TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Tsantsar so page 5

 *Ep_Five.*



_Hazel Kuwa._



Tun bayan shigarta class ɗin su tsawon mintuna ashirin tana zaune bata ce da kowa komai ba haka ma babu wanda ya kulata, domin a ganinsu ita ɗin 'yar girman kai ce ita ba kowa ba sai shegen jama'a jijji da kai ga miskilanci shi ya sa bata shiga harkar kowa kuma kowa baya shiga nata.



Tana nan zaune tana shafa kwikwiyon cike son sa. Arissa ƙawarta da suke zaune benji ɗaya ta shigo class ɗin ta ƙari sa ta zauna tana a je littatafan ta saman desk.



"Barka da ƙari sowa amma fa yau kin makara sosai."



Arissa ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kwikwiyon dake hannun ƙawarta ta Hazel ta ce.



"Kedai bari kawai wani abu ne ya tsayar dani, kina lafiya?."



"Lafiya Qlau. Wani abu ne ke nan?."



Hazel ta tambaya tana kallon ta.



Ba tare da ɓata lokaci ba Arissa ta kwashe dukkan abin ya faru lokacin da suka haɗu da su Teema ta faɗa ma ta.



Hazel ta ce.



"Allah Sarki yanzu haka tana can Hospital ɗin ke nan ya jikin nata?."



"E tana can, lafiya Qlau, domin Doctor ya ce ba wani abu ba ne Kawai firgici ne ta shiga da alama this is the first time na Rayuwarta da ta shiga kalan wannan halin.''



"Ayya."


Shi ne kawai abin da Hazel ta faɗa da yake surutu bai dameta ba ita ma Arissa ta san hakan.



"Althaf fa kuna haɗuwa kuwa kwana biyu?."


Arissa ta kalla Hazel da ta jefo ma ta tambayar tayi Murmushi ta ce.



"Sama sama dai wai kuwa ma kin san cewa jiya saura ƙiris Yayana ya ganni da shi?."


Hazel ta zaro ivy eyes ɗin ta ce.



"Wani Yayan naki ke nan?."



"Hummm ina da wani Yaya da ya wuce Taufan Ali ne?."



Hazel tayi Murmushi kaɗan karo na farko sannan ta ce.



"Sorry na sha'afa ne sam kin san wannan Yayan naki baya shiga harkar kowa shiyasa ma nake mantawa da shi idan ba na ganku tare ba ko kuma nazo gidan ku."



"Hummm."


Kawai Arissa ta faɗa suka canza topic ɗin. Fira suke kaɗan kaɗan kafin su shiga Exam Class.



_________

_Taufan Ali POV_



Cikin tafiya da suke tare da sanyin idaniyar sa abar ƙaunarsa Ƙanwar sa Arissa da ya ɗauko ta daga Tahfiz na safe da ta tafi duk da kuwa yanayin da aka tashi a garin an sha ruwa daren jiya amma haka ta nace sai ta tafi Islamiyya domin suna dab da sauka ne bata son komai ya wuce ta, wannan dalilin ya sa Yayan nata Taufan ya rakota makarantar sannan ya jira har aka tashesu sannan suka kamo hanyar gida tana riƙe da Alkur'ani mai girma shi kuma yana riƙe da ƙaramar kekensa ta training, suna tafiya suna fira kaɗan kaɗan suka hangi Teema Ƙawar Arissa ɗin ita da wata kyakkyawar Budurwa tsaye ga kuma wasu Samari uku gefe sai kuma wata Budurwa da ke tangal tangal zata faɗi bayan buga ma ta sanda da ɗaya daga cikin samarin ya yi.




Arissa ce ta roƙe shi da ya daure ta taimaka musu don ganin yadda ya yi kamar bai gansu ba tasan dalili amma haka ta nace har sai da ya shiga aka yi da shi sannan ne komai da ya faru ya biyo baya.



Bayan ƙari sawa da ita Hospital da suka yi ne bayan Likitoci sun rufu akan ta, bayan wani lokaci Doctor ya fito yake faɗa musu su kwantar da hankulansu ba wani Babban abu ba ne kawai firgici ne ya sameta jin haka yasa Taufan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da bai san kona Mene ne ba, sannan ya umarci Teema da ta wuce ta faɗawa Familyn Samira abin da yake faruwa, nan ne ma take faɗa masa a gidan Sarki take. Bai ce komai ba yaja hannun Ƙanwar sa Arissa suka fito daga Hospital ɗin gaba ɗaya har da Teema domin bai ga amfanin ci gaba da zaman su ba don Doctor ma ya ce ta sama Bacci.



A hanya ne wayar Abokin sa Labib ya shigo masa. Umarni ya yi ma Teema da Arissa da su wuce gida ya bata Training Bicycle ɗin sa ta wuce masa da ita gida yayin da shi kuma kai tsaye ya wuce zuwa wurin da suka saba haɗuwa da Labib ɗin dama sauran Abokansu samarin unguwa. Yayin da Arissa ta wuce gida kai tsaye ta shirya sauri sauri ta wuce school domin ta makara bayan ta bawa kakannin nasu labarin abin da ya faru har yaja ma ta tseko.



"Mutumina sai yanzu ka ƙari so ke nan?."


Labib ya faɗa yana dariya ya miƙawa Taufan hannu suka yi misabaha ya ci gaba magana bayan sun zauna.



"Mutumina shawararka tayi aiki fa finally zan sama muradin zuciyata cikin sauƙi Hazel annurin Rayuwar Labib..."


Ya faɗa yana lumshe ido tare da jan Sunan daga ji zaka fahimci ba ƙaramin so yake ma Hazel ɗin tasa ba.



Abokansu suka kwashe da dariya, Taufan ya yi Murmushi kaɗan, nan suka ci gaba fira da mafi yawanci Labib keyi ba'a kan komai ba sai Hazel ɗin sa, yana faɗa musu Irin TSANTSAN SO da yake ma ta, inda sabo yaci ace sun saba da wannan surutun nasa akan Hazel da bata san yana yi ba ma, domin da sun zauna zaman Majalisa bashi da aiki sai maganar Hazel ɗin sa duk da kuwa yasan cewa ita ɗin ba musulma ba ce, Bama wannan ba, wayar gari aka yi aka gansu a garin ita da mahaifinta da Kakarta ba'asan daga ina suke ba shekaru uku baya ke nan, da yake Sarki Muhammad Raees mai adalci ne bayan gabatar da dukkanin bincike akan su ya fahimci ba zasu cutar masa da al'umma ba ya basu matsuguni cikin Garin....




_____

_Around 9:10pm_


_Arissa_




Kamar yadda suka saba kuma ya zame musu jiki ita da Yayan nata kuma Babban Amininta yau ma suna zaune ne tsakiyar gidan suna shan iska, Arissa tana daga saman tabarma zaune ita da Kakus da gaba ɗaya hankalinta yake kan Radio da take saurare suna taɓa fira jifa jifa da Mijinta Nakowa, Arissa ta kalla Yayan nata Taufan dake zaune gefe saman Plastic Chair yana shafa wayarsa cikin nutsuwa sannan ta ce.




"Ni kuwa Yayana ka koma Asibitin ne?."



"Asibiti kuma?."



Ya tambaya da alamun bai  mene abin da take nufi ba. Ko da ya gane to basarwa ya yi.



"E, na ɗauka ka koma duba jikin nata ne."



"A'a."



Ya faɗa a gajarce.



Tayi Murmushi.



"Okay Tohm Gobe da safe ina so naje na ganta Dan Allah zaka rakani?."



Ta tambaya tana marairaicewa.



Akwai abin da yake yi gashi ta addabesa ta surutun ta hakan yasa shi amsa ma ta da faɗin.



"Okay "



A taƙaice.



"Na gode Yayana."



Ta faɗa duk da tasan ta wuya ya kuma wata maganar.





_________

*_Hayy Gharb, Zamalek, Cairo_*


_Around 11:30am_


_Ambrah POV_




A hankali take taka katafaren matattakalan Benen da ya haɗu iya haɗuwa gaba ɗaya ƙamshinta ya mamaye katafaren palon. Strapless Dress ne jikinta Doguwar Gown da ta wuce gwiwarta kaɗan sai Jodhpurs  trouser da ya matseta a jikinta, ta yane kanta da veil mai kyau da dacewa, ƙafafuwan ta sanye Cikin wasu arnun strappy shoes black color tana riƙe da handbag nata neck ɗin ta kuwa maƙale da festoon necklaces, fuskarta wadace da make-up ba ƙaramin kyau tayi ba domin kyakyawa ce sosai tana tafiya cike da gadara ta ƙari sa saukowa Downstairs ɗin, har ga Allah bata lura da Iyayenta dake daga can side ɗin Dining suna Breakfast ba, take ƙoƙarin sa kai zata fice daga Palon tana karkaɗa car Key's ɗin ta.




"Baby Ambrah Ina ne zaki tafi da sassafiyar nan haka?."



Ta dakata daga ƙoƙarin fita daga Palon da take yi sannan ta juya ta kalle ta fara'ar da ta kasa ɓoyuwa daga fuskarta ta ce.




"Wurin Brother Taufan ɗina mana."



Ta bawa Oum ɗin nata amsa.



Gaban Oum ya faɗi ta kalla Mijinta tana masa nuni da ido na ya ce wani abu.



"Am Ambrah zo nan ɗiyata kiji."



Ya faɗa yana yafitota da hannu.



"A'a Abhie ko mene ne ka faɗa daga nan ina sauraren ka domin yau na rantse banga mai hanani fita daga gidan nan ba domin zuwa ganin sanyin ruhina."



Tsawa Oum ta daka ma ta.



"Ambrah kina cikin hankalinki kuwa Abhie naki kike faɗawa haka?."



Cuno baki Ambrah tayi tana rau rau da ido cikin dasashiyyar murya Irin na mai shirin kuka ta ce.



"Haba Oum ya ya kuke so nayi da rayuwata ne tun shekaran jiya na dawo ƙasar nan nayi nayi ku barni naje naga Brother Taufan da sauran Family amma kun hanani ban san me kuke nufi ba kuma kunsan wani matsayi yake da shi a Zuciyata."



Ta ƙari sa zancen cikin karyewar murya tana share kwalla.




Gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyi Tabbas su sheda ne akan kalar sun da Ambrah take ma Taufan tun tana ƙaramar Yarinya.



Dr Aadnah taja ajiyar zuciya tana tattaro dukkanin nutsuwarta ta mayar kan Tilon Ɗiyar tasu sannan ta ce.



"Please Ambrah ƙari so nan akwai abin da zan faɗa miki kinji Babyna."



Ambrah ba tare da tace komai ba ta fara taku har ta ƙari sa wurin Dining ɗin ta zauna gefan Mahaifinta Prof Yusuf El Mustapha tana cuno baki ita dole an ɓara ranta.



"Uncle ɗin ki baya wannan ƙasar a halin yanzu yana can New York har su Taufan suna can akwai wani dalili na zuwan nasu amma ina mai tabbatar miki nan da One Month gaba ɗayansu zasu dawo daga nan kinga sai ayi magana akan auren ku ko?."



Ta ƙari sa maganar wa ɗiyar ta ta cike da alhini na abin da zata faɗa.



A firgice Ambrah ta miƙe tsaye cike da tashin hankali ta ce.



"What..! New York Oum kuma Dukkannin su Oh My God amma me yasa baki faɗa min ba, ai dana wuce can kai tsaye kawai da ban dawo nan ƙasar ba."




Gaba ɗaya suka kalle ta da tsaban mamaki na kalamin dake fitowa daga bakinta...



* * *


Fitowarsa ke nan daga Bathroom yana sharce ruwan dake ɗiga daga jikinsa da alama wanka ya yi ya hangota zaune gefan Bed ta zabga uban tagumi hannu bibbiyu. Da sauri ya ƙari sa wurin tare da tambayar mene ne yake faruwa ne ta shiga wannan yanayin. Ta kallesa ta ce.




"Prof an ya kuwa akwai Alkhairi a wannan lamarin gani nake wannan makaucin son da Ambrah Ɗiyata ɗaya tilo take ma Taufan Yaro wurin Yayana  Ali Taj Ozan kamar tayi yawa gani nake shi baya ma ta son da take masa tunda har ya iya barin ƙasar da take ba ko waiwaye, nifa na fara karaya da wannan lamarin ka duba fa yadda take kuka ɗazu baji ba gani."




Ta ƙari sa maganar cike da rauni. Ya yi Shiru yana nazari tare da matsota jikinsa yana lallashi.




"Aadnah."



Ya kira Sunanta. Ta amsa sannan ya ci gaba da faɗin.




"Tabbas gaskiya kika faɗa son da Ambrah take ma Taufan yafi wanda shi yake ma ta idan yana matan ke nan, saka kanki a damuwa ba shi ne zai kawo mafita a lamarin ba fa ce ki bisu da addu'a kawai, sannan ina tunanin baki manta cewa bawai da gangar ya tafi ya koma wata ƙasar ya shantake ba, wasiyyar Mahaifiyarsa da ta bar masa yake ƙoƙarin ganin ya cika, kuma in sha Allah komai ya wuce dama Deal ɗin na shekara guda ne, kuma cikin iznin Ubangiji cikin wannan shekara ɗayan kwanaki kaɗan ne Kawai suka rage, a shawara ki daure ki ci gaba da lallashin Ɗiyar ki har Ubangiji ya yi dawowarsu lafiya shi da ƙanwar tasa sannan muga mene ne abin da zai biyo baya kinji Doctor na?."



Ta sauke ajiyar zuciya tana gyaɗa masa kai cike da gamsuwa da baya nansa ta ce.



"Shikenan babu damuwa in sha Allah zan yi ƙoƙari wurin yin hakan."



Ya yi Murmushi.



"Yauwa ko kefa, kawai kinje kina sakamin kanki cikin damuwa da bata miki kyau sam."



Tayi Murmushi ita ma kaɗan.



Nan dai suka ci gaba tattaunawa akan Babban lamarin dake gaban su na dawowar Taufan tare da Arissa da kuma yadda zasu runkaresa da maganar aurensa sa da suke son haɗawa Ambrah.



Post a Comment

0 Comments