TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 49-50

 4⃣9⃣----5⃣0⃣




"Ammm Dad nifa nayi kamu a gidan nan,Ina son Sa'eeda da aure,Dad a taimaka a bani ita"


Darammm!!! Dammm!!! Dammmm!!! Haka ƙirjin Sadam ya bada, baisan sanda ya ɗaga muryarsa cikin fushi  kowa yana jinsa yace


"Anyi mata miji!!! Sai kaɗau na annabawa kuma!!! "


Babu wanda a cikin ɗakin bai kalli Sadam ba,harta ita kanta Sa'eedar kallonsa take ƙirjinta na bada Ras! Ras! Ras! A zuciyarta tana cewa 'Miji? Miji? A ina? Yaushe? Waye? ' tambayoyi ne take ma kanta bila adadin domin maganar tazo bata a bazata,Momin Sadam ce taji maganar tayi bambaraƙwai,wai 'Anyi mata miji' kasa haƙuri tayi tare da cewa


"Sadam yaushe akama Sa'eeda miji wanda mu iyayenta bamu sani ba sai kai? "


Wuri-wuri yayi da idanunsa,shi sai yanzu ya tuno da katoɓar da yayi,Wayyo! Shikenan an ganosa,asirinsa ya tonu,yama rasa wasu kalmomi zaiyi amfani dasu wurin kare kansa karsu gane sirrin zuciyarsa.Shiru yayi babu amsa cak ya miƙe kamar wanda ƙwai ya fashe masa a ciki ya haura sama ba tare da ya kalli kowa a cikin falon,murmushin mugunta Kamal yayi,domin haƙarshi ta cimma ruwa,shi daman bawai yana sonta bane a'a kawai dai tun da yaga kallon da Sadam yake ma Sa'eeda zuciyarsa ta tabbatar da tabbas Sadam ya fada kogon soyayyar Sa'eeda sai dai shi kansa baisan da hakan ba,sannan ka mugun kishinta da yake numawa ra'ayul aini,daman ya faɗi hakan a gaban kowa don ya auna kishin Sadam akan Sa'eeda tunda miskilancinsa ya hanashi bayyana mata ƙaunar da yake mata,gashi tun kan Dad yace wani abu har mugun kishinsa akan Sa'eeda ya bayyanashi mararan a filin Allah Ta'ala,miƙewa Kamal ɗin yayi yabi bayansa,Dr.Nabila ce ta fara magana tana murmushi


" Ai ni daman tun sanda Sadam yazo gidana naga yadda yake santin girkin Sa'eeda nasan akwsi wata ƙasa,bai dai nuna bane saboda shegen miskilancinsa"


"Yoo gashi yanzu ya nuna mararan kowa ya gani daga jin Kamal ya ce yana son a bashi ita Shikenan tun kan Dad ya ce wani abu har ya yanke hukunci, Autan Momy sai Allah da malam gari" cewar Aunty Sakina tana dariya


Suma ƴan ɗakin dariya sukayi ganin kishin Sadam a bainan nasi,har Dad ma saida ya dara,Sa'eeda ce kaɗai abun bai bata dariya ba yooo wannan abun dariya ne,Mominsa Sadam ce cikin farin ciki marar misaltuwa ta ce


"Ai Shikenan sai ayi tuwona maina,dakan ɗaka shiƙan ɗaka,wanga batu yamin daɗi a rai"


Sum sum sum Sa'eeda ta mike tare da nufar kitchen duk da babu abinda zata ɗauko,kunya ce duk da lulluɓeta,ƙara tun tsirewa da dariya su Dr. Nabila sukayi wai ita ga mai kunya,Umman Sa'eeda taji daɗin wannan al'amari duk da bai furta yana sonta ba amma kishinsa ya bayyanasa ba tare dashi kanta ya sani ba.


