TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mun page 3-4

 3️⃣----4️⃣


Tashi yayi ya wuce ɗakinsa, "Maa shaa ALLAH ", kawai na iya furtawa ganin haɗadɗan ɗaki, dan ko amarya sai haka, in fact ko amaryan ma sai wacca ta cika amarya,ɗaki ne mai kyau da tsari, gashi babu wani tarkace dayawa,paint ɗin ɗakin fari ne tas, bed ɗin  ma fari ne haɗe da ratsin gold,acan ta gefe kuma akwai sofa da centre table mai kyau, gaskiya ɗakin ya kai ƙarshan haɗuwa. 

Wanka yayi kana ya fito, a gurguje ya shirye saboda jin an kusa tada sallah, ash color jallabiya yasa mai taushi haɗe da sheƙi, sannan ya daddala kalolin turaruka masu ƙamshi da tsada sannan ya fito,wayarsa da take a aljihu ya ciro jin tana vibrating, ya kalla naɗan wasu seconds sannan yayi picking.

A can naji murya wani yana faɗin"Hello Sadam, yane kana gida ne", Sadam ɗan jimmm kaɗan yayi kafin ya ce"Eh, yanxu zan shiga masallaci",acan naji ance "OK, gani nan zuwa, in shaa ALLAH ", da OK da bishi dashi  kana ya katse wayan.


           @@@@@@@@@@@


 Massallaci ya nufa don sallar Asr, bayan an kammala ya dawo cikin gida da yake a cikin gidan massallacin yake,kafin ya shiga ciki naga ya tsaya, ganin mai gadi ya buɗe tanƙameman gate, wata rantsatstsan motar ta danno cikin gidan, kana ta nufa inda ake parking tayi parking, wani guy ne nagani wanda bai wuce sa'ar Sadam ba ya fito d'an kimanin shekara 20 da haihuwa, Kamal kenan  na hannun daman Sadam, abotarsu ba ta yanxu bane, sunyi makaranta tare tun daga primary har secondary saidai abinda kowa yakeson zama a rayuwarsa ya banbanta, Sadam nason ya gaji mahaifinsa kasancewar shi kadai ne ɗa  namiji a gidansu wato cikakkyan ɗan kasu shiyasa yake son karantar Business Administration a Oxford University, UK. 

Sa'annan Kamal nason zamowa ɗan Jarida, shiyasa yake da sha'awan karantar Mass communication.


           @@@@@@@@@@@@@@


Rungume juna sukayi sannan suka nufa ciki a tare, hannunsu na sarƙafe dana juna, da sallama suka shiga, Mum dake a falon ta amsa musu tare da faɗin "Kamal kazo yin sallama da ɗan uwan naka ne?  Kamal wanda yake a russune ya amsa mata da" Eh Mum ya faɗamin jibi ne tafiyar kuma jirgin safe zai bi ", Mum tashe" Toh maa shaa ALLAH ,Auta ya faɗamin kaima kasami admission", Kamal yace"Eh Mum" 

 "Toh ALLAH yasa Albarkha, yasa Kugama lafiya", da Ameen suka amsa sannan suka nufi sama ɗakin Sadam .

Nan suka fara hira kamar karsu rabu kasancewar Kamal akwai zuba kamar famfo, sai ƙarfe 8:00pm Kamal ya wuce gida. 

Haka dai Sadam yayi shirye shiryen sa, sannan ya ziyarci sister ɗinsa ɗaya wacca ta ke aure a nan KEBBI, tana auran wani ƙusan gwamnati, ita ɗayar sister ɗinshi tana aure a Pakistan da ƴarta mace, sannan washa gari jirginsu ya cilla sararin samaniya sai UK. 


           @@@@@@@@@@@@@@


KADUNA 


Wasa wasa lokacin sauka ya ƙarato, Alhamdulillah Umman Sa'eeda tayi bakin ƙoƙarinta wurin ganin tama Sa'eeda kayan sawa na fitan sauka dai dai gwargwado wanda da adashen kuɗin kayan wankin mutane da ta ke yi ne ALLAH yasa tasamu kwasan farko.

