TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sarauniyar kyau page 29-30

*π‘·π’‚π’ˆπ’† 29&30*







  'α΄‹α΄‘α΄€Ι΄α΄€α΄‹Ιͺ Κ™Ιͺʏᴜ Ι’α΄€Κ™α΄€'





 π‘΄π’‚π’Š_π‘²π’šπ’‚π’–_π‘Ίπ’„π’Šπ’†π’π’„π’†_π‘ͺπ’π’π’π’‚π’ˆπ’†_π‘Ίπ’†π’„π’π’π’…π’‚π’“π’š_𝑨𝒏𝒅_π‘Όπ’π’Šπ’—π’†π’“π’”π’Šπ’•π’šπŸ’





Ta furta sunan da taga an rubuta, a saman makarantar, akan laΙ“Ι“anta sai kuma ta kalla uniform Ι—in dake jikinta skirt pencil iya gwiwa ash color, sai riga white color, sai kuma rigar sanyi a sama maroon color, tana sanye da safa doguwa wanda takai ma ta har gwiwa, ga takalmin Ζ™afafunta shima ash nd maroon color, mai igiyoyi.


Babu hijjab a jikinta sai dai wata hular saΖ™a, mai Ι—auke da launi ash nd maroon color's, ga sumar kanta mai yawa wanda tasha gyara ya zubo ta bayanta.




Da sauri ta kalla Afeefah da tayi parking a cikin makarantar, tun kafin ta ce wani abu Afeefah ta rigata da faΙ—in.


"Surprised" tana dariya, ita ma Deejarh Ι—in dariya ta fashe dashi, sannan ta ce.

"Balarabiyar india, wai yaushe kika san inasan makaranta ne?," 

Afeefah tana dariya ta bata amsa da faΙ—in, "a mafarki naji kina faΙ—a wani lokaci, da nazo bedroom Ι—in ki, naji kina faΙ—in, 'wayyo makaranta ni a sakani a makaranta, kona gudu daga gidannan,"




Fashewa Deejarh tayi da dariya, Afeefah ta ce "koba haka bane?," rufe fuska Deejarh tayi tana dariya, Afeefah ta kuma cewa "shine, ni kuma nace bari nama Daddy magana ya sakaki a school, tun kafin,"  sai kuma tayi shiru tana murmushi bata Ζ™arisa ba.




BuΙ—e back seat tayi ta ciro wata haΙ—aΙ—Ι—iyar backpack ta miΖ™awa Deejarh.


Da sauri Deejarh ta karΙ“a tana murmushi ta ce "kai Balarabiyar india kina surprising Ι—ina highly, yau fa, thank you so much, Allah ya Ζ™arawa Daddy Mister Mai Kyau ake cewa ko?, to Allah ya Ζ™arawa dukiya albarka, kuma ta kasance mai amfani, da kuma yawa fiye da cikin duniyar nanπŸ’΄πŸ’ΆπŸ˜…





Ba shiri Afeefah tayi dariya tana amsawa da Ameen Ameen dear, hannun Deejarth Ι—in ta kamo suka nufa office Ι—in principal, Deejarh sai kalla kalle takeyi, na Ζ™auyanci, don har yanzu abin bai saketa sosai ba.




Kwankwasa glass door Ι—in office Ι—in principal Ι—in Afeefah tayi, daga ciki aka bada umarnin shiga, da sallama suka shiga ciki hannun Deejarh cikin na Afeefah.







Yana Zaune a Royal chair inshi tana juyi dashi, yaba Ζ™ofa baya, saida ya gama shan mulkin shi, sannan ya juya kujerar ta juyo dashi.

Ganin wacca take tsaye tana kallon shi ga wata beautiful Girl kusada ita, yasa ba shiri ya miΖ™e tsaye.

GabaΙ—aya ya da burce, ganin Afeefah wata Ζ™ila bayyi tunanin ita bace, rasa mai zayyi yayi sai kawai ya Ι—aga hannun shi dake rawa yayi salute Ι—inta πŸ˜‚




Ƙumshe dariya Deejarh tayi ganin wannan matashin dattijon wanda akalla ya kai shekaru arba'in da biyar yana saluting Afeefah abin gunin ban dariya.



Cikin Rawar jiki da na murya yake faΙ—in, "ah um madam, ah wai kece, dan Allah zazzzauna mana, ga guri ki zauna hajiya madam mai kyau," gabaΙ—aya cikin zare ido da inn ina yayi maganar in violence.




