TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 45-46

  🏵️ *NACINA YA JAWO MIN* 🏵️







*Narrnarhh Bukar* 

( *The Amazing Pen* ✍️)





*TASKIRA WRITER'S FORUM*

*T.W.F*




*WATTPAD*

https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends




*AREWABOOK*

https://arewabooks.com/book?id=6615ba31404e6e2687888ab9




*TELEGRAM*

https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk




*WHATSAPP CHANNEL*

https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y






*BOOK 2*




4⃣5⃣----4⃣6⃣





Sai can taji kamar idanu na kanta,sai tayi saurin kai dubanta gun ai ba arziƙi ta waro manya-manyan idanunta waje tana da cewa


"Wayyo Allah!!! Mutum ko aljan!!! "


Banza yayi da ita tare da cigaba da aiki a laptop ɗinsa,a zuciyarsa yana cewa 'Lallai yarinyar nan wato aljani ta maidani ko,da alama zan koya mata hankali kenan,batasan waye autan Mom bane'  ko takanta bai ƙarabi ba,duk kallon da take jefa mishi da manyan idanunta duk yana sane,da alama kafin yabar Kaduna saiya koyama wannan yarinyar hankali don yaga tanada rawar kai.Sa'eeda dai ta kafe Sadam da ido  tana jiran ya bata amsa don ita tsakaninta da Allah tsoronsa take saboda taya zata kwaɗa uban sallama amma ya kasa amsawa sannan ta shigo falon idanunta basu ga mutum ba sai yanzu kawai kamar diran mikiya tayi arba da mutum ya kakkafeta da mayun idanunsa kamar zai cinyeta,tsoro ne ya sake baibaye Sa'eeda ganin bai tankata ba saima cigaba da aikinsa da yayi,jakarta ta ɗauka da sauri haɗi da veil ɗinta tayi sama da gudu tana cewa


"A'uzubikalimatillahi tammat min shairi ma khalaƙa,koma aljani ne nafi ƙarfinka da yardar Allah"


Da gudu ta haye sama kamar wacca aka biyo za'a kasheta,har bedroom ɗin Dr. Nabila ta shiga da gudu,shi kuma Sadam dariya abin ya basa,wai koma aljani ne,zako tasan aljani ne kuwa,cije lips ɗinsa yayi kaɗan tare da taɓe baki.Babu sallama Sa'eeda ta banko ɗakin Dr. Nabila wacca a lokacin waya take da Abban twins,da sauri takai dubanta ga Sa'eeda wacca sai uban haki take sai kace tayi gudun kilometer 2,saurin sallama Dr. Nabila tayi da Abban twins duk da basu gama wayar ba tare da tambayar Sa'eeda hankali tashi


"Lafiya Sa'eeda kika shigo ɗaki da gudu? "


Kasa magana Sa'eeda tayi sai dai nuna ƙofa tana haki,ƙara tambayar Sa'eeda Dr. Nabila tayi,saida ta natsu hankalinta ya ɗan kwanta sannan ta fara magana cike da tsoro


"Umm Ummm Aunty wallahi akwai aljani gidan"


Dafe ƙirji Dr. Nabila tayi tana cewa


"Aljani fa kika ce Sa'eeda a gidan nan,wayyo mun shiga uku"


Dr.Nabila da shegen tsoro, itama nan da nan da rikice tana cewa


"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,yau munga takan mu ni Nabila,to ke a ina kika ganshi Sa'eeda"


Sa'eeda bata ɓoyema Dr. Nabila komai game da arangamar da tayi da Sadam ba a falo,dariya Dr. Nabila ta fara harda riƙe ciki au daman Sadam yana nan bai wuce kamfaninsa da yace zaije ba,dariya sosai Dr. Nabila tayi,ita dai Sa'eeda sheƙeƙe tayi tana kallon Auntynta,to miye abun dariya a nan bayan ta sanar mata akan gamon da tayi a falo,sai can Dr. Nabila ta ce


"Look Sa'eeda cousin ɗinki ne fa Sadam,Mominsa ce ta take tare da Ummanki a India,so calm down ok,yazo ne duba companies ɗinsa ne a nan Kaduna don yaga meke tafiya a ciki,daman ya ce duk ran da ya shigo Kaduna zai tako har wurinmu nida Uncle ɗin don ziyara,so kwantar da hankalinta Sa'eeda, miskili ne Sadam na ajin ƙarshe,yana sane ya tsorataki wallahi,ni nama zaci a wuce yaje ya dawo ashe bai tafi ba"



