin window na bedroom ษ—inta, zuge curtains ษ—in tayi, a zuciyarta ta yanke shawarar gobe kawai koma miye zai faru, sai tayi ma Haleesat maganar wannan satar hanyar da takeyi tana tafiya Night Club, koma miye zai faru ya daษ—e bai faru ba, wani yanki na zuciyarta kuma faษ—a ma ta yakeyi kawai ta sama Momy Rafi'at ta ma ta Bayanin komai, yayinda wani ษ“angaren yake gargaษ—inta akan idan tayi haka Haleesat ba zataji daษ—i ba.


Da tunanin ya isheta a fili ta ce, "toh kartaji daษ—in mana miye nawa tunda bani na sakata fitar dare ba ae."


Haleesat kuwa tana fita tun kafin ta ฦ™arisa gurin motar ta cire hijjab ษ—in jikinta, sannan ta saka straw hat ษ—in hular hannunta, akanta, sam bata lura da wata farar mota acan gefe dake fake ba, saboda duhun dare da gurin da motar yake dashi.


Tana shiga motar Zuree taja suka bar gurin, saida ta saita nutsuwar ta sannan ta kalla motar da kyau, bataga Jenny ba 'dum dadam' taji gabanta ya faษ—i na rashin dalili, gabaษ—aya motar mutum uku ciki, hadda ita Zuree dake driving sai Feenah dake gefenta tana shafa wayarta sai kuma ita Haleesat ษ—in ta uku.


*__๐Ÿช__*


'๐‘ท๐‘จ๐‘น๐‘ป๐’€ ๐‘จ๐‘ณ๐‘ณ ๐‘ต๐‘ฐ๐‘ฎ๐‘ฏ๐‘ป'


A hankali Haleesat ta furta sunan saman laษ“ษ“anta tana ษ—an murmushi ganin irin tsadadden club ษ—in da sukazo a yau.


Night club ne wanda yayi  ฦ™aurin suna cikin garin Abuja kuma da kewaye, guri ne na manyan yara, don masu zuwa girin sai wane da wane don ba guri ne na ฦ™ananan qwari ba, shi kanshi kuษ—in parking mota na da ake biya a Club ษ—in ya ishi wani talakan Najeriya jari mai ฦ™arfi, don zunzurutun kuษ—aษ—e ne bana wasa ba, aฦ™alla ana biyan kuษ—in parking mota a haษ—aษ—ษ—en parking lot na Club, sama da Dubu ษ—ari uku parking kawai, sannan yanayi yanayin mota ake bi, don idan motar ka/ki mai masifar tsada ce tofah kuษ—in da mutum zai biya sai haure hakan ๐Ÿ˜Ž


Har yanzu ฦ™ayataccen murmushin fuskar ta bai ษ—auke ba, ta kalla Zuree da ta ฦ™ariso gurin bayan tayi parking a gurin da aka tanadar domin yi.


Ta ce "it's pleasure babe muna wuta fah highly higher kuwa, Yau kuma nan akayo damu ne?,"

Dariya Zuree tayi tana karkaษ—a car key's ษ—in dake hannunta ta ce, "Yeah I you enjoy this ko kuwa a canza wani Club ษ—in?,"  ta tambaya Haleesat ษ—in tana ma ta nuna da gabaษ—aya  haษ—aษ—ษ—en Club ษ—in.


Dariya ita ma Haleesat tayi sannan ta ce "Yeah Yeah I enjoy this special Club, 'PARTY ALL NIGHT',"

Kallon Feenah tayi tana faษ—in.

"yane wai Feenah yau kamar bakya walwala fah, what happening to you?," 

Tun kafin Feenah tayi magana Zuree ta rigata da faษ—in, " ae barta kawai kinsan halin ta fah, ko'ince kinsan halin ku guda na miskilanci."

 

"Toh ina kuma Jenny take?," Haleesat tayi tambayar tana kallonsu su duka, Still Yanzu ma  cikin sauri Zuree ta ce "Yau batajin daษ—i shiyasa fah, that's All ta faษ—a tana ษ—an sosa fuska game da inda inda.

"Alright kuzo mu shige fah guys, don anayi bamu," cewar Haleesat.