Zama Afeefah tayi a kujera, sannan ita ma Deejarh ta zauna kusada ita.

Sai lokacin shima ya zauna yana goge zufa amma fa na tashin hankali.

Murmushi Afeefah tayi dan ta fahimci abin da yasa yake duk  wannan rawar jikin, toh kuwa yayi a banza.



Gyaran murya Afeefah tayi Sannan ta gaisar da shi, yana murmushi ya amsa sannan ya nuna Deejarh yace " ah madam wannan kyakyawar fa, kodai Ζ™anwar kice?,"


"E, Afeefah ta bashi amsa a taΖ™aice sannan ta cigaba da cewa "sunanta Khadeejah,"


Sai kuma tayi shiru batasan miye sunan mahaifin Deejarh Ι—in ba.

Kallon Deejarh tayi dan taji mai zata ce, da sauri Deejarh tace "My name is Khadeejah Abubakar mai kyau."



Da sauri Afeefah ta kalleta sai kuma tayi murmushi ta mayar da kallonta kan principal.

Cikin washe baki yace "aikuwa gashi kuma kuna kama, ita ma Ι—in kyakyawa kamar ku."



Afeefah ta ci gaba da cewa "na kawota ne yanzu, ya za'ayi za'a ma ta interview ne, sannan a sakata a class Ι—in da ya kamata da ita ko kuwa?."


Da sauri principal yace "ai duk abin da kikace, shi za'ayi madam,"

Maida kallon shi kan Deejarth yayi yana kuma washe baki yace "Nanah khadeejarthu, makarantar da kika fito a wani class kike?."


Ɗan jim tayi sai can ta ce "j.s.s two, na kammala, yanzu zan shiga j.s.s Three ne."

Principal yana murmushi ya ce "yauwa Nanah Khadeejarthu, yanzu idan na tambaye ki wasu abubuwa zaki iya bani amsarsu kuwa?."


Deejarth ta ce "in Allah ya yadda."


Principal ya fara "a darasin £nglish, wato Turanci zaki iya faΙ—amin, How many part of speech?,"


Shiru tayi sai can ta ce "guda Takwas {8} ne,"


"Da £nglish zaki faΙ—a,"  cewar principal.


Gyara zaman ta tayi ta Ζ™ara Ζ™anΖ™ame backpack Ι—inta sannan ta ce.


"£ight  ne," 


"Good" cewar principal sannan ya kuma cewa "and what and what."


Ta ce 


"Noun, Pronoun, Verb, Adverb, Adjective, Conjunction, Interjection, Prepositions,"


"Good, and What is Noun?,"


Gyara zamanta ta kumayi sannan ta ce.


"A Noun is a Name of Anything.,"


Murmushi principal yayi sannan ya cigaba da jefo ma ta tambayoyi akan £nglish language. Tana bashi amsa, wasu tayi daidai wasu kuma, yana ma ta gyara.




"Angama da £nglish saura basic science" cewar principal.

Ya kalla Deejarh yace.


"a darasin basic science, What is digestion ?,"


Yanzu ma saida tayi jim kafin ta fara kwararo masa bayani,  wanda yasa Afeefah da ke gefe zaune, ta saki baki tana kallonta cike da mamakin ilmin yarinyar.



"Digestion is the process, by which injested food, material are broken down in to similar particle's."


"Wow, good, and Define what is Brain?,"


Ta ce, "The part inside your head, that controls your thoughts, feelings, and movements."



Haka principal ya ci gaba da jerowa Deejarh tambayoyi daban daban akan subjects kala kala kamar su.


National Value, Agriculture, £conomic, Computer Science, I.r.s, Civic £ducation, £.t.¢.


Daga Ζ™arshe ya rufe da faΙ—in, give me the Ten, word's of £nglish.


T@ ¢£!

1.perfect,

2, Dream,

3, Table,

4, Challenge,

5,Get,

6, Offer,

7, School,

8, chair,

9, office,

10, saluteπŸ€­πŸ˜‡







Tunda ta fara Afeefah ta saki baki tana kallonta tasha mamaki sosai, da Deejarh ta iya wannan.

