TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina yajawo mini Page 11 -- 12

 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️

                           


  Narrnarhh Bukar✍️


 🌹Perfect Essential Writer's

Association🌹

  ✨ P. E. W. A✨



Wattpad:@AISHAABUBAKAR812

Arewabook:@Narrnarhh002




1⃣1⃣----1⃣2⃣


UK


Ɓangaren Sadam autan Mom karatu ya soma zafi gashi Dad  ya hanashi zuwa Nigeria sai ya kammala degree ɗinsa complete sannan ya dawo bautar ƙasa na shekara ɗaya.


Kana ya ƙara tafiya China don yin Masters ɗinsa don ƙara sanin harkar kasuwanci,sosai hakan bai masa daɗi ba,yaso tafiya hutunsa na farko wurin sister ɗinsa Aunty Sadiya wacca a da take Pakistan kafin yanzu su dawo India da zama saboda yanayin aikin mijinta,haka dai ya haƙura da zuwa ko'ina ya ƙara maida hankalinsa kacokan a karatunsa.


Sadam miskili ne na ajin ƙarshe don yanzo miskilancin nasama ƙaruwa yayi saboda ganinsa a wata ƙasar,ƴan mata tun daga kan  turawa da na baƙaƙen fata suna son ya kulasu saboda classy guy ne haɗadɗe ga girman jiki wanda idan ka gansa zakayi tunanin ɗan shekara 30 saboda ya aje ƙasumba sosai.


Yanada aboki guda ɗaya ɗan Nigeria amma shi ɗan kaduna ne mai suna Sadiq,kusan halinsu ɗaya shiyasa abotar tasu tazo ɗaya,duk da course ɗinsu ba ɗaya bane,shi Sadiq yana karantar ɓangaren Computer Engineering ne,hakan baisa abotar tasu ta lalace ba, kowan nansu yana ziyartar ɗan uwansa duk da faculty nasu ba ɗaya bane  amma haka suke abotar tasu,har takai yanzu iyanyansu sun san da abotar tasu.


Haka Sadam ya cigaba da karatunsa a UK don cika burin mahaifinsa akansa kasancewarsa ɗa ɗaya wurin mahaifinsa ,gashi mahaifinsa ya soma tsufa duk yayyinsa mata ne saboda haka dole ya jajirce sosai akan karatunsa dan nan gaba harkar kasuwancin mahaifinsu da kamfanoninsa duk zasu dawo hannunsa ,shiyasa yake jajircewa sosai.Wannan kenan


        @@@@@@@@@@@@@


KADUNA


Bayan sallah hutun su Sa'eeda ya ƙare,sai suka koma makaranta don cigaba da karatu.Sosai Sa'eeda take mai da hankalinta akan karatunta a bangare ɗaya kuma tana koyawa Maryam inda bata gane ba kasancewarta very slow learner ce duk da tana da lesson teacher a gida amma haƙarta bata cimma ruwa ba,gashi koda yaushe Mum ɗinta cikin zigata take akan Sa'eeda hakan yasa take ƙara shige ma Sa'eedan jiki sosai,ita ko Sa'eeda da zuciya ɗaya take tare da Maryam.


Haka suka kammala SS2 cikin nasara da aminci wanda a lokacin Sa'eeda ta samu matsala da ƴan ajinsu saboda shugabancin ɗalibai da aka bata wato Head girl,haƙiƙa ta fuskanci tsana da barazana akan sai ta sauka daga Head girl ɗin don a ganin ƴan aji ƴar talaka bata cancanta da wannan muƙami ba sai dai ƴaƴan masu kuɗi irinsu,da ƙyar abubuwa suka lafa daga baya ƴan aji suka yarda duk da wasu basa sonta da Head girl ɗin.


           @@@@@@@@@@@@@


Sun shiga SS3 wanda  kowanni ɗalibi na shirya shiryen zana jabawan waec,neco da jamb ,hakan ta faru ga Sa'eeda don Ummanta ta shiga adashe har kala biyu duk don karatun ɗiyarta  bancin savings ɗin kuɗi da take yi a account tun daga #100,000 wanda Sa'eeda ta samu lokacin saukarta har da adashen da take kwasa tana saving ɗinsu duk don karatun ƴarta ta,koda yaushe tana samun wankin kayan mutane duk da ma Sa'eeda na tayata sosai da yake Sa'eeda ba raguwa bace akwai son aiki,wani lokacin ma cema maman take ta bari ita zatayi duk don su rufama kansu asiri tunda Abbanta an mallakeshi,sai yadda akayi dashi a gidan.


Wasa wasa su Sa'eeda sun fara shirin zana exams ɗinsu na ƙarshe,sun fara rubuta Jamb wanda within 1week sakamakon su ya fito.


Alhamdulillah yawancin ɗaliban makarantar sun samu nasarar wuce cut of mark na jamb har da su Maryam don ta dage akan sai ta wuce Sa'eeda a score. (Haba Hajiya Maryam na gaba yayi gaba,sai dai a nema wani sarkin dan ko Sa'eeda tayi zarrah😂😂😂).


Sa'eeda tafi kowa marking a school ɗin har ma tawuce 270 a Jamb ɗinta, da wannan score ɗin ba ƙaramin ƙarama kanta baƙin painti  yayi ba a idon ƴan ajinsu,hakan bai dameta ba don  basa gabanta.


Bayan sun kammala jamb sai  suka zana waec da neco sai bayan wasu watanni waec da neco ɗinsu suka fito shima sakamakonsu yayi kyau sosai ,haka Sa'eeda da Maryam sukayi applying post utme a Kasu kasancewar shi suka sa a Jamb ɗinsu sai lokacin screening yayi  suka tafi wanda cikin hukuncin Ubangiji duk suka tsallake har aka basu admission a Business Administration 100L.wannan kenan


       @@@@@@@@@@@@@@@


Bangaren su Umma Kande liyafa ta cigaba don yanzu haka an canja tsarin gidan nasu,anyi painting gidan baki ɗaya sannan aka siminta gidan ya fito kamar sabo,duk wannan aikin ba na kowa bane sai na Nusaiba wacca yanzu ta zama karuwar kanta ,bata cika zama a garin ba yanzu,bata waccan state ɗin bata waccan.


Duk wannan abun da take yi bai damu Umma Kande ba,duk da ansha kawo mata gulmar layi akan maza take bi kuma tana luwaɗi amma sai ta ce ana ma ƴarta sharri da baƙin ciki don anga tanada farin jinin samari.Ƴan layi sunyi gulmar har sun saka ido don har mazan layi sukan tun kari Abbansu Sa'eeda da magana akan abinda yaransa sukeyi amma sai yace baisan yanda zaiyi da uwarsu ba koya mata magana ba amsa shi zatayi ba,gashi baida ikon yima yaran faɗa zata hayayyaƙo mai da masifa akan ya tsana yaranta,ko kuma tace yana bin zugar  mazan layi,babu yanda ya iya sai dai ya zuba ido.


         @@@@@@@@@@@@@ 


Umma Kande ce da Maman Jummalo zaune a ɗakin Umma Kande sun baje pepper soup din kaza suna ci haɗe da gwangwanin maltinarsu mai sanyi suna ci suna  ƴar hirarsu cike da annashuwa.


Maman Jummalo ce ta sauya hirar tasu zuwa magana mai muhimmanci game  da yaransu don ita gaskiya tafi son suyi aure akan wannan tara samarin da sukeyi gashi idan suka fita waje aita zunɗansu akan sun bar yaransu babu aure sai tara samari a layi.

Gyara zama tayi sannan tace "Ni kuwa ƙawas nazo da wata shawara akan yaran nan " 


Umma Kande dake gwaguyar ƙashin cinyar kaza ta ajiye sannan ta baida hankalinta sosai ga Maman Jummalo sai ta ce "Ina jikin ƙawas hala wani alkwairi ne ya ƙara samuwa"


Maman Jummalo tace "Kinga yaran nan duk Allah ya basu samari masu kuɗi sosai gashi shekarunsu ƙara yawa yake ba raguwa ba,shi ne wani tunani ya zomin akan mai zai hana muce musu su fidda samarin da suke so ayi musu aure don gaskiya hankanlin mu zaifi kwanciya kuma zamu hutu da gulmar ƴan layi,ko ya kikace ƙawas?


Ɗan shiru Umma Kande tayi tana nazari don  maganar ƙawarta na kan hanya gwara suyi aure suma su hutu da zunɗen ƴan layi da ba dama su fita sai an nunasu da yaransu,ɗan lunfasawa tayi sannan tace " Maganarki dutse ƙawas, to yanzu ya kike ganin zamu ce da su,don kinga na farin jinin  samari masu kuɗi kawai muka amso musu banda na aure,kinga koda mun musu maganar aure samarin ba fitowa za suyi  ba"


"Hakane ƙawas, to yanzu menene mafita" cewa Maman Jummalo


"Mafitar ɗaya ce,sai dai mu sake komawa gun boka Sankeru akan maganar auran nasu,ko ya kikace"


"Tafiyarmu wurin boka Sankeru wajibi ne gaskiya,gwara suyi auran mu huta"


Umma Kande dake matsar da tiran pepper soup ɗin ta ɗora da cewa "Yaushe kike ganin zamu je wurin boka Sankeru ɗin"


"Mu shirya ranar alhamis tunda baya son ana zuwa ranar jumma'a da litinin sai dai lahadi da alhamis" cewar Maman Jummalo


"Na tuna kuwa,Allah ya kaimu"


Da "Ameen " Maman Jummalo ta bita dashi.


Can kuma suna zaune sai Umma Kande tace"Ƙawas ba kiga waccan mayyar yarinyar mai kama da aljanu sai ƙara kyau take yi ba,kamar basa cikin wahala"


"Abinda ke raina kenan kika rigani fada wallahi,nima hakan na damuna,tsorona kar tazo tafi yaranmu samari masu kuɗi tunda kinga duk tafisu kyau sai kace ƴar india,ke nifa tunani nake anya ƴan ƙasar nan ne kuwa" cewa Maman Jummalo


Umma Kande ta ɗan sauke gauran ajiyar zuciya tace "Bari ke dai,ina ganin tafiyar mu wurin boka Sankeru zai zama biyu har da maganar Sa'eeda don gaskiya baza mu bari tafi ƴaƴanmu ba wallah"


"Sosai ma kuwa dole musan abunyi tun kafin wankin hula ya kaimu dare,don naga alama tanada farin jinin samari sai dai kamar bata kulasu" cewa Maman Jummalo


"Wannan haka yake kar kuma ta samo wanda yafi na yaranmu kinga gwara muyiwa tufkar hanci " 


"Haka ne kuwa,Allah dai ya kaimu alhamis musan abunyi kuwa" cewar Maman Jummalo


Hamma Umma Kande tayi tare da cewa "Ameem dai ƙawas,kinga mun jefi tsuntu biyu da dutse ɗaya"


"Hakane kam".


          @@@@@@@@@@@@@


Kamar yanda suka shirya ,yau take alhamis tun daran alhamis suka kammala shiri tsaf don da sassafe zasu tafi.Da sassafe suka nufi tasha acan suka hau motar da zata kaisu ƙauyen,bayan sun sauka ne suka hau machine ɗaya kasancewar ƙauyen ba'a cika samun abin hawa ba,kamar yanda suka je waccan zuwan a gefan dajin mai machine ya sauke su suka ƙarasa da tafiya har zuwa bukkar boka Sankeru.


Bayan sunzo kusa da bukkar sai suka cire takalmansu kamar wancan zuwan,sai suka juya suna tafiya ba baya da baya har cikin bukkar. (Ni kuma na saka nose mask ɗina saboda tsaro,kar a samu matsala wurin ɗaukar rahoto😷😷😷).


Isarsu cikin bukkar keda wuya suka zube a ƙasa tare da yima boka Sankeru kiraki duk da ba kowa a cikin bukkar suna cewa"Sakeru namu Sankeru na duk mai son ya dace,Shugaban matsubban duniya, Ka cire tuta,Kowa na bayanka, gamu yau munzo da ƙoƙon bararmu gareka mai sha re kukanmu"


Tunda suka fara kirari bishiyoyin nan dake zakaye da bukkar suka fara jijjiga ga warin nan ya soma tashi ,kamar walkiya sai ga boka Sankeru a gabansu zindir haihuwar uwarsa,yana bayyana agabansu sai ya bushe da dariya timbinsa na jijjiga kamar wani alade,sai da yayi mai isarsa kana ya tsagaita.


Dubansu yayi da kyau sannan ya fara maganar cike da amon murya "Nasan zaku dawo,dole sai kun dawo don kammaluwan aikinku hehehe! " kamar an tsikareshi zumbur ya miƙe ya soma tiƙar rawa kamar wani alade.


Su dai su Umma Kande kansu a ƙasa,sai da yayi mai isarsa sannan ya ɗora da cewa"Zancen ku na biyu gane da yarinyar kishiyarki" yana nuna Umma Kande yace"Hmmmmmmmmm bayanku akwai wasu da suke da halin irin naku akan yarinyar da mamanta"


Da sauri Umma Kande ta ɗago idanunta.....................


Tofa ƙaƙa ƙara ƙaƙa,kenan su Sa'eeda da Ummanta sunada wasu maƙiyan a ɓoye bayansu Umma Kande 🤔🤔🤔 ko suwaye.. ....???

Muje dai zuwa✍️✍️✍️


Daga alk'alamin 


🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.

Post a Comment

0 Comments