Ba wanda ya kuma magana acikin su suka shiga ciki, Haleesat cikin tafiyar ta juya tanayima  Feenah magana, sam bata lura ba, taji tayi karo da mutum gamm, a tsiwace ta juyo dan taga wani shafaffe da mai ne ya bugeta, bai iya bada hakuri ba, maganar da tayi niyyar yine ya tsaya cak a maqwogwaronta sakamakon ganin irin mutumin dake tsaye gabanta, dum dadam daram taji gabanta ya tsananta bugu a dalilin haษ—a kwayar idanu da sukayi.

She was very Thither shocked, saboda yadda taga yanayin shi dogo fari, ga faffaษ—an ฦ™irji, ga kyakyawan suffa irinna asalin jaruman sadaukai, ba za ta iya cewa ga yanayin fuskar shi ba, sakamakon sanye yake da face mask.


A hankali ta lumshe kyawawan idanun ta, in few secs, sannan ta buษ—esu tana mai addu'ar sake kallon kyakyawan surar dake gabanta, sai dai me?.

Da buษ—e idanun da zatayi, wayam ba kowa a gurin sama da ฦ™asa, da sauri sauri cikin zafin nama ta juya bayanta, can ta hangoshi a ฦ™ofar fita zai fita da alama wani yake nema ko yake bi.


Da ฦ™arfi ta ciji pink lip ษ—inta na ฦ™asa har saida ya fashe, da sauri  Feenah ta ฦ™ariso gurin tana tambayar ta, ko lafiya ta tsaya a gurin.

Bata ce mata komai ba, ta kama hanyar fita daga gurin, harabar Club ษ—in ta fita, amma bataga kowa ba, koda kuwa mai kama dashi ne.


Wannan karon hadda Zuree suka ฦ™ariso gurin da take, ita taฦ™i gaba haka zalika taฦ™i baya.

Zuree da ษ—an mamaki ta ce "wai Baby Leesat lafiyar ki kuwa, menene kike nema haka?,"


Sai lokacin Haleesat ta ษ—an dawo cikin nutsuwar ta, kallon ta tayi cikin lumshe idanu ta ce.

"me kika gani ne, kika ce haka?," Zuree ta ce "naga kina abu kamar wata mai iska mana,  gashi yau naga kamar akwai abin da ke damunki ko?,"

Murmushi Haleesat tayi ta ce "ba komai, kawai dai yanayin garin ne, amma ba komai, So no need to worry your self, nagode da kulawa fa."


Ciki suka koma Zuree na faษ—in "gabaษ—aya sai naji Club ษ—in yau babu, daษ—i dukanku bakwa cikin walwala," Feenah ta ce "share kawai."


Suna shiga basu tsaya komai ba, kai tsaye suka haye wajen Rawa dama ba'a rabasu da ita rawar, yi suke kamar ba gobe, kuma kamar basa gajiya da ita rawar ๐Ÿ˜‡


IN BRIEFLY


A taฦ™aice dai basu suka fito daga club ษ—innan ba, sai wajen ฦ™arfe biyu na dare.


A mota Haleesat ta kalla Zuree dake driving cike da nishaษ—i ta ce "Babe ya naga baki ษ—auka hanyar gidanmu bane, naga kin miฦ™a wata hanyar daban, ko dai kin manta dani a motar naku ne?." 


ฦ˜in kulata Zuree tayi saima ฦ™ure volume da tayi, ganin haka yasa Haleesat ta mayar da kallonta kan Feenah zatayi magana.


Da sauri kamar tana jira ta kalleta, ta jefa mata wani farin handkerchief a fuska, ko sakan bata ฦ™ara ba, wani bacci mai nauyi ya ษ—auketa.


Dariya suka sheฦ™e da ita a tare hadda tafawa, Zuree tana murza steering ta ce.


"yau Haleesat saita gane aya zaฦ™ine mai masifar ษ—anษ—ano da ita, badai ta shigo hannu ba a yau, hadda wani cewa Feenah ya naga yau bakya cikin hayyacin kine?, tayi maganar tana kwaikwayon irin muryar Haleesat.

Suka kuma fashewa da dariyar shaฦ™iyanci a tare, Feenah tana taunar cingum tass tass ta juya idanu ta ce.


"ae kedai, batta kawai, da shegen zaฦ™in murya Like a sweet," taja qwafa.


Zuree taja qwafa ita ma ta ce, "ae barta shegiya, gata da kyau, gasu  duka ฦดan gidansu masu kyau kamar ฦดa ฦดan aljanu."