Ashe abin ba haka bane da ake ganin wasu mutanen da ke Ζ™auye ko kuma waΙ—anda suke zuwa government school ake musu kallon, jahilai, kodai adinga musu wani kallo na dabam abin ba'a zuwa government school bane, maida hankali da kuma jajircewa ne, dan ba wanda ya taΙ“a yin ilimi yana zaune sai an tashi an zage damtse, an shiga rana sannan da wuya koda daΙ—i πŸ‘


Amma tana tunanin ko'a haka ita Deejarh Ι—in tana cikin wa'innan mutanen da ake kira da Geniuses a turance kennan, sannan ita Ι—in gifted ce.





Murmushi principal yayi yana kallon Deejarh  ta burgeshi sosai da hazaΖ™arta.


"Nice good girl, kin amsa duka tambayoyi sai dai Wanda ba'a rasa ba."


Sannan ya mayar da kallon shi akan Afeefah yana murmushi yace "ta cinye interviewing, duka dan haka za'a sakata a j.s.s.three, she deserved it."


Afeefah tayi murmushi ta ce "okay sir."


Telephone Ι—in dake ajiye kusada dashi, ya Ι—auka ya danna wasu lambobi sannan ya kira, cikin harshen turanci yake maganar har ya gama, sannan ya kalla Deejarh yace "Nanah khadeejartu, taso na kaiki class da kaina,"


Murmushi tayi sannan suka miΖ™e dukansu suka fita a Ζ™ofar office Ι—in.

Afeefah ta kalla Deejarh tana faΙ—in,  "to Deejarh ayi karatu da kyau, idan an tashe ku, Moses driver zaizo ya Ι—aukeki kinji,"


"To shikenan babu damuwa," Deejarh ta amsa, sannan Afeefah ta nufi motar ta, Deejarh na Ι—a ga ma ta hannu.




Kana tabi bayan principal elevator taga ya nufa, ita ma tabi bayan shi suka shiga a tare hawa na uku taga ya danna bayan sun shiga.


Ba'a daΙ—e ba taga Ι—ofar ta buΙ—e sannan suka kuma fita.


Ita dai nata ido, don sai Ζ™arema makarantar kallo, takeyi sosai makarantar ta burgeta ga Ι—alibai kala kala farare da baΖ™aΖ™e hausawa dama waΙ—anda ba hausawa ba.



Wani haΙ—aΙ—Ι—en class taga principal Ι—in ya shiga, kafin ta ankara, da sauri tabi bayan shi sai kuma ta tsaya cak ganin class mai kyau da tsari gashi duka Ι—aliban ciki basu wuce su ashirin ba kai bama sukai hakan ba.



Gaisar da principal Ι—in, taga student's Ι—in sunyi bayan sun miΖ™e, ya amsa musu fuska a tsume kamar bashi ke washe baki yanzu a office Ι—in shi ba πŸ˜…




Nuna musu Deejarh yayi sannan yace "kunyi sabuwar New comer, kallon Deejarh yayi yace, "gabatar musu da kanki, a matsayin sabuwar Ι—aliba duk cikin turanci yake maganar.


Ta fahimci wani abu dan haka kallonta ta Ι—auke daga kanshi,  ta mayar kan students na class Ι—in da suka zuba ma ta ido suna kallo.




Qara RiΖ™e backpack Ι—inta dake bayanta tayi sannan ta fara magana.


"Hello class,  am Nanah khadeejah Abubakar mai kyau, am New comer, kamar yadda mai girma principal ya faΙ—a da farko."


Da turanci take maganar tana haΙ—awa da hausa fa.


Ta ci gaba da cewa "am very Gladness to see you, ina fatan zaku karΙ“eni hannu biyu biyu ko?,"


Ɗan shiru tayi tana kallonsu, sai kuma ta ce "ina fatan dai Ζ΄an uwan nawa Ι—alibai suna fahimtar abin da nake faΙ—a, saboda ni Ι—in ma Ζ΄ar koyo ce, ba komai na iya ba."



GabaΙ—ayan su students Ι—in suka haΙ—a baki wajen faΙ—in "munajin ki, kuma muna fahimtar ki, sannan kuma muma muna masu Farin cikin haΙ—uwa dake kuma muna fatan zaki kasance damu har lokacin da zamuyi Candy."


