TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 12 --14

    Episode Twelve : A Kind Suggestion

Sumayya da tun da Ruqayyah ta fara lissafin ta take tsaye a bayanta rike da kaya a hannu baki a bude cikin mamaki, tasan yaruwar tata tana da dogon biri amma bata taba sanin cewa burin nata ya kai tsahon haka ba sai yau. 


Gida mai hawa uku, balcony, kallon kowa a kasa, lallai Ruqayyah ta wuce duk inda Sumayya take tunani. Tace "Ruqayyah? Duk wannan lissafin kawai dan babarsa ta nuna tana so a haɗa ku? Tun shi bai ce yana son ki ba tun baku fahimci juna ba ballantana ayi zancen auren har kin fara lissafin abinda zaki samu daga gare shi? Tabbas zaki fara ginin auren ki akan tubalin toka dan kuwa shi aure ana gina shine saboda Allah ba wai saboda abin duniya da ake burin za'a samu ba" 


Ruqayyah ta juyo tana kallonta, ita lissafi take yi a zuciyarta ba ta san cewaa fili tayi maganar ba amma so what? Waye baya son kuɗi? Kowa fa aka bashi daɗin su zaiji amma mutane da munafurci sai suke nuna wa kamar basa so. 


Ta hade rai tace "shikenan kuma yanzu Sumayya mutum bashi da ikon ya fadi a binda yake zuciyarsa sai a sako shi gaba da wa'azi? Ni banga aibu dan mutum ya nemi duniya at the same time kuma ya nemi lahira ba. Shi yasa ake addu'a ana cewa rabbana atina fidduniya hassanatan wa fil akhirati hassanatan......." Sumayya tace "kyakkyawar rayuwar ake nema ba wai kudi ba Ruqayyah, kudi ba shine farinciki ba, kudi ba shine abu mafi muhimmanci a rayuwa ba Ruqayyah. Happiness. Ka zauna cikin farin ciki shine abinda ake nema, wannan kuwa baya samuwa sai da wadatar zuci ba wai wadatar aljihu ba, the more kina samun kudi da more kina kara jin cewa ya kamata ki samu wasu, amma in dama baki saba dasu ba You will be contented with the little you have. Ni wannan shine abinda na fahimta, wannan shine abinda nake so. Wadatar zuciya. Kuma su kudi a fahimtata sukan kawo rabuwar kawuna ne a cikin iyali. Idan family da basu da kuɗi kamar mu din nan zaki ga sunfi haɗin kai ana haduwaa rufawa juna asiri but the moment kudi ya shigo ciki sai kiga an samu rarrabuwar kawuna musamman idan wani bangare ne ya samu kudin wani kuma bai samu ba. Ni abinda nake gudar mana kenan. Ruqayyah bound din da yake tsakanin mu yafi min gida mai hawa ukun da kike buri" 


Ruqayyah ta jawo ta jikinta tace "my darling sister, ba kudi ba, babu abinda zai raba tsakanin mu, duk inda zanje a rayuwa duk matakin da zan taka a rayuwa you will always be by my side, family na will always be y top priority, shi yasa a lissafin nawa Baba na fara sakawa nasan yana wahala damu" Sumayya ta zame daga jikinta tace "how can I be always by your side idan kika auri CEO na H and H? Zaku tafi ne unguwar masu kudi ya gina muku gida mai hawa biyar. Ni ma kuma dole zanyi aure, yanzu misali in na auri....... Na auri..... Na auri Adam drivern taxi yaje ya kama mana hayar gidan kasa kinga ai mun rabu kenan, banbancin yayi yawa"


 Ruqayyah ta kuma jawota tace "sai in saka mijina ya gina muku gida a kusa da gidan mu ya baku kyauta dan mu zauna tare" ta hade rai tace "kuma ba zaki auri Adam ba, kar ki ma kuma saka shi a misali" ta fita ta tafi yin alwala tana mita "na tsani wannan gayen wallahi, he is so arrogant and rude, gashi shi ba kowan kowa ba amma in yana magana kamar yafi kowa" tayi tsaki "inyamuri kawai. Watakila ma ba musulmi bane ba".


Ruqayyah tayi ta saka ran taji Baba ko Inna Ade sunyi mata maganar abinda bakuwarsu tace amma sai taji shiru, in ta taso da maganar sai Inna Ade tayi saurin chanja topic saboda bata son sauran yaran su san da maganar, Ruqayyah ta cika tayi ta kumburin ta sai duk suka shareta saboda dama ta saba fushin ta ita kadai.


Sai da dare bayan duk yara sun watse sannan Inna Ade tace wa Baba "Baban biyu ka fahimci inda maganar bakuwar na ta dosa kuwa? Ka gane abinda naso na gane?" Yayi ajjiyar zuciya yace "na fahimce ta uwar biyu, kawai dai nayi shiru ne kuma kema ina son ki cigaba yin shiru akan maganar saboda bama bukatar wani yazo ya gaya mana cewa mutanen nan ba sa'annin auren yayan mu bane ba, bana fatan yiwa yayana aure a gidan da za'a wulakanta su duk da dai su wadannan naga kamar ba irin sauran masu kudi bane ba, ni nafi son suyi karatu su nemi nasu na kansu ba wai su jingina da wani ba. Sannan kuma ita matar nan zata iya yiwuwa kawai nata ra'ayin ta fada bawai ra'ayin shi yaron ba, in yaron yana so da kansa zai zo ya nema. Dan haka mu bar maganar, muyi ta addu'a,idan yazo ya nema din kuma an samu daidaito tsakanin sa da yarinyar sannan mun bincika mun tabbatar da nagartarsa to alhamdulillah sai mu bashi ita" Inna Ade tace "to Allah ya shi ge mana gaba, ni ba wai maganar auren ce ta bani tsoro ba halin Ruqayyah nake gudu,dama Sumayya suka ce da sauki"


Baba ya kalle ta kawai ya dauke kai, amma maganar ta ta tsaya masa a rai. Tabbas gaskiya ta fada, duksu biyun yayansa ne amma suna da banbanci kwarai da gaske ta fuskar halayya.


A ɓangaren su Aunty bayan kuwa bayan sun koma gida su Nafisa suke ta zancen gidan. Hassana tace "Amma Aunty mutanen nan daga ganinsu suna da hali na gari, kinga yadda suka tarye mu da kulawa da karramawa? Basu da kudi amma tabbas suna da kamala" Safiyyah tace "suna kuma da addini, yanayin shigarsu da nutsuwar ƴaƴan ta birgeni" Khadijah tace "da tsaftar gidan, har muka fito banga datti ko digo ba, kayan sawarsu sun tsufa amma babu datti a jikin su" Nafisa tace "gasu kyawawa, kai twins din nan akwai kyau. Wato in suka samu kulawa sai an jinjina irin kyawun da zasuyi" Zulaihat tace "a yanzun ma ni banga alamar yunwa a tattare dasu ba, basu da rama kuma basu da datti. Hoda kawai suke bukata da jambaki" duk suka kwashe da dariya. Aunty tace "nima nutsuwa da tarbiyyar yaran ta bani sha'awa. Allah dai yasa yarinyar nan rabon Hassan ce dan ni kam nayi masa sha'awar ta sosai. Gata yarinya karama yadda juya ta ya kuma tarbiyyan tar da ita yadda yake so" 


Wannan yasa washegari tana tashi ta kira Hassan, Hussain ni ya dauki wayar suka gaisa sannan ya bawa Hassan da yake kwance yana ta juyi. Ya karba ya gaishe ta sannan tayi masa bayanin zuwan da tayi gidan su Ruqayyah


"Jabir ne ya karbo min address din a gurin police, gaskiya Hassan naji dadin ganin yaran nan da iyayensu. Alamu na zahiri sun nuna cewa mutanen kirki ne, badini kuma Allah ne ya barwa kansa sani" Hassan ya shafa sajen fuskarsa yana murmushi a ransa yana jin kamar an yaye masa wani nauyi yace "naji dadi sosai Aunty, naji dadi da kika yaba dasu" sai kuma ya danyi shiru cikin jin nauyin Aunty yace "kin ganta?" 


Sai da tayi dariya sannan tace "na gansu, su biyu ne ita da husainar ta. Kamar su daya komai nasu daga, daga dukkan alamu basu kammala secondary school dinsu ba dan ba gansu da uniform" ya gyada kai yana tuno fuskar Ruqayyah sanda take daure masa ciwon sa,ya lumshe ido ya bude yace "Nagode Aunty" suka yi sallama ya ajiye yana kallon Hussain take ta zabga masa harara, ya dga kafada yace "me nayi?" Hussain ya gyara zama yace "sai wani murmushi kake yi wai kai nan kayi budurwa. A dai bi a hankali" Hassan yayi dariya har sai da yaji wuyansa ya amsa sannan yace "oho dai" Hussain yace "wai yarinyar da ka hadu da ita cikin mintinan da basu wuce talatin ba, sannan kuma cikin tsakiyar dare ita ce kake ta kwarara wannan murmushi saboda ana yi maka maganar ta" ya danyi dan karamin tsaki.


