TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 39-40

3⃣9⃣----4⃣0⃣






Darammm!!! Dammm!!! Darammmm!!! Tashin hankali wanda ba'asa mai rana,zuciyar Maryam ce ta tsinke lokaci guda,ƙwaƙwalwarta ta tafi hutun wucin gadi na wasu sakanni,kirjinta dukan tara-tara ya fara bama uku-uku ba,dafe ƙirjinta tayi da hannu bibbiyu tare da waro idanunta waje tana cewa


"Kishiya Sauban zakamin!!! "


"Ƙwarai kuwa Maryam"


Ai wani irin daka tsalle Maryam tayi,haɗe da cira gyalanta da ɗan kwalinta lokaci guda tana cewa cikin masifa da bala'i har idanunta sunyi ja


"Kan bura Uban can!!! Wallahi tallahi baka isa ba!!! Yau akwai bala'i a gidan nan!!! Yau akwai yaƙin duniya na uku a gidan nan!!! Yau akwai tashin bama-bamai a gidan nan!!! Ni Sauban zaka ci amana tare da yimin kishiya,mene ne bana maka a gidan nan,aikin da ko a gidanmu banayi amma a gidan shi nakeyi,nace ka kawo ƴar aiki kace a'a,still na haƙura duk don saboda soyayyar da nake maka Sauban,amma da kishiya Sauban zaka sakamin,da kishiya, kishiya fa Sauban, inaaaa wallahi bazata saɓu ba bindiga a ruwa,banzan yarda ba wallahi,ban taso gidanmu naga Mom ɗina da kishiya ba,haka duka familinmu baki ɗaya babu mai kishiya saini wacca ko shekara ɗaya banyi ba,Wallahi baka isa ba Sauba......."


"Dallah malama kin cikani da hayagagarki wacca babu abinda zatasa balle ta hana,ke kin isa ki hanani aure ne,yooo ke awa awani dalili,you are just nothing for nothing in the absence of nothing in terms of nothing stupid human being,Mahaukaciya kawai"


A hargitse shima ya taso mata don yaga alama hauka take shirin yi masa,hala kuws domin idanunta duk sun kaɗa sunyi ja,ga kannan nata duk ya yamutse saboda matsifar da take cinta,dole ya taka mata birki,shi yama rasa waca ƙaddara ce ta sakashi auran wannna jalilar da batasan komai a zaman aure ba.


Rashin nasani hausawa suka ce yafi dare duhu domin da Sauban yasan abinda zai ɓallowa kansa da baima ko fara fada  zai mata kishiya ba saboda hauka tuburan Maryam ta fara,tare da kururuwa tana cewa


"Yi huhu!!! Wallahi baka isa ba Sauban!!! Yau zan nuna maka ni cikakkyiyar mahaukaciya ce wacca take da cerficate a psychiartry mai tambarin shugabar mahauka mata a Nigeria yeeeeee!!! Tabbas ni mahaukaciya ce a sonka da ƙaunarka kuma ban yarda wata ta raɓeka da sunan soyayya ko kuma na illata rayuwarta gaba ɗaya!!! Yi huhu ni Maryam mahaukaciya!!! Mallahi saina nuna maka cikakkyar mahaukaciya ce mai certificate yanzu nan!!!


Ai bata jira mai zaice ma ta fara watsi da abubuwan da yake a falon kama daga flower vest,show glasses,television,centre table da dai sauransu,tabbas Maryam ta kwance kamar yadda ta faɗa,domin mai hankali da tunani bazai fara kwatanta irin wannan haukan ba da sunan kishi.Sauban mutuwar tsaye yayi ganin irin aika-aikar da Maryam take yi,tabbas ta hauka ce saboda yadda take watsi da kayan falon zai tabbatar maka ba'a hayyacinta take ba,anya  bata da aljanu kuwa,idan fa ta taka wani uban tsalle kamar wata buriya zata sauka akan abinda tayi niyyar tarwatsawa,sai dai kaji Tatsatsa!!! Tas!!! Ɓas!!! Kas!!! Ya tabbata yaƙin duniya na uku ake a gidan Sauban,ko'ina na ɗakin ya birkice hatta curtains ɗin ɗakin basu tsira a hannun Maryam.


Sauban da yaga alamun tabbas noties ɗin kan Maryam sun kwance yayi saurin cafkota habawa wani gagarumin dambe suka kacame dashi,yana riƙita tana dukansa haɗe ta yaƙushinsa tana cewa


"Kasakeni in cigaba da aikina Sauban!!! Kasakeni!!! Sauban!!! Yau ake yaƙin duniya na uku a gidan nan!!! Saina tarwatsa gidan nan!!! Saina ƙona gidan nan!!! Sauban!!!"


Kamar mai almatsutsai haka Maryam ta koma,da bala'i yayi bala'i zuciyar Sauban takai maƙura haba tuni ya fara jibgarta kamar Allah ne ya aikosa,tun Maryam na iya ramawa har takai ko matsin kirki ta kasa,a fusa ce ya bar gidan baki ɗaya,Allah yasa ma Mom ɗinsa bata nan tayi tafiya lamarin ya afku da ko da ita za'ayi dramar saboda dole idan taji hayaniya ta fito ɓangarensu taji mai ke faruwa.


Sai dare Sauban ya dawo gidan,ko daya shigo falon samunta yayi a idan yabarta a kwance kamar bata motsi,da sauri ya isa inda take,tattaɓata yayi amma ina shiru da sauri jikinsa na rawa ya ɗauketa cak direct sai cikin mota,da sauri ya fizgi motar da gudu wanda har mai gadin saida ya tsorata dashi,gudu yake bisa titi kamar ya samu titin ubansa har ya isa hospital ɗin dake kusa dasu,direct nurses suka ɗauketa zuwa emergency room domin bata taimakon gaggawa.


Safa da Marwa Sauban yake domin ya kasa zama,ga uban gumi dake tsuttsugo masa a duk ilahirin jikinsa,tunani ne ya addabi ransa kala-kala,yama rasa wanne zai ɗauka ya fara,shin da tashin hankalin Maryam zai fara ko kuwa da aikinsa na office wanda tun sanda asalin mai company wato CEO ɗinsu yazo da wasu tsararraki masu tsauri ya daƙile handama da babakeran da Sauban da sauran ma'aikatan sukeyi,kasancewar CEO ɗin companyn nasu wayayye ne,ɗan boko kuma gogagge a harkar kasuwanci,wuta iya wuta,ga kuma auran khairat da immediately tana dawowa daga ƙasar Malaysia Mominsa tace za'a saka ranar auransu,tabbas ko ba'a faɗa ba kan Sauban ya ɗau caji sosai,shi saima yanzu yake ƙara da nasanin mai yasa ya auri Maryam bayan ga Sa'eeda mai hankali ga alkunya,wacca tasan girman naga ba da ita,kacona ni Sauban, nayi wasa da damana.Tunaninsa ne ya ɓace ganin likita ya fito daga emergency room ɗin,da sauri ya isa inda yake,likitan ne ya ce ya sameshi a office,babu musu ya bisa.


Bayan likitan ya zauna sai Sauban shima ya zauna zuciyarsa na dukan uku-uku,yana addu'ar Allah yasa babu wata matsala.Likitan ne ya dubesa tare da cewa


"Kwantar da hankalinka,ba wata matsala sosai,matarka was shock on something sannan kuma jikinta ya nuna alamun an duketa,su ne suka haifar mata da suman har na tsawan lokaci,amma Alhamdulillah she is under treatment zuwa nan da kwana biyu ko uku zamu sallameta saboda sai mun bata gado gaskiya"


"Ok Doctor,ina godiya sosai"


"Karka damu aikinmu ne,yanzu zan rubuta mata wasu allurorai tare da magungunan da zaka siya a pharmacy"


"Ok toh"


Rubuta masa abubuwan da zai siya yayi a paper sannan ya miƙa masa,fita yayi zuwa pharmacy ya siyo maganin tare da allurorin sannan ya tambayi wata nurse da a lokacin daya kawo Maryam tana daga cikin nurses ɗin da suka kai Maryam emergency room,ya tambayi ina ne room ɗin da aka kwantar da ita,direct ta kaishi har ɗakin sannan tayo gaba abinta.Shiga yayi ɗakin  da sallama sannan ya duba ta ,sai kuma ya fito saboda yanaso yaje gida ya ɗauko musu kayan da suke buƙata a asibitin.Wannan kenan




              @@@ @@@@@@



*ABUJA*



A ɓangaren Haj. Zulfa'u kuwa,hankalinta yanzu ya kwanta sosai saboda tama tifkar hanci sannan ta dage Daddyn Fadila ya bana ɗan aminsa da yake sonta aure saboda ayi-ayi auran kowa ya huta,babu musu yabi shawararta saboda shima kansa yafi amincewa Fadila ta auri yaron abokinsa Ambassador.Ranar biki aka saka wanda ba a ɗau lokaci mai tsayo ba just in 5 month coming,hakan yama Haj. Zulfa'u daɗi a rai domin koba komai asirin da ta daɗe tana ɓoyewa bazai tonu ba saboda idan Fadila tayi aure shikenan wani ɓangare na matsalarta ta kau,saura kuma ɗayan wanda kullum dashi take kwana kuma dashi take tashi wato arangama da tsatson maƙiyiyarta,wannan abu naci mata tuwo a ƙwarya idan ta tuna,gashi batasan wace hanya zatabi wurin ganin hana faruwan wannan matsalar ba irin na Fadila, kullum cikin taraddudi ta tsoro take,ta hana kanta saƙat,fita ma ta daina yinta yanzu duk saboda tsoran kar watara ta fita su haɗu wani bala'in ya hau kanta.


Bikin Fadila baifi saura wata Uku ba yanzu,shirye-shirye ne har an fara yinsa musamman Haj. Zulfa'u saboda ta ƙosa ayi-ayi auran hankalinta ya kwanta,an shirya bikin na gani na faɗa wanda yawanci abubuwan auran ba'a a Nigeria aka siyesu ba,gidan ma complete aka sake gyarashi.Haka sukayi ta shirye-shiryansu.




               @@@ @@@@@@@@



*KEBBi*



Ilimi shi ne tubalin komai a rayuwa,sannan idan rayuwa ta kasance bisa tsari haɗi da ilimi to tabbas tasha bambam da wanda baya da ilimi tare da tsari a rayuwarsa.Sadam Dauda Gali Mai Nasara yazama tauraro a cikin matasan Kebbi state masu ji da kuɗi da ilimi, domin cikin ƙanƙanin lokaci tauraronsa ya haska saboda a komai nasa zaka samesa yana aiki da lokaci,baya wasa da lokaci,komai nasa a rubuce yake kama daga cin abincinsa,fitarsa kasuwancinsa da komai nasa a tsari yake shiyasa a lokacin da Daddyn  ya ɗanƙa mishi ƙaddarorinsa ya ƙara maida hankalinsa kacokan a harkar kasuwancinsa,wanda yanzu ƙaddarorinsa sun ƙara yawaita kama daga companies,plazas,petroluem companies harda gidajen gona wanda bai daɗe da siyansu har uku manyan-manya ana noma kayan lambu,kiwon kifi,kaji,talo-talo,geese,da dai sauransu ana fitar dasu zuwa ƙasashen waje, duk  fa a tsakankanin watanin da Daddynsa ya bashi ƙaddarorinsa ne.


Bangaren soyayya tuni Sadam ya ajiyets,bama ya kallon ƴan mata balle wata ta birgeshi ya ce zai aura,lokacinsa kawai na kasuwancinsa ne,don har P.A garesa da bodygaurds masu kare da lafiyarsa,kuma duk inda yaje suna nan tare dashi.Mominsa tasha mishi magana akan yaushe zaiyi aure,amma amsarsa a kullum ita ce shi baiga yarinyar da ra'ayinsu yazo ɗaya ba,ko a lokacin da yake tare da Fadila saboda darajar Sadiq abokinsa ne yasa ya aminta ya soyayyarta ba dan yana son ba,babu yadda Mom ta iya,haka ya ƙyalesa.


Kamar yadda kuka sani duk babbar Sallah familin Alhaji Kabir Dikko suna family meeting don magance matsalolinsu,wannan karon da Sadam akayi family meeting ɗin,harda ƴan Kaduna wato Dr. Nabila da mijinta wanda auran dangi ne aka musu.A nan ne Dr .Nabila take ma Sadam tsiya akan baya da mutunci a ce yana zuwa Kaduna amma ko sau ɗaya bai taɓa cewa zaizo gidanta ba koda da wasa ne,hakuri yayi ta bata akan in shaa Allah idan ya shigo Kaduna zaizo gidan yamayi kwana biyu,duka familyn sai dariya suke musu ganin yadda suke drama kamar ba ɗa da uwa bane.Haka taro ya tashi bayan anci ansha an gwangwaje.Wannan kenan.



            @@ @@@@@@@@@@



*KADUNA*



A ɓangaren su Umma Kande da Maman jummalo  sun ƙara komawa gidan jiya,domin haka kurin bazasu bari gulmar layi ta kashesu da ransu ba,dole su samo mafita kuma mafitar ɗaya ce wato ƙara komawa gun boka Sankeru don tuntuɓar ko basuyi yadda ya umurcesu bane,sannan da ƙara nemama  yaran nasu wasu mazajen daban.(Oooo! Su Umma Kande da alama wahala bata ƙare musu ba kenan😂😂😂🙃🙃🙃).


Kasancewar jiya asabar sukayi shawarar,yau suka buga uban sammaka direct sai tasha,bayan sun sauka a mota sai suka hau machine su biyu,haka a ɗaukesu har gefan dajin inda zai sadasu da wurin boka Sankeru.Bayan ya saukesu suka nufa dajin a ƙafa har bukkar boka Sankeru,Allah yasa yau babu layi sosai mata uku ne a gaban su.lokacin da layi yazo kansu suka shiga ciki a tare .Kamar yadda suka saba mai kirari haka sukayi.


Kamar walƙiya haka ya ɓullo cikin bukkar daman daya gama aiki yake ɓacewa sai kuma idan wasu sunzo sai ya sake bayyana.


Bayyanarsa keda wuya ya tsintsire da wata mahaukaciyar dariya,tumbinsa sai jijjiga yake,su Umma Kande da Maman Jummalo kansu a ƙasa har ya gama dariyarsa sannan ya dubesu dakyau musamman Maman Jummalo na tsawan lokaci sannan ya fara magana cikin amon muryarsa mai firgitarwa


"Nasan Zaku dawo la'anannu!!! Nasan Zaku dawo dangin shayɗanu !!! Kun yarda da shaydanu irinmu hhhhhhhh!!! Ba kuyi kuskure a aikin da nasaku ba saidai ku kuka zaɓama yaranku mazaje !!! Kun nasar damu kuna son yaranku su auri mazaje kowani iri shiyasa muka basu mazaje kowani iriiiiii!!!! "


Har yanzu su Umma Kande babu wacca a cikinsu ta ɗago kanta balle tayi magana,cigaba da maganarsa yayi


"Karku damu tunda kun yarda damu!!! Zamu baku kwalli su shafa  gobe da safe idan zasu fita!!! Na tabbata komai yazo ƙarshe!!! Zasuyi aure ba irin wancan ba !!! Zasuyi aure tabbas! Tabbas! "


Yana gama magana yayi wata jijjiga kamar wani alade tare da sakin wata uba-uban tusa mai ɗoyin gaske,tuni suka toshe hancinsu saboda warin kamar mushe ya mutu.(Da sauri na ɗauko nose mask ɗina na saka saboda kar a samu erro mai Esteem fans😷😷😷)


Zuwa wurin wata ƴan ƙwarya dake rataye a ɓukkar ya ɗauko kwallin tare da  cilla musu, sannan kamar yadda ya saba kasancewa dasu a duk sanda sukazo hakan ta faru,amma fa yafi daɗewa da Maman Jummalo wanda har Umma Kande taji tsoro saboda da ita ya fara,kusan awa biyu yayi da Maman Jummalo kana tafito tana gumi tare da ɗingisa  ƙafa kamar mai ciwo.Haka suka taho gida wanda basu suka iso gida ba sai wurin Isha'i saboda daɗewan da boka Sankeru yayi da Maman Jummalo.


Bayan sunyi wanka sun huta,sannan Umma Kande ta dubi Maman Jummalo tare da cewa


"Ƙawas yanzu ya zamu shawo kan yaran nan su saka wannan kwallin ba tare da sun bamu matsala ba"


"Wata sabuwa inji ƴan caca,tab akwai drama kuwa,kinsan yanzu sun fara biyewa Sa'eeda har da ce mata tayi musu ƙari a karatunsu,kinga da wuya su yadda su saka wannan kwallin kuwa"


Shiru ɗakin yayi kowa na neman mafita,sai can Umma Kande cikin murna ta ce


"Yawwa!!! Na samo mafita ƙawas!!! Wallahi nasamo mafita!!! Kinsan me Ƙawas"


Girgiza kai Maman Jummalo tayi,sannan Umma Kande ta cigaba da cewa


"Mu musanya musu kwallinsu da wannan ta hanyar cire bayan kwallin nasu saimu saka musu wannan kinga ai bazasu gane ba,muyi shiru abunmu,koya kika ce"


"A yyiriri nanaye!!! A Gaskiya ƙawas kin iya bada shawara,haka kuwa za'ayi wallahi, yooo ina dalili ai gwara su sake wani auran mu huta"


"Wallahi kuwa"


Haka suka cigaba da hirarsu cike da annashuwa,abinda su Umma Kande basu sani ba shi ne,Iklima tazo shiga ɗakinsu taji Mamanta da Maman Jummalo suna shawarar yadda zasu sake aurar dasu harda kwallin da zasu musanya musu duk don su shafa a rashin sani,ai tuni ta wuce ɗakinsu Maman Jummalo kasancewar a ɗakin Umma Kande suke hirar,babu ɓata lokaci Iklima ta sanar ma Jummalo abin iyayensu su shirrin aikatawa akansu,haka suka yanke shawarar kar kowaccansu tasa kwallin,tunda ita Jummalo tanada wani sabon kwallin wanda mamanta batasan dashi ba kawai saisu shafashi amma tare da taku kar susan basu shafa ba.


Da wannan shawarar Iklima da Jummalo suka  kwana,haka suma su Umma Kande da shawararsu sukaje suka kwanta,da safe kamar yadda su Iklima suka tsara haka sukayi ba tare da iyayensu sun gane ba kwallin da suka sauya musu bane suka shafa ba.


Bayan wasu satittaka saiga Maman Jummalo da sassafe da fito ɗakinta da gudu tazo wurin inda ake wanke-wanke haɗi da kwara amai babu ƙakƙautawa,da sauri Umma Kande ta ƙasaro inda take domin a lokacin da Maman Jummalo ta fito da gudu,Umma Kande fitowarta  kenan zata zagaya bayi.


"Ƙawas lafiya kuwa,meya sameki haka"


Cikin galabaita Maman Jummalo ta fara magana


"Nima na rasa meke damuna ƴan kwanakin nan wallahi, sai inji zuciyata na tashi kamar zanyi amai,ga yawan bacci da kasala,anya ba shawara bane kuwa? "


"Da alama tunda kina yawan bacci,shirya kawai anjima muje asibiti"


"To"


Taimaka mata Umma Kande tayi ta wanke bakinta sannan tayi brush,sai ta ƙara taimaka mata ta shiga ɗaki.Da ƙarfe 10:21am na safe su Umma Kande da Maman Jummalo suka shirya zuwa asibiti,a gwajin farko likita ta tabbatar musu da Maman Jummalo na ɗauke juna biyu na sati uku da kwana ɗaya,ai kan likita ta kammala bayaninta Maman Jummalo ta miƙe tsaye,jiki na rawa ta fashe da kuka tana cewa


"Na shiga Uku na lalace ni Hafsy,wace baƙar rana ce yau a gareni ni Hasfy"


Umma Kande tayi saurin rufe mata baki kar tayi ɓaran-ɓarama a gaban likiti,jawota tayi suka fita zuwa gida,ko a cikin keke napep ɗin kuka take sosai,bayan sun isa gida Maman Jummalo ta nufa ɗakin ita ma Umma Kande ta biyota bayan ta sallami mai keke napep ɗin.Allah yasa ma gidan babu kowa kasancewar Iklima da Jummalo suna Islamiya,ita kuma Umman Sa'eeda da Sa'eedar duka basanan.


Tana shiga ɗakin ta yakice gyalenta tare da ɗan kwalinta tana kuka tana cewa


"Na shiga Uku ni Hafsy !!! Yau na ɗau ciki boka,shikenan zan haifi ɗan boka,wayyo Allah  ni Hafsy,shikenan tawa ta ƙare!!! Yiiiiiii yiiiiiiiii yiiiiiii !!!! "


Haƙuri Umma Kande tayita bama Maman Jummalo akan tayi hakuri sai a zubar da ciki kawai kar mutane su sani,tun bata da aure,da maganar zubar da ciki Maman Jummalo hankalinta ya ɗan kwanta.


A ranar sukaje inda ake zubar da ciki na sirri,maƙudan kuɗi suka bada sai aka bata magunguna tasha tunda cikin nata ƙarami ne baikai a saka engine a makare tayin ba(Wa'iyazubillah🤔🤔🤔)


Haka suka dawo gida tayi tashan magani babu ƙakƙauwata,amma ikon Allah sai cikin yaƙi fita,har ya fara ɓullowa ana gani, haka suka zuwa  a cire cikin amma likitan ya ce idan aka cire cikin Maman Jummalo zata iya rasa rayuwarta saboda yanayin mahaifarta mai rauni ce.Haka suka ƙi haƙura da yawan inda za'a zubda cikin,amma kamar haɗin baki duk inda sukaje magana ɗaya ce,Maman Jummalo zata iya rasa ranta.Wannan Kenan.




              @ @@@@@@@@@@




A ɓangarensu Sa'eeda kuwa,babu abinda ke damunsu,ga karatun Sa'eeda nata tafiya abun sai sam barkha,shaƙuwarsu da Dr.Nabila kullum ƙara yawa take,ga Iman ma suna ƙawancensu mai tsafta babu munafinci a ciki.



Tun Sanda Sauban ya yaudari Sa'eeda taji ta tsani maza a rayuwarta,tunani take duk halinsu ɗaya ne babu bambamci.Kasancewar Exams ɗinsu na first semester 400 level ya kusa,kowani lecturer yana alla-alla ya gama lecturer ɗinsa ga ɗalibai ya huta,hakan ta faru ga Dr. Nabila.


Kasancewar yau Thursday kuma yau Dr. Nabila take shirin yima su Sa'eeda test,gudu take a titi babu ƙakƙautawa saboda tayi latti,wayar ce a gefanta take kukan agaji,tana tuƙin ta dau kiran


"Hello Abban Twins baidai har kun isa airport ɗin ba"


Mijin nata ne a can ya amsa da cewa


"Eh wallahi muna jira a kiramu ne,kinsan sai 11:00am jirgin namu zai tashi"


"Maa shaa Allah ya kaiku lafiyyyyyyyy"


Ƙkkkkkkkkkkkkiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii!!!! Motar Dr .Nabila tayi da ƙara kamin ta kusa bige wata mata da niƙaf a fuskarta tana sharan titi,taso kaucewa matar amma ina saida motar ta kwance a hannun Dr .Nabila haba tayi sama da matar nan,Allah yasa Dr. Nabila tayi saurin gyara kan  motar da motar ta ƙarabi ta kan matar nan.



Da sauri tayi parking a gefen titin haɗi ta fitowa da sauri jiki na rawa ta nufa inda mutane suka taru a inda matar take,da sauri ta ce a dauki matar a saka a motarta su tafi asibiti, da sauri aka saka matar a motar Dr. Nabila suka nufi asibiti wanda daƙyar aka anshesu wai sai sun kawo police,direct emergency room aka nufi da matar wanda a lokacin niƙaf ɗin na a fuskar matar hankalin kowa baikai wurin a cire mata ba,wani wanda  sukazo da Dr.Nabila a asibiti ya ɗau wayar matar don  kiran makusantanta,ganin an rubuta *SANYIN IDANIYATA* da manyan haruffa yasaka shi kiran numban bugu ɗaya ana na biyu  ta ɗauka tare da sallama


A ɓangaren Sa'eeda tun safe ƙirjinta ke bugu ta rasa dalili,har ta kasa haƙuri  ta sanar ma Iman,sai Iman ta ce tayi ta addu'a in shaa Allah alkhairi ne,sai kuma yanzu ga kiran Umanta wacca tasan bata kiranta a wannan lokacin,cikin sanyi murna tare da tsoro ta amsa kiran


"Assalamu Alaikum"


A can mutumin bai amsa mata basaima ya sanar da ita mai wayar mota ta kaɗe ta yanzu tana asibiti


"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,Allahuma ajurni fi musibati wa'aklifni khairan minsa"


Cikin kuka ta tambayi wani asibiti ne,sanar mata yayi tare ta katse wayar,fadama Iman tayi Ummanta yanzu mota ta bigeta ashe shiyasa ƙirjinta yake bugu ɗazu,babu ɓata lokaci Sa'eeda da Iman suka nufi asibitin da aka sanar musu Umman Sa'eeda na can.


A ɓangaren Dr.Nabila kuwa,sai a lokacin ta tuna wayar na mota,da sauri ta ɗauka wanda taga missed calls ɗin mijinta yafi goma,kiransa tayi tare da sanar dashi abinda ya faru sannan yace suma baifi mintuna ashirin su tashi ba,sallama sukayi sai a lokacin aka fito da Umman Sa'eeda a gadon marasa lafiya,idanunta a rufe suke har ɗakin da aka kwantar da ita,Dr. Nabila ce ta kefe Umman Sa'eeda da ido babu ƙyaftawa,haka tabisu har ɗakin da aka kwantar da Umman Sa'eeda still idanunta na akan Umman Sa'eeda ƙirjinta da fat! fat,tana a wannan yanayin ne saiga su Sa'eeda sun bako ɗakin babu sallama turus sukayi ganin Dr. Nabila a ɗakin,itama da mamaki take kallonsu,cikin murya mai sanyi Dr. Nabila ta ce


"Umman kice wannan Sa'eeda"


"Eh malama"


Waro idanu tayi waje,idan ta kalli Umman Sa'eeda sai ta kalli Sa'eeda don tabbatar da abinda zuciyarta take rayawa game dasu,ai tuni Dr Nabila jikinta ya fara rawa tana kallon kowannansu lokaci guda ta ɗauko wayar,dailing numban mijinta tayi,shi kuma a lokacin yana gab da shiga jirgi,da mamaki ya kalli wayar,lafiya kuwa take kiransa yanzu duka-duka yaushe suka gama wayan,amsawa yayi da


"Hello darling hope lafiya"


Dr.Nabila da duk ta ruɗe ta ce mishi


"Abban Twins kazo asibitin nan yanzu don Allah"


Cikin mamaki yace


"Ban gane nazo asibiti yanzu bayan kinsan tafiya zanyi kuma mai muhimmanci..."


Katseshi tayi da cewa


"Ba tada muhimmanci yanzu Abban twins,na roƙeta kazo kaga abinda nagani da idona,wallahi ƙwalƙwalwata ta rikice,don Allah ka fasa tafiyan sai gobe ka tafi ................"









Mu haɗu a *BOOK 2* in shaa Allah don cigaba da jin wannan rikita-rikitar wanda zaizo muku bada daɗewa ba🙃🙃🙃🙃📚📚📚✍️✍️✍️ 




*Waye mijin Dr. Nabila da take cewa dole yazo yaga abinda ta gani??? Wai idan yazo mai kuke tunanin zai faru??? Mai yasa Dr. Nabila take kallon Umman Sa'eeda da Sa'eeda lokaci guda???*........




*Tofa🤔🤔🤔yanzu dai a Maman Jummalo da cikin boka Sankeru,koya zata kaya????*.....





*a tunaninku kwalbar nan bazata fashe ba har abada ko kuwa akwai wa'adinta indan Allaj yayi????*.....





****Ya zata kasance Shugabar ƴar lawuɗi Nusaiba????......




*Anya Maryam zata yarda da auran da Sauban zai ƙara kuwa???....kuma wani mataki kuke tunanin iyayenta zasu ɗauka idan sukaji za'ama ƴarsu kishiya ko kuwa???*......




*Wace ce Haj Zulfa'u sannan wani sirri ne tale ɓoyewa wanda bataso asani????*........



*Shin kuna ganin Sa'eeda zata samu wanda yafi Sauban ko kuwa????*




*Wasu abubuwa ne suka faru shekaru aru-aru da suka gabata???*........







*Alhamdulillah ala kulli Halin,anan na kawo ƙarshen littafina na ɗaya wanda na biyun yana nan tafe,in shaa Allah, in fatan kun ilmantu,kun nishaɗantu tare da wa'azantuwa a littafina na ɗaya,na biyun ma yana nan tafe wanda yake ɗauke da amsoshinku wa'inda na 'issafa da wa'inda ma ban lissafa ba in shaa Allah, ina godiya sosai da goyon bayan da kuke bani ta hanyar  




Post a Comment

0 Comments