TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 37-38

 3⃣7⃣----3⃣8⃣








Suna cin hakane aka kira wayar Umma Kande wacca tsabar masifa bata duba mai kiranta ba ta amsa kiran


"Hello"


A can ne ake mata magana,wanda lokaci guda ta rikice tana cewa


"Mai wayar!!! "


A can aka ƙara tabbatar mata,habawa sakin wayar tayi a ƙasa haɗi da zaman ƴan bori,tana ihu da kururuwan ta bani ta lalace shikenan ta mutu.Kanta su Maman Jummalo sukayi suna tambayar lafiya mai ya rafu,cikin kuka haɗi da majina take cewa


"Na shiga Uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa!!! Na mutu na lalace wayyo ni Saratu!!!! Yanzu mai yayi saura gareni,yiiiiii!!! Yiiiiii!!! "


"Ƙawas wai meya faru ne,kinsamu a duhu,ga kuma kuka kina yi"


"Maman Jummalo gobara ta tashi da Musa!!! Shikenan ɗana a duniyi,yanzu ya tafi ya barni,ina ganin bala'i da masifa ni Saratu!!! Wayyo Musana!!! Shikenan ko gawan ɗana bazan gani baaaaa!!!! Yiiiiiii!!! Yiiiiiii!!!


Jin abinda Umma Kande ta ce gidan ya kaure da kuka haɗi da iface-iface musamman Iklima wacca suka fi shiri da Musa,tayi kuka haɗi da birgima a ƙasa kamar sabuwar kamu.Maman Jummalo itama tayi kuka sosai tare da ba Umma Kande haƙuri,amma ina Umma Kande kamar wata zautatta haka tayi,gashi tayi zaman ƴan bori haɗi da cire ɗan kwalin kanta tana ihu da kururuwa


" Musa! Musa! Musa! Ka dawo karka tafi ka karbi,kaine rayuwata,ka dawo,ka dawo Musana na roƙekaaaaaa!!! "


Waiwaye


******Abinda su Umma Kande basu sani ba game da rasuwar Musa shi ne,kasancewar Musa ɗan daudu ne kuma mai harka da manya-manyan mata a Calabar,manyan matan suna zuwa ɗaukarshi har gidajensu domin suyi sharholiyarsu  sannan su biyashi maƙudan kuɗi saboda yasan sirrin mata sosai.


Hausawa suka ce tsautsayi baya wuce ranarsa,ranar data kasance ranar da Allah ya ɗauki ran Musa shi ne,wata customersa ce tazo har gidan karuwai ta ɗaukeshi suka tafi gidanta,zama yayi a falonta sai tace bara ta girka musu abinci sai suji daɗin harkar dakyau,bayan matar da ɗaura girki a gas cooker mai mazaunai hudu sai ta fito falon,tana zuwa sai Musa yayita janta da kissarsa ta riƙakƙun ƴan daudu,habawa tuni mata ta manta da abinda ta ɗaura kan gas cooker suka fara masha'arsu,wanda har girkin ya ƙone,tukunyar tayi baƙi amma hankalinsu baya a jikinsu balle suji ƙauri,nan da nan wuta ta tashi a kitchen kan kace me ta gauraye ko'ina,su Musa kafin suyi wani aune,wuta ta shigo falon,haka su biyu suka ƙone ƙurmus sai ƙashi,wannan ne asalin sanadin mutuwar Musa******





*Cikin Labari*




Suna a wannan yanayin ne saiga Baban Nusaiba ya shigo gidan kamar an jefosa,tun daga zaure yake jin ihu da kururuwansu Umma Kande wanda hakan ne ya sashi saurin shiga gidan,samun Umma Kande yayi a zaune a ƙasa,ta wage ƙafafunta haɗi da saka hannuwa a kai tana ihu.cikin sanyin murya ya tambayi lafiya,Iklima ta sanar mishi Musa ne ya rasu,bai sake ce da ita komai ba ya fita daga gidan,fuskarsa babu yabo babu fallasa,shidai gashi nan,mutuwar ma ba damuwa yayi da ita ba,to baya cikin hankalinsa.


Tun safe Sa'eeda da Ummanta basa nan,ita Sa'eeda taje IT, ita kuma Ummanta daga shara ta wuce aikin biki a bayan layinsu,basu san da abinda ke faruwa ba.


