TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 43-44

 4⃣3⃣----4⃣4⃣




Yauma zaune suke a ƙofar ɗakinsu Sa'eeda kasancewar tunda Sa'eeda tayi musu sallama ƙofar ɗakinsu ya koma wurin shan iskarsu,Umma Kande ce  ta kasa haƙuri ganin yadda ƙawarta ta koma gwanin ban tausayi,cikin sanyin murya Umma Kande ta fara magana


"Ƙawas anya ba komawa wurin boka Sankeru zamuyi ba,ko za'a samu wata mafitar game da cikin nan? "


Maman Jummalo ce ta mata wani mugun kallo  tare da cewa


"Haba kawas yanzu abinda ya faru dani bai ishemu ishara ba,nidai na daina zuwa wurin boka in shaa Allah, zan nema gafarar Ubangijina akan laifukan da nayi masa a baya,domin cikin nan nawa ishara ce Allah ya nunamin,a farko Allah ya sanya ishararsa akan ƴaƴanmu amma bamu gani ba kuma bamu dandara ba muka sake zuwa wurin boka,shiyasa yanzu ya sake saukar da ishara babba a kaina,domin sai yanzu nasan zuwa wurin boka babban asara ne,amfaninsa na ɗan wani lokaci ne gajere,kinga Ƙawas mu tuba ga Allah sannan mu naimi yafiyarsa,ko ma rabauta ranar gobe ƙiyama,wacca don ita kike zuwa wurin bokan tabar mana gidan ai"


Taɓe baki Umma Kande tayi tare da turo ɗan kwalinta gaba sannan ta fara magana


"A'aa hahhh! Hasfy ai saiki cemin kin koma malama ustaziya bagadadiyyah,wannan wa'azi haka Allah yace Annabi yace saikace matar Sudais na Makkah,hmmm to bari kiji Hafsy, ni Saratu jikar Sarkin ruwa yanzu na fara zuwa wurin boka,babu gudu babu ja da baya,zuwa wurin boka sai inda mai ya ƙaremin,domin zuwa wurin boka yamin rana babu abinda zance sai godiya,kika sani idan mukaje wurinsa mu samu mafita game da wannan cikin? "


"Allah ya tsareni ni Hafsy na ƙara zuwa wurin boka don neman biyan buƙatuna,bokan daya ɗirkamin ciki shi ne zai nemamin mafita,inaaa babu ni a cikin wannan saɓon,ishara ce Allah ya nunamin kuma nagani na ɗauka masu hali irin nawa ina roƙa musu shiriyar Allah"


Tafi Raf! Raf! Raf! Umma Kande tayi harda buga cinya tare da sheƙawa da wata ƴar bazawarar dariya irin na ƴan bariki tana cewa


"Ahayyeee Chasssss!!! Hasfy yaushe kika tuban da zaki roƙama wasu shiriyar,kin tabbatar da  tuban naki ta amsu,wai wai wai ni jikanyar sarkin ruwa,kodai na dauko miki lasifikan masallanci layi ne ki fara wa'azin Hafsy"


"In shaa Allahu karɓabɓiya ce domin har cikin zuciyata nayi nadama,kema Ƙawas ya kamata ki tuba,domin ita wacca kike don ita da ƴarta basa gidan hasalima bakisan a wace duniyar suke ba,mai zaisa ki cigaba da ɓata lokacinki ƙawas,sannan ni ba wa'azi nake miki ba gaskiya tsagwaronta nake faɗa miki domin wannan rayuwar ba matabbata bace,yau kaine gobe ba kai bane,mai zaisa muyita ɓata lokacinmu muna ɓata rawarmu da tsalle,lokaci na ƙara ƙure mana"


"To! to! Ustaziya Hafsy naji wa'azin,Allah ya karɓa,sai kibari lokacin watan Ramadan idan ya kama sai a nemo miki mai ja baƙi ke kuma kina fassarawa,bari kiji nifa ƙiyayyar Umman Sa'eeda da ƴarta a jinina take,banga abinda zaisa na janye makaman yaƙina akansu ba,koda suka bar gidan nan ba yana nuni da na haƙura da bibiyar rayuwarsu bace,a'a yanzu ma wani sabon aikin nakeso ayi musu ita da ƴarta akan karsu dawo gidan nan  har abada,shiyasa nace mu ƙara zuwa wurin boka kinga kema saiki kai taki matsalar akan batun cikin"


