TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 51-52

 *BOOK 2*





5⃣1⃣----5⃣2⃣






A ɓangaren Haj Zulfa'u duk takun da su Malam Bala Mai Carbi sukeyi tare da bugun zuciyarta suke, tana a haka sai can taji magana a iska ana cewa



"Lokacin girbar abinda kika shuka yayi Zulfa'u!!!, mu mun tafi!!! Ƙarshanki yazoooo!!! "



Ai tuni Haj Zulfa'u ta mike jikinta na rawa tana fuskantar ƙofar ɗakin kamar tana jiran wani abu,suma yaran nata suka miƙe lokaci guda ganin ta miƙe,kamar jira maganar ake ta wuce saiga su *Uncle Hassan da Umman Sa'eeda* sun shigo ɗakin da sallama,lokaci guda ƙwayar idanun Haj. Zulfa'u tayi tozali da nasu Uncle Hassan tare da Umman Sa'eeda,kamar dai yadda suke zuwa mata a mafarki hannunsu yana a tsarƙafe dana juna,kallan-kallo Haj. Zulfa'u ta fara yi dasu,suna a haka Malam Bala mai Carbi suka shigo falon,kamar walƙiya wani haske daga idanun su Uncle Hassan da Umman Sa'eeda ya fito a tare, direct hasken sai cikin idanun Haj. Zulfa'u, ai nan take ta fara haushin kare tare da magana lokaci guda



"Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!! Ni nayi ma Maimuna farraƙu da yaranta Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wayyoooo!!!....."




Bata ƙarasa maganar ba jikinta ya fara jijjiga,fatar jikinta a hankali tana sauyawa daga fresh zuwa na tsofaffi duk fatar ta yamutse irin na tsofaffin nan masu shekaru dayawa,gashin kanta ya canja daga baƙi siɗik zuwa fari fet! Idanunta sun shige ciki-ciki,ada tsaye take ƙyam! Amma yanzu ta duƙa,in taƙaice muku Haj. Zulfa'un da kuka sani ƴar gayu,ƴar ƙwalisa ta koma tsohuwa tukuf! harta gashin giranta ya koma fari,still tana nan tana haushin karnuka,karnukan ma masu babban murya har ɗaga wuya take tana irin kukansu jikake



"Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!!Uuuuuuwuhhhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!!"



Harda gurnanin karnuka Haj. Zulfa'u take babu ji babu gani,ɗakin kaurewa yayi da salati da sallallami,abun al ajabi baya ƙarewa a duniya,yau ga Haj. Zulfa'u mai ji da kuɗi da gayu ta koma tana kukan karnuka,kowa ya kasa zama yana kallon abin al ajabi,yaran Haj. Zulfa'u sai kuka suke suna mamakin yadda uwarsu ta koma lokaci guda, cikin muryar kuka babban ɗiyar Haj. Zulfa'u  wato Haj.Amina ta ce



"Su waye ku? Mai muka tare muku? Me kuka ma uwarmu haka? "



Babu wanda ya bata amsa saima umarni da Malam Bala mai Carbi ya basu da su zauna,babu musu kowa ya samu wuri ya zauna tare mamakin wannan al'amari,Malam Bala Mai Carbi ƙara umurtar yaran Haj. Zulfa'u yayi da cewa



"Ku zauna ayi magana domin idan kuna a tsaye ba fahimtar komai zakuyi ba,wannan azzalumar uwar taku da kanta zata yi muku bayani bamu ba,don hakan kusha kurumunku indai bayani ne zaku jishi dalla-dalla a bakin uwarku"



Haka suka samu wuri suka zauna kamar wa'inda ƙwai ya fashe musu a ciki sai faman sharan ƙwalla suke saboda basu san Hajiyarsu da zalunci ba saima alkhairi.(Haj. Zulfa'u kenan kura mai lulluɓe da fatan akuya,waje Musa ciki Fir'auna🤔🤔🤔🤔😂😂😂😂🙃🙃)




Haj. Zulfa'u kaɗai aka bari a tsaye tanata faman haushin karnuka iri-iri kai harma da kalan haushin karnukan ƙasar waje babu wanda batayi,Malam Bala mai Carbi yasan ba magana Haj. Zulfa'u zatayi ba wannan yanayin da take ciki,dole sai ya watsa mata ruwan addu'a kafin bakin ya ɓude tayi magana tare da fallasa asirinta da kanta,cewa yayi a ɗebo mishi ruwa a kofi ƙarami,babu musu jiki na rawa mai aikin Haj. Zulfa'u taje kitchen ta debo mishi ruwan a ɗan ƙaramin kofi.Amsa yayi tare da tofi a cikin ruwan,guntsan ruwan yayi tare da furzasu a jikin Haj. Zulfa'u,habawa kan kace me Haj. Zulfa'u ta saki wata razananniyar ƙara wanda har ma'aikatan waje saida suka ji,duƙawa tayi kamar kare tana karkaɗa ɗuwawunta kamar yadda kare yake karkaɗa bindinsa,cikin wata irin muryar Haj. Zulfa'u ta fara magana still tana a duƙyan nan kamar kare






*TARIHIN HAJ.ZULFA'U*

( *Tare da abubuwan da ta aikata a shekaru aru-aru da suka gabata* )





Sunana Haj. Zulfa'u Yusufa,ni ƴar asalin Niger ce amma muna zaune a Nigeria saboda a nan babanmu yake kasuwancinsa,na taso da mugun kishi,bana haɗa komai da wani ko kayan salla ba'a mana iri ɗaya da ƴan uwana,komai na fiso nawa ni kaɗai,haka na taso a gidanmu da wannan halin,mamata tana yawan yimin faɗa akan na rage mugun kishi amma ina ƙaruwa ma kishin nawa yayi.



Na aure Alhaji Sani Mai Gado saboda dukiyarsa bawai don ina sonsa ba,na haifi ƴata ta farko Amina sai Alhaji Sani ya bijiromin da zai ƙara aure,hankalina yayi ƙololuwan tashi domin ina tsoron kar wacca zai auro tazo tayita haihuwa maza ta fini samun gado saboda Alhaji Sani yanada kuɗi sosai ga kaddarori a cikin Nigeria da wajenta.Na tada hankalina akan banason yamin kishiya amma yaƙi jina haka aka kawota gidanshi,ni kuma na rantse bazan zauna da ita ba komai zanyi sai nayi don tafita ta barmin gidana.



Maimuna ta shigo gidan da ƙafar dama,babu dadewa saiga Maimuna da ciki,nan ma hankalina ya ƙara tashi saboda naga makircin baya ci,dole na tuntuɓi wata ƙawata akan samun mafita saboda nasan kona faɗama mamata ba saurarana zatayi ba hasalima fada zata rufeni dashi,babu musu ta kaini wurin wani boka  a garin Zaria,na sanar mishi da inaso cikin Maimuna ya zube,amma cemin yayi sai ta haifi cikin dole,fishi nayi muka taho gida.



Haka nayi ta bin bokaye da malamai saboda cikin ya zube amma maganar ɗaya ce akan sai ta haifa cikin,haƙuri nayi har ta sauka,ƴan biyu maza ta haifa wayyo!!! Tashin hankali wanda ba'asa mai rana,na shiga cikin ƙunci da damuwa a wannan ranar amma sai kawata tace kar na nuna damuwata a fili,in dinga janta ajiki tare da yaran suma,haka nake jansu a jiki ba don raina naso ba.Haka muka kasance har wajan shekara uku ina nuna musu soyayyar ƙarya ni kuma a lokacin na haifi ɗiyata da biyu Jamila,a lokaci muka sake neman wani sabon boka don ya mana aiki akanta,munci sa'a kuwa domin aikin yayi saboda a ranar dana dawo a ranar yaran suka mutu,bansani ba ashe tana da wani cikin,shima haka mukayita ƙulla-ƙulla nida ƙawata akan yadda zai ɓare amma haƙarmu bata cimma ruwa ba,ta haifi cikin suma ƴan biyu amma mace da namiji,raina yayi ƙololuwan tashi gashi Maimuna ta daina yarda dani,kome na taba bata amsa,haka tafiya tayi tafiya.Maimuna ta ƙara samun wani cikin tayi bayan nima a lokacin inada yara har uku amma mata,dalilin haka yasani bazama nida aminiyata domin ganin bayanta tunda ni banda ɗa namiji sai ita,gashi Alhaji Sani ya ƙwallafa rai ga yaran nan, nawa kuma ko oho! 




Wani boka da muka samu ne yace shi bazai iya aikin ba amma akwai *Gagara-badau Boka Burumbuɗu* amma yanada sharudɗa idan zan iya bin sharudɗansa to aiki kamar anyi an gama domin aikinsa kamar yankan wuƙa ne,sannan ba kodayaushe yake bayyana ba sai ya ɗau shekaru aru-aru idan na aminci sai ya haɗani dashi,ban tsaya tunani ba nace na aminta a haɗani dashi in har buƙata ta zata biya,ƙawata taso min gargaɗi akan na fara shawara tukun tunda ance hatsabibin boka ne ba kowani irin boka bane,share maganarta nayi tare da sakawa a kwandon shara saboda ni a lokacin idanuna sun ruga da sun rufe bana ji bana gani, bana iya bambance mai kyau da marar kyau, bana iya gane mai illa da marar illa,nidai idan za'a biyamun buƙata ta to naji na gani babu gudu babu ja da baya a shirye nake.



Haka wannan bokan ya bani abubuwan da zai sadani da boka Burumbuɗu tare da cemin sai sali-salin dare zan kirasa kuma na tabbatar ɗakin da duhu,duk yadda zanyi amfani wurin kiransa saida wannan bokan ya sanarmin,haka muka taho gida,kamar yadda wannan bokan ya umurce ni nayi a sali-salin dare haka na tashi nayi,kamar walƙiya saiga boka Burumbuɗu ya bayyana a gareni cikin suffarsa mara kyawun gani,haƙiƙa nayi matuƙar razana da ganin mummunan halittarsa sai kuma daga baya hankalina ya dawo jikina tare da mika mishi buƙatuna akan inaso ya raba Alhaji Sani da Maimuna rabuwa ta har abada harda yaran suma ya haɗa dasu sannan cikin jikinta shima ya haɗa dashi,komai na sanar masa shi kuma ya amsa da in har zanbi sharudɗansa to aikina kamar anyi an gama,ni kuma ba tare da naji sharudɗansa ba na amince,cikin muryarsa mai ƙaraji ya fara karantomin sharudɗansa, banda sallah,banda zuwa hajji,banda amsa sallama sannan duk shekara zan dinga sadakar karnuka guda hamsin,ban damu ba tunda bukata ta zata biya nace naji na gani,ya kara da cewa zai dawo bayan shekara 43 a gareni,nan ma ban musa mishi ba,sannan na ƙara neman wata buƙata akan banaso na tsufa kwata-kwata,nan ma ya cemin anyi an gama su dai a cika sharudɗa na ce mishi na aminta sai ya ɓace.Ashe Alhaji Sani yaji wasu daga cikin tattaunawar da boka Burumbuɗu, hankalina ya tashi sosai ,neman yadda zan hallaka Alhaji Sani na koma ina tunani a daren,ban runtsa ba saida na samo ma kaina mafita akan saka mara guba wacca take cin mutum a hankali ba tare da ansan da gubar ba,da safe na nemota tare da saka masa a abincinsa,kamar wasa Alhaji Sani ya fara ciwo ita kuma Maimuna da yaranta aka nemesu ƙasa da sama aka rasa,haka Alhaji Sani shima bai daɗe ba yace ga garinku nan,haka na fara cin dukiyar Alhaji Sani duk da kaso mafi rinjaye na dukiyarsa na rasa inda suke amma kuma ban damu ba tunda akwai sauran dukiyarsa a hannuna,ƴan uwansa ma duk nayi musu farraƙu ta hanyar boka Burumbuɗu, suma ban sake ganinsu.






*Cikin Labari*





Kamar jira ake ta gama bada tarihi ta koma kukan karnuka ji kake




"Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!! Uuuuuuwuuuhhhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!! Wuhhh!!! "




Ɗai-ɗai kune a cikin ɗakin wa'inda basu zubda ƙwalla ba daman yaran nata tun kan ta bada tarihi kukan suke,gashi kuma yanzu sunji komai idan nace komai ko koman nake nufi,duk abinda ta ɓoye gashi yanzu ta tonashi da kanta,kuka suke sosai yaran nata.Su Uncle Hassan da Umman Sa'eeda ba'a magana domin tarihin ya shigesu sosai ashe wannan azzalumar mata tayi sanadin mutuwar mahaifinsu bama mahaifiyarsu kaɗai ba,wannan wace irin mata ce mara imani duk dan saboda taci dukiya ta hallakar da ahali masu yawa.Malam Bala mai Carbi ne ya ce 




"Alhamdulillah ala kulli halin,yanzu dai komai yazo ƙarshe don haka a ɗauketa daga nan wurin saboda zamuyi magana mai muhimmanci kar ta cika mana kunne da kukan karnuka babu daɗin ji"




Wa'innan amintattun almajiran Malam Bala mai Carbi ne da Mai Babban Gida suka ɗauketa tana kukan karnuka iri-iri tare da karkaɗa ɗuwawunta kamar kare na karkaɗa bindinsa haka suka ɗauketa, mai aikin kuma ta nuna musu wani ɗaki inda za'a sakata,har cikin ɗakin suka sakata zasu fito sai itama ta fara rarrafe kamar kare zata fito sukayi saurin kulleta da key suka taho cikin falon.(Mai Esteem fans a tayani dubawa Haj. Zulfa'u ta koma karya,kai kai kai daɗi kasheni,wanga abu yamin suga wallah😂😂😂🙃🙃🙃)




Bayan sun dawo ne Malam Bala mai Carbi ya fara wa'azi mai ratsa zuciya da gabɓai yana cewa




"To ƴan uwana musulmai,kunga dai ƙarshan zalunci da makirci ko,ita duniyar nan ba matabbata bace,duk yadda kakai ga kuɗi,ɗaukaka,izzah,mulki,dukiya watarana ba kai bane,yanzu al'amarin Zulfa'u bai ishe mutum ishara ba,tayi zalunci iri-iri a tunaninta ƙarshanta bazai zo ba,to amma yanzu fa akwai abinda yakai ƙasƙanci tare da tozarci ace mutum *Ɗan Adam* ya koma kukan wata halitta halittarma wacca mala'ikun rahma basa shiga gidan da akwaita,yanzu duk saboda son abin duniya da ɗaukaka ta aikata wannan aika-aikar to wa gari ya waya yanzu, gashi su wa'inda taso a hallakar dasu Allah yayi nasa nufin akansu gashi sun dawo cikin gidan mahaifinsu sannan da izinin mai sama sun kawo ƙarshanta,a gaskiya wannan babbar ishara ce a garemu,Allah ka tsare mana imaninmu,kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu baki ɗaya"




Haka yayi ta musu wa'azi yawancinsu sai kuka suke musamman yaran Haj. Zulfa'u, ita kuwa tana can cikin ɗakin tana kukan karnuka babu ji babu gani,sai a sannan ne tsoho mai ran ƙarfe Baba Garba ya fara magana da cewa




"To Alhamdulillah dukkan abinda yayi farko zaiyi ƙarshe yanzu dai ga ishara Allah maɗaukakin sarki ya saukar mana akan Zulfa'u,bayan haka tunda Allah yasa komai yazo ƙarshe to maganar gado zamuyi saboda aminina Alhaji Sani yayi dubarar kai kaso mafi rinjaye na dukiyarsa kotu,kuma Ni,Hassan daai Babban gida mukaje kotun domin tuntuɓar dukiyar kafin muzo nan to Alhamdulillahi munyi nasarar amso kaddarorin gaba ɗaya,zuwa gobe kowa idan ya natsu za'a raba dukiyar ga duk wanda ya hallarta kasancewar ba wasu ƴar uwa Alhaji Sani yake dasu ba tun a zamanin da balle yanzu da basu san ina zamu samesu ba tunda Zulfa'u ta riga da tayi musu farraƙu a tsakaninsu"




Hajiya Amina ce ta fara magana tana kuka




"Don Allah ku yafe ma Hajiyarmu,tabbas tayi kuskure kuma gashi tun kan taje lahira ta fara girban abinda da shuka,na roƙeku da Allah ku yafe mata"




Hannu bibbiyu take roƙonsu Uncle Hassan da Umman Sa'eeda suma sauran yaran roƙonsu sukeyi,duk da sunji zafin abubuwan da tama iyayensu haka suka daure suka yafe mata.Godiya kwando-kwando sunsha wurinsu Haj. Amina,haka taro ya tashi.



Girki su Haj. Amina suka ɗora saboda baƙi harda su Momin Sadam da Umman Sa'eeda suka tayasu girkin sukayi nan da nan suka gama babu ɓata lokaci,kasancewar gidan babba ne sosai akwai wadatattun ɗakuna,a empty ɗakunan su Uncle Hassan da sauran mazan suka yada zango,abinci ma can aka kai musu,haka sukaci suka sha hankali kwance duk da yaran Haj. Zulfa'u har yanzu akwai damuwa a ransu amma haka suka baje anata hira dasu,ita kuma *Uwar Gayya Haj. Zulfa'u* tana can tana fama da kukan karnuka babu ji babu gani,sai bubbuga ƙofar take tana haushin,kuma koda mai aikinta takai mata abinci tare da autarta Momin Fadila ai da gudu suka dawo cikin falon suna ihu,kasancewar basu kulle ƙofar ba saboda tsoran da ya cikasu,itama ta biyosu tana rarrafe kamar kare tana musu haushi,ai nan da nan aka cicciɓeta zuwa cikin ɗakin tare da saka key.




Washe gari kamar yadda Baba Garba yace za'ayi rabon gadon,haka kuwa akayi,Malam Bala mai Carbi ne yayi rabon gadon tare da bin ƙa'idojin rabon gadon wanda yazo a cikin Al Qur'ani mai girma.Babu ƙarya Alhaji Sani mai kuɗi ne sosai domin kowanan ya tashi ta dukiya mai tarin yawa,Umman Sa'eeda sai washe baki ake,yaran Haj. Zulfa'u ma sunyi murna da wannan gabon gadon,sannan su Uncle Hassan sukayi shirin komawa gida a ranar saboda masu uzururruka a cikinsu,haka suka amshi lambar juna tare da alkawarin ziyartar junansu,shiga motoci sukayi tare da ƙara yin sallama suka dugunzuma zuwa Kebbi State cike da nasara.




Koda suka iso Kebbi anata kiran sallar Isha'i,su Momin Sadam da Umman Sa'eeda suka wuce gidansu Momin Sadam sai sauran suka nufi family house sai zuwa gobe su Uncle Hassan da Malam Bala mai Carbi zasu wuto Kaduna,tun a ranar Uncle Hassan ya fitar da kuɗi don gidan masallatai da rijiyoyi domin ladar takai ga iyayensu.Wannan kenan





          @ @@@@@@@@@@@ 





*KADUNA*




A ɓangarensu Sa'eeda sun koma makaranta semester na ƙarshe kuma shekara ta ƙarshe wato 400 level,yanzu Sa'eeda da motarta take zuwa makaranta wanda Uncle Hassan ya siya mata bayan sun dawo daga Kebbi saboda ba kullum Dr. Nabila take zuwa school ba sai idan tanada lectures,fara ce motar mai shegen kyau ƴar zamani ta manyan mata ga tsada,a ranar da tazo da motar school kowa saida ya ɗasa saboda haɗuwa motar,Sqaud ɗinsu Maryam da Maryam ita kanta saida suka ruɗe saboda sabuwar fitowa ce motan,baƙin ciki kamar ya kashesu musamman Maryam da kawarta Rahma cewa sukayi su ya dace su hau irin wannan motar ba Sa'eeda ba.




Bayan dawowarsu daga Kebbi da wata ɗaya da sati ɗaya Sadam ya shigo Kaduna domin ya ƙagara ya fallasa sirrin zuciyarsa ga Sa'eeda ya huta,duk da suna waya lokaci zuwa lokaci amma yaki bayyana mata soyayyarsa,ya bari sai yazo Kaduna ido da ido sai ya sanar mata,Sadam yanama Sa'eeda wata irin soyayya mai tsayawa a zuciya,he loves her with the whole of his heart ji yake anya zai iya auran wata in ba Sa'eeda ba,anya kuwa,bai furta mata soyayyarsa ba yana mata irin wannan mutuwar son to inaga ya furta mata,woooow! Abin zai bada kala.(Hmmm miskili ya faɗa tarkon soyayya,koya zata ɓarke Chasss😂😂😂🙃🙃🙃)




Shigowan yamma Sadam yayi Kaduna,har wurin parking motocin suka tsaya,sai aka buɗe mishi ya fito,tare da amsawa mai gadin wanda yake ta fama washe bakinsa kamar gonar audiga saboda duk sanda Sadam yazo gidan sai ya mishi kyautar kuɗi,ilai yauma ya mishi kyautar kuɗi tare da shigewa cikin gidan su suma bodygaurds da Mukhtar suka wuce boys quaters don hutawa.




Sa'eeda na zaune a falon daga ita sai doguwar riga wacca ta ɗan kamata kaɗan taji sallamarsa ciki-ciki kamar bazaiyi sallama ba,ji kake Rasss!!! Zuciyarta ta bada saboda jin muryar wanda yayi sallama,ai da sauri da tashi don ta sako hijab saboda rigar jikinta,kafin ta wucd ya shigo cikin falon,kallonta ya fara yi sama da ƙasa kamar ya samu television tare da ƙarasa shigowa cikin falon,bata bari ya karasa zama ba ta ruga sama da gudu shi kuma idanunsa kyar a bayanta tana gudu,murmushi yayi sannan ya samu two seater ya zauna tare da ɗora ƙafarsa ɗaya akan kujeran,yana a haka saiga Dr. Nabila da sauko ƙasa zuwa falon,murmushi tayi tare da cewa




"A'ahh Autan Mom ne a gidan namu,yau ga wata sabon gani,hmmm koda yake nasan ba wurina wallahi kazo ba Sadam"




"Kai Aunty to wurin wa zanzo ni Sadam"



"Hmmm ɗan bariki wato yawo da hankalina kakeso kayi ko,to ai na daɗe da ganoka,wurin Sa'eeda kazo ba wurina ba na fito maka fiti "




Murmushi Sadam yayi tabbas wurinan Sa'eedarshi yazo,wurin Sahibar zuciyarshi yazo,can yace mata




"Bakiyi karya ba Aunty wurin my Darling Star nazo"




"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'una ni Nabila yau na haɗu da yaron zamani!!! Sadam!!! Sadam!!! Sadam!!! Bakaji kunyar idanun ba kake kiran Sa'eeda da Darling Star!!! Ohh ni Nabila!!? Yaushe Sadam kayi baki haka!!! Ina ka ajiye miskilancin Sadam!!! "




Hannuwanta bisa ƙirjinta take maganar,shi kuma mai zaiyi inba dariya ba harda bubbuga ƙafa,yana cewa




"Miskilanci Huhh!!! Ina miskilanci a ko'ina amma banda wuri biyu,daga Momina sai Sa'eeda sukaɗai ne bazan iya nuna musu miskilancina ba"




"Ehhh lallai Sadam wato mu ka raina ko,ai yayi maka kyau,fatan dai ba soyayyar karya zaka nunawa Sa'eedata ka gudu don nasan ku maza akwai yaudara"



"Inaaa Aunty bana haɗa taura biyu a baka,ki kwantar da hankalinki domin Sa'eeda ita kadai ce a cikin zuciyar Sadam Autan Momy"




"Maa shaa Allah,kai naji dadin haka to tsaya ma,wai ka sanar mata da soyayyarka ko kai kaike kiɗinka kake rawarka "




"Ai shi ne ma maƙasudin zuwana Kaduna don in sanar mata abinda ke cikin zuciya,don Allah ki tayani addu'a Allah ya ɗorani akanta ta amince da soyayyarta,saboda ina mata mutuwar so Aunty ni har mamaki abin yake bani yau ni nake ma wata ƴa mace so irin na ko a mutu ko ayi rai,it's really suprising me Aunt''




" Haka Allah yake yinsa,karka damu in shaa Allah Sa'eeda zata soka sai dai ba irin yadda kake mutuwar sonta"




"Allah yasa,no need ta soni exactly yadda nake sonta but atleast ta amince da soyayyarta,gradually zan koya mata sona"




Haka sukayi ta hira har wurin magrib amma Sa'eeda taƙi fitowa zuwa ƙasa sai faman ƙyalla ido Sadam yake sama ko zaiga fitowarta amma ina, mutunir kunya take ji,haka ya haƙura ya wuce masallaci wanda bashi ya dawo cikin gidan ba sai bayan Isha'i,koda ya shigo falon daman shi suke jira suci abinci daman haka al'adar gidan take, a tare a dining table ake cin abinci baki ɗaya,koda ya zauna a dining room sai rarraba ido yake ko zaiga Sa'eeda amma bata fito ba,bai daɗe da zama ba saigata ta fito daga kitchen tare da jug a hannunta,ajiyewa tayi a kan table ɗin sannan ta samu kujera ta zauna,a nutse suke cin abinci,baka jin motsin komai sai cokulla,idanun Sadam kyar akan Sa'eeda, duk yabi ya cikata da ido,ita ko sai faman juya cokalinta take tana yakutar abincin saboda she feels uncomfortable idan ana kallonta,gashi ya kafeta da mayun idanunshi,kai wannan mutum idan maye ne wallahi ya kamaka ka shiga uku,Dr. Nabila ne ta fara tashi,sai twins,Kauthar ma tashi tayi,ganin ita ƙadai ta rage sai tayi saurin miƙewa tare da tattara kayan zata kai kitchen,shima tashin yayi yana cewa





"Let me help you"



"A'a karka damu zan kwashe kayan"




"Taya bazan damu ba ina ganin lifeline ɗina na aiki"



Saurin juyo idanunta tayi tana kallonsa shi kuma sai ya kashe mata ido ɗaya,Ras! Kirjinta ya bada,a zuciyarta tana cewa 'Wayyo ni Sa'eeda wannan wani irin mutum ne haka' can ta ƙwallama Jamila mai aikinsu kira,da sauri tazo,ce mata tayi ta kwashe kayan ta wanke su,tattaro kayan Jamila tayi tare da kaisu kitchen ita kuma Sa'eeda ta wuto falon,shima Sadam ɗin bayan ya biyo zuwa falon kamar *raƙumi da akala* koda suka zo falon basu samu kowa ba,ashe Dr. Nabila ta tattara yaran zuwa sama saboda suji daɗin tattaunawa,a one seater ta zauna shima sai ya zauna kusa da kujerarta,shiru sukayi na ɗan wani lokaci sai can Sadam ya fara magana



"Sa'eeda"




Kallonsa tayi sannan ta duƙar da kanta,cigaba da maganarsa yayi



"Sa'eeda nazo ne da ƙoƙon barata a gareki,ina neman alfarma a gareki Sa'eeda, zuciyata ke take so da muradi,da sonki nake kwana kuma dashi nake tashi Sa'eeda, Shin Sa'eeda za ki iya aurena? "




Darammm!!! Dammm!!! Dadammmm!!! Haka ƙirjin Sa'eeda ya bada sauri kallonsa tayi don tabbatar da maganar daga bakinsa take fitowa,sassanyar murmushi ya sakar mata ta da cewa




"Ki soni Sa'eeda koda bai kai kwatan-kwatan son da nake miki ba,I love you with every beat of my heart,ina miki son da ban taɓa yima wata ɗiya mace a duniya,please Sa'eeda kice kina sona kuma za ki aureni don Allah Sa'eeda"



Saukowa yayi daga saman kujerar haɗi da saka gwiwan biyu a kasar yana kallonta,tare da hade hannunsa waje guda yana cewa




"Ni Sadam Dauda Ghali Mai Nasara,na ɗau alkawari bazan taɓa yaudararki ba,ko kuma na daina sonki har ƙarshan rayuwata,please Sa'eeda ki amince da soyayyarta, don Allah kice za ki aureni"




Mamaki ne ya cika Sa'eeda yau Sadam ne ke rokonta akan ta amince ta soyayyarsa kuma tace zata aureshi,what the hell is going on! Sadam da kansa,shiru tayi still taki ɗago kanta saboda jin abun tayi banbaraƙwai,babba dashi haba,katse mata tunani yayi ta cewa





"Sa'eeda amsarki nake jira"




Shiru ta sake yi,to ita mai zata ce mishi *Eh ko A'a* idan tace a'a tabbas tayi karya domin itama tana jin wani abu akansa tun ranar da ta fara ganinsa,idan kuma ta ce Eh nan ma ta zubar da class ɗinta,amma bari ta gani,can kuma sai ta fara magana cikin sassanyar muryarta da cewa




"Kabari inyi tunani akai"




Shit Men!!! Ba haka yaso ji ba yaso tace *Eh ina sonka kuma zan aureka* gaskiya bazai yarda da wai sai tayi tunani ba,ce mata yayi




"A gaskiya bazan iya jira sai kinyi tunani ba,in kuma ba so kike ki jini a gadon asibiti ba"



Zaro idanu tayi waje jin abinda ya faɗa,gyada mata kai yayi sannan ya cigaba da cewa




"Eh I mean it Sa'eeda, please just say it"




Shiru tayi sai can ta ce



"Zan faɗa maka ta waya amma a gaskiya I can't tell you face to face"




"Fine,Allah yasa naji alkhairi, yanzu tashi ki shiga ciki dare yayi"



Babu musu ta mike zuwa sama ba tare da ta juyo ba,shi kuma sai binta da kallo yake harta haura saman,sai daga baya ya wuce masaukinsa.A daran ta sanar mishi da ta aminci da soyayyarsa sannan kuma zata aure shi, *Daɗi kasheni!!!* farin ciki iya farin ciki Sadam ya shiga,sallar dare yayi tare da mika godiyarsa ga Allah daya ƙaddara Sa'eeda ta aminta da soyayyarsa.




Tun daga ranar Sadam da Sa'eeda suka buɗe shafin soyayya mai kyau da tsari,a haka har kwanakin da ya ɗiba suka ƙare,yau yayi shirin komawa Kebbi amma bada wuri ba,saida sukayi sallama sannan Sa'eeda taja motarta zuwa school kasancewar ba da wuri Dr. Nabila zata shigo school ba.





A makaranta kuwa ɗalibai ne suka fito daga classes saboda lokacin sallar Zuhr yayi,Squad ɗinsu Maryam ne suke tafiya suna hira harda ita Maryam ɗin,suna cikin hirar ne sai ga wasu baƙiƙyan motoci manya-manya har uku sun jero cikin makarantar har wurin department ɗinsu,Cak! Suka tsaya suna jiran suga suyawa suka shigo makarantar,can sai idon Rahma yake kan numban mota daya sai taga an rubuta *SADAM 001* da manyan haruffa ƙara kallon sauran motocin tayi sai taga iri ɗaya ne,taɓo sauran tayi tana nuna musu abinda ta gani cike da mamaki suka tsaya ganin mai motocin, bodygaurds da Mukhtar ne suka fito daga motan,sai wani daga cikin bodygaurd ɗin ya buɗe kofar da Sadam yake ciki,ƙafarsa ɗaya ya fara fiddowa saida yake tsawan wasu mintuna sannan ya fito complete




"Wooooow!!! Ingarman namiji!! "



 cewar Rahma wacca taji duk duniya babu wanda takeso sai shi,sauran ma haka suka bishi da kallo kai bama su kaɗai har wasu matan da majan haka suka tsaya ƙiƙam!! Sunyi cirko-cirko suna kallonsa, shi kuma ko ajikinsa domin ya saba,wayarsa ya ciro tare da kiran Sa'eeda bugu ɗaya-biyu ta ɗaga kiran da mamaki,magana ya fara da cewa




"Ki fito outside class ɗinku ina jiranki"




"Ehhh kazo school ɗinmu ne"




"Eh mana to ban gaji da kallonki ba shiyasa kawai nace bara na kara kallon kyakkyawan fuskarki kafin na wuce Kebbi"




"Wayyo ka kasheni Sadam,haka ka shigo da motocinka cikin school ɗin ko"



"Eh mana, kinga kefa nake jira kar muyi dare a hanya"




A jiye wayar tayi sannan ta fito, dayake Iman batazo school ba shiyasa duk taji school ɗin babu daɗi,kamar wacca kwai ya fashe mata a ciki haka ta nufi inda yake, shi kuma tun daya ganta ya fara sakin murmushi,inda yake kallo yana murmushi kowa yakai idonsa,Dummm!!! Haka ƙirjin Maryam da Rahma ya bada kar dai ace wurin Sa'eeda yazo,kai!! Tabɗijan ai wani malolon baƙin ciki ne ya tsaya a wuyan sqaud ɗinsu Maryam musamman Rahma da Maryam,daga ganinsa kasan mai kuɗi ne na gaske cewar Maryam a zuciyarta.(Ni kuma nace sai ma kinji ance shi ne *CEO* na kamfanin da mijinki Sauban yake aiki a lokacin zaki saduda😂😂😂🙃🙃🙃)

 



Haka suka kwashe kusan mintuna 20 kafin sukayi sallama ta wuce class ko a jikinta,saboda yanzu ba kamar da bane,bata daukar raini ko kaɗan,su kuma Maryam suka ja ƙafafunsu zuwa mallaci.Wannan kenan




           @@@@@@@@@@




A ɓangarensu su Umma Kande da Maman Jummalo kuwa komai yana musu normal-normal kaɗan kasancewar yanzu cacan kuɗin pampers sukey babu ji babu gani,Abban Sa'eeda kuma yana ƙoƙari wurin cefane babu laifi,su Iklima da Jummalo kuma sun dage da zuwa Islamiya sun baida hankali sosai,sannan idan suka dawo suna koyama Maman Jummalo da Nusaiba saboda itama tayi nadama sosai kullum cikin kuka da neman gafarar Ubangijinta take,saboda laifuffukan da ta aikata.Duk wannan nadama da kowa yakeyi banda Umma Kande ita har yanzu cewa take asiri aka mata da yaranta,su Maman Jummalo dasu Iklima sunyi wa'azin sun gashi sun zuba mata idanu.A ɓangaren cikin Maman Jummalo ya isa haihuwa,don tun watan jiya suke saka ran haihuwarta amma shiru.




Yau Maman Jummalo ta tashi da naƙuda zanga-zanga,a rude su Umma Kande da su Iklima da Jummalo suka tafi da ita asibiti aka bar Nusaiba a gida,koda suka isa asibitin da sauri nurses suka amsheta zuwa *Labour room* saboda haihuwar ta taso mata.




A cikin labour room ɗin nurses uku ne suke taimaka mata wurin amsar haihuwan wanda Maman Jummalo tasha bakar wahala kafin ta haihu,nurse ɗin da take a wurin da yaro ya fito hankalinta tayi matuƙar tashi jin *kukan jaki* to a ina haka? Mamaki ne ya cika sosai, to a ina aka samu jaki ne haka,saiwsta ɗayar nurse ce wacca take kusa da ita ta ƙwalla abun ƙara tana nuna wurin da yaro ya faɗo...........






Mu haɗu a pages na gaba my Esteem fans,🙃🙃🙃✍️✍️✍️🌼🌼🌼




*tofa a ina aka samo jaki kuma har cikin asibiti??? Mai ya assasa ihun nurse ɗin nan sannan mai take nunama sauran nurses ɗin???*......






*Da alama Sadam ya ajiye miskilancinsa agefe,ko ya irin soyayyar tasu zata kasance???*....





*Haj. Zulfa'u an koma karya😂😂😂,wai ya yaranta zasu ƙare ta haj. Zulfa'u???*.........





*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥





*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘

Post a Comment

0 Comments