TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sarauniyar kyau page 21-22

 *page 21&22*


...A hankali ta lumshe idanun ta tana faɗin "oh Allah ko nima yaushe zan haɗu da masoyina na gaskiya ne?."

"Nan bada daɗewa ba Insha Allah, zaki haɗu da Yariman ki, ƴar uwa,"

Taji muryar Bilki tana faɗar haka, ɗan waro ido tayi dan batayi tunanin a fili tayi maganar ba, a hankali Bilki ta dawo kusada Jieddarh ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun tana faɗin.

 "Insha Allahu nan bada daɗewa ba inaji a jikina, kema zaki haɗu da naki Jarumin bi'iznillah, ɗan dariya Jieddarh tayi ta ce "Bilki kenan bazaki fahimta bane kawai," Bilki ta ce "ki fahimtar dani mana?,"

Gyara kwanciyar ta tayi a kujerar sannan ta ce "abar maganar kawai,"  Bilki tana dariya ta ce "a'a wallahi da dai an ci gaba saboda inajin daɗinta,"

Murmushi Jieddarh tayi ta ce "Bilki anya kuwa an taɓa faɗamiki kin zare?," dariya Bilki ta kwashe da shi sannan ta ce "a'a gaskiya ba'a taɓa faɗa ba, amma yau anfaɗa,"

 Murmushi Jieddarh ta kuma yi, "Bilki kenen YOU CRAZY IN FALL IN LOVE ❤.


"Kinsan miye kuwa?,"  Bilki ta tambayi Jieddarh, a hankali Jieddarh ta girgiza mata kai alamar a'a.

Bilki ta ce "yau sai naga kamar ba ƙya cikin special mood fa," "saboda me kika ce haka?,"  Jieddarh ta tambaya, Bilki ta ce.


"Hausawa sukace maganar zuciya a tambayi fuska, alasa nayi hausar dai dai, kinsan hausan nawa sai aslowly fa, abinki da bafulatana,"

Fashewa Jieddarh tayi da dariya, "wai maganar zuciya a tambayi fuska wannan hausan fa, cewar Jieddarh still cikin dariya.

Ita ma Bilkin dariya tayi dama tayi hakan saboda taga fara'ar Jieddarh ɗin ne kuma tayi winning tunda ga Jieddarh tana dariya harda ƙyaƙyatawa.


Gyara zamanta tayi a kujerar tana fuskan tar Jieddarh ta ce


"kinsan wani abu kuwa?," 


"a'a saikin faɗa,"


Bilki ta ce "ina faɗamiki a lokacin da zaki haɗu da yarimar ki zaizo miki yana akan farin doki fuskar shi ɗauke  da ƙayataccen murmushi idanun shi ɗauke da kallon ƙauna zuwa gareki, zai ɗaukeki ya ɗauraki saman farin dokin sa, kuyita zagaye fili sirdi, abinku cike da farin ciki kuma.....Da sauri Jieddarh ta dakatar da ita ta hanyar faɗin "wait a minutes  tsaya_tsaya yarima kikace fa, please faɗamin a wani film kika kalla, hala dai indian film ne nasan sune suke irin wannan labarin soyayyar........Jieddarh tayi ma Bilki tambayar tana zaro ido haɗe da jiran amsa.


Dariya Bilki tayi tana faɗin, "a'a ba'a film na kalla ba, inaji ajikina dake zai faru, haka kawai nakeji a jikina ɗan sarki zaki aura dan dashi kika dace, domin keɗin matar saraki ce, haka zalika matar manya,"  wayyo Allah na harna fara hangoki a gidan sarauta kina zuba mulki, kuma zakiyi kyau da zama gimbiya yasin.....


Dariya Jieddarh keyi tsaban dariya hadda riƙe ciki jin abin da Bilki take faɗi.

Bilki ta ci gaba da cewa "dama kawai ranar gasar nan kiyi shigar sarauta nasan zakiyi kyau, ba kaɗan kaɗan ba."


"to za'ayi kamar yarda kika faɗa your highness, cewar Jieddarh cike da nishaɗi tana sakin murmushi a lokacin da tayi imagine gata cikin kayan sarauta wow abin ba'a magana is so sweet.


Jin ana kiran sallan magarib ne yasa suka tashi a tare suka nufa ciki, yayinda Bilki ta wuce BQ ita kuma Jieddarh ta shiga ciki a main palo ta sama ƴan gidan gabaɗayan su amma banda Heesham, Auntie ne sai aAbba (Alhaji Jafar Komai Naka) da kuma Humaira, magana suke amma tana shigowa sukayi tsit, bata kawo komai ba, ta gaisar da Abba ta haye sama Bedroom ɗin ta domin yin sallah.