Wata nauyayyan ajirar zuciya Sa'eeda ta sauke,yanzu hankalinta ya kwanta ba kamar ɗazu ba,amma kuwa ya matuƙar firgitata sosai,Allah ya isa tsoran da ya bata,tana cikin wannan tunanin haɗi da takaici Dr. Nabila ta katseta da cewa


"Jeki watsa ruwa yanzu,favourite food ɗinki yau akayi "


Murna Sa'eeda ta somayi jin favourite food ɗinta akayi wato jollof ɗin taliya da kifi wayyo daɗi ,da sauri ta wuce ɗakinta,wanka tayi tare da shiryawa cikin rantsattsiyan atamfarta wacca tasha adon stone sai uban walwali take,mai kawai ta shafa sannan ta fito zuwa downstairs,koda ta fito ta zaci zata haɗu ta wannan ɗan rainin wayon wanda ya tsorata ta ɗazun,don tasa aranta wallahi saita zazzaga mishi ruwan masifa da bala'i amma haƙarta bata cimma ruwa ba don baya nan.(Toooo,my esteem fans ku tayani dubawa yaushe Sa'eeda ta koma masifaffa, oh ni indo!!!🤔🤔🤔😂😂😂).


Direct ta wuce kitchen tare da zubo abinci sannan tazo falon ta zauna,kunna TV tayi sai ta fara cin abincinta cikin natsuwa,sai a sannan ne taji shigowansu Kauthar,twins da mai aikinsu Jamila,ashe basa gidan  haba no wonder shiyasa taita kiransu ɗazu basu amsa ba.Direct uwar rigima Kauthar tayo kan Sa'eeda da gudu tana cewa



"Oyoyo Aunty Sa'eeda ina chocolates dina"


Rungumeta tayi tare da cewa


"Yana ɗakina,ai ɗazu inata kiranku kuzo ga promise ɗin amma shiru"


"Uncle Sadam ne ya ce Aunty Jamila da driver sukaimu shopping shi yanzu baida lokaci daya yaje damu" cewar Jawaad



Ras! Ƙirjin Sa'eeda ya bada,ita ta rasa koda sunan wannan Ƙaton taji sai gabanta ya faɗi why!!! Oho ƙila tsoron daya bata ne ɗazun,zama sukayi tare da nuna mata abubuwan da suka siyo suna murna,suna cikin nuna mata ne saiga Dr. Nabila ta sauko daga upstair tana zuwa cikin falon,zama tayi kusa dasu tana cewa


"Oh ni Nabila! Ku bari ta kammala cin abinci kafin ku fara mata shirmanku mana!!! "



Murmushi Sa'eeda tayi tare da cewa


"Ba komai Aunty,suna nishaɗantar dani da surutunsu,i'm happy seeing them next to me always"



"Ai gaki ga su,kwayita shirman tare ai"


Haka suka cigaba da hirarsu sai can sukaji tsayuwan motoci,ai da gudu twins da Kauthar sukayi waje suna cewa



"Oyoyo Uncle Sadam! Oyoyo Uncle Sadam"


Har wurin parking ɗin motoci suka je da gudu,bai gama fitowa daga motan ba suka rungumeshi suna murna,shima ƙara rungumesu yayi don yana da masifan son yara,shiyasa yake sake musu fuska,shifa murmushinsa ko dariyarsa a wuri biyu ne kawai kake gani,kodai yana tare da Mominsa ko kuma yana tare da yara,a nan ne zakaga dariyarsa sosai.haka ya riƙo hannunsu suka dugunzuma cikin falon tare da sallama.Sa'eeda da tunda taji parking ɗin motoci ƙirjinta ya bada Ras! Ƙarin bugun ƙirjinta shi ne sanda su Jawaad suka ce ga Uncle Sadam,wai wani irin abu ne haka,why all these,miye dalilin bugun zuciyarta idan taji sunansa huh! Katse mata tunani sallamarsu Sadam tayi,Dr. Nabila ce ta amsa musu da murmushi a fuskarta,ita ko Sa'eeda ɗaure fuska tayi irin bata ɗaukar rainin nan,tayi kitin-kitin da fuska kamar mai shirin kuka ko kuma an ɓata mata rai,zama yayi a kujerar da take facing ɗin Sa'eeda tare da gaida Dr. Nabila cikin cold deep voice ɗinsa,maganarsa a tsanake yake yinta kamar wani basarake,cike kuma da izza yake gaisheta,kasancewar Dr. Nabila tasan haka ɗabi'arsa take tun yana yaro haka yake magana shiyasa bata damu ba,amsa masa tayi cike da kulawa tana cewa