Feenah ta ce "kedai bari ina faษ—amiki, barinma wannan ฦ™anwar nata, duk tafisu kyau da komai, miye ma sunan ta, wannan wacca ta shiga takarar gasar  ๐’๐€๐‘๐€๐”๐๐ˆ๐˜๐€๐‘ ๐Š๐˜๐€๐”  ษ—innan?,"

Zuree ta ce wai 'Afeefah',"


Feenah ta amsa ma ta da "E, mana ita fa, sunan ma kanshi mai daษ—in faษ—ane, gashi na LARABAWA.

Zuree ta ce "danma bakisan duka ฦดan gidannasu bane, shiyasa ga gashi, ga kyau, ga diri ga komai da komai na more rayuwa haba madam,"


Haka suna gossip ษ—in ฦดan gidansu Haleesat  iyalan MISTER MAI KYAU.

Har suka isa wani madaidaicin flat home, irin ฦ™erarunnan waษ—anda ฦดan haya ฦดan makaranta sunfi zama a irinsu.

Horn sukayi, mai gadi ya wangale musu gate ษ—in gidan, suka shiga da motar, a parking lot Zuree tayi parking, sannan suka fito a tare.

Feenah ce ta buษ—e back seat ta ษ“angaren da Haleesat take kwance.

Zuree ta kamo hannun Haleesat ษ—aya ita ma Feenah ta kamo ษ—ayan, a haka suka nufi cikin gidan da ita.


A wani madaidaicin bedroom suka sauketa sai da suka tsaya suka ษ—an huta, sannan suka ฦ™ara cicciษ“arta suka ษ—aurata saman bed ษ—in.

Feenah ta kalla Zuree tana murmushin winning ta ce, "kira kice aiki ya kammala,"

Wayarta Zuree ta ciro a cikin trouser pocket ษ—in jikinta wata special number ta lalubo sannan ta danna ma ta kira, ringing ษ—aya aka ษ—auka.

"Sir aiki ya kammala," haka kawai Zuree ta faษ—a aka katse kiran, daga ษ—ayan ษ“angaren.


Dariya Feenah ta fashe dashi tana faษ—in "zamu kwashi gara wallahi,"

"ai yau sai ta kasa tafiya, raping ษ—inta zanyi yadda ya kamata, Babe ษ—innan ta taramin kwaษ—ayi da yawa fa, yau saina korar da kwaษ—ayina gabaษ—aya."

Zuree tayi maganar tana suษ—e baki, Like a old prostitute๐Ÿ˜ฐ


Sunkai akalla Ten minutes, suna zaune a bedroom ษ—in can sukaji alamar shigowar mota gidan, da sauri Feenah ta zuge curtains, sannan ta buษ—e glass window ษ—in bedroom ษ—in tana dubawa, wata bakar range rover ce tayi parking, sannan wata kyakyawar budurwa ta fito daga ciki.

Da sauri Feenah ta koma ta zauna daษ“asa saman bed, "lafiyar ki kuwa?,"  Zuree ta tambaya ganin yadda ta dawo ta zauna jiki ba laka.

"Babu komai,"  Feenah ta bata amsa.

ฦ˜amshin sassayan turaren white gold ne ya fara baฦ™untar hancinsu sannan mamallakiyar ฦ™amshin ta bayyana, kyakyawar gaske sanye cikin €nglish Gown mai shaining,  marron color iya gwiwar ta, fuskar ta rufe da face mask, mai rubutun 'GLAMOUR'.


Gabaษ—ayan su suka zuba mata ido, harta sama guri saman doguwar sofa dake a bedroom ษ—in, zama tayi ta ษ—aura ฦ™afa ษ—aya kan ษ—aya.

"bana buฦ™atar kallo ya cika yawa fa, don hakan yana haddasamin  Headache."

Ta furta a hankali kamar mai ciwon baki, cikin sassanyar muryarta.

Da sauri suka janye idonsu akanta cike da kunya,. Zuree ce tayi ฦ™arfin halin faษ—in.

"Gata mun kawo ta, kamar yadda kika buฦ™ata, amma please zamu iya ganin fuskar ki kuwa?,"


"Because Of What Reason?,"


Ta tambaya tana kallon su da kyawawan Blue £yes ษ—inta masu shaining.

Shiru ษ—akin yayi, sai can Feenah ta kore shirun da faษ—in, "ba damuwa, ae basai munga fuskarki ba, yanzu dai gata, sai ki bamu cikon kuษ—in mu,"


Tun kafin Feenah  ta rufe baki sukaji Alert a duka wayoyin su, dake hannayensu, da sauri suka ciro wayoyin nasu suna dubawa, "kan bala'i two million's" Zuree ta faษ—a da ฦ™arfi kuma a fili tana zazzare idanu,  kallon Feenah tayi tun kafin tayi magana Feenah ta ce.

