TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini 21 -- 22

 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️

                           


Narrnarhh Bukar✍️


🌹Perfect Essential Writer's

Association🌹

  ✨ P. E. W. A✨





Wattpad:@AISHAABUBAKAR812

Arewabook:@Narrnarhh002





🌹🌹🌹I'm  not born to be a writer but born to be a great professional writer✍️✍️✍️🙃🙃🙃🌹🌹🌹



🤗🤗🤗Special greetings to y'll my Esteem fans,i love y'll💝💝💝💝🤗🤗🤗





2⃣1⃣----2⃣2⃣




"Kwantar da hankalinki duk wannan kururuwan da kike bashi bane bafita Ƙawas"


"To mai kike so inyi bayan hankalin Babansu Nusaiba ya fara karka garesu, wallahi nasan kashina ya bushe idan na bari hankalinsa ya koma kansu"


"Haba don Allah nace ki kwantar da hankalinki ko,zamu samu mafita akan wannan lamarin,ke bari ma kiji akwai mafita amma mafitar ɗaya ce garemu yanzu "


"Akwai mafita kika ce Maman Jummalo,to mecece mafitar? "


"Ba wata mafita bace illa mu shiya ranar lahadi muje wurin boka Sankeru,ita kadai ce mafitar tamu kinga sai ya duba yaga ko asirin ne ya warware"


"Haka ne kuma,kin kawo shawara mai kyau amma anya zan iya bari har lahadi Ƙawas,lahadi tayimin nisa ji nake kamar yanzu na ganni gaban boka Sankeru,ko hankalina zai kwanta"


"Haba Saratu,kin cika gaggawa a al'amuranki wallahi ina nan ina ranar lahadi,kin manta yau alhamis baifi saura kwana biyu ba amma duk kin bi kin tada hankalinki a banza,haba don Allah"


"Allah ya kaimu ɗin"


A haka Maman Jummalo ta cigaba da kwantar ma Umma Kande hankali har ta natsu,sai daga baya ta wuce ɗakinta ,sallar subh ma da  ta ce zatayi tafasa sai bayan ta dawo daga wurin boka Sankeru zata cigaba da sallah.(Ohhhh niii!!! Duniya ina zaki damu🤔🤔🤔,wannan wani irin jahilci ne haka,kai! Kai!! Kai!!!,to Allah ya kyauta🤔🤔🤔).


Haka duk wunin ranar jikinta a sanyaye yake,abinci ma sai da Maman Jummalo ta lallabata sannan ta samu taci shima kaɗan,duk tayi sukuku da ita kamar mai ciwo ko kuma ance  wani shaƙiƙinta ya rasu haka take ji a jikinta.



                    @@@@@@



Bayan su Sa'eeda sun fito waje sai ta dubi Ummanta tace


"Ummina kinga ikon Allah ko"


"Haka ne sanyin idaniyata,tabbas wannan  ikon Allah ne ba na mutum ba,amma a gaskiya nayi mamakin sauyawan Abbanki lokaci guda haka"



"Nima haka Ummina,Allah shi ne abin godiya"


"Haka ne kuwa Allah shi ne abin godiya, don ba yin mu bane,nufin Allah ne"


"Hakane Ummina,kinga kuɗin nan da ya bani saina ƙara kuɗin mota sannan zanyi sadakar naira dubu ɗaya wa almajirai ko ya kika ce Ummina"


"Wannan haka yake,Allah dai ya cigaba da maido da hankalinsa gare mu"


"Aameen Aameen Ummina"


Haka suka cigaba da hira har  kowa ya nufi hanyarsa.



                @@@@@@@@



Cigarta aji keda wuya saiga Maryam itama ta shigo,murmushi Sa'eeda ta sakarma Maryam sai itama ta maido mata da ɗan murmushi wanda bai kai zuciya ba, babu yabo babu fallasa a fuskar Maryam ta gaida Sa'eeda don yanzu Maryam ta fara jan baya baya da Sa'eeda dalilin samun ƙawaye ƴan gayu masu ji da kuɗi tare da class da tayi.


Yanzu ko karatun da Sa'eeda ta ke koyama Maryam ta daina saboda yanxu Maryam bata ce mata ta koya mata karatu,kusan yanzu Maryam hankalinta yafi karkata ga ƙawaye da gayu,sun haɗe kai su biyar wanda har suka sama group ɗinsu suna da (high classic babes squad).Duk yaran masu kuɗi ne sosai,asha wanka iya wanka sannan a ratayo fashion bags ana yanga amma brain ɗin empty😁😁😁.


Akwai lokacin da Sa'eeda ta taɓa samun Maryam da magana akan ko ta mata laifi ne yanzu take jan baya baya da ita,sannan yanzu kuma bata son suna tafiya gida tare,babu komai Maryam ta iya ce ma Sa'eeda kawai yanzu bata da ra'ayin tafiya gida tare da ita ne,shi kenan Sa'eeda ta ce da Maryam ta wuce abinta,tun daga ranar bata sake yiwa Maryam magana ko kuma ta ce su tafi gida tare ba, saidai idan ta ganta tayi mata murmushi sai ita ma Maryam ɗin ta maida mata.


Karatunsu ya fara zafi yanzu kuma suna gab da fara first semester exams ɗin na 200L,gashi Vice Chancellor ya ce continous semeter zasuyi babu hutu,shi yasa lecturers suke  zafafa musu da karatu babu ji babu gani saboda lecterers ɗin suna so su kammala lectures ɗinsu complete kafin a fara exams.Wannan kenan.


A haka a haka har lokacin exams ɗinsu yayi suka rubuta exams dinsu cikin nasara da aminci musamman Sa'eeda da take karatu babu kama hannu yaro.


Suna kammala exams ranar Friday suka fara karatun second semester 200 level  ranar Monday duk da ba duka ɗaliban suka zo ba kasancewar basu daɗe da kammala exams ba amma lecterers  suka ɗaura sabon babi a karatun nasu.



            @@@@@@@@@@@@



Ɓangaren Sa'eeda da Sauban baza muce komai ba don suna soyayya sosai,Sa'eeda har ji take anya zata iya auran wani inba Sauban ba,zata iya zama ta rayu da wani wanda ba Sauban, a kullun wutar soyayyar Sauban a cikin zuciyar Sa'eeda ƙare ruruwa  take.Sauban yana nuna mata tafi kowacce mace daraja a idonsa kuma ita kaɗai  ce a cikin zuciyarsa.


Sauban yanzu ya gama gane Sa'eeda ta  mutu a so da ƙaunarsa sosai,don wani lokaci idan bai kirata a waya ba ita take kiransa taji lafiya kuwa,hakan na mugun yima Sauban daɗi a rai don yanzu haƙarshi ta cimma ruwa.



Wanene Sauban?



****Sauban Muhammad  Ja'afar Ƙaraye shi ne asalin cikakkyan sunansa,wanda shi ne ɗa na uku a familinsu,su biyar ne mahaifiyarsu ta haiha,yana da ƙanne  biyu mata tare da yayyi biyu duk maza,mahaifinsu asalin ɗan ƙauyen ƙaraye ne a jihar Kano,ita kuma mahaifiyarsu ƴar Zaria ce a jihar Kaduna.


Muhammad Ja'afar Ƙaraye cikakkyan ɗan kasuwa ne amma baiyi karatun boko  ba kasancewar a ƙauye ya taso,a lokacin da yake ɗan 20 ya fara zuwa ci rani a kaduna,yana saro kaya a Kano ya kawosu Kaduna ya saida har Allah ya mai jagora a kasuwancin nasa ya zamo mai kuɗi sosai,a Kaduna ne yaga mahaifiyarsu Sauban lokacin tazo ita da yayarta mace kasuwar bacci siyayya wanda a lokacin  sunzo biki tufun wada ne, a nan ya ganta har Allah ya ƙaddara ya aureta.


Allah ya azurtasu da ƴaƴa har biyar,da yake mahaifinsu Sauban yanada sha'awar karatun boko kasancewar shi baiyi karatun boko ba  sai dai karatun Allo  yasa ya bada himma da ƙwazon ganin yaransa sun tashi cikin karatun boko da na islamiya.


Babu laifa daga mazan har matan sun samu karatu daidai gwargwado duk da matan su biyu  da yayyinsa maza ma duk sunyi aure shi kaɗai ne ya rage baiyi ba.Mahaifiyar Sauban ita kaɗai ce a wurin mahaifinsu Sauban.Allah yama mahaifinsu Sauban rasuwa a shekarar da ta gabata wato shekara ɗaya ke nan.Wannan shi ne taƙaitaccan tarihin Sauban Muhammad Ja'afar Ƙaraye.****



                        @ @@@@@@


Ɓangarensu Umma Kande kamar yadda Maman Jummalo ta bada shawarar suje ranar lahadi haka ko akayi,da sassafe suka buga sammako zuwa wurin boka Sankeru.