________________________~~~~

ɯαʂԋҽ ɠαɾι

-----------------------


ɯαʂԋҽ ɱιʂαʅιɳ ƙαɾϝҽ ɠσɱα ʂԋα ԃαყα ɳα ʂαϝҽ


ʝιҽԃԃαɾԋ


Zaune take a palo saman kujera mai ɗaukar mutum ɗaya gefenta kuwa, Bilki ce tana mopping a palon suna taɓa fira kaɗan kaɗan don Jieddarh tafi mayar da hankalinta akan tv tana kallon wani ƈԋιɳҽʂҽ ԃɾαɱα ~ρɾιɳƈҽʂʂ αɠҽɳƚ~ 𝚗𝚊 𝚓𝚊𝚛𝚞𝚖𝚊𝚛 𝚌𝚑𝚒𝚗𝚊 𝚐𝚠𝚊𝚗𝚊 𝚐𝚞𝚛𝚒𝚗 𝚓𝚒𝚎𝚍𝚍𝚊𝚛𝚑 𝚠𝚊𝚝𝚘  *z̟h̟a̟o̟ l̟i̟y̟i̟n̟g̟*


Gidan ba kowa sai su biyu Auntie ta fita company gurin aiki Abba ma haka shi ma Heesham office, ita kuma Humaira bata daɗe da fita ba, tana karatu a University tana karantar mass.com.


Sai gidan ya kasance su biyu ne ciki, sai kuma mai gadi da sauran masu aiki.


Bilki jin tana magana ba'a kulata ba yasa ta kalla ɓangaren da Jieddarh take a zaune gabaɗaya hankalinta yana kan tv sai faman sakin murmushi takeyi, ganin haka yasa ita ma Bilkin gwanar soyayya, mayar da kallon ta, akan tv dan taga abin da ya ɗaukewa Jieddarh hankali a ciki, ba shiri ta saki murmushi  ganin stars ɗin film ɗinne ake caskalewa.


Jieddarh cike da nishaɗi ta ce "inason wannan jarumar obaa, ta iya faɗa kala kala especially ma kung fu, ga iya acting.


Bilki ce ta tambayeta hanyar cewa, "miye sunan ta," Jieddarh ta ce sunan ta, *ȥԋασ ʅιყιɳɠ* Bilki ta ce cabɗijan ana suna a duniya wani irin sunane kuma 'chao liying ' ko me, ni bama zan iya faɗa ba.


Jieddarh tayi murmushi tana gyara mata sunan ta ce "Zhao liying' ake cewa fa, "jinki fa, wai 'zhao liying' taɓɗi, Bilki ta jajanta tana ya mutsa fuska, ta ci gaba da cewa, "ina faɗamaki ɗazu fa, har wani kallon ƙauna mutumin yamin dana gaisheshi."


Jieddarh harta buɗe baki zatayi magana sukaji door bell, Bilki ce taje ta buɗe ƙofar.


Baki da hanci ta saki ganin wacca take a ƙofar palon Ni'ima ce gabanta kuwa akwatuna ne masu kyau guda biyu, mai gadi ya kawo mata da alama hutu tazo.

Matsa ma ta Bilki tayi don ta sama hanyar shigowa, ganin tana ƙoƙarin tureta ta shiga, ko sallama babu Ni'ima ta shigo palon yayinda mai gadi ya biyota da akwatu nanta, bata kula Jieddarh dake binta da kallon mamaki ba, ta saka key ta buɗe wani bedroom anan palon ƙasan da alama anan take sauka idan tazo tunda ga key a hannunta, buɗew tayi ta shiga in.


Bilki dake riƙe da baki tunɗazu a fili ta ce "jar bala'i yau nake ganin abin mamaki kare da tallan tsire.


Jieddarh tayi murmushi ta ce !Bilki kenan akwai ki da neman magana fa," 

Bilki tayi dariya tana faɗin "ai abinne yafi ƙarfin kaina da ɗan tunanina, inaga ai koda sallama ta mana tunda dai duka musulmai ne, amma na mata uzuri saboda batasan Menene fa`idar sallama ba, da alama."


"Kedai kiyi aikin baganki kawai malama," cewar Jieddarh tana gyara kwanciyar ta saman 3sieter, tana rufe baki saiga Ni'ima ta fito daga ɗakin data sauka, sanye cikin £nglish wears riga brown color, hannun rigar anyanka ta wajen kafaɗarta sai skert pencil black iya gwiwar ta  mai adon stones brown,  kannan nata ko arzikin hula bai samu ba yatsa kitson attach mai tsadar gaske brown, ta zubo kitson ta gaba tayi kyau ba ƙarya sai baza ƙamshin turaren white gold takeyi zama tayi a saman 2sieter, ta ɗauka remote control ta canza channel zuwa na waƙoƙi.


Ba ido kaɗai ba hatta baki da hanci saida malama Bilki ta saki tana kallon ikon Allah, ita kuwa Jieddarh ko a jikinta da alama ta saba da ganin haka.


Saida ta gama shan ƙamshinta sannan ta kalla Jieddarh ta ce "hala dai surukata batanan ne?," 

Jieddarh yi tayi kamar bataji mai ta ce ba, a zuciyarta ta ce "idan ma zaki buɗe baki kiyi magana ki buɗe malama," ganin alamar Jieddarh ba ta jita ba, yasa ta ɗan ɗaga muryar ta ce,


"Jieddarh,  Jieddarh magana fa nake, nace hala dai suruka ta batanan ne?,"

Murmushi Jieddarh tayi sannan ta buɗe idonta da ta rufe kamar bacci ta ce "oh wai Auntie kike magana, ta tafi wajen aiki bata faɗamiki bane hala?,"

"Bata faɗamin ba wallahi, kuma tasan zanzo may be ta manta ne."

Ni'ima ta faɗa tana mai da akalan kallon ta kan Bilki cikin ya tsine fuska ta ce "Bilki kike ko, please dafa min indomie guda ɗaya kwai biyu saiki haɗomin da juice mai sanyi cuz i'm hungry obaa.


Ajiye moppern dake hannunta Bilki tayi sannan ta nufa hanyar kitchen tana faɗin "ba ki da damuwa Auntie beauty wato surukar hajiya jamila."


Tana shiga kitchen ɗin ta ɗauka pot ƙarama, dai dai one indomie, ta wanke sannan ta kunna gas, ta ɗaura tukunyar, kana tasa ruwa kaɗan saida ruwan ya tafasa sannan ta zuba indomie guda ɗaya ta ɗauko mai tasa sannan tasa maggie's kala kala batasan adadi ba ita kanta, tana murmushi hadda ɗan raira waƙanta "yau za'aci indomie, a ƙoshi highly, indomie wanda ba'a taɓa cin kalan shi ba, badai yau anzo kwaɗayi ba, gidan mutane hadda shigan arna to yau za'a gane kure highly highly.

Tana girkin tana raira waƙar abinta spicy's ta ɗi bo a spoon ba adadi ta zuba, sannan tayi twisted.


Tsayawa tayi tana tunanin wani muguntar zata ƙara kuma, "yes na tuna" ta faɗa sannan ta ɗauko onion ta yayyanka a chopping board,  ko wankewa batayi ba ta zuba a haka saida indomie ɗin ya nuna sannan ta juye a plate.


Da sauri ta haɗa lemun abarba da kwakwa, ita da zatasa sugar a juice ɗin amma saboda iya shege salt ta ɗi bo a cokali ta zuba, ta juya saida ta kammala komai sannan ta zuba juice ɗin a cup, Tray ta ɗauka ta ɗaura plate ɗin indomie a ciki sannan ta ɗauka juice ɗin shima tasa a tray ɗin, ɗauka tayi ta nufo waje.

Palo ta fito a lokacin Ni'ima tana waya, ita kuma Jieddarh tana kwance a inda ta barta da alama ma bacci yayi gaba da ita, saman center table ta ɗaura tray ɗin sannan ta matso dashi gaban Ni'imar ta yadda zataji daɗin meal.


Tana aje Tray ɗin ta ce "Auntie beauty gashi nan, na kammala fa," tana gama faɗar haka ta ɗauka mopper ɗinta da sauran abubuwan ta  tabar palon tana dariya lols😂


Ni'ima tana kammala wayar ta matso da table ɗin gaban sosai ta yadda zataji daɗin kai loma, tana buɗe plate ɗin wani ƙamshi da tururi yayi mata sallama lumtse ido tayi tana ayyano yadda indomie ɗin zayyi daɗi.

Ɗan waro ido tayi ganin bata soya mata eggs ɗin da ta sakata ba, qwafa taja tana faɗin wannan yarinyar batada hankali, na sakata aiki taƙiyi."

Ta faɗa a daidai lokacin da takai indomie cokali ɗaya bakinta,  wani uban yaji ne da magi yayi ma ta sallama, ai ba shiri ta dawo da shi waje, da sauri ta ɗauka juice ɗin takai bakinta domin ya ma ta maganin raɗaɗin azabar da ya ziyarci bakinta.

Tana sakawa a memakon taji sasauci ina, ai saima wani uban gishiri da taji har wani ɗaci ɗaci game da bauri bauri yakeyi.