"Kwarankwatsa nima haka ne, Two million's, na gani kamar a mafarki."


Gabaษ—ayan su suka mayar da kallonsu kanta cikin rawar jiki da baki, Zuree ta ce "madam duka waษ—annan  kuษ—aษ—en nawa ne, two million's fa?,"


Sha re maganar tayi, ta kalle su ta ce "ku fara aikin da yake a zuciyoyin ku."

"Mu fara aikin da yake zuciyoyin mu, kuma, kamar ya ya?,"


Zuree ta tambaya da ษ—an mamaki.

"aikin fini sa ni, oya ku fara domin nima naga yadda akeyi,"


Tuni Feenah ta ramfo menene budurwar take nufi, da sauri ta ce "mu fara fa, kikace ke banda ke?,"


"E, ta bata amsa, ta ci gaba da cewa "inaso na koya ne, shiyasa na ce ku fara ae,"

Wannan karon Zuree ce, ta ce "to a gabanki kikeso muyi, kike nufi?,'

tayi ma ta tambayar tana fito da ฦ™ananan idanun ta waje, ita sai yanzu ta fahimci abin da take nufi.

"E, haka nake nufi, ko bazaki iya bane, na nemi wasu, ko kuwa dai rashin kunyar naku bai kai nan bane?,"

Da sauri Feenah ta ce "iyawa ma kuwa, yanzu zakiga iya aiki, tashi tayi ta haye saman bed ษ—in, kallo ษ—aya ma zaki fahimci yadda ake harkar, madam kyakyawa, cewar Feenah ษ—in sannan ta fara kici_kicin๐Ÿ˜ฌ


Kamar a mafarki taji ana shafata, ana kuma ฦ™oฦ™arin rabata da tufafin jikinta๐Ÿ˜ณ


A hankali take buษ—e idanun ta da suka ma ta nauyi, biji biji ta fara ganin mutane akanta, ga wani shafa da ake ma ta kamar za'a yaga mata fatar jiki, ba shiri ta buษ—e idanun ta gabaษ—aya, abin da ta gani ne, yasa ta ฦ™ara rumtse idanun ta, tana fatan idan ta kuma buษ—ewa taga mafarkine, ba gaske ba, amma ina tana kuma buษ—ewa abin da ta fara gani da farko shine ta kuma gani yanzu ma.

Da sauri ta yunฦ™ura zata miฦ™e tsaye, ganin haka yasa Feenah ta mayar da ita da ฦ™arfin gaske.


Matsananicin kokawa suka farayi Haleesat tana ฦ™oฦ™arin qwatar kanta, yayinda su Zuree suka dage, baji ba gani, akan saisun rabata da tufafin jikinta, ita kuma taฦ™i ta basu damar hakan๐Ÿ˜ซ


Da Allah ya ba ta sa'a ta buga kan Feenah da headboard da ฦ™arfin gaske, amma kamar ta bige dutse, saima wani gurnani da Feenah takeyi ta kuma dawowa har tana tsinka ma ta mari a fuska.


Jama'a saiga Haleesat tana ihun neman taimako, wani cizon da Zuree tayi ma ta a cinya ne yasa, ba shiri Haleesat ta saki ihun da yasa budurwar dake zaune gefe tana kallon komai rufe kunenta da duka hannun ta tana rumtse idanu.


Da ฦ™arfi ta faษ—in "ku rabu da ita, I say Stop It Please," 


Amma ina kamar tanayi da dutse, buษ—e murya tayi da wani tsawa take faษ—in.


"ku rabu da ita nace," ku wasu kalan dabbobi ne wai, mace ฦดar uwanku kuke ฦ™oฦ™arin yima fyaษ—e, anya kuwa kuษ—in mutane kuwa?,"


Da sauri Zuree dake wuya, ta juyo zata ma ta magana a zafafe, wannan juyawar da tayi, yaba Haleesat dama, aikuwa bata tsaya jiran komai ba, ta dage iya ฦ™arfin ta na bara dana bana ta haษ—a ta gannawa Zuree cizo a damtsen hannu๐Ÿ˜‚


ihun azaba Zuree ta saki tana rumtse ido, dan kuwa cizon ya shigeta yadda ya kamata, ko kafin Feenah tayi wani yunฦ™uri, Haleesat ita ma tayi kukan kura ta buga kan Feenah da headboard na gado da masifar ฦ™arfi ta ฦ™ara bugawa saida tayi hakan fin sau huษ—u, Wanda hakan yasa Feenah sakin ihun azaba nan take ta sume a gurin๐Ÿ˜…


