TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini 19 -- 20

  🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️

                           


Narrnarhh Bukar✍️


🌹Perfect Essential Writer's

Association🌹

  ✨ P. E. W. A✨



Wattpad:@AISHAABUBAKAR812

Arewabook:@Narrnarhh002





My Esteem Fans ina matuƙar alfahari daku, i love y'll all Lodi Lodi🤗🤗🤗🏵️🏵️🏵️🌼🌼🌼🌹🌹🌹🙃







1⃣9⃣---2⃣0⃣



Yanzu ma haka su Sa'eeda sun tashi daga school kasancewar yau Friday da wuri suke tashi.Bayan sun fito daga department ɗinsu ita da Maryam zasu nufo gida,sukaji horn ɗin mota a bayansu,dukkansu babu wacca ta juyo suka cigaba da taifiyansu,mai mota da yaga alamun ba tsayawa zasuyi ba, sai yayi saurin parking a gefen titi kana ya fito daga motar.


Wani handsome and classy guy ne ya fito daga motar,yana sanye da shadda mai kalar sararin samaniya,sanye yake da hula mai ƙube wacca ta saje da kalar kayan.Yana da tsayi sosai,baƙi ne amma ba cancan ba,sannan fuskarsa zagaye take da gemu wanda kana gani kasan yana shan gyara,his face look very innocent,babu laifi guy ɗin ya haɗu sosai,da murmushi a fuskarsa ya nufo wurinsu da ɗan sauri kasancewar tafiya suke.


"Assalamu Alaikum Malamai"


Maryam ce ta amsa mishi da fa'arta,ita ko Sa'eeda ko kallansa batayi ba,idonsa na kan Sa'eeda yana murmushi,don mace mai aji tana burgeshi sosai.


"Naga akwai rana sosai yau,gashi kuna tafiya  babu mai keke napep suka balle ku hau,mai zai hana na rage muku hanya koda ban kaiku gida ba,kar kusha wahala"


A lokacin ne Sa'eeda ta bashi amsa da cewa"Kaga munyi ma kana da musu son a rage musu hanya ne,to karka damu,mun gode da kulawarka amma......."


Bata ƙarasa zancen da tayi niyya ba Maryam tayi saurin cewa"Babu komai muje Sa'eeda, kinsan uzirin da ya bari ya ce zai rage mana hanya ne? "


Sunan ya sake maimaitawa a zuciyarsa ' Sa'eeda suna mai daɗi'


Babu yadda Sa'eeda ta iya tunda abokiyar tafiyarta tana son a rage musu hanya amma a ranta baso take ba tuno da nasihar Ummanta akan kula samari,haka dai ta shiga  motar.


Maryam ce ta zauna a front seat,ita kuma Sa'eeda ta shiga baya,tada motar yayi suka fara tafiya.


Motar shiru babu mai magana sai can ya katse shirun da cewa"Wani department kuke? "


"Department of Business Administration muke,100level" cewar Maryam


" Woow,ashe fresh students ne ku"


"Eh wallahi amma yanzu  muna a second semester ne"


"Allah ya taimaka,ya bada sa'a"


"Ameen ya Rabbi" cewar Maryam


"Wai ƙawarki  kurma ce,bata magana ne? "


Dariya Maryam tayi sannan ta ce"Magana kuwa sosai,saidai da alama ƴan surutun basa nan yau"


"Oh really ai naga alama kuwa"


Maryam ce take nuna mishi hanya,har ya kai daidai inda take so a sauke su wato hanyar da zata sadasu da layinsu,sannan yayi parking gefen titi,ya juyo yana duban Maryam yace.


"Sunana Sauban Muhammad ƙaraye,ina aiki a wani kamfinin sarafa shinkafa a matsayin Manager nice meeting you friend"


"Nice meeting you too"cewar Maryam


Dukkansu fitowa sukayi,a tare har shima don yana son magana da Sa'eeda amma ta mishi kwarjini a fuska.Har zasu wuce yayi saurin cewa


"Friend ko zaki aramun wannan ƙawarta taki mara son magana,zsmuyi magana ne just for 2 minutes"


Yana maganar da zolaya duk don Sa'eeda da tanka amma shiru,hasalima ƙara murtuke fuska tayi.


Ɗan jimmm Maryam tayi sannan ta ce "Haba bara na matsa,sai ku tattauna da ita"


Matsawa tayi ɗan gaba dasu,shi kuma ya matso kusa da Sa'eeda da murmushi a fuskarsa,sai da yayi gyaran murya sannan ya fara magana da cewa.