"Ai na zaci ka wuce kamfanin sanda  na barka ashe bata tafi ba a lokacin"



Cikin cold deep voice ɗinsa ya amsa mata da cewa



"Eh wallahi,akwai wasu ayyuka da nake shirin kammala kafin na tafi a lokacin"


"Ayya! Sai kuma ka tsoratamin daughter ko Sadam"



Dariya ce ta taso masa amma sai kuma ya gimtse,cikin ɗaure fuska irin kar Sa'eeda ta kawo mishi raini yace



"Daman kinada daughters ne banda su Kauthar"


Wani tuƙuƙi ne yaje malolan wuyan Sa'eeda ya tsaya,lallai ma wannan Ƙaton wato a tunaninsa da gan-gan ta tsoratani kenan,daman ashe yana magana shi ne yayi banza da ita ko,huh  baisan wace ce Sa'eeda bane,katse mata tunani Dr. Nabila tayi da cewa



"Cousin ɗinka mana Sadam,sunanta Sa'eeda,nasan halinka da basarwa,ce nake Aunty ta sanar maka da bayyanar Hussainan Abban twins da ƴarta"



"Eh ta sanar min suna ma India tare,amma ai ni bansan yarinyarta ba"


"Hakane kuma,ke Sa'eeda bakiga yayanki Sadam bane,duk da ɗazo ka tsorata ta har taso ta tsoratani da badan tamin baya ni da nima tsorata zanyi"



Dariya take shirin taso masa amma ya dake,a zuciyarsa ta cewa 'Au ashe matsoraciya ce ma kenan' magana Dr. Nabila ta katseshi da cewa


"Au da gaske ne ka tsorata ta da gan-gan Sadam, yarinya duk tabi ta rikice...."



Bata ƙarasa maganar ba Sadam yace



"Calm down Aunty bani na tsorata ta ba,ita dai ne taso ta tsorata kanta,batamin magana in a good manner ba,how did you expect me to give her answer,cewa tayi mutum ko aljan,to na mata kama da aljani ne ko kuma taga kofato ne a ƙafata"



"To dai komai ya wuce Sadam,ke Sa'eeda nace ga yayanki ku gaisa amma kinyi shiru"



Sa'eeda da da lula duniyar tunani,tana ayyana abubuwa dayawa tare da neman yadda zata rama tsoratatan da yayi mata,taji Dr. Nabila na sake jefo mata tambayar bata gaisheshi ba,gaisuwa fa yooo mutumin da ya rikita ta ɗazu ne zata gaisar,tabb saidai to ita bata iya rashin kunya bane,da wallahi babu abinda zaisa ta gaidasa,cikin zazzaƙar muryarta ta ce


"Ina wuri,fatan kazo lafiya?ya aiki? Ya gida? Ya iyali? ya rayuwa? "



Lokaci guda ta masa tambayin duk don kar ta sake mishi magana,shi kuwa gogan tun sanda ta fara magana  ƙirjinsa ya bada Ras! Why hakan ke faruwa dashi ne  game da wannan yarinyar,meyasa muryarta take mishi daɗi ne,har so yake tayi magana duk don yaji muryarta why! Why! Why! All this is happening to him,katse mishi tunani Dr. Nabila tayi da cewa



"Sadam ya tana gaidaka amma shiru kaƙi bata amsa,ai irin haka da kayi ne ɗazu ta tsorata"


"Sorry,kowa da komai na lafiya Alhamdulillah"



Shima amsar ya bata a dunƙule don yaga sai wani ciccijewa take tana kitin-kitin da fuska,Dr. Nabila ta ce


"To  can kamfanin fatan komai yana tafiya daidai babu wata matsala"


"Eh Aunty Alhamdulillah,komai yana tafiya a yadda na tsara,sannan wannan handama da babakeran da manager tare da wasu daga cikin ma'aikatan da sukeyi duk na daƙile hanyoyinsu baki ɗaya"