Da sallama Sa'eeda ta shigo gidan,cak ta tsaya ganin ikon Allah,yau su Umma Kande ne ke kuka haka duk da lokacin rasuwar Zaliha tayi kuka amma wannan karon kamar hauka take,wai meke faruwa ne? Mai ya samesu haka?,tambayar kanta tayi,wanda babu amsa,taso ta buɗe ɗakinsu ta shiga ba tare da ta tambayi mai ya samesu ba,amma ina bazata iya ba,ita mai raunin zuciya ce ga mutane,haka tayi kasadar tambayar Iklima mai ya faru.Cikin kuka Iklima ta sanar ma Sa'eeda Musa ne ya rasu yanzu.


"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,Allahumma gafir lahu,warhamhu,wa'afi anhu,Allah ya gafara masa,yasa ya huta,yasa kuma  aljanna ce makoma a garesa,Allah ya baku haƙuri tare da juriyar rashinsa"


Iklima da Jummalo ne suka iya bata amsa,amma Maman Jummalo tare da mai gayya mai aiki wato Umma Kande basu san mai take cewa ba tsabar tashin hankali da ruɗun daya samesu.Ɗaki Sa'eeda ta wuce wanda bata jima ba saiga Ummanta ta dawo,itama tambayarsu tayi mai ya faru,Iklima ce ta bata amsa,salati tayi tare da yi mishi addu'ar Allah ya gafarta masa ta wuce ɗaki.


Haka su Umma Kande suka ci-gaba da zaman makokin Musa wanda har ƴan uwanta da Maiduguri saida sukazo ta'aziyya,yanzu kullum da hijabi zakaga Umma Kande haɗe da carbi saikace tasan me ake cewa😂😂😂,bayan anyi arba'in ɗin Musa wanda ba'a kawo gawarsa ba kasancewar ƙurmus ya ƙone,Umma Kande ta yaki ce saka hijabi haɗi da riƙe carbi,wannan karon Nusaiba batazo ba saidai kira a waya tai musu ta'aziyya saboda yanzu bata samun lokaci sosai,tauraronta ƙara haskawa yake a harkar luwaɗi da kuma lesbianism,wanda bata wannan ƙasa bata waccan.


Bayan rasuwar Musa da wata biyu su Iklima da Jummalo suka shiga islamiyar da Sa'eeda tayi sauka,ajin matan aure suka shiga saboda babu wani abun kirki da suka sani dangane da addinsu su.Wannan kenan



            @@@ @@@@@@@@



*Bayan Wata Shida da Sati Biyu*




A ɓangaren karatun Sa'eeda kuwa,sun kammala IT yanzu kuma sun shiga shekarar ƙarshe a karatunsu wato 400 level,yawanci lecturers ɗin da suke ɗaukarsu sababbi ne,masu zafi  babu wasa a tattare dasu.Farkon shigarsu ajin wata sabuwa lecterer ƴar gayu ta fara ɗaukarsu wani course,shigowanta ajin tayi tozali da Sa'eeda, cak ta tsaya tana kallonta babu ko ƙyafta ido,kowa a ajin kallansu suka komayi ganin wannan ikon Allah, mata daga zuwa aji ta kafe Sa'eeda da kallo babu ko ƙyartawa,kusan seconds 20 sai kuma lecterer ta ƙarasa cikin ajin still idanunta akan Sa'eeda, kasa haƙuri matar tayi ta tambayeta da harshen turanci


"Young Lady  what's your name please? "


Sa'eeda da tunda ta haɗa ido da wannan sabuwar lecterer ƙirjinta ya fara duka,gashi taga matar sai kallonta take babu ko ƙiftawa,miƙewa tayi cikin ladabi ta amsa mata cikin hatshen turanci


"My name is Sa'eeda Sulaiman"


"From which State"


"From Kaduna"


"Alrght seat down"


Ba haka ran matar yaso ba domin akwai abinda takeso ta tabbatar akan garinsu,saboda wani abu take ji a zuciyarta game da wannan yarinya,amma ya zata tabbatar tunda ta ce ita ƴar Kaduna ce,sha re zancen tayi,tazo gaban Allon haɗi da gabatar da kanta cikin harshen turanci wanda take magana cike da ƙwarewa


"Good morning class,My name is Dr.Nabila Abubakar Kabir Dikko,nice to meet you all"


Duka ajin suka amsa mata cike da murna saboda matar ta gama tafiya da imaninsu,ga turancin da takeyi daga ji kasan ba'a Nigeria tayi karatu ba,saboda yadda take amfani da phonex wurin lanƙwasa harshenta.Cike da ƙwarewa Dr. Nabila take musu karatu,gashi ta iya bayani mai gamsarwa,lokaci-lokaci idanun Dr.Nabila na kanta Sa'eeda wanda har yanzu ta kasa gasgata  abinda zuciyarta take ayyanawa game da yarinyar,haka ta kammala musu lecterers ta fita,kamar jira ƴan aji suke tana fita kowa ya fara yaba Dr. Nabila saboda ƙwarewa da gayunta.


Haka suka ci-gaba da karatunsu a 400 level  first semester cikin nasara,a semester ɗin ne aka rarraba ɗalibai ga project supervisors nasu,luckily Sa'eeda aka bama Dr.Nabila, haƙiƙa Dr Nabila taji daɗin bata Sa'eeda da akayi a matsayin project student ɗinta,koba komai zata samu damar tambayanta abubuwa da dama wanda suke cikin ranta tun a ranar da tayi tozali da ita.


Sa'eeda ma haka abin yake a wurinta domin har labarin Dr Nabila take ba ma Ummanta,saboda tanada kirki sosai gashi tunda Dr.Nabila ta zama supervisor ɗinta take taimakonta da kuɗi ko wasu abubuwa,duk da Sa'eedar bata son amsa amma babu yadda ta iya saboda jan idon da Dr. Nabila take ma Sa'eeda idan taƙi amsa,ƴan aji sunyi gulmar har sun gaji musammam squad ɗinsu Maryam wai Sa'eeda na shisshigema Dr.Nabila saboda taga tanada kuɗi sosai,ga sabuwar Land Cruiser baƙa wanda take hawa,haka dai suka gaji da gulmar suka sa musu ido.


A ɓangaren ƙawancen Sa'eeda da Iman baza muce komai ba saidai muce maa shaa Allah,domin ƙawancen da sukeyi na tsakani da Allah ne babu hassada balle ƙyashi,ba ƙaramin daɗi Iman taji ba ganin yadda Dr.Nabila take son Sa'eeda, hakan na mata daɗi a rai koba komai ganin ƙawarta cikin farin ciki na daɗaɗa ranta.Wannan Kenan



          @@@@@@@@ @@@@



A ɓangaren LOVE BIRD🕊️🕊️🕊️ wato Sauban da Maryam,tunda ya ce ma Maryam taje gidansu gyaro hali tare da koyan girki har yanzu bata dawo ba kusan wata biyar kenan,gashi har sun koma makaranta amma taƙi dawowa hasalima acan take tafiyarta makaranta abunta,tunda iyayenta sun ɗaure mata gindi akan sai Sauban yazo da kansa ya bada haƙuri kafin ta koma gidansa,shi kuma ya rantse koza ta shekara a gidansu ba zaije bikonta ba,domin laifinta ne ba nasa ba.Maryam nasan komawa gidan mijinta amma bata samu fuska gun iyayenta ba saboda sun kafe akan lalle-lalle-ilalla sai yazo ya bada haƙuri da kansa.


Shi kuma Sauban yanzu ya fita a harkarta musamman shawarar da Mom ɗinsa tazo mishi dashi wanda ya aminta sosai akan shawarar da ta yanke.


Yau ne ya shirya zuwa gidansu Captain Fu'ad domin yanason ya bashi shawara tare da ƙara bashi haƙurin abinda ya faru a gidansa kasancewar Captain Fu'ad auransa ya matso saura sati ɗaya,kuma ya samu hutu a wurin aikinsa  Port harcourt.Bayan mai gadi ya buɗe ma Sauban gate ya shigo da motarsa yayi parking tare da nufar part ɗin Captain Fu'ad, da sallama ya shiga falon kasancewar ƙofar a buɗe take, amsa masa Captain Fu'ad yayi tare da miƙewa yana sakin wani shegen murmushi babu gaira babu dalili,tunda Sauban yaga yana mishi wannan munafikin murmushin yasan mugunta ya gani,cikin ɗaure fuska Sauban ya ce


"Malam ya da shigowa na ka mike tare da sakin murmushi"


Dariya Captain Fu'ad yayi tare da cewa


"Haba Angon Mairo kuku,kyau naga ka ƙara shiyasa ni sakin murmushi ganin aminina kuma ɗan uwana na samun kwanciyar hankali"