Huci kurum haleesat take tana faษ—in "Shegu ฦดan iska kawai, maciya amana condemned kawai Allah yayi wadaran hallinku, ฦดan kutmarrr  ๐Ÿ˜ณ๐Ÿƒ


Gabadaya Haleesat bata cikin hayyacin ta, ga dogon gashin kanta ya rufe ma ta fuska.


Juyowa tayi kan budurwar dake gefe tana kallon ta babu alamar tsoro tare da ita.

A hankali ta sauko ฦ™asa ta zauna tayi tagumi hannu bibbiyu, tana kallon budurwar, a hankali budurwar ta takai hannu ta cire face mask ษ—in dake rufe da fuskar ta.

Nan kyakyawar fuskarta ta bayyana, wanda sai da tasa Haleesat lumshe ido, duk da har yanzu bata gama dawowa hayyacinta ba, sannan ta buษ—esu kar akan budurwar da bata taษ“a ganin ta ba, ko haษ—uwa da ita ba, tsawon rayuwarta sai yau kuma yanzu, a wannan taฦ™in da suke ciki.


"wato dai idan na fahimta, kece kika sakasu ko?," "to amma meyasa?,"

Haleesat ta jerowa budurwar waษ—annan tambayoyin, shiru ta ma ta, kamar ba zata bata amsa ba, sai kuma can ta nisa sannan.

Buษ—ar bakinta sai cewa tayi, "haka kawai, na sakasu,"


Da mamaki Haleesat take kallonta, sai kuma tayi murmushi ta ce "badai haka kawai ba akwai dai dalili, kuma wannan dalilin nakeson sa ni."


ฦŠan murmushi budurwar tayi sannan ta ce "ki yarda dani haka kawai, naji inaso nasan yadda akeyin abin, don naga Al'ummar yanzu ko nace matan yanzu sunfi raja'a akan yin hakan,"


"oh wato shine kuma, kikace bari ki gwada akaina ko?,"


Haleesat ta tambayeta cike da takaici, sannan ta ci gaba da cewa "amma sha re wannan, kinamun kama da wata, amma kuma na manta ko wacece, to komadai wacece matsalar ta,  yanzu ki faษ—amin, a inda kika taษ“a ganina, da har kikaji sha'awar gwada hakan akaina,"


kai tsaye budurwar ta bata amsa da "a Club ne, wata ranar Sunday, idan bazaki manta ba, kinyi ma wani ma'aikacin Night club, ษ—in faษ—a akan ya kawo miki whiskey ko?,"


"oho kice anan kika ganni ko, yanzu  na fara fahimta," cewar Haleesat.


Budurwar ta ci gaba da cewa, shine ni kuma tun daga ranar na saka miki ido, har taฦ™aitaccen tarihin ki na sa mo."


Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke, duk wannan maganar fa, da sukeyi cikin nutsuwa sukeyi kamar ฦ™awaye ko kuwa waษ—anda suka san juna.

sannan ta ce "shin zan iya sannin sunan ki?,"


"๐–ง๐–ค๐– ๐–ฑ๐–ณ ๐–ข๐–ง๐–ค๐–ญ๐–ฆ ๐–ฉ๐–ด๐–ญ๐–ฆ"  budurwar ta bata amsa, Nice name, Haleesat ta faษ—a, ta kuma cewa zan iya tambayar ki wani abun kuma?,"


Jinjina mata kai Heart tayi alamar 'E', haleesat ta ce "kin taษ“ayin lesbian ne?,"


Da sauri Heart ta ce "a'a," 

Haleesat tayi nodding kai, ta kuma cewa "kin taษ“ayin zina?,"


Yanzu ma da sauri Heart ta girgiza ma ta kai alamar dai 'a'a' sannan ta fara magana.


"Ban taษ“a aikata zina ba, ko lesbian, amma anso asakani a hanyar yi,"


"a'ina kuma suwa?,"


Haleesat ta jero mata tambayar, Heart ta ce "a school kuma ฦ™awayena," ta cigaba da cewa "baso ษ—aya ba, ba kuma sau biyu ba ฦ™awayena sunsha ษ—aureni, suce sai sunyi raping ษ—ina amma basu taษ“a samun dama akaina ba, abin har mamaki yake bani,"


"Saboda me" cewar Haleesat ido waje, Heart ta ce "nima dai bansani ba, amma dai wasu suna cewa saboda kyawuna ne, yayinda wasu suke faษ—in saboda diri,"


Dariya Haleesat tayi ta ce "ai sun faษ—a gaskiya, shiyasa akeso mace ta dinga suturta jikinta da hijjabi a koda yaushe."


"Menene kuma hijjabi?," Heart ta tambaya, ษ—an murmushi Haleesat tayi tama, manta ko wacece a gabanta, ta ce.


"Sanya hijabi bin umarnin Allah ne da annabin sa, kariya ne daga fitina, alamace ta tsarkin zuciya, kyakkyawan ษ—abi'a ce, garkuwa ne daga faษ—awa halaka, sutura ce daga al'aura, kariya ne da ga mazaje marasa mutunci fasiฦ™ai, kariya ne daga aljanu, kariya ne daga shiga cikin azabar Allah da fushinsa, bautar Allah ne sanya hijabi."


Ajiyar zuciya Heart ta sauke jin Haleesat takai aya, sannan ta ce "to zan iya saka hijjab ษ—in?,"  murmushi Haleesat tayi ta ce "zaki iya mana."


Juyawa tayi tana kallon su Zuree da Feenah da sukayi tsuru tsuru dasu ta ce "me kuka yima Jenny?,"

Da sauri Zuree ta ce "Feenah ce ta saka mata qwayar bacci a lemu."


Girgiza kai Haleesat tayi sannan ta ce "kunyi ma kanku, kuma ban yafe ba, ta faษ—a tana miฦ™ewa saman bed ษ—in, tahau ta ษ—auko ribbon's ษ—inta da hularta ta saka.


Kallon Heart tayi bayan ta dawo ta zauna a ฦ™asan ta ce, "sunana 'Haleesat Abubakar Mai Kyau', am very amazing to meet you," ta ษ—anyi shiru sannan ta ci gaba da cewa.


"zamu iya ฦ™ulla ฦ™awance dake?, tayi ma ta tambayar tana miฦ™a ma ta fresh hand ษ—inta.


Hannun Haleesat kawai Heart take kalla sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.


"yanzu bakiji haushin abin da naso ayi miki ba?,"


Haleesat tayi dariya sannan ta ce "ko kaษ—an banji haushi ba,  saima darasin rayuwa dana koya, da ma can tun farko laifi nane da nake zuwa Night club, amma yanzu, na fahimci wani abu a rayuwa, wannan abun shi ne bada kowa ake yadda ba, a duniya, komai dangantakar ka da mutum kuwa."


Murmushi Heart tayi sannan ta miฦ™awa Haleesat hannunta tana faษ—in "kamar yadda na faษ—a miki a farko sunana HEART CHENG JUNG' Naji daษ—in haษ—uwata dake."


Murmushi ita ma Haleesat tayi sannan tasa hannunta cikin na HEART suka ฦ™ulla ฦ™awance.


Clock ษ—in dake manne a wall na ษ—akin ta kalla lokaci yaja sosai ฦ™arfe huษ—u na asuba saura.


Kallon su Feenah tayi ta galla musu harara kamar qwayar idonta zai fito, sannan ta kalla Heart ta ce inaga fa saidai mu kwana ana gidan, saboda lokaci yaja sosai,"


"Okay baki da damuwa Heart ta bata amsa, tana murmushi.


Tashi Haleesat tayi ta shiga toilet bata daษ—eba ta fito, kan bed ta haye abinta kallon Heart ta kuma yi, tayi murmushi sannan ta ce "saida safe, sabuwar ฦ™awa,"


Heart da ษ—an mamaki ta ce "bakyajin tsoron su kuma yunฦ™urin yi miki wani abun?," tayi ma ta tambayar iyakar  gaskiyar ta, dariya Haleesat tayi ba shiri sannan ta ce.


"Idan na amince da mutum na gama nawa, saura ya rage nasa ya kyautatamin ko ya ha'inceni, Nikam banada matsala shida Allah."


Heart ta ce "kina burgeni sosai fa," 


Haleesat tayi dariya, "da gaske nake fa" cewar Heart, "ai na sa ni," Haleesat ta bata amsa. 