Hassan ya mike daga kwanciyar da yake yi ya hade rai yace "ai ba mintuna ko lokacin da muka hadu ɗin ne madu muhimmanci ba, abinda tayi a cikin mintinan shine abu mai muhimmanci, ni na kasa gane kan ka Hussain, yarinyar nan fa rayuwata ta ceta, I owe her my life. Amma maimakon ace ka kasance mai farin ciki da ita sai kake furuci masu daci a kanta. It hurts me wallahi, and it makes me question matsayi na a gurinka" 


Hussain ya ajiye magazine din hannunsa yace "haka ne, I should be grateful to her, but bansan me yasa ba nake jin something odd about her ba, kawai ji nake sam ban yarda da ita ba" Hassan yayi murmushi yace "kamar yadda nima farkon soyayyar ku da gimbiya nake jin ban yarda da ita ba, gashi yanzu na fara sabawa da ita har muna zama muyi hira, kamar yadda na yarda da gimbiyar ka kaima one-day zaka yarda da tawa gimbiyar".



Sai da suka yi sati uku a can sannan suka dawo Nigeria, a lokacin Hassan ya warware sosai har ya maida kibar sa kuma yayi haske abinsa, Hussain wata daya yaso suyi amma Hassan yaki yarda dan shi Allah Allah yake yi su dawo yaje yaga Hassanar sa. "Kar tayi fushi, tace naki zuwa"


Ai kuwa Ruqayyah tayi fushin, tun tana kirga kwanaki har ta koma lissafin sati, gashi iyayenta sunki kwata kwata suyi mata maganar, Sumayya ma ta share ta. She became very edgy daga an taba ta sai bala'i har yan gidan duk suka share ta suka daina shiga harkarta. A haka har suka kammala neco dinsu, shikenan suna daina zuwa makaranta tunda ba waec zasu yi ba. Wannan zaman gidan shi ya cigaba da frustrating Ruqayyah, har mafarkin Hassan take yi wai ya dawo daga kasar waje ya siyo mata sabuwar waya mai kyau ƴar yayi.


A ranar kuwa ya dawo kasar, washegari ya taho ganin ta. Drivern da ya kawo su Aunty shi ya saka ya rako shi gidan tunda ba zai gane ba. Suna yin packing yabi katangar gidan da take rabi ta langa langa da kallo yana tuno memory din ranar nan sai ya jinjina hikimar ubangiji, ya tuna sanda ya shiga gidan ta tsakanin langa langa ya kwanta a toilet din gidan yana birgima saboda azabar ciwon da yake ji a kafarsa da jinin da yake zuba a wuyansa. 


Ya tuna sanda ta shigo toilet din tayi fitsari a gabansa ba tare da tasan yana gurin ba, yayi murmushi tare da alkawarin wata rana sai ya tsokane ta da abin, ya lumshe idonsa yana misalta yadda zata ji kunya ta kifa kanta a kirjinsa tana cewa "kaga bana so, ka daina tsokana ta, Allah zan rama nima" ya sake yin murmushi shi kadai yana girgiza kai, yasan da Hussain yana kusa dashi da sai ya dungure shi yace masa "idiot".


Drivern ne ya fita ya nemo yaro sannan ya tambayi Hassan "oga Hassan wa za'a ce ana kira?" Ya sake murmushi kamar idiot sannan yace "Hassana. Kace Hassan ne yazo yana son ganin Hassana" yaron da drivern duk suka yi dariya sannan yaron ya shiga ciki. 


Wanke wanken kwanuka take yi tana mitar Zunnur da ya ki cin abinci dare da Sulaiman ya zuba nasa daban ya kara mata kayan wanke wanke. Sumayya tana dora wa yara karatu akan baranda Inna kuma tana ruɗa tuwo. Yaron ya gaishe da inna sannan yace 

"Inji wani mai babbar mota yace wai Hassana tazo inji Hassan" 


Karaf a kunnuwan Ruqayyah, ta saki kwanon hannunta tana juyo wada sauri idanuwa a waje, suka hada ido da Inna, sai ta mike da sauri tana wanke hannunta da ƙafafuwan ta. Inna ta ajiye muciyar hannunta sannan ta bita dakin, kafin ta shiga har Ruqayyah ta birkito dukkan kayan su na cikin bagko tana neman wadanda suka fi ko wanne kyau. Inna ta tsaya tana kallonta tace "gashi kuma baban ku baya nan ballantana a tambaye shi izinin ki fita gurinsa" 


Ruqayyah ta yar da rigar hannunta ta juyo idonta har ya ciko da kwalla "Inna yanzu kuma jira zai tayi a waje har sai Baba ya dawo? Baban da bamu san lokacin da zai dawo ba? Inna tunda ke kina nan ki bani izinin mana, in Baba baya nan ai ke ce wakiliyarsa" Inna Ade ta girgiza kanta tana tabbatar wa da kanta hasahen da tayi akan Ruqayyah dai dai ne, sai dai kuma abinda Ruqayyah ta fada gaskiya ne, bai kamata abar bakoa waje yana jira ba kuma ita bata da waya ballantana ta kira baban biyu ta gaya masa labarin zuwan bakon. 


Sai tace "bana son ku tsaya dashi a waje, bana son kuma ku zauna a cikin motarsa, gashi kuma bamu da soro ballantana ya zauna. Abinda za'a yi bara in sallami yaran nan sai ayi masa shimfida a tsakar gida ku zauna ku gaisa, dake da Sumayya zaku je. Ni kuma zan zauna a daki. Ki kiyaye ni Ruqayyah, in kika nuna masa halinki wallahi xan saka baban ku ya gaya masa kar ya sake zuwa gidan nan" Ruqayyah tayi saurin gyada kanta, ta yarda, ta yarda da ko wanne sharadi in dai za'a bata wannan chance din. Wannan chance ne one in a million ta samu kuma ba zata yi wasa da shi ba.


Tana cikin shirya wa Sumayya ta shigo itama ta wanko fuskarta, duk basu yi kwalliya ba sai mai da suka shafa suka saka kaya da dogayen hijabs dinsu. Sannan Sumayya ta shimfida tabarmi guda biyu a kasan bishiya sannan ta shimfida sallaya a saman tabarma daya. Ruqayyah kuma ta dauko sabon kwanon shan ruwan Inna Ade ta debo ruwa ta ajiye sannan ta dora kofi akai.


Sumayya ce ta fita kiransa. Yana motar dai a zaune suna hira shi da drivern, lokaci zuwa lokaci yana kallon kofar shiga gidan zuciyarsa tana son ganin fitowarta. Sai ga Sumayya ta fito, idonta ya sauka kan motar amma da yake tinted glass ne bata hango na ciki ba amma shi ya hango ta, yaji bugun zuciyarsa ya karu, ya dakata da hirar da yake yana samun damar kare mata kallo tare da tunowa da waccan fuskar da ya gani ranar nan. Abinda ya fara fahimta a tare da ita shine yadda take tafiya cikin nutsuwa. Ta tsaya a gaban motar cikin yanayin rasa abinyi. Sai kuma tayi sallama tare da knocking window din. Yaji dadin sallamar da yaji tayi. Ya sauke glass din window din a hankali sannan ya sauke idonsa cikin nata. Tayi murmushi mai fadi, ko ba'a gaya mata ba ta san shine wannan duk da cewa ranar nan bata wani ga fuskarsa sosai ba. 


Ta dan durkusa kadan tace "ina yini, sannu da zuwa" ya jefa mata best smile dinsa yace "lafiya lau....." Sai ta katse shi "ammmm an ce ka shigo ciki, Ruqayyah Hassana tana ciki" ya kankance idonsa yana kallonta cikin mamaki, sai ta danyi yar dariya tace "ni sunana Sumayya...." Yace "Hussaina?" Ta daga masa kai ya bude kofar motar ya fito ya na kallon ta yace "gwara in gane ki sosai kar aje ayi min chanje" 


ta sake dariya, ya fahimci tana da fara'a sosai tace "baza ayi maka bama, ka kwantar da hankalinka" suka jera yana cewa "amma kuna kama sosai fa" tace "haka ake cewa, amma if you get to know us zaka gane banbancin mu" ita ta fara shiga sannan shi, abinda ya fara lura dashi shine tsaftar gidan da kuma alluna alamar ana koyar da karatu a gidan. Sai kuma yaga shimfidar da akayi masa sannan yaji kamshin tuwon da yake kan wuta. Ya zauna akan shimfidar sannan Sumayya ta durkusa ta sake gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa sannan ta tambaye shi mutan gida. 


A lokacin Ruqayyah ta fito daga dakin su, kanta akasa, hannayenta a boye a cikin hijab dinta, fuskarta cike da wani yana yi mai wahalar fassara. Tun da tayi taku na farko taji idonsa ya saukaa kanta, sai taji wani irin yanayi ya lullube ta taji abin duk ba yadda tayi tsammani bane ba, taji ta kasa dago kai ta kalle shi, taji kuma tana son ta kalle shi din. 


