TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 33-34

 3⃣3⃣----3⃣4⃣







Ɓangaren Umma Kande ita da Maman Jummalo komai na tafiya musu normal,kamar kullum yau ma suna zaune a kan tabarma suna hirarsu cike da annashuwa kawai sukaga mutum ya faɗo cikin gidan babu sallama, haba da sauri suka miƙe dukansu,cikin tashin hankali Maman Jummalo tace




"Ni Hasfy wazan gani haka babu ɗan kwali balle hijabi,meya sameki Jummalo? "



Wuri-wuri takeyi da idanunta kamar wata motsattsa,gata tayi baƙi sosai kasancewar bleaching take,yanzu babu kwanciyar hankali balle a shafa cream😀.Maman jummalo ce ta riƙo hannun Jummalo da sauri Jummalo ta fizge hannunta tana ja da baya tare da  girgiza kai hawaye na zuba a bisa kuncinta   ta ce



"A'a! A'a! Karki taɓani mama,wallahi nayi da nasanin zamowarki uwa a gareni,baki bani tarbiyya mai kyau ba,kin ɗorani akan turbar son abin duniya da dogon buri,gashi tun a daren farkona naaa........."



Bata ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa ba Umma Kande tayi saurin rufe mata baki,ita kuma Maman Jummalo ta jata ɗaki har uwar ɗaka tare da rufo ƙofar har da jan labulan windo don kar ajisu,suna shiga ɗakin Jummalo ta ƙara fizge hannunta daga hannun Maman Jummalo don yanzu ta ɗau ma kanta alƙawarin baza da sake biye musu  sukaita ga halaka,zama Jummalo tayi akan gado su kuma suka zauna kusa da ita duk hankalinsu a tashe.Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka harda shassheƙa,bata jira mai zasu ce ba tara magana cikin shassheƙan kuka mai ratsa zuciya



"Nayi nadama tafi dubu,nayi da nasani tafi cikin kwando,kaicona da biyewa ruɗin duniya,Mama kin cuce rayuwata,kin cuceni Mama,baki bani tarbiyya mai kyau ba,Allah sarki babaaaa naaaaa!!!........."



Ƙara sakin wani sabon kukan tayi mai ƙarfin gaske,Umma Kande ce tace ta rage sautin muryarta kar ajisu,galla mata harar tayi sannan ta cigaba da maganarta,ita dai Maman Jummalo  kallon ƴarta take babu ko ƙiftawa saboda muguwar ramar da tayi,ga wani mugun baƙi da tayi kamar baƙin tukunya.




"Tun ranar da aka kaini gidan aurena,a ranar na fara fuskantar baƙin ciki da tsangwama,ga duka,zagi,tozarci,aikin wahala duk babu wanda bangani ba a zaman aurena,kullum cikin baƙin ciki da da nasani nake akan biye muku,Allah ne yanzu ya kuɓutar dani,kuma daga yau bazan sake biye muku ba sannan su Zaliha da Iklima ku gaggauta zuwa ɗaukosu saboda nasan suna cikin halin dana tsinci kaina a ciki,kuma ku jini dakyau wallahi na daina biye muku ,sannan Islamiya zan koma in shaa Allah"




Miƙewa tayi ba tare da ta kallesu ba ta fito falon ta ɗau buta don zagayawa,su kuma  su Umma Kande binta sukayi da kallo,sai can Umma Kande ta fara magana cike da damuwa




"Mun shiga uku ƙawas,anya ba zuwa zamuyi muga halin da su Zaliha suke ciki ba"




"Hmmmmm ni nama kasa magana wallahi don bansan me zance ba Ƙawas,kinsan me kawai gobe da sassafe mu shirya muje gidan nasu,inta kama ɗaukosu zamuyi kawai mu ɗaukosu,ji yadda Jummalo ta kuma don Allah"




"Allah ya kaimu,a gaskiya hankalina yayi ƙololuwan tashi ganin Jummalo a irin wannan hali,amma a gaskiya boka Sankeru bai mana adalci ba,ai ba haka mukayi dashi ba,daga munce munason yaranmu su samu mazaje masu kuɗi kawai zai haɗasu da bala'i,kai kai kai ni Saratu jikar sarkin ruwa munga takanmu"




