TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 9-10

 9️⃣----🔟


Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tun daga shigowa gidan da kuma farajin masifar Gwaggo Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa 'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,Toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata, toh wacece kakata, kenan Gwaggo Ladi ba ita bace ta haifi Ummina ba'. 

Haka taita karatun zuci daga ƙarshe ta dauki kayansu zuwa inda Baba ya umurcesu, ɗaki ne ɗan ƙarami da ƴar katifa itama ƙarama wacca batafi ta kwanciyar mutane biyu ba, sai labulen ƙofa da na window, ɗakin ba laifi a gyare yake kamar ansan da zuwansu.

 Ciki ta iske Ummanta a zaune akan katifar tayi tagumi, da sauri Sa'eeda ta ajiye kayan hannunta ta nufi gun Ummanta don arayuwarta bata ƙaunar ganin damuwa a fuskar Umman nata, haka da sassarfa ta isa gunta tare da cewa " Ummina don ALLAH kidena tagumi, Banaso please kidaina "

 Sai kuma ta fashe da kuka,har da shashsheka, don ita ta rasa wannan baƙin jinin da suke dashi, kowa baya sonsu, ko a makaranta haka ta ke fuskantar tsana da tsangwama daga ƴan ajinsu, wurin Maryam kaɗai ne ta ke samun sassauci.

 Ummanta ne riƙo haɓarta tare da girgiza maka kai alamun tayi shiru duk da itama kanta hawayan ne suke kwaranya a bisa kuncinta tare da cewa " Duk wani ƙunci da tsanani maganinsa yana ga UBANGIJI ne, haƙuri da juriya suna kai mutum mataki babba arayuwa, kasancewarmu a wannan yanayi baya nuni akan dawwamarmu  cikinsa, don haka mu cigaba da haƙuri tare da  juriya wataran sai labarin kinji sanyin idanuwa na"

 Sa'eeda da tunda Ummanta ta fara magana ta ke shashshekar kuka ɗan ɗaga mata kai tayi tare da tambayarta alokaci guda " Ummina meyasa Gwaggo Ladi ta kiraki da mara asali?

 Tirƙashi lokaci guda yanayin Umman Sa'eeda ya sauya ita a tunaninta Sa'eeda bataji surutan Gwaggo Ladi ba, saida ta ɗan sauke nauyayyan ajiyar zuciya kafin ta fara magana "Banso kika ji zantuttukan Gwaggo Ladi ba, hasalima shiyasa tun kina ƙarama rabona da zuwa garin nan saboda banason hankalinki ya tashi,nabar hakan ya zamo sirri agareni ba tare dana sanar miki ba, amma tunda allura ta tono garma, kibari anjuma da daddare bayan munyi sallar Isha'i sai na baki tarihina kamar yanda nima mamata ta sanar min, kinji"

Sa'eeda da ke kallon Ummanta ta amsa da "Toh, ashe nima inada kaka"

 Murmushi Umman Sa'eeda tayi ganin wauta da shirme irin na Sa'eeda tare da cewa "Daman ance miki babu wanda baida kakane, kema taki ALLAH Yayi mata rasuwa ne"

Ɗan lunshe sexy eyes ɗinta Sa'eeda tayi sannan ta ce " Allah ya kai haske a ƙabarinki kakata da na al'ummar musulmai baki ɗaya"

 da "Ameeeeeen", Umman Sa'eeda ta bita dashi, kana suka cigaba har hirarsu. 


         @@@@@@@@@@@@@@


Kamar yanda Baba ya faɗa za'a girko musu abinci hakan ta kasance, don ɗan saƙon da aka aika gidan Mairi yana sanar ma ta fara murna saboda duk acikin ƴaƴan Gwaggo Ladi tafi kowa sonta tare da mahaifiyarta kafin ta rasu.

 Habawa ai da ɗan aiken ya sanar mata, daman tana kiyon zabbi , kaji da awakai, sai tasa a yanka mata zabbi guda biyu, bayan an yanka mata su, tayi zaman gyaransu ita da ƴarta mai kimanin shekara 14 dayake bata haihu da wuri ba,sannan ta ɗora sanwan girki, tayi musu tuwon dawa da miyar kuka wacca tasha manshanu haɗe da naman zabbi duk da ba duka tayi miyar dasu ba, ta soya sauran tasa alanga haɗe da na tuwon da miyar, nan fa ta aiki ƴarta ta dashi a babban kwando. 


       @@@@@@@@@@@@@


Da sallama ɗiyar Mairi ta shiga gidan, sai tayi sa'a Gwaggo Ladi na ɗaki kasancewar lokacin azahar ne, sai ta wuce ɗakin baƙi dayake mamanta ta faɗa mata inda baƙin suke. 

Sallama tayi a lokacin Sa'eeda na sallah ita kuma Umman Sa'eeda ta kammala sallah tana zaune,jin anyi sallama yasata amsawa tare da cewa"A shigo"

yarinyar ce ta shigo tare da russunawa ta gaisheta, Umman Sa'eeda cike da fara'a ta ke amsa mata ganin kamannin ƴar uwarta ta kuma masoyiyarta wacca bata da kamarta, cike da ladabi yarinyar ta ce"Mamata ta ce gashi in kawo muku kuma tana muku sannu da zuwa, gobe bayan sallar Idi tana nan zuwa "

faɗaɗa murmushinta tayi da faɗin" ALLAH ya kaimu, kice mata ina godiya sosai, sannan tsarabarta na nan saita zo"

 yarinyar  tace "Toh", har lokacin Sa'eeda na sallah bata idar ba.

Yarinyar na tafiya Sa'eeda ta kammala sallah,ta cire hijab ɗinta suka fara cin abinci, duk da yau ake hawan Arfa, Sa'eeda na period ita kuma Umman Sa'eeda na fama da chronic ulcer kuma yanxu an ɗorata akan magani shi ya hanata ɗaukar azumin Arfa. Haka suka kammala cin abincinsu tare da hamdala sannan kowa ya sami wuri don warware gajiyar tafiya. 


      @@@@@@@@@@@@@@@


Baba dai har lokacin bai dawo ba, dayake Umman Sa'eeda tasan ɗabi'arsa na sai bayan Isha yake dawowa, yau ma sa'a tayi ganinsa a gidan.

Bayan sallar Isha ya dawo gida, ita dai Gwaggo Ladi alwala ce ta ke fito da ita sai kuma girkin abin shan ruwa da tayi su kaɗai ne yasaka ta fitowa don ita ta tsani Umman Sa'eeda matuƙa ainun gashi tana aure a birni ita kuma yaranta a ƙauye dukkaninsu suke aure, a duk sanda ta tuna sai ranta ya baci(Fans da alama dai batasan baƙar wahalar da Umman Sa'eeda da ƴarta suke sha a gun Umma kande da Maman Jummalo ba shiyasa ta ke wannan bacin ran🤔).

Gwaggo Ladi ce ta fito da tabarma don shimfiɗama Baba kasancewar yafi son cin abinci a waje, bayan ta shimfiɗa tabarmar sai ta kawo mai abinci sannan ta wuce ɗaki don batason haduwa da Umman Sa'eeda kuma tasan yana gama cin abinci sai kirata(Gwaggo Ladi duniya🙃, wannan tsana sai kace kishiyarta ai ko kishiyarta sai haka😂😂😂).

 Kamar ta sani bayan ya kammala cin abin yako kira Umman Sa'eeda, tako fito ta samu wuri gefan tabarmar ta zauna.

Ƙara gaisawa sukayi sannan suka fara hirar yaushe gamo, tun tana ƙarama ta saba da Baba,saboda yana jawota a jiki sosai kamar ƴaƴansa,sun shaƙu da juna sosai. Sun daɗe sun hira abinsu har kusan awa sannan sukayi saida safe, shi ya wuce ɗakin Gwaggo Ladi ita kuma ta wuce masaukinsu. 


          @@@@@@@@@@@@


Shigarsa ɗaki ya samu wuri kusa da Gwaggo Ladi ya zauna don yanada buƙatar magana da ita saboda ya gaji da wannan ƙiyayyar da ta ke nunawa marainiyar ALLAH, ya isheshi haka, tun tana yarinya ta ke fuskantar ƙalubale har auranta.

 Gwaggo Ladi da tun shigowarshi ɗakin tana kwance tana jinsa amma tayi burus sai tayi kamar tayi bacci, don yau ya bata haushi sosai akan marar asali yake daka mata tsawa wanda rabon da suyi hayaniya ko fada ta manta ranar.

Zama yayi tare da cewa " Ladi ina son magana dake yanxu"

 tana jinsa amma taƙi amsawa, saida ya sake magana kana ta tashi daga kwancen ta zauna.

Shiru ɗakin yayi , sai can Baba ya katse shurun da faɗin"Yanxu Ladi abinda kikayi ya dace kenan, yarinya tazo ko zama bata yi ba, kike mata masifa tare da faɗa mata marar asali, wai shin kinada hankali kuwa,kina da tabbacin marar asalin ce da kike kiranta dashi tun kan tasan hankalinta har girmanta, wata hujja kike da ita Ladi "

 Gwaggo Ladi dai ko Uhmmm bata ce ba, tana nan zaune, saida ya ɗan lunfasa sannan ya ɗora da cewa" Don ALLAH ki canja halinki, tsufa kike ƙarayi amma kullum kina abu kamar wata yarinya haba, a kullum inaji a jikina Husaina na da asali saidai ƙaddarar da ta afka ma mamanta na ciwo "

 Yanxu ne Ladi ta buɗe baki tace" Ni tunda ka kawo su gidan nan na tsane su,bara kaji har na koma ma mahaliccina da tsanarsu zan koma musamman Husaina, don haka ba ruwana da har karta, tunda gidan kane, ta shekara a ciki wannan kai ta shafa bani ba,sannan idan wa'azin kake sonyi ka tafi masallaci kayi, baza kazo kana min wata nasiha ba, ehehhh!

haka Baba ya kyaleta ya kwanta tare da roƙon mata shiriya don da alama tayi nisa. (Ni kuma nace hassada ne da baƙin ciki ya mata katutu a zuciya 😂🙃😇). 


        @@@@@@@@@@@@@


A bangaren su Umman Sa'eeda kuwa, bayan ta shiga ɗaki ita duk a tunaninta Sa'eeda tayi bacci, ashe tana nan tana karatu,(Jikar Mongo Park ba ko kuma Al huda huda🙃🙃🙃) .

shiga ɗakin tayi tare da cewa"Ashe bakiyi bacci ba, duk azatona zanzo na nasamu kinyi bacci"

 murmushi Sa'eeda tayi sannan tace "Ummina Ina zanyi bacci banji tarihin kakata ba, ai bacci bai ganni ba"

dariya Umman Sa'eeda tayi sannan tace " Toh karkaɗa kunnuwanki yanxu zakiji tarihin kakarki"

 Gyara zama Sa'eeda tayi tana fuskantar Ummanta, sannan Ummanta tafara bata tarihin kakarta. 

Labari 

***Na taso a gidan nan tare da mahaifiyata cikin ƙasƙanci, a lokacin mamata tana da tsohon ciki ni kuma ban wuce skekara 6 ba,Baba  na kula ta mamata tare da ni sosai kasancewar cikinta na a watan haihuwa,a lokacin mahaifiyar baba na araye,duk sanda Gwaggo Ladi kema mamata masifa mahaifiyar Baba wacca muke kira da Tasalla ta ke shigar mamata faɗan tayiwa Gwaggo Ladi tatas, don Tasalla na son mu kamar yanda Baba ke son mu.

 Sanda mamata zata haihu alokacin babu asibiti, Tasalla ta amsa haihuwar, mamata ta haifo ƴan biyu duk maza kyawawa amma ɗaya yazo babu rai sai kuma ɗan uwansa yabi bayansa, bayan haihuwa da kwana huɗu, tun sanda mamata ta haihu ta kamu da ciwo kuma ankasa gane kan ciwon, wanda ko fita da ƙyar ta ke yi. 

Kuma duk sanda aka tambayeta ina ne ahalinta suke to ranar babu wanda zai rintsa, ta dinga firgita haɗe da iface iface a gidan, dalilin haka yasa tunda su Baba suka tambayeta sau biyu hakan ta faru basu ƙara tuntuɓarta da batun inane ahalinta suke ba.

 A duk sanda Gwaggo Ladi tai min gori ko ta kirani da marar asali sai mamata tace min "Husaina ke ƴar gata ce, kuma kinada asali, kin fito daga tsatso mai kyau, kuma ƴar dangi ce, bancin ƙaddar da ta afka mana tare da ɓatan ɗan uwanki Hassan wanda kullum zuciyata dashi ta ke kwana kuma dashi ta ke tashi, inaji a jikina yana araye bai mutu ba,nasan ko ba daɗe ko bajima zaki sadu da ahalinki, inaso kikasance mai haƙuri da juriya a duk inda kika tsinci kanki,ki kasance mai ibada a koda yaushe, don inajin lokacina ya kusa Husaina "

Haka mamata ta ke faɗamin a duk sanda Gwaggo Ladi ko ƴaƴanta suka kirani da marar asali,na ɗau nasihar mamata na adanata acikin ƙwaƙwalwata, duk da a lokacin banfi shekara 12 a duniya ba, mahaifiyar Baba ta rasu, Ina gab da shiga shekara da 13 mamata tabar duniya, nayi kuka iya kuka wanda babu mai lallashina daga Baba sai Mairi wacca ɗiyarta ta kawo mana abinci ɗazu, duk da sa'a ta ce amma tanada hankali, ita kadai da Baba nake samun natsuwa wurinku.

 Bayan rasuwar mamata rayuwa ta ƙara min zafi don lokacin na fara fuskantar asalin gallazawa wurin Gwaggo Ladi, ga aikin gida duk da ƙarancin shekaruna haka nake komai agidan sai afakai ce Mairi ta ke tayani aiki, kasancewar Baba ba zama yake a gida ba shiyasa baisan meke faruwa dani ba,sai dare yake dawowa, a daran ne nake samu naci abinci sosai.

 Haka rayuwa da cigaba da tafiya ina a wannan yanayin har na zama budurwa, kyakkyawa dani, don samarin garin nan sunyi harsashe babu wacca ta kaini kyau, hakan ba ƙaramin batama Gwaggo Ladi rai yake ba saboda lokacin itama ƴan matanta sun girma, don akwai mata biyu wa'inda suka girmeni sannan Mairi wacca muke sa'a da juna, haka samari sukaita zuwa wurin Baba neman aurena alokacin inada shekara 16,gasu masu kuɗi  harda yaron mai gari,saboda wannan farin jini da ALLAH ya bani na ƙara samun ƙuntata gun Gwaggo Ladi.

Alokaci guda aka saka mana rana da sauran ƴan matan Gwaggo Ladi har da Mairi,duk samarinsu a ƙauye suke har da na Mairi, Ni kuma mahaifinki a lokacin ba laifi yanada kuɗi kuma a birni yake da gida, haka aka daura mana aure wanda ko tsinke ban samu daga Gwaggo Ladi ba saidai Baba,shi yayi ruwa yayi tsaki, bayan ɗaurin aure aka wuce dani birni gidan mahaifinki duk da bamu samu tarbar arziƙi wurin Umma kande ba, haka suka tafi suka barni, inata kukan rabuwa dasu, a da maihaifinki na matuƙar sona wanda baya iya ɓoyewa a gun kowa, sai daga baya lokacin na haifeki kinyi yawo, na fara ganin sauyi wurinsa har yakai ya fara nuna min kyara da tsangwa, wanda ni kuma na rasa abinda nayi masa, a haka dai har aka kawo yanxu, wanda a kullum nake Addu'ar ALLAH ya karkato da hankalinsa guna dake.

 Toh kinji tarihin kakarki mai suna Maimuna, kuma har yanxu ban cira rai da saduwa da ahalina ba kamar yanda mamata ta ke faɗamin duk sanda aka min gorin marar asali***


      @@@@@@@@@@@@@@@


Cikin labari


Sa'eeda dai tun sanda Ummanta ta fara bata labari da natsu har zuwa ƙarshe sannan ta saki nauyayyan ajiyar zuciya har seda Ummanta taji kana ta fara magana " Ummina yanzu  baki san asalinki ba koda gari ne"

 Umman Sa'eeda murmushi tayi sannan tace " Tabbas bansan asalina ba, kuma mamana bata taɓa sanar min daga wani gari muke ba, saidai a kullum tana maimaita inada asali, ni ƴar gatace kuma ƴar dangi ce haka ta ke fadamin, kuma inaji a jikina zan sadu da asalina"

Sa'eeda ce tace " Ummina shi Uncle Hassan har yanxu bakisan inda yake ba",(Uhmmm su Sa'eeda masu Uncle tun Kan aganshi har an bashi wannan respect d'in😂😂😂).

 Dariya Umman Sa'eeda tayi kana tace " Niko ina zan sanshi tunda tun muna Yara ya ɓata, kinga bazan sanshi ba, saidai mamata na yawan cemin muna kama dashi sosai sede nafishi hasken fata"

Shiru ɗakin yayi kuwa na nashi tunanin,Umman Sa'eeda ce ta katse shirun da cewa" Dare yayi zoki kwanta, yanzu dai sai a sakarmin mara na huta tunda kinji tarihin kakarki ko"

 Dariya Sa'eeda tayi tare da cewa " Eh Ummina yanxu na gamsu sosai da bayananki, kuma zan cigaba da yi mana addu'ar ALLAH ya sadamu da ahalinmu"

murmushi Umman Sa'eeda tayi sannan tace"yawwa sayyin idaniya na, ALLAH ya amsa mana"

  da  "Allahumma Ameen" Sa'eeda ta bita dashi kana kowa ya kwanta. 


      @@@@@@@@@@@@@@


Yau ta ke babbar sallah,da sassafe su Sa'eeda suka tashi tare da gyaran gida sukayi wanka sannan suka shirya zuwa masallaci kasancewar Umman Sa'eeda tasan masallacin. 

Bayan sallah suka dawo gida wanda a lokacin ne aka yankawa Baba ƙaton ragonsa, a nan Umman Sa'eeda da Sa'eeda sukayi ma  Baba Barkha da sallah, sannan suke nufi cikin gidan, direct Umman Sa'eeda ta musu jagora zuwa ɗakin Gwaggo Ladi, a nan ta tarar da ƴaƴanta tare da jikokinta suna hira haɗe da raha abinsu, suna ganinta suka tamke fuska banda Mairi wacca tun shigowarta gidan ta ke alla alla su dawo taga ƴar uwata ta.

Russunawa sukayi  ita da Sa'eeda suka mata Barkha da sallah, a daƙile da amsa sannan suka gaida ƴan ɗakin, suma dai a daƙilan suka amsa musu sannan suka wuce ma saukinsu. 

Mairi ce ta bisu da fara'arta ko takan ƴan ɗakin bata bi ba ta wuce wurinsu. Koda zuwansu ɗaki sukaga an ajiye musu abinci wanda babu shakka Mairi ce ta kawo musu, zamansu keda wuya sukaji sallamar Mairi, da fara'a Umman Sa'eeda ta amsa  mata sannan suke rungume juna haɗe da murnar ganin juna bayan rabuwa. 

Haka dai sukayi hirarsu cike da annashuwa, sallah kadai ta ke tayar dasu kasancewar agidan Mairi zata kwana haka al'adar garin take.

 Haka dai su Sa'eeda sukayi shagulgulan sallah sannan suka dawo gida tare da ɗumbin alkhairai daga wurin Baba da Mairi.

Bayan dawowarsu da wasu kwanaki su Sa'eeda suka koma makaranta. Wannan kenan


      @@@@@@@@@@@@@@


ABUJA


Kasancewar duk babban sallah wannan family suke taruwa wurin shagalin bikin sallah yasa wannan Karon ma haka ta kasance.

Maa shaa Allah kawai zan iya furtawa ganin wannan family duk sunzo tun daga wa'inda suke Nigeria har ƴan UK ba sunzo banda Fadila saboda ƙaranci hutu da suka samu yasa Dad ɗinta yace baza tazo ba tunda ai tazo tayi 1 week a Nigeria, haka tayi ta kumbure kumbure daga ƙarshe haka ta haƙura da zuwan saboda school.

Garden ne nagani an ƙawatashi da wasu balloons kala kala anyi decorating garden yayi kyau sosai gashi an shimfiɗa wata babbar tabarma ammafa mai shegen taushi  kamar carpet ƴan aikin sunata kai kawo wurin ganin an cika wurin da abubuwan ci da na sha tun daga soyayyun kaji, abinci kala kala tun daga na Nigeria har na ƙasar larabawa haka aka jerasu ga gasashshan naman rago an banƙareshi  a tsakiya, haɗe da wuk'an yanka mai kyau.

 Gaskiya wurin nan ya ƙayatu matuƙa ainun, bayan gama gyaran wurin da ma'aikata sukayi sannan wannan familin suka zagaye wurin suna murna da ganin juna, haka suka ci suka sha suna dariya da shewa. 

A nan ne na hango Hajiya zaune a tsakiyar jikokinta tayi shiru, yaran suna mata wasa amman sama sama ta ke amsa musu,babbar ɗiyarta ne ta kula da yanayin mahaifiyartasu kasancewar tana kusa da ita.


             @@@@@@@@@@@@


 Bayan an kammala ci da sha  suka koma cikin gida,direct Hajiya ta nufi ɗakinta don batason hayaniya yau hasalima tun sanda shaiɗanin bokan nan ya mata maganar basu mutu ba hankalinta ya gaza kwanciya, bacci ma saidai ya saceta saboda tunani da zullumin daya addabi ruhunta, haka akayi sallama a ƙofar ɗakinta bata amsa ba saidai ta bada umarnin a shigo.

Babbar ɗiyarta ce Amina tashigo ta zauna kusa da ita tare da cewa "Hajiyata meya sameki ne ko bakida lafiya ne"

murmushi tayi a ranta tana cewa 'dama rashin lafiya ne ai mai sauƙine akan tashin hankalin da nake ciki'

sai kuma afili tace " kwana biyu nan ina fama da ɗan zazzaɓi da kuma rashin bacci"

habawa ai tuni Amina ta rikice da sauri ta ɗauki wayarta jikinta na rawa ta ke danna ma number family doctor sun don arayuwarta batason damuwa ko kuma rashin lafiya atattare da Hajiyarta, kiransa tayi tare da cewa yazo yanzu yanzun nan banda ɓata lokaci.

 Abinka da Naira duk da lokacin sallah ne amma haka Doctor ya taho gidan saboda yana girmama ƴan gidan sosai. (Ni kuma nace yana girmama Hajiya Naira ba😂🙃😇). 


     @@@@@@@@@@@@@@


Haka Doctor yazo ya dubata amma ya ce shi gaskiya baiga abinda yake damunta ba, hasalima tana cikin ƙoshin lafiya,duka familin suna ɗakin don Amina ta sanar da rashin lafiyar Hajiya ga kowa, suma da tashin hankali suka isa ɗakin nata. 

Bayan Doctor ya gama bayaninsa ya tafi,ɗakin ya koma shiru can Amina ya katse shirun da cewa " Kodai ashirya miki Visa ne yau, gobe mu wuce India a dubaki acan"

 Hajiya ce tayi murmushi tare da cewa "karku damu zan samu sauki don hakan na faruwa dani tun kuna yara,  karkusa damuwa aranku"

Haka dai sukayi jimaminsu sannan kowa yayi shirin komawa inda ya fito. A haka aka bar Hajiya cikin tunanin da yanxu ya zamo mata jiki. 


       @@@@@@@@@@@@@@


KEBBI 


Familin Alhaji Kabir Dikko family babbane  kuma sanan ne acikin birnin Kebbi, wanda ko mai machine ka sanar ma gidan Alhaji Kabir Dikko zai Kaika, yasan gidan kasancewar babban gidane wanda ya shafe layi guda cur da zuri'ar Alhaji Kabir Dikko da na ƴan uwansa, gidan yakama tun daga ƴaƴan Alhaji Kabir Dikko da ƙannansa, wanda duk sun rasu saura ƴaƴa da jikoki suka rage kuma har yanxu suna zumuncinsu ba tare da nuna banbanci ba.

Cikakkun ƴan boko ne kuma ƴan kasuwa sanannu a harkar kasuwancin cikin Nigeria da wajanta.Mom da kuka sani Maman Sadam(Auta) ta kasance jika ga Mariya ita ce babbar   ƴa ga Alhaji Kabir Dikko.

Duk babban sallah suke haɗuwa a family house ɗinsu ayi shagalin sallah tare da family meeting wanda ya ƙunshi magance matsaloli da kuma tallafama juna wurin ganin family ya samu daidaituwa. 

Alhaji Abubakar ɗa ne na biyu ga Alhaji Kabir Dikko kuma wanda ya rage a duk gidan tun daga kan ƙannan Alhaji Kabari Dikko har sauran ƴan uwansa wanda keda kimanin shekara 80 a duniya yanada yara hud'u a duniya. Kowa a familin yana matuƙar girmama Baba Garba wanda haka suke kiransa dashi tun daga  kan yara har jikoki da ƴaƴan jikoki haka suke kiransa dashi. 

Wannan Karon ma haka suka gudanar da shagulgulan sallah tare da family meeting ɗin da suka saba na kowani babban sallah, daga haka taro ya watse kowa ya nufi idan ya fito. 


       @@@@@@@@@@@@@@


UK


Bangaren Sadam autan Mum karatu ya soma zafi gashi Dad ɗinsa ya hanashi zuwa Nigeria sai ya kammala degree ɗinsa complete sannan ya dawo bautar ƙasa na shekara ɗaya, kana ya ƙara tafiya China don yin Masters ɗinsa don ƙara sanin harkar..................... 




Post a Comment

0 Comments