TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 31-32

 3⃣1⃣-----3⃣2⃣








Isarta  ƙofar gida,ta ciro #500 ta bama mai keke napep ba tare da ta amshi canji ba ta shiga gidan ko sallama babu,sa'arta ɗaya Ummanta bata daɗe da dawowa ba daga aikinta na shara,banko ƙofar ɗakin tayi babu sallama tare da cewa




"Ummina,Ummina na shiga Uku,sun yaudare ne Ummina"




Kawai ta ƙara ƙarfin kukan nata,Umman Sa'eeda dake zaune akan ƴan tabarmarta tana hutuwa ta miƙe a rikice tare da duban ƴarta ta da kuma maganar da take cewa,cikin ruɗewa Ummanta ta ce




"Suwa suka yaudarki Sa'eeda ?"




"Ummina Sauban da Maryam aure zasuyi saura sati biyu bikinsu Ummina,na shiga Uku!!!"




"Baki shiga uku ba Sa'eeda kwantar da hankalinki"


Jiri ne ya fara ɗiban Sa'eeda ji take duniyar na juya mata,haba kan kace me Sa'eeda tayi ƙasa tana dafe da kai da sauri Ummanta ta riƙota a rikice tare da cewa



"Innalillahi Wa'inna I'aihi Raji'un!!!Sa'eeda!!! Sa'eeda!!! "



Jijjigata takeyi amma ko motsi,da sauri ta ɗebo ruwa a babba roba jikinta na rawa ta watsa mata a jiki,haba nan da nan Sa'eeda ta sauke nauyayyen a ajiyar zuciya lokaci guda kuma tana dafe da ƙirjinta wurin saitin zuciyarta,cikin sanyin murya mai rauni ta fara magana



"Ummina zuciyata zata fashe,ƙirjina zai tsage Ummina,wayyo Allah Ummina zuciyata zuciyata Ummina zan mutu zan mutu!"



Haka Sa'eeda tayita nanatawa hannunta na a saman ƙirjinta daidai zuciyarta,ƙara ruɗewa Umman Sa'eeda tayi,da sauri da ɗauko hijab ɗinta tare da jakarta sai ta riƙota suka fito waje,zaunar da ita tayi sannan ta kulle ɗakinsu, taimaka mata tayi ta miƙe daƙyar sukayi hanyar fita waje,suna gab da fita saiga su Umma Kande da Maman jummulo sun shigo gidan,tsaya sukayi ganin Umman Sa'eeda ta riƙo Sa'eeda suna tafiya a hankali zasu fita,da sauri Maman Jummalo tace



"Babu lafiya ne Sa'eeda"



Fuskar Umman Sa'eeda a ɗaure ta amsa mata da bata da lafiya ne,don tasan halinsu da shegantaka,tayi tambayar ne don su samu abun aibantasu,Umma Kande ce ta taɓe baki tare da huro guntayen hancinta  da cewa



"Sai wani ƙunbuya-ƙunbuya kuke,an faɗa muku bamu san mai kuke ciki bane,dan nasan kullum fitar da take da sunan makaranta  sai anjawo abin kunya,ai gashi nan za'aje a zubar da cikin shege"



Ba Umman Sa'eeda ba hatta ita kanta Sa'eedar saida ta waiwaya jin wannan sabon sharri kawai daga mutum baida lafiya shikenan sai sharri,Umman Sa'eeda ta mayar mata da martani cike da ɓacin rai



"In shaa Allahu bakinki saidai ya sari ɗanyen kashi,sannan sharri da kike nufin mu dashi Allah bazai barki ba,Allah yana tare da masu gaskiya a kowani yanayi,abinda kikewa Sa'eeda fata saidai ki ganshi a ɗakinki bi'izinillahi"



Rai a ɓace take maganar dan yau Umma Kande takaita bagon,haƙurinta ya fara ƙarewa,ita kuwa Umma Kande ƙara taɓe baki tayi irin ko a jikintan nan,ƙara jefo mata wata mummunar maganar tayi da cewa




"A hayye chassssssss!!! Umman Sa'eeda kenan ai na gaba yayi gaba na baya kuma hhhhhhhh!!! Sai tsintar hula,nida na aurar ina zanga abin kunya ai seke mai karuwa a ɗaki wacca kullum saita fita da sunan karatu,zamu gani dai koya kikace ƙawas"



"Kkkkwaraiiiiii da gaske aminiyar arziƙi,wannan haka yake,zamu gani,ayi mugani in tusa zata hura wuta"



Bata ƙara bi takan zantuttukansu ba ta wuce waje da Sa'eeda, sauƙinsu ma ana samun keke napep sosai a unguwar kasancewar akwai titi yasa basu wani ɓata lokaci ba suka samu keke napep ya kaisu asibiti.