"Allah ya sawaƙe ni Hafsy da ƙara zuwa gun wani zindiƙin ƙato don biyan wata buƙatata yanzu,da Allah na dogara,kuma nasan shi zai biyamin buƙatuna"


Huro gajerun hancinta Umma Kande tayi tana sake taɓe baki tare da cewa


"Awo Allah!!! Lallai kuwa!! Au yanzu ne kika san zuwa wurin zindiƙin ƙato bayi da amfani Hafsy, da can da kike zuwa bakisan da haka ba sai yanzu,hmmm abin da ban mamaki"


Haka   Umma Kande da Maman Jummalo sukaita musayar baki akan zuwa wurin boka, ita Umma Kande tanaso ta sake dulmiyar da Maman Jummalo,ita kuma Maman Jummalo na mata wa'azi akan ta tuba ta koma ga Allah tunda wacca take zuwa wurin boka don ita tabar mata gidan.


A ɓangaren yaransu Jummalo da Iklima makarantarsu suke zuwa  safe da rana,ko samari ma basu kulawa balle ayi maganar aure,kai in taƙaice muku dukkaninsu tsoron maza suke yanzu(su Iklima anji maza😂😂😂🙃🙃🙃),ji suke idan sukayi wani auran komawa gidan jiya zasuyi.Kasancewar ajin matan aure  Jummalo da Iklima suke,basa shiga sabgar ƴan ajin saboda duk sun girmesu sosai wasu ma zasu iya haihuwarsu.


Iklima da Jummalo suna zaune a aji suna jiran malami ya shigo,kunnan Iklima ya yajiyo mata abinda ya kusa birkita mata lissafi wato Maman Jummalo nada ciki cikin ma na boka,wata ce a bayansu take sanar ma matan suna dariya harda shewa.Da sauri Iklima ta taɓo Jummalo haɗi da ce mata ta saurara abinda ake faɗa a baya,babu musu Jummalo ta kasa kunnanta don taji me ake cewa,ai wani irin Damm!!! Darammm!! Damm ƙirjinta yayi,jin wata a cikin matan na cewa Mamanta nada cikin boka shiyasa yanzu take saka niƙaf.Da sauri Jummalo ta miƙe tana kallansu,jikinta na rawa zatai magana Iklima tayi saurin rufe mata baki dan tasan idan batayi haka ba,matan auran zagesu tsaf! zasuyi ciki da waje tare dayi musu gori saboda halin iyayensu,gwara tun kar ayi karma a fara,jan hannunta tayi zuwa waje tare da ɗaukar jakan makarantarsu,wucewa gida sukayi,Jummalo babu abinda take inba kuka ba,tana mamakin wai yau mamanta ce da cikin boka a jikinta sannan ita kuma zata samu ƙanwa daga tsatson boka,wayyo wayyo ni Jummalo,wannan wace irin ƙaddara ce ta samesu haka rana tsaka,a haka suka iso gidan Iklima na faman bama Jummalo haƙuri akan tayi shiru mutane na kallansu amma ina bata mutane take ba,ita ta wannan ƙaddarar da ta samesu ne hankalinta yake.


Shigo gidan su Jummalo sukayi afu jajan hankali tashe,Umma Kande suka taras tana zaune ita kuma Maman Jummalo ta kewaya bayi,Jummalo ce cikin kuka ta ce


"Umma Kande da gaske ne mamana nada cikin boka a jikinta"


"Waya ce miki Jummalo" cewar Maman Jummalo wacca fitowarta kenan daga bayi


"A Islamiya ne muka ji matan aji suna zancen cikin boka harda dariya da shewa a lokacin malami bai shigo aji ba" cewar Iklima



