TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sarauniyar kyau page 15-16

 💓*SARAUNIYAR KYAU*💓

*Page 15&16*


Da sauri Bilki ta kalla Jieddarh hadda dafe ƙirji ta ce "wani YaYa Heesham ɗin, Badai masoyina ba?,"

"Of course yes, shi fa," cewar Jieddarh, miƙewa Bilki tayi zata bar gurin, Da sauri Jieddarh ta ce "ina zaki je ne, Haka?," "Hmm ke dai Jieddarh barni kawai zanje naga mai son masoyinane," Da sauri Jieddarh ta ce "to ki tsaya na faɗamiki wani abu mana.


Dawowa da baya Bilki tayi to gani faɗamin halayenta ina sauraronki,"  "haba malama Bilki toki nutsu mana saina faɗa miki yadda kema zaki fi fahimta," zama Bilki tayi cikin ƙosawa ta ce "to faɗamin ina sauraro," Ajiyar zuciya Jieddarh ta sauke sannan ta ce "kedai Bilki na farko dai ko shekara bakiyi a gidannan kina aiki ba watan ki bakwai ne, dan haka baki gama sanin halayyar ƴan gidannan ba ma balle kuma ƴan waje," ɗan shiru Jieddarh tayi sannan ta ci gaba cewa "ita wannan Ni'ima beauty da kika ganta ba'a shiga harkar ta, saboda bata da kirki ko kaɗan sannan kuma tanason YaYa Heesham highly highly kuwa," Jieddarh tayi maganar tana dariya, Ɗan kallon ta Bilki tayi cike da takaici da kishin Ni'ima ta ce "Yasin Jieddarh da nasan wannan shirmen zaki faɗamin da ban tsaya ba, Yo ni Allah na tuba kar tayi kirkin mana ina ruwa na da ita," Da sauri ta miƙe ta shige palon, Jieddarh ta bita da kallon tausayi kawai, Eh mana dole ta tausaya mata saboda wannan makauniyar soyayya da takewa Heesham, Jieddarh tasan halin Auntie yadda ta tsani talaka fiye da yadda ta tsani mutuwar ta da wuya wannan Auren ya yuwu gashi kuma soyayyar ɓangare ɗaya ne sai dai kawai Bilki ta sha wahala.


Bilki tana shiga palon ta samesu zaune sunyi ɗaiɗai saman Royal sofa's ɗin dake palon sai fira sukeyi da Auntie.

Kai tsaye kitchen ta shiga bayan wani lokaci ta fito hannun ta riƙe da Tray mai ɗauke da cups guda huɗu a saman, ciki juice ne mai sanyi, Ƙarisowa gurin su tayi ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana raba musu wannan juice, Saida ta gama raba musu tas sannan ta dawo gurin Yarinyar Nafisah tana mata wasa ita kuwa Yarinyar sai ɓangale baki takeyi tana dariya, Dama ance mai ɗa wawa ganin haka yasa Nafisah cewa "Hi young lady what is your name?,"  Da sauri ita ma Bilki ta harhaɗa ɗan turancin da ta koya a makarantar gwamnati da tayi ta ce "year Aunty My name is Bilkisu Adam Mai gazon Zinare."

Dariya Nafisah tayi ta ce "aikuwa sunan ki mai ɗadi it's deserved to you beauty.

"Na gode highly highly" cewar Bilki a lokacin da take ɗaukar Yarinyar zata fita da ita, Harta kai ƙofa taji Ni'ima na faɗin "Yanzu fisabilillah Mamy Nafisah wannan bagidajiyar Yarinyar zaki bari ta ɗaukar miki ƴa kamar bakisan zafin haihuwa ba kwata kwata Yarinyar nan naki ko shekara batayi ba haba adai duba lamarin," Nusaiba ta amsa da faɗin barta Allah yasa a kwaso mata cutar talakawa babu ruwanmu ciki," ita dai Bilki fita tayi tanajin Nafisah na basu amsa ita kuwa tayi tafiyar ta a zuciyar ta ta ce "wannan Ni'imar anyi shegiya tayi da baki kamar mariƙin lema saina koya mata hankali soon na lura bata da wani cikakken hankali akanta.


Ƙarisawa gurin da Jieddarh take zaune Bilki tayi ita ma ta zauna kallon Jieddarh Tayi ganin Yadda gabaɗaya ta Mayar da Attention ɗinta akan tsadaddiyar Wayarta ƙirar SAMSUNG GALLAXY dake hannunta, Ta ce "lafiya kuwa Jieddarh wannan ƙurawa Salulah ido fah bakya tsoron Ya shafa lafiyar idanunki?".


Ajiyar zuciya Jeiddarh ta sauke Still idonta Yana kan Wayar hannunta Ta ce "kedai Bilki Bari kawai domin kuwa Wani ƙayatacce kuma haɗaɗɗen Labari Nake karantawa shiyasa Banma san Lokacin da kika ƙariso bah," Murmushi Bilki Tayi sannan ta ce "ato ae dama daga ganin Yadda kika Mayar da gabaɗaya hankalin ki akan wannan tsadaddiyar Wayar hannun ki nasan da wata a ƙasa, Toh dai Yanzu Zan iya Sannan Sunan wannan ƙayataccen labari Wanda Ya Tafi da gabaɗaya hankalin ki, Idan akwai dama, ma sai kiyim ƙarin bayani akan Yadda zan samu na siya nima na karanta cikin nutsuwar zuciya."

Ƙayataccen murmushi Jieddarh Tayi sannan ta ce "Tabbas akwai dama highly highly mah Yanzunnan zanyi miki dogon Bayani akan wannan shahararren Labari Wanda Yazo da salo na daban.........

Da Farko dai Sunan Wannan Katafaren Labari shine 🅂🄰🅁🄰🅄🄽🄸🅈🄰🅁 🄺🅈🄰🅄 sannan ya sama rubutu ne daga Alƙalamin sabuwar marubuciya 🄺🄷🄰🄳🄸🄹🄰🅁🅃🄷 𝕎𝕒𝕥𝕠 🆃🅷🅴 🅽🅰🅸🅽🅰🆁🅷 🅺🅳, sannan kuma wannan labari zaki iya samun shi a kafar yanar gizo kamar irinsu, FACEBOOK WHAT'SAPP TELEGRAM WATTPAD, ke idanma kina da buƙata zan iya baki phone number na wannan marubuciyar domin tayi adding ɗinki a what'sApp Group nata da take Tura SARAUNIYAR KYAU ciki fah.


Washe baki Bilki Tayi Sannan Ta ce "ah gaskiya daga Jin wannan Bayani Naki Nasan Wannan Novel zai Bada Jitta obaaaaa ae ina faɗamiki Jieddarh Yanzunnan Zan kwashe What'sApp lamba Nata domin na dunga samun updates wannan ƙayataccen labari don kar a barni a baya🤓

Murmushi Jieddarh Tayi sannan ta ce "aikuwa dai ya kamata don kema ki ƙaru da abinda yake ciki.


Bilki Ta ce ohoo kaji ƴar gari kuma ƴar birni, yanzu abinda za'ayi kawai phone number na wannan Marubuciya zaki bani yanzu na lalubota, "Zan baki amma ba yanzu ba", "to sai yaushe Bilki ta tambaya jin abinda Jieddarh ta faɗa.

Murmushi Jieddarh tayi ta ce "saima gama ja miki aji sannan " Humm amma Yasin Jieddarh kina da wulakanci sai dai ya na iya da saurayin ummata haka zanyi haƙuri ki gama jamin ajin" Bilki tayi maganar Like a orphan tana mai yin alamun tausayi murmushi kawai Jieddarh tayi ba tare da ta ce komai bah.


Haka dai suka ci gaba da fira da Jieddarh sun daɗe suna fira kafin wani lokaci su Nafisah suka fiffito, Da alama tafiya  zasuyi gurin su Nafisah ta ƙariso karɓar ɗiyar ta sai dai kuma me aikuwa Yarinya ta fara kuka ba za ta je wajen ta ba, Wai ita harta saba da Bilki dariya Bilki tayi ta ce "Yau na sama ɗi ya ɓagas gashi kuma banma san sunanta ba amma ta maƙale min" Nafisah na murmushi ta ce "sunanta khausar", "wow nice name shiyasa take sona ashe taga ɗiyarta ne" cewar Bilki tana washe baki "da gaske haba kice sunan mama ce da ita Nafisah ta tambaya cikin murmushi, "Yasin kuwa sis" cewar Bilki tana jijjiga khausar ɗin dake kuka, "gashi kuma taƙi ta yarda dake yanzu ya za'ayi gashi kuma jiran ki akeyi Jieddarh ta faɗa ganin yadda Yarinyar kamar wata mai wayo taƙi zuwa wajen mahaifiyar ta😕.


Ni'ima ce ta ƙariso gurin cikin isa da gadara Like a ɗiyar Gwamna "lafiya kuwa Mamy Nafisah kizo mu tafi mana kin tsaya magana da wannan dirty girl ɗin."

"To Ni'ima yarinya dai taƙi yadda dani fah"

"Taƙi yadda dake kuma ban gane taƙi Yarda dake ba, kar dai ace an asirce miki ƴa ne daga raino" Ni'ima tayi maganar tana ɓalawa Bilki harara dan haka kawai taji bata mata.

Ba wanda ya kulata a cikin su, saima bawa kurma da blind da mara aikin yi, Ajiyar ta da sukayi😇.


"Please Mamy Nafisah ki karɓa ɗiyar ki mu tafi mana, dare nayi fah, Ni banma san dalilin da yasa mukazo gidan Mamy Jamila da Yamma ba gashi garin hadarine highly" Ni'ima tayi maganar da iya gaskiyar ta, Da ƙarfi ta karɓa Yarinyar a hannun Bilki tana faɗin "aikin kawai, ke Mamy Nafisah sai ki zo muje ae", tayi gaba abinta haƙuri kawai Nafisah taba Bilki jin an fara ruwan sama, ta ce "karki damu Bilkisu ina nan dawowa wata rana zan dawo, kuma a gurin ki khausar zata wuni, kuma ke zanba yayenta idan lokaci yayi tunda naga tana sonki insha Allah," Murmushin jin daɗi Bilki tayi ta ce "ba komai sis Nafisah, kuma ina sauraron ranar da za'a kawomin lovely Khausar momyna yaye," "Lallai ma wato har kin saka mata suna Lovely momy ko?," cewar Jieddarh cikin murmushi, ita ma Nafisah murmushi kawai tayi sai dai ba ta ce komai ba saboda rashin lokaci, sallama sukayi su Nafisah suka tafi, su kuma Jieddarh suka koma ciki jin ruwa ya tsinke kamar da bakin ƙwarya.


🅱🅰🆈🅰🅽☆🆂🅰🆃🅸☆🅱🅸🆈🆄


         


ABUJA


Kwance take tayi ɗaiɗai, Tana kallon sararin samaniya kamar mai ƙirga taurarin dake a sararin samaniyar, Ta saka hannun ta ɗaya tana murza dogo kuma baƙin gashin kanta wanda ya baje a saman koranyen ciyawu wato Grass carpet dake a cikin garden ɗin da take ciki kwance, wanda aka qawata da shuke shuke da kuma bishiyu kala kala kamar su  mangwaro,gwaiba,taura ayaba. Da dai sauran su, da sauran su.

Headphone ne manne a kunen ta tana sauraron lyrics na mawaƙiwa celline Dion mai taken "A New day has come" ta lumshe idanun ta Yayinda take bin waƙar a hankali cikin ranta.


Gefen ta kuwa Afeefah ce, zaune a kujera mai lilo dake a garden ɗin Al qur'ani ne a hannunta tana tilawa.

Riga ce top fara a jikin ta sai wando crazy jeans black kanta kuma Baby hijjab ne black shima, shiga kala ɗaya ne a jikinsu su biyun kammala karatun nata ne yayi daidai da haske da wayarta tayi alamar dai kira ne ya shigo, waƙar shani'a Twain, "Forever and for always," ya karaɗe gurin hannu tasa ta ɗauki wayar dake a gefenta, nan sunan  SISTER NAINARH, ya bayyana saman screen ɗin wayar, sallama tayi bayan tayi picking call ɗin.

Zuba mata ido Lailah dake Kwance saman Grass carpet Tayi, shiru taga tayi da alama magana ake ta ɗayan ɓangaren, Can sai kuma taga Afeefah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "eh da sauƙi dai......Shiru ta kuma yi can ta kuma cewa "a'a nima dai ba na ce ba kawai dai muna zaune a palon ƙasane mukaga ta faɗo daga saman step's na staircases mu kuma muka kaita asibiti kuma koda muka dawo mun duba bamu ga komai a ta gurin da ta faɗon ba, sannan mun tambaye ta ta ce ita ma bata san meya faɗo da ita ba kawai dai abin ya faru ne in insticnt.."

Ɗan shiru ta kuma yi alamar sauraron maganar da mai kiran nata takeyi, Zumbur ta miƙe tsaye fuskar ta cike matsanancin farin ciki take faɗin "Please sis ki rantse, yaushe kuma a wani airport ɗin gamu nan zuwa Yanzunnan," sai kuma ta katse wayar tana kallon Lailah data zuba mata kyawawan idanun ta tana kallo.

Ta ce "Hello babe Aunty Nainarh ta shigo ƙasar fah, Yanzu take faɗamin, don haka ki taso mu tafi airport mu ɗaukota kawai ba saimun tsaya jiran drivers ko escort bah."

Ɗan waro ido Lailah tayi alamar mamaki ta ce "sister Nainarh kuma ita kaɗai ce, ko kuwa dai." Cike da ƙosawa Afeefah ta ce "ke dalla malama ki taso mu tafi mana, ita kaɗai ne mana dan  kema kinsan wannan mijin nata mai kama da zabiya ba zuwa zayyi ba.

Ɗan taɓe baki Lailah tayi "well koma miye ae ita taja ma kanta ace mahaifiyar ta guda ta sama karaya amma sai da akayi sati biyu shine zata wani ɗauko ƙafa ta taho" Lailah tayi maganar cike da takaici, tana miƙewa, suka shiga cikin gidan su fara shiryawa sannan su wuce airport ɗin.


****

💓💔💓

****

"Wai kuwa gwaggo na nace yanzu muna sauka a motar nan shikenan mun shiga birni ko kuma ma a birnin garin habuja ko?, daga yau shikenan bani ba ƙauyenmu,bah su delu babu ƴan ƙauyenmu balle kuma na rama abinda sukamin shikenan sun shani a musilla."

Wata kyakyawar matashiyar Budurwar Yarinya ce duk take wannan zubo zancen ga gwaggon ta a cikin motar da suke zaune a gidan baya ga sauran mutane nan a motar gaba da baya.

Ta ci gaba da cewa "waima gwaggo na yanzu aikin me zan dinga yine idan munje gidan aikin da zaki kaini?, bata tsaya ba ta ci gaba da cewa "kuma shikenan kina kaini zaki dawo gida kiyi auren ki, abin ki, Ki barni a Habuja ni kaɗai bansan kowa ba kowa bai sanni ba, kawai saita fashe da kuka, Gwaggo ta kalleta cike da takaici ta ce "au yanzu dije tun kafin na kaiki gidan aikin zaki faramin kuka kamar na dake ki faɗamin na dake kine ko kuwa gidan aikin kikeyi ma kukan ban sani bah."


Cikin muryar kuka budurwar ta ce "toh gwaggo ba kece kika ce a birni zaki barni ba ni kaɗai ba, kuma ae nace miki kiyi hakuri bazan ƙara faɗa dasu hanne ba, kuma fah su suka fara tona na shine ni kuma na rama kuma ke gwaggo ma ae kinsan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi shine sukamin duka, gefe ɗaya kuma ga dukan da wannan matar tayimin gashi jiki na baigama warkewa bah, fuska ta ma haka shi ne kika kawo ni aiki don a ƙarisani."


Ɗan tausayinta ne ya kama gwaggon nata, a hankali gwaggon ta ce "ae ke ce dije na hanaki wasan banza dasu hanne amma ba kyaji sannan kuma da kike cewa na kawoki aiki birni ae mahaifin ki shine ya ce a kawo ki aiki birnin bani ba.".


shiru budurwar tayi tana kallon gwaggon sai kuma tayi murmushi ta ce "toh gwaggo makaranta na fah zan ci gaba da zuwa anan abujan kuwa?, ɗan shiru gwaggon tayi kamar mai tunani sai kuma can ta ce "eh to idan kika nutsu highly, ƴan gidan suka ga irin nutsuwar ki wata ƙila su iya saki a makarantar.


Dariya tayi cike da farin ciki da yarinta kamar ba ita ce mai kuka yanzu ba ta ce "shikenan yanzu sunana ya tashi daga dije sai dai Nanah ko kuma ace min Deejarth ko Deejarh irinna ƴan birni, na bar su hanne da wahalar ƙauye da sunan ƙauye," ta kuma gyara zaman ta a motar tana kallon cikin garin abuja ta glass ɗin motar, sannan  ta kuma juyowa tana kallon gwaggo ta ce "gwaggo yanzu fah, su ƴan birni sunan su bah irin na ƙauye bane koh?," gwaggo tayi dariya ta ce "sosai ma, aisu ƴan  birni sunan su na daban ne, special ne in miki na turawa.


Dije ta ce "ae ina faɗamiki gwaggo na muna zuwa gidan aka tambaye ni sunana zance Deejarh ta faɗa tana nuna yadda zatayi wajen faɗan sunan nata idan aka tambaye ta, wannan karon ba iya gwaggo ne tayi dariyar ba hadda sauran ƴan motan wata mata a motar ta ce "Deejarh aikuwa suna mai daɗi, it's nice name."


Dije tana yanga ta ce "tnx" wai irinna ƴan birni matar ta kuma cewa "hala daga ƙauye kike, Ah ah su Dije an sama guri ga abokiyar hira ta samu ta ce "Yasin kuwa kamar kin sani, daga ƙauye nake amma yanzu na shigo birni ae," matar da alama ita ma "A" ce a gurin surutu ta ce "to su sunan ƴan ƙauyen da naji kina faɗa ya suke?.

wannan karon kallon matar Dije tayi highly, ta dai ga alama gilama ko sunan ƙauye matar bata sani ba.


Hadda sauke Ajiyar zuciya tayi sannan ta ce "sunan ƴan ƙauye yanzu kamar dai ace sunan ki Hafsat a birni tofah a ƙauye ina faɗamiki sai dai a kira ki da hanse ko kuma ace hansi ko kuma hansatuwa 🤣😂😅.

 

ko kuma sunan ki sa'adatu a birni tofah ina faɗamiki idan a ƙauye ne sai dai ace miki sa'ade ko kuma a kira da sa'a duk da dai sunan gwaggo nane sa'aden amma Yasin na faɗa.


Gwaggo dake gefe ta ce "ae dama kin rainani shiyasa kike kiran sunana haka gatsal"  Dije tayi dariya ta ce "gwaggo kenan ae wannan bayani nakeyi shiyasa kikaji na faɗa sunan ki a haka,"  Dije ta kuma kallon matar ta ce "ni kuma yanzu kamar ni sunana "khadeejah" amma a ƙauye kinsan me ake cemin kuwa?, matar tana dariyar Dije ta ce "a'a saikin faɗa ae zan sani ko?."

Dije ta girgiza kai alamar takaici sannan ta ce "wai fah Dije ake cemin, wasu ma har magajiya suke cemin, a birni kuwa ae sai dai kiji ance deejarth Deenah ko kuma ace Nanah ko Nainarh koma hadiza ga sunan nan dai kala kala sai wanda mutum ya zaɓa a birni.


Wata budurwa ce ta ce "ni kuma sunana AYSHA idan a ƙauye ne, me ake kiran mai sunan?... Dije ta kalli budurwar da ta kira kanta da AYSHA gata ƴar gayu kyakyawa da ita, sannan tayi murmushi ta ce "ae Yasin ina faɗamiki Yadda kike da kyau ɗinnan a ƙauye ba ruwan su sai dai kiji ankira ki da a'i ko kuma indo ko esha ko ma shatu, bah wani sunan ki AYSHAN NAN Yasin, AYSHA tayi dariya ta ce "amma za'a iya cemin Humaira ko A`ishatu acan ɗin ko?," Dije ta ce "idan kinci sa'ah ba."



Post a Comment

0 Comments