Isarsu keda wuya suka ga mata dayawa na layi a wurin bukkar boka Sankeru,mamaki da al'ajab ya cikasu har da riƙe baki,lallai boka Sankeru ya  fara  shahar sduba da yadda suka bugo sammako har sun tarar da layi ba kamar da ba da zaku shige direct.


Haka suka jira har layi yazo kansu,Umma Kande ce ta shiga kasancewar ita Mamam Jummalo rakiya tayo,tana shiga kamar yadda suka saba ta mishi kirayi tare da ƙasƙantar da kanta garesa(Wa'iyazubillah,Allah kasa mufi ƙarfin zukatanmu baki ɗaya😞😞😞).


Bayyanarsa keda wuya ya tintsire da wata mahaukaciyar dariya yana bubbuga ƙafa tare da nunata da yatsa yana ƙara tintsirar dariyarsa.Ita dai Umma Kande kanta a ƙasa.(ummm su Umma Kande masu ladabin ɗan tsako😂😂😂🙃).


Saida yayi mai isarsa kana ya tsagaita yana dubanta tare da cewa


"Yanzu tafi ƙarfinki Umma Kande!!! Tafi ƙarfinki!!! Saidai kiyi haƙuri"


A razane Umma Kande ta ɗago kanta tare datakai dubanta ga boka Sankeru sai kuma ta fashewa da kuka tana roƙo da magiya akan ya taimaketa kar asirinta ya tonu saboda tasan mijinta yafi son Umman Sa'eeda akanta bayan haka danginsa da batason su raɓesa yanzu zasu dinga zuminci sosai daga ƙarshe zasu maidata saniyar ware ita da ƴaƴanta,haka taita roƙonsa tana kuka sao kace wata yarinya.


"Naji! Naji!! Najiiiii !!! "


Sai kuma yayi shiru na tsawan wasu mintuna,Umma Kande har ta zaci bazai sake magana ba,sai kuma taji ya fara magana cikin amon muryar nan nasa mai sauti tare da firgitarwa.


"Akwai sharaɗi mai girma Umma Kande!!! Sharaɗi babba Umma Kande!!! Sharaɗin shi ne,zamu baki kwalba wanda ruhinsa ke aciki,sannan karki sake!!! Karki kibari!!! Karki yarda !!! A hir ɗinki !!! Kibari kwalbar nan ta fashe!!! Idan kuma ba haka ba....................





Pages ɗin yau babu yawa kasancewar banda caji a wayana,in shaa Allah pages na gaba zai kasance🔥🔥🔥




Ku cigaba da kasance da alkalamin Narrnarhh Bukar✍️✍️✍️ zaku nishaɗantu tare da ilmantuwa harda ma wa'azantuwa In shaa Allah🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝💝



***Anya babu wani dalilin da yasa Maryam ta sauya Sa'eeda kuwa bancin ƙawaye???



****Shin bakwa tunanin soyayyar da Sa'eeda takewa  Sauban baiyi yawa ba,karfa a samu matsala fa???



****Mai kuke tunani akan kwalbar da boka Sankeru yake da niyyar bawa Umma Kande???   Sannan mai yasa yace karta bari kwalbar ta fashe??? Shin wai idan ta fashe mai kuke tunani????




Ku cigaba da kasance dani taku har kullum Narrnarhh Bukar🤗🙃🌹💝 domin tafiyar tamu ta dabance🙃🙃🙃 na tabbata zaku ilmantu sosai tare da nishaɗantuwa in shaa Allah🤗🤗🤗 kudai ku cigaba da zubomin ruwan comments🤗🤗🙃🙃🙃 ni kuma bazan gaji da suburbuɗo muku da  sababbin updates a kullum ba wanda zaku wa'azantu sosai da sosai🤗🤗🤗🤗💝💝💝💝💝💖💖💖💖🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🌹🌹




Ina Kaunarku da yawa da yawa my Esteem Fans Allah ya barmu tare har a jannatul firdausi💖💖💖💖🏵️🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🤗🤗🤗🤗🙃🙃🙃




Ina yinku over my Esteem Fans🤗🤗🤗🤗🌹🌹🌹🌹🏵️🏵️🏵️🏵️💗💗💗🌼🌼🌼




Daga alƙalamin 

🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.

[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 

Post a Comment

0 Comments