TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Tsantsar so page 4

 *Ep_Four.*




_HAZEL POV_



Yau ma kamar kullum ta shirya tsaf cikin uniform nata na school tayi sallama da Granny ta fito domin tun sassafiya Mahaifinta wato Astrid David da ake sama laƙabi da Father kuma da yawan mutane haka suka sanshi a garin kuma ake kiransa, sakamakon shi ɗin Babba ne kuma wanda ake ji da shi cikin Babban church guda ɗaya tal dake Garin, yanzu haka ma can ya yi sammakon zuwa domin meeting suke yi na bikin Christmas da ya matso.




Tana tafiya kamar ko yaushe silently da ita littatafan ta rungume a chest ɗin ta ta karyo kwana ta shiga layin da kai tsaye zai sadata da school nasu da masarautar RAEES ke daura da ita masarauta ma girman gaske da ɗin bin tarihi.



Wani ƙaramin ɗan kwikwiyon kare ne da yazo wucewa ta sai tin ta ya ja hankalin ta.

Aikuwar da sauri ta ƙari sa wurin sa tare da tsugunawa ta ɗauke sa tana ƙare masa kallo. Saman laɓɓanta ta karanta harufan da aka rubuta jikin wani abu dake jikin doguwar sarƙe dake ɗaure a wuyan ƙaramin kwikwiyon.




"My H."



Ta karanta rubutun tana Miƙewa tsaye, waige waige ta fara ko zata hangi mamallkakin karen sai dai sakamakon yanayin garin da yake luf luf anyi ruwa mutane ɗay ɗay kune ke wucewa ta yankin.

Ta sauke ajiyar zuciya ganin bataga kowa ba, tana shafa kwikwiyon da ya lafe a hannunta lokaci kaɗan taji son kwikwiyon ya mamaye  ruhinta.


"My H, ni dai banga kowa ba, saboda haka na sama kwikwiyon daga yau Sunan ki little H."



Hazel ta faɗa tana kallon kwikwiyon cike da farin ciki dan ta fahimci mace ce. Gyara littatafan ta tayi sannan ta fara tafiya hannunta riƙe da kwikwiyon da tayi ma laƙabi da Little H.



Labib ya fito daga maɓoyarsa yana Murmushi.



"Yes tarkona ya kama, da alama tanason kwikwiyon sosai."



Ya faɗa tare da fara tafiya sauri sauri har ya cimma ta, suna jerawa tare bai kalleta ba ya ce.



"Am bakiji ba, wannan kwikwiyon nawa ne fitowa ta yi daga gida ban sani ba, na fito ina neman ta. Allah ya taimaka ashe kece kika gansa, na gode sosai bani ita mu koma gida kar sanyi ya ma ta illa."



Dam...! Shi ne sautin bugun da ƙirjin Hazel ya bada lokacin da ta gama jin abin da yake faɗa. Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka ta ce.



"Wayyo Dan uwa ka barmin mana please ina son ta sosai fa."



Ya yi Murmushin gefan fuska da bai bari ta lura ba, sannan ya ɗan tamke fuska ya ce.



"Akan me zan baki shi bayan ce miki nayi ita ɗin mallaki nane?."



"Am so sorry gata nan ka cinye idan ana ci."



Ta faɗa a fusace tare da cilla masa kwikwiyon jin yana ƙoƙarin buga ma ta tsawa abin da ba'a taɓa ba, duk tsawon zaman ta da kakarta Granny ko dungurinta bata taɓayi ba, balle uwa uba Father da ko kukan ta bai son ji. Duk soyayyar da take ma kwikwiyon ta haƙura akan dai ya yi ma ta tsawa.



Labib ya yi kasaƙe yana bin bayan ta da kallo hannunsa riƙe da kwikwiyon da ta wullo masa ya yi saurin cafewa.



"Tofa wai fushi tayi nan?."


Ya tambaya kansa, ganin babu mai basa amsa, yasa shi saurin ƙari sawa wurin ta har tayi nisa.



"Koda yake na lura kina son ta gata nan dake tafi dacewa."


Ya faɗa yana miƙa ma ta. Batayi fushi ba kamar yadda ya yi zato. Ta washe baki tare da Juyowa ta kallesa ita sai yanzu ma ganesa ashe Mutum jiya ne kuma ta lura yana yawan bin hanyar nan da take bi wurin zuwa school sannan suna yawan karo ba tare da sun sani ba.




"Da gaske na gode sosai kuwa."



Ta faɗa, tana yunƙurin karɓar kwikwiyon a hannunsa.



Ya ja baya da sauri. Ta zuba masa ivy eyes ɗin ta domin jin abin da zai ce.



"Kafin na baki karyata yana da kyau muyi Deal dake."



"Okay Tohm Ina sauraren ka."



Ta faɗa cike da ɗan ƙosawa.



"Koda yake zan faɗa miki Deal ɗin daga baya yanzu dai gata nan ki kulamin da My H kamar kwai idan wani abu ya same ta kamar ni ya sama ita ce ni, ni ne ita."



"Kaji dashi dai badai ka bani ita ba."


Ta faɗa ƙasan ranta, a fili kuwa cewa tayi.



"Tohm na gode."



Ta faɗa tare da karɓar kwikwiyon daga hannunsa.



Ya yi Murmushi.



"Zan shiga makaranta."



"Okay take care."


Tayi Murmushi kaɗan ba ta ce komai ba, ta shige ciki hannunta riƙe da kwikwiyon har ta ƙari sa izuwa class ɗin su S.S.3,A science yau ne Ranar da zasu zana Final paper na kammala school ɗin.




Fuskar sa ɗauke da murmushi sai da ya tabbatar da shigarta school ɗin sannan ya kara wayarsa a kunne bayan ya lalubo lambar Abokinsa Taufan ya danna kira.



Sallama ya yi bayan an yi picking, ya yi Shiru domin jin abin da zai faɗa ta ɗayan ɓangaren.



"Wai kana ina ne haka naji hayaniya?. Asibiti.! Okay na fahimta, idan ka dawo sai mu haɗu a can ɗin."



Ya katse kiran tare da nufar hanya ya bar wurin.




_____________

_Aaqilah POV_




"Daga ina kike haka jikin ki gaba ɗaya duk taɓo, faɗi kikayi a taɓon da girman ki, ina hijabin ki, ko haka kika fito ganɗai ganɗai dake babu ko lulluɓi?."



Mamanta ta jero ma ta tambayoyin lokaci guda tana tsareta da ido.




"Mtsww, wai Mama mai kika mayar dani ne Yarinya ko me, sannan Mene ne aibin shigata a haka, banason zafi shiyasa na fito haka sannan...."



Katseta tayi a fusace.



"Sannan me yanzu Tantirancin naki yakai ki kalla tsaban idona ina faɗa kina faɗa, lallai ne na fahimta, kiyi gaggautawar ficemin daga gida yanzu yanzu tun kafin raina ya fara ɓaci shashashar banza."



Mama ta faɗa a fusace daga ƙasan zuciyarta a karye take ayyana wa take.



Shikenan an gama ita an lalata ma ta rayuwar 'ya. Ji take bazata taɓa yafe wa Lami da Salame ba har abada domin sun cutar da ita.




"Wow dama wannan ranar nake jira ashe kin yarda ni Tantiriya ce, wai Aikuwa tantiranci salo salo zan fito da, sannan ki kwantar da hankalin ki zan fice Miki daga gida ba zama ya kawo ni ba, dama labari na samu bakyajin daɗi sai dai na lura ma kin warke zan tafi."



"Da yafi dai Umma ta gaida Aysha."



Aaqilah tayi Murmushin takaici tana juyawa daidai lokacin ita kuma Teema ta shigo gidan da sallama. Turus taja ta tsaya baki sake.





"Wannan kallon fa nifa banason gulma Mene ne ya faru har kin dawo daga Asibitin ne ya jikin nata?."



Aaqilah ta faɗa a dake tana zuba ma ta coals eyes nata da ɓacin rai ya fara rinar dasu.


"E, na dawo ne na faɗa ma Gidan Sarki abin yake faruwa, dama acan take, tana lafiya likita ya ce ba Babban abu ba ne kawai ta tsorata ne ta yi. Anty Aaqilah Mene ne yake faru ne wai, mai ya haɗaki da Mama nake jiyo muryoyin ku tun daga waje?."




"Ban sani ba gulma awiya kawai, abin da na tambaye ki daban amsar da kike bani daban, sannan ki shirya zanzo anjima ki rakani na ganta. Koda yake barshi ma na fasa sai gobe."



Ta faɗa ba tare da ta jira abin da Teema zata kuma faɗa ba ta raɓa ta gefanta ta fice daga gidan gaba ɗaya.




"Mama.."!



Teema ta kira Sunan Mahaifiyar nasu da tabi Ɗiyar tata Aaqilah da kallo tana ma ta fatan shiriya daga wannan murɗaɗɗen halin nata.



"Mene ne ya faru naji ta ce asibiti, kiyimin Bayani illa tayima wata ko me?."



Maman ta tambaya tana ɗan fito da ido da alama a tsorace take tun lokacin da aka ambaci asibiti.



"Mama ke nan, ba wani abu tayi ba, kawai akasi aka samu."


Teema ta faɗa sannan ta bawa Mahaifiyar tasu labarin duka abin da ya faru daga farko har zuwa yanzu. 


Mama taja salati cike da tarabbabi sai dai ta kasa faɗin komai.




______

_Aaqilah kuwa._



Da fitarta kai tsaye Gidan mahaifinta ta koma da Babu nisa sosai da gidan da Mahaifiyarta ke aure bai fi gidaje huɗu zuwa Biyar ba tsakani.



Hayaniya ce ke fitowa daga cikin gidan da alama mutanen gidan sun fara sana'ar tasu.




"Mtsww Baba dai ya mutu ya bar ma mutanen Duniya ala ƙaƙai ko menene yake faruwa kuma yanzu oho."



Ta ƙari sa zancen zucin tana shiga gidan. Karo taji tayi da mutum. Sai dai bata damu da sanin ko wanene ba tasa kai zata shata ta gabansa ta wuce.




"Ke daga gidan uban wa kike a haka babu ko mayafi?."



Ta kalle sa ɗere re sama da ƙasa kai tsaye ta basa amsa da.



"Daga gidan uban ka mana."



A fusace ya kai Hannu da niyya kifa ma ta mari. Ta tsaya ƙyam tana jira.



Inna Lami tayi saurin riƙo ta ta janyo ta tana faɗin.



"Haba Umaru wai Yaushe zaka dena biyewa wannan Yarinyar Aaqilah ne kullum naga zubar da girman ka, baka tsoron ta raina ka?."




A fusace ya juya ya kalle Mahaifiyar tasu ya ce.



"Haba Inna Lami kina ji dai zagina tayi ni ɗin sa'an tane ko me?."



Ya faɗa Muryarsa na kakkarwa da alama Ransa ya ɓaci sosai.




"Kayi haƙuri to, ke kuma Aaqilah ki dena kalan wannan ki basa haƙuri yanzu komai ya wuce."



Tayi Murmushin rainin wayo ta kalla Inna Lami ƙere re.



"Wai wannan abin zan bawa haƙurin never wallahi."



Ta faɗa tana gaba ta shige cikin Gidan tana watsawa Inna Sahura da ta dataka daga cacar baki da suke yi ita da Yaran gidan kamar sa'o'inta wata uwar harara mai cike da ma'anoni.




"Kizo ki zubamin waina ta idan kuma ta ƙare ne a ga Ruwan Bala'i, kai kuma kayi sauri kaje ka kaima wannan kucakar matar taka waina da ta aikoka amsa tun kafin ta biyo ka mijin ta ce kawai."




Huci Umaru yake tsaban takaici yasa kai ya fice daga gidan hannunsa riƙe da kular waina da aka zubawa matar sa.




"Aaqilah kinsan abin da kikeyi bai dace ba ko, ke fa Mace ce ki sani gidan wani zakije yana da kyau ki gyara hali tun kafin lokaci ya ƙure miki."




Aaqilah taja tsuka kaɗan shikenan kuma zata fara nasihar nata.



Inna Lami bata damu da ƙin kulata da Aaqilah tayi ba domin inda sabo ta saba ta ci gaba da ma ta nasiha akan rayuwa can ƙasan zuciyarta kuwa wani irin nadama ne na Rayuwar ta ta baya ta takeji, ta sani tana da saka hannu cikin halin da Aaqilah ta tsinci kanta a rayuwa sai dai yanzu tayi nadama ta ƙudurce a ranta zata tara kuɗi na cinikin wainar ta domin zuwa a karya baƙin Asiri da aka ma Aaqilah tun Ranar da ta fito Duniya....



Post a Comment

0 Comments