TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 15 & 16

 Episode Fifteen : The New Driver


Adam ya bi motar da kallo har ta kule, shi dai bai ga alamar wannan mutumin daga wannan gidan ya fito ba dan bai ma yi kama da unguwar ba ballantana gidan. Waye shi? Kwalliyar da yayi da kamshin da yake yafi kama dana wanda yazo zance, amma zance gurin wa? Ya kalli nashi kayan jikin, basu mutu ba amma kuma ba zasu tsaya a jere dana wanda ya bar gurin ba. 


Ya dan tsafa kansa yana kallon gidan, shi bai taba zuwa zance ba, sai kuma ya tambayi kansa in da gaske zancen yazo. Shi dai yasan yaran sun tsaya masa a rai, kamannin halittar su da bambancin halayyar su yana bashi mamaki kuma yana kara sawa yaji tsoron Allah a zuciyarsa. Wannan ya sa ya kasa cire su a ransa, sai ya mayar da makarantar su gurin zuwan sa kullum idan lokacin daukan dalibai yayi, a haka watarana ya gansu wata rana kuma sai dai yayi ta rarraba ido ba tare daya gansu ba, haka zai hakura ya koma gida. 


To yanzu kuma kusan sati uku kenan kullum in yaje school din baya ganinsu, sai kawai yaji zuciyarsa babu dadi, haka kawai yaji shi lallai yana so ya gansu duk da cewa bashi da wani dalilin ganin nasu. Wannan yasa yanzu yana tashi daga aiki ya taho unguwar su yazo dai dai inda yake sauke su ya fara tambayar ko akwai wanda ya san su. Bai sha wahala ba "ohh Sumayya da Ruqayyah kake nufi? A can layin suke amma bansan gidan su ba, sai dai in kaje can din ka tambaya" yana shiga layin ya tambaya sai aka nuno masa gidan, sai kuma yaga wannan hadadden saurayin yana kokarin barin gurin.


Yayi ajjiyar zuciya yana tattaro duk courage dinsa. Bai san me zai ce musu ba, bai san kuma yadda zasu karbe shi ba. In sun tambaye shi dalilin zuwansa bai san me zai ce musu ba. But he is going to try, ko Ruqayyah zata wulakanta shi yasan Sumayya ba zata wulakanta shi ba, kuma shi bai damu da wulakanci ba, in da sabo ya saba, babu abinda bai gani ba. Ya ci dubu sai ceto.


Ya kira yaro ya tura shi, "kaje kace wai Sumayya tazo inji Adam" sai yaji abin odd, sai yayi murmushi sannan ya jingina da jikin motar taxi dinsa.


Yaron yana shiga ya bude muryarsa ya kwada sallama sannan ya fadi sakonsa "kutumelesi! Wannan dan rainin hankalin me ya kawo shi gidan mu? Uban waye ya nuna masa gidan mu" Inna Ade tace "ke Ruqayyah! Menene haka? Ban hana ki irin wannan maganganun ba?" Ta juya kan Sumayya "waye kuma Adam? A ina kika samo shi shi kuma?" 


Sumayya ita ma data cika da mamakin jin adam din a gidan su tace "Inna ban san yadda akayi yasan gidan mu ba, mai taxi ne kawai da wani lokaci yakan kawo mu gida daga makaranta" Inna tace "dan taxi? Dan taxi fa kika ce min Sumayya, menene hadin ki da dan taxi?" Sumayya tayi kamar zata sa kuka tace "wallahi inna babu komai a tsakanin mu, kawai......" "Babu komai a tsakanin ku yasan sunan ki?" 


Yaron da yake tsaye a gefe yace "me zance masa?" Sumayya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta, Inna tace "ki fita, ki tambaye shi me ya kawo shi, in bai gaya miki dalili mai kyau ba ki ce kar ya kara zuwa gurinki, bana son jaye jayen mutane kina ji ko?" 


Sumayya ta mike da sauri ta shiga daki, Ruqayyah ta mike ta bita "ki bar ni inje in korar miki shi, irin wadannan mutanen in ba korar kare aka yi musu ba ba hakura suke yi ba" Sumayya ta saka hijab dinta tace "thank you, but I don't need your help. Zan iya yi masa Magana da kaina".