"Abban Sa'eeda don ALLAH ka taimaka koda na pure water ne mu samu tunda kaga ranar asabar ne saukan, gashi yau ne kasuwa ta ke ci", 

Duk wannan zancan da Umman Sa'eeda ta ke yi yana jinta a kishingiɗe a ɗan gadonta yaƙi kulata, ta ƙara da faɗin" kayi shiru Abban Sa'eeda "

Buɗar bakinsa ya ce" Toh mekike so nace, nina sata makarantar dazan bada wata gudun mawa na ehhh! , tun farkon karatunta ai nace miki banda halin biyata mata kuɗin makaranta amma ke gaki ƴar iyayi ke don ace ɗiyar tana makaranta kikayi cuku cuku har tafara, kina wahalar da kanki da wankin dauɗar mutane!!!

saida ya lunfasa duk tana jinsa bata ce komai sannan ya ɗora da faɗin"Don haka karki sakemin maganar karatun Sa'eeda kuma wannan kashedi ne na miki, ban hanaki ba ko dako zakiyi don ƴar gold ɗinki tayi karatu bai shafeni ba, ki ƙarata can da gulmarki"

Zunbur ya miƙe ya kakkaɓa babbar rigarsa zai ƙara gaba, Umman Sa'eeda ta tashi da sauri tana dubansa sannan ta ce"Duk naji bayananka, kamar yanda kace karatun Sa'eeda bai shafeka ba,toh in shaa ALLAH daga yau bazaka sake jina na maka batun karatun Sa'eeda ba, wannan alƙawari ne, kuma sai Sa'eeda tazamo fila mai haske wannan gidan wanda yake cike da duhu, in shaa ALLAH "

Taɓe baki yayi kana yace" Wannan ke ta shafa, ni kinga tafiya ta"

 da sauri ya ƙara gaba, Sa'eeda da ta ke bakin ƙofa tayi saurin matsawa, ALLAH yasa bai ganta ba,da tasha ranƙwashi, ita wallahi ta rasa mai tayiwa mahaifinta yake kyararta baya sonta, sai dai ƴan ɗakin Umma Kande wanda basuda aiki sai tsagwaran talla titi titi da garage garage din motoci, duk sun sha bleaching, har da sa'arta Iklima tafara bleaching da taɗi a zauransu.

 Duk fa wannan zancan acikin zuci Sa'eeda ta ke yi,zumbur kamar wacca aka tsikara ta dawo hayyacinta ta shige d'akin. 


           @@@@@@@@@@@@@@


"Ummina mai ya sameki kike kuka, kinaso in fara kukane, Abbana ne koh, toh kiyi haƙuri wataran sai labari,banason zubar hawayanki Ummina"

 tana maganar muryarta na rawa saboda zuciyarta na mata suya akan maganganun da mahaifinta ya faɗama Ummanta kamar bashi ya haife ta ba.

 Hawaye suka fara sulalowa bisa kuncinta, ganin haka Ummanta tsagaita kukanta tana dubanta, don a rayuwarta ta tsana jin kukan ƴarta ta,haka ta tallafo kuncinta  tana dubanta da murmushi ta ce " Haba sayyin idaniya na, bansanki da saurin karaya ba, da juriya da jarumta nasanki, don haka bar kukan nan, sha re tsadaddun hawayanki kinji, abar kaunata"

da wannan kalaman Sa'eeda ta tsagaita da kukanta ta ɗago sannan ta kalli Ummanta tace "Toh kema ki daina kukan kinji Ummina"

 Cike da shagwaba ta ke maganar har taso ba Ummanta dariya, tace "Toh nabari tawan", a tare suka murmusa,sannan suka cigaba da sabgar su. 


        @@@@@@@@@@@@@@


Umma Kande ce da ƴaƴanta mata uku da namiji ɗaya wanda ya kasance babba a gidan ɗan kimanin shekara 25,suna zaune a ɗaki suna ƴar hirarsu cike  da annashuwa har da shewa. 

Nusaiba wacca ta ke bima Musa tace" Wai ni ya waccan Allazi bokon da mamanta suka ƙare da babane, ya basu gudun muwan ne, naji biki bamu chapter munsha ba"


Umma Kande ta sheƙe da wata bazawarar dariya har da buga cinya,"Yo kema kinsan maganar gizo bata wuce na koɗi,zan bari babanku ya bama wannan mai kama da mayun tallafi ne, haba ina bade ni jikan sarkin ruwa ba sai dai wata"

Sai suka ƙara sheƙewa da dariya sannan da ɗora ta faɗin"Ai kusha kurumunku, in har kunga kuɗi sun fita daga aljihun Babanku saidai ku za'a ma hidimar, don wlh ko zanyi yawo tsirara sai naga ƙarshen wa'incan mayun"

Alamar jinjina naga ƴaƴan suna mata tare da wasata kamar ƙaura. Haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallah amma babu wanda a cikinsu ya iya miƙewa don yin sallar(Wa iyazubillah🤔🤔🤔) . 


      @@@@@@@@@@@@@@


Yaune ranar sauka, fili ne nagani babba wanda yake cike da kanopils, ƙananun kujeru da na alfarma, filin ya cika maƙil da mutane har babu masaka tsinke, a bangare guda ƴan sauka nagani ajere suna shigowa filin don fara karatu, haka suka kammala karatun cikin tsari da burgewa.

 Manyan baƙi tun daga kan wakilin sarki da na hakimi,ƴan siyasa da masu hannu da shuni duk sun hallarta . Alhamdulillah haka karatuttuka sukaita wakana da wa'azuzzuka da dai sauransu har aka fara shirin bada kyaututtuka ga wa'inda suka cancanta.

 Mc mai magana ya fara da faɗin  "Toh yanxu yanxu bada jimawa ba zamu fara bada kyaututtuka ga ɗaliban da suka cancanta sannan sukayi zarra"

Kowa a filin ya natsu don sauraron zakarun shekaran, Umman Sa'eeda na hango can a zaune tasa wata atampa roba taji jiki sosai, sai murmushi ta ke ganin yau ƴarta tilo ta kammala haddan Al Qur'ani mai girma cikin nasara da aminci duk da tasamu ƙalubale a baya sannan yanxu ma dai bata gama fuskan ƙalubalan ba  hasalima wasan yanxu aka soma(wasa farin girki).

Mc ne ya fara da ce wa " Wacca tafi kowa hak'uri da natsuwa itace Sa'eeda Sulaiman", haka ta taso tana murmushi tazo filin inda za'a bata kyautar wanda wakilin mai girma sarki zai bada, haka akai ta bada kyatuttuka wanda kusan Sa'eeda tai ta tasamu.

 Daga ƙarshe Mc ya fara wasa gwarzon/gwarzuwan shekaran, nan da nan fili da rincaɓe da hayaniya don jin zakara/zakariyan shekaran, Mc yace"Gwarzo ko gwarzuwan shekaran nan shi ne ko ita ce", sannan ya tsagaita, mutune sai tsuma suke da ƙosawa don jin overall best student, Mc ya ƙara da faɗin "ita ce Sa'eeda Sulaiman", filin ya ɗauka da kabbara"Allahu Akhbar!!! 

 haka taje ta amsa kyautarta had'e zunzurutun kuɗi har #100,000,wanda kyauta ne daga wakilin sarki abama wanda yayi Zarra.


      @@@@@@@@@@@@@@@


Haka suka dawo gida ita da Sa'eeda da maƙotan da suke mutunci dasu, wa'inda kwata kwata ba sufi mata uku ba, don Umma kande woman leader ɗin unguwan ne . Daidai gwargwado Sa'eeda da gudanar da walimar saukanta wanda ƴan walimar basuda yawa daga Maryam aminiyarta ta boko sai wasu sa'oninta ƴan layi.

 Bayan sallar Isha'i, Sa'eeda ta dubi Ummanta tace"Ummina ya za'ayi da wannan kuɗin da nasamu ", Umma Sa'eeda tace" Zan buɗe account asa kuɗin gobe in shaa ALLAH don tun yanzu zan fara tarin kuɗin karatunki na jami'ah, tunda nasan bazan samu daga Abbanki ba kuma Koda na fara sana'a ba karɓuwa zatayi ba, saboda Kande, ko ya kike gani ke"

 Sa'eeda saida ta lunfasa sannan tace"Toh ummina duk yanda kika tsara banda jayayya, ALLAH yayi mana jagora ",  da" Aameen ", umminta tabita dashi, sai sukeyi shirin bacci don garin ya soma yin shiru.


           @@@@@@@@@@@@@@@ 


Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau da daɗi gobe babu daɗi, a bangaren Sa'eeda sai a hankali, hutun boko ya ƙare sun koma makaranta ka'in da na'in babu kama hannun yaro.

 Ta shiga SS1  Art class saboda tun tana ƙarama ta ke da sha'awan kasuwanci kuma Ummanta tanason haka, shiyasa ta ke son karantar Business Administration,saboda fannin kasuwancine, haka ta fara SS1 cikin nasara da aminci.

Sa'eeda karatu ta ke ba dare ba rana tunda yanzu ba islamiya ta ke zuwa ba sai dai tilawan Al Qur'ani mai girma da litattafai,karatu yayi nisa sun fara shirin exams na kammala SS1 zuwa SS2......................... 




Post a Comment

0 Comments