"Nasan ba a jinki bane magana a hanya amma taimako nake nema wurinki,don Allah ba dan ni ba ki taimaka min da number wayanki,Don girman Allah"


Hannu biyu ya haɗa alamar roƙo,fuskar nan ta shi tayi kalar tausayi,Sa'eeda a da bata da niyyar ba shi numbarta amma haɗata da Allah da yayi yasata aminta saboda ta tuno nasihar Ummanta da ta ce ' Sa'eeda duk wanda ya nemi abu wurinki kuma ya roƙeki da Allah koda cutarki zaiyi ki basa,sannan ki barshi da Allah' tuno da wannan nasihar yasata amsar wayarsa tasa numbarta sannan ta miƙa mai wayar tare da wuce wurin Maryam suka nufo gida.


               @ @@@@@@@@@@


Ƙarfe 11:53am ta iso gida,lokacin Ummanta ta dawo daga aikin sharanta tana ɗaki.


Da sallama ta shiga gidan kasancewar yanxu babu ƴan mata a gidan daga ita sai Nusaiba,ita kuma Nusaiba ba zaman gidan take ba, yanxu ma kamar kodayaushe shiru gidan saika ce  babu mutane ko a da can da akwai mutane a gidan ba amsa sallamarta da Ummanta suke ba.


Direct ta wuce ɗakinsu,haɗe da sake Sallama, Umman Sa'eeda dake a tabarmarta ta amsa mata tare da cewa.


"Da wuri haka"


"Eh Ummina,kinsa ranar jumma'a bamu cika lectures da yawa ba,yau kuma lecturer ɗaya ne ya cigo ajin namu"


"Ai gwara,zaku ɗan dinga hutawa,ba ace kullun sai wurin biyar zaku dinga ta shi ba,wahalar yawa zata muku"


"Nima Ummina nafi son duk ranar Friday mu dinga tashi kamar haka wallahi"


Buta Sa'eeda ta ɗauka ta zagaya bayan gida,bayan ta dawo ne taji wayarta na ringing,sai ta nufa jakarta ta ɗauko wayar.Sabuwar numbar ta gani,ɗan jimmmm kaɗan tayi har saida Ummanta ta ce


"Kina ji ana kiranki amma kin wani tsaya kamar hoto kina kallon wayar"


Picking call ɗin tayi haɗe da karawa a kunnanta sai tayi shiru,acan bangaren aka fara magana.


"Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareki  Sa'eeda"


"Wa'alaikumussalam" 


A gajar ce ta amsa haɗe da tsuke fuska kamar mai shirin kuka Ummanta dai na binta kawai da kallon mamaki ganin yadda take amsa wayar,a can a ka cigaba da Magana.


"Nasan kin gane mai maganar don koda jin kamar kina ɗaure fuska nasan yes kinsan mai maganar"


A zuciyarta ta ce 'Sai ka ce maye,to taya yasan na tsuke fuska na,ohon masa' katsa mata tunani yayi da cewa


"Sa'eeda ganinki na farko da nayi a ɗazo,lokaci guda kika shiga raina,kuma a gaskiya bazan ɓoye miki ba ina sonki da aure ne ba da yaudara ba,zuciya ta gama yarda da ke ce wacca take adduarka samu a kullum haɗe da burin kasancewa  tare da ita a matsayin miji da mata,please Sa'eeda ba nazo dan na yaudareki bane ko ko wata manufa tawa don in cimma,a'a ko kaɗan nazo ne a gareki saboda ƙaunarki da nake yi wanda lokaci kuda ya shigeni,don Allah ki aminta dani please,in ma kina tunanin karatunki ne ni a shirye nake tare da goyon bayan karatunki ɗari bida ɗari,inaso kiyi tunani akai don girman Allah Sa'eeda bada wasa nazo gareki ba"


Duk wannan surutan da yake wayar na a kunnanta kuma tana ji amma ta kasayi mishi magana,hasalima shiga kogin tunani tayi 'Wai yana sonta da aure huhh',ita da a tsarin rayuwarta bata kawo aure nan kusa ba,amma shi yanzu yana mata maganar aure.


"Hello,baki jina ne Sa'eeda"


Firgigit ta dawo hayyacinta tare da fara magana cikin murya mai sanyi da dadi ta fara magans"Ina jinka,but can you please give me some days to think about it?


"Quite sure dear"


"Alright Nagode da kulawa" 


Bata jira mai zai ce ba ta katse kiran,sai da dubi Ummanta da tun ɗazu da zuba mata na mujiya.


"Naga sai wani taɓe baki  kike haɗe da ya mutsa fuska tunda kika ɗau wayan lafiya? ”


" Wallahi Ummina wani ne mai suna Sauban ɗazu ya takuramin haɗe da haɗa ni da Allah in taimaka mishi da number na,lokacin mun taso daga school ni da Maryam kuma yanzu da ya kirani sai sai..."


"Uhmmm ina jikin sai kuma me"


Kwashe duk abinda ya ce mata tayi ta sanar da Ummanta har aikin da ya ce yakeyi duk ta sanar mata, shiru Ummanta tayi tana kallonta sannan ta ce


"To ke kuma me kika ce masa"


"Nace ne ya bani lokaci zanyi tunani a kai"


"To ai shikenan,amma dai ki kula da kanki Sa'eeda,don mazan yanzu wasunsu ba abin yarda bane,sun iya kalamai masu daɗi ga ƴan mata duk don suja hankulansu,ina ƙara fadamiki ki kula da kanki sosai,ban hanaki kula samari ba amma ki duba wanda yasan ya kamata sannan kuma mai addini da halaye masu kyau a cikinsu sai ki kulashi,amma ba kowani kala ba,ko kuma kita tara samari,kin jini ko"


"Toh Ummina,zan kula sosai in shaa Allah"


"Allah yasa"


"Aameen"


Sai kuma suka cigaba da wata hirar .


            @@@@@@@@@@@@@


Bayan ƴan wasu kwanaki


Sa'eeda dai ta aminta da soyayyar Sauban,dan yanzu yakan zo har ƙofar gidansu,duk da a wata baifi sau ɗaya yake zuwa ba kasancewar Sa'eeda bata cika son hira ba hasalima shi yake matsa mata akan yanason yazo koda sau ɗaya ne a wata.


Sunyi exams ɗin second semester wanda azumi baifi saura kwana shida a ɗauka ba suka gama,duk wannan lokacin suna tare da Sauban wanda yanzu soyayyarsa ta riga da ta gama mamaye ilahirin jikinta da gaɓoɓinta gaba ɗaya.


Sauban ya iya kashe mace da salon soyayyarsa,don zance professor ne a ta wannan  fannin,ya kama zuciyar mace taji duk duniya babu wanda take so sai shi,haƙika ya rikita Sa'eeda da kalaman soyayya masu saka mutum shauƙi,sannan yana kula da lamarinta sosai duk da idan ya bata kuɗi bata amsa sai in ya mata jan ido kana take amsa haɗe da yi masa godiya.


Haka sanda aka fara azumi ya kawo mata ramadan basket da ƙyar ta amsa saboda Ummanta ta hanata yawan amsar kaya wurin samari,haka zalika lokacin sallah kaya kala biyar ya mata haɗe da jaka da takalmi masu tsada,shima da ƙyar ta amsa sannan ta masa godiya sosai.


Duk wannan abubuwan da Sauban yake ma Sa'eeda sai ta faɗama Maryam tun daga kalaman soyayya da yake mata,kyaututtuka da dai sauransu,duk da wani lokacin ba Sa'eeda take fara bata labari ba,ita Maryam da kanta take tambayar ta ya friend ɗinta,to a nan ne sai ita kuma Sa'eeda tai ta zubo mata zancansa.


Haƙiƙa wannan sallar su Sa'eeda sunyi shi cikin farin ciki da annashuwa ba kamar saura shekarun da suka gabata ba kasancewar yanzu babu laifi Umman Sa'eeda na ƙoƙarin ganin sunyi cima mai kyau.


Bayan sallah da sati ɗaya suka koma 200 level,soyayyar Sauban bai hana Sa'eeda karatu ba hasalima yanzu karatun nata ya ƙara bada wuta saboda tana so taga a kowanni result ta fito da flat A,shi yasa kullun zaka ganta da littafi a hannu tana karatu.


Akwai specific time da taba ma Sauban zai dinga kiranta ba koda yaushe ba,kuma hakan ta faru sai lokacin yake kiranta don baya son matsa mata da yawa.


           @ @@@@@@@@


Waje guda kuma,rayuwarsu Umma Kande da Maman Jummalo ta cigaba da tafiya cikin daɗin rai da annashuwa duk da ba kamar sanda yaran nasu suke gida ba,don yanzu basa samun ko sisi a hannun yaran nasu wa'inda suka aurar hasalima tunda a kayi auran nasu babu wacca ta leƙo gidan da sunnan gaishesu,kuma idan suka tuntuɓi mai yasa sai dai suce mazajensu sun hanasu zuwa,abu fa kamar haɗin baki.


Kamar kullum Sa'eeda da Ummanta sun fito daga ɗaki zasu wuce  sai ga Abbansu Sa'eeda ya shigo gidan da sallama, amsawa su ka yi,sai ya dubi Sa'eeda fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce


"Sai ina Kuma Sa'eeda "


Banbaraƙwai Sa'eeda taji maganar tazo mata sai ta ce


"Abba makaranta zani"


"To ina unifoam ɗinki,a haka zaki makarantar ne,ko kinaso a miki duka ne"


"A'a Abba,yanxu ba nasa unifoam ai"


"Bangane ba,makarantar kuma yanzu bakya mata unifoam idan zaki,kodai unifoam ɗinki ya lalace ne,sai ki siya wani? "


" A'a Abba,ai yanzu ba'a secondary school nake ba"


"To kina ina ne yanzu"


"Abba ai na shiga university ina karantar Business Administration a Kasu"


"Au haba!,yaushe kika fara zuwa makarantar,ai bansani ba"


"200 level nake ma yanzu ai saura shekara biyu na gama"


"To to,maa shaa Allah,ki maida hankali sosai a karatunki kinji Sa'eeda"


"To Abba in shaa Allah"


"Yawwa ƴar albarka"


Hannu yakai aljihunsa ya ciro kuɗi ƴan dubu dubu da yawa wanda ni kaina mai ɗaukar rahoton bansan nawa bane ya miƙa mata  sannan ya ce 


"Ki ƙara kuɗin mota,tunda makarantar da nisa"


Har ƙasa ta ɗurƙusa hannu bibbiyu ta amsa kuɗi haɗe da yi masa godiya da adduar buɗi agaresa,Sosai ya amsa mata cike da kulawa.


Haka suka fito ita da Ummanta cike da ɗunbin mamakin sauyawansa lokaci guda.


Tun daga fara maganar Abbansu Sa'eeda da Sa'eeda Umma Kande dake da niyyar fitowa don tayi alwalar sallar subh duk taji kuma a gaban idonta Abbansu Sa'eeda ya fito da maƙudan kuɗi ya miƙa ma Sa'eeda.


Tashin hankali wanda ba'a sa mai rana ai a rikice ta shiga ɗakin Maman Jummalo ko sallama babu ta banko ƙofar ɗakin ta shiga,Maman Jummalo dake bacci cikin kwanciyar hankali tayi saurin buɗe ido jin an banko mata ɗaki babu sallama balle izinin shiga.


"Lafiya Ƙawas? "


"Ina fa lafiya Maman Jummalo, shi ke nan,tawa ta ƙare! "


"Bangane ba ƙawas,fahimtar dani,kin barni a duhu"


"Aikin gama ya gama ƙawas,yau da idona naga Babansu Nusaiba na miƙa ma Sa'eeda kuɗi masu uban yawa harda sa mata albarka wai ta maida hankalinta akan karatunta"


"Kuɗi!!! Kuɗi!!! Kuɗi fa kika ce,anya kin gani da kyau kuwa? "


" Wallahi tallahi,billahillazi Kinga har da salati nayi ko, to nagansu da idona Maman Jummalo! Nace miki nagansu! Ke kwarankwatsa tannatsa! Na gansu da idona kuma  ni ganau ce ba jiyau ba,har da tambayarta makarantarta haɗe da samata albarka,yihuhuuuuu ni Serere jikar sarkin ruwa na mutu! Na mutu ho ho hooooo! "


"Kwantar da hankalinki duk wannan kururuwan da kike bashi bane bafita Ƙawas"


"To ne kike so inyi bayan hankalin Babandu Nusaiba ys fara karka garesu,ai wallahi kashina ya bushe"


"Haba don Allah nace ki kwantar da hankalinki,zamu samu mafita akan wannan lamarin,ke bari kiji akwai mafita amma mafita ɗaya ce garemu yanzu "


"Akwai mafita kika ce MamanMaryam

lo,to mecece mafitar? "


"Ba wata mafita bace illa...................



Sai mun haɗu a pages na gaba in shaa Allah🙃🙃🙃


****ya kuke ganin soyayyar Sauban da Sa'eeda, shin zai kaisu har aure ko ko wata ƙaddara zata gitta???



****Shin wace mafita ce Maman Jummalo ta ce akwai??



***Mai yasa ƴaransu Umma Kande da Maman Jummalo kamar haɗin baki babu wacca tazo ganin gida???,Mai hakan yake nufe??? Mai yasa mazajansu suka hanasu zuwa ganin gida?? sannan yaya zamansu da mazajansu yake???


Duk ku biyoni zuwa next pages domin samun amsoshinku✍️✍️✍️🙃🙃🙃🙃🙃🙃💝💝💝💝💝🌹🌹🌹🌹


Ku cigaba da zubo ruwan coments da reactions My Esteem Fans ni kuma zan cigaba da suburbuɗo muku updates wanda zak nishaɗantu tare da ilmantuwa🌹🌹🌹💝💝💝🏵️🏵️🏵️🏵️😁😁😁🙃🙃🙃



Ina matuƙar alfahari daku my Esteem Fans🤗🤗🤗🏵️🏵️🏵️🏵️🙃🙃🙃




Daga alƙalamin 

🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.

[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 

Post a Comment

0 Comments