Shiru Maman Jummalo tayi tana kallon ƴarta,ita tama rasa wasu haruffa haɗi da kalmomi ne ya dace ta tattaro wurin gina  jimlolin da ta tabbata zasu bada ma'ana tare  da  fahimtar da ƴarta ƙaddarar da ta samesu,babu yadda suka iya,Umma Kande ce ta katse shirun da sukayi,tana cewa



"To mene ne abin kuka Jummalo, ai matsalar daga mamanki ce,tuntuni nace mata mu ƙara zuwa wurin boka ko za'a dace cikin ya fita amma taƙi,ita ga mai tsoran Allah wai ta tuba da zuwa wurin boka,kinga kuwa ai dole a dinga gulmarku tare da zunɗanku akan wannan cikin"


Cikin fushi Maman Jummalo ta ce


"Haba ƙawas ya kuma ina neman yadda hankalinta zai kwanta ba tare da tasan abinda ke faruwa ba,ke kuma kina neman canjamin alƙalami,haba ƙawas a gaskiya banji daɗin abinda kikayi ba,ƙaddara ce kuma tana iya faɗawa kan kowa,kinga Jummalo abinda matan ajinku suka faɗa a kaina gaskiya ne,ishara ce Allah ya nunamin game da zuwa wurin boka,na tuba na koma ga Ubangijina,ita ma ƙawas naso ta gane ishara ce Allah ya nuna mana amma taƙi,ya zanyi da ita"


Gyara ɗaurin girji Umma Kande tayi,sannan ta kakkaɓe tabarmata haɗi da cewa



"To Malama  Ustaziya Hafsy jikar Sudais idan kin gama wa'azin, Allah ya bada lada,ni nayi ɗaka"


Binta sukayi da kallo,sai can Jummalo ta ce


"Naji daɗi da kika gane abinda tun tuni muke fatan ku gane akan illar zuwa wurin boka,daga yau kome ƴan aji zasu ce game daku,bazamu sake tankawa ba"


"Hakane kuwa Jummalo, kar mu biye musu, kawai maida hankalinmu akan karatunmu"cewar Iklima


Haka dai su Jummalo da Iklima suka cigaba zuwa Islamiyarsu,sannan tun daga ranar suka dena biyewa ƴan aji,ko kuma ƴan layi.Wannan Kenan



            @@@@@@@@@@@@




*ABUJA*



Wani irin ƙasurgumin daji ne Haj. Zulfa'u ke faman gudu a cikinsa,ko'ina na dajin duhu ne babu haske,ga wani irin baƙaƙyan tsuntsaye masu yawan gaske a kan bishiyun dajin suna wani irin kuka babu daɗin ji balle sauraro,ciyayin da suke a dajin masu ƙayoyi ne,duk takun da Haj. Zulfa'u zatayi sai ƙara ta soketa,amma ba jin zafin sukar da ƙayan taimaka take  ba a'a mutanan da suke tunkarota ne take jin tsoronsu tare da fargabar kar su cimmata,amma ina gudu Haj. Zulfa'u take kamar ba gudu takeyi ba,kamar wuri ɗaya ne take babu canji ga wa'inan mutanan ƙara kusantota suke ,dukkaninsu da fararan kaya,ga wani irin haske na baibaye dasu,a sama suke tafiya ba tare da ƙafarsu ta taka wa'inan ƙayoyin ba,tana wannan gudun ne sai gasu sun cimmata har gabanta.Dariya suka fara yi babu ƙakƙautawa,sunayi suna nunata,ita kuwa sai uban haki take tana rufe idanunta saboda haskensu dayake kashe mata idanu.Mace ce mai tsohon ciki ta riƙe hannun wasu ƴan biyu maza,sai  kuma wasu ƴan biyun Mace da Namiji amma manya ne sosai don zasu wuce shekara talatin da takwas a duniya,su kuma suna gefe ɗaya.Matar nan mai ciki ta fara magana cikin amon muryarta mai firgitarwa


"Zulfa'u!!! A tunaninki zaki iya guje mana ne!!! A tunaninki dubararki zatasa kar mu cimmiki ne!!! A tunaninki hangen nesanki zaisa bazamu iya taddoki bane!!! Inaaa Zulfa'u kinyi kuskure!!! Kuskure babba!!! Domin kuwa kin yanke bishiya amma kin manta baki haɗa da tushanta ba!!! A lokacin da ƙwaƙwalwarki ta raya miki bishiyar ta bushe ta zama itáce babu genyan,sai kuma a lokacin Allah ya tayar da tushan nan ta baki cire ba,sannan tushan ya zama reshe biyu mabanbanta,wanda gefe daya da ganye wani gefan babu ganye,sai kuma Allah ya ƙara nufinsa da mayar da reshan mara ganye ya zamu mai ganye hadi da kusanto da rassan guda biyu wuri ɗaya!!! Dubararki ta ƙare Zulfa'u!!! Alƙalamin rubutunki ya ƙare domin zasu dawo ɗaukar fansa Zulfa'u!!! Zasu dawo nan kusa Zulfa'u!!! Ƙarshanki ya kusa zuwa Zulfa'u!!! Kinga Tushan da kike manta baki cire ba can!!! "


Nuna wa'inan ƴan biyun mace da namijin tayi,duk a lokacin Haj.Zulfa'u hannunta na kan fuskarta ta kare idanunta saboda hasken mutanan, mai cikin ne ta cigaba da cewa


"Ki jira ƙarshanki Zulfa'u!!! Rassan nan suna nan dawowa!!! "


Dariya suka cigaba dayi suna nunata harda ƴan biyun nan maza dake riƙe a hannun mai cikin suma dariyar suke, sai kuma Difff !!! Mutanan suka ɓace,ihu mai ƙarfi Haj. Zulfa'u ta fara tana cewa


"Karku dawo!!! Karku zo wurina!!!"


A gigice Haj. Zulfa'u ta farka daga mummunan mafarkin da tayi babu salati balle sallallami sai ba kiran Boka Burumbuɗu don ya kawo mata agaji(Wa'iyazubillah🤔🤔🤔)


Mafarkin akwai  firgitarwa da bada tsoro sosai,dube-dube ta fara yi don tabbatarwa ko ba'a cikin wannan ƙasurgumin dajin take ba,ga duk ilahirin jikinta ya jiƙe da gumi kamar wacca ta fito daga wanka,tashi tayi tare da kunna wutar ɗakin,agogon ɗakin ta duba haɗi dazaro idanu waje ganin ƙarfe 2:35am na dare,wannan mummunan mafarkin ya sameta.Haka ta zauna ƙirjinta da dukan tara-tara tana tunanin me zatayi ganin kar tsatson maƙiyiyarta su cimmata, don idan suka cimmata ta tashi aiki kenan,domin ƙarshanta ne zaizo,tunani ne kala-kala fal a ranta,ta rasa ƙwaya ɗaya da zata ɗauka,kowace hanya idan ta ɗauka saita karkace ta kasa bullewa,ta kasa kawo mafita akan wannan matsalar da take ci mata tuwo a ƙwarya,ta hanata rawar gaban hantsi,kar dai ace reshe ne ke shirin juyewa da mujiya,wayyo!!! Da shikenan tata ta ƙare babu sauran wata rina a kaba.Haka tayita tunani har daga ƙarshe ɓarawo bacci ya sureta batasan da zuwansa ba.


Washe gari haka ta tashi da kasala tare da ɓacin rai,jinta take kowama ta tsane shi illa ahalinta,ji kake kamar da hallaka duniya ta zauna ita kaɗai da ahalinta,haka ta shirya zuwa downstair domin karin kumallo.Kasancewar bikin Fadila ya ƙarato yanzu baifi saura sati biyu ayi bikin ba,har ƴan biki na nesa sun fara zuwa wato ƴan uwanta na Niger dayake mahaifin Haj. Zulfa'u ɗan asalin Niger ne,ci-rani ne ya kawoshi Nigeria har Allah ya ƙaddara zaman a Nigeria.


Haka  lokacin biki yayita ƙaratowa,ƴan uwa na nesa dana kusa duk sunzo,har da ita uwar gayyan wato Fadila da iyayenta sun iso Nigeria. Haka aka sha shagulgulan bikin Fadila tare da programmes kala-kala,duk wannan shagulgulan bikin da aka sha Haj. Zulfa'u jininta a ƙumba yake domin tsoro takeji kar  tayi arangama da tsatson maƙiyiyarta ta banu,haka aka kammala biki lafiya tare da kai amarya gidan mijinta wanda a satin ya wuce da amaryarsa Jordan inda yake aiki.Wannan kenan.




           @@@@@@@@@@@@@



*KADUNA*



A ɓangarensu Sa'eeda,tunda Ummanta da Momin Sadam suka ƙetara zuwa India ta koma gidan Dr. Nabila da zama wanda yake a ƴan Majalisu,gidan babba ne sosai mai hawa ɗaya,akwai garden da swimming pool a ciki,ga wurin parking motoci babba wanda sai iya cin motaci harda biyar,kai na taƙaice muku,gidan ya haɗu iya haɗuwa.



Wani hadadɗan ɗaki mai bayi a ciki Dr.Nabila ta ce Sa'eeda ta zauna,kunsan ni da bin ƙwaƙwaf,haka nima na shiga ɗakin don kashema idona kwarkwata,wooow!!! Aljannar duniya, gaskiya ko amarya sai haka,don ɗakin ya haɗu iya haɗuwa.



A washe garin ranar Dr.Nabila takai Sa'eeda saloon tare da wurin gyaran jiki,nan da nan Sa'eedarmu ta koma kamar ƴar larabawa,sheƙi kawai fatarta take,ga gyaran gashi tasha sai tace amarya,tafito yayi kyau abinta kamar ka saceta ka gudu,wunin ranar a saloon da wurin gyaran jiki Dr. Nabila da Sa'eeda suka ƙare sai wurin 5:40pm suka wuce makarantarsu Jawaad da Jadwa wato twins wa'inda basu wuce shekara 13 ba sai ƙaramarsu Maimuna mai sunan kakarsu Sa'eeda amma ana kiranta da Kauthar,hada suka ɗunguma zuwa gidan.



Kullum sai sunyi waya da Ummanta a wayar Momin Sadam Kasancewar yanzu jikinta yayi sauƙi sosai,a nan ne take sanar ma Sa'eeda daga India zasu wuce Saudiya don aikin Umrah kafin lokacin Hajji yayi sai ta koma,daɗi kasheni haka Sa'eeda takeji aranta ashe faɗin hausawa da suka ce *BAYAN WUYA SAI DAƊI* ba ƙarya bane,gashi yanzu duk wahalar da suka sha a baya ta zama labari,Suna cikin farin ciki da annashuwa,ga ci mai kyau,sha mai kyau,tufafi mai kyau,gida mai kyau,babu abinda zasu ce sai Alhamdulillahi.



A ɓangaren makaranta kuwa,tare suke zuwa da Dr. Nabila tana riƙe da jakar Dr.Nabila duk inda zata,ranar farko ƴar aji sunyi gulma sosai kamar bakinsu zai koma na zaɓa,kasa haƙuri Iman tayi ta sanar musu  cewa Dr.Nabila Auntyn Sa'eeda ce haka mijin Dr.Nabila kawun Sa'eeda ne,Kasancewar Dr. Nabila na gab da fita daga ajin  Iman tayi magana,cak! Dr. Nabila ta tsaya,tambayar Iman tayi what's going on daya sakata faɗin haka,Iman bata ɓoyema Dr. Nabila cin kashin da ƴan aji sukama Sa'eeda ba harda Cin amanar da Maryam tama Sa'eeda saida Iman ta faɗama Dr. Nabila duk da Maryam kwana biya ta rabu da zuwa school. Ɓacin rai iya ɓacin rai Dr.Nabila ta shiga,zazzagama ƴan aji ruwa masifa da bala'i Dr. Nabila tayi haɗi da cewa da sun san suwaye ahalin Sa'eeda da kullum idan tazo aji russunawa zasu dungayi suna gaidata domin ita ƴar dangi ce gaba da baya sannan ahalinta gogaggun ƴan boko ne kun cikakkun ƴan kasuwa wa'inda sukayi fice a duniya bama Nigeria ba, tun daga ranar ƴan aji basu sake gulmar Sa'eeda ba hasalima janta a jiki suke ita.



Kasancewar yau Dr.Nabila bata da lecturs bata je school ba,Sa'eeda ta fita da motarta zuwa school don yanzu Sa'eeda ta iya tuƙin mota sosai,jiran Uncle Hassan take ya dawo ya siya mata mota dayale yace yana dawowa sai siya mata ita mota tunda ba kullum Dr. Nabila take zuwa school ba sai in tana da lectures,kasancewsr da wuri aka tashesu,haka ta nufo gida bayan taje supermarket tama su twins shopping,danno motarta tsyi cikin layin sai taga jerin motoci har uku baƙaƙe a wurin gate ɗin gidansu,mamaki ne ya cikata,baƙi sukayi a gidan da alama,sai kuma idanunta suka kai kan numban motar wanda aka  rubuta *SADAM 001* a matsayin numban motan,tsaki taja tana ƙunƙuni ita kaɗai tana cewa



"Sun wani zo sun ajiye motacinsu a gaban gidan mutane,mtwss! "



Haka taja motarta zuwa gate ɗin gidansu,horn tayi da ƙarfi sai mai gadi yazo da sauri ya bude mata gate,danno motarta tayi cikin gidan har inda ake parking ɗin motoci,saida ta kashe motar sannan ta fito,ƙirjinta sai bada Dummm! Dummm! Dummm! Yake ta rasa dalili,haka ta ƙarasa cikin falon da sallama haɗi da ƙwalla ma Kauthar kira da twins tana cewa


"My Twins!!! Kauthar where are you guys,I come with some  chocolates for you guysss!!! "



Cikin muryarta mai shegen daɗi kamar ana *Busa Sarewa* haka maganarta take fita.Sadam da tunda yaji an ƙwaɗa sallama ƙirjinsa ya bada Dummmmm! Bai taɓa jin murya mai shegen daɗi irin wannan muryar da tayi sallama ba,to wace ce tazo wurin Aunty Nabila mai murya zazzaƙa haka? Bai ƙarasa tunaninsa ba yaji tana kiran twins da Kauthar ai cak! Ya tsaya da danna system ɗinsa tare da kafe idonshi a wurin da yaji sautin muryar na fitowa.Sa'eeda da taji shiru ba'a amsa sallama ba kuma sannan su Kauthar basu zo ba kenan suna upstair,ƙarasowa cikin falon tayi tare da cire gyalenta,sai ta ajiye jakarta tana wani miƙa irin ta gaji ɗin nan,duk wannan bidirin da take Sadam idonshi kar! A kanta,ita ko batasan da mutum ba shiyasa take ta haukanta ita kaɗai harda ƴar rawa(Oh!!! My Esteem Fans ku tayani dubawa Sa'eeda ta koma wata abu daban 😂😂😂🙃🙃🙃)



Sai can taji kamar idanu na akanta,sai tayi saurin kai dubanta gun ai ba arziƙi ta waro manya-manyan idanunta waje tare da cewa.................





Mu haɗu a pages na gaba don cigaba da karanta wannan chakwakiyar chakwalkwali haɗi da  rikita-rikita 🙃🙃🙃🙃✍️✍️✍️✍️




*Tofa🤔Kaiko Sadam wani irin kallo ne haka sai kace maye,mai ya assasa bugawar ƙirjin Sa'eeda da Sadam??? Shin mai Sa'eeda ke shirin cewa jin yadda tayi ta hauka ita kaɗai harda ƴar rawa???*......




*wani irin mummunan mafarki ne Haj. Zulfa'u tayi haka mai firgitarwa haɗi da tsoratarwa??? Suwaye ne tsatson maƙiyiyarta???Wace ce Haj. Zulfa'u*.......




*Da alama Maman Jummalo an tuba,shin Umma Kande taza tuba ko kuwa har yanzu wahala bata ƙare mata ba???*.....




*wai in Nusaiba,a wace duniyar take???*.........





*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥






*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments