TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 7-8

 7️⃣----8️⃣


Sujjada naga tayiwa wannan halittar tana cewa "yakai Sarkin Tsageru! yakai gagara badau!! , yakai buhun ƙara kafi ƙarfin danna!!!, ya kai Shugaban matsafan duniya!!!! , haƙiƙa ka cika alƙawarinka gareni akan bullowarka bayan shekara 43 da suka wuce, kuma ina nan ina bin dokokinka da ka sharɗantamin". (toh shikuma wannan nashi salon tsafin kenan sai bayan shekaru aru aru yake bayyana, babbar magana 🤔🤔🤔).

 Wata dariya naji har ƙasa na girgiza  ashe wannan halittar ne ke busar dariya, can ya tsagaita kamar ruwa ya ɗauke ya fara magana jikake kamar ƙasa zata tsage 

"Haƙiƙa kinbi sharudɗanmu na ƙin sallatar Asr da Subh tare da ƙin azumin watan Ramadan haɗe da sadakar baƙaƙen karnuka 50 duk shekara, lallai ke tamu ce! Ke tamu ce!!!

Sai kuma ya fara kuka kamar ana ruwan sama can kuma ya tsaya,(fans nifa hallittar nan ta kusa sani fitsari tsabaragen tsoro, da ƙyar na iya tsayawa dan ɗauko muku rahoto 😖😖😭). 

Sai can ya cigaba da cewa"Irinta  basu gushe a doran ƙasa ba suna nan har yanzu, wasu na a cikin ƙasƙanci wasu na a cikin farin ciki ,tabbas sai sun dawo bada jimawa ba, wannan haka yake, he! he!! he!!!

A razane ta ɗago  kanta zuciyarta na dukan tara tara cikin rawar murna da inda inda ta fara magana " Su..... Suss.... Sussa nan a ra.... raye da... daman basu mutu ba?

 Daka mata tsawa yayi yana magana cike da amon muryar"Karya zamuyi miki,dole ne su dawo, munyi iyayinmu sun gagaremu, suna sallah biyar kullum arana, suna nafila, suna azkhar na safe da na rana, suna azumi, suna Tasbihi da Hailala"

Cak ya tsaya ya kuma sake fashewa da kuka wanda yafi na farko ko ita kanta  ta razane matuƙa ainun, sai kuma ya dakata da kukan sai ya ɗora daga inda ya tsaya a magana " kullun sai sun karanta baqara mu kuma bamaso,ruhunsu baya zama wuri ɗaya,lokacin dawowarsu yayi dole su dawo!!!

Ita dai  har fitsari ya soma zubo mata, can kuma ya ce"Mun muki alƙawarin halittar jikinki zata tsaya ahaka in har kika cigaba da bin sharudɗanmu, zan koma, zan koma sai bayan shekara 5!!!

Lokaci kuda hasken ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, haka dai ta tashi jiki duk a sanyaye ta boye kayan tsubbunta a wani akwati mai shegen kyau sannan ta kuma sashi cikin wani akwati babba tasa a ƙarƙashin tamfatsetsan kadonta na alfarma wanda ko queen Elizabeth sai haka(🙃🙃🙃).

Duk wannan gyaran da ta ke yi bayan ta kunna bulb din ɗaki ne, dayake can cikin salisalin dare ne wanda alokacin bayin ALLAH suke ganawa da mahaliccinsu amma ita da shaydani ta ke ganawa dashi (ALLAH kasa mufi k'arfin zuciyoyinmu). 


          @@@@@@@@@@@@


Haka  ta kwanta cike da tashin hankali duk da tawani bangare ya mata alƙawarin barin mata halittar jikinta batare da tsufaba, sai kuma kareta da familinta gaba daya, shi ne kadai yake sassuata mata zuciya.

Ta jima bacci ɓarawo bai saceta ba, sai gabanin sallar asuba bacci ya ɗauke ta.

 Washe gari sai wurin ƙarfe 11:17am na safe ta tashi, ita daman ba sallar Subh ta ke yi ba. Ƙwankwasa kofar ɗakinta naji anayi, ko kala batace ba, sai kusan minti 8 kafin tace "A shigo" , wata mata ta shigo ƴar kimanin shekara 50,babu sallama saboda tasan halin Uwar ɗakinta, ta tsufa sosai hasalima tafi uwar ɗakinta tsufa, za kayi tunanin ko ita ƴar aikin ce yayar.

Shigowa tayi har wurin makeken gadon uwar ɗakinta kana durƙusa haɗe da gaisheta "Barkha da safiya Hajiya"

wacca aka kira da Hajiya dake kwance ta tashi zaune da faɗin "Barkha"

Mai aikin tace "An shirya abincin  a dining room Hajiya ",  

 "To" kawai tace sannan ta wuce bayi don yin wanka.

Ita ko mai aikin karatun zuci ta fara'Toh wai lafiya naga yau batama son yin magana, meke faruwa ne',  tunda babu mai bata ansa ta tashi ta fita daga ɗakin.

 Hajiya ta fito daga wanka ta shirya cikin haɗadɗan  boyel lace milk color wanda ya ɗinku wurin masana ɗinki kuma ya zauna mata a Jiki ɗas,takalmi ta saka wanda ya dace da kayan, sannan ta sauko zuwa ƙasa don yau batajin hawa lifter kasancewar akwai lifter a gidan.

Saukowa tayi zuwa dining room don karin safe, baya ta kammala ne ta fito falo, kallon falon nayi wanda ya tsaru iya tsaruwa, saikace falon shugaban ƙasa saboda yanda naga annarka dukiya a ɗakin kai in taƙaice muku gidan ma gaba daya ya haɗu don idan kashigo gidan zakayi tunanin a Dubai kake, zama tayi sannan ta kanna TV. 


        @@@@@@@@@@@@@


Ƙararrawar ƙofar aka danna, alamun ana son shigowa, bata tashi ba sai dai naji tana kiran"Saude zo ki buɗe"

 Mai aikinta naga tafito daga kitchen da sauri ta nufa ƙofar, budewa tayi sannan da ɗan ja baya, wata budurwa nagani mai kimanin shekara 17 tashigo da gudu da faɗa jikin Hajiya tare da fad'in"Granny I really miss you alot, da ƙyar dad ya barni nazo Nigeria saboda rashin tsaro"

Magana ta ke ma Hajiya amma cike da shagwaba, murmushi Hajiya tayi don yau bata cikin good mood ɗin magana, shafa bayanta tayi tana faɗin"yanxu ai gaki a Nigeria koh"

 murmushi budurwar tayi sannan tace "Granny bara naje nayi wanka I'm very tired" da "ok" Hajiya ta bita dashi. 

Gaskiya a rayuwarta tana tsanani son ahalinta don zata iya komai don farin cikinsu, yaranta uku ne duk mata, biyu suna aure a cikin garin Abuja ita kuma ɗayar  wacca ta ke ƙaramarsu tana aure a UK da yarinyarta ɗaya Fadila wacca tazo Nigeria hutun 1 week.

Amina itace babbar 6arta wacca ta ke da yara biyu duk mata amma sunyi aure da kuma yaransu,sai Jamila mai yaro daya shima yayi aure da yaro ɗaya. 

Duk babbar sallah duka familin suke haɗuwa don yin shagulgulan sallah.Fadila bayan tafito ta wuce taci abinci sannan ta dawo wurin grannyn ta don yin hira, a nan ne ta ke sanar ma Hajiya zuwa next year zata shiga  Oxford University don karantar bagaren jarida. 

Haka suka cigaba da hirarsu sannan   kowa ya nufi ɗakinsa ita Fadila taje sallah duk da ba iya sallar tayi ba ita kuma Hajiya ta wuce ɗakinta don yin bacci,Wannan kenan. 


      @@@@@@@@@@@@@@@


KADUNA


Zaliha ce tafito da kayan wanki tanayi, sai taji an kwaɗa sallama, ɗagowan da zatayi tayi arba da Maman jummalo da ita Jummalon, haba sai ta saki wankin ta ruga da gudu ta rungume Jummalo, itama  Jummalo rungume tayi tana murna, ƴar uwar sharholiya ta dawo, ji kawai sukeji ance "Ai saiki saketa ta huta mana, kin wani rirriƙeta sai kace za'a ƙwace maki ita"

 Umma Kande ce tafito daga ɗaki jin Zaliha na ihu, Maman Jummalo ce ta nufi ɗakinta wanda yake kusa da na Umman Sa'eeda,ta buɗe ta shiga,Jummalo ma shiga tayi sai Zaliha tabisu da kayan da suka zo dashi tana murna.

 Maman Jummalo ƙawar Umma Kande ce kuma ta hannun damarta, duk wani makirci tare suke ƙullashi,mijin Maman Jummalo ya rasu kuma abokin Abbansu Sa'eeda ne, shiyasa bayan mutuwarsa yaga ya dace ta zauna gidansa tunda daman a gidan haya suke kuma ƴan uwansu suna ƙauye da zama, wannan shi ne dalilin fara zaman Maman Jummalo a gidan. 

Sai kuma akayi rashin sa'a halinsu yazo ɗaya da Umma Kande nan da nan suka ɗinke suna gallazama ma Umman Sa'eeda, batajin daɗinsu kwata kwata, sun haɗe mata kai. Tafiyar Maman Jummalo da Jummalo ƙauyen su ne Umman Sa'eeda ta ɗanji sassauci kaɗan. 


         @@@@@@@@@@@@@@


Kasancewar Umman Sa'eeda bata gida taje barka a maƙotansu wa'inda suke ɗan abun arziƙi yasa bata san da dawowarsu ba, itama Sa'eeda taje makaranta.

 Umma Kande ce ta shigo da kula mai kyau da abinci sai kuma jug ɗin ruwa mai sanyi tana ƙara musu sannu da zuwa, Maman Jummalo ta amsa da fara'arta tana faɗin "Har da ɗawainya ƙawas" 

 Umma Kande tayi murmushi ta ce "Haba ƙawas ai babu komai, bari kedai gama cin abinci mufara chapter"

dariya Maman Jummalo ta kwashe dashi tana cewa " Haba dai ƙawas bara naci sai mufara sana'ar".

Haka dai Maman Jummalo da Jummalo suka kammala cin abinci, ita Jummalo ta wuce ɗakin Umma  Kande don yin hira da  ƴan uwanta Zaliha da Iklima Kasancewar manyan mata  Nusaiba bata nan ta tafi nata harkokin(Ni kuma nace ta tafi tata sana'ar karuwanci ba koya kukaci my esteem fans🙃😂).

 Maman Jummalo ce ta fara magana "ƙawas naga sauyi sosai a gidan nan, ko Babansu Nusaiba ne ALLAH ya buɗa masa ko ko Musa ne halan " 

murmushi Umma Kande tayi sannan tace"Ai ƙawas duk basu bane hasalima Musa na Calabar kasuwanci ,Nusaiba ce ALLAH ya haɗata da wani attajirin mai kuɗi Alhaji Sagir, yana matuƙar sonta,kuma yana sakar mata kuɗi sosai, to shi ne ya gyara mana wannan gidan ai" 

Ɗan jimmm Maman Jummalo tayi a zuciyarta tana faɗin 'zama bai ganni ba, dole Jummalo tasamo saurayi mai kuɗi wanda muma zamu fancama' 

Umma Kande ce ta katse mata tunani da faɗin"Ni na kawo wata shawara yanzu, mai zai hana mu komawa wurin boka Sankeru ya samoma Jummalo, Zaliha da iklima samari masu kuɗi kamar yanda Nusaiba tasamu mai kuɗi kinga shikenan munyi sallama da talauci ko ya kikace ƙawas"

Shiru Maman Jummalo tayi tana nazari acikin ranta tana faɗin 'Kamar kin shiga raina aminiyar ƙwarai, nima nayi wannan tunanin saboda gaskiya bazan koma ƙauye ba'

Can ta fara magana "Gaskiya yau nasan kin cika aminiyar arziƙi mara baƙin ciki don da wata ce shikenan ta daina abota dani"

Murmushi mai sauti Umma Kande tayi tare da cewa "Ai a duniya banga abinda zaiza nabar abota dake ba, kin manta, kefa ce kika fara haskamin hanya har nazo wannan gaɓar kuma sai nabarki, a'a ba haka nake ba"

Ɗan dariya Maman jummalo tayi da cewa " Shiyasa nake yinki Over kawas".

Tare suka saki dariya haɗe da shewa harda tafawa, can Maman Jummalo tace" Wai ina waccan mayyar da ɗiyarta su  ke ne, naga banji motsinsu ba"

 dariya tasaki da faɗin"Ohon musu naga ɗazu ta fita ita kuma ɗiyarta ta tafi gantali wai acewarta makaranta, ni kinga yanxu wallahi basu a gaba na, don na gaba yayi gaba"

Dariya Maman Jummalo tayi sannan tace"Da kyau ƙawas kina wuta Ina binki ta petrol " tare suka sake kwashewa da dariya. 

Umma Kande ce tace" Ranar lahadi saiki shirya muje wurin boko Sankeru ɗin", Maman Jummalo tace "To ALLAH ya kaimu". 


          @@@@@@@@@@@@


Haka suka cigaba da hirarsu, a nan ne sukaji sallamar Umman Sa'eeda amma babu wanda ya amsa, ita dama ta saba ko akwai mutane a tsakar gida babu mai amsa mata sallama ita da ƴarta ( Hmmmm wannan rayuwa🤔). 

Ɗakinta ta wuce babu jimawa sai ga Sa'eeda ta shigo itama da sallamarta haka akai banza da ita, ta shiga ɗaki da sallama sai ta gaida Ummanta tare a rataya jakarta, ta ɗauki buta sannan ta nufi bayi da sauri saboda fitsari ya matseta tun a hanya.

 Bayan ta fito daga bayi tayi kiciɓis da Maman Jummalo ta fito daga ɗakinta, sanin Maman Jummalo ta tsanesu yasata razana tare da ɗan russunawa da gaisheta.

Wani mugun kallo Maman Jummalo ta ke ma Sa'eeda a zuciyarta tana faɗin 'Haka wannan yarinyar ta dawo, ga kyau kamar mayya, ga diri saikace wata babbar mace,ko ƴan matan gidan duk tafisu kyau, gata da gashi kamar mamanta, ai dole na tsaneki tunda kinfi ƴan matan gidan nan kyau,gashi kyaunta yanxu yake ƙara bayyana'

 Duk wannan zancan a zuci Maman Jummalo takeyinsa, ko amsata batayi ba ta wuce abinta, daman Sa'eeda tasan hakan zata kasance,tafiyarta tayi abinta tayo alwala ta wuce ciki. 

A ɗaki kuwa Sa'eeda ke hira da Ummanta, tana cewa "Ummina mun kusa hutun babban sallar, mai zai hana muje ƙauyen  Damari sallah, don mun rabu da zuwa tunfa banida wayo"

 Shiru Umman Sa'eeda tayi tana sauraranta, can tace " Hakane kuwa, sai muje tunda kinason zuwa,babbar sallarma ai saura kwanaki yanzu"

 Duk da  Umman Sa'eeda ba son zuwa ta ke ba, saboda ba daɗin garin ta ke ji ba, haka suka cigaba da hirarsu. 


         @@@@@@@@@@@@@


Yau ta ke lahadi, su Umma Kande tun daren jiya suka kintsa  tsaf saboda inda boko Sankeru yake akwai nisa don a machine ake zuwa wurin dajin sai a ƙarasa da ƙafa still shima ɗin akwai tafiya sosai, haka su ka ƙula sammako sai tasha,sai suka hau motar ƙauyen da dajin inda boko Sankeru yake,bayan sun sauka sai suka hau machine guda saboda k'arancin ƴan machine a ƙauyen , haka sukai ta tafiya har aka sauke su a wani gefen daji,Umma Kande ta biya mai machine sannan suka dosa dajin da tafiya a ƙafa. 

Sunsha lafiya sosai kana suna isa wurin wata ƴan bukka wacca ta ke zagaye da manya manyan bishiyoyin kuka sunkai bakwai kana suka tsaya, dukkansu cire takalma sukayi sai suka fara tafiya da baya da baya har suka shiga bukkar(Fans kunsanni da ganin ƙwaƙwaf haka nabisu ciki don ɗauko muku rahoto🙃😇😇). Shigarsu keda wuya naga sun zube ƙasa suna mai kirayi kamar haka "Sankeru namu Sankeru na duk mai son ya dace,Shugaban matsubban duniya, Ka cire tuta,Kowa na bayanka, gamu yau munzo da ƙoƙon bararmu agareka mai share kukanmu", (Wa'iyazubillah, ALLAH kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu, wannan kafirci haka duk don son abin duniya🤔).

Bukkar naga tafara girgiza kamar samanta zai buɗe, ga bishiyoyin kukan nan sai jijjiga suke,ga wani irin wari mai saka mutum kamar yayi amai ya fara tasowa (my esteem fans dole na saka nose mask ɗina saboda warin da yake tasowa don idan bansaba sumewa zanyi shikenan ba ɗauko muku rahoto 😷😷😷), wani jibgegyan mutum ya bullo cikin bukkar kamar walƙiya, mummuna dashi, ga ƙaton timbi kamar randa, gashi a tsirara ya bayyana garesu, Umma Kande da Maman Jummalo sai duƙar da kai suke, duk da ba zuwansu na farko bane. 

Bayyanarshi keda wuya ya fara tintsirar dariya, timbinsa na wata girgiza kamar ana bubbugata ƙwarya ,can bayan yaɗau wasu ƴan mintuna yana sheƙa dariyarsa can kuma ya tsaya a sannan ne ya fara magana cikin sautin da yake sa bukkar girgiza haɗe da bishiyoyin yana faɗin"Basai kun ɓata makunanku wurin sanarmin ba nasan meke tafe daku, kuma wannan kamar yankar wuƙa ne, amma kunason ƴaƴan naku susamu kowani irin masu kuɗine"

 Cikin ladabi suka amsa da"Eh mai sha re kukanmu"(Ni kuma nace zai saku ku cikin wahala da bala'i ba😂😂😂).

 Dariya ya kuma sakeyi wannan karon harda miƙewa yana taka rawa da juyi duk ilahirin jikinsa yana raws saikace wani alade in yana gudu,su Umma Kande kansu dai har yanxu a duƙe yake, can kuma  ya dakata da rawar, sannan ya nufa wata  ƴar ƙwarya ya ɗauko kullin magani ya cilla musu da cewa "Ku basu acikin abinci suci dukkansu alokaci guda"

Godiya sukai ta faman yimishi tare da kirari, daga baya Umma Kande taciro kuɗi zata miƙa mishi sai ya dakatar da ita da cewa"Yau jikinku shi ne fansarku don haka kowacce saina kwanta da ita"

 Basu kaɗai ba har ni mai ɗaukar rahoto saida na zaro ido, sake cewa yayi " In kuma kukayi jayayya to tun anan zaku fusanci hukunci don dole sai kun haukace"

 Da sauri suka amsa da"Mun aminci "

Dariya ya kece dashi ya faɗin" Shegu mayun kuɗi", can ya sake miƙewa yana taka rawa kamar alade(Fans anya wannan bokan bai fara hauka ba, wannan irin rawa haka😂😂😂). 


         @@@@@@@@@@@@@@


Da Maman Jummalo aka fara masha'ar, saida ya shafe tsawan awa 2 cur kana tafito dayake Umma Kande tafito waje saboda umarnin boka Sankeru, sai Umma Kande ta shiga  yayi bidirinsa da ita har tsawan awa biyu da rabi sannan itama ta fito.

 zai goge zufa sukeyi, haka suka lallaba har zuwa bakin dajin duk jikinsu sai wari yake kamar mushe, can Umma Kande tace"Wai ba naga kamar kin ɗauko turare ba sanda zamuzo har kika sake fesawa a mota"

Maman Jummalo tashe"Wannan haka yake bara na ɗauko mufesa don kar a ƙi ɗaukar mu''

Da ƙyar suka samu mai machine suka hau su biyu, basu suka dawo gida ba sai wurin yamma lilis.

 A daren kamar yanda boka Sankeru ya Umurcesu, suka sa musu maganin cikin abinci suci a tare, kamar yanda yace. 


***Gareku ƴan uwana mata, haƙiƙa wani lokacin idonmu yakan rufe saboda abun duniya kamar yanda su Umma Kande da Maman Jummalo nasu ya rufe ruf, saboda son abin duniya mai ƙarewa suka lalata rayuwarsu da na ƴaƴansu baki  ɗaya, haƙiƙa sun tafka babban kuskure domin ko sallarsu bazata amsu ba har na tsawan kwana arba'in kuma sun kafirta kamar yanda yazo acikin hadisin manzon ALLAH (S. A. W) yana cewa "Duk wanda yaje wurin boka ko mai duba haƙiƙa ya kafirta kuma sallarsa baza ta amsu ba har na tsawan kwana arba'in",.ALLAH kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu gaba ɗaya.***


         @@@@@@@@@@@@@

Tun daga ranar su Umma Kande sukaga sauyi wurin ƴaƴansu don yanzu kowacce cikinsu nada saurayi mai kuɗin gaske gashi suna sakar musu da kuɗi sosai. Tabbas kamar yanda Umma Kande tace sunyi hannun riga da talauci lallai kuwa sunyi don suna fantamawa da kuɗi sosai. 

Bangaren su Sa'eeda sun fara shirin 1st term exams na SS2 har time table ya fito, ita da uwarta basa shiga sabgar ƴan gidan haka Abban Sa'eeda yanxu ko ɗakin Umman Sa'eeda ya daina shiga kwata kwata. Sa'eeda karatu ta ke baji babu gani, yanda ta ke karatu zakayi tunanin a University ta ke, haka sukayi exams ɗinsu cikin hukuncin Ubangiji. 

A lokacin saura kwana biyu sallah, haka suka fara shirye shiryen tafiya ƙauyen Damari, ana gobe sallah kuwa suka kama hanya. 


           @@@@@@@@@@@@@


ƘAUYEN DAMARI


Dayake da safe sukayi tafiyar, sai wurin 11:00am na safe suka iso tashar garin, haka suka ɗau mai machine da  ƴan kayansu kala bibbiyyu saboda ba daɗewa zasuyi ba. Wani gida mai ginin ƙasa naga mai machine ɗin ya faka, suka sauka Umma Sa'eeda ta biya mai machine ɗin kana suka shiga cikin gidan da sallamarsu.

Wata tsohuwa nagani mai kumanin shekara 69 zana zaune kan tabarma tare da ita kuma ɗan ƙaramin radio ne tanajin labarai, ganinsu yasa wannan tsohuwa miƙewa zunbur kamar an tsikareka tana faɗin "Miya kawoki gidan nan, ba nace miki karki kuskura na sake ganin baƙar ƙafarki agidan nan ba"

 Russunawa Umman Sa'eeda tayi cike da girmamawa ba tare tabi takan zantuttukan tsohuwar ba ta gaishe ta, ƙin amsawa tayi tare da cewa"Riƙe gaisuwarki, in kinje birni tamiki amfani marar asali kawai"

 Hawaye suka fara kwaranya a idanun Umman Sa'eeda, a zuciyarta tana faɗin 'ALLAH ka kawomin mafita nida ƴata, kabamu ikon cin wannan jabawar'. 

Jin sallamar wani dattijo mai kimanin shekara 76 amma inka ganshi zakace baikai haka saboda jikin mutan da dana yanzu ba ɗaya bane,shigowarsa ya katse mata tunani da faɗin"Lale marhabin da mutan birni, Hussaina ce nake gani ba'a mafarki ba"

Umman Sa'eeda ne juyo tare da russunawa wurin gaisheshi da cewa"Baba mun sameku lafiya"

 Cike da murna Baba ya amsa da "lafiya lau Hussaina, ya kuke, ya bayan rabuwa"

 Umman Sa'eeda tace"Alhamdulillah Baba duk sunce a gaisheku"

 suna cikin gaisawa wannan tsohuwar da katse musu hirar da faɗin "Tsintacciyar mage bata taɓa zamowa mage" 

Daka mata tsawa tsohon nan yayi tare da cewa "Ladi ya isheka haka, wannan gidana ne, kuma ni nakeda iko akansa bake ba, kar na sakejin maganarki anan, ko kuma ranki in yayi dubu wallahi sai ya ɓaci", (Fans dama tsoho kamarsa yana fad'a haka, tabbb, ni nayi nan karya had'a dani wallahi🙃🙃🙃). 

Shiru kuwa wacca aka kira da Ladi tayi , can kuma ta wuce ɗaki, juyowa yayi gun Umman Sa'eeda tare da cewa"Kiyi haƙuri nasanki da haƙuri kamar mahaifiyarki, ga ɗaki can kukai kayanku ciki,zansa Mairi da girko muku abinci yanxu"

 da "Toh" Umman Sa'eeda ta bishi dashi, Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tunda suka shigo gidan da farajin masifar Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata toh wacece kakata................ 




Post a Comment

0 Comments