Kan daya tabarmar taje kusa da Sumayya ta zauna tare da gaishe shi murya can kasa " ya jikin? Allah ya kara lafiya" ya dan kalli dakunan d aduke gefe, ya san akwai mutum a cikin dakin dan haka dole yayi ajjiyar kalamansa sai wani jikon kuma. Amma shi kam yasan zuciyarsata tafi ga wannan yar karamar yarinyar da take kokarin gaisheshi. "Ya naki jikin? Ina fatan ranar nan baki ji ciwo ba" ta girgiza kanta tace "babu ciwo, Nagode" ya sunkuyo yana kokarin kallon fuskarta sai ta kara jawo hijab dinta ta kara rufe fuskar, ya danyi murmushi mai sauti yace "kin gode da me?" Tace "da ka damu dani har ka tambayi lafiya ta" yace "lallai ke ɗin ta daban ce tunda har zaki yi min godiya bayan nine ya kamata inyi miki godiya. Ki sani Hassana, bana jin akwai abinda zanyi miki wanda zai nuna irin godiya ta gare ki, duk abinda zanyi kwatanta wa ne kawai amma ninba zan iya biyan ki ba, Allah ne kadai zai biya ki. Ina kuma fatan ya biya ki da aljannar firdausi" 


Sumayya tace "ameen, tare da mu baki daya" ya sake kallon dakin yana feeling uncomfortable, akwai maganganu daya ta tsarawa tun a India amma duk ba zai iya fadin su ba a wannan setting din, dole ya bar wannan ziyarar a matsayin ta godiya kadai in yaso in ya kuma xuwa ya fara kafa gwamnatin sa. Amma duk da haka zai gwada ko dan kadan ne, at least dan asan inda ya dosa.


Ya kalli Sumayya yace "kinga har na gano banbancin ku da Hassana ta" Sumayya ta bude ido tace "menene banbancin?" Yace "Hassana ta ta fiki nutsuwa, ta fiki kunya tunda gashi nan ta kasa kallona har yanzu kuma ta kasa bari in kalli fuskarta. Ki roka min ita ta kalle ni ko da sau daya ne kar ta saka yau in manta hanyar gidan mu in dawo nan in kwana" 


Sumayya tayi dariya tace "in kai ka manta drivern ka aishi ba zai manta ba" ya dafe kai yace "haka ne fa. To amma ai na kasa bacci ko? In banyi bacci ba kuma kinga ba zan samu karfin da zan dawo gobe in tambayi Baba ya bani izinin fara zuwa zance gurinta ba" Sumayya ta sake dariya, Ruqayyah ma ta danyi dariya a cikin hijabin ta, tana kallon saitin fuskarta ta cikin hijab din yace "kuma na sake gano wani banbancin naku, ta fiki kyau, dan na hango dogon hancinta ta jikin hijab" Ruqayyah tayi sauri ta kuma jan hijab din gaba yadda fuskarta ba zata fito ba. 


Yayi gyaran murya yace "abinda duk nake nema zan iya cewa na same su gabaki daya a gurin ki Hassana. Addini, tarbiyya, kunya, nutsuwa, kyau duk kina dasu. Ni na riga na samu mata Ruqayyah in dai kin amince kina sona ni da gaske nake aurenki zanyi in dai har iyayenki zasu bani ke" ya sake rage murya yace "amma ai ba zaki amince ba in nayi miki, ba zaki gane nayi miki ba kuma sai kin kalle ni" Sumayya ta kuma yin dariya, sai yaga tana tuna masa da Hussain ta bangaren fara'a. Sai ya samu kansa da fara yi mata hirar Hussain. 


Ruqayyah ta dan bude fuskarta kadan ta mike ta zuba masa ruws a kofi tace "ga ruwa, ka sha" ya karba yana cewa "nagode sosai" sannan ya kalli Sumayya yace "kinga inda aka damu dani an fahimci ban sha ruwa ba, ke kuwa sai magana kuke saka ni" Sumayya tace "to bara in tashi in tafi in ya so sai kuyi hirar kurame tunda na fahimci ba magana zata yi maka ba" ya shanye ruwan ya ajiye cup din yace "kiyi zamanki, nine dai zan tafi. Ki mika min gaisuwata a gurin Mama sannan ki yi kokari gurin kafa min gwamnati na, ki fara da Foundation mai kyau dan ginin da nake so inyi na har abada ne" 


ya mike sannan yace "in Baba ya dawo ki gaishe min dashi sannan ki gaya masa in babu damuwa gobe da kamar wannan lokacin zan dawo ina son magana dashi" ta amsa masa da insha Allah, sai ya dauko daurin kudi ya ajiye akan shimfidar yace "gashi ki sayi sweet, dan naga alamar kina da kwadayi" 


Ranar Ruqayyah bata iya bacci ba. Tana ta sakawa da warwarewa.


Washegari ya dawo kamar yadda yayi alkawari. Baba kuma already yana zaune yana zamn jiransa kuma ya yanke shawarar abinda zai gaya masa, danda aka aiko ya zo sai Baba ya saka Sulaiman ya shimfida musu tabarma a waje daga gefe inda mutane ba zasu dame su ba, sannan ya fita gurinsa. 


Ganin haka yasa Ruqayyah ta kira Zunnur ta tambaye shi a inda suke, ita kuma ta tafi dai inda suke daga cikin gida tayi shimfida ta zauna tana yanke farcenta. Kawai haka nan taji zuciyarta tana son taji maganar da zasu yi. 


A waje Hassan ne tare da Jabir, yaso Hussain yazo du taho tare amma sai ya kirkiri wani excuse ya kawo amma Hassan ya fahimci zuwa ne baya son yi kuma yaji babu dadi. Bayan sun gaisa cikin mutunci da girmama juna, sun kuma yo doguwar godiya a bisa taimakon da aka yiwa Hassan a gidan sai Jabir ya shigar da maganar kudirin Hassan na neman izinin fara neman auren Ruqayyah. 


Baba ya masu kudurin su cikin nuna jin dadin wannan karramawar amma kuma sai yace "amma wani hanzari ba gudu ba, ni ba zan boye maka ba tun ranar dana fara ganinka naji zuciya ta tana sonka, naji a raina ina ma dai kai dana ne, kuma yanzu zanji dadi sosai idan ka zamo dan nawa wato in ka auri yata, sai dai, in har ka amince ina son ka chanza daga Ruqayyah ka nemi Sumayya" 


Ruqayyah ta dago kai daga yankan farcen ta, ba tare da ta ce komai ba ta mike ta tafi daki tana jin zuciyarta ta zama tamkar dunkulallen garwashin wuta.


Wannan littafin na kudi ne, duk mai son siya tayi wa wannan number din magana 09135803002 



Episode thirteen: The Strategy


Duk suka yi shiru suna kallon sa, Hassan cikin sanyin jiki yace "saboda me Baba?" Baba yace "Saboda kamar yadda na fada ina sonka, duk su biyun yaya na ne basu da banbanci a guri na kuma suma duk ina son su, dan haka nake fatan idan sunyi aure auren nasu zai zauna har mutuwa, bana fatan ka auri yata kuma ka rabu da ita saboda wani hali nata da zaka ga baiyi maka ba, wannan shi yasa nake ganin alakar ku zata fi tafiya daidai da Sumayya, saboda a yadda na fahimta kamar halin ku yafi zama daya akan ita Ruqayyah"


Jabir yayi gyaran murya yace "Baba ita Ruqayyah tana da wani aibu ne? Wani hali da ya kamata a sani kafin a aure ta? Ko tana da wata cuta ce?" Baba ya girgiza kai, Ruqayyah yarsa ce kuma yana sonta, kuma son da yake mata ne ya saka shi wannan batu, aure ba abin wasa bane ba, ba kuma a gina shi a kan ƙarya da rufa rufa in dai har ana so ya dore. Yana son auren Ruqayyah da Hassan ya dore in dai ya kasance, shi yasa zai gaya masa in zai aure ta a haka shikenan in kuma ba zai iya ba sai ya karbi Sumayya in ita ma baya so shikenan. 


Yace "Ruqayyah tana da zafin zuciya sosai, taurin zuciya da kafiya, ko mu iyayenta muna fama da ita a kan hakan. Bata da son mutane sosai saboda tana da fada, bata da tsoro sam. Kai kuma na fahimci mutum ne mai jama'a dan haka nake ganin kamar tafiyar ku ba zata zo daya ba" 


Hassan ya shafa kansa yana sauke ajjiyar zuciya, shi baiga aibu a duk abinda Baba ya fada ba, dama ai ya riga yasan da rashin tsoron da taurin zuciyar tun sanda ta taimaka masa, rashin son mutane kuma shi zai iya cewa abin dadi yayi masa dan shi din ma ba mai son mutanen bane ba dan haka kullum yake fatan kar ya samu mace mai kwashe kwashen mutane yadda zasu ji dadin zamansu su kadai.


Yayi murmushi yana kallon Jabir shima da yake murmushi, sun dai fahimci cewa Baba mutum ne mai karanci da yawa yadda har zai fada musu abinda yake ganin aibu ne akan yar da ya haifa a cikinsa saboda ya kyautata dangantakar sa da su. Hassan yace "Baba ni ina ganin wannan ai duk ba wani abu bane ba, wannan ba abinda zai hana ayi aure bane ba, kuma ni itan dai Baba in za'a bani ita nake so Sumayya kuma sai ta zama kanwata" Jabir yace "wannan haka ne, kuma kusan duk halin daka lissafa irin na Hassan ne" ya fada cikin tsokana, "haka muke ta fama dashi, baya daukan raini ga kafiya, ina jin abin nasu a sunan ne" suka yi dariya su biyu banda Baba, shi gani yake yi kamar basu fahimce shi bane ba, amma zama da Ruqayyah su kansu da suka haife ta dauke kai kawai suke yi a lokuta da dama, suna ta yi mata addu'a kuma suna saka ran idan ta kara girma zata rage, sai dai baiyi tsammanin za'a zo neman aurenta haka da wuri ba. Yayi wa Hassan tayin auren Sumayya ne saboda yana ganin Hassan da Ruqayyah ba wai saba wa suka yi da junansu ba.


Yace "shikenan tunda kunji kuma kun amince, kunga nan gaba ba zaku zo min da korafi ba kuma. Zamuyi ta muku addu'a, Allah yayi mana jagora baki daya, Allah ya hada kanku. Na baka damar ka neme ta, idan kuma ka chanza shawarar a tsakiyar neman ka sani ba zan kullace ka ba sai dai ba kuma zan baka Sumayya ba a lokacin".


Hassan yace "insha Allahu hakan ma ba zata faru ba. Kowa a duniya ai dole yana da wani aibu da wadansu daga cikin mutane ba zasu so ba, ko ba Ruqayyah ba nasan bazan samu mace da take da komai ba dole sai an samu aibu".


Suka yi godiya, sannan Baba ya jero musu doguwar addu'a duk duka shafa suka tashi. Hassan yaso yaga Ruqayyah amma kuma yana jin nauyin Baba, haka ya shiga mota suka tafi yana kallon kofar gidan da fatan ko Allah zai saka yaga giftawar ta.


Ruqayyah tana shiga daki sai ta kwanta akan katifa ta jawo zani ta lulluba duk da ba wai sanyi take ji ba, so take tayi kuka amma kukan yaki zuwa, haka taje ji lokuta da dama idan aka bata mata rai sai dai tayi ta jin zafi a ranta ba zata iya kuka ba har sai ta samu tayi masifa tukunna zata ji ta huce. Idonta ya kada yayi jawur kamar garwashin wuta. Anya kuwa Baba ne ya haife ta? Anya kuwa uban da ya haifi ya zai iya yi mata abinda Baba yake shirin yi mata? Har zai ce zai bawa Hassan Sumayya? Zai ce da Hassan kar ya aure ta? Ita kuwa wanne irin laifi tayi wa Baba da yayi mata irin wannan tsana haka?


A lokacin Sumayya ta shigo dakin, farko bata lura da Ruqayyah ba sai daga baya ta ganta a takure a karshen katifa, ta taba jikinta da sauri "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ruqayyah baki da lafiya? Menene ya same ki?" Sai a lokacin Ruqayyah ta samu hawaye suka zubo mata, ai kuma ta fara rera kuka marar sauti kamar zata fito da zuciyarta, Sumayya kawai ya rungume ta ta barta tayi ta kukanta sai data gama sannan tace "Sumayya Baba baya sona ya tsane ni" da sauri Sumayya ta rufe mata baki tace "subhanallah, me kike fada haka? Baba yana son mu mana, yana son mu sosai da sosai" Ruqayyah tana girgiza kai tace "yana sonki dai amma banda ni. Ni ya tsane ni kamar bashi ya haife ni ba" sai ta bata labarin abinda taji.


Sumayya ta dora hannu aka fuskarta rubuce da tashin hankali sannan ta sauke tace "me ya kaiki Ruqayyah? Me ya kai ki zuwa kiji abinda zasu ce, ina ruwanki" Ruqayyah tace "magana ta fa zasu yi, zuciyata tana ta gaya min inje inji abinda zasu ce ashe akwai dalili, ashe zuciyata bata yarda da Baba bane ba"


Sumayya tace "wato ke kuma shikenan duk abinda zuciyarki ta gaya miki shi zakiyi? Ba zaki yi tunani da kwakwalwar ki ba sai kiyi aiki da zuciyarki? Ban shiga ran Baba ba Ruqayyah, bansan menene dalilin sa na fadar abinda ya fada ba amma nasan ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana tsoron halinki, yana tsoron kar kije gidan kiyi ta musu halayyar ki azo aji kunya, kuma ni banga laifinsa ba" Ruqayyah ta fara ture ta tana kokarin mikewa tsaye tana kunkuni, Sumayya tace "ko me zaki ce sai dai kiyi ta cewa amma ni dai ba zan daina gaya miki gaskiya ba, kuma ina so ki sani, ko maza sun kare a duniya bazan auri Hassan ba dan haka kar ma ki saka wani abu a ranki, tunda Hassan ya nuna yana sonki to kuwa tabbas ya haramta a gareni. Amma in baki chanja hali ba zaki yi loosing dinsa, ko Baba bai hana shi ke ba shi da kansa zai gudu yace ya fasa" 


Ruqayyah tayi hanyar kofa zata fita kuma sai ta tsaya, sai ta juyo tana kallon Sumayya tace "menene zai saka yace ya fasa?" Sumayya ta jawo ta ta dawo da ita zaune tace "halinki. Yadda na fahimce shi shi kamilar mace yake so mai kyawawan dabi'u, to in kina so ya aure ki sai kin zama mai wannan halin, abu mafi muhimmanci kuma sai kin cire son abinsa a zuciyarki, dan in dai ya fahimci kudinsa kike so bashi ba to kuwa zai gudu, ki nuna kudinsa bai dame ki ba, kinuna masa kina sonsa sosai, watakila ma kiga har kin fara son nasa da gaske" 


Ruqayyah tace "waye yace miki bana sonsa yanzu" Sumayya tayi murmushi tace "ina fata. In ma kina sonshi to kinfi son dukiyarsa a kansa, ba Hassan kike so ba CEO na H and H kike so, ko ba haka bane ba?" Ruqayyah tace "shi din dai shine duk biyun, to menene abin damuwa a ciki?".


Sun jima suna hirar abin a tsakanin su, Sumayya tana ta bawa Ruqayyah shawarwari a ranta kuma tana fatan Hassan bai karbi tayin Baba ba saboda in ya karba dole zata yi wa Baba musu, dan ba zata iya auren Hassan din Ruqayyah ba. Ko da ace ita yace yana so zata iya barwa Ruqayyah shi dan a zauna lafiya. Ita farin cikin family dinta shine gaba da komai a gurinta.


A bangaren Ruqayyah kuwa hankalin ta ya kwanta sosai ta jin ikirarin Sumayya na cewa ba zata auri Hassan ba, kuma tasan indai Sumayya tace haka to Baba ba zai matsa mata ba. Sai kuma ta fara duba shawarwarin da Sumayya ta bata, ta kuma yarda lallai Hassan mace ta gari yake nema kuma indai ta nuna masa iri dabiun ta zai iya cewa ya fasa sai dai duk su biyun suyi asarar sa, ita kuma bata fatan wannan irin babbar asara ta same su. Ba dai mace ta gari yake so ba? To kuwa tabbas zai samu mace ta gari. Ita Ruqayyah ta kama shi a cikin faratan ta kuma ba zata taba releasing dinsa ba har sai burin ta ya cika, burinta na zama matar CEO of H and H.


Tagwayen sunyi ta jira suji Baba yayi musu magana akan abinda suka tattauna da Hassan amma bai ce musu komai ba, dan haka suka kasa tantancewa ko Hassan ya karbi tayin Baba ko kuma bai karba ba. Ruqayyah kuma tayi iyakacin kokarin ta na dannewa bata nuna wa Baba cewa taji tayin da yayi wa Hassan ba, sai dai a zuciyarta ta kuduri aniyar cewa zata tabbatar cewa watarana yayi nadama, wata rana sai yayi nadamar zaben Sumayya akan ta.


A bangaren Hassan kuwa fushi yake yi sosai da Hussain saboda halin ko in kula da yake nunawa akan Ruqayyah, rigima a tsakanin su har gaban Aunty "Aunty yaron nan wai yaje yaga yarinyar nan yayi mata godiya akan abinda tayi min amma yaki, kiri kiri yake nuna min kiyayyar sa akanta" Hussain yace "ni nace maka bana sonta? Ni nace maka ina kinta? Kawai hankali na ne bai kwanta da ita ba" Hassan yace "ta yaya to hankalin naka zai kwanta da ita idan baka je ka ganta ba? Ta yaya zaka yarda da ita in baka fahimce ta ba?" Hussain ya mike yace "alright, send me the address, zanje gobe mu gaisa shikenan?" Hassan yace "ba shikenan ba, sai kaje sannan maganar zata wuce". 


Suka mike a tare suka fita suna cigaba da rigimar, aunty ta bisu da kallo sannan ta girgiza kanta, ita da aka zo gurinta da niyyar tayi Shari'a amma ba'a bar ta tace komai ba har aka gama shari'ar.


Bayan sun fita daga gurin Aunty dai suka ajiye maganar Ruqayyah suka koma hirar Company, dama batan Hassan ne ya tsayar da maganar amma yanzu tunda komai ya lafa zasu cigaba da shirye shiryen su. Hassan yace "already dama na riga nayi sanarwar wadanda aka yiwa interview su dawo a sake musu, tunda na rasa duk bayanan su a cikin mota ta data bata" Hussain ya daga kafada yace "shikenan, duk abinda kace haka za'ayi. Ina dai son mu gama daukan ma'aikata as early as possible saboda in samu in mayar da hankali na kan ginin gidan can da kuma sauran al'amuran biki" Hassan ya juya ya kalli side din da twin houses dinsu suke. 


