TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 17 & 18

 Episode Seventeen: Ungrateful


Hassan ya dauke kai tana bata fuska "kai dai baka da zance sai na mutuwa, kullum sai ka ambaci mutuwa kake jin dadi, at the same time kuma kana gina rayuwa kamar ba zaka mutu din ba. Sometimes I find you confusing wallahi" Hussain yayi dariya "to mutuwa ai dole ce, kullum saka rai nake cewa ba zan kai gobe ba shi yasa bana taba barin abinda zan iya yi yau ince sai gobe, at the same time kuma ina living rayuwata the fullest tunda nasan in na mutun bani da second chance, ina kashewa kaina da mutanen da suke tare dani kuɗi saboda ina ganin basu da wani amfani banda a kashe su din, to inna ajiye me zasu yi min? In na mutu sai dai dangi suyi fada akan su to ba gwara in basu ba sanda nake raye? Ni fa kullum ina addu'ar ka da Allah ya bani kudin da ba zan iya kashewa ba". 



Hassan ya jinjina maganar Hussain a ransa, to ko dai ya bawa Baba gidan nan ne yanzu? Yana tunanin rikicin da zasu yi akan gidan kafin ya karba amma kuma sai ya yanke wata shawara. A iya kacin saninsa da Baba yasan babu abinda yake so sama da iyalinsa, dan haka dasu zaiyi amfani. Ya gama shirinsa tsaf sannan ya yiwa Ruqayyah waya "hello sweetie. Ya gida" ta gyara kwanciyarta tace "lafiya kalau. Ya office?" Yace "na dawo ai tun dazu. Baba yana gida kuwa?" Tace "eh, ya dawo" yace "Okay, ko zaku tambayeshi dake da Sumayya da su Zunnur ku shirya zan zo in dauke ku mu tafi unguwa" ta mike zaune daga kwanciyar da take tace "ina zamu je?" Yayi murmushi "it is going to be a surprise" tace "ina ne dan Allah" yace "to in na gaya miki kuma ai bai zama surprise din ba kenan" 


Tayi rolling idonta cikin takaici, ita bata taba ganin mai zurfin ciki irin Hassan ba, baya taba gaya mata komai, shi hirar sa kawai ta kalaman soyayya ce wanda dasu da kuma kwarjinin sa yake amfani gurin kashe mata baki ta kasa challenging dinsa, amma sam bata jin dadin yadda alakar su take tafiya, sam bata jin dadin abubuwan da take fahimta a tare dashi sai dai ba zata yi magana, ko da zata iya challenging din nasa ma ba zata yi ba saboda kar ya fahimci true color dinta yace ya fasa. Target dinta daya shine a daura auren dai, in ta riga ta shiga gidan sa a matsayin matarsa kuma ai shikenan tana da control over duk wani abu da yake nasa.


Ta tashi ta fita tsakar gida in da sauran yan gidan suke, Baba ya a magana "Zunnur in na dauki albashin wannan watan keke zan siya maka. Saboda ka rage wahalar zuwa makaranta" Zunnur ya tashi da murna yan uwansa suna taya shi, Ruqayyah ta tabe baki, su keke manya. 


Ta durkusa a gaban Baba "Baba dama Hassan ne yayo waya yace mu shirya ni da sauran yara zai zo ya dauke mu zamu je unguwa" Baba ya bata fuska "unguwa kuma? Wacce unguwa?" Ta tabe Baki "nima bai gaya min ba fa, ya dai ce wai wani mamaki zai bamu. Ba zai wuce shopping ne zai kai mu ba" a ranta ta karasa da cewa "it is about time daya kamata ya bude wannan matsatstsen aljihun nasa" 


Baba yayi shiru bai ce komai ba, Inna Ade tace "tunda da sauran yara zasu je ai ina ganin babu komai ko Baban biyu? Kaga bikin ya fara matsowa sosai yanzu haka wani abu ne daya shafi bikin nasu" Sumayya cikin doki tace "baba mu shirya, yanzu haka gidan da zasu zauna zai kai mu mu gani" Inna Ade tace "haka ne kuwa, shi din nema yanzu haka" Baba yace "sai ku tashi ku shirya ai, ku bi a hankali, banda rawar kai banda kwadayi".


Ai kuwa cikin murna suka mike da sauri suka shirya, su Ruqayyah suka yi dressing daga cikin sababbin kayan su suka yi wa juna kwalliy mai kyau, sunyi kuma matukar kyau da yanayin su mai daukan hankali. Sun gama shiryawa kenan Hassan yayo waya cewa gashi nan ya kara so, suka yi wa Inna sallama suka fita tana yi musu fatan alkhairi.


Suna fita ya bude musu mota suka shiga. Ruqayyah ta zauna a gaba kusa dashi su kuma duk suka shiga baya suna hada baƙi gurin gaishe shi. Ya amsa musu individually kowa yana tambayarshi makaranta, sai da suka nutsu suna kus kus a tsakanin su suna santin motar sannan ya juya side din Ruqayyah yace "ranki ya dade" tayi murmushi tana sunkuyar da kanta tace "tare da naka" daga nan bata kuma cewa komai ba, hankalin ta yana kan titinan da suke bi tana lissafin wanne mall zasu je, wanne nema wanda yake tashe yanzu?