Haka sukaita jimamin abinda ya samu yaransu,Jummalo kuwa zama tayi ta basu labarin tun daga daren auranta har zuwa yau da wuya tasata barin gidan afujajan babu ɗan kwali balle hijab.Umma Kande ta shiga tashin hankali tare da zullumin su Zaliha da Iklima ko a wani hali su kuma suke ciki da mazajen nasu,idan ita Jummalo mai shan giya ne mijinta su kuma fa gashi daman suna son saka ranar zuwa gidan kowaccansu saboda basu taba zuwa ba,sai gashi kan susa ranar zuwa Jummalo tazo musu da labarin da ya kirkita musu ƙwaƙwalwa tare da lissafi.





          @ @@@@ @@@@ @@@@




Ƙarfe 9:45am na safe su Umma Kande da Maman Jummalo suka shirya tsaf don zuwa gidajen su Zaliha, Umma Kande ce ta bada shawarar su fara zuwa gidan autarta Iklima sai daga baya su zarce gidan Zaliha, haka kuwa akayi direct suka ɗau drop ɗin keke napep har gate ɗin gidan Iklima,basu sha wahala ba kasancewar layinsu Iklimar sananne ne.Bayan sun sauka daga keke napep ɗin, sai Maman Jummalo ta biya mai keke napep kuɗinsa sannan suka nufa gate ɗin gidan,babu laifi gidan hadɗaɗe ne ya tsaru iya tsaruwa,ga wasu flowers masu ban sha'awa an shukasu a gefe-gefan gidan masu launin orange colour da milk,kowannansu bakin buɗe yana kallon kyau da tsarin gidan wanda ya tafi da imaninsu,Maman Jummalo ce ta ce




"Kai gidan nan ya tsaru saikace a ƙasar waje?"




"Ke dai bari Ƙawas ni namá kasa cewa komai,don gidan nan ya tafi da sauran imanina"(Tofa Umma Kande ɗan sauran imanin naki gida  ya tafi dashi tun kan ki shiga ciki,jahilci baiyi wallahi😂😂😂)




Ƙarasawa sukayi bakin gate ɗin gidan tare da ƙwanƙwasawa,shiru babu amsa,ƙara ƙwanƙwasawa sukayi,sai a sannan mai gadin gidan ya buɗe ƙofar,kallonsu yayi ƙasa da sama kafin ya ce




" lafiya,wa kuke nema"



Gyara tsayuwa Umma Kande tayi irin gamai ɗiya tana auran mai kuɗi ta ce



"Munzo ganin ƴar muce Iklima fatan dai tana nan"



Shiru yayi mai gadin yana kallansu sai can kuma ya ce

 


"Ina zuwa"



Bai jira mai zasu ce ba,ya juya tare da kulle ƙofar ya nufa ɗankinsa ya ɗauko waya haɗi da kiran mai gidansa,kira yakai sau uku yayi masa,sai ana huɗun ya ɗauka,cikin girmamawa ya fara gaida mai gidan nasa sannan ya ce




"Yallaɓai iyayen madam ne sukazo  amma nace su jira sai na kirata"



A can mai gidan nasa ya bashi amsa da cewa



"Good,ka barsu su shigo,amma idan sun shigo tsakiyar gidan bayan ka kulle ƙofar sai ka sakar musu  Pistol da Ninja su tayasu exercise"



"An gama yallabai"





Katse wayar yayi tare da sakin wani munafikin murmushi,har ya fara harsashen yadda zasu kaya da Pistol da Ninja.




Kamar yadda mai gidansa ya umurcesa haka yayi,bayan su Umma Kande sunkai tsakiyar gidan,sai ya kulle ƙofar gidan tare da nufar cages ɗin Pistol da Ninja,ya buɗe kowannan su,fitowa sukayi tare da girgiza jikinsu,manyan karnuka ne na turawa baƙaƙe,kumatunsu duk sun zazzago ga miyau da dalala,fuskar nan tasu a kwaɓe take,haba kamar jira suke,tunda sukayi tozali dasu Umma Kande suka nufo inda suke da gudu tare da haushi ganin baƙi a gidan.




Umma Kande da Maman Jummalo da basusan meke faruwa ba,suka ji haushin karnuka a bayansu,juyawar da zasuyi sukayi aran gama da jibga-jibgan kurnaka wanda tunda suke basu taɓa ganin irinsu ba,ganin kansu karnukan sukayo,habawa ƙafa mai naci ban baki ba,kowa sakin jakarsa yayi ya fara gudu,karnukan biyosu sukayi,gudu suke suna ihun a kawo musu ɗauki amma ina gidan shiru alamun babu kowa,Umma kande ce tana gudu tana da cewa




"Mun mutu mun lalace! Mun kawo kanmu ga halaka! Jama'a! Jama'a! A kawo mana ɗauki zasu cinyemu ɗanye! Wayyo ni Sarere jikar sarkin ruwa! Iklima dan Ubanki ki buɗe ƙofar! Iklima! Iklima! Auta! Auta buɗe mana ƙofar! Karnuka zasu cinyemu! Iklima!!! "



Haka tayita nanatawa tana gudu,zaninta ma da yaji wahala saida ya kwance,saukinta ma akwai skirt da abin ya munana kasancewar  tana da manyan ɗuwawuka,sai saɓaɓar saɓaɓar suke tana gudun.Ita ko Maman Jummalo babu bakin surutu sai ihu,mai gadi dai na  zaune akan benchinsa sai video yake musu  yana dariya,saboda yadda suke ihun da gudun dole idan ka gani ya baka dariya,karnuka bisun suke babu ƙakƙautawa,idan sukeyi hagu suma suyi hagu haka idan sukayi dama suma suyi dama,abin gwanin ban dariya.



Iklima dake baccin wahala kamar a mafarki taji muryar mamanta tana kiranta ta kawo mata ɗauki,buɗe idanu tayi tare da sake jin tabbas muryar mamanta ne da Maman Jummalo suna ihu,da sauri ta sauko daga kan gaɗon ta nufo falo tana tafiya a gwale kamar wacca aka mata kaciya haka nufi wurin windonta tare da jaye labulan,zaro idanu tayi waje tana ganin yadda Maman Jummalo da mamanta babu zani a jiki suke shan gudu babu ƙakƙautawa ga karnuka na biye dasu a duk inda suka nufa suna haushi,da sauri ta buɗe ƙofar tare da kiransu Maman Jummalo da mamanta, ai a sittin sukayo ɗakin suma karnuka basu fasa binsu ba,saura ƙiris karnukan su shigo ɗakin,Allah ya taimake su Iklima tayi saurin rufe ƙofar ɗakin.



Su Umma Kande na shiga falon kowaccansu ta baje a ƙasa tana haki,ga uban zufar da take tsuttsugo musu a duk ilahirin jikinsu sai kace sunyi gudun kilometer 3 haka suke ji.



Iklima ce take bin kowaccansu da kallo,kallon ma irin na takaici sai kuma can ta ce



"Yanzu saboda ɗan wannan gudun da kuka sha kuke haki haka,Allah ya bani haƙuri nida kusan kullum sai maza sama da biyu sun afkamin ta gaba da ta baya"



Zaro jajayen idanunsu sukayi suna kallonta cike da mamakin furucinta,Maman Jummalo ta ƙara tambayarta don ta gasgata zancen nata



"Maza sama da biyu suke afka miki Iklima,to shi ina mijin naki? "



Taɓe baki tayi irin na autoci sannan ta ce



"Harda dashi ai,a daren farkona ma a ta duburana ya biya buƙatarsa,sannan bayan kwana hudu yazo da abokansa kusan su uku sukayi lalata dani,ta baya da ta gaba,kuma tun daga wannan ranar kusan duk sati sai sunzo sunyi lalata dani gashi harda videon abinda suke aikatamin yake,yanzu tafiyata ma ta canja,a gwale nake tafiya saboda muƙurƙusar da nake sha gunsu"




Kowacce a cikin zaro idanunta tayi waje tare da dafa ƙirji kamar haɗin baki,Umma Kande ta fara magana da cewa



"Innalillahi Wa'inna Wa'innar Raji'ana,Iklima shi ne tunda muke waya dake baki taɓa sanarmin ga halin da kike ci ba,na shiga uku ni Saratu,mun kawo yaranmu cikin bala'i,innalillahi Wa'inna Wa'innar Raji'ana,Sambuhanillahana!!! " (My Esteem Fans ku koyi Innalillahi wurin Umma Kande tare da Sumbuhani.....kai! kai! kai! bazan iya ƙarasawa ba😂😂😂😷😷😷)




"Yamin kashedi akan kar na sanar ma kowa idan ba haka ba,zai ɗora videos ɗin da yimin a sanda suke lalata dani a social media kowa ya gani"



Maman Jummalo ce ta cire tagumin da tayi sannan ta ce



"Hmmmm ni nama sara mai zance yanzu,kalmomi duk sun ɓacemin,ƙwaƙwalwata ta rikice ta daina bani haɗin kai,ke yanzu Iklima ko guduwa kin kasa yi,ace kina cikin irin wannan mawuyacin hali kin zauna kina kwasar baƙin ciki Iklima ummm"



Zama Iklima ta gyara a hankali kamar wacca akama kaciya sannan ta ce



"Nayi yunƙurin guduwa amma ban samu dama ba,ni tsorana ma  yanzu kar yazo shida la'anannun abokannan nasa su afka muku"




Ai da sauri suka kai dubansu ga Iklima jin abinda take faɗa,nan da nan suka rikice suna dube-dube kamar sunyi ajiya duk tsabar ruɗewa ne da sukayi,Umma Kande jikinta na ɓari ta fara magana



"Mun shiga Uku mun lalace,su afka mana kikace Auta,yanzu ya zamu gudu daga gidan nan harda ke"



Maman Jummalo ce ta cafke maganar da cewa




"Iklima musan abunyi kar mutanan suzo gidan nan mu shiga Uku"



Dogon tunani Iklima ta lula,tare da tunanin yadda zasu kuɓuta daga hannu  mijin nata da abokansa,dubara ce tazo mata sai ta dubi su Umma Kande tare da cewa



"Mafita ɗaya ce yanzu,akwai ƙofar sirri wacca idan misali gidan yayi gobara mutane suke fita don su samu su tsira da rayukansu,amma yanzu matsalar saina nemi key ɗin ƙofar wacca zata sadamu har wajen gidan ba tare da mai gadi yasan da fitarmu ba,bara in tashi yanzu nan kar suzo don nasan suna hanya wallahi"



Ƙara rikice su Umma Kande sukayi jin ƙilama suna hanya,a gwale Ikilima take tafiya tana botsaro ɗuwawunka waje ta nufi gun drawers ɗin bedroom tana dubawa,suma tayata dubawa sukayi,daƙyar Iklima ta gano key ɗin,ai da sauri tabama su Umma Kande manyan hijabai kasancewar sun zubar da gyaluluwansu a sanda karnuka suka biyosu,harda zani Iklima taba Umma Kande, komai nata ta ɗauko har kuɗi masu yawa da mijin nata yasa a jaka ta ɗauko suka nufo ƙofar,cikin sa'a ta buɗe suka fito ta wani layin daban,samun mai keke napep sukayi babu ciniki suka shiga,sai a sannan ne Umma Kande ta sauke nauyayyen ajiyar zuwa tana da cewa



"Kaiiiii! Wannan bala'i haka,hmmmm"



Maman Jummalo  itama ta sauke nata ajiyar zuciyar sannan ta ce




"Yanzu gidan Zaliha zamu nufa ko sai gobe"



"Sai gobe mana,yanzu direct zamu fara zuwa asibita a duba Auta,don gaskiya a yadda take tafiya ya nuna akwai matsala"



"Hakane "



Haka suka nufi asibitin da Iklima don a dubata,bayan likita ta dubata sai ta fito tare da cema su Umma Kande su biyota office rai a bace.Isarsu office keda wuya ko zama basuyi ba likita ta rufesu da faɗa akan ya zasu bar ƴar yarinya wacca bata girma cikin irin wannan halin,sannan suwa suka mata wannan muguwar aika-aikar.Tsuru-tsuru sukayi  da idanu babu amsa,to wai me zasu ce bayansu suka siya wahalar da kuɗinsu,haka likita tayi masifarta ta gama ko ummm babu wacca tace a cikinsu.Likitar ce ta ce za'a ba Iklima gado saboda an illata ta sosai Allah ma ya rufe asiri bai kai stage ɗin da kashi zai dinga fito mata ba bisa ƙa'ida ba saboda afka matan da akai ta dubura.



Kasancewar akwai kuɗi a hannun Iklima wanda ta ɗauko na mijinta ,dashi suka biya kuɗin asibitin sannan aka bata gado,Maman Jummalo ce ta zauna da Iklima sai Umma Kande taje gida kiran Jummalo dan ta zauna da ita saboda gobe suke so suje gidan Zaliha suga ita wani kalan bala'i take a ciki.



Haka kuwa akayi,Jummalo ce ta zauna da Iklima,sai suka bata kuɗaɗan da zasuyi amfani dashi,sai suka tafi gida.



        @@ @@@ @@@@ @@@@




Washe Gari





Kamar jiya har yau  da safe suka nufi gidan Zaliha, amma a wannan karan basuyi kalle-kallan gida ba saboda wuyar da sukasha jiyan,bayan mai keke napep ya saukesu,sai suka sallameshi,gabansu na dukan uku-uku suka ƙwanƙwasa gate ɗin gidan,wani basamuden ƙato ne ya buɗe ƙofar gidan,ja baya su Umma Kande sukayi ganin wani gabjejan ƙato ga kwalli ya rambaɗa a idanunsa sai mazurai yake,cikin deep voice irin na manya-manyan gardawa ya ce dasu




"Wa kuke nema!"



Inda-inda suka fara yi,kowacce ta kasa magana,sai can Maman Jummalo tayi kasadar fara magana,wacca a rikice takeyin maganar haɗi da inda-inda



"Ammm amm amm dddamman wwwurinnn Zzzalihaaaa mukazo neeee yeeee"



"Ina zuwa"



Haka kawai yace musu ya kulle ƙofar,sauke ajiyar zuciya su Umma Kande sukayi a tare sai Maman Jummalo ta ce



"Oonii Hasfy!! Yara duk babu sa'a,Allah yasa gidan babu karnuka irin gidan Iklima"



"Ameen dai Maman Jummalo dako mun shiga uku"



Bayan mai gadin ya kulle ƙofar sai ya kira Ogansa akan iyayen Zaliha sunzo wurinta,dariya Ogan nasa ya tintsire dashi tare da cewa



"Aikin gama ya gama ai,barsu su shiga su ɗau sauranta"



"To Oga"



Katse wayar yayi sannan ya buɗe musu ƙofar suka shiga.Cikin sanɗa su Umma Kande da Maman Jummalo suka fara tafiya saboda tsoran kar suma sunada karnuka irin gidan Iklima. A haka har suka isa ƙofar ɗakin tare da ƙwanƙwasawa.



Zaliha dake a zaune a falon ta ce a shigo kasancewar ƙofar kodayaushe a ɓude take ba'a sa mata key,saida ta maimaita a shigo har sau uku sannan su Umma Kande suka shigo kasancewar Zaliha bada ƙarfi take magana ba,shigarsu ɗakin suka fara salati haɗi da sallalami,Umma Kande ce ta fara magana cike da ruɗewa



"Me zan gani  ni Saratu! Zaliha haka kika koma,maiya sameki! "



Ɗan murmushin wahala Zaliha tayi sannan ta ce



"Kunzo ɗaukar gawata ne mama,Allah ya amsa addu'ana akan ƴan uwana suzo ɗaukar gawana saboda mutuwata tazo banaso in mutu a acikin ahalina ba,mama kin cuci rayuwata, kaicona da samun uwa irinki mai son abin duniya,gashi ta hanyar son abin duniyar zan rasa raina,don Allah mama ki roƙamin yafiya gunsu Umman Sa'eeda da ita kanta Sa'eeda akan su yafemin duk laifukan dana musu,son abin duniya ya kaini da halaka gashi mutuwata tazo"



Babu wacca a cikinsu bata zubda ƙwalla ba ganin yadda Zaliha jikinta ya koma kore shar  ga idanunta sunyi yellow kamar wata aljana ba mutum ba,babban tashin hankali ma shi ne wani fari-farin ruwa yake fita  a ta gabanta sai uban wari,cikin rawar murya Umma Kande ta ce



"A'a! A'a! Zaliha bazaki mutu ba,bazaki mutu ba Zaliha, muje asibiti Zaliha! Na shiga uku yau ni Saratu"



Girgiza kai Zaliha tayi tare da cewa


"Karku ɓata kuɗinku a kaina saboda ni tawa ta ƙare yannnnnzzzz......."




Tari ya saƙeta babu ƙakƙautawa a lokaci guda jini na fito mata ta baki  ta hanci,da sauri su Umma Kande sukayo kanta tare da tallafota sukayo waje, sunci sa'a gidan a buɗe yake,direct sukayi hanyar waje,Maman Jummalo ce ta tarin musu  keke napep suka shiga,cikin tashin hankali Maman Jummalo ta ce su tafi  asibiti,a hanyarsu ta zuwa asibiti ne tari yasha ƙarfin Zaliha wanda a ƙarshe ta ce ga garinku nan.




Cak abubuwa suka tsayawa Umma Kande a ƙwaƙwalwarta,ji take kamar duniya ta juye babu sauran kows,lissafi ya ɓace mata kwata-kwata,wani ƙaramin hauka Umma Kande tayi a cikin keke napep ɗin tare da girgiza Zaliha wai ta tashi,amma ina rai yayi halinsa.




Haka akayi zaman makokin Zaliha wanda sai a lokacin Nusaiba ta dawo gida shima don kiranta akayi akan Zaliha ta rasu,da labarin abinda ke faruwa da ƴan uwan nata,tayi kuka tayi baƙin ciki sosai tare da godewa Allah da bata wanke fuskarta da wannan ruwan da boka Sankeru ya bada ba,da yanzu itama tana cikin tashin hankali.




Ko dayake hanyar da itama ta ɗauko ba mai ɗore mata bane,domin yanzu  Nusaiba ta zama INTERNATIONAL HOMOSEXUALITY GANG STAR,tauraronta  ne ke haskewa yanzu,bata waccar ƙasar bata waccan,har competition ɗin cin duri suke wanda yawanci ita ke ci,shiyasa bata cika zama gida ba saidai ta turo da kuɗi masu yawa,kuma Umma Kande da Maman Jummalo duk sun san mai take aikatawa amma ko ajikinsu tunda kuɗi na shigo musu babu ƙakƙautawa.




A haka a haka har akayi bakwan Zaliha sai a sannan ne Jummalo da Iklima suka dawo gida an sallamesu daga asibiti kasancewar yanzu Alhamdulillah sauƙi yazo ma Iklima,dan yanzu ta rage gwala ƙafa idan tana tafiya,kwana goma da rasuwar Zaliha Nusaiba ta koma ƙasar da tafito wato Germany,shi kuma Musa bai samu zuwa ba saida ya kira waya yayi ta'aziyya.Wannan kenan




       @@@ @@@@@ @@@





A ɓangarensu Sa'eeda rayuwarsu na tafiya normal babu wata matsala,koda ma akayi rasuwar,tare dasu akayi zaman makokin,kasancewar Abban Sa'eeda ba'a hayyacinsa yake ba duk surutan da mazan layi suke masa akan yadda yaransa suka koma ko ajikinsa,hasalima idan ya tafi kasuwa bashi ke dawowa gida sai 8:00pm kuma yana dawowa yake wucewa turakarsa yayi kwanciyarsa,dayake yanzu lokacin rani ne baya zuwa gona,shidai rayuwa yakeyi gashinan gashinan dai.





Wasa-wasa lokacin exams ɗinsu Sa'eeda yazo kamar yadda tama Ummanta alƙawarin maida hankalinta kacokan a karatunta haka tayi,kwata-kwata ta daina tunanin Sauban aranta,gobe ne zasu fara exams duk shirin daya dace tayi duk tayi,a ranta take cewa



'I'm ready to face every single challenge in my life! I'm  ready to face the battle with great speed! I want to become my own hero! Ready for whosoever come my way! I have change to a new version !!! '



Da wuri Sa'eeda taje hall ɗin exams ɗinsu,Iman ma acan ta sameta,shigorwa Maryam hall ɗin sai ƴan ajin suka kaure da ihun Amarya! Amarya!Amarya!



Sa'eeda taɓe baki tayi ko a jikinta,in fact ko kallon inda ake cewa ga Maryam ɗin batayi ba,focusing tayi ga summary dake a hannunta tana jiran su fara exams,haka suka fara exams,hall ɗin  yayi tsit! Invigillators sai zagaye hall ɗin suka don tabbatar da tsakani da Allah ɗaliban suke rubuta jarabawan babu satar answer.




Bayan sun gama exams ne suka fito ita da Iman zasu nufo gida,Iman ce tama Sa'eeda raɗa a kunne tare da nuna mata wani abu da yatsa,Sauban ne yazo ɗaukar Maryam,kuma shiɗin Iman tama Sa'eeda raɗa a kunne ta kallesu.



Direct Sa'eeda fuska a ɗaure ta nufi inda su Maryam suke,Iman na kiranta amma inaaa,bata saurareta ba,saidai Iman ita ma ta biyota kar a samu matsala.Sa'eeda bata tsaya ko'ina ba sai a wurin inda Sauban yake,tsayawa tayi tare da kallonsa ido cikin ido  ta fara magana cike da Izza wanda ba'a santa dashi ba



"To munafiki,mayaudari,annamimi,kai a tunanin zan mutu ne saboda soyayyar da nake maka ko! Never!!! Wallahi kayi kaɗan ɗan akuya,wato ka nunamin halinku na maza tare da waccan munafukar"



Nuna Maryam tayi wacca tayi mutuwar tsaye don jin irin lafuzzan dake fitowa daga bakin Sa'eeda wacca tasan bata magana,in fact ko yatsa kasa a bakin Sa'eeda bazata ciza ba amma yau gata tana magana cike da izza ta ƙasaita,katse mata tunani Sa'eeda tayi da cewa



"Ni Sa'eeda Sulaiman bana manta alkhairi haka zalika bana manta sharri, I hate deceivers in my life,ku jira ƙarshen ku ku ɗinnan"



Nunasu tayi sannan ta cigaba da cewa



"In shaa Allahu sai Allah ya sakamin tata-izan da gaggawa,wallahi wallahi wallahi idan inada da hakƙi daidai da ƙwayar zarra akanku sai Allah ya bimin hakƙina,sannan rashin asalina da kuke ta ja-inja a kai kusani,haka Allah yaso ya ganni kuma ina ji a jikina na kusa haɗuwa da ahalina,daga ƙarshe ina tabbatar muku da sai kunzo da ƙafafunku wurina kuna roƙon inyafe muku,trust me Sauban that time will surely come in shaa Allah"



Raf!Raf!Raf! Iman tayi da hannunta tare da jinjina ma Sa'eeda tabbas Sa'eedarta ta canja,Sa'eeda batabi takan mai zasu ce ba taja hannun Iman sukayi gaba.



Mutuwar tsaye Sauban yayi,saida ƙwaƙwalwarshi ta tafi wucin gadi na wasu seconds kana hankalinsa ya dawo jikinsa,Sa'eeda ce da wannan kalaman,yarinyar da batada magana,to yaushe ta fara zubo zance.(ba Sa'eedar da kasani a da bace ehe😏,ta yanzu bata ɗaukar raini🙃🙃🙃😂😂😂).




Juyowa yayi kan Maryam tare da hararta haɗi da cewa



"Uban me kike jira da baki shiga motar ba ehhhh!"



Da sauri Maryam ta shiga motar don yanzu tsoran Sauban take sosai,tunda ya mata dukan tsiya akan zagin Mom ɗinsa da tayi take shakkarsa,gashi ya hana a ɗauko mata ƴan aiki,ita take aikin gidan,har part ɗin Mom ɗinsa kasancewar a gidan suke da zama,babbar matsalar ma rashin iya girkinta,kasancewar ko a gida ƴan aiki suke musu girki shi kuma Sauban yace girkinta yakeso,kwaɓa takeyi wanda a ƙarshe saidai da zubar da abinci shi kuma waje resturant ya musu takeaway,sannan ya ce da ita zuwa resturant bazai fisshesu ba gwara ta koya girki ko kuma ya ƙaro wata(Tofa tun a first week of marriage an fara maganar kishiya,babbar magana su Maryam sai a gyara🤔🤔🤔).




Abu dayawa ga tsangwamawan da Mom ɗin Sauban take mata tun ran da ta zageta taji Maryam ɗin ta fitar mata a rai,sati guda da auransu amma tafara fuskantar challenges daban-daban.




Bayan Exams su Sa'eeda suka tafi IT a wajaje ma banbanta,sai bayan wata shida zasu dawo school kuma ajin ƙarshe wato 400 level.wannan kenan.




          @@@@ @@@@@@@


 


ABUJA




Ƙarfe 2:30am na dare



Ɗaki ne mai duhu  sai ɗan wani haske kaɗan da nake ɗan iya hangowa wanda bai wadaci ɗakin ba, ga tururin hayaƙi daya turniƙe ɗakin, ni kaina da kyar na iya shiga ɗakin haɗe da addu'a dan ɗauko muku rahoto, wasu surutai kamar suddabaru naji muryar  wannan matar ta shekarun baya  tana faɗi wanda nakasa gane mai ta ke cewa, kwatsam kamar wancan karon naga wani haske kamar walƙiyar ya ɓullo ta cikin bangon ɗakin ya haska ko'ina, wannan halittar nagani kamar mutum amma wada, kansa a ƙasa yake, shi baiyi ƙasa ba kuma bayi sama ba, yana a tsakatsaki, tsawansa bai  wuce tsawan hannu ba, sai rangwajejan kai kamar ƙwarya,yanada idanuwa kamar na mage, da sharɓa sharɓan kafakuwa kamar na babban mutum, kai in taƙaice muku, halittar nan batada kyawun gani hasalima mai ciki zaka iyayin ɓari ganin wannan muguwar hallitta,sujjada tama wannan hallitar tare da cewa



"Yakai Sarkin Tsageru! yakai gagara badau!! , yakai buhun ƙara kafi ƙarfin danna!!!, ya kai Shugaban matsafan duniya!!! Haƙiƙa ka cika alƙawarin da ka ɗauka akan bayyanar bayan shekara biyar!!! "




 Wata dariya naji har ƙasa na girgiza  ashe wannan halittar ne ke busar dariyar, can ya tsagaita kamar ruwa ya ɗauke ya fara magana jikake kamar ƙasa zata tsage 




"Karki yarda ayi auran!!! Karki bari ayi auran!!! Idan kuma ba haka ƙarshenki yazo Zulfa'u,yaaazoooo ƙarshenki Zulfa'u!!! "




Da saura ta ɗago kanta tana kallonsa don a gaskiya ita batasan da wani aure ba,to wani aure yake magana akai,kasa haƙuri tayi ta tambayesa cikin girmamawa tare da ƙan-ƙan dakai




"Ya kai Sarkin matsafan duniya, yakai Boka Burumbuɗu wani aure ne zan hana afkuwarsa"(daman sunan wannan halittar Boka Burumbuɗu,tabbb yaci sunnansa kuwa🤔🤔🤔😂😂😂😂)




Dariya ya tsintsire dashi  har ƙasa na girgiza,sai kuma ya fara kuka ko'ina na ɗakin rawa yake can ya tsagaita  tare da cewa 




" Karki bari!!! Karki yarda!!! A hir ɗinki ki bari  ayi auran..........








Mu haɗu a pages na gaba hmmmmm wuta kan wuta🔥🔥🔥🔥





****Auransu waye ne Boka Burumbuɗu yace kar Zulfa'u ta bari ayi????.......





****Shin su Umma Kande da Maman Jummalo sun tuba ko kohar yanzu basu saduda ba???........





****Yaya zamantakewar Maryam zata cika ba a gidan Sauban ganin tun a satin farko Maryam ta fara fuskantar ƙalubalai iri-iri???.........






Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️







Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓





Post a Comment

0 Comments