Ihu ta kurma wanda yayi Sanadin tashin Jieddarh a tsorace, saboda azaba Ni'ima tama kasa magana sai hawayen wahala take zubarwa gashi ta riga ta haɗiye juice ɗin da ta kafa a baki maƙogwaronta har wani qurjine ya fito dan azaba lolz.😳


Da sauri Jieddarh ta miƙe ta ɗauko mata ruwan gora ever, a fridge ta bata, hannunta na rawa ta karɓa ta kafa a baki saida ta kwankwade shi tass, sannan tayi jifa da gorar tana sauke haki na wahala, ido jajur.

Jieddarh sai faman ƙumshe dariya takeyi ganin yadda kwalliyar Ni'ima ya tashi aiki jam baki har kumatu tasan wannan kaɗanne daga aikin Bilki 😀


Zama tayi a kujera tana kuma kallon yadda Ni'imar take faman kakarin amai, amma yaƙi zuwa, "sannu kinji Ni'ima beauty sannu fa,"  Jieddarh ta faɗa tana kuma umshe dariyar ta,

Ko kallon ta Ni'ima batayi ba ta shige ɗaki ta banko ƙofar, jikake garamm.

"a'a ai bani na kar zomon ba, rataya aka bani Auntie Beauty,"  cewar Jieddarh tana fashewa da dariya a fili ta ce "Bilki kin taho march wallahi, Allah yasa kinada ƴan wasa lol 😂

Remote ta ɗauka ta sauya tashar waƙoƙin da Ni'ima tasa zuwa korean drama MY STRANGE HERO.


~~~~


𝙳𝚊 𝚢𝚊𝚖𝚖𝚊 𝚠𝚞𝚛𝚊𝚛𝚎𝚗 𝚔𝚊𝚛𝚏𝚎 𝚋𝚒𝚢𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝚛𝚊𝚋𝚒 𝚗𝚊 𝚖𝚊𝚛𝚎𝚌𝚎.


ʝιҽԃԃαɾԋ☆ʝυɾαҽʝ


Kamar yadda ta saba Jieddarh tana kwance a garden saman lallausar carpet ɗin da ta shimfida, laptop ne a gabanta tana search na  'ρɾιɳƈҽʂʂ ԃɾҽʂʂ' kala kala a youtube.

Gefenta Bilking ce zaune a ɗaya daga cikin resting chairs na garden ɗin  taci ado cikin riga da zani na atamfa, ga ɗan kwalin nan tayi ɗaurin zarah bahari dashi, tayi kyau ba ƙarya Fuskar nan tasha light make up da Jieddarh ta ɗanɗasa ma ta.


Hannunta kuwa yasha jan henna lalle, wanda ya ƙarawa farar fatarta kyau, Bilki kyakyawa ce ita ba laifi.


Kallon ta Jieddarh tayi tana ɗan murmushi ta ce "wai duk wannan kwalliyar kamar zakije gasar SARAUNIYAR KYAU ta duniya, duka na yaya 'H' ne?, gaskiya anaji dashi sosai fa,"


Ƙayataccen murmushi Bilki tayi tana wani fari da ido ta ce "to ya san ranki, yauwa Jieddarh dama inaso kifaɗamin abinda zance mishi ne, idan ya dawo, kinga yanzu ya kusa dawowa fa,"

"ke Bilki kifa dinga bi aslowly, idan ba haka tom, shawara ce,"

cewar Jieddarh dan ta lura idan ba tana dakatar da Bilkin a wasu abubuwan ba, tofah ita Bilkin ita ce zata sha wuya ba kowa ba.

"kedai malama kawai ki faɗamin abin dana tambayeki kinji,"  Bilki ta faɗa ko'a jikinta da abin da Jieddarh ta ce ma ta.


"inaga kawai kice mishi welcome yayi," 


"haba Jieddarh wani 'welcome' kuma?, ai welcome ya zama tsohon yayi gaskiya."

Cewar Bilki tana kyaɓe fuska.

Jieddarh ta ce "toni kinga dai ba soyayya nake ba, balle nasan me zance miki ko,"  Bilki ta ce "amma kuma, ai kinyi karatu kinfi ni nida na tsaya iyaka secondary school,"

Jieddarh tayi dariya tana faɗin "ai duk kanwar ja ce, don nima dai iya kana secondary school ɗin."

Waro ido Bilki tayi ta ce "haba yanzu kamar ke haka kin kammala secondary shine  saboda jin daɗi, kika tsaya a haka baki ɗaura ba,  ni ina mamakin abin da ya hanaki shiga University, gaskiya da walaki,"

Jiiddarh ta ce "bana ra'ayine kawai, that's why, ba wani abu ba," 

Bilki tana ya musta fuska alamar ita bata yarda da abin da Jieddarh ɗin ta ce ba, ta ce.

"haka kawai saboda iya shege kice bakya ra'ayi kawai dai da wata a ƙasa ki yarda da wannan madam,"


Zata kuma magana taji durar motar Heesham zumbur ta miƙe tsaye, ɗaukar gyalenta tayi ta nufi cikin gidan babu magana.


Girgiza kai Jieddarh tayi kurum a fili ta ce "gaskiya ni bansan wani kalan soyayya Bilki take ma Heesham ba, sai kace aikin sihiri?."


Ita kuwa Bilki da sauri ta ƙarisa parking lot a daidai lokacin da Heesham ya fito daga motar hannun shi riƙe da briefcase, har zai wuce ya jiyo muryar ta tana faɗin.


"yaya Heesham,"  juyuwa ya ɗanyi, aikuwa sukayi four eyes da Bilki zuba mata kyakyawan idanun shi yayi yana jira yaji mai zatace, gabaɗaya sai taji ta ruɗe ta duburburce da kyar ta iya haɗo kalmomi ta haɗasu guri guda.


Tana ɗan inda inda ta ce "amm uhm yaya Heesham 'welcome back home' ya gajiya?, umm dama nace kawo jakar naka na riƙe maka kaji?," da kyar ta iya haɗa kalmomin ta faɗa saboda yadda ya zuba mata ido ba ko kyaftawa.


Baice komai ba ya miƙa ma ta briefcase ɗin, hannun ta na rawa tasa ta karɓa, shikuma yayi gaba tabi bayan shi hadda ɗan saurinta.


Gabaɗaya Bilki ta manta da babin wata Ni'ima da irin laifin da ta mata har, saida suka shiga palon sukayi ido huɗu da ita, zaune saman 2sieter ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana taunar cingum

Hango shigowar  Heesham ne yasa ta wani taso da saurinta zata rungumeshi.


Da sauri ya matsa gefe yana kwaɗa mata harara sannan ya fara magana  kai daga jin maganar kasan ranshi ya fara ɓaci da irin halinta.


"Ni'ima meyasa bakyajin magana ne, dubi shiga ki fa, ya miki kala da shigar yaran musulmai?, kuma na faɗa miki ba sau ɗaya ba, akan, ki dena ƙoƙarin hugging ɗina, cuz keba muharrama ta bane, amma ba kyaji ko, so this is the last warning da zan miki akan wannan ugly ɗabi'ar taki.


Cike da shakwaɓa Ni'ima ke faɗin, "haba my world, mana yanzu miye laifin wannan shigar tawa?, sai kace baka waye ba, come on mana, ka shigo zamani mana,"

Ta faɗa tana kuma yin juyi a gaban shi. cike da takaici ya kalle ta.

Ya juyo ya kalla Bilki da tayi tsuru tsuru, yace "duba nan, dubeta, a tsakanin ita dake wacece tayi shigar rashin da'a fisabilillah faɗamin?,"  kallon Bilkin ita ma Ni'imar tayi taga shigar jikinta ya mutsa fuska tayi tana faɗin, "haba my world dubeta fa, wannan ai shigar ƙauyawa tayi.


Da sauri Bilki ta kalla Ni'ima jin abin da ta ce lallai ta latsa ta, ita Ni'imar sanye take cikin €nglish gown black color, mai hannun vest ko gwiwar ta rigar bata kaiba gashi ta ɗameta ɗam numfashi ma, da kyar takeyi.


Bai tsaya jin abin da zata kuma cewa yayi gaba abin shi, da sauri Bilki tabi bayanshi, suka bar Ni'ima a tsaye kamar gunki.

Suna shiga bedroom ɗinnashi dake upstairs ta aje mishi briefcase ɗin a palo ta dawo down ta sauko bataga Ni'ima ba dan haka batama damu ba garden ta koma gurin Jieddarh zuciyarta qhal💦


D̬̂â̬ĝ̬â̬ Â̬l̬̂k̬̂â̬l̬̂â̬m̬̂î̬n̬̂


*🌼ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ🌼*


🅰🅱🆄🅹🅰


**

Yau juma'a wanda yayi daidai da kwanakin Dije {Deejarh} biyar da zuwa gidansu Afeefah kuma yaune gwaggon ta wato Auntie sa'adah zata koma ƙauye, Zuwa yanzu Deejarh ta fara fahimtar kaɗan daga cikin halayen mutanen gidan, farko dai kamar:


'𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉' ta fahimci mace ce ita, mai masifar rashin son shiga jama'a bawai kuma miskila bace, a'a ita haka halinta yake, sannan kuma ta fahimci tana masifar ƙaunar ƴan uwanta sannan kuma tana da kirki sai dai bata nuna kirkinnata kamar   AFEEFAH ita NAINARH nunawa take kamar bata da kirki, amma idan ka zauna da ita zaka fahimci ko wacece ita.


'𝑵𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉' ta fahimci itaɗin mace ce ƴar bin ra'ayin kanta kamar mahaifiyarsu MOMY RAFI'AT sannan kuma kirkinta ragagge ne bisa kowa na gidan.


'𝒁𝒂𝒚𝒏𝒆𝒓𝒃' ita kuma Deejarh ta fahimci ZAYNERB mace ƴar komai saina shiga ma'ana ita dai ZAYNERB akwaita da neman rigima amma ga ƴan uwanta kuma rigima irin wacca za'ayi wasa da dariya.


'𝑯𝒂𝒍𝒆𝒆𝒔𝒂𝒕' cabɗi sarkin miskilanci kenan yadda Deejarh ta mata laƙani, don ta fahimci a rana guda ma za'a iya ƙirga adadin magana da HALEESAT tayi, sannan ta lura Haleesat mayyar Bacci ce, sannan kuma na lura Haleesat tana tafiya Club, sai dai bata yi gigin faɗawa kowa ba, sakamakon dalilai.


'𝑳𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉' ta fahimci ita kuma ƴar Ji_ji da kai ce, ga kuma mugun iyayi, da alfahari da dukiyar iyayenta, sai dai ita ma tanada kirki iya nata, sannan kuma ta iya yaɓa magana babu taunawa ko wata kala ce kuwa.


'𝑨𝒇𝒆𝒆𝒇𝒂𝒓𝒉' uwar gayya kenan, a gaskiya Deejarh ta kasance tanajin daɗin zama da AFEEFAH fiye da kowa a cikin gidan MISTER MAI KYAU har shi kanshi dama matar sa MOMY RAFI'AT

Deejarh ta fahimci Afeefah mace ce ita mai masifar kirki highly domin kuwa ba ruwanta da kowa bata faɗa da kowa, haka zalika kowa nata ne ba ruwanta, sannan bata ɗaurawa kanta Ji_ji da kai ba sam, sosai akwai bambanci mai yawa tsakaninta da ƴan uwanta especially ma LAILAH, sam Afeefah bata wulaƙanta kowa akan dukiyar da mahaifinta yake dashi. ko kuma wai irin ta nuna bambanci tsakaninta da ƴan uwanta akan ƙaunar da mahaifinsu MISTER MAI KYAU yake nuna ma ta sama da kowa sam bata haka, sannan tun zuwan Deejarh gidan bata taɓaji Afeefah tayima wani ko wata daga cikin ƴan aikin gidan tsawa ko masifa ba. ba kamar Lailah ba da a gaban Daddynsu ta mara ƴar aiki akan 'As depleted ta zubo mata tea a jiki ba tare da ta sani ba.


Afeefah tana da kirki fiye da tunanin mai tunani, sannan Babban mafarkinta a duniya shi ne zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya gabaɗaya, Burinta kuma shine zama Babbar Likita da ƙasarta zatayi alfahari da ita, Fatan ta kuma shi ne zama House Wife ta gari💃


________________________________________________________________________________


Tun safe ake abu ɗaya da Deejarh, ta maƙale akan sai tabi gwaggon ta ƙauye ita kuma gwaggon ta ta ce, ba za ta koma da ita ba, yanzu ma haka abin da ake ciki kenan da ita.


Tsaye suke a parking lot Afeefah, Deejarh, Auntie sa'adah sai kuma Zaynerb da Lailah dake gefe suna kallon ikon Allah.


"Deejarh ki bari ta shiga mota, mana driver yaja su tafi, kinga lokaci yana ƙurewa fa, ko kinaso tayi dare a hanya ne?,"

Duk wannan maganar Afeefah ne takeyi ma, Deejarh a hankali kuma cikin rarrashi.

Deejarh tana sha re hawaye ta ce "to zata dinga zuwa dubani, a koda yaushe, da yaushe 😳.

Da sauri Auntie sa'adah ta ce "E, mana Dije na, ai duk wata zandinga zuwa duba ki ba fashi,"

"toki rantse min," cewar Deejarh iya gaskiyar ta.

Dariya Afeefah tayi ta ce "ai ba seta rantse ba, idan ma bata zoba nida kaina zan kaiki ƙauyen, ki ganta ko," da kyar dai akasamu Deejarh ta bari Auntie sa'adah ta shiga motar driver yaja, suna ɗagama juna hannu har suka fice daga gidan.


Su kuma suka koma ciki suna shiga Deejarh ta ɗare saman 3sieter kamar ba ita bace ta gama kukan rabuwa yanzu, zama Afeefah tayi a gefan Deejarh tana faɗin "dubeki kamar ba kece mai kuka yanzu ba,"

Dariya Deejarh tayi ta ce "to ai ni haka nake, yanzu zakiga ina kuka anjima kuma dariya."


Zaynerb ta kalla Afeefah lokacin da ta zauna a kujerar kusada ita ta ce.

"ni banga kina wani shirye shiryen gasa bane fa, kallon Zaynerb Afeefah tayi ta ce "shirya shirye kuma sai kace wacca zatayi aure?,"

Lailah tana shafa wayarta ta ce "bawai haka ba, amma ai ya kamata ko ɗan gyaran jiki kiyi ko?."


Baki Afeefah ta saki tana kallon Lailah sai kuma tayi dariya, "lallai Lailah bakiji da kyau ba, kawai saboda wahala sai naje ina wani gyaran jiki saboda gasa, a'a to bada ni ba,"

 Lailah ta ce "Wallahi da gaske nake fa,"


 Afeefah ta ce "nima ai da gaske nake,"


"nifa yau banga wulƙawan Auntie Nailah ba kwata kwata, Zaynerb tayi maganar.


Deejarh ta ce "ai lokacin da kika tafi makaranta ne suka fita ita da wannan ƙawan nata mai kama da jarumar india 'Pooja Hegde' ɗinnan, ni banmasan sunanta ba,"


"amma wallahi baki da kirki sadiqqa ce take kama da Pooja ɗin?," cewar Zaynerb tana dariya.


Dariya ita ma Deejarh tayi ta ce "Yasin Auntie wannan ƙawar Auntie Nailah ɗin, da pooja take kama har tsayin da hasken ɗaya, yanayin  gashinta ne, kawai bansani ba."


"ke kuma a'ina kikasan tsayin pooja ɗin?, uwar ƴan sanin kamanni?,"

Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "a cikin film mana,"

"wanne a ciki?,"  Lailah ta kuma tambayarta.


Ta ce "wannan wanda tayi ita da allu arjun ɗin mana na dai manta sunan shi ne."

"wai 'Alavaikunthapurramuloo' kike nufi?,"  Afeefah ta tambaye ta bayan ta faɗa sunan film ɗin, da sauri Deejarh ta ce "E, shi nake nufi.


Zaynerb ta ce "ai tafi jaruman india na yankin telugu kyau gabaɗaya."

Lailah tace "a'a wasa dai kikeyi ko amma me za'ayi da wata 'pooja' bayan gasu 'kajal aggarwal' a gefe,"


Zaynerb ta ce "wake maganar kajal, ai wannan ta tsufa,"

" a gurin ki ba, cewar Lailah, Afeefah ta ce "to Ladies a'ina kuka bar Rashi Khanna ɗin, gasu Tamannah Bhatia, Mehreen dasu Samantha duka a gefe,"

"faɗa ma ta dai sister," cewar Lailah ta ci gaba da cewa "ga kuma Shruti Hassan madam ina faɗamiki idanun nata kamar kamar me kyau da kyau aka haɗa fa."


Deejarh ganin suna magana suna haɗawa da turancine, gashi ita ba komai take fahimta ba, a zuciyarta ta ce "bari dai nima nayi turanci nan na haɗa da indian ci😎


Gyaran murya tayi sannan ta kalla Lailah dake kwance a  2sieter ta ce "Auntie Lailah na tambaye ki wani mana?,"

"inajinki da sauraronki cewar Lailah.

Deejarh ta ce "karfa kice bakyajin yaren da zan miki maganar dashi,"

Lailah ta ce faɗa mana baki da problem, to banda abinki Dije ta ƙauye yaruka goma nake ji fa, kuma duka na qware akan jinsu highly.


Deejarth ta kuma gyara zaman ta alamar za'a fara sannan ta ce.

"Menene is poonakaalu ahora?,"


Tashi zaune Lailah tayi tana faɗin, "ban fahimci me kike nufi ba, please ɗan maimaita muji, maimai tawa Deejarh tayi.


"Menene is poonakaalu ahora."


A hankali Lailah ta kuma maimai tawa ita ma, girgiza kanta tayi, "ke bansani ba, wannan ai hauka kawai kika haɗa."


"Ba hauka bane fa, tambaya tayi miki,"

Cewar Zaynerb kallon Deejarh Zaynerb tayi murmushi ta ma ta sannan ta ce.


"na farko dai da ta ce 'Menene' hausa tayi, na biyu kuma da ta ce 'is' turanci tayi, na uku kuma da ta ce 'poonakaalu' yaren telugu tayi, na huɗu kuma da ta  ce 'ahora' yaren spanish tayi."


"Nifa wannan dogon bayanin, ba ganeshi nakeyi ba jeki gundarin magana kawai kai tsaye," cewar Lailah.


Da sauri Afeefah ta ce "tana nufin ta ce 'ƙarfe nawa ne' fa, shine ta haɗa yare kala huɗu ko ba, haka bane?,"  tayi maganar tana kallon Deejarh ɗin, dariya tayi ta ce "E, mana Balarabiyar india haka nake nufi."


Fashewa da dariya Lailah tayi har tana faɗowa daga saman sofa.

Duk suka zuba mata ido, ita ma Zaynerb dariyar takeyi ba laifi.

Saida Lailah tayi dariya ma'ishi sannan ta dakata. Kallon Deejarh tayi cikin dariyar take faɗin, "amma fa, kinyi ƙoƙari waima, ke a'ina kika koya, wannan yarukan kala kala haka?,"


Deejarh ta ce "nima kawai naji na iya ne fa," dariya Lailah ta kuma fashewa da shi.


Afeefah da abin ya isheta buɗar bakinta cewa tayi, "Lailah kodai kin sama taɓuwa ne?,"  


Lailah ta ce "lafiyata qalau, kawai dai na manta rabon da, a sakani dariya kalar haka ne," 

"ai saikiyi da kyau an baki aiki cewar Afeefah.


"Lailah zoki rakani gidan Sunainah mana?," cewar Zaynerb tana miƙewa tsaye.

Tsayawa Lailah tayi da dariyar da takeyi ta kalleta "amma dai wasa kike ko?,

Zaynerb tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinta, ta juyo ta ce "da gaske nake, don akwai abin da nakeso ta koyamin, kinsan course ɗin da nake karanta shi ta karanta ko?,"

 

Tana faɗan haka ta shige ɗakinta, bata daɗe ba, ta fito sanye da hijjab blue black har ƙasa ga folder's rungume a chest ɗinta, kallon Lailah tayi ta ce

"zo mu tafi mana."

"Inason zuwa, amma wallahi ina tsoron karen gidanta,"  Lailah ta faɗa iya gaskiyar ta.

"ke matsoraciya, indai saboda kare ne, ba zaki ba to kisa ranki a inuwa domin karen yana ɗaure ma kaca."

"ke tayaya kikasani?,"

Lailah ta tambaya, Zaynerb ta ce "ita ta faɗamin, kinsan kuma ba zatamin ƙarya ba ko,"

Tashi Lailah tayi ta ɗauka gyalenta dake a gefen kujera ta yafa a kafaɗarta.


"Nima zan biku kinji Auntie Zaynerb, tunda na shigo gidannan, ban fita ba,"

Cewar Deejarh iya gaskiyarta, "idan bakyajin tsoron kare, kizo muje,"  cewar Lailah tana dariya, "banajin tsoron shi," 

"to zo muje," Zaynerb ta amsa ma ta.

Da sauri ta miƙe tsaye ɗakin da yake matsayin nata, ta shiga ta ɗauko hijjab ɗinta iya gwiwa fari.


"ke yanzu nanda maƙwabtan ne, saikin saka wani hijjab," cewar Lailah tana kallon Deejarh da koɗaɗɗen hijjabinta. Zaynerb ta kalla Deejarh ta ce "rabu da Lailah kawai don ta iya tonon tsiwa kala kala, ɗunguma sukayi wajen fita daga palon su ukun.


Suna taɓa fira a hanyar su har suka ƙarisa gidan, ƙwanƙwasa ƙaramar kyauren gate ɗin gidan, Zaynerb tayi shiru taji hannu tasa ta tura ƙofar tajita a buɗe.

Shiga gidan sukayi basuga mai gadi a kujerar shi, ta zama ba, basu kawo komai ba suka nufi cikin gidan a tsakiyar palo suka tsaya suna kwaɗa sallama, amma ba amsa.


"Kai kodai bata nan ne?," Deejarh ta tambaya, Zaynerb ta ce wata ƙila, wata ƙila kuma.....zata kuma magana saiga Babah Dije mai aikin ta fito, "yauwa Babah wai Ummyn Farhana tana nan kuwa?,"

Zaynerb ta tambaya, Babah Dije ta ce "aikuwa Ƴar nan bata nan ta fita ita da mai gidan, wato Alhaji Sohailu."

"to bata faɗa miki inda zata ba?," wannan karon Lailah tayi tambayar.

Babah Dije ta ce "eh inaga gidan surukanta suka tafi," "okay ba damuwa, idan ta dawo kawai kice mata munzo bamu sameta ba, Zaynerb ta faɗawa Babah ɗin hakan.

Da 'to' Babah Dije ta amsa musu, su kuma suka fito.


Lailah ta ce "danasani ma, ban biyoki ba, tunda dai batanan....Zaynerb ta ce "ai kin motsa jiki koba komai inagaa!....kasa ƙarisa maganar tayi ganin abin da ke gabansu, "kinaga mene?," 

Lailah ta tambaya jin Zaynerb ɗin ta kasa ƙarisa maganar bakinta.

A hankali takai kallon ta inda taga 𝑍aynerb ɗin ta saki baki da hanci tana kallo.




Post a Comment

0 Comments