Eh tabbas! Yau naga ta kaina da Fu'ad, nasan kashina ya bushe,badai yazo gidana yaga yadda muke rayuwa ba shikenan ai na kaɗe ni Sauban, katse mishi tunani yayi da cewa


"Ka zauna mana Angon Mairo kuku,kana hutawa fa"


"Oooo God!!! Haba Fu'ad wani irin iya shege ne haka,ko ruwa baka bani nasha ba amma ka wani cikani a surutu marasa ma'ana"


Dariya Captain Fu'ad ya tintsire dashi harda riƙe ciki yana nuna Sauban yana sake tintsire dariya,ɓacin rai iya ɓacin rai Sauban yake ƙololuwa.Cike fusata yace da Captain Fu'ad


"Wallahi zanbar maka ɗaki naje na gaida Mom tunda naga alama ƙwaƙwalwarka ta taɓu"


"Sorry friend wallahi yadda ka koma ne yasani dariya"


"Ok nagane wato ga mahaukaci yazo ko? "


"A'a fa Sauban,why are misunderstanding my words,ummmm wallahi ba haka bane"


"No hakane mana,ga angon Mairo kuku ba wacca kaja girkinta harda amai da shan gorukan ruwa har biyu,ai dole kamin dariya Fu'ad"


Dariya Captain Fu'ad yayi tare da yima Sauban waƙa harda rawa yana cewa


"Da so samu ehh!!! Ace ta iya girki,ƴar fara first lady mai kyau sannan ace tanada kirki ehh,inba kasamu ehh! Inba kasamu ehh!! Inba kasamu ehh ehh ehh habawaaa!!! "


Dafe kansa Sauban yayi yana cewa


"Kai kai kai yau naga ta kaina,shikenan ai tunda kasan sirrin gidana na kaɗe,don Allah mubar wannan shirma,muyi abinda ya dace Fu'ad"


"Tohhh Angon Mairo kuku,ina sauraranka"


Baza yayi da abinda ya ce don idan ya biye halin Captain Fu'ad sai su shekara a haka,cikin muryar damuwa Sauban ya fara magana


"Fu'ad wallahi ina cikin matsala babba"


With serious voice Captain Fu'ad ya ce


"Subhanallah,meke faruwa Sauban"


" Ai komai ma ya faru Captain, Mom ce tazo min ta wata shawara a lokacin Maryam nace taje gidansu gyaran hali akan na ƙara aure,duk da nima inada wannan burin amma ba'a nan kusa ba,kwata-kwata yaushe akayi bikinmu ace har na ƙara aure, gashi Maryam duk yadda naso ta natsu tasan hakƙin mijinta amma ya gagara,idan na lanƙwasota ta nan saita ɓalle ta can,tana  da matsaloli masu yawa  wallahi,rashin iya girki,baƙar magana,rashin girmama na gaba da ita,ga uban ƙazanta,gayu kawai ta iya amma duk abinda matar aure ya dace ta sani babu abinda Maryam ta sani,could you imagine pads ɗin da tayi amfani dashi after her mensturation a toilet ta barshi saidai ni dana shigo toilet ɗin na ɗauke tare da jefarwa,how did you think i can tolerate her stupid atitude Fu'ad, common gyaran ɗaki Maryam bata iya ba,balle akai kan uwa uba girki,inaa inaa dole na samo ma kaina mafita wallahi,don bazan iya jurar halayanta ba,gashi tunda nace taje gidansu gyaran hali har yau taƙi dawowa,kuma na rantse babu inda zani bikonta"


Shiru Captain Fu'ad yayi yana kallon aminin nasa cike da tausayi duk da shi yajama kanta tun farko,sauke ajirar zuciya Captain Fu'ad yayi kafin ya ce