Isarsu asibitin keda wuta jikin Sa'eeda ya rikice da sauri nurses suka amsheta direct suka nufi emergency room da ita don taimakon gaggawa,Alhamdulillah likitoci da nurses ɗin sunyi nasarar maido da ita hayyacinta tare da mata allurar bacci don ta huta,sai aka basu gado wata nurse tasa mata drip don tasamu ƙarfin jiki sosai.



Kwananta biyu a asibiti, a rana ta uku saiga Iman tazo kasancewar tazo school bata ga Sa'eeda kuma tasan bata fashin makaranta saida dalili,kiran wayanta tayi sai Umman Sa'eeda ta ɗauka kasancewar ita Sa'eedar bacci take a lokacin,sanar mata tayi Sa'eeda bata da lafiya yau kwanansu uku kenan a asibiti amma Alhamdulillah ta samu sauƙi.A ruɗe Iman ta tambayi asibitin da aka kwanantar dasu da kuma numban ɗaki,sanar mata tayi da sunan asibitin da numban ɗakin da suke,babu ɓata lokaci Iman ta hau sabumar motarta da Daddyn ta ya siya mata kwanan nan ta nufi asibitin a ruɗe.



Shigarta asibitin keda wuya tayi saurin parking motarta  sannan ta nufi females ward direct zuwa numban ɗakin da Umman Sa'eeda ta sanar mata,tana shiga ɗakin ta tsaya cak ganin yadda ƙawarta ta koma lokaci guda,ga hancinta ya ƙara fitowa saboda ramar da tayi,idanunta kuma sun shige ciki sosai,tabbas duk wanda yasan Sa'eeda dole ya zubar mata da ƙwalla idan ya ganta a yanzu,a hankali ta nufi gadon da Sa'eedar take a kai tare da riƙo hannunta wanda ba'a saka canula ba,hawaye ne suka fara ganganrowa bisa kuncinta wanda batasan da zubowansu ba,cikin sanyin murya mai cike da rauni Iman ta fara magana



"Allah ya baki lafiya Sa'eeda, yasa kaffara ne a gareki,in shaa Allah bazasu gama da duniya lafiya ba sai Ubangiji yabi miki hakƙinki,Allah ya baki lafiya Sa'eeda, Allah ya tashi kafaɗunki Sa'eeda,sai Allah ya saaakkata mik.........."




Bata ƙarasa maganar ba ta fashe da matsanancin kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai sauraronta,kuka take sosai tare da tausayawa aminiyarta  ganin irin halin da take ciki duk saboda yaudara tabbas Ubangiji baya yafe hakƙin wani akan wani,sai Allah yabi mata hakƙinta.Tana cikin wannan kukan ne sai Umman Sa'eeda ta dafata tare da girgiza mata kai alamu tayi haƙuri tabar kukan amma ina kamar ƙara ƙarfin kukan nata akeyi tuno da labarin da wata ƴar ajinsu Emmanuella ta bata akan abinda ya faru ranar Friday.





Waiwaye




*******Kasancewar ranar Friday Iman batazo school ba saboda suna da gagarumin biki a familinsu sai Monday ta shigo,Iman ta shigo class amma babu Sa'eeda har wurin ƙarfe 9:12am na safe kuma tasan bata latti balle fashin makaranta,gajiya tayi  Iman da zama sai ta tambayi wata course mate ɗinsu Emmanuella da suke mutunci da ita akan akwai wani abu ne daya faru ranar Friday,Emmanuella  ta cire mata biri har wutsiyar abinda ya faru harda shiƙiyancin da ƴan aji sukaita ma Sa'eeda akan rashin asalinta sannan kuma tace mata saurayin Sa'eeda  ne Maryam zata aura in 2 weeks coming kafin exams.tashin hankali wanda ba'a saka mai rana,dole Sa'eeda taƙi zuwa makaranta, lallai ma Maryam wato kashedi haɗe da gargaɗin da ta mata bai shiga ƙwaƙwalwarta kenan.Ita tama rasa da wanne zata fara,shin kiran Sa'eeda zatayi taji halin da take ciki ko ta fara cin Uban ƴan aji lakada a waje,wata zuciyarta ne ta bata kyakkyawar shawara akan ta fara saita Maryam da muƙarrabanta sai daga baya ta kira Sa'eeda, hakan kuwa a kayi godiya tama Emmanuella sannan ta tashi daga seat ɗinta ta nufi seat ɗinsu Maryam wanda a lokacin suna hira abinsu cikin annashuwa,babu wanda yasan da zuwanta saidai sukaji saukan mara Tasss!!!! Tassss!!!! Babu wanda a cikin bai riƙe kuncinsa ba a tunanin kowa koshi aka mara amma jin babu abinda ya samu kumatunsu sukayi saurin kallon Maryam wacca a lokacin tayi sumar wucin gadi tsabar shigar marin,Rahma ta ɗan taɓa ta kamar an tsikareta ta dawo hayyacinta hade da sakin wata razananniyar ƙara wanda ya karaɗe ilahirin ajin ,babu shiri ƴan aji suka waiwayo jin wannan ƙara kamar drum,sai a sannan ne ta fashe da matsanancin kuka saboda ba ƙarya marukan sun shige ta matuƙar ainun.



Ita kuma Iman tana tsaye ƙyam a wurin sai wani jijjiga take riƙe da ƙugu,ga manya-manyan idanun nan nata sun kaɗa sunyi jajur kamar garwashi,duk wanda ya ganta a lokacin dole ya firgita ga wani huci da takeyi kamar wani kumurcin maciji mai jiran casss! yakai sará,cikin muryar da babu wanda  santa dashi ba ta fara magana



"Wato kashedin da naki akan Sa'eeda bai shiga cikin ƙwaƙwalwarta ba ko ehhhhh!!!!! Ba nace ki fita a harkarta ba ko bance miki ba ehh!!! Ba dake nake ba kosai na ƙara saukar miki da wasu lafiyayyun marukan da sukafi na dazun zaki bani amsa !!!  "



Diffff kamar an ɗauke ruwan sama haka Maryam ta tsagaita kukanta jin za'a ƙara mata wasu sabbin marukan da sukafi na ɗazun,cikin rawar murya haɗi da inda-inda ta fara magana



"Ehhh ddddda ddammman kin min kkashedi wallahi tallahi bani na fara mata magana ba ki yarda da........."



Kafin ta ƙarasa maganar taji Iman ta ƙara jefa mata wata tambayar



"Uban waye ya fara mata maganar a cikinku!!! "



Da sauri kowa ya nuna Rahma wacca tayi tsuru-tsuru da idanu kamar na mujiya,kafin ta lalubo amsar da zata ba Iman taji saukan maruka hagu da dama wanda lokaci guda duniyar ta fara mata juyi,wasu taurari tagani suna zagaye mata kai,haba itama razananniyar ƙara ta taki tare da fashewa da kuka tana taɓa kumatunta don ta tabbata suna nan ko ko sun cire.Haƙuri sukaita bata tare da cewa bazasu ƙara shiga sabgar Sa'eeda musamman ma Maryam tafi kowa a cikinsu bada haƙuri,buga desk ɗinsu Iman tayi da ƙarfi wanda saida suka ƙanƙame juna saboda ƙarar daya bada sannan ta ce



"Wallahi tallahi duk randa na sake ji daidai da rana ɗaya wata a cikin ko kuma ƴan aji tama Sa'eeda kallon hadarin kaji saina ci Ubansa lakada a waje sai kuma naga uban da zai tsaya mata,ƴan iska,musamman ma ke Maryam"