Sama sama Hassan yaje hira da kannen Ruqayyah, lokaci zuwa lokaci kuma yana juyo wa ya kalle ta yayi mata murmushi itama ta mayar masa, shi shirun ta da nutsuwarta suna burge shi sosai, wannan yana nuna cewa bata da hayaniya kamar yadda yake so sannan kuma bata da mita.


A kofar gidan ya tsaya, duk suka juya suna kallon gidan with different thought a zuciyoyin su. 

Ruqayyah "wait! What? Ba dai nanne gidan da zamu zauna din ba"

Sumayya "kai!!!, Ji wani gida mai kyau"

Sulaiman "duk sanda na tashi yin gidana irin wannan kofar zan saka"

Zunnur "me muke yi anan?" 


Hassan ya bude motar yana cewa "okay, we are here, kowa ya fito" suka fara fitowa daya bayan daya duk idon su akan gidan, Ruqayyah trying so hard not to scream. Ya dauko key ya bude gidan fuskarsa cike da farin ciki yace "ku shigo, kowa ya zagaya ya gaya min view dinsa akan gidan nan".


Ruqayyah a tsakar gida ta tsaya tana jin kamar kafafuwanta ba zasu iya kaita double door din da taga sun shiga ba, sai da Sumayya ta dawo da sauri ta ja hannun ta. "Zo ki gani, Ruqayyah, har furnitures an saka" Ruqayyah bata ce komai ba ta dai bita a baya kirjinta yana bugawa. 


Ɗakunan guda uku duk an saka musu set din gado masu kyau da labulaye, falon ma an saka set din kujeru irin wadanda ita kanta Ruqayyah ta san cewa bata taba hawa irin wannan kujerar ba amma duk da haka ji tayi sam basu yi mata ba, sam basu dace da ceo na H and H ba. Ga set din kayan kallo, plasma tv ce amma Ruqayyah a idonta sai taga it is not big enough, ita katuwa ta ke so. 


Hassan sai murmushi yake yi yadda yaga yaran suna zagaya gidan cikin murna, ko bai tambaya ba yasan cewa gidan yayi musu. Yaga Ruqayyah a tsaye a falo tana daddanna wayarta sai ya saka hannu ya karbe wayar yana cewa "I am here, ba sai kin kalli hotuna na ba" ta dan yi murmushi tace "to ai baka tsaya na kalle ka ba, kana ta zagaye" yace "ke ma ba sai ki zo muyi zagayen ba?" 


Tace "bana jin dadi ne, kafafuwana suke ciwo" taga yanayinsa ya chanja, ya durkusa a gabanta yana kallon kafafuwanta da suke sanye da takalmi tace "subhanallah. Wacce ce daga ciki take yin ciwon?" ta kara jan skirt dinta kasa tana kuma rufe kafafuwanta tace "ba nan bane ai yake ciwon" ya dago kai yana kallon ta yace "ina ne yake ciwon?" Ta juya masa baya tana jin zuciyarta tana zafi, kamar zata yi kuka take ji. 


A lokacin ne su Sumayya suka fito daga dakin da suka shiga na karshe, suka dawo palo, Zunnur yace "kai! Wannan tv da girma take, zata yi dadin kallon ball" Hassan yayi dariya yace "you like it?" Duk suka amsa da yes banda Ruqayyah data juya musu baya tana kokarin rike hawayen ta. Sumayya tace masa "nan ne gidan ka? Anan zaku zauna da Rukee?" Yace "yaya Ruqayyah, yaya Ruqayyah zaki ke ce mata ba Rukee ba, and no, ba gida na bane ba kuma ba anan zamu zauna ba" Ruqayyah ta juyo tana jin kamar an yaye mata wani abu a kirjinta. Yace " wannan sabon gidan ku ne dana siya muku , nan nake so ku dawo tare da Baba da Inna ku cigaba da rayuwar ku anan".


Yaran suka dauki sowa gaba ki daya, Ruqayyah ma ta rufe bakinta tana dariya, wannan ce dariya ta farko data yi tunda suka shigo gidan, Hassan yace da samarin "ga naku dakin can a soro, akwai tvn ku a ciki da zaku yi ta kallon ku a ciki. Ku zo muje in nuna muku" suka bishi a baya da sauri suna hada hanya. 


Sai a lokacin Sumayya ta zagaya da Ruqayyah ta ga gidan, sai a lokacin taga kayan sunyi mata kyau amma da duk dusu dusu ta gan su. Sai a lokacin ta lura da cewa toilets din modern ne. Suka fito suka yi joining sauran a dakin soro inda aka yi masa tsarin samari da toilet dinsu. Sai da suka gama sannan suka fito, ya rufe gidan suka shiga mota suka juya suna barin gurin. Ruqayyah ta juya tana kallon gidan, sai taga baiyi mata kama da gidan su matar mamallakin H and H ba.


A hanya ne yake ce musu. "Ya kuka ga gidan? Yayi muku? Suka yi dariya, Sumayya tace "yayi mana, sosai ma kuwa. Mungode mungode Allah ya saka muka da alkhairi Allah ya biya ka da aljanna" yace "ameen na gode nima da addu'a. Yanzu abu daya nake nema daga gurinku shine ku taimaka ku lallaba min Baba ya yarda ya karbi gidan nan. Ku hada kanku ku nuna masa kuna so ya karba. Kunji" 


Duk suka amince, ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta zabga murmushi yace a hankali "do you like it" tace "sooo much. Yayi kyau sosai. Mungode Allah ya saka da alkhairi" yace "bana hana ki yi min godiya ba? Duk abinda nake dashi naki ne, to menene in mutum yayi amfani da abinsa?" Taji wani irin dadi a ranta, duk abinsa nata ne, tabbas bata da sauran wata damuwa a duniya.


Bayan ya ajiye su ne yace musu, "bayan gida kuma, akwai Napep da Hussain ya bashi shima saboda transport da kuma ko zai kezagayawa dashi, na san Baba baya son zaman banza" ya karasa maganar yana fadada murmushin sa. Sumayya ta taya shi murmushin "lallai kasan Baba. Ai kuwa Hussain ya kyauta sosai ayiwa Baba Godiya" 


Sama sama Ruqayyah take jinsu. Tunda kalmar Napep ta shiga kunnuwan ta taji kunnen ya toshe. what? Baban nata ne zaike yin hayar Napep bayan ya taso daga aikin gadi? Ta juya ba tare da tace da kowa komai ba ta shige gida. Hassan yana sallama da yaran vai lura da shigar ta ba sai daya waigo yaga bata nan. Ya ji babu dadi, ya so su dan taba hira kadan amma kuma sai ya bata uzuri da maybe ta gaji ne, gashi kuma dama tace kafarta tana ciwo. 

.

Ruqayyah tana shiga gida ta fara masifa "Napep fa yace, wannan wanne irin cin mutunci ne da cin fuska. Me nayi wa Hassan da zai ke wulakanta ni irin haka? Wannan ce sakayyar da zai yi wa taimakon da nayi masa?" Sumayya data biyo bayan ta tace " ke baiwar Allah! Yanzu menene laifin Napep din? Menene laifin wanda yaso mahaifin ki da arziki?" Tace "arziki? Ina arzikin yake? Napep din ne arziki? Mutumin da na tseratar da rayuwar sa shine zai jefi ubana da keke Napep? Ji nake a sanadiya ta ne ya samu ransa, kuma ya samu dukiyar sa daga hannun wadanda suka sace shi. Ji nake naira billion daya aka xe an karba daga hannun barayin kuma an bashi kayarsa? Me ya bani a ciki? Me ya taba bani? Sim card din?" 


Sumayya tace "wannan ra'ayin sa ne ya baki ko ya hana ki, ganin damarsa ce. Amma ya kamata ace abinda kika samu daga gare shi ki gode Allah. Yaushe rabon da kinkwana da yunwa? Yaushe rabon da kici mai da yaji? Ji nake duk a dalilin haduwarki dashi ne? Yanzu kayan da suke jikinki ta dalilin wa kika samu. Ina laifi? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki aiki ya daina leburanci da turin baro? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki Napep yace yayi sana'a dashi? Gidan daya siya mana kuma fa? Mai tilesda ac da ban dakin water system? Shima duk bai kyauta ba?" 


Ruqayyah tace "wannan kuturun gidan kike magana akai? Ai wannan gidan is nothing in aka duba irin dukiyar sa, wannan gidan ai bai kai gidan da a za'a nuna ace ga gidan surukan mutumin daya mallaki kamfanoni ba. Ban taba lissafin cewa zan auri mai kudi ba sai da na hadu dashi, ban kuma san cewa marowacin mai kudi zan aura ba sai yau. Wallahi yayi da yar halak, ba dai za'a yi bikin ba? Ba dai zan shiga gidan sa a matsayin matarsa ba, wallahi sai na chanza masa takunsa tunda dai ace duk motocin da yake ta shiga yana fita dasu ya rasa wadda zai bawa mahaifina sai ya bashi Napep. Wallahi har wannan gidan sai ya chanza in dai yana son zaman lafiya" 


Ta wuce Sumayya kamar kububuwa. Duk maganganun su Inna Ade tana tsaye akan baranda tana jinsu. Sai da Ruqayyah ta zo zata wuce ta sannan tace "zo nan Hassana" ta dakata da tafiyar da take yi amma bata juyo ba ballantana Inna Ade ta saka ran amsawa. Inna Ade tace "yanzu rashin godiyar Allahn naki har ya kai haka Ruqayyah?" Ruqayyah tayi magana kasa kasa sannan ta juya zata shige daki. Inna ta saka hannun ta na hagu ta finciko ta baya sannan ta saka na dama ta wanke ta da mari tace "watakila wannan ya dawo dake cikin hayyacin ki".


Hussain yana ta shirye shiryen sa. Gida ya kammala, an gama finishing touches da komai. Takanas aka yo masa yawa daga masarautar kano akan cewa kar ya saka wa Fatima komai a dakunan ta. Bai so haka ba, amma sai ya bar musu ya fara zuba kaya a nasa dakunan, the best of the latest of komai yake sakawa. Hassan ya fada tuntuni cewa shi zai yiwa da Ruqayyah kayan daki. Amma kuma Hussain ya ga shiru, kullum in yayi masa magana ko kuma yayi masa tayin wani design na kaya sai yace ai zaiyi ne "tunda nace maka zanyi ka bar ni mana, ina ta planning irin wadanda zan saka da wanda zan saka mata, ba lallai ta so irin naka ba kasan taste dinta ba irin na gimbiya bane ba" Hussain yace "ka tambaye ta ne kaji wanne taste ne da ita? Ko kuma dan sunan ta Hassana sai ya zamanto tana da ra'ayi irin na Hassan?"


Daga nan bai kuma bi ta kan Hassan yakira kamfanin daya bawa kwangilar nasa aikin yace su shiga gidan Hassan su saka komai "kaya masu kyau zaku saka a ko'ina, karku gaya masa, in kuma yazo ya same ku kuna aikin kuce masa ni na saka ku" ai kuwa kamfani suka zage dantse suka fara kure adakar su a gidan Hassan. Gashi dai gidan ba za'a kira shi da katon gida ba amma kuma sanda suka gama aikinsu sai ya zamanto kyan da gidan yayi ba karami bane ba. Babu abinda zaka kalla ba tare da ka kuma kallo ba. 


Sanda Hassan ya samu Hussain da fadan me yasa ya taba masa gidan sa sai yace "ba kai na sakawa ba, Ruqayyah na saka wa. It is my wedding gift to her, it is just my little way of saying thank you for saving my brother".




Kuyi hakuri in kunga typos......


Wannan littafin na siyarwa ne, duk mai so tayi min magana ta wannan number din 09135803002


No calls please, WhatsApp only.




Episode Eighteen : His Religion


Ranar da Hassan ya bawa Adam complimentary card dinsa, a hanyar sa ta komawa gida yana ta bitar hirar su da Sumayya yana murmushi, yana mamakim kansa yadda har ya iya ce mata he likes her. He saw the look in her eyes kuma ya fahimci abinda take tunani, alaka tsakanin su zata yi wahala gaskiya, bazai ce impossible ba saboda yasan babu wani abu da yake impossible agurin ubangiji, idan Allah yayi zasu kasance tare to ko sama da kasa zasu hadu tabbas sai sun kasance din. 


Rayuwar sa kadai ta isa misali a gurinsa na cewa nothing is impossible indai aka saka Allah a ciki. Bai taba tunanin zai yi wannan rayuwar ba, sanda ya fara ta kuma bai taba tunanin zai yi surviving ba amma gashi nan yanzu har ya saba. Da dadi ba dadi he still prefers wannan rayuwar akan wacce ya baro a baya. 


Yanzu gashi cikin ikon Allah da kudirarsa sai gashi ya fada hannun ogan h and h, gashi har yace yaje ya same shi a office zai bashi aiki, wai aiki a matsayin driver. Still yana feeling excitement in ya tuno da yadda aka tsara masa aikin, irin benefits din gaskiya abin ya burge shi sosai. Dan haka monday da sassafe yana tunanin shi kansa Hassan din sai dai yaje office ya same shi yana jiran sa. Fatan sa kawai kar ya ganshi cikin hasken rana ya fahimci ko wanene shi yace ya fasa bashi aikin. Kamar yadda yake tsoron ranar da baban Sumayya zai kama shi yace kar ya sake dawo masa gidan sa. 


Haka ya karar da weekend din nan cikin saka da warwara, sai dai ko sau daya tunanin sa bai bashi cewa ya fasa zuwa ba dan shi mutum ne da yakan doshi abu ko da kuwa yasan da illarsa ballantana wannan da bai tabbatar ba, dan haka monday nayi ya shirya ya tafi, sai ya zamanto har ma ya riga shi kanshi Hassan din zuwa office din. Ya zauna ya jira har aka ce masa yazo, sannan aka sanar da Hassan zuwan Adam sai yace ya jira shi. Daga nan Adam ya zauna jira, shiru shiru shi dai yana zaune yana jira yana kuma lissafa yadda rayuwarsa zata kasance a matsayin drivern gidan masu kudi, yayi murmushi yana girgiza kansa yana tuna drivers din da suke gidansu yana kuma zaben wanne daga ciki zaiyi koyi da, but sai dai duk cikin su babu yaro karami kamarsa, babu mai background irin nasa dan haka babu wanda rayuwarsu zata zo daya. 


Ba zaiyi koyi da kowa ba he is going to live as himself.


A haka aka leko aka kira shi. Ya shiga yana kallon fuskar mutumin da suka gaisa ranar nan amma da yake ranar da daddare ne sai yanzu ya samu ya ga cikar halittar sa da kwarjinin sa. A ina Ruqayyah ta samu wannan? Me yasa ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure? When? Where? How? Why Ruqayyah bayan duk yammatan da suke gari babu wadda zai ce yana so tace a'a? Sai kuma yayi saurin kawar da tunanin sa daga kan maganar, zuciyarsa tana kwabarsa da cewa "ina ruwanka? Kai da kazo neman aiki ina kai ina bin diddigin insa ogan ka ya samo budurwar sa?


Ya zauna akan kujerar da Hassan ya nuna masa sannan ya gaishe shi, ya amsa yana rubutu a takardar da take gabansa, sai Adam yaga kamar he is not as nice as he was ranar nan. Sai da ya gama rubutun sa ya dago kai sannan yace "barka da zuwa. Sorry I kept you waiting. Ban dauka zaka zo yau ba ban kuma dauka zaka zo da wuri ba, already akwai masu appointment so I have to see them first. Ina fatan ka gane" Adam ya gyada kai da sauri. Sannan Hassan ya tambaye shi full name dinsa. "Adam......." Hassan "Adam who? Adam ya dauke kansa gefe yace "Adam Clement Young" ya fada yana studying Hassan yana so yaga yadda zaiyi reacting to the name amma sai yaga ya rubuta ba tare da yanayin fuskarsa ya chanja ba. Daga nan ya cigaba da jero masa tambayoyi, "age" "23" "tribe" "igbo" "state of origin" "imo" "religion" "islam" haka suka yi tayi yana jero masa tambayoyi akansa shi kuma yana amsawa, ya tambaye shi contact address dinsa sai ya bashi adireshin dakin da yake haya sai kuma ya tambayeshi permanent home address sai ya kuma bayar da same address. Hassan ya dago yana kallonsa sai shi kuma ya sunkuyar da kai, Hassan ya ajiye biron hannunsa yace "for this, you have to give me address din inda mahaifanka suke, gidan ku nake son sanin a ina yake" Adam yace "Kano" Hassan yace "kano wacce unguwa, wanne layi wanne number din gida?" Adam ya dago kai yace "that's a very private question" Hassan ya bude baki cikin mamaki yace "you think so? I am about to give you a very private job na entrusting rayuwar only brother dina a hannunka, and you are telling me address din gidan ku is a private thing? I have to know as many things as possible akan ka kafin in iya baka wannan aikin".


Adam ya gyada kai, ya yarda da abinda yake cewa but it is just that bai fiya magana akan parents dinsa ba sai in ta kure, kamar yadda ta kure yanzu dan gaskiya yana son wannan aikin sosai saboda chance din da ya gani a cikin aikin na komawa makaranta. Yana son karatu sosai. Dan haka ya fada "house number 14, badawa layout, Nassarawa local government, kano state" 


Daga nan tambayoyin suka ci-gaba kamar ba zasu kare ba, "wannan mutumin da bin kwakwkwafi yake" Adam ya fada a zuciyarsa. Sai kuma ya yi kokari wajen ganin cewa ya fadi gaskiya to the best of his knowledge. Sai da suka gama sannan Hassan ya rufe file din gabansa and for the first time tunda ya shigo yayi masa murmushi yace "that will be all. Kayi kokari sosai, but I will have to run a background check on all what you said, ba zai dauki lokaci ba zan gama within this week next week insha Allah zan kira ka in gaya maka yadda ake ciki" Adam yaji gabansa ya fadi, ya dago da budaddun idanuwa yana kallon Hassan, Hassan ya daga kafada yace "yes now, ta haka ne zan tabbatar da gaskiya, ko akwai wani abu da kake boyewa ne?" Adam ya sunkuyar da kansa yana girgiza kansa, wani bari na zuciyarsa yana gaya masa cewa yace ya fasa neman aikin amma kuma ita magana ai kamar zarar bunu ce inta fita bata komawa. There is no going back. Fatan sa kawai in Hassan ya samu abinda yake fatan kar ya samu to kar ya gayawa Sumayya. Idan zai gaya mata to shi zai gaya mata da kansa.


Adam yana fita Hassan ya dauko wayarsa yayi kira "Hello. Kanawan dabo. Kana lafiya? Ya iyalin? Dan Allah dan wani taimako nake nema, zan turo maka info din wani yaro ina son kadan bincika min shi. Eh nan kano yace min unguwar badawa. Okay, just find out if there is anything that I should know about. Thank you." Ya kashe wayar yana murmushi, rami ya gina wa Adam kuma ya fada ciki.


Tun sanda ya ganshi yana zagaya gidan Baba kuma ya fahimci gurin Sumayya yake zuwa kuma ya fahimci cewa ita ma Sumayyan kamar tana da interest akansa sai ya kudurce a ransa yana so yayi bincike akansa amma ya san ba zai bashi hadin kai ba shine ya yaudare shi da aiki dan yaga alamar yana bukatar aikin, yanzu sai yayi binciken sa sosai akansa, in ya samu alkhairi zai bashi aikin kuma yayi masa jagora zuwa ga Sumayya in kuma ya samu sharri sai yayi warning Sumayya kuma aikin ma ya bi ruwa.


Bayan ya tashi daga aiki ne ya koma gida ya tarar Aunty tana palo tana jiransa "kudin nan fa sai ka karo su Hassan. Kaya gasu an fara siya basu fi rabi ba amma kudi sun kusa karewa, ko boxes din ba'a siya ba. Ga sauran kayan al'ada da ake yi duk ba'a siya ba" ya shafa kai, "aunty, kayan nan wai me zata yi ne dasu? Ji nake dai sakawa zata yi a jikinta in tazo gidana ko? To ba gani ba muna tare? In tazo din duk abinda take so ai za'a siya mata" Aunty ta girgiza kai tace "ba shi kadai ne amfanin lefe ba, ai ana rabawa dangi, kusan rabin kayan ma rabarwa ake yi ballantana su da ba masu kudi ba ai kaga duk zasu so su rarrabawa dangi suma su samu albarkacin ta ko? Shi yasa nake siyan kayan kashi biyu akwai masu tsada sosai akwati daban za'a saka su a matsayin nata, masu dan saukin kudi kuma sai a siya da yawa a basu a ce a raba wa yan'uwa" yayi ajjiyar zuciya "mata dai da al'ada. Shikenan nawa za'a karo yanzu?" Ta gaya masa, ya bude baki yana mamaki tace "to boxes din ma set uku zan siya, biyu nata daya na rabo" ya rufe bakin yace "set daya ya ishe ta, set daya na rabon. Yarinyar nan ba sabawa tayi da irin wannan spending kudin ba, nafi so kuma ta cigaba a haka. In an siya da yawan ma sai dai tayi ta ajiiyar su sai a hankali zata saba da amfani da wasu abubuwan ma. Dan haka gwara a bari in tazo din ta fara sabawa a hankalin sai ake introducing dinta to sauran abubuwa" Aunty tace "in an siya mata a kayan lefen nata ai dole zata koya, in bata dasu ta yaya zata koya? Kuɗi fa sai ka fito dasu komai wayon ka" yayi dariya yace "shikenan Aunty, zan kawo gobe" tace "yauwa, kuma ina son inji yadda kuka yi da ita akan sauran hidimomin biki, nawa zaka bata?" Ya sake bude baki "bikin ai da saura ko" tace "sauran wata daya ba? Yanzu lokacin yadda yake gudu kafin ka gama lissafin ka wata dayan ya kare. Kaje ku zauna da ita ta fada maka shirye-shiryen ta sai ka lissafa ka bata abinda zai ishe ta" ya mike tsaye yana cewa "an gama Aunty" tayi dariya tace "zaka gudu ko? To ai ban gama da kai ba" yace "in na cigaba da zama sai kaina ya kunce saboda lissafin kudin da za ki cigaba da yi min".


A bangaren Ruqayyah ranar da ta sha mari a gurin Inna kusan kwana tayi ta kasa bacci, ba wai marin ne yayi mata zafi ba a'a yadda akayi mata marin a gaban kannenta sannan inna ta wanke ta tas da soso da sabulu shi yafi kona mata rai. Yanzu ai sai su raina ta su cigaba da kallon ta da sunan da Inna ta kira ta dashi "butulu".


Ita kuma Inna hankalinta gaba daya a tashe yake da jin kalaman Ruqayyah, ita da kanta wai take ikirarin saita wa mijin da zata aura zama idan anyi auren su. Wannan kadai ya nuna cewa ita ba ta rike alkhairi a ranta ba akan auren nata, Inna taji tana jin tsoro, tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata a gidan mijinta. Sai taji a ranta cewa kamar ta bawa Baban biyu shawarar cewa ya dakatar da auren baki daya, amma kuma tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata in akace an fasa wannan auren, zata iya yin komai koda kuwa abinda zai lalata mata rayuwa ne, tsoron wannan yasa Inna Ade ta kasa yiwa Baba maganar.


Ita dai tuntuni ta san cewa Ruqayyah jarabawa ce a gare su ita da Baba, iyakacin iyawarta tayi tarbiyyar, ta bada ilimin, ta kuma yi addu'ar. Ba dan Allah ya saka sauran ya'yan sunyi turning out good ba da sai taga kamar laifin sune su iyayen amma yanzu su sun sani, Allah ya sani, sannan duk wanda ya san su ya sani cewa sunyi kuma suna yin iyakacin kokarin su. Allah shi ya barwa kansa sanin yadda zaiyi da Ruqayyah.


Da safe yaran suka zagaye uban. "Baba ba ka ga gidan ba, bandakin fa irin wanda ake korawa da ruwa ne" "kaga kujerun Baba? Wannan in inna ta zauna ba zata iya tashi ba" Sumayya ta fada tana tsokanar Inna, Inna ta harare ta tace "ai dai kinsan ba daga ruga aka dauko ni ba ko? Sai dai ki fada wa zazzagawa sune basu saba hawa manyan kujeru ba" Baba yayi shiru bai kula ta ba duk da ya fahimci tsokanar sa take yi, shi wannan lamari da yaran nan suka kawo masa yana da girma sosai, gida kuma? Har da dakuna kowa da nasa? Da bandakuna na zamani da palo mai kujeru da talabijin? Anya kuwa abinda yaron nan yake yi bai yi yawa ba? Anya kuwa ya dace ya karbi wannan kyautar? In ma zai karba ai kamata yayi ace sai bayan biki tukunna sai ya iya karba a matsayin surikin sa amma yanzu gani yake yi anytime yaron zai iya zuwa yace ya fasa auren. Inna tace "Baban biyu, nima gaskiya ina tsoron karɓar gidan nan, daga yadda suke kwatanta shi kasan ba karamin gida bane ba. Ya bar mu anan din mu tunda gashi nan har kana kokarin yin katangar nan" yace "har plaster nake so ayi wa dakunan nan ayi musu penti kafin bikin" yaran duk suka fara bata rai "dan Allah Baba, dan Allah Inna yace fa da sunan ka ya sayi gidan nan, kyauta ya baka shi, bana jin ko ba'a yi auren ba zai dawo da kalaman sa baya" Sumayya tace tana karya wuya. Sulaiman da Zunnur suka durkusa kusa da ita suna hade hannayensu "dan Allah Baba ka karba, dan Allah Baba ka karba".


Baba yayi shiru yana kallon su yana tunani sannan yace "shikenan ki ce wa Hassana ta kira min shi tace in ya samu dama yau da magariba yazo ina son magana dashi..


Sakon yana zuwa kunnuwan Hassan ya gane cewa akan maganar gida ne, ya shirya ya taho yana addu'ar Allah yasa ba rejecting gidan Baba zai yi ba. A tsakar gida aka shimfida musu tabarma suka zauna daga can bakin kofar shigowa. Hassan ya gaishe shi cikin ladabi da jin kunya, Baba ya amsa sannan yace "jiya yara suka zo min da wani lamari mai girma, shine na kira ka inji daga bakin ka" Hassan yace "gaskiya ne abinda suka fada baba, ina kuma fatan ba za'a ki karba ba kamar yadda aka ki karbar kuduri na na bada jarin sana'a, yadda na hakura na bayar da aiki ina fatan wannan karan nima za'a dube ni a karbi wannan din. In ba'a karba ba gaskiya zanji babu dadi, zanga kamar......" Baba yace "kamar an raina?" Hassan yace "a'a kamar ba'a sona tunda ba'a son abin hannuna" Baba yace "ba haka bane ba, son naka da nake shi yasa nake maka haka. Bana son in cutar da kai" Hassan yace "ta yaya zaka cutar dani Baba? Karbar wannan kyautar ai faranta min zaiyi ba bakanta min ba" Baba yace "haka ne, amma ina matukar jin kunyarka" Hassan yace "Allah yasa hakan yana nufin za'a karba" Baba yayi ajjiyar zuciya yace "na karba Hassan. Allahu yayi maka albarka ya baka masu yi maka kaima a lokacin da kake bukata" Hassan ya sunkuyar da kansa, fuskarsa tana nuna irin jin dadin da yayi yace "Nagode sosai Baba, na gode da karamcin ka da soyayyar ka" Baba ya dago kai yana kallon sa, yaron kirki ne, sam bai dace da Ruqayyah ba, sai yaji kamar baiyi masa adalci ba.


Hassan da kansa ya turo da driver ya debe su zuwa sabon gidan su. Kafin su tafi duk suka shiga gidajen unguwa suka yi musu sallama tare da basu kwatancen sabon gidan su. Kayan sakawarsu kawai suka dauka da dan abinda suka san zasu bukata a sabon gidan sannan suka rufe dakunan su suka rufe gidan suka tafi, zuciyoyin su fal da mabanbantan feelings. 


Yaran suna jin feeling na murna sosai, suna ganin sun taka wani babban matsayi a rayuwa kuma suna ganin wannan wani chanji ne mai kyau a rayuwarsu yayin da iyayen suke jin rashin dadi na barin gidan da suka yi shekara da shekaru suna zaune a ciki, suna kuma alhinin shiga wata sabuwar rayuwa wadda basu san menene a boye a cikin ta ba. 


Ruqayyah kuwa a nata bangaren, ji take yi cewa wannan chanjin kamar misalin wanda zaije sama ne sai ya taka dutse, wannan ba komai bane a gurin ta, wani step ne da ta taka zuwa gaba.


Wannan kenan...........


A bangaren Gimbiya Fatima kuwa shirye shirye sun kankama sosai, a da lokacin da aka saka bikinta wata takwas ji tayi kamar ta dora hannu aka tayi kuka saboda ganin tsayin lokacin da kuma zakuwar da tayi na ganin ta kasance da hasken idanunta, Hussain. Sai gashi yanzu har watan bikin ya kama. Tana ta shirye shiryen ta iyayenta suma suna yin nasu. Duk tsarin gidan Hussain babu abinda bata sani ba dan tare suka tsara kayan su, sun kuma shirya duk events din da zasu yi. Ita a bangaren ta zata yi bridal shower a gidan babban yayan su a nan cikin garin kano, sai kuma kamu da yini da za'a yi rana daya anan cikin palace ranar Friday, ranar Saturday kuma za'a yi grand dinner da maimartaba ne da kansa ya shirya musu kuma har da ango da abokan sa da yanuwansa duk za'ayi. Ana saka ran zasu zo su wuni ranar Saturday din da daddare ayi dinner sannan su kwana sai da safe a daura aure su tafi da amaryar su zuwa Kaduna.


Duk wasu ashobis sun fitar uta da kawayenta wadanda yawancin su tare suka yi jami'a a Europe, sai wadanda suka yi secondary school tare a Abuja, sai kuma family friends dinta. Sun gama tsara komai kuma Hussain ya sakar musu kudi wanda wani lokacin har sai ta daga masa hannu dan bata son kawayen natakuma su mayar dashi saniyar tatsa dan shi duk abinda suka ce ya basu basu kawai yake yi. An aika an gano gida kuma kusan komai an gama siya jira kawai akeyi bikin ya kara matsowa sai aje ayi jere.


Sakamakon binciken da Hassan ya tura ayi masa a kano a kan Adam ya fito, kuma kusan komai yayi tallying da abinda ya fada banda abu daya. Hassan ya dago da kansa daga karatun report din yana shafa sajensa, fuskarsa da alamar damuwa. Ya dauko form din daya cike biography din Adam yana kuma dubawa dan yayi confirming maganar, sai kuma ya dauko wayarsa ya saka number din da Adam din ya bashi ya kira. 


Adam ya ciko mota passengers yana tukin sa a nutse kamar kullum, yaji vibration din yawarsa da take ajjiye akan dash board, ya kalle ta, sunan daya gani ne ya saka shi daga kafarsa yana kara rage gudun motar sannan ya sauka gefen titi yayi packing yana cewa "excuse me Please, I have to answer this" sannan ya daga wayar da sallama.


Hassan yayi mamakin sallamar da yaji amma sai ya maze yace "kazo gobe, around noon ina son ganinka" Adam yace "yes sir. Insha Allah" Hassan ya katse wayar still yana noticing insha Allah din da Adam yace.


A ranar da daddare Hassan yaje zance gurin Ruqayyah, suna zaune a dakin su Sulaiman kamar yadda suke zama kullum. Tana ta so ta shigar masa da maganar shirin biki amma ta rasa ta yadda zata fara ba tare data bata pentin da tayi wa kanta a gurin sa ba. Sumayya ta shigo da sallama ta zauna a hannun kujerar da Ruqayyah take zaune, ta gaishe da Hassan ya amsa yana tsokanar ta. "Ance min kina ta kuka wai ba kya son rabuwa da friends dinki" tayi ajjiyar zuciya, ita duk ba wannan ne problem dinta ba, ba shine abinda yake hana ta bacci tunda suka dawo ba.


Tace "yaya Hassan, dama tambayarka zanyi......." Ya gyara zama yace "ina jinki" tace "yaje kuwa? Yaje office din naka kuwa?" Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tace "wa? Waye zaije gurinsa?" Sumayya ta dauke kanta daga kallon ta ta sake mayarwa kansa tana jiran amsa, ya danyi murmushi duk da ya fahimci wa da take nufi amma sai yace "wa kenan fa?" Ta dan vata fuska tace "mutumin ranar nan" ko da wasa bata son Ruqayyah ta san maganar Adam. 


Ruqayyah ta sake cewa "wai waye kike magana akan sa? Bashi da suna ne?" Sumayya tace "shi yasan maganar wanda nake yi ai" Hassan yayi yar dariya, ya fahimci Sumayya tana boyewa Ruqayyah wannan Igbon. Ya gyara zama da dariya a Muryar sa yace "yes, na gane wanda kike nufi, and yes, yaje munyi magan dashi" cikin zakuwa Sumayya tace "and?" Yace "and, sai gobe zai dawo mu karasa maganar" Sumayya tayi ajjiyar zuciya tace "okay, thank you. At least nasan yaje din, ina ta tunani ne kuma bani da hanyar sani shi yasa na tambaya" yace "kar ki damu. I have his phone number if you want" Sumayya tayi saurin miko wayarta da Baba ya dawo mata da ita bayan sun dawo sabon gidan tace "yauwa saka min Please" yana dariya yace "ko kunya babu" ya karba yana saka mata Ruqayyah tayi mata alamar tambaya da hannunta ita kuma sai ta dauke kai kamar bata gane me take nufi ba, ta san dai yau sai sunyi rigima a daki".


Yana gama sakawa ya miko mata, tayi saving sannan tayi masa godiya ta fita, Ruqayyah ta jiyo tana kallon sa da alamar tambaya sai yace mata "wani aboki na ne". Daga nan bata iya ce masa komai ba duk da bata yadda da amsar daya bata ba.


Sumayya direct dakin da yake matsayin nasu ita da Ruqayyah ta zarce, ta rufe kofa sannan ta zauna a bakin dago ta kira number din da aka saka mata. Ring biyu ya dauka da sallama kuma a take ta gane muryarsa. Yace "who is on the line please" sai data dan jima sannan tace "someone, da ka manta" ko a cikin mafarki ne zai gane muryarta. Ya matsa daga gurin da abokan su suke hira yana cewa "Sumayya? Ke ce da gaske? A ina kika samu number ta?" Bata bashi amsa ba sai kuma yake "ohhh I get it. Yazo zance....." Ya fada da dariya a muryarsa. 


Ta dan bata fuska tace "ni da na damu da inji yadda kake ai na ajiye kunya ta a gefe na nemi number dinka" yace "oh dear , you have no idea sau nawa nake zuwa unguwarku a rana. Sumayya kullum sai naje, kawai dai na kasa samun courage din da zan aika a kira ki tunda ranar nan kince min za'a yi miki fada, bana so ayi miki fada, bana so in jawo miki trouble. In naje kawai hoping nake ko zan ganki an aike ki ko kin fito unguwa"


Ta lumshe idonta tace "ni ba'a aike na, ni babu inda nake zuwa, sai in kwana biyu ban fita daga gida ba, dama zuwa school ne kuma yanzu bama zuwa, islamiyya ma a gida muke yi anan muke daukan karatu kuma mu dora wa yaran unguwa karatu" yace "wow, har karatu kuke koyarwa?" Tace "gidan mu ai makaranta ce, makarantar addini ce" sai taji yayi shiru har sai da tace "hello?" A hankali yace "zan iya shiga nima? Makarantar gidan ku zan iya shiga?" Tace "ban gane ba, ba ka yi sauka ba ko akwai littattafan da kake son sani?" Sai da ya danyi shiru sannan yace "banyi karatu ba ni. Bani  da ilimin addini ni"

Post a Comment

0 Comments