*Waiwaye*



A lokacin da Sa'eeda ta ruga sama da gudu,shima dariya ya tintsire dashi harda bubbuga ƙafa cigaba da aikinsa a laptop sai kuma can ya kashe laptop ɗin tare da miƙewa ya fito waje,P.A ɗinsa ne mai suna Mukhtar ya iso inda yake da sauri  yana cewa



"Barkha da fitowa yallaɓai"


Bai amsa masa ba sai suka nufi inda motocinsu suke ,da sauri wani bodygaurd ɗinsa ya buɗe masa mota ya shiga,sai shi kuma Mukhtar ya zauna a front seat,drivan ne ya tambayi Sadam cike da girmamawa akan ina zasu,ce masa yayi *Rice company* wato kamfanin sarrarfa shinkafa ,babu musu yaja motar tare da sanar ma sauran drivers na motocin biyu,a tsakiya motar da Sadam yake ta ciki take, gaba da bayan duk bodygaurd ɗinsa ne masu baƙakyan suit,haka suka isa kamfani babu ɓata lokaci kasancewar akwai jiniya a motar bodygaurds ɗin shiyasa suka iso da wuri.


A ɓangaren manager wato Sauban da ma'aikatan kamfanin duk sunyi cirko-cirko a cikin kamfanin suna jira zuwan *CEO* ɗinsu wato *Sadam Dauda Gali Mai Nasara* mazansu da matansu kowa murna yake tare da ƙosawan zuwan mai gidansu banda manager wato Sauban da tsirarun wasu ma'aikatan masu handama da babakere a kamfanin,dan P.A ɗinsa Mukhtar ya daɗe da sanar da suna hanya,shiyasa dukkanin ma'aikatan harda masu shara,gida,securities duk sun hallara.Ma'aikatan mata sai gyara fuskarsu suke,wasu ma harda ƙara powder da jan baki ko Allah zaisa ya taya,duk da sunji raɗe-raɗin baya kula mace duk kyawunta.


Jiniya suka da alama mai gidan ne ya iso,ai da sauri mai gida ya wangame gate ,sai motocin suka danno cikin kamfanin da gudu,direct suka isa inda ma'aikatan suke a tsaye,motoci ne suka tsaya,da sauri bodygaurd suka firfita har da P.A sai kuma wani bodygaurd ya buɗe kofar inda Sadam yake ciki,ƙafarsa na dama ya fara fiddowa sai da yakai kusan mintuna uku kafin ya fito complete,Wooow! Wasu daga cikin ma'aikatan mata suka faɗa,nima mai ɗauko muku rahoto juyawa nayi don ganin meya sakasu irin wannan shauƙi haka, ai babu shiri nima na furta Wooow! Ba tare da nasan sanda kalmar ta fito ba,domin dole duk macan da tayi arba da Sadam ta ruɗe,saboda ɗan gaye ne na ajin farko,kyakkyawa ne sosai,ga sajensa yayi luf! Gwanin ban sha'awa,sumar kansa da gemunsa duk sun sha gyara,kai daga gani kasan ana kashe musu dollars,yanada tsawo amma ba can ba,gashi da faffaɗan ƙirji,kai in taiƙaice muku Sadam za'a iya kiransa da *Ingarman namiji* wato mai cikakkyan halitta,ga tsadaddun kayan da ya saka duk da farin yadi ne amma mai shegen tsada,ga hularsa mai ƙube ta asalin Maiduguri,agogansa ma abin kallo ne,ga zoben azurfa da yake maƙale a hannunsa na da shegen kyau,kai! Kai! Kai ! Abun dayawa,kar na cikaku da suturu lokaci ya ƙure,da sauri Sauban ya iso gunsa haɗi da russunawa yana gaisheshi,suma ma'aikatan haka sukayi,shi kuma gogan ko uhmm! Bai ce musu ba,saidai Mukhtar ke amsa musu gaisuwar.



Sauban yayi musu jagora ko'ina na kamfanin haɗi dayi ma Sadam bayani dalla-dalla cike da girmamawa akan yanayin yadda abubuwa suke gudana a kamfanin,sai daga baya kowa ya nufi office ɗinsa da murna domin kuɗi ne aka bi kowannansu dashi mai yawa.Office ɗin manager Sadam  nufa tare da Sauban da Mukhtar, a nan Sauban ya baje masa komswi dake tafiya a cikin kamfanin bisa tsarin Sadam, umarni Sadam ya bada a kira masa accountant shima yazo yayi masa bayani,ba'a ɗau lokaci ba saiga accountant yazo,shima kamar yadda Sauban yayi bayanihaka yayi shima,yadda kuɗi ke fita da shiga da duk abinda ya jiɓanci harkar kuɗi saida yama Sadam bayaninsa,tare dayi masa albishir ɗin asusun kamfanin ya ƙaru sosai ba kamar da ba,daɗi sosai Sadam yaji jin komai na Kamfanin na tafiya a yadda ya tsara.



Saboda wannan albishir da accountant ya bama Sadam, shima albishir ya bama su Sauban akan ya ƙarama kowani ma'aikaci dubu #5000 ga salarinsa ma'ana daga yanzu  an ƙara dubu #5000 ga salarin kowa.Wannan abu yama kowa a kamfanin daɗi harda ƙananun ma'aikata alkhairin ya shafa ,godiya tare da addu'ar gamawa da duniya suka shiga jera masa musamman masu shara,securities da masu gadi,bai ƙara awa ɗaya ba ya baro kamfanin zuwa gidan Aunty Nabila saboda ya gaji,yanada buƙatar hutawa.




*Cikin Labari*




"Maa shaa Allah Sadam, Allah ya tayaka riƙo tare da kawo maka mata ta gari,don gaskiya na ƙagara naga kayi aure Sadam"




Shiru yayi babu amsa,to mai zece mata shi da ko budurwa baida ita,ina shi ina aure yanzu,shi fa har yanzu baiga macen da yake ra'ayin aura ba,katse mishi tunani Dr. Nabila tayi cewa



"Hmmm daman nasan ba amsani zakayi ba,kaiɗin Sadam Allah yasama kanada budurwar"



"Aunt bazaki gane ba,wallahi har yanzu banga wacca ra'ayinta yazo ɗaya da nawa bane"



"Toooo daman sai ra'ayi yazo ɗaya ake aure kenan,hmmm mubar zancen don nasan baso kake ba,yanzu dai tunda kaine baƙo a gidan, me kake so a girka"


shiru ya ɗanyi tana tunani sai can yace



" Alkubus da miyar ganye  da pepper soup ɗin naman rago"



Taɓe baki Sa'eeda tayi a zuciyarta tana cewa 'yayaya da yayan ganye,mtws! Sai shegen iyayin tsiya,katse ta Dr. Nabila tayi da cewa



"Sa'eeda tashi ki girka mana alkubus da miyar ganye sai Jamila ta taya aiki tunda yayanki yana so"




"Wannan ce zatayi girkin"


Nuna Sa'eeda yayi,ɗagowa tayi Sa'eeda tana masa kallon irin yama rainata,Dr. Nabila tace



"Sosai ma kuwa,she knows how to cook sosai,don't worry kaida kanta zaka jinjina mata"



Taɓe baki yayi tare da cewa



"Hmmm Allah yasa"


Miƙewa Sa'eeda tayi ko kallon inda yake batayi b ta nufi kitchen ɗin tare da kiran Jamila don ta tayata aikin,nan da nan girki ya kammalu wanda sai wurin bayan magrib suka kammala,basu sukaci abinci ba sai bayan isha'i wanda daman haka al'adan gidan take.



A wurin cin abinci kamar yadda Dr. Nabila ta ce sai Sadam yayi santin abincin haka kuwa akayi,don ajiye miskilamcimlnsa yayi s gefe ya fara kwasar girkin Sa'eeda yana santi,Kauthar uwar surutu sai da ta ce


"Uncle Sadam girkin da daɗi ko?


Murmushi ya mata don babu bakin magana,itako Sa'eeda ko takan zantuttun da suke batayi ba tacigaba da cin abincinta hankali kwance.


Haka Sadam ya kwana gidan kasancewar akwai enough room a gidan su kuma P.A da bodygaurd ɗinsa a boys quarter suka kwana ,sai washe gari ya wuce Kebbi da maƙarrabansa,ita kuma Sa'eeda ta cigaba  da shirye-shiryan exams ɗinsu da first semester 400 level wanda baifi saura kwana biyar ba.