Gida ne Hussain ya siya ajikin gidansu, mai gidan ne Allah yayi masa rasuwa sai magada suka saka gidan a kasuwa shi kuma Hussain ya siya, katon gida ne na gaske, amma Hussain ya saka akazo akayi flat dashi, a lokacin sai da suka yi ta rigima da Hassan saboda shi yana ganin rashin dacewar hakan. "Wannan ai almubazzaranci ne" shi kuma Hussain yace "plan din mutum daya ne a gidan, ni kuma so nake muyi twin houses ni da kai yadda zamu zauna da iyalan mu seperately but together, sannan kuma ga Aunty a kusa damu".


Sai dai kuma ganin cewa da akwai sauran lokaci ya sa har yanzu bai mayar da hankali wajen kammala ginin ba saboda so yake yayi shi a nutse, using the very best of komai, dan Hussain baya karbar komai in ba best ba.


Hassan ya bude motar sa yana shiga, Hussain ya leko da kansa yace "zanje fa" Hassan ya haɗe rai yace "kar Allah yasa kaje ɗin".


Washegari Hussain ya shirya yaje. A kofar gidan da aka kwatanta masa da Google map ya tsaya yana karewa gidan kallo sannan ya juya yana karewa unguwar kallo, yana lura da yadda mutane yara da manya suke ta kallon motarsa. Ya dan sauke glass ya kira wani yaro wanda ya taho da gudu yana leka cikin motar. Hussain yace "ka shiga gidan nan kace wai ana kiran Hassana tayi bako" yaron ya girgiza kansa yace "babu Hassana a gidan" Hussain ya hade rai yace "babu Hassana kuma? Sai wa?" Yaron yace "akwai Sumayya akwai Ruqayyah" Hussain ya tabe baki yana sake kallon gidan, tabbas nan ne gidan ta yadda aka fasalta masa shi. 


Yace "to kace ana kiran su duk su biyun" da sauri yaron ya shiga. Yana bude kofa kofar gidan suka kusa yin karo da Ruqayyah wadda taji alamar tsayuwar mota ta taho yin tsegumi, a ranta tana fatan Hassan ne ya dawo kuma gurinta yazo ba gurin Sumayya ba. Ta ja yaron gefe, "waye a waje?" ya wangale mata baki cikin murna yace "wani farin kyakkyawan saurayi ne yake kiran ku ke da Sumayya" ta bata fuska cikin mamaki "fari kuma? Baki dai ko? Ko baka gani sosai ba?" Yaron ya girgiza kansa yace "fari ne wallahi, tas ma kuwa" 


Ta juya tana kallon dakin da Inna Ade take ciki sannan ta leka ta tsakanin kofa, ba irin motar ranar nan bace wadda Hassan yazo da ita, wannan ta ci uban waccan, ita bata taba ganin irin wannan motar ba ma. Ta koma da baya tana dafe kirjinta. Waye wannan kuma? Ko Hassan ne yayo mata aike a daya daga cikin motocin sa? Ko motar ya aiko mata da ita kyauta?


Muryar Inna Ade taji daga bayanta, "me kike yi a gurin nan Ruqayyah?" Ta dan tsorata kadan sai kuma ta saki fuskarta. "Wai wani ne yake kiran mu ni da Sumayya" Inna Ade tace "kuma shine kike leka shi" ta juya gurin yaron tace "kaje kace waye" yaron ya fita ya tambayi Hussain, ya danyi tsaki yana kallon agogon hannun sa yace "kace hussainin Hassan ne" yaron ya koma ya fada. 


Ruqayyah ta dan bata rai. Me yasa shi Hassan ɗin ba zai zo ba sai ya bawa Hussain motarsa ta taho? Ko dai ya karbi shawarar Baba, ko kuma har yanzu yana tunani ne akan shawarar. Inna tace "ku saka hijaban ku ku je, zuwa yayi ku gaisa" sai ta dauki kudi a cikin kuɗin da Hassan ya ajiye musu shekaran jiya ta bawa yaron tace yaje ya siyo lemo guda daya da ruwan roba guda daya.


A tare suka fita, ya bi su da kallo yana studying dinsu har suka zo gaban motar suka tsaya sannan ya sauke glass din. Sumayya tayi masa murmushi, sai ya mayar mata kuma yaji bai kamata suna tsaye a waje shi kuma ya zauna a mota ba. Ya bude motar ya fito. Wani irin lugude zuciyar Ruqayyah take yi. What? Wannan ai yafi Hassan dinta haduwa, ya akayi dan uwansa ya fishi haduwa?


Ta sauke idonta kasa tana tuno karin maganar hausawa da suke cewa ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau. 


Sumayya ce ta fara gaishe shi sannan Ruqayyah ita ma ta gaishe shi. Ya amsa yana rarraba ido a tsakanin su. Yace "wacce ce yayar tawa a ciki?" Sumayya tace "ka chanka" ya kalle ta ya kalli Ruqayyah da idonta yake kasa yace "hmmm. Hassan yace min hassanar sa tafi yaruwarta komai, hankali, nutsuwa, kyau, bla bla bla. Jiya haka ya kwana yana min sambatu duk ya hana ni bacci shi yasa nace yau dai sai nazo naga wannan Hassana na huta, kuma from all indications..." Ya nuna Ruqayyah "ke ce Hassanar" Ruqayyah taji sanyi a ranta, wato Hassan bai chanja ra'ayin sa ba, Baba bai yi convincing dinsa ba.


Sumayya tayi dariya tace "son kai yake yi fa da yace ta fini komai" Hussain yace "na yarda dake, ta dai fiki sunkuyar da kai. Kin fita fara'a kuma daga alama zaki fita son mutane" ya fada cikin sigar tsokana, Ruqayyah ta danyi murmushi tana wasa da bakin jihab dinta sannan tace "na gane niyyar ku, so kuke ku hade min kai dan kunga baya nan ballantana ya tare min" Hussain yace "ohhh ashe kina magana. Ni na dauka ai mu biyu zamuyi hirar mu ban da ke"


Yace "to Malama Hassana, nazo ne......." Ruqayyah ta katse shi "Ruqayyah" yace "what?" Tace "Ruqayyah shine sunan" yace "ohh, ni kuma Hassana ake ta gaya min a kunnuwa na" tace "wannan shi kadai yake fada ai. Special" yayi dariya sosai yana bayyana dimple dinsa, Sumayya ma ta taya shi dariyar tana cewa "Ruqayyah yaushe kika kile har haka?" Hussain yace "wallahi Hassan ya taro match. Kuma kamar kin fada a kunnuwan sa" ta dan rufe fuska alamun kunya "kar ka gaya masa dan Allah".


Yace "kinsan me? Naga alamar kamar zaku daidaita da Gimbiya ta, Fatima sunanta, ita ce wadda zan aura. Tunda taji labarin ki take addu'ar ku daidaita da Hassan sai a hada bikin mu nan da wata biyar" ya zaro wayarsa yana bude lock din yace "ki saka min number dinki sai in bata ta kira ki ku gaisa" ta karbi wayar tana kallon hoton da yake kan screen din. Hoton sa ne tare da wata kyakkyawar yarinya wadda kallo daya tayi mata ta san ta fita komai, taji wani abu ya tsaya mata a wuyanta yana so ya kawo hawaye cikin idonta 


Ta yi sauri ta mika masa wayarsa tace "bani da waya ai ni" Sumayya tace "kasan yanzu ne muka gama secondary school, Baba kuma dama yace sai mun gama zai siya mana waya" ya dan bata rai yana tunani yace "ku ka gama ko zaku gama? ai ba'a gama exams ba an dai yi neco saura waec. Ba zakuyi waec din ba?" Suka yi shiru duk su biyun, sai ya fahimci bashi da amsa dan haka yayi saurin chanja topic din da cewa "amma dai zaku cigaba da karatu ko?" A tare suka ce "eh" yace "good, Allah ya taimaka".


A lokacin ne yaro yazo ya kawo masa lemo da ruwa a jere akan karamin faranti tare da kofi akai. Sumayya ta karba sai ta bude motar ta ajiye masa sannan ta rufe. Yace "Nagode sosai. Dama kishirwa nake ji. Bara inzo in tafi kar in gajiyar daku da magana, ni bana gajiya da magana. Sai dai kuma gashi ban kawo muku komai ba" da sauri Ruqayyah tace "lah, babu komai, ai zuwan shine mafi muhimmanci akan wani abu" Sumayya ta kalle ta da mamaki sai kuma tayi saurin gyara fuskarta tace "haka ne" yace "a'a ba haka bane ba, ita kyauta ai abu ne mai kyau saboda tana kara soyayya a zukatan mutane, ko mai kankantar abu in aka baka shi kyauta sai kaji wanda ya bakan ya kara samun daraja a gurinka. Nima kunga yanzu ruwan da kuka bani ai naji dadi har cikin raina. Koda mutum ya fika komai na duniya in kuka hadu samu wani abu ka bashi, zaka kara daraja a gurinsa"


Ya cigaba "wannan yasa duk wanda na hadu dashi ina kokari inga na bashi wani abu da zai ke tunawa dani kuma yaji yana son mu sake haduwa. Ku ma kuma ba zaku zama exceptional ba. Ban taho da leda ba amma na san a jikina ba za'a rasa wani abu ba, ko cash ne" sai ya fara laluben jikin sa, yayi tsaki "these days sai mutum ya duba jikinsa yaji wai bashi da kudi".


Ruqayyah ta sake cewa "ba wani abu fa, ka barshi kawai".


Sai ya bude motar ya bude aljihun mota, sai gashi ya dauko rafar farare bugun Abuja, ya fito ya miko wa Sumayya, ga wannan kwa sayi jambaki" Ruqayyah tayi saurin rike hannun Sumayya duk kuwa da cewa sumayyan ba wai miko hannun tayi ba tace "uhm uhm, ba zamu karba ba gaskiya." Da mamaki yace "saboda me?" Ta sunkuyar da kai still hannunta rike dana Sumayya Tace "kawai dai. Babu abinda zamuyi dashi. Mungode" 


Yace "ban taba jin yammata sunce babu abinda zasuyi da kudi ba sai yau. Ni sisters dina kullum complain suke kudi yayi musu kadan, kullum suna cikin siyan kayan kwalliya, jaka takalmi, da sauransu" Ruqayyah tace "mu duk wannan basu dame mu ba" 


Yayi ajjiyar zuciya sannan ya jefa kudin cikin mota, Ruqayyah taji tamkar zuciyarta ya ciro ya jefa a mota amma ta maze, yace "ban taba yin kyauta an dawo min da ita ba sai yau. Amma babu komai, nasan ta inda zan bullo muku" duk suka yi murmushi. Yayi musu sallama ya shiga mota suka matsa ya tafi. 


Sumayya ta juyo gurin Ruqayyah "what? Kece kika mayar da wannan kuɗin da kanki?" Tayi ajjiyar zuciya "kar ki kara min bakin ciki akan wanda nake ji already. Ke fa kika yi min wa'azin in chanja hali, to halin nake chanja wa" ta wuce ciki a ranta tana mitar yadda Hussain zai dauki wannan uban kudin a motar Hassan yayi kyauta dashi, Allah kadai yasan irin barnar kudin da yake yi masa.


Hussain yana kallonsu ta mirror har suka shiga gida sannan ya mayar da hankalinsa fully kan tukinsa, ya girgiza kansa, shi har yanzu bai ji tayi masa ba duk kuwa da cewa bashi da wani dalili na feeling like that. He test them with money kuma sunci jarabawar amma still.......


Ya dauki wayarsa ya kira Hassana (kanwarsu) "zan turo miki kudi yanzu kije ki fitar ki danyo min siyayya irin taku ta mata, kaya masu kyau, komai guda biyu iri daya. Zan kuma yi miki aike sai ki hada da kayan ki bawa drivern da yasan gidan su Hassana akai musu ita da yaruwata".


Bayan sun gama wayar ya kira wani dealer na waya da yake kawo masa wayoyi yace "ina son wayoyi guda biyu, latest. Ka aika min dasu gida".


Da daddare suna zaune a tsakar gida suna cin tuwon shinkafa miyar taushe har da nama, duk a cikin kudin da Hassan ya ajiye ranar nan ne. Gaba dayansu su hudu a tray daya Inna kuma da Baba suma suna ci tare, ga maganin sauro an kunna a gefe ga iska tana kada su. Baba yana basu labari "wato gobe akwai drama, an sake aiko mana fa mu koma wannan inta uku din nan. Gashi yaron nan Hassan naga alamar bai san dani a ciki ba sai dai kawai ya ganni" a lokacin suka ji tsayuwar mota sannan aka yi sallama. Sulaiman ne ya fita, an jima kadan sai gashi da bagco guda biyu da kuma karamar leda yana ta washe baki. 


"Wato yammatan nan sai kun bani tukuici, wai wannan kayan sako ne inji Hussain yace ace muku "asha yammatanci lafiya".



Wannan littafin na siyarwa ne, in baki sani ba kika karanta a rashin sani to yanzu kin sani. In kina son cigaba ki nemi wannan number 09135803002 



Episode Fourteen : The Gate man


Da sauri Ruqayyah ta mike, zuciyarta fara kal kamar takarda, it is about time daya kamata suma su fara shigowa gari. Wannan talauci haka har ina!


Ta tari Sulaiman a hanya tana karbar karamar ledar cikin zumudi tace "inji Hussain ko inji Hassan?" Ya dan dakata yana tunani sai kuma yace "kamar dai Hussain yace min, oga Hussain, haka yace. Amma bara in koma in sake tambayar sa" ya ajiye kayan zai juya Inna Ade tace "kai! Dawo nan. In Hassan in ma Hussain menene abin tambaya? Duk daya ne in daya ya bayar tamkar dayan ya bayar ne " 


Ruqayyah ta bude ledar hannunta, jikinta har rawa yake yi, tayi arba sa kwalayen waya guda biyu "wayyo Allah na" ta fada tana rungume kwalin wayar a kirjinta "Sumayya wayoyi ne, handsets ne ta so ki gani!" Sumayya ta ajiye cokalin hannunta ta mike da sauri tana karbar guda daya a hannun Ruqayyah sannan suka saka ihun murna suna rungume juna. Samarin kuma suka bude jakankunan suka fara fito da kayan ciki. Kayan sawa ne da sauran kayan bukatu na mata. Zunnur yace "wannan duk sanda ya sake dawowa sai naje na gaishe shi nima na samu rabona".


Baba ya daga murya yace "lafiyar ku kuwa? Menene haka kuke yi? Menene wannan din?" Inna Ade ta karbe wayoyin hannunsu Ruqayyah sannan ta ja jakar zuwa gaban Baba, Ruqayyah ta biyo ta tamkar magnet, Inna tace "kaya ne baban biyu, Hussain ne dazu da bakanan ya zo yaga yaran nan shine yanzu ya aiko musu da kaya. Ta fada tana kokarin firfito masa da kayan, ya hade rai yace "kayan lefe ne?" 


Ta yi dariya "kayan lefe kuma Baban biyu? Kayan lefen ne za'a aiko driver ya kawo?" Yace "to kayan menene?" Tace "kyauta ce kawai yayi musu" ya kuma hade rai "gaya masa sukayi suka ce basu da suttura? Ko kuma sutturar jikinsu ya raina" Inna ade tayi shiru, ya juya kan yammatan, "rokonsa kuka yi kuka ce ya siya muku?" Da sauri Ruqayyah, cikin rawar murya tace "wallahi Baba ba rokonsa muka yi ba, daya bamu kudi ma cewa muka yi bama so, shine kawai ya aiko mana" ya juya kan Inna Ade "to ba da ni za'a yi wannan abin ba. Yanzu me kike tunanin zai faru idan Hassan din yace ya fasa aurenta? Ya zamuyi mu biya su kayan su? Gidan nan zan saka a kasuwa?" A hankali Ruqayyah tace "ba zai ce ya fasa ba" ya juyo yana kallonta yace "to fitsararriya, ina magana kina mayar min ko? Ta yaya kika san ba zai ce ya fasa ba? Kin san abinda gobe zata zo dashi ne?" 


Inna Ade tace "amma Baban biyu bana jin irin mutanen da zasu yi mana haka ne, in sun fasa ma bana jin zasu ce a biya su kayan su, kuma ma ai ba rokonsa suka yi ba" yace "to kaddara ma ba zasu ce a biya su ba. Yanzun in kika bawa wannan yarinyar" ya fada yana nuna Ruqayyah data rungume kwalin waya a kirjinta idonta ya kada yayi jawur "wannan wayar, kika kuma bata sannan leshin ta saka, idan ba'a yi auren ba ta yaya zata cigaba da girmama wannan" ya nuna wayar hannunsa "da kuma wannan" ya nuna kodaddiyar atamfar jikin Inna.


Ruqayyah ta maimaita "ba zai ce ya fasa ba" yayo kanta "in kika kara Magana sai na kakkarya ki a gurin nan na zubar da kasusuwanki" Inna Ade ta shiga tsakani tana bashi hakuri "dan Allah kar ka taba ta Baban biyu, dan girman Allah kar ka dake ta" ya juyo kanta "ki tattara kayan nan ki nemi gidan wata kawarki ki kai a ajiye, duk ranar da akayi auren sai a dauko su a basu" 


Ruqayyah ta durkusa "Baba dan girman Allah kar ka karbe kayan nan, dan Allah ka bar mana abin mu, na tuba Baba wallahi na daina duk abinda baka so, dan Allah ka bar min kayana Baba" Inna Ade ta taya ta roko "ko ba zaka bar musu wayar ba ka bar musu kayan suma su samu suyi kwalliya, ba rokon su suka yi ba kyauta ce suka basu kuma shima Hassan din ai zai so ya ganta fes fes, gashi yan'uwansa suna zuwa, dan Allah Baban biyu kayi hakuri ka bar musu" yace "wato da saka hannunki kenan ko? Shikenan, su rike kaya amma babu ruwana"


Ya juya ya saka takalmi ya fita, Inna Ade tasan fushi yayi amma kuma bata son abinda zai kara hargitsa tsakanin sa da Ruqayyah, kuma ita tana ganin babu laifi in an karbi kayan. 


Bayan ya tafi suka zauna suna dudduba kayan duk da dai duk jikinsu a sanyaye yake da fadan da Baba yayi, banda Ruqayyah da take ta lissafin wanne tailor ne yafi kowa iya dinki a kaduna? Gurinsa zata kai dinki. Ta dora wata doguwar riga kenan a cinyarta sai wata envelope ta fado daga cikinta, ta duba ta lura babu wanda ya gani sai ta zare ta ta saka a rigar ta. Tasan kudi ne a ciki, maybe kudin dinki, Bata so Inna Ade ta gani dan in ta gani karba zata yi kuma ba zata bata wani abin kirki ba kamar yadda wancan dubu ashirin din da Hassan ya ajiye musu duk Baba aka bawa ya siyo musu kayan abinci.


Bayan sun gama suka tattara kayan suka mayar ,inna tace sai da safe sai su dauki wanda zasuyi amfani dashi su kai gurin dinki "sai dai kuma sai an nemo kudin dinkin" inji Inna.


A daki bayan sun kwanta ita da Sumayya ne tace "Sumayya, kina ganin Hassan zai iya cewa ya fasa aure na?" Sumayya ta juyo tana kallonta tace "me yasa kike tambaya?" Tace "kawai dai. Baba baya son auren nan. Bansan me zai faru ba, ina jin tsoro" Sumayya tace "ki ji tsoron Allah. Kiyi ta addu'a" suka yi shiru kowa yana tunanin sa, har bacci ya fara daukan Sumayya sai Ruqayyah ta kuma cewa "Sumayya? Ya kika ga Hussain dazu? 


Sumayya tace "ya kuwa na ganshi? He is okay" Ruqayyah tace "ba haka nake nufi ba, ina nufin yafi Hassan haduwa ko?" Sumayya ta mike zaune tana kallon ta tace "no......bai fishi haduwa ba, kar ma ki sake wannan tunanin dan Allah" Ruqayyah ta mike itama zaunen tace "ba wani abun nace ba ai, kawai dai kamar ya fishi....." Sumayya tace "gayu? Ko kuma bagu da mota da kaya masu kyau da sababbin kudi" Ruqayyah ta fadi abinda yake ranta "ya fishi kyau" Sumayya ta runtse idonta tana jin zafin abinda yar uwarta take neman yiwa Hassan tace "bai fishi kyau ba. Ya dai fishi fari" Ruqayyah tace "ya fishi fari ko kuma dai kice shi fari ne shi kuma baƙi?" Sumayya tace "fari da baƙi duk halittar Allah ce, amma ni personally ma nafi son bakin mutum akan farin. Sannan ni bayan kalar fata banga wani banbancin halitta a tsakanin su ba dan kamannin su har abin mamaki ne dashi, hanci, baki, ido, shape din fuska, tsaho kirar jikinsu duk iri daya. Kuma Hassan yafi kama da matured kamilallen mutum shi kuma Hussain yafi kama da ladies man, ni in nice da zabi zan zabi Hassan sau goma kafin in zabi Hussain sau daya" ta koma ta kwanta tare da juya wa Ruqayyah baya cikin jin zafin maganar ta. Tana jin Ruqayyah tayi addu'a sannan ta kwanta, sai kuma tace "har dimple ne dashi" 


Sumayya ta kuma juyowa cikin fushi tace "gaya min gaskiya Ruqayyah, zaki juyawa Hassan baya ne ki ce hussainin sa kike so kuma? Kina ganin hakan mai yiyuwa ne?" Ruqayyah tace "Ni haka kika ji nace miki? Dan Hussain ya fishi kyau ai ba wai ya fishi komai ba ne ba, Hassan shine babba, sannan shine mai kudin," Sumayya tace "wrong. Wannan ba shine dalilin da ya kamata ki fada ba na zaben Hassan, ya kamata ki zabi Hassan ne saboda Hassan shi yake sonki ba Hussain ba, Hassan shi ya kamata ki so ba Hussain ba" Ruqayyah tace "shi nake so ɗin ai. Amma dai ai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau".


Sumayya ta runtse idonta tana hana zuciyarta rinjayar ta gurin juyowa ta rufe Ruqayyah da duka. Sai taji cewa ta fahimci menene problem din Ruqayyah, ba wai bakar zuciya ko fada, ko son abin duniya ne da ita ba. A'a rashin godiyar Allah ne da ita. In taga abu zata kwallafa ranta akan tana sonsa amma da zarar ta samu to kuwa ya zama banza abinda ya fishi kuma take hari. And now she have her eyes on Hussain, and Sumayya knows that abinda yasa kawai ba zata rabu da Hassan ta makale wa Hussain ba shine saboda kuɗi, saboda tana son kudin Hassan din. Sai Sumayya taji tana tausayin Hassan. Tana kuma tausayin Ruqayyah saboda karin maganar hausawa da suke cewa "duk wanda bai gode Allah ba to kuwa tabbas zai gode wa azabar Allah".



Washegari da sassafe Baba ya fita yace musu ya tafi gurin interview, suka yi masa fatan alkhairi ya tafi. 


A bangaren su Hassan kuwa suma da sassafe suka fita. Hassan ya kai Hussain airport ya tafi China zai siyo injinan da wancan karon bai samu damar siyowa ba, dama kudin su ne ya hada da kudin da yake account dinsa ya bayar kudin ransom din Hassan, yanzu kuwa tunda alhamdulillah kuɗin sun dawo shine zai koma ya siyo duk da cewa yasan ba zai same su a wadancan price din ba.


Daga airport shi kuma Hassan gurin interview ya zarce, dan yasan cewa yanzu mutane suna nan sun taru suna jiransa shi kuma baya son ya bar mutane suna jiran sa. 


Baba yana zaune akan layi tare da sauran mutane, wani ya fara mita "haka kawai bayan mun riga munzo munyi interview din nan, sai da akayi wata guda kuma sannan sai a dawo a sake cewa muzo mu kuma yin wata? Shikenan yanzu a duniya masu kudi basa tausayin talakawa? Wannan ai zalunci ne, gashi kuma mum zo din sannan an shanya mu a waje kamar wasu kayan wanki".


Baba yace "haba bawan Allah, ba ka san abinda ya samu mutumin nan bane ba? Masu garkuwa da mutane ne fa suka sace shi da kyar ya tsira da ransa" wasu a gurin suka fara jajanta abin wasu kuma suka ce "ina ruwan mu to mu, mu muka sace shi ko kuma mu aka bawa kudin diyyar? Ai irin wannan abin da masu kudi suke yi wa talakawa yana daya daga cikin abinda yake jawo musu irin wancan balain" 


Sai Baba yayi shiru kawai ya barsu, dan wadansu mutanen ko yaya ka kai da bayani ba zasu bude kwakwalwar su ba ballantana su fahimce ka. A lokacin ne Hassan ya shigo gurin da saurinsa, Baba ya lura da yadda yake amsa gaisuwar mutane cike da kulawa sannan ya dan bada hakurin jiransa da akayi sai kuma ya shige ciki. Sai Baba yaji dadi a ransa, yaji yana alfahari da shi yana kuma kara saka ran ya zamo surikin sa dan ya yarda dashi, sai dai ita yar tasa ce bai yarda da ita ba.


Akayi ta kira ana shiga ana fitowa har aka zo kan Baba. Ya shiga da sallamar sa. Hassan ya amsa tare da dago kai, suna hada ido da Baba sai ya mike. "A'a, Baba, sannu da zuwa." Ya fada yana shafa kai, Baba ya zauna sannan shima ya zauna yana gaisheshi sannan yace "Baba ai da an kira ni ni sai inzo gida ba sai anzo nan ba" Baba yace "a'a, ai ba wani abin bane ba, maganar aikin nan ce ta kawo ni an kira mu ance mu sake dawowa za'a sake gwada mu" Hassan ya danyi shiru yana tunani sannan yace "wai wannan aikin dama kaima kazo wancan watan?" 


Baba yayi murmushi yace "nazo mana, ai ba zaka gane ba tunda mutanen da yawa" Hassan yayi shiru yana tunani, shi dai ba zai iya hana Baba aikin nan ba ba kuma zai iya bashi ba. Aiyukan na labourers, messengers da kuma na masu gadi ne, ba zai iya saka Baba aiki ba, ba zai iya aikensa ba ba kuma zai iya kullum yana bude masa kofa in zai shigo ba. A matsayin sa na surukinsa hakan bai dace ba. 


Ya gyara zama yace "Baba, yanzu misali in aka samu wani kasuwanci haka aka baka, zaka iya hakura da aikin nan?" Baba yace "to Hassan, ni dai ban taba yin kasuwanci ba, ni abinda na sani shine aikin karfi shi nake yi nake ciyar da iyali na har yanzu. Dan haka ba lallai ne in na fara kasuwancin ya dore ba tunda ban san kan abun ba, aikin dai shine, nasan abinda kake tunani kuma ina so ka cire komai daga zuciyarka ka gwada ni idan naci ka bani, wannan shine taimako mafi girman da zaka yi min".


Hassan yayi ajjiyar zuciya yace "Baba ba zan so in ke ganin ka kana wahala ba, nafi so inke ganin ka kana hutawarka" Baba yace "amma zaka ji dadi in ka ganni ina neman halak dina ko? Hutu kuma ai da saura na tunda da karfi na ba wai shekaru na ne suka ja ba, in lokacin hutawar yayi zan huta ne".


Haka suka yi ta ja in ja, a karshe dai a dole Hassan ya buga offer ya bawa Baba ya sallame shi saboda wadanda suke kan layi suna jira. Amma a ransa ya kudurce abinda ya kamata yayi akan lamarin.


Baba yana zuwa gida da murnar sa ya fara bawa iyalinsa labari "alhamdulillah, aiki ya samu, aikin gadin nan dai da nake ta buri gashi nan Allah ya kawo shi" ya bude takardar yana nuna musu ita upside down. Inna ta karba tana dubawa duk da ba gane wa take yi ba fuskarta lullube da farin ciki. "Masha Allah baban biyu, Allahu ya sa albarka a ciki, Allah yasa ka fara a Sa'a. Amma na dauka ba yanzu za'a baku ba sai an gama tantancewa" ya zauna yana cewa "haka ya kamata, amma yaron nan Hassan kinsan shine mai abin, a take ya buga min takarda a matsayin mai gadi ya bani".


Ruqayyah data fito daga toilet da buta a hannunta ta saki butar "mai gadi?" Ta fada, fuskarta tana nuna bacin ranta "wanne irin maigadi kuma? Yanzu Hassan din ne da kansa ya baka aikin maigadi a kamfanin sa? Wannan ai cin fuska ne" 


Inna Ade tace "haba Ruqayyah, in ba'a gode masa ba ai kuwa ba za'a zage shi ba. Aikin gadin bashi baban naku yake nema ba? Ba dan shi ba kuma aikin gadin ma zai iya rasawa ya koma ya cigaba da leburanci da dako" cikin bacin rai Ruqayyah tace "amma wannan lokacin ai ya wuce, wannan sabuwar rayuwa ce, a matsayin sa na wanda zai zama surikinsa ba kamata yayi ya bashi babban office a kamfaninsa ba?" Baba ya fara fada "bana son diban albarka Hassana, da wanne takardun zai bani aikin office din? Me zanyi a office din? Shi cewa yayi ma in hakura da aikin ya bani jari inyi sana'a nace a'a, saboda ni bana son dogara da wani. In ba zaki yi murna da abinda Allah ya bamu ba ki wuce ki bani guri".


Bata kuma cewa komai ba ta wuce daki tana kunan zuci. Tabbas sai ta takawa Hassan burki, in dai yana sonta sai ya chanja wannan aikin, wannan ai ita zai zubarwa da kima a idon yan'uwansa da sauran jama'ar sa, shikenan kuma sai ace babanta shine mai gadin kamfanin mijinta? Ina! Ai sam ba zata sabu ba.


Da daddare dan halak din yazo zance. 


Yaune zuwansa zance officially na farko. Yayi mata kwalliya sosai ya kuma gama shiryo kalaman da zai yi mata. Yayi packing sannan ya aika kiranta. Ita ma kuma a nata bangaren ta saka ran zai zo kuma ta shirya nata kalaman. Dan haka ana cewa ana sallama da ita ta saka hijab ta fesa daya daga cikin turaren da suke cikin kayan Hussain. A bakin kofar gidan ta tsaya ta gyara expression din fuskarta zuwa irin wanda tasan yana so, na yarinya mai kunya da nutsuwa 


A jikin mota ta ganshi a tsaye ya rungume hannunsa. Farin yadi ne a jikinsa mai taushi wanda ya karbi kafar jikinsa sosai ya kuma fito da kyawun gyararriyar sumar kansa wadda ta sha gyara kuma take a bude. Bakin takalmi, bakin agogo da bakin tabarau, sai kuma kyakkyawan murmushi a fuskarsa. Zuciyarsa kuma cike da soyayyar hassanar sa.


Tayi masa murmushi itama. Sannan ta tako sannu a hankali tazo inda yake ta dan durkusa kadan ta gaishe shi. Ya amsa yana kara fadada murmushin sa. "Barka da fitowa uwar yayan Hassan" ta rufe fuska da hannunta. Yayi dariya yana karewa siraran dogayen yatsun hannunta kallo ya gyara tsayuwarsa yace "kinyi kyau sosai. Sai dai matsalar daya ce" ta bude fuskarta amma idanuwanta a kasa tace "wacce matsala kenan fa?" yace "wannan kunyar nake rokon alfarmar a rage ta ko yaya ne a bani dama inga cikin idanuwanki. Kullum su nake gani cikin baccina amma kuma a zahiri an hana mini ganin su" ta fara kokarin sake rufe fuskar ya hade hannayensa a guri daya yace "dan Allah, a tausayawa marayan Allah".


Tace "maraya?" Ya cire glass din idonsa Yace "eh. Baki sani bako?" Tace "Allah yaji kansa" yace "Allah yaji kansu zaki ce. Duk su biyun babu" tace "ohhh, ya Salam, na dauka ai....." Yace "Aunty? Ba ita ta haife mu ba, amma uwa ce a gare mu, haihuwar mu ne kawai baya yi ba".


Ko cikin abokan sa ba kowa ne yasan cewa ba Aunty ce ta haife su ba amma wannan ai Hassana ce, wannan aurenta zaiyi kuma aure akan gaskiya ake gina shi. 


Tayi masa gaisuwa sai ya bata brief labarin asalinsu da kuma cikakkiyar dangantakar su da Aunty, ya kuma lissafa mata sunayen kannensa mata sannan ya gaya mata irin soyayyar da yake wa yan'uwansa. 


Itama kuma sai ga bashi labarin nata asalin da sunayen nata family members din da stage din karatun kowanne. A lokacin ne ta ga time din shigar da maganar Baba yayi. Tace "ammm akan maganar Baba" sai ta dago kai kamar yadda tayi plan cewa zata saka idonta cikin nasa ta gaya masa ya chanja wa baban ta aiki. Amma the moment da suka hada ido sai komai nata ya ruguje, wannan mutumin ba wannan mutumin bane daya same ta a toilet yace mata "help me Please" wannan wani mutumin ne daban. Wannan is so strong and so sure of himself. Wannan mutumin will not be controlled, not by her, not by anyone.


Ta sauke idonta kasa tana jin komai yana rushe mata, plan dinta duk ya ruguje, yace "uhum, ina jinki, me zaki ce min a game da Baba?"cikin sanyin murya tace "cewa zanyi dama an gode madallah da aikin da ka bashi" yace "noo. Babu godiya ai a tsakanin mu. Baba ai babanane, tunda nawa baban ya mutu kinga ai yanzu na samu Baba ko?" 


Ta kuma cewa "an kawo mana sako kuma, mungode" ya dan bata fuska yace "sako kuma? Tace "eh" a ranta tana tunanin bashi din bane ba kenan, sai ta kara da cewa "Hussain yazo jiya, da dare kuma sai ya aiko mana da wayoyi ni da Sumayya da kuma kaya" 


Hassan yayi dariya yana bayyana farin cikin sa yace "ya kyauta sosai. Ko gaya min bai yi ba. Hussain yana da kirki sosai yana kuma da kyauta sosai. Kinga ya rigani, ina ta lissafin siyan wayar amma bana so inyi laifi a gurin Baba tunda ban sani ba ko ba ya son kuyi waya yanzu"


Ta harare shi ta gefe yadda ba zai gani ba sannan tace "ai kuwa yayi fadan, sai da kyar ya bari" yace "to Alhamdulillah tunda ya bari ɗin, yanzu an kunna ta kenan a bani number in samu ta rage dare? Kinsan abinka da gwauro" tace "bamu bude bama, sai mun siyo sim card" yace "gobe zan aiko, da sassafe ma kuwa" 


Sun dan jima suna hira, ita kanta Ruqayyah tasan taji dadin hirar Hassan yadda yake komai a nitse, sai kuma yace "naga alamar akwai sauro, gwara in barki ki koma gida kar ya cizar min ke ko?" Da haka suka yi sallama ya raka ta bakin kofa ta shiga sannan ya juyo.


A lokacin ne wata taxi ta shigo layin, mai taxin ya dan wuce motar Hassan kadan sannan yayi packing. Ya fito a dai dai lokacin da Hassan yake kokarin bude kofar motar sa. Ya mika masa hannu, sai da Hassan ya kare masa kallo ya ganshi dan karamin saurayi da ba zai wuce ashirin zuwa ashirin da biyar ba, ya mika masa nasa hannun suka gaisasai ya nuna gidan su Ruqayyah yace "dan Allah nan ne gidan su wasu twins masu kama daya?" Hassan ya gyara tsayuwarsa yana studying saurayin yace "eh nan ne ya akayi?" Saurayin yace "Okay dama gidan nake nema shikenan na gode" Hassan ya kuma cewa "me yasa kake neman gidan su?" Saurayin yace "ohhh, dama muna haduwa ne dasu yawanci a school dinsu, to kwana biyu ban gansu ba shine nazo in duba su kuma mu gaisa" Hassan yace "really? Da wa zaka gaisa a cikin su?" S aurayin yace "Ruqayyah nasan ba zata kula ni bama, so.....da Sumayya zamu gaisa" Hassan yayi murmushi ya nuna masa kofar gidan yace "bismillah" sannan ya shiga motarsa ya bar unguwar zuciyarsa fara kal. Hassanar sa mai kamun kai ce ita, Hassanar sa mutuniyar kirki ce.

Post a Comment

0 Comments