TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 1 & 2

 👬🏻 TAGWAYE 👭🏻



Episode One: The Bad Dream


Free episode


Bismillahir Rahmanir Rahim


Ina rokon ubangiji ya bani ikon gama littafin nan lafiya kamar yadda ya bani ikon fara shi lafiya. Ina kuma rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi, ya haneni ga rubuta sabo.


Ga masu bin rubutu na tun a Maimoon, zaku fahimci cewa a cikin wannan labarin mun koma can baya ne mun dauko wani zaren labari da muka ajiye, yanzu zamu jawo shi mu hade da sauran labarurrukan mu. We are going far back in time. Please bana son jin "a zamani kaza babu kaza da kaza" saboda ni ban fadi a wanne zamanin labarin ya faru ba. Babu littafi na dana rubuta shekara. Just read and understand.


We are going to look at life from the villain side of the story.


Let's be villains. Lol


ILYSM



Tafiya yake yi, yana jin jikinsa cikin yanayin tafiya amma kuma baya jin alamar ƙafafuwan sa suna taka kasa, jinsa yake yi tamkar wanda yake shawagi a sama, wannan yasa yayi saurin bude idanunsa da da suka kasance a rufe, idanuwansa suka sauka a kan fuskar ta. Yaji wani abu da baisan menene ba ya taba zuciyarsa a dai dai gurin da ba'a taba taba masa ba. Ya kura mata idanu yana son ya haddace dukkan kamannin ta a lokaci daya amma ya kasa, gashi dai yana kallon ta amma baya ganinta, so yake ta kalle shi ko yaya ne ya samu ya kalli cikin idonta amma taki kallon nasa. Wannan yasa ya bude muryarsa da niyyar yi mata magana ko Allah zai saka ta kalle shi koda kallo daya ne, ko da na second daya ne, ko yaya ne. 


Amma ga mamakin sa, maimakon yaji murya ta fito daga bakinsa kamar ko da yaushe in yayi magana sai yaji kuka ya fito, kuka mai dauke da sauti irin na jarirai.


Cikin mamaki ya sauke idonsa kan jikinsa, sai a lokacin ya fahimci dalilin da yasa yake jin kamar yawo yake yi a iska, yake jin yana tafiya amma baya taka kasa, ashe shi jariri ne, ashe a rungume yake a hannun wannan matar da ta taba can cikin zuciyar sa. Sai a lokacin ya fahimta, ashe mafarki yake yi.


Mafarki yake yi da mahaifiyar sa, abinda bai taba yi ba tunda yake a duniya, wannan fuskar da yake kalla amma ya kasa gani fuskar mahaifiyar sa ce. Wannan ya saka shi ya sake rudewa tare da sake dagewa wajan tattaro dukkan karfinsa dan ya yi mata magana ya samu ta kalle shi amma sai kokarin nasa ya kare a canyarewa da kukan jariri.


Ba tare data kalle shi ba ta saka hannu tana dan jijjiga shi kadan da niyyar rarrashi, fuskarta cike wani yanayi da yayi masa kama da tsoro, fargaba hadi da damuwa amma sam babu soyayya a fuskarta ko da ta digon alkalami. 


"Why?" 


Yayi kokarin tambayar ta a cikin muryar sa ta kukan jarirai. Wannan itace tambayar da yake da burin yi wa mahaifiyar sa a duk ranar da Allah ya hada su. 


"Me yasa ba kya so na me nayi miki?" 


Maimakon ta amsa masa sai yaga ta jawo bakin dankwalin ta da tayi amfani dashi gurin rikon sa ta rufe masa fuska dashi yadda ganin nata ma ya daina. Nan ya fara kusur kusur da harbe harbe irin na jarirai a ransa yana burin sake ganin fuskar ta. Har ya samu ya bude fuskarsa, sai ya kalli gurin da suke tafiya. 


Gefen titi ne, kuma daga dukkan alama cikin dare ne dan gurin yayi duhu sosai amma yana lura da bishiyoyin da suke wucewa alamar wajen gari ne. Sanyi yake ji yana ratsa jikinsa saboda kasancewar babu kaya a jikinsa sai dankwalin da ta rufe shi dashi.


Ya hango fitilar mota ta taho, sai yayi murna a ransa yana tunanin wani ne yazo zai taimaka musu sai dai ga mamakin sa sai yaga ta yi sauri ta buya a bayan wata bishiya, sannan ta saka hannu ta toshe masa baki dan hana kukansa fitowa, numfashin sa yaji yana kokarin daukewa saboda cikin rashin sani ta hada ta rufe har hancinsa wannan ya saka shi harbe harbe da kokarin kwace kansa amma bata cika shi ba har sai da motar ta wuce.


Data bude masa baki da hancin ko kallon fuskarsa bata yi ba...........


Gajiya da wahala ya saka ya kwanta lamo yana maida numfashi yayin da ita kuma ta cigaba da tafiya. Suddenly yaji ta tsaya. Ya kalli inda suka tsaya din sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi.


Ba zai taba manta gurin ba, dan shine inda ya fara kira da kalmar "home" a rayuwar sa. "Nigerian National Orphanage". Tsohon gate din gurin ne da kuma tsohon ginin. A hankali yaga tana bin jikin katangar dan kaucewa hasken fitilun da suke gurin, yayin da hannunta yake rufe a bakinsa. A dai dai kofar ta tsaya sannan without thinking twice ta durkusa ta ajiye shi a kasa. 


Tana ajiye shi ya dage da duk karfinsa yana kuka, yasan me take yi, amma ba wannan me damuwarsa ba, damuwarsa shine rabuwa da ita, rabuwa da dumin jikinta. Burinsa kawai a lokacin shine ta kalle shi, ko da sau daya ne, ko da second daya ne, ko yaya ne. 


Bata kalle shi ba bata taba shi tace "good bye" ba, asali ma hankalinta a tashe yake kar wani ya ganta, burinta shine tayi sauri ta bar gurin. Yana ji hannunta ya bar jikinsa and his heart went with it. 


Kuka yake sosai, kukan da bai taba sanin cewa ya taba yin irinsa ba sai yau. Sanyi yake ji, tsoro yake ji. Cikin kukan nasa ne yaji takun mutum, wannan yasa ya sassauta, a hankali fuskarta ta kuma bayyana a gare shi tana tsaye a kansa, wani irin dadi yaji a ransa wanda bai taba jin irin sa ba, ashe dai tana sonsa, ashe dai tace 


"good bye my son, ina sonka sosai zan rabu da kai ne kawai dan dole ba dan zuciya ta na so ba amma nayi maka alkawarin zan dawo gare ka" 


Wannan sune kalmomin da kullum yake gaya wa kansa a matsayin wanda mahaifiyarsa ta gaya masa sanda zata yar da shi.


Amma maimakon haka, sai yaga ta durkusa ta zare dankwalin ta data lullube shi dashi, sannan ba tare data kalle shi ba, ba tare data ce komai ba, ta ruga da gudu ta shige cikin bishiyoyi..........


Wani azababben sanyi yake ji, wani irin kuna zuciyarsa take yi. Tsakuyoyi da kasar gurin suna sukar fatar jikinsa. Sai a lokacin ya lura da ko cibiya bata yanke masa ba daga shi har mahaifar sa ta yar.


Kuka yake yi, kuka wanda zai ratsa zuciyar duk wanda zai ji shi a lokacin. 

Amma banda zuciyar wadda ta ajiye shi.

Banda zuciyar wadda yake ganin tafi kowa kusanci dashi a lokacin.

Wadda yake tunanin zata fi kowa son shi.

Mahaifiyar sa.


A firgice ya farka. Kukan jaririn ne ya farkar dashi, kukan sa. Ya tashi zaune gabaki daya jikinsa yana kakkarwa yana jin sanyi yana ratsa kasusuwansa tamkar yadda yaji a cikin mafarkin. Ya jawo gwuiwoyinsa zuwa kirjinsa sannan ya dora kansa akan gwiwarsa a hankali yana kiran sunan ubangiji har yaji nutsuwa ta fara zuwa masa sannan ya karanto addu'ar da annabi ya koyar cewa ayi idan anyi mummunan mafarki.


Lallai wannan mummunan mafarki ne, bai taba yin irin wannan mafarkin ba, irin mafarkin da zaka yi kaji tamkar gaske ne amma kuma kasan mafarki ne. Bai taba mafarki da mahaifiyar sa ba. Bai taba ko da tunanin ta irin haka ba. A cikin mafarkin fuskartar babu ko da digon sonsa ne, babu tausayinsa ko kadan. 


Kullum in tunanin iyayensa yazo masa yana consoling kansa ne da cewa dole ce ta raba su, suna sonsa amma babu yadda zasu yi shi yasa suka yar da shi amma wannan mafarkin ya goge wancan tunanin.


Ya mike yana taka lallausan kafet din dakinsa ya wuce zuwa toilet ya wanke fuskarsa da yake jin ta dauki zafi kamar mai zazzaɓi. Sai ya samu kansa da karewa kansa kallo a cikin mudubin gabansa. A hankali ya furta "Amir, mafarki kayi ba wai gaskiya ba ne ba" wani bari na zuciyarsa yace dashi "idan kuma ba mafarki bane ba memory ne fa?" 


Ya girgiza kan sa da sauri, it can't be a memory, ranar da aka haife shi ne, ta yaya zai samu memorin abinda ya faru ranar da aka haife shi? Ya shafa gashin fuskarsa da hannayensa biyu "this is crazy, it can't be" sannan ya lura cewa magana yake yi shi kadai.


Ya goge ruwan fuskarsa dana hannunsa a jikin towel sannan ya dawo cikin Bedroom din ya kalli agogo, karfe daya dai dai, ya rage ac ya koma kan gado ya kwanta. Maybe gobe yaje asibiti gurin Moon ta duba kwakwalwar sa, maybe ya fara tabuwa.



Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account 

GT Bank

Account Name : Nafisa Usman Tafida

Account Number : 0139433741


Sai su turo screenshot na transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin

08067081020


Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin

08067081020.


Sai na jiku....👬🏻 TAGWAYE 👭🏻



By



Maman Maama





Episode Two: The Beginning


Labarin ya samo tushen sa na farko ne daga wasu ma'aurata biyu, Alhaji Aminu da Hassana. Alhaji Aminu dan kasuwa ne kuma maaikacin gwamnati, yana kuma da dukiyarsa dai dai gwargwado. Asalinsa dan Gombe ne, zama da aiki ne ya kawo shi Kaduna inda anan ne tushen labarin yake. Matarsa Hassana ita ma ƴar Gombe ce, daga can ya auro ta ya taho da ita Kaduna, ganin cewa bata da kowa a Kaduna ya saka iyayenta suka hado ta tare da kanwarta Amina dan ta ke debe mata kewar gida kuma take tayata yan aiyuka. 


Amina a lokacin tana da shekaru goma sha biyar. Dan haka suna zuwa Kaduna aka saka ta a makaranta dan ta cigaba da karatunta, kuma yayarta da Alhaji Aminu suka rike ta sosai. Shekara biyu da auren Alhaji Aminu da Hassana sai Allah ya bata ciki, ciki mai cike da tarin laulayi tare da tarin girma. Inda tun a awon farko aka tabbatar wa Hassana da cewa tana dauke da tagwaye. Hakan ya saka su cikin matsanancin farin ciki duk kuwa da cewa dama suna saka ran hakan saboda kasancewar Hassana tana da abokiyar tagwaitaka ya saka chances dinta na haihuwar tagwaye ya zama yana da yawa.


Ganin wahalar da cikin yake bata ya saka mahaifanta suka nemi su tafi da ita gida ta haihu a can amma son da Aminu yake yi mata ita da cikin yasa ya kasa barinsu su tafi ya nemi a bar masa matarsa shi zai ke kula da ita da kansa. Aka bar masa ita, ya kula da ita tamkar sabon kwai, har lokacin haihuwar ta yayi. 


Da farko sanda ta fara nakuda likitoci sun dauka zata iya haihuwa da kanta, sai data yi awanni babu wani progress sannan aka fara shawarar yi mata aiki dan gudun samun matsala. Sai da aka gama shirya ta tsaf sannan kuma sai jini ya balle mata, a haka akayi mata cs aka fitar da tagwayen maza, masu kama daya, sai dai daya ya dauko fatar babansa "baƙi" dayan kuma yayo fatar Hassana "fari".


Bayan an dawo da ita dakin hutawa ne ta farfado aka saka mata jariran a hannayenta biyu, Hassan a hannun dama, Hussain a hannun hagu. Ta rungume su a jikinta, a haka Allah ya dauki ranta. Fadar bakin cikin Aminu tamkar bata lokaci ne, dan mutane har sun fara tunanin ko zai bita ne, amma sai soyayyar yayansa ta danne bakin cikin rashin matarsa. 


Da farko anyi niyyar karbar yaran daga hannunsa a tafi dasu Gombe gurin kakannin su amma Aminu yace sam babu mai raba shi da yaransa. Wannan yasa bayan dan gajeren zama tsakanin iyayensa dana Hassana aka yanke shawarar aura masa Amina. A gurin aka biya sadakin aka kuma daura auren. Bayan dan karamin biki a Gombe aka dawo da amarya kaduna gidan mijinta tare da tagwayen ƴaƴan ta.


Da farko Amina ta dauki auren ta tamkar wasan yara dan ita babu komai tsakanin ta da Alhaji Aminu bayan mutunta juna, ganinsa take tamkar yayanta da suka fito ciki daya. Abinda yake gabanta kawai shine karatunta da kuma marayun da aka bar mata wadanda ta dauki son duniya ta dora akan su, dan har ba'a iya banbance wanda yafi son yayan a tsakanin ta da Alhaji Aminu wanda kullum a jikinsa suke bacci.


An samo mata matar da zata ke tayata kula da yaran saboda lura da karancin shekarun ta da kuma makarantar da take zuwa, amma fa tana dawowa zata karbo yayanta. Ranar nan bayan ta dawo daga school ta samu mai renon tace "Baba Yaha Dan Allah ko kinsan maganin da za'a sha ruwan nono ya zo?" Baba Yaha ta kalle ta da mamaki tace "me zaki yi da ruwan nono Amina?" Tace "a makaranta an gaya mana irin amfanin nonon uwa agurin jarirai, yaran nan nake tausayi, su basu samu wannan alfanun ba tunda kinga madara suke sha. Shine nake so in samu magani insha sai inke basu nawa" baba Yaha ta jinjina irin soyayyar da Amina take yiwa yaran sannan tace "to wannan dai ba magana ta bace ba, kije ki samu mijinki kuyi shawara a tsakanin ku, in ya amince shikenan sai in samo miki, amma in bai yarda ba dole ki hakura. Dan haka sai ki lallaba shi".


Da wannan Yaha ta kashe maganar, dan a lokacin babu yadda za'a yi Amina ta samu Alhaji Aminu da magana makamanciyar wannan saboda sam basa irin wannan da shi, ko wasa ma basa yi saboda shi ba mutum ne mai son wasa ba.



Amma tsakanin mata da miji hausawa suka ce sai Allah. Tagwayen suna da shekara biyar a duniya sai ga Amina da ciki. Ai kuwa ranar da tagwayen suka fara lura da cikin a jikinta suka sakataa gaba da jerin tambayoyi har sai da ta gaya musu cewa baby ne a cikin, baby zata haifa musu watarana. Nan suka fara tsalle a saman gadonta suna adungure zuwa kasa. Alhassan yace "Please, Please aunty ki haifa mana namiji dan muke wasa tare" Alhussain yature shi yace "me za'ayi da namiji, anyi ta haihuwar mazan kenan? Mace zata haifa mana shikenan na samu budurwa" nan sai fada, harda kokawa, sai da kyar ta raba bayan sun gama doddoke ta. Sannan ta zauna tana dariyar sokonci irin na Hussain, ko ta yaya yar da zata haifa zata zama budurwar shi? 


Haka yake shi Hussain, akwai surutu, akwai fitina, akwai karambani kuma akwai kokari a makaranta. Shi kuma Hassan shine mai wayo, manyance, da zarar magana. In yayi wani abin zata ce yafi karfin shekarunsa, komai sai ya nuna kamar ma ya fika iyawa kuma ba wai iyawar yayi ba. Komai na shi careful yake yinsa, in dai taga anyi barna to tasan Hussain ne, shi ko abinci kika bashi daga kitchen ya kawo daki to sai ya zubar a hanya.


Hussain ne yayi nasarar wannan musun nasu. Dan mace ta haifa wadda aka mayar mata da sunan Hassana kuma ake ce mata Hassana ɗin. Daga ita kuma sai ta haifi Safiyya, Khadijah, Nafisa, sannan Zulaihat. Duk kusan a jejjere tayi su. Daga nan kuma sai ta dakata tukuna tace sai sun girma zata sake wani set din. 


Amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi. 


A shekarar da tagwayen suka gama secondary school dinsu a shekarar ne Allah yayi wa Alhaji Aminu rasuwa bayan yar gajeriyar jinya. Ya mutu ya bar mata daya da yaya bakwai. Maza biyu mata biyar.


Wannan mutuwa ta taba ba wai family dinsa ba har wadanda suka sanshi da sauran abokan aikinsa kowa sai da ya koka kuma ya tausayawa iyalinsa, kasancewar su kanana babu wanda za'a ce ya rike kansa ballantana ya rike yan uwansa, ita kanta uwar ba wasu shekarun kirki ne da ita ba. 


Bayan anyi arba'in sai yan'uwa suka nemi su koma Gombe su zauna a cikin dangi. Hussain ya shafawa fuskarsa toka ya ce babu inda zasu je "yanzu yaran nan sai a cire su daga makarantun su kenan? So kuke yi mu koma can a fara yi mana dauki dai dai? Wannan uncle din ya dauki uku wancan ya dauki biyu wannan auntyn ta dauki daya?" 


Aunty Amina ta share hawayenta, dama Hussain shi take tunani, tasan shi da rigima, tasan shi zai bata problem, tace "to Hussain ya kake so muyi? Eh? Ya kake so inyi da raina? In bamu koma Gombe ba ina zamu je? Wa zai rike mu? Ni dai kasan ba zan iya ba, kasan ba aiki nake yi ba ba sana'a nake yi ba, kasan kuma ba dogon karatu nayi ba ballantana in saka ran zan samu aikin da zan rike ku dashi. Ku kuma baku kawo karfi ba tukunna, kuma mai taimaka muku kuke bukata a yanzu, kuna bukatar wanda zai shige muku gaba ku cigaba da karatun ku. Yan uwanku yaya zakuyi dasu? Duk fa primary suke Hassana ce kawai take ajin farko a secondary. Hussain dole muna bukatar taimako, ba kuma zamu samu taimakon nan anan ba sai mun koma cikin yanuwanmu".


Ya mike tsaye yana girgiza kai yace "duk wanda yake bukatar taimaka mana a cikin yanuwanmu ai zai iya taimaka mana muna zaune anan. Kuma ma ai bama bukatar taimakon kowa aunty. Mu, ni da Hassan zamu rike kan mu zamu rike ku" Hassan ya mike yana kallon sa yace "ta yaya? Ta yaya zamu rike kan mu Hussain? Gaya min me muke dashi? Ko da karambani zamu rike kan namu? Ana maganar reality ne fa anan, ana maganar future din mu ne data yaran nan kannen mu" Hussain yace "in ba zaka iya ba kawai kace ba zaka iya ba ba sai kayi min dogon sharhi ba" ya wuce shi ya dawo gaban Amina. "Aunty ki yarda dani dan Allah. Wallahi zan iya" tayi ajjiyar zuciya tace "zaka iya? Ta yaya?" Ya zauna a kan kafafuwansa yace "kasuwanci zan shiga, ba da akwai kudade a hannun mu ba? da akwai wasu a bank? Ga kuma motoci har guda uku a waje? Kuma ga filayen da Abba ya siya ya ajiye? Mu siyar dasu ku bani kudin in shiga business dasu.........." 


Hassan ya dawo kusa da Aunty da sauri yace "hauka ma kenan. Yanzu in business din zamuyi Hussain sai mu dauki dukiya mu baka? Kai din? In ka lalata ta kuma shikenan sai mu dawo mu zuba tagumi? Gaba ake dubawa Hussain. Komai a hankali a kuma nutse ake binsa, kullum sai na gaya maka wannan amma kai baka ji" 


Hussain yayi masa kallo daya ya dawo da dubansa kan Aunty yace "Please Aunty, ki bani wannan damar dan Allah. Wallahi zan iya, ki rabu da Hassan. Shi yana living ne in the future ni kuma ina living now, in dama tazo wa mutum kawai yayi amfani da ita ba sai ya jira wata damar tazo sanda yayi masa dai dai ba.


Yanzu ne damar mu Aunty, ki bani wannan damar dan Allah.


Aunty ta jima tana kallon sa, tasan halinsa sarai, tasan karambanin sa da daukan abinda yafi karfinsa ya dora wa kansa, tasan kuma kokarin sa dan duk sanda ya fadi baya zama a kasa yayi kuka mikewa yake yi ya cigaba da tafiya. Duk abinda yake bashi wahala kuma sai yayi ta maimaita wa har sai ya iya.


Ta tuna farkon sanda aka siyo musu kekuna, ana kawowa Hussain ya dauka ya hau ai kuwa ya fado ya kukkurje, amma bai hakura ba, yayi ta hawa keken nan yana faduwa har sai da ta dauke saboda tausayin sa sai babansu yace ta bar masa ai a haka ake girma. Hassan kuwa sai yayi ta studying keken nan yana gwada yadda komai nasa yake aiki har sai da ya fahimce shi sannan ya hau, shima kuma a hankali yadda ko ya fadi ba zaiji ciwo ba, kuma bai fadin ba, sai yake tukawa a hankali yadda in yaga zai fadi sai yayi sauri ya sauka, ko kuma yake bin jikin bango yana dafawa. 


A karshe sai ya zamanto Hussain ya riga Hassan iya keke, amma kuma duk ya ci uban keken nasa ya babballashi. Sanda Hassan ya iya nasa keken, keken Hussain ya riga ya lalace. 


Amma kuma akwai wani abu a dangane da Hussain tun yana yaro, yana balain, tsananin son sana'a. Duk wani abu indai ance abinda zai kawo kudi ne to Hussain ya sanshi kuma yana sonshi. Hussain har fruits din bishiyar umbrella din gidansu yake cira ya siyar wa da yaran unguwa. Hussain in yaje da abu makaranta wani yaron yace yana so yakan iya siyar masa ya kara riba sannan ya fito waje ya sai wani. Amma fa kudin in ya samu rabarwa mutane yake yi. 


Ta tuna wata rana da ya dawo daga school da ulu da kwarashi, ta tambaye shi inda ya samu sai yace "Nanny din mu ta makaranta na gani tana saƙa, tace min ana samun kudi sosai in akayi saƙa, shine na bata kudi ta siyomin zan ringa yin saƙar hula ina bata tana siyar min" sai da baban su ya zane shi akan sakar nan sannan ya daina.


Babansu ya taba tambayar su abinda zasu zama in sun girma. Hassan yayi shiru yana tunani sannan yace "ban sani ba Abba, sai nan gaba in nayi tunani" ana tambayar Hussain sai ya washe baki yace "Dangote".


Ta dawo da tunaninta kansa da har yanzu yake durkushe a gabanta yana roko, ya kamata ta bashi dama, amma ya kamata tayi tunani, saboda kamar yadda Hassan ya fada wannan future dinsu ne basu kadai ba harda yan kananan yaranta mata. Dole zata yi tunani kafin tayi taking wannan risk din kuma dole zata yi shawara. Shawara da abokin shawarar ta sarkin tunani. Hassan.


Tace "shikenan Hussain ka bani lokaci inyi tunani, duk abinda na yanke kuma shine final babu jayayya" 


Ba haka yaso ba, amma yadda take so dole hakan za'ayi.


Bayan ya fita sai ta juyo ta kalli Hassan, a take ya girgiza mata kai. 

Ta sauke ajjiyar zuciya tace "bana son discouraging dinsa, ka bani shawara yaya zanyi?" 

Ya gyara zama yana kallon carpet yace "dukiyar marayu ce aunty, ina ji masa tsoro, kinsan halin Hussain in ya kafa kasuwancin ma raba wa mutane zai tayi" Ta gyada kai cikin fahimta, ya cigaba da cewa "a shawarce ina ganin a raba, a fitar masa da kasonsa a bashi ya kafa kasuwancin dashi yadda ko sun rushe ba zai rusa mu gabaki daya ba, mu dashi zamu samu abinda zamu dogara dashi. Idan kuma ya zama successful sai a kara masa wata"


Aunty taji dadin wannan shawarar, amma kuma a ranta bata son rabon gadon nan saboda tana ganin kamar raba kan ƴaƴanta ne, taso a ce komai zasuyi tare zasuyi. Amma kuma shawarar abar dubawa ce.


Haka akayi, aka raba gado aka bawa Hussain nasa, sauran kuma suka ajiye suna amfani dashi gurin harkokin rayuwarsu. Hassan yayi amfani da wani kaso a cikin nasa gurin nema wa kansa makaranta.


A lokacin da shekara ta zagayo Hussain ya kira su yana nuna musu lissafin abubuwan da yayi da kudin da ya samu sai su ka ga cewa kudin da yake dashi a yanzu ya ninka wanda yake dasu a waccan shekarar sau huɗu har da doriya. Suka rike baki suna mamaki, shi kuma ya gyara zama yana murmushi yace "na gaya muku ai, Dangote zan zama"


Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account 

GT Bank

Account Name : Nafisa Usman Tafida

Account Number : 0139433741


Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin

08067081020

 

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin

08067081020.


Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only


Sai na jiku....👬🏻 TAGWAYE 👭🏻



By



Maman Maama

Post a Comment

0 Comments