TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini 23 -- 24

  🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️

                           


Narrnarhh Bukar✍️




🌹Perfect Essential Writer's

Association🌹


🌹Special greetings to y'll my Esteem Fans, ina kaunarku over,ina alfahari daku domin da bazarku nake taka rawata🙃🙃🙃💖💖💖💖💝









2⃣3⃣----2⃣4⃣



Sai kuma yayi shiru na tsawan wasu mintuna,Umma Kande har ta zaci bazai sake magana ba,sai kuma taji ya fara magana cikin amon murya mai sauti tare da firgitarwa.


"Akwai sharaɗi mai girma Umma Kande!!! Sharaɗi babba Umma Kande!!! Sharaɗin shi ne,zamu baki kwalba wanda ruhinsa ke aciki,sannan karki sake!!! Karki kibari!!! Karki yarda !!! A hir ɗinki !!! Kibari kwalbar nan ta fashe!!! Idan kuma ba haka ba asirin zai karye kuma zaki kuka da kanki Umma Kande!!! Tabbas zaki kuka da kanki!!! Sannan muma zai shafe mu, don haka dole ki kula !!! Dole ne ki kula !!! Ki kula da kwalbar kamar ruhinki Umma Kande!!! Idan ba haka ba komai naki zai rushe!!! Komai zai taɓarɓare miki Umma Kande!!! "


Bayan ya gama faɗin sharaɗinsa sai kuma ya ɗaga hannunsa na hagu  sama yana a tsayan tare da yin wasu surkulle,yana cikin yin surkullen ne sai wata guguwa mai ƙarfin gaske da taso,duka bishiyoyin nan da suke zagaye da bukkar sai karkaɗawa suke,gayyayakin suna kakkaɓa,kamar za'ayi ruwan sama,tabbas wannan asirin mai girma ne ba irin kowani asiri da boka Sankeru yake basu bane,Maman Jummalo da take a zaune a wajen wata bishiya saida da tsorata matuƙa ainun,ganin yadda lokaci guda guguwa ta taso gashi yanzu ba lokacin damuna bane balle ace ruwan sama ne zai sauka,haƙiƙa da tsorata harda ma sauran matan da suke kan layi saida suka tsorata wasunsu ma harda ƙankame juna saboda firgici da ya shigesu lokaci guda.


A cikin bukkar kuma bayan ya gama surkullensa sai kuma guguwar ta tsaya cak kamar daukewar ruwan sama,bishiyun suma suka daina rangaji,haba kamar walƙiya sai ga wata  kwalba matsakaiciya ta bayyana a hannunsa sannan ya miƙa ma Umma  Kande tare da cilla mata hararar gargaɗi,a natse kamar ƙwai ya fashe ma Umma Kande ta miƙa hannayanta bibbiyu tare da russunawa cike da girmamawa ta amsa kwalbar jin gargaɗi haɗe da kashe din da aka mata akan kwalbar,a zuciyarta take ayyana dole ta kiyaye wannan kwalbar kamar ranta.


Bayan ta amsa kwalbar sai ta cire ɗankwalinta tare da nannaɗe kwalbar sosai kasancewar ɗankwalin nata mai girma ne sosai sannan ta lallaɓa a hankalin kamar ƙwai tasa kwalbar a cikin jakarta cike da kulawa kana ta kulle jakarta ta.


Boka Sankeru ne ya ƙara da cewa bayan ta saka kwalbar a jakarta.


"Wannan sihirin na daban ne Umma Kande!!! Ba kowa muke bamawa ba sai wanda yayi tsawan lokaci yana mana biyayya tare da bin dokokin mu haɗe da sharudɗanmu,haƙiƙa kinyi tsawan lokaci kina bin dokokinmu tare da sharudɗan mu,shiyasa muka baki,don haka ki kula!!! Ki kula Umma  Kande!!! Sihirin nan ba irin wanda kika saba sani bane,dole ki kula kar asamu matsala!!! Don muma zai shafemu idan aka samu matsala Umma Kande!!! "


Cikin rawar murya Umma Kande ta fara magana saboda tsoro da firgicin da ya shigeta tun lokacin da guguwan nan  ta taso  har zuwa yanzu da ta ƙara jin kashedi tare da gargaɗi akan kwalbar.


"Zzzan kula shugabanmu,mai sha re kukanmu,ba.. ba.. bbaza a masu matsala da yardarka "(wa'iyazubillah,shirka!!! Shirka,ke duniya ina zaki damu🤔🤔🤔,Allah shi kyauta)


"Da yafi miki!!! Ko kuma kiyi da nasani mara adadi Umma Kande!!! "


Kamar yanda boka Sankeru ya saba kasancewa da Umma Kande yau ma hakan ta kasance,sai daga baya Umma Kande ta fito waje tana tafiya a hankali  kamar ƙwai ya fashe mata a ciki sannan ta nufa inda Maman Jummalo take.Zaune ta sameta wurin wata bishiya tana shan iska,miƙewa tayi da sauri tare da tambayarta ya ta ƙare da boka Sankeru sannan mai ya haddasa guguwa.


Shiru tayi tana dubanta idanunta duk sun shige ciki kamar wata mars lafiya, har wata ƴar rama tayi,cikin murya mai sanyi ta fara magana.


"Dole na kula ƙawas,dole na kula da kwalbar nan ko kuma in shiga uku"


"Wace kwalba kuma"


"Kwalba boka Sankeru ya bani tare da min gargaɗi mai tsauri akan karna kuskura na bari kwalbar ta fashe saboda ruhin baban Nusaiba na a cikin wannan kwalbar,idan kuma nabari ta fashe shikenan komai nawa zai taɓarɓare"


Tare da nuna mata jakar a hankali sannan ta cigaba da cewa


"Yanzu ƙawas wani irin mugun ɓoyo kike tunanin zanyi ma kwalbar nan don wallahi na shiga ruɗu haɗe da tsoro Maman jummalo? "


Maman Jummalo shiru tayi tana nazari tare da tunanin yanda za'a ɓoye kwalbar ta yadda babu abinda zai sameta,bayan ta gama tunani sannan  ta ce


" Mai zai hana tunda yanzu baki da yara duk sunyi aure,ki ɗau kwalbar kisata cikin akwati ƙarami saiki saka a ƙarƙashin gadonki,koya kike ce ƙawas? "


"Haka za'ayi kuwa ƙawas,yanzu dai mu wuce gida ma kammala zancen a can kar a samu matsala don ni tsoro nakeji "


"Haba ƙawas kin cika tsoro wallahi,kidai kula da kwalbar sosai"


Haka suka doshi hanyar garinsu wanda basu suka iso gida sai wajan magrib kasancewar layin da suka bi wurin ganin boka Sankeru wanda a da babu layi saidai kawai ka shiga yanzu saida tabi layin kafin  ta samu  shiga ciki.


Kamar yadda Maman Jummalo ta bawa Umma Kande shawara akan tasa kwalbar a cikin ƙaramin akwati sannan tasa a ƙasan gadonta  haka tayi.Kuma tun daga wannan lokacin kuma a ranar Abban Sa'eeda ya ƙara rikicewa tare da juyawa su Umman Sa'eeda baya haɗi  da musguna musu sosai.


Tun a ranar da Umma Kande tazo da kwalbar gidan,abubuwa suka ƙara rincaɓewa,don saida ya kusa dukan Sa'eeda  ba tare da tamishi laifi ba,kuma abinda ma baita taba yi ba a baya,yana faɗa tare da zage-zagen da babu dalili haka nan daga shigowarsa gidan kaar yaji a duniya ya tsani ya buɗe ido yaga su Umman Sa'eeda tare da ita Sa'eeda,ji yake kamar ya koresu daga gidan ko zuciyarsa zatayi sanyi.


Ranar Umman Sa'eeda da Sa'eeda sunyi kuka iya kuka a ɗaki babu mai basu haƙuri ko tausaya musu,abinda bai taɓa musu ba a baya duk da a lokacin hankalinsa ba  a kansu yake amma bai taɓa musu irin cin mutunci da wulaƙanci kamar na wannan ranar ba.


Umma Kande da Maman Jummalo daɗi kamar ya kashesu saboda abin baita taɓa yima su Umman Sa'eeda ba yau yayi musu wato wulaƙantasu,ita Umma Kande wallahi taso a ce ya kore su Umman Sa'eeda daga gidan,shikenan sun yada ƙwallan mangoro su huta da ƙuda.(Kai kai kai wannan baƙin kishi haka,Allah karka bamu irin wannan zuciyar mai baƙin kishi da hassada🤔🤔🤔)


                 @@@@@@@@@@


Wai ina amare?



Bangaren Jummalo tun sanda aka kaita gidan mijinta ta soma cin karo da ƙunci haɗe da baƙin ciki tun a daran farkonta.Kamar yadda a al'adar malam bahaushe take,a duk sanda aka kai budurwa ko bazawara ɗakin mijinta,Ango yana zuwa da kaza tare da drinks don raya daren cikin farin ciki da annashuwa tare da amaryarsa.


Amma Jummalo bata samu wannan farin ciki ba saidai ma Angon ya shigo mata ɗaki a bige,ya sha giya yayi tatil sai sumbatu yake tare da jayo duk abinda ya gani ya bugashi a ƙasa yana surutai marasa ma'ana,ita kuma lokacin tana kan gado an lullubeta da mayafi babba,jin surutai da jefe jefen kaya ya sata tayi saurin fitowa daga bedroom ɗin a firgice haɗi da tsoro,fitowarta falo taga abinda ya kusa zautar mata da ƙwaƙwalwa tare da birkita mata lissafi,wai yau da zai kasance ranar farin cikinta,ranar da take so da ganin Allah ya kaita lokacin amma sai yaza mata a matsayin ranar baƙin ciki mara misaltuwa,ace angonta yazo mata ɗaki a bige,wannan wani irin ƙaddara ne,wani irin tashin hankali ne haka.Jin motsi  Ibrahim angon nata yayi saurin duban wajan,haba kamar an tsikareshi ya nufota gadan-gadan yana huci kamar wani kurcin maciji tare da ɗaukar abu a hannunsa saikace yaga abokin hamayyarsa.


"Bbbanna kiraki tun ɗazo ba,amma sai yanzu kkkika ga ddammann zuwa ehe!!! Sssaboda ni ni ɗanki ne ko!!! Kkkaruwa,shegiya mayyar mmmaza kawai" 


Jummalo da take tsakanin falo da bedroom tayi saurin juyawa tare da rugawa toilet a guje haɗe da saka key,ganin akwai abu a hannunsa kuma  kanta yawo tare da surutai wanda bama fahimtar me yake cewa take ba.Kamar kuwa ta sani kanta yayo,tsayawa wurin ƙofar toilet ɗin yayi tare da bubbugawa haɗi da faɗin


"Ki buɗe na ce!!!,madara da kaza zan baki,ki buɗe! Ki buɗe mmana Jummalota,tawan taaawan...."


Bai ƙarasa da zancan ba ya fara kwararo amai babu ƙakƙautawa,mai uban wari da ɗoyi sai kace mushe.Jummalo dake a toilet ta fashe da matsanancin kuka a ranta tana faɗin  'Yanzu a daren farkona a ɗakin mijina nake fuskantar wannan baƙin cikin,meyasa na biyewa mamata ne da Umma Kande akan saina aure mai kuɗi kaicona ni Jummalo,gashi tun kan aje ko'ina,a daren farkona na fara fuskantar bacin rai da damuwa,kaicona da biyewa mamana akan dole saina aura mai kuɗi,gashi yanxu na aura mai kuɗin amma babu kwanciyar hankali tana zancen zuci a lokaci guda  tana kuka.(Hausawa suka ce kwaɗayi mabuɗin wahala😁😁😁,gashi tun a daren farkonki kin fara fuskantar baƙin ciki,Allah ka tsare mana imaninmu 🤔🤔🤔)


Shiru taji ɗakin yayi,a tunaninta ko yafita ne,a hankali da buɗe toilet ɗin,ta fito da sanɗa,taka ƙafar da zatayi a ƙasa sai taji ƙafarta ta tako wani abu mai yauƙi yauƙi,da sauri ta ɗaga ƙafarta haɗi da duba wajen,ai ba arziƙi ta toshe hancinta da mayafinta jin wani wari ya taso kamar mushe tare da duban mijin nata a gefe yana ta sharɓar baccinsa hankalinsa kwance,ko'ina na wurin ƙofar toilet ɗin duk ya ɓaci da amai,da sauri da yaye mayafin nata tare da  cillashi  kan gado sannan ta koma toilet ɗin,ruwa ta zubo a bucket  saita saka dettol haɗe da omo sannan ta ɗauko mopper ta fito.


Tana kuka tana mopping ɗin aman,saida ta goge wurin tsaf sannan ta saka air freshner a ɗakin lungu da sako sannan ta cire kayanta ta saka na bacci tayi kwanciyarta haɗe ta tunani iri iri wanda ya sata kasa bacci da wuri,sai wajan 2:12am bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita.


Da safe kuma ita ta rigashi farkawa,still yana nan a wurin yana bacci abinsa,ɗauro alwala tayi don yin sallar Subhi duk da gari yayi haske tar haka tayi sallarta kasancewar ko a gida sai wurin 9:00am suke yin sallar subhi wani lokacin ma bayi suke ba harda iyayen nasu.


Sai wurin 10:39am ya farka haɗe da miƙa babu salati babu adduar tashi daga bacci ya wuce toilet direct, wanka yayi sannan ya fito yasa kaya,a lokacin da yake saka kaya ne Jummalo ta shigo cikin bedroom ɗin tare da sallama,amsawa yayi babu yabo babu fallasa.Wuri ta samu a gefan gado ta zauna,saida ya kammala shirinsa tsaf sannan ta dubeshi hade da yi mishi maganar abinda ya faru jiya da daddare,har complain din rashin kawo mata kazar amarci da yayi duk saida ta fadama masa.


Tunda ta fara magana yake kallonta sheƙeƙe,a ransa yana faɗin 'Wai mai wannan yarinyar take dashi a jiki ne da ya sakani nace dole saina  aureta,ko fasali bata dashi,mtwsss' saida ta kammala ƙofarinta sannan ya fara magana cike da izgilanci.


"Ke! Ni sa'arki ne da zaki dinga min magana irin haka,to indai shan giya ne kike ma wannan ƙorafin to yanzu na fara ke banda ma shan giya har ƴan mata inna gadama zan kawosu gidan nan muyi yadda mukeso babu abinda zaki iya saboda gidana ne inada iko dashi,don haka karki sake min magana akan shan giya na,is my choice so you can't change me,ok"


Shiru tayi a zuciya tana faɗin 'Ni Jummalo na ɗebo ruwan dafa kaina da kaina.


Haka dai rayuwar Jummalo ta cigaba da tafiya a gidan mijinta duk da bata taɓa faɗawa mamanta ba don kar hankalinta ya tashi,gashi ko nan da can ya hanata fita,kullum cikin ɗibo ƴan matansa yake kala kala,kuma buba abinda ta isa tayi.Duk da bai hana ci da sha amma fa wani lokacin har duka yake mata idan ƴan iskan nasa suka motsa.Wanan kenan.


            @@@@@@@@@@@@


Ɓangaren Zaliha kuwa sai dai in ce gwara Jummalo so dubu akan nata zaman auran.A sanda aka kaita gidan mijinta bayan kowa ya wuce,angon ya shigo ɗakin nata babu sallama lokacin ita ma kamar Jummalo an lulluɓeta da mayafi,zama yayi kusa da ita baice mata komai ba,can sai taji abu na mata waiwayi a jiki,da sauri ta yaye mayafin nata takai duba gun inda abun yake.


Wani irin ihu ta saki tare da ƙanƙame mijin nata tana tura fuskarta  cikin ƙirjinsa duk ilahirin jiki yana rawa,shi kuma mijin nata kunnanta ya lalubo ya fara magana.


"Ɗayan mijin naki kike gudu  ummmm Zaliha,shima yazo angonci ne haɗe da kazarsa"


A razane ta ɗago kanta tare da fashewa da matsanancin kuka, tana kukan ta fara magana


"Na shiga uku ni Zaliha!!! Wayyo ni!!! Wayyo ni!!! Don Allah ka fitarmin dashi,wallahi ina matuƙar tsoransa,na roƙeka da Allah"


"Mijin naki kike tsoro kuma"


"Don Allah ka cireminshi daga kan gadon nan"


Ƙara ƙanƙameshi take tare da runtse idanunta da ƙarfi


"Wallahi babu inda zaije Zaliha,kamar yanda kowani ango yake angoncewa a daren farkonsa tare da amaryarsa to haka shima zai angon ce dake"


"Niii!!! Kana nufin da...................







Mu haɗu a pages na gaba My Esteem Fans,domin tafiyar ta fara ɗaukar🔥🔥🔥🤗🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹💝💝💝💖💖💖






****Hmmmmm🤔🤔🤔,ita kuwa Zaliha da wani abu ne zata angon ce haka gashi tana tsoransa??? Dama maza biyu ne ta aure ba ɗaya ba??? kai kai kai gaskiya da alama ita ma ta ɗebo ruwan dafa kanta da kanta😁😁🙃🙃🏵️.




***Shin a tunaninku Umma Kande tayi kyakkyawan ajiya ga kwalbar da boka Sankeru yabata kuwa???



Ku biyoni don jin amsoshinku a pages masu zuwa🔥🔥🔥



Ina matuƙar alfahari daku My Esteem Fans,taku har kullum  Narrnarhh Bukar✍️✍️✍️ 🤗🤗🤗



Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🤗🤗🌹🌹🌹🌹🏵️🏵️ni kuma bazan gaji ba wurin sambaɗo muku  new updates wanda zai nishaɗantar daku tare da fadakar daku haɗi da wa'azantar daku🤗🤗🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🔥🔥🔥





I love y'll My Esteem special fans,ina alfarahi dak sosai,Allah yabar ƙauna 🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🌹🌹🌹






Daga alƙalamin 

🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.

[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:

Post a Comment

0 Comments