A jikin taxi dinsa ta same shi kansa a kasa yana daddanna wayar sa, fuskarsa da murmushi. Sai da tayi sallama sannan ya dago yana kallon ta yana kara fadin murmushin sa yace "ameen wa alaikumus salam Sumayya. Nice to see you a cikin kayan da ba uniform ba" sai ta samu kanta da yin murmushi "it is nice to see you too" sai kuma ta tuna da abinda tazo gaya masa "ya akayi kazo gidan mu Adam? Me kuma ya kawo ka gidan mu?" Ya mayar da wayarsa aljihu yace "laifi ne kenan dan na nemo gidan ku? In laifi nayi kiyi hakuri. Nazo ne kawai dan in ganki, ko shima laifi ne?" Ta girgiza kanta "wannan ba dalili bane ba, babata da kyar ta barni na fito kuma cewa tayi inzo in sallame ka, idan kuma Baba yazo ya ganni anan tare da kai inajin sai ya targada ni, dan haka dan Allah Adam ka tafi kafin yazo ya ganmu" 


Yayi ajjiyar zuciya, fuskarsa tana nuna rashin jin dadi yace "lucky you. Yar gidan inna da Baba. Inna zata ce miki bari Baba kuma zai yi fada, kinji dadinki. Shikenan bara in tafi. Dama kwana biyu bana ganin ku a school ne shine nace bara inzo in duba ku ko lafiya?" 


Sai taji kuma babu dadi, taji something a tone din da yayi magana dashi ya taba ta tace "lafiya lau Adam. Mun gode sosai. Mun gama exams ne dama neco kadai zamuyi. Mun gode sosai da kulawa" ya gyada kai yana cewa "I understand. Allah ya bada Sa'a. Allah kuma yasa kuyi amfani da result din ku. Ni ga nawa nan a ajjiye suna ta kura" ya dan huri iska ta bakinsa, trying to hide his emotions ya sake cewa "bara in tafi nasan zaku je islamiyya ko?" 


Ta girgiza kanta "mu bama zuwa islamiyya ai. Inna Ade ce islamiyya mu, a gurinta muka koyi komai na ilimin addini da kuma duk wata tarbiyya ta musulunci" yayi murmushi "yan gata, kunji dadi. Lemme go kafin Baba yazo yayi fadan ganin ki tare da ni" sai taji tana son jin dalili chanjawar fuskarsa, amma kuma tana tsoron jan maganar kar tayi kaifi a gurin Inna Ade ko Kuma kar Baba yazo ya same su. 


Ta tsaya tana kallon sa har ya bude motar ya shiga sannan tazo kusa da motar ta sunkuyo tace "thank you Adam for the visit. I relly appreciate it" yayi murmushi yace "thank you for seeing me" ya ja motarss yana daga mata hannu ya tafi. Ta bi motar da kallo har ta kule, sai taji a ranta tana son ta ji abinda yake zuciyarsa, tana son taji menene labarin sa, kuma taji tana son su sake haduwa watarana.


Da safe kafin Hassan ya tafi office ya biyo ya kawo wa Ruqayyah sim card dinta. Tana fitowa ta gashi a mota ta gaishe shi tace "na dauka aikowa zaka yi ashe da kanka zaka zo? Ko Hussain ai da sai ka aiko?" Yayi dariya sosai yace "Hussain? Hussain baya min ladabi ai, yace da minti biyar kawai na girme shi, baya ma kasar nan ya tafi China jiya. Akwai yara dai da zan iya aikowa amma I didn't want to miss the chance to see you, ina so inga wannan early morning look din naki" tayi murmushi tana dan juya masa baya tace "bayan ko wanka banyi ba" yace "and yet, you look like a model". 


Ta dauko kwalin wayar da har yanzu bata ko farke ta ba, amma bai kar ba ba sai ya sa hannu ya bude mata daya side din motar yayi mata alama da hannu cewa ta zagaya ta shiga. Ta zagaya ta danyi jim tana kallon motar kafin ta shiga, ita bata taba shiga cikin private car ba sai yau, kuma tasan wannan motar ko a cikin motoci sunanta mota. Ta zauna tana zagaye idonta a cikin motar sai suka hada ido da Hassan yana mata murmushi, sai ta nuna alamar jin kunya, cikin kwantar da murya yace "you like it?" Ta gyada kanta tace "tayi kyau, sosai" yace "thank you. Sai anyi bikin mu zan koya miki mota, kinga in zaki je unguwa sai ki dauki mota a gida kawai ki fita abinki ba sai kin nemi driver ba" tayi murmushi, fuskarta cike da annashuwa sai kuma ta girgiza kanta tace "ni me zanyi da mota. Ni babu inda ma zan ke zuwa" yace "dan dai baki saba yawo babe ba, ba dan kar Baba yayi fada ba da sai in kaiki yawo yanzu kiga gari" ta mika masa wayar hannunta tace "ni dai hada min wannan wayar, ni babu yawon da zanje, ni ba inda nake zuwa".


Ya karba ya bude ya fito da ita yana nuna mata, yana jin dadin excitement din fuskarta kuma ya fahimci a matsayin ta na wadda bata taba yin waya ko raka ni kashi ba dole ta zana excited idan tayi irin wannan wayar. Ya kunna ya saka mata komai yayi mata duk setting din daya kamata. Yana yi yana mata bayani dalla dalla na yadda zata yi operating komai. 