Nunata tayi yatsa sannan ta cigaba da cewa



"Ke  gaki butulu mayaudariya,shegiya,munafuka,ke a tunanin Allah zai barki ne,kije ga auran kiyi wallahi ko ba daɗe ko bajima sai Allah ya sakama Sa'eeda tata-izan da gaggawa,sai Allah ya ɗaukakata sama daku,sannan kuma rashin asalin da kike cewa bata dashi in shaa Allah sai Allah ya sadata da asalinta,kuma inaji a jikina Sa'eeda ƴar babban gida ce, kaddara ce ta samesu ita da Ummanta,badai saboda ɗa namiji bane kika yiwa Sa'eeda muguwar sakayya to ki jira ƙarshanki keda munafin saurayin nata, wallahi da ƙafafunku zakuzo kuna roƙonta akan ta yafe muku la'anannu kawai,aje asha biki but put that at the back of your mind ƙarshanku yana nan zuwa bi'izinillahi!! "



Tabbas bama su Maryam  da muƙarrabanta ba kowa a ajin saida jikinsa yayi sanyi don sun tsorata sosai da Iman,haka ta koma seat ɗinta ta zauna saboda natsuwarta ta dawo mata,sai can daga baya ta kira Sa'eeda wanda a lokacin bacci take sai Ummanta ne ta ɗauka,a nan ne ta sanar mata da Sa'eeda bata da lafiya an kwantar dasu a asibiti amma Alhamdulillah ta samu sauƙi, cikin ruɗewa Iman ta tambayi asibitin da aka kwantar dasu,babu ɓata lokaci Umman Sa'eeda ta sanar mata da sunan asibitin da numban ɗakin da aka kwantar dasu.*******






Cikin Labari





A hankali Sa'eeda ta farka daga bacci tare da motsa hannunta wanda babu canula jin kamar an riƙe mata hannun,da sauri Iman ta ɗago kanta jin Sa'eeda ta farka daga bacci,kallon junansu sukayi sai Sa'eeda ta sakarma Iman murmushi,ita ma mayar mata tayi da martanin murmushin sai ta ce



"Sa'eeda ya jikin naki,wallahi bansan baki da lafiya sai yau,  dazu da naje school aka sanar min abinda Maryam ta miki sai na kira wayarki Umma ta ɗauka sai a lokacin ta sanar min da baki da lafiya kuma an kwantar daku a asibiti"



Cikin muryar marasa lafiya Sa'eeda ta fara magana



"Eh wallahi amma Alhamdulillah naji sauƙi sosai yanzu"



"Maa shaa Allah, Allah yasa kaffarane agareki "



"Ameen ya Rabbi"



Likita ne ya shigo tare da wata nurse tana biye dashi,dubata yayi tare da mata wasu tambayoyi,ita kuma amsa mata cikin sanyin murya, sai ya dubi Umman Sa'eeda ya ce



"Alhamdulillah jikinta ya samu sauƙi sosai don haka yau za'a sallame ku in shaa Allah tare da baku magungunan da zata dinga sha, ki kula da ita sosai sannan a daina barinta ita kaɗai tana tunani,saboda shiyake haifar da damuwa  wanda a ƙarshe mutum yakan samu matsala ko ciwon hawan jini ya sameshi ko kuma ciwon zuciya,dan Allah a kula sosai"



"In shaa Allah likita zamu kula sosai"



Fita yayi shida nurse ɗin,sai Iman ta bisu waje don tanason ta biya kuɗin sallama da na magani,nurse ɗin ce tayi directing ɗinta kun chasheir don ta biya kuɗin.Bayan ta biya ne sai ta komai ɗakin wanda a lokacin Umman Sa'eeda na haɗa kayansu sai a sannan ne ta faɗa ma Umman Sa'eeda akan ta biya kuɗin sallama dana magani su wuce kawai gidan yanzu.kasa magana Umman Sa'eeda tayi don batasan wani irin godiya zatama Iman ba saboda ta taimake su sosai da badan zuwanta ba da shikenan kuɗin da take saving na registration ɗin Sa'eeda zata cire ta biya.Iman tasha godiya sosai wurin Umman Sa'eeda harda ita kanta Sa'eedar,haka suka ɗunguma suka nufo gida a motar Iman.



Bayan sun sauka ne sai Umman Sa'eeda da Sa'eeda suka nufo cikin gidan ita kuma Iman ta tsaya kashe motarta,a lokacin su Umma Kande da Maman Jummalo kowa da ɗaurin ƙirji sun baje kan tabarma suna hira abinsu,da sallama suka shigo gidan amma babu wanda a cikin ya amsa masu saima Umma Kande da ta miƙe kamar an tsikareta tare da cewa



"Yiririiiii!  Wata sabon gani,ƴan zubar da cikin ne sai yau Allah yayi dawowarku gida,ai bamu san  asibitin ba da kun ganmu"



Iman ce da shigowarta gidan kenan taji kamalan Umma Kande,kasa daurewa tayi saida ta mayarwa Umma Kande da martani 



"To tsohuwar kilaki,mai kama da gwaggwan biriya,mai baki saikace na jaɓa,yaranki ne zasu zubar da ciki ba Sa'eeda,shaiɗaniyar tsohuwa kawai"



"Aww iyyeeee,ke kuma waya sako bakinki a ciki maganar gida ehhh"



Kafin Iman ta mayar mata da martani Umman Sa'eeda taja hannunta suka shiga ciki,saboda batason tashin hankali,haka ta zaunar da ita tare dace mata karta biyema haukansu don ita mahaukata ta ɗaukesu.



Haka Iman ta wuni a gidan sai da yamma ta wuce gida tare da tabbatar ma Sa'eeda zatazo gobe dubata in shaa Allah.



Kusan sati biyu Sa'eeda tayi tana shan magungunanta,Alhamdulillah babu laifi sauƙi yazo domin yanzu har ƴar ramar da tayi ta ciko ga haske da fresh da jikinta ya ƙara kasancewar bata zuwa makaranta taimakonta ɗaya sun gama lectures ɗinsu gaba ɗaya,revision kawai da tutorial sukeyi a aji.



Kasancewar yau asabar  Umman Sa'eeda bata fita shara ba,suna zaune dukkansu a ɗaki suna ƴar hirarsu ta uwa da ɗiya,sai a sannan Sa'eeda tayi tunanin ta sanar ma Ummanta shawarar da ta yanke game da karatunta,ƙara gyara zama tayi sannan ta fara magana da cewa



"Ammm Ummina daman inaso da sanar miki da cewa kawai zan ajiye karatuna saboda ƴan ajin mu basa sona ga iya shegen Maryam takemin ita da ƙawayanta"



Shiru Umman Sa'eeda tayi tana kallon ƴarta ta cike da dunbin mamaki,a ce duk wahala da suka sha a baya sai yanzu da baifi saura shekara ɗaya ba amma ta ce ta fasa,haƙiƙa ran Umman Sa'eeda yayi ƙololuwan ɓaci jin kalaman ɗiyarta ta,cikin takaici da baƙin ciki Umman Sa'eeda ta fara magana



"Lallai Sa'eeda ashe ina miki kallon mai hankali da tunina ashe ba haka kika ba,yanzu saboda ƴan ajinku da Maryam zaisa ki fasa karatunki Sa'eeda, mai ya shiga ƙwaƙwalwarki ne Sa'eeda, ina jarumtar da nasanki da ita,ina NACIN da nasanki dashi akan karatu,ina kika kai so da ƙaunar da kike ma karatunki,ina yake Sa'eeda,yanzu duk wahala da nasha babu ko sisin mahaifinki akan karatunki zai tashi a banza kenan Sa'eeda,sakayyar da zakimin kenan a matsayina na mahaifiyarki wacca bata da wani buri illa ganin rayuwarki ta ginu,ban damu da ci ko sutura mai kyau ba duk ganin rayuwarki ta ginu amma aaaam.........."



Fashewa tayi da matsanancin kuka harda shessheƙa,da sauri Sa'eeda da dawo hayyacinta daga tunanin da da nasanin faɗawa mahaifiyar wannan magana,cikin rawar murya Sa'eeda ta fara magana cike da dana sani



"Ummina  kiyi haƙuri don Allah ki daina kuka,wallahi na haƙura zan cigaba da karatuna Ummina, ki yarda dani Ummina"



Girgiza mana kai Umman Sa'eeda tayi tare da cewa 



"A'a Sa'eeda shikenan ai sai ki haƙura da karatun naki,saboda wasu wa'inda basu suke baki ci da sha ba kikeso ki rushe tsarin ginin rayuwarki Sa'eeda, saboda wani can banza wanda baisan kina sonsa ba kikeso ki lalata rayuwarki Sa'eeda, ina juriya da jarumtar dana sanki da ita,ina kika kaisu Sa'eeda!!! "



Tabbas maganganun Umman Sa'eeda ya ratsa ƙashi har zuwa ɓargon Sa'eeda sannan ya shiga kusufa-kusufa na jini dana jijiyar Sa'eeda tabbas yanzu zata dawo da NACINTA a karatu,sannan tana saka ran NACINTA ZAI JAWO MATA NASARA,dole ne ta farka daga nauyayyen bacci da take,dole ne ta iya fuskantar kowani irin ƙalubale a rayuwarta,cikin dakiya tare da tabbatarwa Sa'eeda ta fara magana



"Na ɗau miki alƙawari Ummina, zan dawo da juriya da jarumtar da kika sanni da ita,zan kasance jaruma mai fuskantar kowani irin ƙalubale da zaizo min a rayuwa,zan dawo da NACINA domin zai JAWO MIN NASARA babba a rayuwata,ki yarda dani Ummina,daga ranar irin ta yau na cire so da ƙaunar da nikewa Sauban a zuciyata,bazaki sake jina da maganar Sauban ba koda shi ne autan maza,in shaa Allah zan cigaba da addu'ar Allah ya zaɓamin wanda ya fisa zama alkhairi a rayuwata"



Jinjina kai Umman Sa'eeda tayi saboda ganin gaskiya tare da tabbatuwa a cikin zantuttunkan ƴarta,murmushi ta saki sannan ta ce



"Dakyau sanyin idaniyata,haƙiƙa naji daɗin cire Sauban da kikayi a zuciyata sannan da maida hankalinki da zakiyi a karatunki,Allah ya miki zanbin miji na gari mai sonki da ƙaunar,ya baki nasara a karatunki,ya tsare gabanki da bayanki,ya miki katangar ƙarfe tsakaninki da maƙiyanki,ya albarkaci rayuwarki baki ɗaya"



"Allahu Aaaamen Ummina, in shaa Allah daga yau kin daina kukan baƙin ciki a kaina saidai na farin ciki"



"Allah ya yarda sanyin idaniyata"



Haka suka cigaba da hirarsu cike da annashuwa kamar ba wani ɓacin rai mai samesu ba,tun daga ranar Sa'eeda tayi deleting contact ɗin Sauban,messages ɗinsa,hotunansa,da komai nasa a wayarta sannan ta ƙara bada himma a kan karatunta saboda exams ɗinsu baifi saura kwana biyar ba.Wannan kenan.








TUNATARWA





******Ƙalubali ga mata masu makauniyar soyayya,kusani wasu mazan suna amfani da wannan damar ne don su cimma wata manufa tasu a gareku saboda suna ganin baza ku iya rayuwa babu su ba,tabbas wannan hanya ce dayawa daga cikin maza suke amfani dashi wurin lalata rayuwar mata wanda daga ƙarshe zusa wulaƙantasu,su ɓata tarbiyyar ta iyayensu suka daɗe suna ginawa,mu kula ƴan uwana mata,Allah ka tsaremu da samari shaho,ka haɗamu da masoyanmu na gaskiya.



Ƙalubale ga mata masu bayyana sirrikansu da ƙawayen,kamar caka ma kanka wuƙa kake ba tare da kasani ba domin wasu ƙawayen ba tsakani da Allah suke tare da suke,bayan haka ma ɗan Adam yakan canja daga yadda kasansa,mu kula ƴan uwana mata,Allah mana tsari da ƙawayen banza masu nuna suna son a bayyane amma a ɓoye suna sukarmu******




                  @@ @@@@@@@




Ɓangaren Sauban sai shirya-shiryan bikinsa yake yama manta da wata Sa'eeda a rayuwarsa hasalima komai nata ya gogeshi a wayarsa,hankalinsa kacokar ya koma kan Maryam saboda a ganinsa tafi Sa'eeda wayewa gashi bata da asili.



Kasancewar yau asabar saura ƴan kwanaki bikinsa,yana zaune shida  da amininsa Captain Fu'ad suna tattaunawa game da bikin wanda Captain Fu'ad ya gaza haƙuri saida ya yayi masa magana saboda abin na ci masa tuwo a ƙwarya



"A gaskiya Sauban bazan ɓoye maka ba,kaci amanar Sa'eeda wallahi,mai tayi maka da zaka mata irin wannan muguwar sakkaya,in fact bama kai kaɗai harda wacca zaka aura,guna ganin kun mata adalici ne musamman ma kai"



Taɓe baki yayi irin ko a jikinsa ɗin nan, a da baiso tanka masa ba sai kuma yace



"Naci amanarta huhhhh!!!,mai zanyi da marar asali wacca bata waye ba,kai ko ɗan taɓa hannun Sa'eeda ban taɓa yi ba,common outing Sa'eeda bataso wai sai munyi aure,haba  i'm tired of her stupidity "



Girgiza kai Captain Fu'ad yayi tare da cewa



"Marar asali kuma,bata da mahaifi ne?"



"No tanada mahaifi saidai mamanta da kakarta tsintarsu akayi a titi suna gararamba"



"Innalillahi Wa'inna Ilahi Raji'un yanzu saboda wannan ne yasa ka fasa auranta Sauban,ina hankalinka da tunaninka ya shiga ne,who knows asiri akama kakarta ko kuma ƴan gudun hijira ne,haba Sauban  wallahi kaban mamaki,tukunna ma waya faɗa maka bata da asali"




"Ƙawar Mum ce sannan kuma Aunty Maryam ta sanar mata hakan kuma kasan ba ƙarya zata faɗa ba"



"Mata! mata! Akwai makirci wallahi, yanzu in mum ta kasa gane makirci ne suka ƙulla don ka auri Maryam kai bazaka iya hankalta ba Sauban"



"Mtssss! Don Allah mubar zancen nan mukoma yadda zamu tsara bikin kaina ma harya fara ciwo"



"Dawa Allah ya sawwaƙe ni Fu'ad na zauna  don aci amanar wata,Allah ya kiyaye,ai tunda nasan dalilin rabuwarka da Sa'eeda wallahi kaji na rantse bazaka ga ƙeyata a bikinka ba domin ni ba mayaudari bane"



Sauban kallon Captain Fu'ad yake da mamaki sai kuma yace



"Mai zai hana ka aureta mana sai ka tusa mana baƙin ciki"



Dariya Captain Fu'ad yayi sai ya ce



"Wallahi da badan ansa ranar aure na ba da kuwa babu abinda zai hana na aureta saboda she is complete"



"Can ta matse maka"



"Kasani Allah baya barin hakƙin wani akan wani,kaji tsoran Allah Sauban, kasan yanzu wani hali take ciki dul saboda kai,in shaa Allah sai Allah yabata wanda ya fita komai wallahi kuma muna nan dakai"




Fuuuuuuu ya ɗau makullin motarsa ya ƙara gaba ba tare da yama Sauban Sallama.wannan kenan




           @@@@@@@@




Ɓangaren Umma Kande ita da Maman Jummalo komai na tafiya musu normal,kamar kullum yau ma suna zaune a kan tabarma suna hirarsu cike da annashuwa kawai sukaga mutum ya faɗo cikin gidan babu sallama, haba da sauri suka miƙe dukansu,cikin tashin hankali Maman Jummalo tace




"Ni Hasfy wazan gani haka babu ɗan kwali balle hijabi,meya sameki....................




Mu haɗu a pages na gaba domin cigaba da suburbuɗo muku wannan cakwakiyar labari🙃🙃🙃💘💘💘💖💖💖✍️✍️



 


*****tofa,wacece a cikin yaranya su Umma Kande ta shigo babu ɗan kwali balle hijabi







Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️





Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓





Post a Comment

0 Comments