Dariya Deejarh tayi {Ɗalibai kenan, basu daΙ—e da shiga j.s.s Three ba amma suna tunanin fita daga school Ι—inma gabaΙ—aya, ae haka muke Ι—alibai akwai mu da Buri kala kala πŸ₯°πŸ‡³πŸ‡¬}






Ta ce "Nima haka, ina muku fatan nasara a rayuwa, sannan kuma, ku cinye jarabawar j.s.c.e. hadda ma s.s.c.e. gabaΙ—ayaπŸ˜‡



Dariya sukayi hadda ita, principal yace "yanzu tunda kun gaisa kunsan juna saiki sama guri ki zauna."



"To," ta amsa masa, sannan ta nufi gurin zama, da sauri wata kyakyawar matashiyar budurwa ta ce "baki faΙ—amana wani abu ba."



Lokacin da tayi maganar principal ya fita kuma dama can ba teacher a class Ι—in.



Deejarh ta tambayeta, "Menene abun?," budurwar tana dariya ta ce "baki faΙ—amana, Menene burinki ba, sister,"


Dariya Deejarh tayi sannan ta ce "burina shine naga wata rana, an wayi gari na zama babbar likita wacca take taimakon talakawa da marasa Ζ™arfi, SO I WANT TO BE A DOCTOR.





Tafi class Ι—in ya Ι—auka rafraf suna faΙ—in munayinki wallahi our new comer { kuma kunsan students idan malami baya class 😁 }






Deejarh tayi murmushi a takaice sannan ta ce "nima dai zanso naji Burin ko wannenku ko?,"


Budurwar da tayi magana ne ta miqe dama bencin farko take kuma ita kaΙ—a ce.


Ta tsaya gaban blackboard kusada Deejarh, Sannan ta miΖ™awa Deejarh Ι—in special hand Ι—inta ta ce. "AM FALILAT KHAM££S, AND I WANT TO A DOCTOR TOO."





Murmushi Deejarth tayi sannan ita ma ta miΖ™a ma ta hannunta dake sanye cikin handglove ash color ta ce "nice to meet you miss Falilat,"



Falilat ta koma ta zauna, wata ma tazo sukayi kamar yadda sukayi da Falilat, haka suka dingi yi har aka gama da Ι“angaren mata.




Wani saurayi ya fito ya miΖ™owa Deejarh hannu, wai su gaisa, murmushi tayi sannan ta juya hannunta ta baya ta karkaΙ—a mishi ta ce "haka akeyi saboda ni ba muharramarka bace."



Murmushi yayi yana faΙ—in "na gode da tuni, And am Farhad Khamees, i want to be a perfect £ngineer


Deejarh tana dariya ta ce "amma dai ku, twins ne da Falilat ko?,"

 

Amsa ya bata da faΙ—in, "E, haka ne, tayi murmushi haka suka ci gaba da yi mazan suma ba'a gaisawa sai dai a karkaΙ—a hannu. inji Deejarh.



Bayan sun gama ta sama guri a bencin farko, ta zauna kusada Falilat suna taΙ“a fira sama sama akan karatu, suna haka saiga wani malami ya shigo, miΙ—ewa sukayi aka gaisar dashi, bayan ya amsa suka zauna.


Deejarh ta kalla Falilat dake ciku cikun ciro littafi a jakarta ta ce "wani darasi wannan malamin yake koyarwa?,"


Falilat ta amsa "£nglish language," jin haka yasa Deejarh ta ciro book Ι—inta a jakarta ita ma.

Saida ta tsallake pages Ι—in da aka wuce ta sannan ta fara copyn writing Ι—in da malamin yakeyi a blackboard.


Bayan ya kammala ne yayi musu dogon explaining saida period Ι—inshi ya fita sannan ya bar ajin.


Wani ma ya shigo bayan ya fita, aka kaΙ—a bell lokacin Break, ganin kowa yana fita, Banda su yasa Deejarh ta kalla Falilat ta ce.


"nace ke banda kene a fita Break Ι—in?,"


Murmushi Falilat tayi sannan ta bata amsa, "ki tsaya kiga ikon Allah mana."

Jin haka Deejarh tayi gum, can saiga Farhad da snacks da kayan maqulashe kala kala ya duresu a gaban su, sannan ya kalla Falilat yana faΙ—in.


"Auntina waΙ—annan hadda qawarmu," yayi maganar yana kallon Deejarh da ta saki baki tana kallon su, yayi murmushi sannan yace "mamaki kike ko?,"


"Sosai ma," cewar Deejarh, yace "to ai ba abin mamaki bane, auntina ce ita idan kuma baki yadda ba, ki tambaye ta yana faΙ—in haka ya fita waje, wajen abokanshi.






Deejarh ta kalla Falilat zatayi magana, Falilat ta rigata da faΙ—in  "haka ne ni ce babba awa Ι—aya tsakanin mu, kuma yana girmama ni, nima ina bashi girmanshi."


Deejarh ta ce "amma kuma ana ganin shi, aka ganki za'a ce shine babba,"


Falilat ta ce "Eh mana saboda shi namiji ne ae."


Haka suka cigaba da fira suna taΙ“a snacks Ι—in gaban su har aka dawo class.



Wannan karon macece ta shigo ta koyar dasu Hausa language,  'Malama Fateema' bayan ta gama ta fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi sallah bayan sunje sunyi, sun dawo islamic aka koyar dasu dayake haka tsarin makarantar yake.



Ƙarfe uku dai dai aka tashe su, a tare Deejarh da Falilat da kuma Farhad suka fito.



Tsaye suke a bakin gate na makarantar, Falilat ta kalla Deejarh tana faΙ—in.

"to kodai zamu rage miki hanya ne, tunda drivern naki bai Ζ™ariso ba?."

Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "an karki damu fa, kuje kawai nasan nan bada Ι“ata lokaci ba zai Ζ™ariso,"


"to shikenan,"


Falilat ta amsa ta sannan ta shiga motar su driver yaja suka tafi.

Akalla takai minti biyar a tsaye sannan ta hango wata farar mota ta parker, a kusa da ita, da sauri Moses driver ya Ζ™ariso yana faΙ—in.

"am sorry ma'am Mrs mai kyau ce ta aikeni shiyasa ban Ζ™ariso da wuri ba."

Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "ba komai Moses yanzu shiga mu tafi gida, dan Yunwar da nakeji ba za ta faΙ—u ba, shiga motar tayi bayan shi ma ya shiga yaja suka bar gurin sai gida.









KANO





Da Gudun tsiya ta taho saboda tsananin saurin da takeyi, in twin's take taka staircases Ι—in da sauri ta Ζ™arisa tsakiyar palon tana sauke haki.


"Ke Jieddarh lafiyar ki kuwa?," 


Auntie da Humaira suka haΙ—a baki wajen tambayar ta ganin yadda ta sauko kamar wani abu ya biyota.

Tana sauke haki ta musu nuni da haΙ—aΙ—Ι—iyar princely gown dake hannunta.


Cike da farin ciki take faΙ—in Auntie na kammala, a yau na kammala haΙ—a gown Ι—innan.


Da sauri Humaira ta karΙ“a rigar tana faΙ—in.


"nicely Jieddarh barkanki dai, wannan aiki haka, shimfiΙ—a rigar tayi a tsakiyar palon tana bin haΙ—aΙ—Ι—iyar rigar da kallo ta haΙ—u sosai ba Ζ™arya.


Ɗinki ne irinna Ζ΄a Ζ΄an sarakuna, yaran sarakunan ma ba Ζ™anana ba.



Da wani kalar tsadadden yadi aka tsara Ι—inkin rigar, yadi mai masifar kyau da tsada, sky blue color mai haske.


Rigar bata da hannu, daga sama wajen Ζ™irji an matse rigar,  daga Ζ™asa kuma ta buΙ—e, amma ba sosai ba, yanayin tsarin dai irinna Ι—inkin yaran sarakai.

Wasu kyawawan stones farare da kuma sky blue color da aka jeresu jikin yadin, da aka Ζ™awata saman rigar dasu sai sukayi kamar sarΖ™a.

Daga tsakiyar rigar kuma ta wajen Ζ™irji wasu haΙ—aΙ—Ι—un flowers ne, sirara sosai aka taho dasu har izuwa Ζ™asa, yayinda wasu guda bibbiyu kuma aka jasu ta baya ko wani Ι“angare biyu.

Sai kuma wani haΙ—aΙ—Ι—en yadi fari ta bayan rigar, doguwa ce rigar sosai, dan sai taja ma ta Ζ™asa, duk da cewa ita ma Jieddarh ba baya ba akwai ta da tsayi ba Ζ™arya.


Sai kuma wani haΙ—aΙ—Ι—e kuma kyakyawan yadi fari da aka Ζ™awata shi da stones sky blue color, sannan aka Ι—inke, shi aka  zagaye ma'ana dai zayyi kamar shine hannun rigar amma shi daban yake ba haΙ—e da Rigar ba.


Gefe ma ga wasu Beautifuls hand Gloves farare suma masu Ι—auke da adon stones sky blue color, suma sak, ko ince fiye da na yaran sarauta suma daban a gefe ba'a jikin Rigar ba.



Kallon Jieddarh Humaira tayi Bayanta kammala Ζ™arewa gown Ι—in kallo obaa highly.

Tana murmushi ta miΖ™awa Jieddarh hannunta tana mai faΙ—in "a gaskiya na yaba da wannan haΙ—aΙ—Ι—iyar Rigar tayi Ι—ari bisa Ι—ari 100%. Jieddarh tawa sannu da Ζ™oΖ™ari fa."



Sannan ma zatayi ma wacca ta Ι—inka kyau Ι—ari bisa dubu, dariya Jieddarh tayi tana faΙ—in.

"wayyo Humaira bakiji yadda nakeji ba, jina nake kamar nayi tsuntsuwa, naje na yanjo Ranar gasar nan ya dawo yau, kuma yanzu sannan kuma adai dai wannan lokacin  a wannan gaΙ“ar" 😝



Humaira ta ce "kisa ranki a inuwa kamar kinyi, babban baΖ™o ya mutu da dare.


Championship day Ι—in aita kusa nan da jibi ne ae."


Kallon Auntie Jieddarh tayi tana washe farare kuma Ζ™ananan teeth Ι—inta ta ce.

"Auntie ya kika ga wannan Rigar tayi kuwa?,"

Auntie dake zaune a saman three sieter ta ce, "sosai ai saima Ranar gasa Ι—iyata zata fito a cikakiyar princess ta fasa Taro da kyawunta mai ban mamaki."



Fashewa Jieddarh tayi da dariya tana faΙ—in "wayyo Auntie kuna fasamin kai fa, da wannan ya bawar,"


"Yoo ai gaskiya ake faΙ—a keΙ—in kyakyawa ce, a cikin kyawawa ina faΙ—amiki, mutumiyar keΙ—in, tauraruwa ce, a cikin kyawawan taurarin dake haske guri," Humaira ce take kwararo wannan zancen a yayinda da take ninke haΙ—aΙ—Ι—iyar gown Ι—in.




Jieddarh ta ce "wow it's so very very amazing oh my glamorous Time."



Please Humaira can you imagine, yadda zan kasance a ranar gasar kuwa?."

Ta faΙ—a tana yin zaman Ζ΄an bori a tsakiyar palon tayi tagumi hannu bibbiyu tana lumshe ido, ga fuskar ta har yanzu a sake take, wanda hakan yaba kyawawan dimples Ι—inta duka biyun damar bayyana, dama kuma can koda tayi murmushi ko batayi ba a haka fuskarta take koda yaushe dimples Ι—inta a bayyane suke.




Humaira ta ce "komai yayi  zam zam, sai dai abu Ι—aya da kika manta da shi."


Da sauri Jieddarh ta ce "Menene shi wannan abun?,"


Murmushi Humaira tayi sannan ta ce "banga kin nuna mana, wannan Ζ΄ar sandar da yaran sarakuna suke riΖ™ewa ba."


Jieddarh ta bata amsa "ina nan da ita, tana bedroom gata ita ma launin ta sky blue ne, nd White color,"

 

Humaira ta ce "na lura da gaske kike wannan shirin fa,"


"sosai ma," cewar Jieddarh tana washe baki kamar gonar auduga.


Tashi Humaira tayi ta koma saman two sieter tana faΙ—in "da kikace 'glamorous' ma tunomin da wani chinese drama mai suna 'OUR GLAMOROUS TIME', kikayi, inason dramar sosai," 


Jieddarh ta ce "ni kuma wacca take cikin dramar nake so, Humaira ta ce 'Zhao liying' kike nufi?,"


"E, mana ta iya act sosai da sosai take burgeni I LIKE HER SO VERY MUCH." Jieddarh ta faΙ—a tana nufar staircase hannunta riΖ™e gown Ι—in.






ABUJA



Da sallamarta ta shiga palon tana cillah school bag Ι—inta sama ta cafowa.

Amsa ma ta sallamar Lailah dake zaune saman two sieter gabanta laptop tayi.

Ɗa go da kanta tayi daga kan laptop Ι—in, ta sauke akan Deejarh daketa faman washe ma ta baki.


"ah ah barkanki dai Ζ΄ar school, to ya ya school Ι—in?, ina fatan dai anyi karatu sosai da sosai?," cewar Lailah cike da fara'a kamar ba ita ba.



Zama Deejarth tayi a tsakiyar palon tana amsawa da "yauwa Auntie Lailah, hala ke kaΙ—ai ce a gidan?,"



"Me kika gani?," 


Lailah ta tambaya tana kallon Deejarh Ι—in, dan kuwa ba Ζ™aramin kyau yarinyar tayi ma ta cikin school uniform ba.



"naga kamar banga kowa bane sai ke, " ta bata amsa, Lailah ta ce "Auntie Zaynerb da Haleesat suna school, sai zuwa anjima zasu dawo, su kuma Auntie Nainarh da Nailah suna up, Momy kuma ta fita hospital kinsan bata cika zaman gida ba."



" toh Balarabiyar india fa, tana ina Deejarh ta tambayeta, murmushi Lailah tayi sannan ta bata amsa.


"Balarabiyar indian ki tana garden tana hutawa, yanzu sai ki tashi ki shiga kiyi wanka ki canza kaya sai ki fito kici lunch Ι—inki yana jiranki, shalelen Balarabiyar indiaπŸ˜ƒ





"To shikenan,"  


Ta amsa sannan ta miΖ™e ta shige Ι—akinta, tana shiga aje jakarta tayi a saman bed, sannan ta cire uniform Ι—in jikinta, ta Ι—aura towel ta shiga bathroom wanka tayi da brush sannan ta fito ko lotion bata tsaya shafawa ba, ta buΙ—e wardrobe ta ciro kayan da zata saka.


Cikin Ζ™anΖ™anin lokaci ta shirya cikin English wears, riga doguwa wacca bata wuce gwiwarta ba purple color, sai wando pencil fari, Ribbon tasa ta kamo doguwar sumarta kanta na ainihin fulani baki siqiq ta Ι—aure ta, in cute ponytail, sannan tasa p-cap fara.



School bag Ι—inta ta buΙ—e ta ciro wasu littafai guda uku, Ι—aya £xercises Book na subject Ι—in Basic science, biyu kuma Note Books ne.


Palo ta fito ta sama Lailah bata da alama bedroom Ι—inta ta shiga wata Ζ™ila.


Dinning room taje ta zauna a kujerar dinning Ι—in, sai da taci abinci ta Ζ™oshi sannan ta miΖ™e hannunta riΖ™e da Books Ι—in ta fita waje.




GARD£N ta nufa, a hankali ta Tura Ζ™ofar garden Ι—in ta shiga akan wasu haΙ—aΙ—Ι—un kujeru, na hutawa ta hango Lailah da Afeefah zaune, Afeefah tana karanta wani £nglish Book 'HOW TO MAKE FALL IN LOVE,' yayinda Lailah take sarrafa system Ι—in dake saman lap's Ι—in ta.



Akan kujerar dake lilawa ta zauna tana faΙ—in "Auntie Lailah ashe Nan kika taho?," 

Lailah ta bata amsa "ae nan na gudo nima,"


Kallon littafan hannun Deejarh Ι—in, tayi sai kuma tayi murmushi tambayarta tayi, "wa'innan fah ?.


Dariya Deejarth tayi sannan ta ce "kai Auntie Lailah karatu fa, zanyi da Rubuta, kuma akwai wani Assignment da aka bamu yau a school zaki koyamin."


Lailah tana murmushi ta ce "ah lallai Ζ³an makaranta daga zuwa yau har an fara baku Assignment?, to wani subject ne?,"


"Hausa language ne fa, kuma zasuyi wahala sosai," cewar Deejarh tana ya mutsa fuska.


In rushing Lailah take faΙ—in "to tunda Hausa ne, ki bari in anjima kya ba Auntie Nainarh, tunda ita Hausa ta karanta,"



Deejarh ta ce "ke bazaki iya bane?," 

Lailah ta ce "rabani da wahala, Hausa ai akwai wuya yafi Turanci wahala sosai fa."


Dariya Deejarh tayi ta ce haka Ζ³an class Ι—inmu suketa faΙ—a,  lokacin da malamar ta bada Assighment Ι—in,  gata akwaita sauΖ™in kai ga fara'aπŸ€“


Post a Comment

0 Comments