A ɓangaren Umman Sa'eeda jiki saidai mu ce Alhamdulillah domin lafiya ta samu,yanzu ma suna shirin tafiya Umrah tare da Momin Sadam sai daga baya su wuto Kebbi inda suma su Sa'eeda suna kammala exams zasu taho Kebbi domin yin ƙwarya-ƙwaryar walimar murnar dawowar Umman Sa'eeda da ƴarta cikin ahalinsu.Wannan kenan




           @ @@@@@@@@@@




A ɓangaren *LOVE BIRDS* 🕊️🕊️ wato Sauban da Maryam abubuwa sai a hankali duk da yayan Momin Sauban yazo tun daga Zaria don yayi sulhu akan Maryam ta koma gidan mijinta tayi haƙuri,amma ina ƙin haƙuri iyayen Maryam sukayi wai sai Sauban ya janye auran da yace zai ƙara don su a danginsu ba'a yin kishiya.


" Wannan ne baku isa ba"


Cewar Momin Sauban, harara da dalla ma Haj. Labara wacca ta ce sai Sauban ya janye auran daya ce zaiyi,ƙarawa tayi da cewa


"Aure wannan kamar anyi angama ne,kuma idan ma nan gaba yanada ra'ayin ƙara aure zai ƙara koda biyu ne kinga sai su cike hudun,zama da kishiya dole ne agareta,sannan ni *walki ce dede ƙugun kowa* duk wacca ta shirya nima na shirya,mu zuba mu gani"



Cikin ɓacin rai Haj.Labara ta bata amsa da cewa



"Ahhhayye chasssss! Ashe ko tsautsayi yana niyyar kaiki ramin kura,domin ba'a taɓa dangin mu a zauna lafiya,idan ke yanzu kika zo to mu a nan muka kwana,mu nan da kike ganinmu"


Nuna kansu tayi wato ita da Momin Maryam tare da wata ƙanwarsu Momin Maryam sannan ta cigaba da magana



"Mu Tsuliyar dodo ne wallahi! Wallahi! Wallahi duk wacca ta taɓamu to ta taɓoma kan bala'i da masifa,ke a hirɗin wallahi karan-batta damu babu daɗi fa,da munsa haka kuke da ko mutuwa Maryam zatayi wallahi baza mu bari ta auri ɗan iskan ɗanku ba"



Cikin masifa Momin Sauban ta ce



"Da nasani tabb! Ai ni nayi da nasanin haɗa zuri'ah daku,dangin marasa tarbiyya,baku koyawa ƴarku komai ba sai rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da ita shi ne kuke iya cewa kunyi da nasani,da nasaninku na banza da yofi"



Yayan Momin Sauban yayi saurin dakatar dasu da cewa



"Haba wani irin hauka ne haka,kuna manya daku amma kuke yin abu kamar yara,sasanci ya kawoni ba jin shirmanku ba,ni yanzu nazo kuyi haƙuri Maryam ta koma ɗakin mijinta kawai "



Momin Maryam ce ta ce


"Idan kaga Maryam ta koma gidan nan to sai Sauban ya janye magana auran da zai ƙara wallahi"



Momin Sauban ita ma a hasale ta ce



"Aure ko babu gudu babu ja da baya sai anyishi,idan kun gadama ku ƙara tarbiyantar da ƴarta tare da nuna mata sanin girman na gaba da ita ko kuma ku riƙe ta karta dawo gidan wannan ya rage ruwanku,amma ku sani babu Sauban babu sakin Maryam har abada ko bayan raina ban yarda ya saki Maryam ba domin saina tabbata muku da alfaharin da kuke akan danginku ba'a muku kishiya ni na kaudashi,domin dole Maryam ta zauna da kishiya"



Tashi tayi ba tare da tabi takan zantuttun da Haj. Laraba dasu Momin Maryam suke kamar zasu cinyeta da masifa ta wuce abinta,shima yayanta biyo bayanta yayi yana mata faɗa akan biye musun da dayi,murmushi tayi,sai da suka shiga mota tace


"Bari kajiYaya,ai rashin sani ne yaya na bari Sauban ya aura ƴar danginsu,duk da ƙawata ce Haj. Labara ta ƙut da ƙut amma bamu taɓa maganar kishiya da ita ba,shiyasa bansan yadda danginsu yake ba kuma koda tazo min da cewa, yarinya da Sauban yakeso ya aura bata da asali sai nace ya fasa auran yarinya kawai tunda bata da asali,sai ta sake cemin ko zai aura Maryam yarinya ƴar uwarta saboda tanada hankali da natsuwa,ban musa ba nace ya aure ta,ashe ashe shegiyar mata makirci ne suka ƙullama yarinyar da asali Sauban yakeso mu kuma bamu sani ba,saboda ƴarsu Maryam na mutuwar son Sauban shiyasa sukayi ƙulla-ƙulla haɗi da makirci duk don ya auri Maryam ɗin,dama ace tanada tarbiyyar wannan mai sauƙi ne,shegiya ce yarinya ta bugawa a jarida,bata iya kula da miji ba,rashin tsafta,rashin iya girki,ga uwa-uba rashin kunya duk ta haɗa"



Riƙe baki Yayan Momin Sauban yayi yana mamaki wato saboda rashin ta ido suke cewa wai baza a mata kishiya, ehhh lallai ai da sauransu dan ko nan gaba Sauban yace zai ƙara aure to saiya ƙara.Haka sukayi ta faɗa a mota har suka isa gidan Momin Sauban, shi kuma Yayanta ya wuce Zaria.Sai Momin Sauban ta cigaba da shirye-shiryan bikin ɗanta Sauban da Khairat.Wannan kenan.




            @@@@@@@@@@@@



A ɓangarensu Umma Kande da Maman Jummalo komai normal yake duk da ba wani kuɗi yake zuwa musu sosai ba kasancewar yanzu basa samun kuɗi ta hannun Nusaiba,summa kwana biyu basuji Nusaiba a waya ba,duk da ko'ina take a ƙasar waje saita kira Umma Kande tare da ce mata tana ƙasa kaza da kaza.Abban Sa'eeda kuma sai dai na abincin yau da kullum yake basu domin babu laifi yana matuƙar ƙokari da iyalinsa wurin ci da shansu.



Maman Jummalo dai an koma ga Allah,kullum idan su Jummalo da Iklima suka dawo daga Islamiya sai sun koya mata abinda aka koya musu, babu laifi abubuwa da dama na rayuwarsu Maman Jummalo, Iklima da Jummalo sun canja musamman yin sallah akan lokacinta,basa wasa da sallah,duk abinda suke da sun ji an kira sallah zasu miƙe suyo alwala haɗi da sallah,harda wa'azuzzukan malamai da dama a wayoyinsu,kullum cikin saurare suke musamman Maman Jummalo domin tayi yaƙinin gyara bayanta don lahirarta tayi kyau.Ita kuwa sha kundum uwar gayya Umma Kande ko ajinkinta hasalima da sun fara jin wa'azi zata tashi daga wurin ko kuma da wuce ɗakinta.Ta riga da ta gama imani da aikin boka(Wa'iyazubillah🤔🤔🤔)


A kullum gani take shirme suke yi,shiyasa yanzu bata shiga harkarsu harda ƴarta Iklima saboda wa'azin da take mata a kullum akan ta tuba kamar yadda Maman Jummalo ta tuba amma ina ta riga da tayi nisa bata jin kira.



Kasancewar yau Juma'ah babu Islamiya,su Iklima na tsakar gida tare da iyayansu suna hirar cikin farin ciki da annashuwa ga cikin Maman Jummalo sai girma yake,suna cikin hirar sukaji sallama tare da shigowa,maza ne su biyu sun saka nose mask suns riƙe da wata mata wacca na kasa gane wace ce har cikin gidan inda su Iklima suke da iyayansu suka kai matan tare da ajiyeta,da sauri su Iklima da su Umma Kande suka miƙe tare da toshe hancinsu saboda uban warin da matan take sai kace kashi,cikin tashin hankali Umma Kande tace




"Wazan gani ni Saratu!!! Nusaiba kece................





*Mu haɗu a pages na gaba my Esteem fans🙃🙃🙃✍️✍️✍️*




*wata sabuwa inji ƴan caca,tofa mai ya samu Nusaiba haka harda  kowa ya toshe hancinsa???ya akayi ta rame tayi baƙi???? Meke faruwa da ita haka???*........




*Da alama akwai drama babba tsakanin Sadam da Sa'eeda ganin yadda basa jituwa amma kuma zuciyoyinsu suma ayyan abu ɗaya??? To mene ne wannan abun haka???*......





*Love birds anata yaƙin duniya na uku anƙi karewa,ko yaushe zasu ƙare oho,shin Maryam zata haƙura da komawa gidan Sauban ko kuwa har yamzu sonsa na nan a zuciyarta???Wani irin shiri iyayen Maryam sukaye game da ƙarin auran Sauban ganin yadda ba'a ma danginsu kishiya???*....





*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥






*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments