TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina yajawo mini Page 13 -- 14

 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️

                           


  Narrnarhh Bukar✍️


 🌹Perfect Essential Writer's

Association🌹

  ✨ P. E. W. A✨



Wattpad:@AISHAABUBAKAR812

Arewabook:@Narrnarhh002






  




1⃣3⃣----1⃣4⃣



Da sauri Umma Kande ta ɗago da idanunta mamaki duk ya cika ta a zuciyarta tana cewa 'wato bancin ni akwai wasu ma kenan,babbar magana'


Katse mata tunani yayi da cewa"Su nasu ba irin naki bane hasalima tun daga tsatso ne ake bibiyarsu,sannan ita yarinyar nan da kuke gani hmmmmmmmmm"


Shiru yayi na ɗan wasu mintuna sannan ya cigaba da cewa"Akwai ƙalubale a rayuwarta ita da mamanta,sannan maganar samari wannan kusha kurumunku indai wannan ne kuke tunani akai bazata taɓa samun samari kamar na yaranku ba"


Can kuma ya miƙe tsaye tare da jijjaga yana wani sumbatu ,sai kuma ya ɗaga ƙafarsa ɗaya sama tare da sakin wata tusa mai ɗoyin gaske,tuni su Umma Kande suka toshe hancinsu.(Ni kuma da sauri da ƙara ɗora nose mask har uku akan nawa😷😷😷🙃)


Dariya ya sheƙe dashi tare da cewa "Akwai ƙamshi ko? "


da "Eh'' suka amsa masa, sai kuma ya juya musu baya tare da sakin wasu zafafan tusa ajere ,ji kake"ɓur ɓuɓurr ɓuɓuɓuurrr ɓuɓuɓuɓurrrrrrr" 


Haba saiga Maman Jummalo da amai daman ita akwai ta da saurin gurɓacewan ciki,ita kuma Umma Kande ƙara toshe hancinta tayi sosai.(Ni kuma ba arziƙi na fita da gudu ina haki don kar na sume ku gaza samun rahoto sai can kuma na dawo cikin bukkar😷😷😷)


Juyowa yayi tare da tintsirewa da dariya sai wani tattakawa yakeyi tare da juyi,sai kuma ya tsagaita tare da cewa"kuna son yaranku su auri mazaje ko wanni iri kuma masu kuɗi"


Atare suka ce"Eh boka Sankeru mai sha re kukanmu"


Zama yayi ya ɗaga hannunshi na hagu sama sannan yayi wasu surkullensa sai ga wata ƙwarya ƙarama baƙa ta bayyana a saman hannunsa,sai ya ajiyeta gabansa sannan ya saka hannunsa ciki tare da ciro wani ƙullin magani ya jefa musu haɗe da cewa"Ku nemi kare baƙi da fari ku yanka su sannan ku tara kofin da wannan garin maganin yake a ciki ,jinin karnukan ya zuba ciki sannan ku samu ruwa tafashashshe ku zuba maganin wanda ke haɗe da jinin ku ƙara tafasasu sannan ku bar ruwan yayi ɗumi sai kusa yaran su wanke fuskarsu sau uku uku,na tabbata auransu yazo,yazo yaaaazooooo ho ho ho!!!


Godiya suka shiga yi masa,Umma Kande ce ta ciro kuɗi a tunaninta yau babu abinda zai shiga tsakaninsu dashi amma daka mata tsawa yayi tare da cewa" Jikinku muke so don haka dole ku bamu,wannan dole ne,he he he!!!


Ai ba shiri suka zare idanu don sunsan babu daɗi haɗuwarsu dashi amma ya zasuyi tunda son abin duniya da dogon buri ya rufe musu ido.


Kamar wancan lokacin haka wannan karon ma ya kasance dasu kuma ya ɗau tsawan lokaci da ko waccansu yana masha'arsa da ita kana suka taho wanda lokacin kusan yamma ne,a haka suka biyo cikin dajin sai wari da hamami jikinsu ke tayi,sun iso bakin dajin da kyar sannan Maman Jummalo da fito da turare suka fesa sai suka tari mai machine wanda a nan ma sai da suka daɗe sannan suka samu mai machine ya ɗaukesu zuwa cikin ƙauyen daga nan suka nufo tasha sai gida wanda basu suka iso gida ba sai wurin 5:00pm na yamma,a gaggauce sukayi wanka sannan suka baje don huta gajiya.



***Tunatarwa***



****Shin bakwa tunani akwai mata masu irin wannan ɗabi'ar irin nasu Umma Kande da Maman Jummalo na son abin duniya da dogon buri a duniyar nan ???

Tabbas!!! Har yanzu akwai mata masu wannan ɗabi'ar zuwa wurin boka da neman biyan buƙata wanda a ƙarshe halaka suke faɗawa sannan imaninsu ya ragu!!!

Yake ƴar uwata mai daraja kisani zuwa wurin boka ko malamin duba ba mafita bace agareki hasalima ƙara nisanta kanki kike daga rahmar Ubangiji,amfaninsa na ɗan wani lokaci ne zai miki wanda a ƙarshe illarsa tafi dutsen Uhudu a girma.

Shin mai zai hana cikin salisalin dare a lokacin da wasu suke bacci ke kuma ki tashi ki ɗauro alwala kiyi sallar nafila koda raka'a 12 ne sannan kiyi wutri ki sallame,kina mai kirari ga Ubangijin Talikai akan ya biya miki buƙatunki na fili da na ɓoye kina mai ƙan-ƙan da kanki a garesa.Tabbas zakiga canji a rayuwarki imma kishiya ce ta tasoki a gaba kina sallar dare tare da azkar ɗin safe da na yamma wallahi kinfi ƙarfinta da tsafinta da ikon mai sama.amma karki ɓata lokacin a banza tare da aljihunki wurin zuwa gun boka,wai shin ba kuga Umma Kande da Maman Jummalo yadda suke wahala bane gun boka sannan koda ya biya musu buƙata a ƙarshe wahala ce zata koma.

Misalin nemama yaransu mazaje da sukayi wurin boka Sankeru bayan yace musu suna son kowani irin mazaje ga yaransu masu kuɗi suka aminta sun manta da kalmar kowani iri yana nuni da koda mara kyau ne ko kuma masu cutarwa amma suka yarda,zakuga yadda zasu ƙare a ƙarshe.Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu ya kuma tsafe mana imaninmu.******


         @@@@@@@@@@@@@

Cikin Labari


Maman Jummalo ce bayan sun ɗan huta sunci abinci ta ce ma Umma Kande wacca tayi ɗaiɗai da ƙafafunta a tabarma "ƙawas ina kike ganin zamu samu jinin karnuka har kala biyu ,sannan muyi yanda boka Sankeru yace damu?


"A tunani na mai zai hana mu samu gwarawa tunda kinsan suna cin karnuka da aladu"


" Haba! "


"Allah kuwa,ke bara ma kiji har tsire da balangun karnuka sukeyi"


"To ke ina kika san suna tsire da balangun karnuka" cewar Maman Jummalo tana riƙe baki tsabar mamaki


"Nima Musa ne wani zuwa da yayi yake bani labari,inyamurai da gwarawa suna cin karnuka sosai,ya ƙara da cewa acan Calabar suna da kwa'ta nasu na kunsu,inda ake siye da siyarwan naman aladu da na karnuka,shiyasa ma bayacin namansu don baisan ko naman alade ko na kare ne suka sa a abincin ba"


"Allah ɗaya gari bambam,to shikenan faɗuwa tazo dai dai da zama,kinga sai mu nema inda gwarawa suke a nan ko"


"Hakane kuwa,Allah ya kaimu gobe sai mu nema kwa'tan nasu,shikenan ma cika aikin boka Sankeru da wuri"


"Sosai ma kuwa,wallahi na ƙagara yaran nan suyi aure mu huta"


"Nima kuwa ƙawas"


Da wannan hirar su Umma Kande sukaci lokaci suna yi sannan Umma Kande ta nufo ɗakinta dan kwanciya kasancewar a ɗakin Maman Jummalo suke hirar.Ƴan matan nasu suna waje suna hira da samari sannan daga baya kowacce ta shigo gida wanda lokacin kusan ƙarfe 10:00pm da wasu ƴan mintuna,amma ko ajikin iyayen nasu.


         @@@@@@@@@@@@@


Kamar yanda suka shawarta akan neman inda kwatan gwarawa yake aiko sunyi sa'a don sun samu kwa'tan gwarawa a cikin Farin gida wanda yake hanyar Mando.Sun samu ana gab da fara yankan karnuka da aladu dayake da sassafe suka fita,nan suka fara ai watar da aikin boka Sankeru sannan suka nufo gida dan kammala aikin.


Haka suka yi exactly yanda boka Sankeru ya ce dasu don kar asamu kuskure.Yaransu suka taru wuri ɗaya kamar yanda boka Sankeru ya ce dasu.


Da Iklima aka fara,matsowa kusa da bottle ɗin ruwan tayi sannan sai Umma Kande tace ta wanke fuskarta sau uku,haka tayi yanda tace ba tare da musu ba,sai Jummalo itama tayi yanda Iklima tayi, sannan Zaliha.


Duk wannan abun da suke Nusaiba na gefe ta chatting abinta.Maman Jummalo tace da Nusaiba tazo itama tayi,dan taga alama batada niyyar yi kamar yanda ƴan uwanta sukayi.


Buɗar bakin Nusaiba tace"Nifa gaskiya bazanyi wannan abun ba,kawai kuyi haƙuri dan komai zakumin bazanyi ba"


"Laaaaa!ehhh lallai Nusaiba wuyanki ya isa yanka" cewar Umma Kande


Kowa a ɗakin duban Nusaiba yake da mamaki itako ko ajikinta don ta rantse bazata wanke fuskarta ba kamar yanda taji jiya Mamanta suna hira da Maman Jummalo.


Waiwaye


Alokacin da su Umma Kande suke tsaka da hirar yanda zasu samo jinin karkuna susa a maganin da boka Sankeru ya basu,ita kuma Nusaiba ta dawo kenan zata shigo ɗakin Maman Jummalo dan nuna mata wani sabon film a waryata dayake Maman Jummalo akwai son kallon fina finai.


Isarta ƙofar ɗakin keda wuya ta jiyo hirarsu akan aurar dasu zasuyi aikuwa tsayawa tayi wurin ƙofar ɗakin taji komai sannan ta wuce ɗakinsu a zuciyarta tana faɗin 'Wallahi ba auran da zanyi,kurum ina cikin cin duniya ta da tsinke zaku wani tado da batun aure to wallahi bazata saɓu ba wai bindiga a ruwa,bazan taɓa yin yadda kuka ce ba,bayan auran babu komai cikinsa sai wahala da bauta,gashi sugar ɗina Alhaji Sagir yamin alƙawarin dani zaije Dubai muyi sati ɗaya kuma nasan zan ƙara wayewa ,da sake wallahi inaaaa tabb!!


Ɗaukar buta tayi ta nufa bayi dan karma mamanta tasan da dawowarta gidan.


Cikin Labari


Maman Jummalo ce ta katse shirun da mamakin da ya cika ƴan ɗakin dashi "Haba Nusaiba gata fa muke muku,kowace mace ba tada buri inta girma tayi aure ta hayayyafa,kinga ba daɗinmu bane ace muganku haka ga samari Allah ya baku amma ba kuyi aure ba,kuma ku kanku kunsan da zunɗen ƴan layi da muke sha mu da ku"


"Nasan da wannan Maman Jummalo amma gaskiya kumin uzuri bazan wanke fuskana ba da wannan ruwan, shi aure ai nufi na Allah ne ,kuma yanada lokaci,idan lokacin aure na Allah ya nufa nayi ai zanyi basai kun ɓata kuɗinku".(Hakane kam Malama Nusaiba ikon Allah😂😂🙃).


"Yanzu Nusaiba watsa mana ƙatsa a ido zakiyi kenan ,kinsan wahalar da mukasha duk don faranta muku rai amma da abinda zaki saka mana dashi kenan" cewa Umma Kande


"Nifa sai dai ayi haƙuri amma bazan wanke fuskana ba wallahi" cewar Nusaiba tare da mikewa ta fita daga ɗakin,kowa ya bita da kallo haɗe da mamaki musamman su Umma Kande da Maman Jummalo don su kaɗai suka san wahalar da suka sha kafin samin wannan maganin.


Babu yanda suka iya tunda tace bataso ,ai ba tilas farin cikinsu ma shi ne su sauran yaran sunyi musu biyayya kuma suna sa ran haƙarsu zata cimma ruwa koda Nusaiba kaɗai ce batayi aure ba sun rage jin surutun mutane akan yaransu.


        @@@@@@@@@@@@@@


Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta sunata shirye shiryan fara karatun Sa'eeda a KASU.Babu laifi Sa'eeda ta ɗinka ƴan kalolin kayanta kala shida da hijabai uku da veils guda uku, sai takalma uku da jakar makaranta ƴar madaidaiciya sai kuma side bag ɗaya baƙa.Umman Sa'eeda ta siyoma Sa'eeda waya Vivo ƴar ƙarama second hand wacca batasha jiki ba saboda tasan zata buƙaci babbar waya tunda yanzu tana a university ne.


Haƙiƙa Sa'eeda tayi farin ciki sosai da wannan wayar duk da ƙarama ce amma ji take kamar iphone 14 pro max aka bata,tana tama Ummanta godiya yafi cikin kwando.


Kasancewar yau asabar,Umman Sa'eeda da ita suna ɗaki suna hira akan batun shirin fara karatun Sa'eeda ranar Monday


Umman Sa'eeda tace "Sa'eeda Monday zaku fara karatu,ina mai miki nasiha da kiji tsoran Allah a duk inda kike,ki guji ƙawayan banza wa'inda suke kai mutum ga halaka,ki maida hankalinki sosai akan karatunki,banda samarin banza duk da inada yaƙini akan tarbiyar da na ɗoraki akai,amma kiji tsoran Allah ba mutum ba,ki kasance mai haƙuri da juriya tare da yafiya wa wa'inda suka zalinceki,amma karki yarda a wulaƙantaki ko kuma a takaki ,ki kasance jaruma mai fuskantar duk wani ƙalubalan da zaizo miki a rayuwa hakan zaisa ki cimma babban rabo a rayuwarki,banda kwaɗayi da hangen nesa,kinga dai yanda Allah ya yayi damu don Allah ki gode masa banda kallon na sama dake a kullum ina baki shawaran ki dinga duban na ƙasa dake hakan zaisa miki natsuwa da kuma godewa Allah akan ni'imar da yayi miki bisa wasu"


Ta ɗau lokaci tana ma ƴarta nasiha game da rayuwa tare da hankaltar da ita abubuwa da yawa dangane da rayuwa,kasancewa University zata fara zuwa,akwai kala kalan mutane a can,wanda kamar bariki ne kazo nazo kowa yana yin yanda yaso ne babu takura ba kamar secondary ba shiyasa tayi mata nasiha duk da ta yarda ɗari bisa ɗari akan tarbiyar ƴarta.


Sa'eeda dai shiru tayi tanajin nasihar Ummanta wanda ke ratsa ƙashinta ya shiga cikin jijiyoyinta har ya kewaye ko'ina na jikinta,haƙiƙa jikinta yayi sanyi sosai kuma tasa aranta duk wuya duk rintsi bazata wofantar da nasihar Ummanta ba,kamar painti ne a dutse wanda baya taɓa goguwa ,haka kamar kwaɗone wanda aka kulleshi ta key sannan aka jefa key ɗin a tsakiyar taiku wanda babu ranar ɗaukowa to haka ta ɗau nasihar Ummanta.


Bayan ta kammala mata nasihar ne ta ƙara da cewa"Niko Sa'eeda na manta ban faɗa miki ba na samu aikin gwamnati za'a dinga biyana dubu #20,000 duk wata,kinga zan dinga saving ɗin #5000 a banki saboda registration ɗin karatunki na duk shekara,sai kuma #15,000 na dinga baki kuɗin mota sannan kuma sauran muci abinci dasu"


Murna Sa'eeda ta somayi don jin wannan abin alkhairi daya samesu,haƙiƙa Allah abin godiya ne,cikin murnar Sa'eeda tace "Ummina wani kalan aikin gwamnati kika samu kuma waya miki hanyar aikin?..................


**Maa shaa Allah Fans wani kalar aiki kuke tunanin Umman Sa'eeda tasamu???

**Shin kuna ganin Sa'eeda zata ɗauki nasihar mahaifiyarta idan ta fara karatu a University???

**Da gaske kamar yadda boka Sankeru yace auran yaransu Umma Kande da Maman Jummalo yazo shin yazo ɗin ko akwai matsala???

Duk ku tattaro ku hanzarto ku biyoni muje zuwa amsoshinku suna nan tafe✍️✍️✍️


Ina matuƙar alfahari daku my Esteem Fans🏵️🌹🌼,I love y'll💖💓💝💗


Daga alk'alamin 


🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.

[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 


[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 

Post a Comment

0 Comments