Sai da ya tabbatar ta gane sannan yayi kamar zai mika mata sai kuma ya juya wayar ya dauke ta a hoto. Ya jima yana kallon hoton sannan ya miko mata, itama ta kurawa hoton ido, camera din ta fito da fuskarsa sosai tayi kyau, ga background na mota mai kyau, ga kuma kyakkyawan murmushi a fuskarta, sai taga kamar ba ita ce ba, sai taga kamar irin yayan masu kudi din nan wadanda basu da matsalar komai a rayuwa. Yes, that's who she wants to be, yes, that's who she is now.


Da yamman ranar ta shiga makotansu gidan su Minal, a tsakar gida ta same ta taba kwance tana daddanna wayarta. Ruqayyah ta zauna tana cewa "albishirinki Minal" sai ta mika mata sabuwar wayarta. Minal ta karba sannan ta mike zaune baki da ido a bude. "Na shiga uku! Ruqayyah a ina kina samu wannan wayar" Ruqayyah tayi dariya tana jinta tana yawo a saman gajimare. Sai dai tayi plan din ba zata gayawa friends dinta ba tukunna, so take tayi surprising dinsu, so take kawai sai dai su ga iv. 


Tace "a inda nasamu bashi da muhimmanci, abu mai muhimmanci shine na samu din" Minal ta kuma juya wayar a hannun ta sannan tace "Ruqayyah wannan fa babbar wayar mijin Aunty Hafsa ne. Irin wannan din yaso siya ya kasa shine ya sayi karamarta " (yayarta, wadda da kudin mijinta suke ji a gidan su' Ruqayyah ya kara kumbura tace "kuma gashi ni nayi ta ba. Kinga, ni zuwa nayi ki bude min irin su facebook din nan da sauran su. Ni na kasa gane yadda zan bude" 


Nan take Minal ta bude mata facebook account, tayi mata komai sannan tace "saura hoton da za'a saka miki" Ruqayyah tayi sauri tace "akwai wani hoto, zaki ganni a cikin wata mota shi zaki saka min" Minal ta budo hoton sannan tace "wannan motar kuma fa, motar waye?" Ruqayyah ta juya idonta tace "ina ruwanki, in ba zaki saka min ba ki barshi" sai Minal tace "daga tambaya? Ke fadan ki bw matsalar ki. Kinga, a shawarce kar ki saka hotonki, saboda shi facebook guri ne na maza da mata gabaki daya, kinga babu dadi ki saka hotonki maza suna ta kallonki, gwara ki saka wani abu haka" Ruqayyah ta gyada kai tana daukan shawarar ta, yasan Hassan ba zai kasa yin facebook ba, kar yaje ya ga hoton ta kuma a samu matsala, amma kuma taso yin fafa da wannan hoton, sai dai dole ta hakura.


Tana komawa gida ta tarar da Sumayya a zaune a daki ita kadai, daga ganin fuskarta tasan akwai problem, tace "ke kuma fa? Lafiya?" Sumayya ta dauko farar envelope ta miko mata tace "wannan kudin na gani a cikin rigar ki, kudin menene" Ruqayyah ta bata rai tana miko hannu tace "kudi nane, bani abina? Sumayya tace "a ina kika same su? Yaushe aka baki su" Ruqayyah tace "a cikin kayan nan aka sako su, inna tana gani nasan Baba zata bawa ninkuma ina bukatar su shi yasa na boye" Sumayya taji ranta ya kuma baci tace "tun yanzu? Tun yanzu Ruqayyah har zaki fara boye abin duniya dan kar family dinki su mora, nan gaba me zai faru kenan?" Ruqayyah ta warce kudin tace "ai na bayar da wancan, wannan kuma ina bukatar sa kuma bazan bayar ba" Sumayya tace "kin duba kinga yawan kudin nan kuwa? Na tabbatar kudin sun isa ayi katangar gidan nan dasu, kinga ai kema in Hassan yazo ba zaki ji kunya gidan ku babu katangar arziki ba" Ruqayyah ta daga kafada tace "a haka ya ganni, a haka kuma yace yana sona. In baya son gani gidan nan ya gina mana wani".


A ranar bayan Baba ya dawo gida Sumayya ta dauki wayarta ta kai masa "Baba ga wannan, ni babu abinda zanyi da ita kuma naga kamar zata yi tsada sosai, a siyar da ita mu gani ko kudin zai isa ayi katangar gidan nan" Baba ya karbi wayar yana jujjuya ta sannan yace "Nagode sosai Hussaina. Allah yayi miki albarka". 


Kwana biyu bayan nan Hassan ya zo gurin Ruqayyah zance, sai yayi mata bayanin cewa a karshen satin nan suke saka ran zuwa Gombe gabaki dayansu shi da yan'uwansa, idan kuma sunje zai shigar da maganar auren su dan azo a nema masa. 


Ruqayyah murna kamar tayi rawa amma ta maze tace "da wuri haka? Da ka bari ai an dan kara kwana biyu mun kara fahimtar juna ko?" Yace "menene baki fahimta nawa ba in fahimtar dake yanzu? Ni dai a bangare na babu wani abu da nake ganin ya kamata in kara sani, abinda na sani ya gamsar dani sosai" 


Kamar ranar nan, suna yin sallama tana shiga gida sai ga Adam a tashi motar yayi packing a kusa da Hassan. Hassan ya gane motar, Adam kuma ya gane Ruqayyah duk da bai ga fuskarta ba, a ransa yace "ta tabbata zance yake zuwa" ya fito kamar ranar nan suka gaisa da Hassan sai yace "ashe zance kake zuwa gidan nan? Gurin Ruqayyah" Hassan ya rungume hannunsa a kirjinsa yana studying yaron gabansa yace "kai kuma zance kake zuwa gurin Sumayya" Adam yayi dariya "noo, ba zance nake zuwa, na shigo ta nan layin ne kawai dan maybe in samu in ganta, but in na aika ba lallai ma a barta ta fito ba dan ranar nan ma da kyar aka barta ta fito" Hassan yace "and you want to see her?" Adam yace "yes, I do. I really do. But I guess babu bahaushe Musulmin da zai bar yarsa take kulani ko".


Hassan yace "no, no, no. Kar kace haka. Babansu yana da kirki sosai. In baka shawara? Kayi kokari ka ganshi ka gaya masa abinda yake ranka, bana jin zai ki amincewa. Ina iyayenka?" Yace "basa nan" sai ya dauke kansa gefe, Hassan yace "a ina kake da zama" yace "daki nake renting, ni da friend dina" Hassan yace "school fa?" Adam yace "na gama secondary, zan cigaba in na tara kudin".


Hassan ya dauko wayarsa ya kira layin Ruqayyah. "Sorry na danyi mantuwa. Turo min Sumayya Please" sai ya kashe ya mayar da ita aljihu yace "gata nan fitowa, you can see her" Adam yayi murmushi, Hassan yana lura da yadda yaji dadi sosai.


Ruqayyah ta ajiye wayar tana cewa "yes! Sumayya kije waje Hassan yana kiranki, sako zaki karbo min" Sumayya bata ce komai ba ta dauki hijab dinta ta fito, har yanzu haushin yaruwarta take ji na hana babansu kudi duk da tasan yana bukatar su.


Tana fitowa taga Adam a tsaye tare da Hassan, take taji bakin cikin ta ya yaye farin ciki ya maye gurbin sa, ta rufe baki tana dariya, shima dariyar yake yi yana tahowa inda take. Sai Hassan yaga sun bashi sha'awa sosai, Sumayya tace "Adam? You are here" yace "yes am here, na shigo layin, hoping to see you sai wannan bawan Allah ya taimake ni ya kira min ke. Da fatan ranar nan ba'a yi miki fada ba" tace "no, ai cewa tayi kar in dade kuma ban dade ba"


Ta juya tana kallon Hassan tace "ina yini" yace "hmmm. Sai yanzu kika ganni? Ai ni har nayi fushi" ta karaso tana cewa "ayi hakuri babban yaya, ya zanyi in kasa ganinka bayan gaka a gabana?" Yace "na sani ko wani ya rufe miki ganin ki?" Ta danji kunya kadan tace "haba dai".


Ya danyi murmushi sai ya dauko complimentary card dinsa ya mika wa Adam yace "come to my office duk sanda ka samu dama, I might get something for you" ya karbi katin yana kallon sunan sai yayi dariya yana rike baki, ya juya kamar wanda zai rungume Sumayya sai kuma ya rungume hannunsa, yace "thank you sir, thank you so much. Amma bani da credentials din da zaka bani aiki dasu" 


Hassan yace "I am already getting an idea na aikin da zan baka, ba ka iya driving ba?" Adam ya kalli motarsa yace "sosai ma kuwa" Hassan yace "hmmmm, then maybe it is about time da ya kamata Hussain ya samu personal driver. Yana dawowa daga wannan tafiyar zan zuga shi ince bai kamata dangoten Kaduna yake driving kansa a mota ba, he will like you, tunda naga kana da tsafta da gayu, a matsayin drivern Hussain zaka sami daki a gidan mu, zaka ke samun abinci kaga baka da wannan matsalar, Hussain ba mazauni bane ba, dan haka you will have alot of hutu im baya nan, in yana nan ma am sure sometimes mantawa zai ke yi da kai. Motar ka sai ka vayar ana yi maka haya ana kawo ma ka balance, that, plus albashinka and all the goodies da za kake samu daga gurin Hussain zai ishe ka kayi sponsoring karatun ka" 


Adam daya kasa rufe baki ya juya ya kalli Sumayya ita ma da take ta murmushi yace "sai in biya mana makaranta ni da Sumayya mu tafi tare" Hassan ya gyada kai yace "I like you, I really like you".



Wannan littafin na siyarwa ne. In kina so kiyi min magana ta wannan number 09135803002.

WhatsApp only, banda calls please.




Episode Sixteen : The Houses


Bayan Hassan ya tafi Sumayya tace wa Adam "ka je fa ka same shi din, yana da kirki sosai" yace "zan je, gobe weekend amma ranar Monday first thing in the morning zanje in same shi" ya sake jujjuya card din a hannunsa yace "H & H fa" tace "yes, tashi ce" yace "to who is Hussain?" Tace "dan gayun brother dinsa" suka yi dariya gaba ki daya. 


Yace "yanzu in zan iya biya mana school tare, Baba zai barki ki je?" Tace "it is so nice of you to say that Adam. But bana jin Baba zai yarda ka ce zaka boya min. Shima yana da burin ya biya mana muyi karatu sannan kuma Baba mutum ne da bai fiya son ayi masa abu ba, yafi son komai yayi da kansa in dai zai iya" yace "Ruqayyah fa? Ita ma zata yi karatun? Naga....." Ya nuna inda Hassan ya tsaya, ta dan bata rai tace "tare muke da niyyar zuwa, but yanzu all of a sudden Hassan yazo da maganar aure kuma nasan ba zai jira ta gama makaranta ba, to gaskiya ban sani ba ko zai barta bayan aure ta cigaba da karatu" 


Adam yace "yanzu misali, just for example, idan..... Idan na aure ki nima, kinga ai ni zan biya miki karatu ko?" Tayi dariya, "Adam kenan, aure fa kace" ya dan hade rai "aure fa, ko ba zaki auri Igbo ba" ta dago kai tana kallonsa, ita dai tun ganinsa na farko ta san ba Bahaushe bane ba amma bata iya tayi placing yarensa ba. Kuma bata tantance ko musulmi ne ko akasin haka ba. To yanzu gashi ya fada mata, Igbo. Akwai kabilar da suka fi Igbo samun sabani da hausawa kuwa?


Ta sunkuyar da kanta ai taji shima yayi shiru bai kuma cewa komai ba, ta dago kai sai taga bacin rai a fuskarsa, ya juya yana cewa "it is okay, bara in tafi before I put you in trouble" yayi taku biyu tace "Adam" sai ya dakata amma bai juyo ba, ta karasa inda yake ta zagaya ta gabansa tana noticing kirar jikinsa, tace "Igbo, hausa, fulani, yaroba, Igala, kanuri duk ba shine mai muhimmanci ba, babu wanda yafi wani muhimmin a gurin ubangiji sai wanda yafi tsoronsa" ya gyada kai yace "na sani, but a gurin ubangiji kika ce ai, ni kuma a gurinki nake tambaya, can you.......marry an Igbo guy".


Ta kuma sunkuyar da kanta kasa, maganar aure ba karamar magana bace ba, sai ta juya maganar tace "ba la san hausawa yanzu cewa suke auren wani yaren yafi dadi ba? Yace "hausawa ne suka fada ko ke ce kika fada? Ni view dinki nake son ji ai bana haudawa ba" da daga kai tana kallonsa a cikin hasken farin wata, ita dai tasan he is the most handsome man data taba gani a rayuwarta, fuskarsa irin fuskarnan ce da in ka kalla ba ka iya cire ta daga ranka. 


Tace "my view, tribe doesn't matter, what matters is the person himself. In dai kasan mutumin da zaka aura kuma dabiun sa sunyi maka kuma shima haka, tribe dinku doesn't matter" yayi murmushin daya kara wa fuskarsa kyau yana kallon cikin idonta yace "then, nayi miki?" Tayi kokarin cire idonta daga cikin nasa amma sai taji ta kasa, sai taji bata so, she want to live there forever. Kasa kasa tace "I can't say, I don't know you" shima kasa kasa yace mata "I know you and I like you" taji maganar sa ta shige ta har cikin ƙafafuwan ta sai tayi saurin cire ionta daga nasa ta zagaye shi tana tafiya zuwa gida tace "good night Adam" bai juyo ba yace "good night Sumayya". 


Taji sautin dariya a cikin muryarsa itama sai tayi murmushi. A tsakar gida still da murmushi a fuskarta suka kusan cin karo da Ruqayyah. Yace "na jiki shiru, nace bara inbi sawu inji ko lafiya" Sumayya ta wuce ta tana cewa "ya tafi ai yariman naki, tun dazu" Ruqayyah ta bita a baya "and? Ina sakon?" Sumayya tace ba tare data kalle ta ba "bai bani ba komai ba, gaisawa kawai muka yi, sai dai ki kira shi ki sake tambayarsa ko ya kuma mantawa ne". Ruqayyah tayi tsaki tana kananan maganganu ta wuce Sumayya ta shige daki. 


Sumayya bata gaya mata zancen zuwan Adam ba kuma bata da niyyar gaya mata din saboda tasan zata iya gayawa Inna, ita kuma tafi son in Inna zata ji ma ya kasance daga bakinta zata ji bana wani ba.


A dakin su ta kwanta still da murmushi a fuskarta, idonta a lumshe tana tuno murmushin Adam, Ruqayyah ta kalle ta tayi tsaki tace "this one that you are smiling kamar wadda aka yiwa kyautar mota" Sumayya ta sake murmushi tace "abinda aka bani yafi mota muhimmanci a gurina. But I guess ke ba zaki fahimta ba".


Saturday family din Aunty baki dayansu banda Hussain da baya kasar suka tafi Gombe, a can suka yi weekend, a cikin weekend din ne kuma suka shigar da maganar neman auren da Hassan yake yi suka nemi alfarmar azo a nema masa officially. In kuma anje naman an bayar din suna so a saka rana ta zama daya data Hussain da kuma Hassana. 


Ranar Monday suka dawo da safe, Hassan ne ya sama suka yi fitowar sassafe saboda yana so yaje office akwai abubuwa da yawa a gabansa. A office din ne bayan ya gama abubuwan da yake yi sai yaga kiran wani agent da ya saka ya samo masa gida. Ya daga a ransa yana tunanin an samu kenan. Dan yasan in baa samu ba mutumin ba zai kira shi ba tunda specifically ya yi masa bayaniy irin gidan da yake so, hatta girman gidan, yawan dakunan da tsarin dakunan sai daya lissafa masa. Shi komai nasa a tsari yake yin sa and he sticks to wannan tsarin nasa. Ba dan emergency yake neman gidan ba ma da gina wa zaiyi yadda zai yi exactly irin yadda yake so. 


Tun sanda Allah ya hada shi da Ruqayyah da family dinta yake tunanin mai ya kamata yayi musu, farko yayi tunanin kudi, sai kuma ya fahimci Baba ba mutum ne mai son ake bashi kuɗi haka nan ba, ya san in zai karba ma sai sun kai ruwa rana kamar yadda suka yi ta yi akan aiki, kuma shi yana ganin girman sa sosai baya son yayi tayi masa musu. 


Wannan yasa ya yanke shawarar siya masa gida saboda ganin yanayin yadda gidan nasu yake ciki. Dama yana da kuɗin sa da yake tarawa, kudin albashin sa a matsayin sa na chief of staff na H &H group of companies. Tun sanda Hussain ya bude kanfanin sa na farko ya bashi wannan matsayin kuma shi yake running kusan komai, ma'aikata da yawa basu san Hussain ba Hassan suka sani. Da yawa daga cikin su kuma suna yi masa kallon kamar shine mai gurin shi kuma bai taba tsayawa yayi wa wani bayani ba saboda yana ganin babu bukatar yin bayanin.


Albashin sa account dinsa yake shiga kawai, baya taba using dinsa sai dai in zai siya wa kansa wani personal abu kamar kayan sawa ko kuma in zaiyi wa wani kyauta, amma duk kudin da ake kashewa a gidan su, duk bukatun Aunty da yammatan ta, duk motar da take cikin gidan na Hussain ne, shi yake komai amma ta hannun Hassan, check book ya samu duk yayi signing ya ajiye a dakin sa yace da Hassan "duk abinda ake bukata kawai ka cike ka fitar ba sai an neme ni ba, ni bani da lokaci kar inje inke manta important things".


Amma Hassan bai taba cirar ko da kwandala yayi buƙatar kansa ba.....


Da lissafin sa shine zai yi amfani da kudinsa gurin siyawa kansa gidan da zasu zauna shida iyalinsa in yayi aure, amma kuma sai ga Hussain ya sai gida ya fara gina musu tare. Abinda ya saka baiyi rejecting ba shine idea din tayi masa kyau na zamansu tare, iyalinsu tare sannan kuma a kusa da su Aunty. Yana ganin wannan zai karfafa zumunci a tsakanin yayansu da matansu. Amma duk da haka sai ya kuduri aniyar gina gida da kudinsa ya ajiye shi a matsayin nasa in yaso ko haya ya bayar. Tunda dai gidan da zasu zauna din na Hussain ne dan bai furta yace ya bar masa kyauta ba, kuma baisan abinda gaba zata haifar ba.


Sai dai kuma yanzu ga Hassana ga iyayenta da kannenta, wanda Hassan yake jin yanzu kamar sun zama responsibilities dinsa. Dan haka yayi niyyar daukan kaso mai tsoka a cikin ajjiyarsa ya siya musu gida. Shi nashi ginin can wait.


Ya daga wayar yana cewa "an samu kenan" mutumin yace "an samu oga Hassan, naga kamar yayi dai dai da bukatar ka sai dai in ka samu lokaci sai inzo muje in kai ka ka gani kafin ayi finalising" Hassan ya yarda da hakan, gwara yaje ya gani da idonsa kar ya sayi abinda bashi yake so ba. 


Washegari da sassafe kafin yaje office agent din yazo ya dauke shi suka je ganin gidan. Madaidaici ne kamar yadda ya bukata. Cikin gidan akwai dakunan bacci guda uku da kuma madaidaicin falo kowanne daki kuma da bandaki a ciki. Sai tsakar gidan da aka rufe kasan sa da interlocks, sai kitchen da bandaki a tsakar gidan. Akwai kuma dan siririn soro, a cikin soron akwai daki wanda yake da kofa guda biyu daya ta soro daya ta tsakar. Ya gyada kai cikin gamsuwa, komai yayi yadda yake so kawai dai yaso a samu shago a kofar gida inda yayi niyyar zubawa sulaiman kayan provisions ya ringa siyarwa inya dawo daga school. With that and salary din daya yi doubling ya bawa Baba, da kuma shi a matsayin sirikin gidan, yana ganin they are set for life.


A take ya saka hannu a takardar siyan gidan sannan kuma ya tura kudin, duk da cewa yayi tunanin cewa gidan yayi tsada da yawa but for Hassana it is worth it. Yayi tunanin irin farin cikin da gidan zai saka ta, ya tuno irin farin cikin da ya gani a idobta ranar daya ke kunna mata wayar da Hussain ya siya mata. 


Briefly ya sa akayi furnishing gidan, light furnitures irin wanda yasan ko shi zai iya amfani dasu sannan wadanda yasan su din zasu yi murna dasu sosai. 


Daga nan kuwa sai ya sake ware wasu kudin masu kauri ya kaiwa Aunty "Aunty maganar lefe, nace kina ganin wannan kudin zai isa?" Ta duba kudin tace "zai isa mana, in dai ba irin na Hussain kake son kayi ba" ta karasa tana dariya, shima yayi dariya yace "Allah ya kiyaye, wadannan barsu kawai, Hussain shi kudi kamar mintsinin sa suke yi" sai kuma ya kara da cewa "kuma shi saboda irin gidan da ya debo wa kansa aure ya saka banyi masa maganar ya rage kayan ba, abu ne na manya da manya" ya fada sarcastically.


Aunty ta girgiza kanta tace "kasan halin Hussain ko ba gimbiya Fatima bace bama irin abinda zai yi kenan. Ballantana kamar yadda ka fada ai shi tuwon girma miyarsa nama ce" Hassan ya mike yana cewa "ai shikenan. Sai yaje yayi ta cin naman" Aunty ta sake daukan kudin ta juya tace "amma fa in bai isa ba zamu ce maka ka karo" yana dariya yace "manage it aunty, bafa gimbiya Fatima ba ce ba".


An sanar da Baba maganar zuwa neman aure amma sai ya umarce su dasu hadu a Zaria gidan yayansa Malam Isyaku. Haka akayi kuwa suka hadu acan suka tambayar wa Hassan auren Hassana , a take aka ce an bashi, sai suka nemi a saka musu ranar da zata hadu da ta yan uwansa nan da wata uku da yan kwanaki. Malam Isyaku yace "anya kuwa? Wata uku ai yayi mana kadan ace mun shirya aurar da ya a cikin su. Kuyi dai wancan din wannan kuma sai a shirya a tsanake sannan ayi shi daga baya. 


Baba Mustapha, ganin baban su Hassan yace "haba malam, wacce shiryawa zakuyi kuma? Mu ai ƴa kawai muka zo nema gurin ku bama bukatar komai daga gare ku. A yadda Hassan ya a bani labarin yarinyar nan ai nasan idan ma bashi zata aura ba shi zai yi mata kayan daki ballantana shi zata aura. Babu wani abu. Ita kawai zaku bamu. Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya da zuriya mai albarka". Anan jayayya ta kare, date fixed.


Bayan dawowar Baba daga Zariya ne yan uwa suka yi ta tururuwar zuwa gar gida suna yi musu murna shi da Inna Ade. Fatsar su tayi babban kamu. Ruqayyah kuwa kullum bata iya rufe bakinta dan murna, lissafi take tayi na irin shagalin bikin da za'a sha, irin wanda aka jima ba ayi irinsa a Kaduna ba. "I can't wait to see the reaction on my friends faces. Ruqayyah a ina kika hadu da mai H & H? Ko yanuwanku ne dama?" Ita kuma will be like "gani na kawai yayi a hanya ya like min. Yaga irin zubin matar manya" ta lissafa adadin parties din da za'a yi, dinner, luncheon, Arabian night, mother's day, sisters eve. Irin kayan da zata ke sakawa zuwa kowanne event da kuma irin kawayen da zata je dasu "ba kowa za'a gayyata ba, kar suje su ba ni kunya a cikin dangin miji".


Bayan Hussain ya dawo ne ya aiko wa da Ruqayyah tsaraba. Wani set din mayukan gyaran gashi ne, ya kira ta yace "gimbiya ta ce ta bani sako in siyo mata, shine kema na siyo miki ban sani ba ko zaki so shi. Kayan ku ne na mata, ni ban san kyansu ba" Ruqayyah ta bude dan akawatin kayan tana dubawa, ita duk bata san ma ya akeyin amfani dasu ba. Tayi tsaki ta mayar ta rufe. "Wannan Fatimah daga dukkan alamu ta fiya iyayi".


Hussain yana dawowa ya tarar an gama saka rana, dan haka shi kuma sai ya mayar da hankalinsa kan ginin gidajensu. Shi Hussain a nasa tsarin so yayi yayi mudu ginin iri daya, komai daya, amma Hassan yana ganin plan din ya girgiza kai yace "wadanna dakunan duk me za'a yi dasu? Ni gaskiya bana son wannan plan din sai kace ba za'a bar duniya ba" Hussain yayi kamar zaiyi kuka yace "dan girman Allah kar ka bata mana tsarin nan, mun riga mun gama shirya komai na gama magana da engineers din nan sun gama fitar da plan dinsu....." Hassan yace " sai ayi maka naka plan din daban ayi min nawa daban. Ni I won't be feeling comfortable a irin wadannan gidajen" haka Hussain a dolensa ya hakura saboda babu yadda zaiyi amma shi a son ransa yaso ace iri daya suka yi, komai iri daya.


A karshe sai da Hussain ya hada baki da engineers din sannan suka shawo kan Hassan ya bari aka dora masa bene, amma shi da cewa yayi shi baya son bene "ni bana jin zan iya rayuwa a sama kamar wani tsuntsu" sai engineer yace "amma oga Hassan tunda an riga an dora wa Hussain in ba'ayi a naka ba gidajen ba zasuyi kyau, zasu zama dogo da gajere kenan. Sannan kuma ginin oga Hussain zai toshe maka iska a naka gidan". Da wannan aka samu Hassan ya yarda, amma shi ya tsara kayansa. "Two bedrooms a sama three bedrooms a ƙasa. Shikenan sun ishe mu. Ni plan dina na rayuwa da mace daya ne ni Hassana ta ishe ni har abada. Tunda muna kusa da gida nasan ba wasu baƙin kwana zamu ke samu ba sai dai daga nata bangaren, suma in sunzo dakunan kasa guda uku sun ishe su" Hussain yayi ajjiyar zuciya yace "wannan Hassana, ina tausaya muku kai da ita".


Haka aka yi ginin part din Hassan aka gama, kullum yana gurin yan tabbatar wa cewa anyi masa yadda ya tsara abinsa. Ssi da aka gam ak koma kan na Hussain anan aka kure adakar gayu. Part dinsa daban na gimbiya daban na bakinta daban na bakinsa daban. Faluka iri-iri, ga gym ga swimming pool, irin kofofi da fitulun da aka saka a gidan ma kadai abin kallo ne. Amma Hassan ko a jikinsa bai ji cewa gidan Hussain ya burge shi ba. Shi tsarin nasa yafi yi masa kyau sosai dan har yana tunanin in ya fara gini irin wannan tsarin zaiyi sai dai maybe ya dan fi wannan girma saboda lokacin an fara tara iyali. He just can't wait yayi rayuwa da hassanar sa a wannan gidan.


Ana tsakiyar shirye shiryen ne ya dauki Hussain ya kai shi gidan daya siyawa Baba ya gani, yayi masa bayanin aikin daya dauke shi da irin albashin daya bashi. Hussain ya gyada kai yace "ka kyauta sosai, yayi kyau sosai. Ni kuma a tawa gudun mawar zan siya masa napep yake zuwa dashi gurin aiki, ranar kuma da bashi ne da duty ba sai ya zagaya ya samu karin kudin cefane"


Hassan yayi masa godiya suka bar gidan. A hanya Hussain yake cewa Hassan "amma sai yaushe zaka bashi?" Hassan ya yi murmushi yana shafa kansa yace "sai satin bikin mu, sai su tare a sabon gida suyi bikinsu acan" Hussain yace "why? Hassan the planner. Da nine a ranar da na siya, maybe ma kafin inga gidan shi zan dauka muje mu gani tare. To me zan jira kuma? Yanxu in kai ka mutu kafin biki ko kuma shi ya mutu kaga ai siyan  gidan bai yi serving amfaninsa ba". 


Post a Comment

0 Comments