Murmushi Heart tayi sannan ta kwanta a saman doguwar kujerar da take.


Lumshe ido Haleesat tayi tana tuno kyakyawan mutumin da ta haษ—u dashi ษ—azu da kyakyawar surarshi, mutumin da ko ainihin fuskarshi bata sa ni ba, balle kuma sunan shi.


*๐Ÿฉธส‚ฮฑษพฮฑฯ…ษณฮนแƒงฮฑษพ ฦ™แƒงฮฑฯ… ๐Ÿฉธ*


*☆ฦšิ‹าฝ ษณฮฑฮนษณฮฑษพิ‹ ฦ™ิƒ☆๐Ÿค™*


Kiran sallah ne ya tasheta da ga baccin da ya fara ษ—aukarta, a hankali ta buษ—e kyawawan idanunta, bakinta ษ—auke da addu'ar tashi daga bacci saukowa tayi daga kan bed ษ—in toilet ta shiga ta ษ—auro alwala, sannan ta fito, dagewa tayi iya ฦ™arfinta ta ษ—akawa Zuree duka, a firgice kuma ta gigice ta tashi zaune tana zare ido.


"Bani key ษ—in motar ki,"  Haleesat ta faษ—a a dake kuma fuska a ษ—aure, ba musu Zuree tasa hannu a trouser pocket ษ—inta, ta ciro key ษ—in sannan ta miฦ™a ma ta.


Karษ“a Haleesat tayi sannan ta fita can parking lot motar Zuree ta buษ—e ta ciro hijjabinta da kuma handbag ษ—inta.


Cikin bedroom ษ—in ta dawo bata ga Heart ba, da alama toilet ta shiga handbag ษ—inta ta buษ—e ta ciro wani madaidaicin scarf shimfiษ—a shi tayi bayan saka hijjabinta ta tayar da sallah, tana idarwa bata tashi daga wajen ba saida tayi azkhar.


Wall Clock ta kalla ฦ™arfe bakwai da rabi na safe, kallonta ta mayar kan Heart da tun fitowar ta daga toilet taga tana sallah ta zuba ma ta ido ba ko gyaftawa.


ฦŠan murmushi tayi sannan ta ce "barkanki dai madam yanzu zan iya tafiya gida?,"  murmushi Ita ma Heart tayi sannan ta amsa da  "yauwa barka, zaki iya."


Tashi Haleesat tayi ta ษ—auka handbag ษ—inta, bayan ta saka scarf ษ—in aciki.


Waje suka fito dukansu hadda su Feenah da Zuree waษ—anda ko sallah ma saida rana ta fito gatsau sannan suka gudundura.


"Ko zan iya rage miki hanya" Heart ta tambaya tana kallon Haleesat ษ—in.


Haleesat bata ce ma ta komai ba ta nufi motar Heart ษ—in, har zata shiga kuma saita juyo, ta kalla su Feenah ta ce "daga yau nida ku anyi baram baram kar ษ—ayanku tayi gigin koda kirana a waya ne daga yau nida ku  b.s.b.s.,"


Tana gama faษ—in haka ta shige motar Heart taja suka bar gidan, ba wanda ya iya magana acikin har suka iso unguwan su Haleesat ษ—in, sai kuma lokacinne Haleesat ta fara jin faษ—uwar gaba daurewa kawai takeyi.


Guri Heart ta samu a gefen wata tree a unguwan tayi parking, fitowa Haleesat tayi ta zagaya ta ษ“angaren da Heart take, ษ—an kwankwasa glass ษ—in window tayi.


Buษ—ewa Heart tayi tana kallon Haleesat ษ—in, murmushi Haleesat tayi sannan ta ce "nagode fa, amma please karki ฦ™ara tunanin sannin wannan abun,"

"saboda me?," Heart ta tambaya, "saboda babu kyau,"  Haleesat ta bata amsa ta cigaba da cewa "zan iya samun phone number ษ—inki?,"

Heart ta ce "sosai ma, why not,"  wayarta ta ciro a cikin handbag ษ—inta tana rubuta lambar wayar da Heart take karanto ma ta.


ฦ˜urawa wayar ido tayi bayan ta gama rubuta lambar da Heart ษ—in ta karanto ma ta ganin lambar bana Nigeria bane yasa ta kalla Heart ta ce "wannan lambar fa?,"


"Number nane na ฦ™asata, ฦ˜asar France yau zan koma na gama abin da ya kawoni nan ฦ™asar,"


 Heart ta bata amsa.

Qura ma ta ido Haleesat tayi ita sai yanzu ma take ฦ™arewa Heart ษ—in kallo yadda ya kamata.


Kyakyawa ce sosai, don bata mayi kalar ฦดan nigeria ba, da gani ma bata da wata alaqa da ฦ™asar, amma kuma meyasa taga kamar tana mata kama da wata?, amma kuma ta kasa tuna koda wa Heart ษ—in take kama.


Sha re tunanin tayi, sannan ta kalla Heart ta ce "okay Allah ya tsare hanya, bari na shiga gida," ta faษ—a bata jira amsar taba tabar gurin.

Ganin haka yasa ita ma Heart taja motar ta tabar haษ—aษ—ษ—iyar unguwan.


Kwankwasa ฦ™aramar ฦ™ofar gate ษ—in Haleesat ta farayi zuciyarta na harbawa jin ba'ada niyyar zuwa a buษ—e ma ta ne, yasa ta ฦ™ara ฦ™arfin bugun amma shiru, can taji alamar za'a buษ—e, ษ—an matsawa tayi gefe.

Isah ne ya buษ—e gate ษ—in yana faษ—in "bama za'a bar mutum ya samu koda baccin sa fe yayi ba, anzo an takura da bugu nasan ma bazai wuce ฦดan maula ba, to ai sai aja please a rungumi sorry  domin Alhaji Abubakar Sameer Lamiษ—o  bayanan kuma ma.......


Sauran maganar da yayi niyyar gasa ma koma waye ne, ta maqale a bakin shi, sakamakon ganin wacca take tsaye a ฦ™ofar, da sauri ya matsa gefe yana goge zufar da ta fara wanke mishi fuska, dan kuwa bai manta wahalar da ya sha ba a lokacin da yayi ma Lailah dariya ba, da tasa aka kusa korar shi daga aiki saida ฦ™yar ya samu Lailah ta haqura.


Haleesat ko kula sannu da zuwan da Isah yake ma ta batayi ba ta shige ciki gabanta na bugu da qarfin gaske.


Knocking ษ—in ฦ™ofar palon ta shiga yi baji ba gani, a zuciyarta kuwa tunanin yadda zazu kwashe da ฦดan gidan take, dan ma sauฦ™inta ษ—aya taji Isah na faษ—in Daddynsu Mister Mai Kyau  baya nan.


Jin an buษ—e ฦ™ofar ne, yasa ta ษ—ago daga tsugunawar da tayi, domin har wani ciwon mara takeji.


Ajiyar zuciya ta sauke ganin ERINA ce mai gyara palo, hanya Erina ta bata ta wuce ciki, shiga palon tayi bakinta ษ—auke da addu'o'i kala kala.

Bata ga kowa a palon ba, dan haka da saurinta ta nufi hanyar bedroom ษ—inta, har ta saka ฦ™afa zata shiga ษ—akinta taji muryar Auntie Nainarh tana kiran sunanta.


Rumshe idonta tayi da ฦ™arfin gaske sannan ta juyo dahm da dahm taji zuciyarta ta bada bugu saboda tsananin tsoro.


Duka ฦณan gidan ne zaune a dinning table hadda Momy da ta warke tsaf tana tafiya abinta. 


A hankali ta fara taka ฦ™afafunta tana ฦ™arisawa dinning ษ—in, yayinda gabaษ—aya sassan jikinta babu inda baya rawa kamar mazari, cak taja tunga ta tsaya a tsakiyar palon taฦ™i gaba taฦ™i baya, kamar suna jira ta tsaya gabaษ—ayan su suka taso sukayo kanta da tambayoyi kowa da kalar tambayar da yake jefo ma ta.


Ganin haka yasa Momy Rafi'at ta daka musu tsawa cikin faษ—a ta fara magana.

"wai ku wasu kalan mutane ne, a haka ne zata baku amsa koya da kalar tambayar da yake ma ta, taya zata iya baku amsa, ku sama guri ku zauna mana."


Umarnin ta suka bi gabaษ—ayan su suka zazzauna Nainarh, Nailah, da kuma Zaynerb a Three sieter, sai kuma Afeefah, Lailah a two sieter, sai Deejarh one sieter, sannan momyn ta kamo hannun Haleesat ta riฦ™e suka zauna a three sieter a tare da ya ke kujeru set biyu ne a palon.




Post a Comment

0 Comments