Direct Sadam ya wuce bedroom ɗinsa tare da faɗawa kan gado,bai daɗe da kwanciya ba yaji sallamar Kamal,tsaki yayi shifa haushi Kamal yake ji ya rasa dalili,jin ba'a amsa sallamar ba Kamal ya shigo ɗakin har bedroom ɗinsa,da sallama ya shiga tare da cewa


"Assalam salam ango Sa'eedatu Baiwar Allah"


Tsaki yaja mai tsawo ba tare da ya ɗago daga kwanciyar ba ya ce


"Kai kasani kuma,nidai na fada maka tun wuri ka janye makaman yakinka domin mijinta ba kanwar lasa bane,kaje ka nemi wata "


Wata bazawarar dariya Kamal ya tintsire da ita,yi yake babu ƙakƙautawa harda bubbuga ƙafa,haushi dariyar Kamal tabama Sadam wato ya maidashi mahaukaci kenan kome,a harziƙe ya tashi daga kwanciyar yana cewa


"Ok nagane,wato ka maidani mahaukaci shiyasa duk maganar da zanyi zata zamo abin dariya a wurinka ko,fine"


Tsagaita dariya Kamal yayi ganin abokin nasa na niyyar yin zuciya kuma yasan halinsa da bakar zuciya ba ƙara bi takansa zaiyi ba,bayani ya fara masa da cewa


"Man! Calm down and understand me,wallahi ba son Sa'eeda nake ba,daman plan ne nayi don na auna kishinka tare da soyayyar da kake ma Sa'eeda wanda ka kasa bayyana mata,shiyasa nace bara na gwada tambayar auranta naji ya zaka ce,sai kuwa abinda nake harsashe akai ya tabbata domin tun kan Dad ya ce wani abu har ka bada amsa a gaban kowa ba tare da kaji shakku akai ba,yanzu in nine kai ajiye miskilancina zanyi a gefe tare da mika wuyana ga Sa'eeda"


Shiru Sadam yayi yana kallonsa wato daman plan ne yayi duk don yasa asirinsa ya bayyana, 'Oh God mai ya shiga ƙwaƙwalwana ne ɗazu da na gaza tuno da halin Kamal wurin iya shirya plans',murmushin gefan baki Sadam yayi tare da cewa


"Hmmm wato shiryamin tarko kayi Kamal, ya maka kyau tunda kasa na fallasa sirrin zuciyata a bainar nasi"


"A'a fa bainar iyayenka ne,kuma hakan yamin daɗi a rai,look Sadam don Allah ka cire wannan shegen miskilancinks tare da jiyeshi a gefe don Allah ,show her your love,show her your care,show her she is the only woman in  this whole  planet you love and care for,mata suna son mai nuna musu so,ƙauna tare da kulawa,kaga ni yanzu maganar da ake har iyayen sun shiga ciki,maganar aure ake yanzu, kaima idan ada baka da wacca zuciyarka take so to yanzu ai akwai,kawai ka bada kai malam bori ya hau"


"Kamal bansan yadda zan fuskanci yarinyar bane wallahi, she's so confident and bold,tana da kwarjini sosai,kullum tunanin yadda zan fuskance nake amma na gaza samun wannan ƙarfin gwiwar"


"Karka damu da wannan yanzu tunda kowa yasan da irin son da kake mata shikenan,kai kuma sai ka dinga nuna mata soyayyar ka a fili,don nasan itama daga gani tana sonka,nifa nagane ku tun dazu a wurin taro,kowa na begen ɗan uwansa amma kun kasa bayyana ma junanku abinda yake a cikin zuciyarku"


"In shaa Allah zanyi yadda kace,nagode sosai da shawarka dan uwa,plans ɗinka ya tafi a yadda ya dace"


Shaking hands sukayi suna dariya,Kamal bashi yabar gidansu Sadam sai wurin 9:15pm na dare tare da yima ƴan falon sallama kasancewa suna nan suna hira har ya sauko.Tun daga wannan rana Sa'eeda ta fara wasan ɓuya da Sadam,batason su haɗu ko wurin cin abinci ne,idan taji tsayuwar motocinsa sai ta miƙe tayi sama,Ummanta dai na sane da takunta,a zuciyarta tana cewa 'Zama ki bari yarinya duk randa aka kaiki ɗakinsa'


Wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin Momin Sadam da Sa'eeda domin tun a ranar da ta fara ganin Sa'eeda tama Sadam sha'awar auranta saboda natsuwa da tarbiyyarta,sai gashi shi da kansa ya bayyana kansa.


Sati Uku aka basu Sa'eeda a school,yanzu sunci sati ɗaya a gidansu Momin Sadam, Umman Sa'eeda da Momin Sadam  zasu  z wuce can family house saboda yau za'ayi maganar tafiyarsu Abuja wurin Haj. Zulfa'u don tunkararta kawai ayi a wuce wurin tare da magana gadonsu na kotu.Suna zaune a dining area suna karyawa duka family harda Sadam wanda hankalinsa kusan akan Sa'eeda yake, kowa a wurin yana sane da abinda yake harda Dad,ita kuma Sa'eedar duk taji ta takura saboda irin kallon da yake mata daman ya daɗe bai gamta ba saboda duk hanyar da zai samu don ya kanta ta yanke ta ko break fast ma batayi a dining room,yau ne Mom ta ritsata akan tare da kowa zata karya babu yadda ta iya,shiyasa yace bara ya kalleta son ransa tunda ta daƙile hanyoyin da zai dinga ganinta.Baida niyyar bayyana mata soyayyarsa a Kebbi,yafiso sai sun dawo Kaduna sai yaje can yayi sati ɗaya,tun da kamar a nan tana jinta a takure take ba kamar Kaduna ba,haka kowa ya kammala break fast ɗinsa tare da barin dining area ɗin,su Momin Sadam da Umman Sa'eeda suka fara wucewa can family house ɗin saboda uncle Hassan da wani abokin Baba Garba na Kusfa-Zaria sukazo tare duk saboda maganar tafiyarsu Abuja ne,malami ne na addini wanda Allah ya bashi baiwar sanin makarin sihiri kowani iri,duk da ya tsufa amma kuma saninsa na nan bai gushe ba.


Su Dr. Nabila da yayyin Sadam sai anjima zasu je can family house ɗin, daman haka Sadam yakeso wato Mominsa da Umman Sa'eeda subar gidan don yaga alama su Sa'eeda take jin kunya,Uwar surutu ya kira wato Kauthar,ce mata yayi taje tace Dad na kiran Sa'eeda a garden zata amshi saƙo ,babu musu ta ruga aguje zuwa kitchen inda Sa'eeda take da mai aikinsu tana tayata aiki,tana haki tace


"Aunty Daddyn Sadam yace kisameshi a gardan zai baki saƙo ki kawo ciki"


"To Cwedy gani nan zuwa"


Tsam! ta cire hannunta a aikin da take yi tare da nufo garden ɗin,zuciyarta na dukam uku-uku tana tunanin wani irin saƙo ne haka da har sai tazo garden sannan zata amsa,hango mutum tayi duk da bayansa take gani amma saida gaban ya faɗi,don wannan jikin bana tsoho bane,haka ta tako wurin kujerun da suke a gadin ɗin masu kyau da tsari,yana jin takunta amma sai ta share,bari yayi sai tazo gabansa kafin ya miƙe,don yanaso yakai ƙarshan ɓoye-ɓoyen da take kafin yazo Kaduna ayita ta ƙare,har inda yake taje haɗi da sallama duk da bata ƙarasa har gabansa ba,miƙewa yayi tare da amsa mata yana murmushi,ita ko lokaci guda ta ruɗe tana inda-inda haɗi da cewa


"Umm ummm don Allah bakaga Dad ba a nan wurin,yace nazo na amshi soko ne"


Tabe baki yayi still yana kallonta,kamar bazaiyi magana ba sai kuma can yace


"Ni na aiki Kauthar ta kiramin ke,babu wani Dad,ɓoye-ɓoyen da kike akaina ya isa haka Sa'eeda"


Yammm! Haka jikin Sa'eeda yayi saboda kusancin da yake tsakanunsu,ta kasa ɗago kanta ta kallesa saboda jin kaifafan idanunsa akanta,'wayyo Allah ni Sa'eeda anya wannan mutum ba maye bane,idan ya fara kallon mutum baya gajiya,mtws! ' turo baki tayi waje  sannan ta fara magana cike da shagwaɓa


"Um um um ni nace ma ina ɓoye-ɓoye ne,ka wani zo ka cika mutum da mayatattun idanunka masu tsoratar da mutum"


Dariya taso bashi amma ya dake,yadda take magana is just woow! Sai kace ana *Busa Sarewa* her voice is so sweet and innocent,gyara tsayuwa yayi sannan yace


"Hmmm wannan bakin wallahi idan bakiyi wasa ba saini cinyeshi wataran,da anyi magana saiki wani turo ɗan ƙaramin bakinki waje ke ga mai tsiwa ko,fine zanzo Kaduna next month kuma one good week zanyi a gidan Aunty Nabila,akwai batuttukan da nakeso muyi idan nazo gidan,shi ne ma dalilin kiranki da nayi,abinda yasa nace Kauthar ta ce Dad ne saboda zaki fi zuwa amma idan ni ne wallahi ba zuwa zakiyi ba,yau  da ƙarfe 12:00pm na rana jirginmu zai tashi zuwa China,zanyi sati huɗu a can saboda wasu muhimman abubuwa da zanyi na game da business ɗina,immediately na dawo da kwana uku zan shigo Kaduna,ungo wannan"


Bandir ɗin #500 har uku ya miƙa mata,ita ko ta amshe abinta.(My Esteem fans yaushe Sa'eeda tasan daɗin kuɗi haka,ko jan aji babu chaiiii😂😂😂🙃🙃🙃🙃)


Cigaba yayi da cewa


"Manage this ok,zan amsa numbanki gun Aunty Nabila, we will talk on phone idan na sauka"


"Allah ya tsare hanya"


Haka bakinta ya furta,kunya abin ya bata,'wai Allah tsare hanya' zata wuce yace mata


"Ki kulanmin da kanki"


Rasss! Haka ƙirjin Sa'eeda ya bada 'ki kulanmin da kanki? ' yaushe muka fara haka dashi ne,da sauri tabar garden ɗin ba tare da ta waiwayo ba,shi kuma kallon inda tabi yayi da idanu tare da sakin murmushin gefan baki.Su Sa'eeda sun riga Sadam barin gidan zuwa family house,shi kuma sai daga baya bodygaurd ɗinsa da P.A ɗinsa wato Mukhtar suka iso,babu jimawa suka hau hanyar zuwa Airport wanda tare da Mukhtar Sadam zaiyi tafiyar.


A can Family house ,su Momin Sadam da Umman Sa'eeda su iske su ake jira,direct falon tsoho mai ran ƙarfe Baba Garba suka nufa saboda a can ne zasuyi meeting ɗin,da sallama suka shiga falon,mutane huɗu ne a cikin ƙyataccan falon Baba Garba mai cike da kyau da tsari saikace ba falon tsoho ba,Baba Garba ne da wani dattijo sa'ansa  suke zaune da two seater,sai Uncle Hassan da Kabir wanda ake kiransa da mai Babban gida suna zaune a one-one seater,zama su Momin Sadam sukayi a three seater,tare da kai gaisuwa da dattijan sai daga baya suka gaisa dasu Uncle Hassan,Baba Garba ne ya nuna wannan dattijon tare da cewa


"Wannan shi ne Malam Bala Mai Carbi,aminina ne tun ƙuruciya,malamin addini ne sosai kuma Allah ya bashi baiwar sanin makarin sihiri kowani iri ne,bayan taron da mukayi da kwana biyu na kira wayansa  akan zuwan mu Abuja tare da yimishi bayani ita matar,sai yace ns bari yayi Istikhara tukunna,washe gari ya kirani akan al'amarin Zulfa'u babba ne,bazamu taba iya zuwa gidan ba,saboda bokanta ba ƙaramin sihiri yayima gidan gaba ɗaya ba,shigarsa akwai wahalar gaske amma yanzu Hassan yazo dashi domin yayi mana bayanin yadda zamu shawo kan wannan al'amarin na Zulfa'u"


Gyaran murya Malam Bala Mai Carbi yayi,sannan ya fara magana cike da dattaku irin na manyan malamai


"Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah"


Saida suka amsa kafin ya cigaba da cewa


"Bayan istikhara da nayi game da ita wannan mata,a gaskiya shigarku gidan kai tsaye ba zaiyu ba,saboda sihirin da gidan yake tattare dashi ba ƙarami bane,don haka nima zan shiga tawagar masu tafiya zuwa Abujan tare da amintattun Almajirai na kuma hafizai,bayan haka tafiyar tamu akwai sharudɗa uku a cikinta,sharaɗin farko shi ne idan har da mata zamuje tafiyar to da wa'inda basu da najasa zamuje dasu wato masu *jinin haila* sai kuma zai zama idan muna hanyar tafiya kowa zai dinga *istigfari* na ƙarshen kuma mai muhimmancin shi ne,duk wanda yasan dashi a tafiya to dole tun daga yau ɗin nan zai fara karatun Al Qur'ani mai girmu zuwa nan da sati Uku ta yadda zai kammala sauke Al Qur'ani mai girma,kowa a cikinmu dole ne yayi idan har dashi za'ayi tafiyar,sannan idan munje gidan karkowa yace wani abu saina bada umarnin haka,driver ma kansa saiya sauke Al Qur'ani mai girma sannan za'ayi tafiyar dashi,domin wacca zamu fuskanta da bokanta wanda yake rabi mutum rabi dabba dole muyi taka-tsatsan,matar tana aiki da shaiɗanin boka sannan ta sadaukar da ruhinta ga aljanun da take ma aiki,sannan akwai wani ruhin na daban a jinta wanda idan yana jikinta bazata taɓa yin tsufa ba,don hakan kowa ya fara shiri tun daga yau ɗin nan"


Shiru ɗakin yayi baka jin motsin komai sai A.C dake sanyaya ɗakin,sai can Baba Garba ta fara magana bayan ya nisa


"To kunji sai sharudɗan Malam Bala,don Allah kowa ya fara shiri tun daga yau ɗin nan,da yaddar mai sama zamuyi nasara akan Zulfa'u da hatsabibin bokanta, dole ne mu kawo ƙarshan matar nan da yardar Allah"


"In shaa Allahu Baba Garba tun yau zamu fara shiri,kuma zamubi sharudɗan Malam Bala" cewar Momin Sadam


Haka kowa ya amince da sharudɗan Malam Bala,sannan Malam Bala ya koma Zaria,tun a ranar aka sanar ma amintattun drivers ɗin da za'ayi tafiyar dasu,suma  tun a ranar suka fara karatun Al Qur'ani mai girma.


Sa'eeda da Dr. Nabi'a sun kwashe kusan sati uku chur! A Kebbi state kafin suka ɗungumo zuwa Kaduna,wanda babu jimawa suka koma makaranta har su Kauthar daman suma hutun sukeyi,su kuma su Uncle Hassan da Umman Sa'eeda tare da wa'inda zasuyi tafiya kowa sai shiryawa yake,Allah ma ya ƙaddara babu wacca a cikin matab zatayi jinin haila a wannan lokacin kamar haɗin baki.Wannan kenan




         @@@@@@@@@@@@



*KADUNA*



Wani ɗaki ne ɗan ƙarami mai ƙofa babu window,gashi duka bango ɗakin akwai rubutun larabci ko kuma ayayoyin Al Qur'ani shi dai gayanan ban iya gaee abinda aka rubuta duk bin  ƙwakƙwafina da gulmata nayi-nayi amma ina haka na haƙura da ɗauko muku rahotan rubutun ɗakin,wani malami ne yasha babbar riga,ga sharɓeɓan carbi mai ƙafa dubu a hannunsa na dama,a gaban kuma wani  abu ne mai faɗi mai kama da faranti wanda bansan sunansa ba,baƙar ƙasa ne a cikin abun,hannunsa na hagu yake amfani wurin zane-zane a ƙasar amma bansan me yake zanawa ba.Haj. Laraba da Momin Maryam ce suke gurfa ne a gabansa suna jiran mai zaice bayan sunyi mishi bayanin abinda ke tafe dasu,an ɗau tsawan lokaci  malamin yana duba tare da zane-zane amma bai ɗago kansa ba,saima uban gumi dake tsuttsugo masa a bisa goshinsa har wuyansa,can malamin ya dago kansa tare da sharce gumin daya tsatsubu masa da handkachef sannan ya fara magana cike da damuwa


"A gaskiya bazaku iya da wannan matar ba,domin tafi ƙarfunku ta ko'ina,yaran da kukeso ayi aiki akansa shima a kafe yake, baya saba umarninta koda wasa,da manyan malaman  *KUSFA* take aiki,ko'ina zakuje ɓata kuɗinku zakuyi domin taɓasu bala'i ne ba gareku kaɗai ba harda wa'inda sukayi aikin,shawara ce agareku ku janye makamanku akan matar nan,ku naimi wata hanya ba wannan ba,amma fa idan kunji"


"To ita wacca shi yaron zai aura bazaka iya aiki akanta ba"


"Aa'aahhh! ina babban bala'in kenan,ai ɗiyar wani babban malami ne a Zaria,taɓata kamar soka wuƙa ne a cikin mu baki ɗaya,nidai shawara ce na baku,ku naimi wata hanyar"


Haka su Haj. Labara da Momin Maryam suka bar ɗakin cike da ɓacin rai da damuwa,badu dandara ba suka sake zuwa wurin wasu malaman tsubbu har uku amma duka maganar ɗaya ce bazasu iya da ita ba tafi ƙarfinsu,sune har Niger amma basu dace ba,haka suka tattaro zuwa Nigeria tare da zubama sarautar Allah ido.


Maryam kuma duk tabi ta tashi hankalin Mominta akan ita ta gaji da zaman gidan zata koma gidan mijinta tunda tana sonsa,babu yadda ba'ayi da Maryam ta haƙura da gidan Sauban amma fafur taƙi ji,haka suka kyaleta ta fara shirye-shiryan komawa gidan Sauban.


A ɓangaren Sauban kamar yadda Mominsa ta ce  a ɗaura auran kafin Khairat ta dawo haka kuwa akayi,sai bayan ɗaurin aura da sati biyu Khairat da dawo ƙasar complete kasancewar ta kammala karatunta,bautar ƙasa ya rage yanzu tayi wanda a gidan Sauban ɗin zatayishi,walima akayi sannan ta tare a gidan Sauban, kasancewar part ɗinsa babba ne,shiyasa abin yazo a daidai,ita ta ɗau part ɗaya Maryam ta zauna a part ɗaya.


Tabbas ba ƙarya kamar yadda Momin Sauban ta ce ƴar mutunci ce,maganarta dutse domin har wata ƴar ƙiba Sauban ya fara tare da ƙyallin angonci wanda bai samu wurin Maryam ba,gata da kyau daidai misali,ta iya girki babu laifi ga sanin ya kamata,saboda ɗiyar malamai ce,ta taso gidan tarbiyya da sanin ya kamata.


A satin Khairat na uku da tarewa saiga Maryam ta diro gidan kamar diran mikiya,babu ko sallama ta shigo part ɗinsu,direct ɗakinta ta nufa wanda yana nan a yadda yake,babu gyara fashe-fashan da tayi duk babu abinda aka ɗauke balle tunanin gyarawa,haka taɗan ɗauke abubuwan da suka fashen tare da ɗan rarrabke ɗakin duk da ba wani gyaruwa yayi ba,da daddare saiga Sauban ya shigo gidan da mamaki ya nufa part ɗin Maryam ganin wutan ɗakin a kunne,yana shiga ya sameta tana zaune a falo indomie a gaban da ƙwai tana ci,zama yayi akan one seater yana binta da kallo,ita ko sai cin jagwalgwalan girkinta take abinta,sai can yace da ita haka ake yima miji sannun da zuwa babu gaisuwa,daman kamar jira take ta fara balbalin masifa,ta inda take shiga ba a nan take fita,tsam! Sauban ya miƙe ya fita abunsa ba tare da ya saurari masifarta ba,yooo tunda akwai inda sai taɓa yaji sanyi ai shikenan ta shekara tana masifar.


A ɓangaren zamantakerwasu da Khairat babu mai shiga harkar wani kowa yana nasa bidirin ne,ita Khairat bata shiga sabgar mutum koda Maryam ta takale sai dai ta shige ɗaki abinta.A ɓangaren girki kowa nasa yake,haka rabon kwana ma bibbiyu yake a ɗakin kowacce,idan yana a ɗakin Maryam baya da kwanciyar hankali,ko abincinta ma baci yake ba,kullum cikin masifa da bala'i suke.Wannan kenan




           @@@@@@@@@@@


  


*ABUJA*



A ɓangaren Haj. Zulfa'u hankalinta ba'a kwance yake ba duk da kwanan nan suja gana da bokanta kuma ya tabbatar mata zai kareta da duk kariyarsa sannan kuma ya zagaye gidan da duk shaiɗanun aljanunsa harda estate ɗin gaba ɗaya,babu yadda zasu iya shigowa gidan har suyi ido biyu da ita,duk da wannan albishir da boka Burumbuɗu yayi ma Haj. Zulfa'u hankalinta ya gaza kwanciya,gashi kamar haɗin baki duka yaranta su ukun sun zo gidanta har Momin Fadila ta UK kuma kwanaki zasuyi saboda mai aikinta ta sanar musu a ɓoye halin da Hajiya take ciki kuma tace don Allah kar suce ita ce ta sanar musu,kawai suce ra'ayin kansu ne yasa suka zo,Haj. Zulfa'u tayi-tayi dasu akan kowacce ta komai gidanta don ita lafiyarta lau amma sunƙi komawa,haka ta haƙura kawai,koma miye ayita ta ƙare saboda ta riga da ta karaya gabaki ɗaya saboda mugayan mafarkan da take da tsatson maƙiyiyarta zasu zo gareta.



Yau Haj.Zulfa'u ta tashi da mutuwar jiki wanda ta rasa mai ya assasa hakan,idanunta duk sun sauya kala,ga faɗuwar da gabanta yake akai-akai,babbar ɗiyarta ce tace ko a kira mata likita amma ina taki yarda,fadama ta fara mata akan ta ce su koma gidansu amma sunƙi,haka ta fito falon bayan ta karya a dining area,suma yaran nata falon suka dawo tare da zama suna hirarsu hankali kwance,ga TV a kunne,idanun Haj. Zulfa'u kyar a TV amma hankalinta ba'a a can yake ba,ta shiga dogon tunani ne.


A ɓangarensu Uncle Hassan dasu Umman Sa'eeda yau ɗin nan suka shirya tunkarar Haj. Zulfa'u da bokanta,domin kowanne a cikinsu ya sauke izu sitin a sati ukun da Malam Bala Mai Carbi ya umurcesu da suyi,haka-zalika Umman Sa'eeda da Momin Sadam babu wacca a cikinsu take jinin haila,tawagar mutune goma ce,Malam Bala Mai Carbi sai amintattun ɗalibansa su huɗu,sai Tsoho mai ran ƙarfe,Mai Babban gida wato Kabir,Uncle Hassan,Umman Sa'eeda sai Momin Sadam haka suka ciga motoci har uku,drivers ɗin motocin ma duk sun sauke Al Qur'ani mai girma, haka ƴan uwa da abokan arziki suka shiga yi musu adduar nasara tare da tsarin Ubangiji agaresu,haka suka dugunzuma hanyar Abuja,kasancewar Uncle Hassan yasa a mishi binciken gidansu Haj.Zulfa'u, address ɗin gidan aka turo mishi ta whatsapp wani abokinsa,basu suka isa Abuja ba sai wurin  2:00pm  na rana,haka suka nufi address din da aka basu,suna isa estate ɗin komai ya koma fili kamar ba'a taɓa gini ba,mamaki ya cika kowannansu banda Malam Bala Mai Carbi daman yasan hakan zata faru kuma a shirye yake dasu,cema driver yayi ya tsaya da motar,babu musu driver ya tsayar da motarsa,motocin bayan suma suka tsaya,fitowa Malam Bala Mai Carbi yayi tare da kallon gabas yayi addu'a,ya kalli yamma shima yayi addu'a,kudu da arewa duka ya tofe da addu'a,sannan ya kalli saman nan ma yayi addu'a, haka-zalika ƙasa ma yayi mata addu'a kamar a mafarki saiga gidajen estate ɗin sun bayyana kamar walkiya,shiga motar sukayi tare da tafiya zuwa cikin estate ɗin tare da addu'o'i a bakunansu,har daidai address din gidan da aka ba Uncle Hassan sukazo,gida ne babba wanda yafi kowanni gida girma,kyau hadi ta tsari,sauka dukkaninsu sukayi daga motocin,Malam Bala ne ya ce su biyo bayanshi sannan kowa ya kashe wayarshi,kar wanda ya kuskura yayi magana sai ya umurcesu da suyi,haka kowa ya fito ta wayar tare da kashewa,haka suka dosa gidan amma ga mamakinsu sai gidan ya koma *Daji* mai duhun gaske,Malam Bala bai damu da gidan ya koma daji ya cigaba da tafiya cikin dajin,a zahiri ƙofar gidan a buɗe take shiyasa suka samu daman shiga,a baɗini dajin Allah ta'ala ne wanda baida ƙarshe,babu abinda kakeji a cikin dajin sai kukan karnuka da na mujiya,haka sukaita tafiya cikin dajin Malam Bala Mai Carbi na gaba suna biye dashi tare da addu'o'i a bakunansu,wasu irin halittu ne marasa kyawun gani suke a tsattsaye a gefansu,duk sun tsura musu idanu,halittu basu da kyawun gabi,babu wanda ya kallesu suka cika da tafiya,a zahiri gidan babba ne sosai domin kafin kaje asalin cikin gidan saikasha tafiya,su kuma motocin sun barsu a waje,masu tsura musu idanu kuma ma'aikantan gidan ne ganinsu da yawan gaske,a baɗini haka suka isa har gindin wata bishiyar tsamiya wacca akwai ƙofa a gabanta sannan a saman ƙofar boka Burumbuɗu ne fuskarsa a murtuke yake kallansu,a zahiri wani baƙin tsuntsu ne a saman ƙofar yana tsaye yana kallansu yaƙi wucewa,Malam Bala ya fara magana


"To la'anan ne yau ƙarshanka yazo kaida mai bauta maka,in shaa Allahu zamuyi nasara a kanku"


Boka Burumbuɗu ne ya tsintsire da dariya,duka ilahirin ƙasar wurin sai girgiza take,babu wanda a cikinsu ya tsorata,sai can ya fara magana cikin amon muryarsa mai firgitarwa


"Ƙarya ne,dole ku koma saboda mune  zamuyi nasara akan kun....."


Bai ƙarass maganar Malam Bala Mai Carbi ya fara karanto addu'o'i yana tofa masa,lokaci guda boka Burumbuɗu ya fara ƙaraji hadi da ihu wanda ya cika ilahirin dajin,a zahiri baƙin tsuntsun ne yake kuka sosai,sai kuma can ya ɓace kamar walƙiya,a baɗini kuma boka Burumbuɗu ne yake ƙonewa tare da ɓacewa lokaci guda,nan take asalin ƙofar ɗakin ta bayyana,dajin ya ɓace,idanunsu Malam suka koma ganin asalin gidan,kabbara sukayi tare da hamdala sannan,Malam ya umurci Uncle Hassan da Umman Sa'eeda su riƙe hannun junansu ya tare da fara shiga ɗakin da ƙafar dama hadi da sallama kasancewar ƙofar ɗakin ita kanta a buɗe take kamar ansan da zuwansu,kamar yadda Malam Bala Mai Carbi ya umurcesu haka sukayi,tare da shiga ɗakin da ƙafar dama haɗi da sallama.


A ɓangaren Haj Zulfa'u duk takun da su Malam Bala Mai Carbi sukeyi tare da bugun ƙirjinta suke, tana a haka sai can taji magana a iska ana cewa


"Lokacin girbar abinda kika shuka yayi Zulfa'u!!!, mu mun tafi!!! Ƙarshanki yazoooo!!! "


Ai tuni Haj Zulfa'u ta mike jikinta na rawa tana fuskantar ƙofar ɗakin kamar tana jiran wani abu,suma yaran nata suka mike lokaci guda ganin ta mike,kamar jira maganar ake ta wuce saiga su *Uncle Hassan da Umman Sa'eeda* sun shigo ɗakin da sallama..............






*Yau akeyinta a gidan Haj. Zulfa'u, mu haɗu a pages na gaba,domin akwai🔥🔥🔥🔥,kar kuyi missing next pages my Esteem Fans domin  akwai 🔥🔥🔥🔥🙃🙃🙃🔥🔥🔥✍️✍️✍️✍️🌹🌹🌼💖*




*Ali yaga Ali,kura taga damisa,ga Haj. Zulfa'u ga su Uncle Hassan da Umman Sa'eeda koya zata kaya????*.....



*Maryam dai an haƙura an koma gidan miji,koya zaman nasu zai cigaba da kasancewa????*.......



*Da alama dai Sadam ya fada tarkon so da ƙaunar Sa'eeda,shin zata aminta dashi ganin abaya an yaudareka ko ko yaya???*.......



*Wai ina Haj. Nusaiba mai pampers da uwar gayya Umma Kande,wace gwaramar suke ciki????....




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥




*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘






*Daga alƙalamin* 

🖍️📚*Narrnarhh Bukar* 📚🖍️



*Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah*.




Post a Comment

0 Comments