"Kaga illar dana hango maka tun a baya kaƙi ganewa,irin wannan matsalar na hango maka Sauban amma ina sai kayi burus da shawarata,ka irinta nan Sauban kwata-kwata yaushe kayi auran amma har ka fara fuskantar matsalolin da ko wa'inda suka shekara goma basu fuskanta ba,i told you from initial not just by mere looking zaka san wacca ta dace ka aura ba,shi aure da kake ganinsa akwai features da mutum yake bi kafin yasan wacca tafi cancanta ya aure,amma kai ina kyau da gayu haɗi da social life ya ruɗeka,kai kafi son mace very social,beautifuland classy bayan the most impotant features ɗin aure ka barsu,like addinin mace,kamewarta,natsuwarta,tsaftarta,ɗabi'unta da dai sauransu,duk da wannan baka duba ba sai kyau da wayewarta kawai,taya zakuji daɗin auran bayan turbar da kuka ɗauka kaida ita ba mai ɓulle muku bane,alhakin Sa'eeda ne tun kan aje ko'ina Allah ya fara saka mata,mace mai hankali, natsuwa,ilimi,ga uwa uba tarbiyya duk Sa'eeda ta tattarasu amma saboda wani dalili wanda baikai ya kawo ba,ka wofantar da damarka Sauban"


Shiru Sauban yayi yana sauraron abokinsa,wanda sai yanzu yake gane kuskuransa,tabbas yayi wasa da damarsa,sauke  ajiyar zuciya yayi kafin ya ce 


"Duk abinda ka faɗa Fu'ad gaskiya ne,na riga na ɓata rawata da tsalle,sai yanzu na gane illar da kake nunin abaya amma nayi burus da shawararka,yanzu dai nothing we can do tunda is already a past"


"Hakane,yanzu wacece Mom ta baka shawarar da aura "


"Cousin sister ɗina ce wacca take a Malaysia tana karatu,yanzu haka baifi watanni huɗu ya rage ta dawo ba"


*Waiwaye*




****Wata ɗaya da tafiyar Maryam,Mom ɗin Sauban ta kirasa har bedroom ɗinta,bayan ya shiga da sallama ya samu wuri ya zauna,cikin girmamawa ya gaisheta,ita kuma ta amsa masa cike da kulawa  tana murmushi,shiru ɗakin yayi na tsawan wasu seconds duk a lokacin idanun Momin Sauban yana kan Sauban ganin ya rame sosai,gashi ba annuri a tattare dashi,gyaran murya tayi sannan ta kira sunansa cikin sassayyan murya


"Sauban"


Gaban shi ne ya faɗi jin irin wannan kiran sunan da ta masa,domin idan Mominsa tanason ta faɗa mishi wata muhimmiyar magana,sunansa take fara kira cikin sanyin murya.Dagowa yayi yana kallonta tare da cewa


"Na'am Mom"


Cikin muryar damuwa ta fara magana


"Yanzu haka Sauban ka koma? Duk ka rame kayi baƙi,ko baka da lafiya ne?"


Girgiza mata kai yayi alamun a'a sannan ta cigaba da cewa


"Sauban wata shawara na kawo maka kuma na tabbata mai ɓullewa ce da yardar Allah"


"To Mom ina sauraranki"


Ci-gaba da maganarta tayi tana cewa


"Aure nake so ka ƙara Sauban,tunda ita waccan batasan mai yake me yake mata ciwo ba"


Daramm! Gabansa ya faɗi jin wani sabon tashin hankali,ba wai bayason ƙara aure bane,a'a da wuri haka ko shekara ɗaya ba suyi ba,cikin girmamawa ya ce


"Momina  da wuri haka,nifa ko budurwa banda ita yanzu"


"Da wuri kuwa Sauban tunda ba samun kulawa kake wurin Maryam ba,hasalima ban ga amfanin auran ba tunda ana yinsa ne don samun natsuwa,amma kai sai akasin haka,yanzu dai akwai Khairat ƴar wajan Auntynku Habiba wacca take karatu a malaysia,tana da hankali da natsuwa ga ilimin addini dana boko,ita naso ka aura tun farko amma ka nuna kai Sa'eeda kakeso wanda ni sai yanzu nagane ashe makirci Haj.Labara ta ƙulla don ka auri ƴar ƙwantarta,gashi dai yanzu aure baiyi riba ba hasalima faɗuwa aka samu,zan baka numbanta ku daidaita kafin ta dawo tunda ta kusa kammala karatun nata"


"To Mom ba damuwa,Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi"


Daɗi ya kama Momin Sauban jin ɗanta ya karɓi shawarata,murmusawa tayi sannan tace


"Allah  ya maka albarkha,yasa ƴaƴanka sumaka biyayya irin yadda kamin kuma kake faranta mun rai,Allah yasa ta zamo sanyin idaniyarka tare da farin cikinka"


"Aaaameen ya Hayyu ya Qayyum"


Tashi yayi haɗi da mata sallama ,yasan khairat farin sani,tabbas ba ƙarya tanada tarbiyya sosai da natsuwa, haba sai yanzu yaji hankalinsa ya fara dawowa jikinsa.


Tunda ya amshi numban khairat soyayya ta ƙullu a tsakaninsu,babu laifi akwai natsuwa a tattare da ita.*****




*Cikin labari*



Bayan Sauban ya gama faɗawa Captain Fu'ad yadda sukayi da Mominsa harda soyayyarsa yanzu ta ƙullu a tsakaninshi da Khairat, ya wuce gida.


Kwana uku da zuwansa gidan Captain Fu'ad sai ga Maryam ta shigo gidan kamar an jefota,a lokacin yana falo ya baje abincin da yayo takeaway ɗinsa yana ci.Sallama tayi ta shigo tare da akwatinta,babu yabo babu fallasa ya amsa sallamarta ya cigaba da cin abincinsa hankalinsa kwance.Kasa haƙuri Maryam tayi ganin yadda bai nuna yayi maraba da zuwanta ba ta ce


"Haba Sauban ko sannu da zuwa babu"


"Oooh sorry,sannu da zuwa"


Ƙara maida hankalinsa yayi ga abincinsa,sai can ya ce


"Hope kin gyara halin naki da nace ki gyara"


Kallonsa tayi da mamaki wai halinta,to ita wani hali take dashi da zata gyara mtsw! Sai kuma can ta ce


"Na gyara shikenan"


"Better"


"Wai Sauban wani irin wulaƙanci ne haka,jiba yadda kake amsamin magana babu kulawa haba"



Cak ya tsaya daga cin abinsa,sai ya ɗago yana kallonta ƙasa da sama a zuciyarshi yana cewa 'Wai me wannan take dashi da na dage sai na aureta,gashi babu abinda na mora sai wahala,damn it! ' katse mishi tunani tayi da cewa



"Ko zuwa gidanmu bikona bakayi ba,gashi ba kira a waya balle nasan ka damu dani,yanzu kuma na dawo ko maraba ba kayi da zuwana ba,wai miye haka,nima fa shegiyar kaina ce wallahi,bar ganin kana duka na ina ƙyaleka,kaci darajar son da nake maka ne wallahi"



Wannan karon miƙewa yayi yana mata wani shegen kallo irin na in kin isa,sai kuma ya saki ƙyayataccan murmushi yana kallonta kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya ce



"Darajar so huhhh!!! Kina sona ne kike zagin Mom ɗina? Kina sosa ne kike ƙin abinda nake so? Kina sona ne kike faɗamin baƙar magana,haka ake so a garinku? To bari kice gwara na sanar miki tun yanzu karki ce na munafin ce ki AURE ZAN ƘARA"



Darammm!!! Dammm!!! Darammmm!!! Tashin hankali wanda ba'asa mai rana,zuciyar Maryam ce ta tsinke lokaci guda,ƙwaƙwalwarta ta tafi hutun wucin gadi na wasu sakanni,kirjinta dukan tara-tara ya fara bama uku-uku ba,dafe ƙirjinta tayi da hannu bibbiyu tare da waro idanunta waje tana cewa


"Kishiya Sauban zakamin!!! "


"Ƙwarai kuwa Maryam"


Ai wani irin daka tsalle Maryam tayi,haɗe da cira gyalanta da ɗan kwalinta lokaci guda tana cewa cikin masifa da bala'i har idanunta sunyi ja



"Kan bura Uban can!!! Wallahi tallahi baka isa ba!!! Yau akwai bala'i a gidan nan!!! Yau akwai yaƙin duniya na uku a gidan nan!!!...............






Mu haɗu a pages na gaba don jin wannan Chakwakiyar chakwalkwalin da yake faruwa a gidan LOVE BIRDS wato🕊️🕊️🕊️ Sauban da Maryam😂😂😂😂✍️✍️✍️




*****shin su Umma Kande da Maman Jummalo sunyi nadama ko ko har yanzu akwai sauran rina a kaba???......







*****Shin mai yasa Dr Nabila take kyautatawa Sa'eeda sannan wasu abubuwa takeso ta tabbatar game da Sa'eeda???......




****shin Maryam zata yarda Sauban ya ƙara aure kuwa,ganin yadda ta haukace lokaci guda???......




Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥





Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments